Share this page
4 / 9
Amir din dake zane su ya sake sara masa yana furta" Morning sir" dan gaba daya yanzu Amir ya daina yi masa gaisuwa irin ta cikin gida, a ko'ina ya riga ya bi jinnin jikinsa gaisuwar nan itace yake yi masa dan girmansa karra hauhawa yake a idannuwansa Bai iya amsawa kowa ba, sakamakon abinda ya dane masa harshe A hankali ya furta" Hajia fa?" Amir ya sake matsowa yanna fadin" Na'am Abah?" SULAIMANE ya dan kalle shi gannin bai ji ba hala? Sai kuma ya juya wajen mai bodar ihun kukan nan tamkar wata tinkiya tana ihun ta shiga uku wayo Allah ta shiga uku, ya sake juyowa inda Amir yake a hankali ya ce" Ka hannasu kuka da ihu mana, hakan na saka ciwon kai, su yi a hankali......ko ba komai ai mata ne............." Da sauri ya juya ya ce" Ke yi a hankali mana ko meye wannan shirmen kamar na kashe ki?" "Ka ji tsoron Allah Amir, ka ji tsoron Allah, haba dan Allah dan kawai nace ka masu abinda ka ga dama kuma kukanma hannasu zaka yi baki bude? Zahra ba zaki fadi amsar da ake tambayarki ba ko?, Shikenan ki yi , ki ci gaba da yi Zahrah na gode.......!" Mamah ta fada muryarta na neman nuna rauninta a kan yarinyar Hankalin FATIMA ne ya sake tashi, hankalinta tashe take girgiza kanta a rikice ta ce" Mamah, dan Allah kar ki koreni mamah, dan Allah mamah kar ki koreni, saurayina ne shine yace na zo zai ganni shi yasa na je" Ido suka zarro gaba dayansu banda SULAIMANE dake tsaye kikam yana kallon ikon Allah "Ji sakarci, saurayinki kike fada mana a nan?" Amir ya fada yana katseta da muguwar tsawar da ta sakata hade kanta da gwuiwa tana sake fashewa da kuka A sanyaye Hajia ta ce" kora kuma na koreki gidan uban wa wai?? Saurayi kuma Zahrah, saurayi gareki har ya isa da ke ban sani ba? " Da bacin rai Amir ya ce" Da an fara yi mata fada ko duka sai tana wani abu tamkar mahaukaciya, bari ki ji Zahrah babu wanda zai kore ki a gidan nan dan gidanku ne, duka ne zaki ci tamkar jaki idan bakya jin magana babu abinda za'a yi dan haihuwarki aka yi, an isa da ke , saurayi ne ya fitar da ke a irin lokacin nan ko? Ba ke ba shi daga yau dan ubansa kina da darajarki ba zai wulakanta mana ke ba!" "Wayo Allahna, innalilahi wa inna ilaihi rajune, yaya dan Allah ka min rai kar ka shiga tsakanina da shi domin ina sonshi tamkar rainah yayana" Fatima ta saki maganar a tsume tana nade kanta dan ta sani ne yanzu zata ainahin daku ba dukkan dazu ba Da sauri ya sake cira kansa ya sauke mata duba daya tak, sannan ya girgiza kansa ya juya ya karasa inda Hajia ke sallalami tana neman fashewa da kuka, Ζ΄aΖ΄anta mata sunna tayata harda wace ta silale ta dora hannayenta biyu saman kanta tana fadin" Mun shiga uku, yau ba ke ba muma sai mun sha dukan safe innalilahi haba Zahrah me mukai maki?" Hannun Hajia ya riko , hakan ya sa ta dube shi tana sauke ajiyar zuciya muryarta a birkice ta ce" Baban gida ka ji wani balakin ko?" Bakinsa ya dan tabe , bai bata amsar nan ba a hankali ya ce" A asibiti Manal ta kwana, bata da lafiya ne Hajia " Hajia ta yi dan tsam, har a ranta ta ji babu dadi, ta kuma tausaya fiye da tunanin bawa, dan kuwa a yadda ba wani zuwa da zowa tsakaninsu da Manal din sai idan wata sabga ta tashi ta yi kokari ainun ta hanyar nuna damuwarta tana fadin" Subahanalah, aya , zazabin nan ne ko? ALLAH ya sawaka , Baban gida kana jin me y'ar cen tace kuwa? Ka ji zata tona min asiri ko babah? ya dace ka mara nasiha" A hankali dan makoloton wuyansa ya yi sama kadan sannan ya yi kasa , ya lumshe idannuwansa sai kuma ya sake rike hannunta a hankali ya ce" Allah ya sanyaya mana Mamah" Hanci kawai take ja, har ya saki hannunta ya juya bata ankara da mutuwar gwuiwarsa na rashin binsa da bata yi ba, batama lura da yannayin da yake ciki ba sam, hankalinta ya fi karkata wajen da Amir ke neman karya mata ya'ya, domin ba Zahra kadai yake jibga ba harda sauran , yace ne tabas sun san me yake faruwa suka yi shiru, yau ko shi ko su A lokacin da ya kusan fita gaba daya daga bangaren ne Hajia karama ta karaso, wato Aunty Amarya mahaifiyar FATIMA ZAHRAH Dan ja ya yi kadan, da girmamawa na matsayinta na matar mahaifinsa ya sake maido mata gaisuwar da take yi masa yana kokarin kore damuwar da ya kunso a ciki Aunty Amarya da kula ta ce" πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ• *DAƘIƘA BIYAR* πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ• _MALLAKAR_ *SAJIDA NIGER* *Da sunan Allah mai rahama mai jin Ζ™ai* _6_ *Garabasa , garabasa, 😁πŸ₯°, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°* Aunty Amarya da kula tana dubansa ta ce" Baba asibitin zaka koma ne? Muma gamunan zuwa yanzu yanzu abin kari na saka a sake hada min da gagawa, Allah ya bata lafiya" Sai ya ji wani sanyi a zuciyarsa, irin yadda ta nuna damuwarta da kuma yadda ta nuna gasunnan a zazafe din kan ya saka shi yin dan murmushi yana bata hanya ta shige ciki shi kuma ya nufi wajen motar Amir ya bude ya shiga yana tunanin ko yaushe Amir zai daina barin ky a mota? Yana tafe ne yana jin wa'azin Docter a kan girman aure da irin yadda ma'aurata ya dace su ringa girmama darajar aure har ya tsaya a bakin danja.............. A hankali ya jimke hannunsa na dama jijiyoyin jikinsa na sake daukan mugun yannayi na bacin ran da yake ciki Bai san dalili ba, sai ya shiga tunanin wasu manyan kalamai da yakan yi a zamanin da.....kalaman sunne kamar haka *So daban rayuwa ma daban, bai zama lallai sai ka rayu da wanda kake so ba idan Allah bai kaddara hakan ba, amma ita kaddarar aure girmamata a garemu wajibi ne, hakika zuciyata kauna take so, nima kauna nake so.........................., Ina iya zabar kauna bayan a tunanina a yanzu na wuce wannan bigiri din......?.................. So TAMKAR RAI.......uhum* Da salama ta shigo falon, itama ta shigo ne a daidai lokacin da Amir le sake tsulawa Fatima bulalar hannunsa, dan a duniya shi yakan rasa nutsuwarsa a gaban mutun mai gardama, Fatima kuwa ta zamto top sai dai ace Allah ya shirya, ta budo baki ta fadi sunnan mutumen da ta gama rantsuwar ba ita ba shi ne ta kasa, a yanzu kuma ji take yi kamar za'a rabata da ranta ne dan za'a rabata da masoyinta Kallon wajen sau daya tak ta yi, shima a rashin sani, tun daga nan bata sake kai dubanta ba ta nufi wajen da Hajia ke tsaye ta kasa barin wajen sai zufa take yi tana faman sai an ji sunnan tana kuma hada Amir da Allah kan ya daina tsulawa da karfi mana sai ya kashe mata ya'ya ne? Tana murmushi ta ce" Barka da warhaka Hajia" A fuzge Hajia ta amsata tana dauke kanta, dan hankalinta ba a kanta ba yake kwata kwata "Amir, idan ya gagara barta ka ji? Dan Allah ka barta" ta fada tana dan daga muryarta, shi kuma ya yi kwafa ya ce" Hajia kin san Allah, sai ta fadi sunnan nan yau ko na wuni ina zane su, su suma su farfado ba zan gajiya ba, ni da su a ga kyasashe yau!" "Hajia, dama nace wa zai zauna a wajen Manal din ne? Inaga da wuya a sake su yau fa" Aunty karama ta fada , muryarta a sanyayen nan tana dan sake rage tsayinta dan girmama Hajiar Da haushi haushi Hajia ta juyo tana kallonta ta ce" haba ke kuwa , bata da dangi ne da zaku wani nemi kwasar mata mutane ku kai salon a zo ana raina mana wayo? Danginta su zauna mata kawai " Dan shiru Aunty ta yi, dan bata so hajia na yin haka dan matar babban gida bata da kula, shi ya dace a duba a kyautatawa, baban gida ai baban gidan ne walahi A sanyaye ta ce" to shikenan, ki kimtsa mu je Hajia Bara na koma na hado kayan karin" Harara hajia ta maka mata tace" Ama ai kin tardoni cikin wani aikin mai mahinmanci ko? Ko dole sai da Ni za'a tafi?". Kanta dake kallon kasa ta dago a hankali ta kalli hajia, ba zaka taba yin doguwar magana da hajia bata hada maka ciwon kai da hawan jinni ba, ama a haka hajia itace mutun mafi dadin zama da zuciya daya a kan sauran, ita zata zaga gaskiya komai dacinta, kuma zata fadeta a gabanka sai dai ko wace wace Tana kallon idannuwanta ta ce" Eh hajia, dole da ke zamu tafi, kuma yanzu zamu tafi, sai mun fito" Daga haka ta yi gaba ta bar hajia baki bude ta mutu da takaici, Tsaki ta ja ta ce" Ka ga fitsara ko Amir? Matan Docter babu wanda ya kai wannan mai shegen kyan iya tafka fitsara, to zo ki kuleni ki kaini!" Amir da ya sarara da zane Ζ΄aΖ΄an sai susa suke yi sunna kuka ya ce" kai ku yi kasa kasa!" Sannan ya kalli hajia ya ce" Momy ki tafi mana,na ji da sauran" Hankali tashe Ummi ta ce" Momy dan girman Allah ki kwace mu, ni dai sunnansa kawai na sani wani ko Ma'awiya ko makawiya?, Bayan nan ban san sauran ba Allah momy, asalima shi kadai take kulawa a sanina kamar wani wanda ya fi sauran mazan wani abu" Da takaici ya ce" Ke makawuya ne ko Ma'awiya sunnan?" Baki na bari Zahra da fuska ta yi mata sundum , jiki ya mata luhu luhu ta ce" Ma'awiya ne" Amir ta tabe baki ya ce" Ba damuwa, Allah ya hadani da shi, sai na ci ubansa shi dan iska, idan kanwarsa ce aka fitar na san sai ya ji ba dadi, ku bace min da gani maza ku shirya na kaiku makarantar da kaina, ku yi aniya na sako ku a gaba walahi ni da ku a ga kyasashe, ku ba bakwa jin magana ba? Har kun kai wajen take dokar Malan? Da Ζ΄aΖ΄an gidanmu ake koyi baku isa ku cenza haka ba, a kan tarbiyarku sai na baka banza na yar, kuma ku yi aniya Baban gida ya saka maku hannu shashashu!" Zungwai zungwai suke wucewa ta gabansa bayan sun duka sun yi godiya sai an fara hawa sama a zabga da gudu ana sake fashewa da kuka har gogar ta shige itama fuska ta sundume mata Rai bace Hajia ta ce" Yanzu Amir ban hannaka dukan min ya'ya da hannu ba? Ba'a dukan mutun da hannu bale mace, ka kuma dukar mata fuska, kar ka ringa yin haka bashi da anfani, ya dace ka ringa binsu ta laluma kar su tsaneka, ka ga walahi sun fi jin tsoron yayanka a kanka, shi ka ga bai taba dukansu ba, bai kuma taba zaginsu ba, karewarta zan kawo masa kararsu sai dai ka ji yace wanen? Idan aka ce eh sai yace wane kar ka kuma ka ji? Daga nan kuwa ba za'a kuma ba, kai ba zaka yi koyi da shi bane?" Murmushin da bai shirya bane ya subuce masa, uhum lalle, sai a bar iyayensa, da ace sun san waye dansu a cikin gari da kuma wajen aiki da sun ce ikon Allah, ai yadda ba zai tsaya ya yi yawan magana da kai ba a cikin aikin aikatawa ne maganar tasa zata fito, to dama yaushe zai tsaya yana an yi ba'a yi ba da kai? Yana iya bada fili ku daku kai da shi ne kawai in hakan ka fi so, in tsagera kake kama ce masa sai an kuman mana ko ka kuma maimaita abinda ya hanakan, a nan ne zaka gane me ake nufi da baba baba ne Zama ya yi yana shan ruwa , sannan ya dubi mahaifiyarsa a tausashe ya ce" Momy, yaushe zaki shirya din ne?" Sai a lokacin ta sake tunawa da maganar, Baki ta tabe ta ce" Ba inda zan je Amir, ita wani damuwa ta yi da mutane daga iya har danginta?, Ni babu inda zan je rashin lafiya ne Allah ya bata lafiya!" Kureta ya yi da kallo yana ta tunanin ta inda zai biyo mata A sanyaye ya ce" Mamah, ki yi hakuri ki jure ki tafi, ba dan komai ba sai dan yaya, Mamah ki yi dominsa, ki faranta ran danki mai faranta maki wanda baya hadaki da kowa, kar ki manta mamah rai ake gaisarwa, kar kuma ki manta shi ya kawota cikinmu, shi din kuma namu ne, bamu da kamarsa, ko da me ta zo mu mun yarda dan wanda ya isa ya kawota kin ji maman Baban gida?" Sosai take kumbura tana cika tana batsewa, da kyar dai ya samu ya samu kanta har ta sauke ajiyar zuciya ta yarda zata je din, ama wai sai zuwan rana Shi dai a haka ya fice yana jiran yan matan har suka sauko suka yiwa Mama salama kowace sanye da nikaf dinta da saffar kafa da zumbula zumbulam hijabansu suka karasa suka shige motar ya dauki hanya yana kallon inda ya saka a kimar masa shegen mai gadin nan dake bata hanya, domin a jiya tana tafe kamar Yar maye yana biye da ita a kafa, dan tunda ta fito daga motar nan shi kuma ya shanyo kwana ya daleta da fitila sai ya labe ya bar motar ya sauko a kafa ya rakota har fitar yayansa a kan idannuwansa, dalilin da ya sa ya kwana a gidanma dan sai da ya yi dan bincikensa a kan masu tsaron kofar gidan Tukin garari ya yi da su a hanya har ya sada su da kofar makarantarsu mai hade da Islamiya ya ja birki da garaje ya juyo yana nuno su da yatsarsa ya ce" A cikinku wace bata dauki gargadin da na yi mata da kunnen basira ba dan Allah ta sake mayar da hankali wajen aikata laifin da na hannata, in sha Allah zamu baje kolin rashin ji kowa ya dauki kasonsa!" Su dai basu ce komai ba, Allah Allah suke yi su bar masa wajen kowace ta fice da sauri ta shige ciki Ajiyar zuciya ya sauke a ransa yana ayyana ' Allah dan girmanka ka kare mana su, ka tsare mana mutuncinsu, ka sa mu yi masu aure mu mika su dakunnansu cikin mutunci, ya ubangiji idan da wata mai mumunar kadara a cikinsu ka cenzata zuwa kyakyawa alfarmar annabi da Alkur'ani.....' Sai kuma ya tayar da motar ya nufi asibiti, daga cen zai wuce office dan ya san da wahala yau MarΓ©chal ya samu dogon zama a asibitin Jiki ba karfi suke tafe daya na bin daya a bayanta har suka karaso wajen da zasu rarabu Babar cikinsu ce ta ce" Ke Zahrah zo nan" Dakatawa ta yi da tafiyar da take ta juyo, idannuwanta suka sauka a kan Furera wace yau basu yi mota daya ba, kennan basu dambatu yau ba A tausashe, sai dai amon muryarta da dan zafi ta ce" Kin ga abinda zan fada maki a kan maganar wannan saurayin naki shine ki raba kanki da wahala, bana son abinda zaki kuma janyo mana ko barcin asubahi bai sake mu ba a ringa kwalo da mu kamar gangunna, ke gaki da taurin rai ko kasheki za'a yi ba zaki yi magana ba, to walahi mu dai bama so kin ji na fada maki, kar na kuma jin wai ya neme ki har kin amsa shi dan miji goma ba uba goma bane, bale kuma saurayi goma ba uba goma bane , ki rufawa kanki asiri Allah ya fitar maki da miji ki yi tafiyarki dakinki salim alim , kar ki ja mana Baban gida ya dube mu a kan rashin jinmu!" "Wani abu ta aikata ta ja maku duka ne?" Furera ta tambaya tana sake matso su harda rike tsatso tana kallonsu Da sauri Ummi ta kalleta ta dauke kai, a gaskiya sun kasance basa jituwa a tsakaninsu a cikin bangarensu, ama rashin jin Furera ya yi kamari, irin abinda take yiwa ZAHRAH ya yi yawa sosai Fuska auntynsu ta hade ta raba ta shige gaba daya makarantar ta dauki hanyar ajinsu ba tare da ta ba Furera amsa ba, dan bata son maganar ta yi tsayi, ita kuma furera kishinta a kan Fatima ya kare, su kam ba zasu wuce gona da iri irin haka ba, Mamah ba zata taba barinsu su aikata abu irin haka ba Kallon kallo suke yiwa junna ta cikin nikaf din, sai kuma Furera ta yi wani murmushin raini tana fadin" Dan bani hanya mana na shige malama kin wani gajen hanya kamar kina da iko da ita" Bata ce mata komai ba, sannan bara matsa a lokacin ba sai da ta yi niya dan kanta ta juya ta shige itama ta nufi nasu ajin tana jin irin yadda karamar wayarta ke giiiigiiiii alamun kira na shikowa ama ta yi banza da ita ta shige ta zauna ta sada kai ita daya a cikin aji tun kafin kowa ya shigo Mintunnanta uku da yan dakiku ta ji an janyo kujera an zauna a gefenta, lokaci daya aka nemi kama nikaf dinta da muryar wace ko bata dago ba dama ta san itace zata yi mata haka ta ce" Yan mata yau kece farkon zuwa ko lafiya?" A hankali ta saka hannunta tana rike nikaf din da ta so dagawa kasa kasa ta ce" πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ• *DAƘIƘA BIYAR* πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ• _MALLAKAR_ *SAJIDA NIGER* *Da sunan Allah mai rahama mai jin Ζ™ai* _7_ *Garabasa , garabasa, 😁πŸ₯°, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°* A hankali ta saka hannunta tana rike nikaf din da ta so dagawa, kasa kasa ta ce" Ke kar ki cire mana, kin zo kuma zaki fara ko?" Muryarta ta sakata dan zuba mata ido, a hankali ta ce" Kamar kin yi kuka ?" Idannuwanta da bata son dagowa ta sake kin dagowar, yanzuma ta ce" Wai ina daliban ne? Yau malan ba zai zo da wuri bane?" "Me yake damunki ne? Ina magana kina zilewa? Gashi har kin manta yau bamu da karatu da safe kwata kwata sai da yama na islamiya?, Muma mun zo ne dan yau mune da Shara ko kin manta?" Ta fada mata da dan mamaki tana kallonta Sai a yanzu ta dago idannuwantada sukai mata nauyi tana kallonta, sai kuma ta dafe gabam goshinta wanda shima ke dauke da shatin bulala, dan Walahi sun daku iya dakuwa ta ce" Ya Allah, kin ga na sha'afa, kwata kwata na manta, islamiyarma kin mamta wa'inda basu kawo harda kadai bane akace su zo? Mu ai mun kawo malan Habibulah yace kar mu zo yana so ya ware wa'inda basu da niyar sake yin sauka ko?" Hannunta ta riko da sauri tana jan hijabinta tana zarro ido ta ce" ke menene wannan? Meye a jikinki haka?" Sai kuma ta warce nikaf din nata , ai bata shirya ba ta sake mikewa tana magana hadi da fashewa da kuka, dama ita mutun ce mai saurin kuka, bale fuskar Zahrah ta tsoratar da ita ainun, a rikice ta ce" Innalilahi, Fatima menene a fuskarki? Dukanki aka yi ne? Waye ya dake ki?" Ido kawai Fatimah ta zuba mata ta ki ta amsata, har ta gama rikicewarta tana share hawaye ta dauki jakarta ta ce" Ai sai ki tashi mu tafi a baki magani dan walahi ba zaki zauna a haka ba , sai ki ci gaba da rike damuwarki a cikinki tunda baki daukeni da mahimmanci ba, ba zaki taba sanar min da matsalarki ba dan baki daukeni yadda na dauke ki ba!" Da ido ta bita har ta ga ta fice, a dole ta mike ta mara mata baya dan ta sani ne ba zata taba saurara mata ba kuma, kai Aisha ba dai rigima ba walahi Sunna zuwa maimakun a yi mata aikin aa, sai aka tsayar da ita kan dole sai ta sanar wanda ya ji mata wannan ciwon, dan makarantar ba karamar makaranta bace, ba zasu ringa barin abubuwa irin wannan ba Amsar dai ita ce, wato shiru, har sai da ran docter ya bace ya sa aka yi kiran yan uwanta, warau yayunta domin itama tana amsawa da dunnan FATIMA DOCTER AHMAD SULAIMANE ne Yayarsu ce ta sanar cewa laifi suka yi a gida aka zane su Sosai aka yi masu nasiha cewar su ringa kiyaye abinda zai taba zuciyoyin iyayensu, su ringa yiwa iyayensu biyaya in dai sunna son gamawa da duniya lafia Sosai aka kula da lafiyarsu sannan aka salamesu, kusan kaf yan matan gidan ne suka zo kiran domin da ta ki yin magana du wani mai amsa sunnan Ahmad SULAIMANE aka kirawo ya kuma amsa Su uku ne suka nufi hanyar bishiyoyin da dalibai ke zama sunna yin karatu, ko mace su biyu ne Furera na biye da su a baya Wanu wawan tsaki ta ja tana dan daga kafarta kasa kasa ta ce" Sai a ringa zakewa ana neman ja mana masifa, ko me kika aikata ke da ita, a daina yi mana anfani da sunnan uba mai daraja ana watsarwa kamar yadda ake watse, wai wani Miji goma ba uba goma bane ta yiwu uban goman ne , ama mijin goma kam sai mai asali, ko daya da kamar wuya!" Aisha ce ta tsaya tana kallon Furera gabanta na faduwa, a wajen dai su uku ne, su uku ne kadai, uwa uba maganar da ta yi sai da ta tsaya ta yi tana kare masu wani irin mugun kallo Murya a dan rikice Aisha ta ce" A'uzubilahi mina shaidanin rajim, me kike fadi haka Aunty Furera?, Wannan wace irin magana ce tsakani da Allah?" Da zafi Furera ta ce" Maganar da na yi ce, kuma nake kai a tsaye!, Mtssss ke wama ya raba da ke ne barw ki dauka? Ni dai na fada kar ki kuma jan abinda za'a kirayi mahaifinmu yana cen yana tsaftace kansa a banza!" Gaba daya sai Aisja ta rsa ina zata saka ranta, bama da ra juyo ta dubi Fatimah ta ga ta lumshe idannuwanta, ta sadda kanta, sannan ta juya ta karasa wajen zama ta zauna ta dago kaffafuwanta ta rungume a kirjinta sannan ta dora kanta, hakan ya ba farin hannunta damar fitowa mai dauke da dan carbinta na dannawa a hankali tana dannawa, wanda idan ba kallon hannun ka yi da kyau ba, ba zaka fahimci dannawa take yi ba "Fatima, yaya zaki ringa kallon aunty Furera tana yi maki mugwayan kalamai irin haka ba tare da kin kwaci kanki ba? " Aisha ta fada hankalinta a tashe matuka Shiru dai ta sake yi mata, hakan ya sa ta ce" Ba nufina ki yiwa auntynki rhin kunya ba Fatima, ama ai kishin iyaye ba hauka bane, a kan me zata ringa magana kamar tana shegantaki tana neman ciwa iyayenki mutunci? Idan har tana da tunani har kanta take neman wulakntawa dan kuwa mahaifinta shine mahaifinki!" "Aa, ba shine mahaifina ba" Fatima ta fada tana kallon Aisha tsai cikin ido Aisha ta yi wani iri

Chapter 4 of 9