Share this page
nan, gidan da Ya Hafiz zai zauna Haya ce ya kama a fadaman mada, layin gidan Mamar tsohon gwamnan Bauchi Isa yuguda. Duk wani kayan gata an saka min anyi min auren gata kowa ya sani, shi kanshi Ya Hafiz yasan yadda Iyayena suke kaunata. Yadda muka fara da soyayyarmu me tsayawa a raina kowa ya ganni sai ya yi maganar aure ya amshe ni, gashi dai nice karama amma ayi min goyon auta ba don na koyi girki a gabansu Mama da Yadiko, haka yasa nayi ta kula da mijina, watanmu uku da aure Ya Hafiz ya kawo min shawarar tunda ina karatu na fara shan maganin hana daukar ciki yana tausayina nayi karama ga kuma karatu, cikin soyayya da kulawa ya bani wannan shawarar, ni kuma na amsa hannu bibbiyu. Saboda Abba ya gaya min Ya hafiz ba zai tab'a cutar da ni ba, kuma na yarda da wannan magana, haka Kakanmu Baba Malam wanda shi yayi ruwa yayi tsaki akan lamarin ya gaya min haka, ashe kiransu yake yayi ta gaya musu yadda yake kaunata, shi baya fatan na mutu na barshi gara shi ya fara mutuwa. Haka nayi ta karatu ina kuma shan magani ban tab'a fadawa kowa ba. Nayi imani da Allah nice sanadin matsalata. Duk abinda Ya Hafiz zai aikata ban tab'a ganin laifi ko kuskure ba. Shekararmu daya na fara tsintar wasu abubuwan a jikin wandonsa ko rigarshi wato condom, ban tab'a magana ba, na zama makauniya akanshi bana fadar aibunsa, bai sauya min ba sai da na fara wani irin kiba, wai ashe maganin da nake sha ne. Idan da xan gaya muku yadda Ya Hafiz yake min a lokacin kwanciyar aurenmu ni har mamaki nake, domin kamar wata yar iska haka zai ta min, ni kuma bana son ya ji ba dad'i sai na hakura na barshi yayi yadda yake so, kibar da na fara sai ya sa na kasa tabuka abin arziki. Lokacin ina aji hudu na jami'a, an tura ni IT, wani bank na samu horo. Ranar ya kasance Juma'a haka yasa na dawo da wuri kuma mun yi zan tsaya gidan Ya Umar Aunty Azizat ta haihu. Na manta kayan barkan a kan gadona. Na koma gidan dauka, yadda na shiga na ga motarshi jikina yayi bala'in sanyi, domin kuwa ya ce min zai yi tafiya ne zuwa Kano. A kofar shiga cikin gidan na ga takalmin mace, haka na shiga cikin gidan domin ina ga ko Kannensa ne da yake suna zuwa. Koda na shiga ban kawo kome a raina ba, haka na shige can dakina ina d'aga labulen mace na samu akan Ya Hafiz suna masha'a, bugawar da zuciyata yayi yasa na juya parlourn da sauri na zauna, jin karar takuna yasa suka fito, lokacin da suka fito suka same ni ina kallon, murmushi nayi mishi nace mishi. "Dama baka tafi ba ne?" A dan razane, ya ce min. "Eh!" Yana kallon yadda nake kallon tv, haka yarinyar ta fito tana kallonshi. Shi kuma ni yake kallo. Tana fita na koma dakin na dauki abinda xan dauka na fito. " Ina zaki? " "Ka manta dai sunan Aunty Azizat ne? " "Muje na ajiye ki! " Ya kai hannu zai tab'a ni nayi maza na matsa, ina murmushi na ce mishi. " Huta kawai! " Haka na bar gidan, a can na wuni anan ake gaya min umarar bana ma za a tafi damu, sannan Abba ya cire zakkar da yake cirewa duk shekara an bawa Ya Ado kudin ya haɗa da na wanda yake hannunsa an saya min gida Tambari housing estate, ina jin haka na ce musu kawai zamu koma can, ganin haka kuwa suka mara min baya domin yadda kowa yake sonshi saboda ina sonshi ne, laifin da yayi min sai na barshi a matsayin ajizanci. Muka cigaba da rayuwar har muka taso daga unguwar da muke muka koma sabo bayan sallah.. shekararmu biyar cib wanda yayi da yin bautar kasana, Ya Hafiz ya fara kulafunci Yara, a lokacin hankalina ya tashi nayi ta zaryan asibiti amma babu labari. Bani mantawa wata rana ina kwance wurin karfe tara na dare ya shigo da wata mata, don zata girme ni. Ya ce bata daki ta kwana. Haka nayi kuwa na bata daki da na ware shi don bakinmu, kwana ɗaya sai ya zama kwana biyu kai a takaice dai sai gashi ta share kwanaki a gidan. A cikin wannan yanayin na kama shi da ita, a lokacin na saka a raina gara ya aure ta, yaki har da gaya min wai karuwa ce, na ce haka zai yi hakuri, a cikin lokaci kalilan na shawo kanshi, ya kai sadakin karima, kowa a dangina yaji maganar aurenshi, hmm mutum sai Allah sai ga magana ya fito ta Jama'are cewa ai dalilin aurensa don ni na kashe mahaifina da shan kwayar hana daukar ciki, a lokacin dangi kowa ya juna min baya nima kuwa na tashi da rikici na ce ba gidana ba, Abba da Baba Malam suka zo har gidan suka ci mutuncina tunda ni bana kaunar Hafiz shi yasa na sha maganin hana daukar ciki ban isa ba a gidan zai zauna da Matarshi. Haka nayi hakuri na dauke kai, aka yi auren. Suka yi ta min iskanci da renin hankali. Wallahi tun bana iya dauka har na fara, abin da ban sani ba akan shi kai kara, abu kaɗan ya kai ƙarata, ayi ta zagina ana ganin laifina. Kwatsam sai ga Matarshi da ciki aka yi ta murna ana farin ciki. Nima dai nayi murna, nayi farin ciki. Sai dai watanin cikin da auren bakwai, da safe muka samu hatsaniya da ita, kuma Ya Hafiz din Yana nan shi ya raba rigimar, bayan ya fita kasuwa kawai jini ya ɓalle mata, haka aka kwashe ta zuwa asibiti. Haka muka je ko awa daya na ayi ba ta haifi Yarta mace, aka fito aka gaya mana, muka yi ta murna haka na koma gida na gyara inda jini ya bata na wanke gidan, wurin karfe biyar na yamma aka sallame ta, suka dawo gida washi gari Ya Umar ya zo ya min shegen duka, wanda ya fusata Aunty Hindatu a lokacin tayi ta fada tun daga nan ta tsaya min, wai ashe labarin abinda ya faru Ya Hafiz ya gayawa Baba Malam shi kuma ya kira Abba yake ce mishi ga can Lubabatu zata kashe mata da ciki jini ya ɓalle mata.. shine Abba ya ce ko a samu wani ya min duka. Ko kuma ya sake Mama. Wannan abin ya fusata Ya Umar.. Danginta da kowa yana jin haka, har shi ya Hafiz din, sai da nayi zazzaɓi, yan uwanta don gulma sai sun zo duba ni. Haka na daure na yi ta hidima dasu har aka gama suna abu daya na musu fintinkau, iyayenta talakawa ne na fitar hankali hatta abubuwan da aka yi na suna daga gidan Iyayena ne, ranar sunan da yamma na shiga naji suna min dad'i. Ni ban kula su ba sai Aunty Raliya da ta wanke su tas ta ce musu. "Ai ku san tarbiyya irinta gidan yasa aka zane ta kada ta kara aikata shirme, gidan da Yarku take abincin da Yarku take ci daga arzikinmu ne, shi kanshi mijin dai bai da nashi na kanshi sai na matarshi don haka mu yar mu tana da tarbiyya domin bamu sake ta tayi ta bin titi kwaro-kwaro ba. Ga sittin ga degree. Haihuwa kuwa ba akanta aka fara rashinsa ba, Allah ya karawa Nana A'ishah yarda itama har tayi wafati Allah bai bata haihuwa ba. Mun san islamiyya domin mun zauna gaban Malamai " daga haka suka yi shiru. Tun daga nan ta koma bayana, Yan uwan ya Hafiz suka koma jikinta hatta Hajiya komawa tayi jikinta. Haka aka watse wani renin hankali, sai su bawa yarinyar maganin barci su kawo min ita haka zasu ta iskanci wani lokaci kuma haka zasu kawota ko za mutu tana kuka ba zasu amshe ta ba, haka na ci wahalar yarinyar nan. Gashi da na gama bautar ƙasa result dina yana fitowa aka so niman min aiki Amma da yake mugunta na ransa ya hana.. Haka nayi ta rayuwa da kunci da wahala, gashi ya hana ni cigaba Umaran da muke zuwa ya dauke min damuwa, idan ya Hafiz yana son wani abu a guna tow wallahi a lokacin zai ta kashe ni da soyayya har sai na fara jin anya ba rashin fahimta bane, amma ina haka dai muka cigaba. Akwai shekarar da Abba ya biya musu Umara shi da Karimah kanta yayi ta rawa haka suka tafi watan Mauludi. Bayan sun dawo takuma daukar ciki, a lokacin Firdausi ta zo ta zauna a gidan, na ga iskanci ganin idanuna. Na gama secondry School ina sha shekaru goma sha bakwai, na gama jami'a ina da shekaru ashirin da biyu, a duniya. Haka kafin ta haihu ya ado ya zo ta sauya min kayan gidan ashe ya samu karin mukami ne, a lokacin na ji labarin tun dukana da Ya Umar yayi suka daina magana, dama shi ne mai tsaya mishi akan kayansa da yake shigo da su ya cire hannunsa. Kai abin fa sai da aka yi zama sosai domin a ganan Abba Ya Ado ya ce mishi.. "wallahi billahi azmin, duk wnada ya kara taɓa Lubabatu sai kotu ta raba ni da shi, saboda me aka sauke Suratu hujara?" Akan wannan rigimar Ya Umar ɗin ya shirya min birthday da na cika 23, ina zaune aka zo aka dauke ni, sai gidan Ya Umar a can aka yi birthday party din ya bani motar da kowa sai da yayi mamaki ya ce min na kira Ya Ado na gaya mishi, na kira na gaya mishi na tura mishi motar ya gani shine dalilin shirinsu, tun daga lokacin Yayuna suka dauki nauyin tura min kudi, Amma ya Hafiz ya shiga kwacewa, duk shekara idan muka je Umara sai na sayi yan kunne gwal kamar yadda su aunty Hindatu suke yi domin dukkanmu Yaran Abba mata yake biya mana, har su Aunty Munah aunti Raliya. Karimah ta haihu ana saura kwanaki uku ba dawo haka na saya mata kayan Baby, lokacin da na dawo na samu an gyara min parlourn, ai kuwa na dawo da kwana biyu aka yi suna yan'uwana a parlour, ga girkin da aka yi musamman ni da muke shiri da yan unguwar suka yi ta shigowa saboda ni, bayan suna shima suka tattaro min yaran bakiɗaya, haka nayi ta hidima da su har tsawon shekaru biyar cif. Duk wani abinda nake da shi Ya Hafiz ya ga na cigaba ne dai ya raba ni da shi hankalinsa yake kwanciya. * Kiran sallah farko ne ya sani share hawayen da ya zuba min yanzu na fahimci dalilin da yasa min haka. Na ga tashin hankali a rayuwata na ga abinda zuciya ba zata iya karba ba, amma na amshe shi hannu bibbiyu, danginmu kowa ya juya min baya. Uwar da ta haife ni ta tsame Hannunta a kaina, Mahaifina ya watsar da ni, a koda yaushe nayi kuka Ya Hafiz xai nuna min ai ba kome ba ne, saboda kawai dan karamin mistake ai ba wani abu ba ne can babba da zai saka ni damuwa, Ya Hafiz Dan uwana ne tunda da Baban Jama'are da Babana uwa daya Uba daya, sannan Ya Hafiz ya boye munannan halayenshi ya bayyana kowa kyawawan halaye da Dabi'u, babu wanda zai ga ya Hafiz ya zata yana da mugun hali. Sai dai kowa yasan mai kyau kuma yasan mara kyau, idan da ni ce Ya Hafiz ba zan taba saka shamaki a tsakanin zuciyoyin da suka yarda da ni ba. Amma sai ya lalata min rayuwata da future dina da kuma duk wanda zai kalle ni ya tausaya min, sai ya cusa min kin kaina da rashin accepting kaina. Ya danna min tsoron duk wani d'a namiji da kuma duk wanda zai kalle ni a matsayin mace, ya nuna min cewa ni ai ba mace ba ce. Ya kuma gaya min cewa kaf duniya da zuriar Baba Umar Jama'are babu wanda zai ganni ya ji sha'awar zama da ni ko kaunar zama da Ni. Bayan ya ga bani da amfani ya cigaba da ajiye ni domin a ga yadda yake namijin ƙoƙarin kula da rayuwata. Ba zasu fahimci waye shi ba, sannan idan zasu shekara dubu ba zasu tab'a gano waye Ya Hafiz ba hawainiya ne shi mai sauya launi daga wannan zuwa wancan..... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI* Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu *Littafin nan na kudi ne akan 1500* *1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 16 12 40 my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641 Posting Arewapen da Telegram SHA UKU HAFIZ Da farko bai zata zai haukace akan tafiyar Lubnah ba, bai taɓa kawowa a ransa tana da amfani har haka ba sai da ya wuni yana bibiyar dangi da yan uwa ko ta je wurinsu, amma babu labarin kai ko a mafarki babu labarin Lubnah haka yasa hankalin kowa ya tashi ban da yan dakinsu da sun san mafarin. Yadda Ya Hafiz yake playing victim sai ka rantse da Allah, ba shi yake yi sanadin barinta gidan ba, aikuwa Washe gari sai ga Baba Malam, shi da Baban Jama'are da Hajiya Asiyah,Goggo Alti da Goggo Uwani sai Goggo talatuwa. Hankalin kowa yayi bala'in tashi, rayuka sun b'aci. Tambayar da Baban Jama'are da Goggo Alti suka mishi ya sake cillashi cikin wani tashin hankalin. "Me ya haɗa ka da Lubabatu da har ta dauki wannan matakin?" "Wallahi na rantse da Allah ban mata kome ba, kishi yake janta." "Yarinyar da magana ma bai dame ta bane zata yi kishi har na fitina? Hafiz kasan ina da labarin abinda kake aikatawa!?" Inji Mahaifinsa, take Baba Malam ya rufe shi da fada. "Ya ana cikin wannan tashin hankalin zaku kara mana da wani. Ku barshi da ji da damuwar da yake damunsa ba a kara masa wani ba, gaya min me kuke son cewa." Goggo Alti ta ce mishi. "Baba Hafiz munafiki ne, ba kan Lubnah ba hatta Sirajo sai da Hafiz yayi sanadin barinsa shagon Shehu, yanzu haka ya koma wurin Babana yana zaman shagon, Allah ya gani tunda ka yi sanadin da Babana ya bar shagon na fara tunanin ya kuke zaune da Lubnah kowa yasan yadda kake nunawa ka damu da ita bayan kuma kai ne shaidanin da kake rabata da duk wani farin cikinta, Shehu da kanshi ya kira ni yana gaya min ya kori Sirajo ina laifin ya ce min na ja mishi kunne, bayan abinda Sirajo ya sani gaskiya ne, Ali ka ganshi idan akace min zai dafa mutum ya ci zan yarda domin munafiki ne na gaya muku gaskiya. " " Alti ina magana! " " Baba dole fa mu fadi gaskiya domin Lubnah kaɗai ba zata iya fadar abinda take ji ba, azzalumi mugu hatta dukiyarta sai da ya lalata mata ya kwashe maha'inci, kai akanka ba ka bar kanka na balle wani haba don Allah wacce irin rayuwa kake yi ne haka? Wacce irin manufa kake so ne? Ina tausaya maka Shehu yaranka da ka watsar ka ce basu tausayinka wata rana su zasu dafa maka domin. Wannan munafikin ya hmm! " Tayi murmushi mai ciwo, tsoro ya kama Ya Hafiz haka dai aka tashi zuciya ba dad'i. Mama ita kanta yanzu ta fara tsoron kada wani abu yake faruwa Lubnah ta bar musu Bauchin, take hankalinta ya dawo kan Lubnah bayan Goggo Alti tayi mata tas, ta ce mata. " Idan baki tsaya mata ba, wallahi zaki kashe yarki shi Shehu bai da asara haka Hafiz bai da asara gara ki tsaya mata kafin lokaci ya kure mata." Wannan maganar ya rikita Mama da Yadiko, don haka tayi ta addu'a Allah yasa Lubnah tana hannu na gari, wasa wasa sai da aka kwashe kwana biyar babu labarin Lubnah, haka ya kara fusata Abba wato Baban Bauchi, wanda kai tsaya ya tara Yaranshi da suke Bauchi ya ce ko su dawo da Lubnah ko kuma ya sake Mama, kuma ta bar mishi gidansa wallahi zai aikata, abinda yasa yayi haka faduwar da Hafiz yayi a kasuwa, aka kai shi asibiti akace jininsa yayi azabar hawa, ba sai ga Hafiz ya fadi ba. Abin kamar alamara, sanin cewa Lubnah yake bukata yasa Abba ya fadi haka, shiru Umar yayi kafin ya ce mishi. "Gobe idan Allah ya kai mu zata dawo abin bai kai har ha..." Tass Mama ta wanke shi da mari ta kara wanke shi da mari. "Dama kasan inda take kayi shiru!" "Dukkanmu mun san inda yake ni na bata kudin motar na kaita tasha!" Inji Ya Tahir, ba sai yadiko ta rufe shi da duka tana kuka ba, abin fa ba karamin al'amari bane, haka yasa a ranar suka kira Almu shi kuma ya ce ayi hakuri ranar juma'a zai zo. Domin Lubnah ma ya kaita 44 ganin likita bata da lafiya. Da wannan aka kashe case din sai ta zo, kasancewar kowa ya gama jin ranar da zasu sake haduwa tunda ranar talata aka yi zaman. ** Lubnah Tun daga ranar da na isa gidan ban kara samun damuwa ba, sai dai rashin lafiyar da nake a tsaye, bana cin abinci sosai. A lokacin da Ya Almu suka kai ni asibiti na ciro takarda asibitina na nuna musu. Kallona Likita yayi ya ce mishi. "Kanwarka ce?" "Eh likita." Basu takarda yayi ya ce yaje yayi test yana jiranmu, haka muka tafi aka yi min test din sannan na zauna zaman jiran, idan mutane na magana sai nayi ta jin maganar har cikin kwanyana yana wani irin ciwo. Haka yasa ina karban result din na kai mishi. Shiru yayi ya ce min. "Akwai ciwon kai?" Gyada kai nayi ya gyada kai yana mamaki ya ce min. "Akwai test din da zan baku sai dai ina ga kamar a Kano ake yi ban sani ba ko an samu asibitin da suke yi anan din." Bamu hoton ƙwaƙwalwa yayi muka tafi Ya Almu ya kai ni aka min, sannan na dawo kiran wani likita yayi ya zo, yana mai gaya mishi case ɗin. Kallon Ya Almu suka yi kafin suka ce. "Officer maganar gaskiya, kanwarka akwai wani sanadarin da yake sakata jin ciwon da take ji, na farko akwai drug din da take sha ta daina wanda ya ke hana wancan sinadarin aiki sosai, na biyu abin ya tab'a mata ƙwaƙwalwa da yasa take jin ciwon kai, a takaice dai Mentally healthy dinta ya tabu, sannan tana fama da rashin lafiya resilant, daga yadda take gabanmu kawai dai saka ka fahimci tana fama da kanta, amma zan bata magani!" Anan ya Almu ta gaya musu ai ina ganin likita a Bauchi, take suka ce zasu so ganin record dina, shiru Ya Almu yayi kafin ya ce musu, "daga Bauchi take idan aka ce sai anyi haka zai iya daukar lokaci!" Haka suka yi shiru suka kallona, kafin daya likitan ya ce mishi. "Ko zaka samu wani da yake da alakata da ita akan matsalar." Tunawa yayi da Aunty Innah, don haka ya kirata ya gaya mata abinda yake faruwa. Shiru tayi ta ce ya bawa likitan wayar, ya mika mishi suka gaisa kafin suka shiga tattaunawa da yake abu na masu ilimi da sanin ya kamata, na wane da wane,a fagen da kowa ya kware. Maganar da suka yi da Aunty ya sakawa likitan tabbaci da hasashensa. Sannan ya tambaye ta maganin da nake sha, ta gaya mishi sannan ya canza min wasu magungunan. Ya kalli Ya Almu ya ce mishi. "Yana da kyau ta ga asalin likitan ƙwaƙwalwa da na zuciya." Shiru yayi kafin ya cigaba da cewa. "Cikin fahimtar da nayi duk da ban duba ɓangaren zuciyar ba yana da kyau a san da zuciyar na da matsala ko babu." Sun jima suna magana wanda rabin maganar ba fahimta nake ba, bayan mun bar asibitin Ya Almu ya mai da ni gida, tunda muka isa na zauna a parlourn don shi ya umarce ni na zauna ya kawo min ruwa da magani ya bani na sha. Sannan ya ce min. "An samu matsala a gida, ranar juma'a zan mai dake gida kin ji!" Gyada kai nayi ya cigaba da cewa. "Zamanki a daki bai da amfani kin ga Saliha bata nan, ki zauna a parlourn kafin ta dawo. Akwai abinci." "Yaya tafi zan kula da gidan!" "Are you sure?" Gyada kai nayi ina mai kallon gefe. Amma idanuna kwalla ne yake taruwa a hankali. Fita yayi ya bar gidan na lumshe idanuna na kwanta a wurin, dama ko na zauna a dakin ba barci nake yi ba, ina zama ne nayi ta nazarin yadda Allah zai kawo min mafita tow ina ganin kamar na tsira amma ashe ina zan koma gidan jiya, hawaye ne suka zubo min a hankali nayi ta zubar da hawaye ban sani ko don ina son na samu iskar yanci ne amma ni dai nasan na gaji, ban san lokacin da na dauka ina zubdar da hawaye ba sai da barci yayi gaba da ni. Ina ga a cikin maganin da nasha akwai na barci ne. Ina ga rabona da barci me kyau tun muna tambari housing estate, yau sai gashi nayi barci kamar bani ba, sai karfe biyar na farka shima muryan Zunnur ya saka na bude idanun yana tambayata Aunty barci kike yi baki yi sallah ba! " A hankali na tashi ina faɗin. " Na gode Babana da ka tashe ni! " Ya Almu da yake aiki a laptop dinsa ya ce mishi. " Father akan me zaka tashi Yarka! " " Dady tayi Sallah! " Murmushi nayi na wuce dakin da nake nayi sallah kasancewar kasaru zan yi, bayan na idar na zauna sai ga Aunty Saliha da abinci haka na taɓa sannan na cigaba da zaman dakin. Da dare yayi Ya Almu ya kara bani maganin na sha nayi barci sai na samu sauƙin ciwon kan, sannan na samu barci a hankali tunanin da nake yawan yi ya ragu, sai tsoron yadda zan isa gida, ya zamu kare da Iyayenmu? Sai tsoro ya kara kamani. Haka kwanakin suka tafi har zuwa ranar da zasu mai da ni, da wuri muka bar Kaduna, domin ya ce yana son ya dawo ranar ne, haka yasa muka fita da wuri da yake maganina ya saba da jinina ba wani barci, sai dai nayi kaɗan kafin muka iso saminaka. Ya Almu ya sayi tsaraba muka cigaba da tafiya har zuwa rahama rishi, tunda muka iso nabardo na ji tsoro ya kara mamaye ni, kafin karfe biyu na rana mun iso garin Bauchi. Sai a lokacin na rude kamar zan shiɗe, har muka iso kofar gidan aka bude get din gidanmu ya shigar da motar, kasa fitowa nayi bayan yayi parking. "Darling sister shiga gani nan zuwa!" "Tow!" Na fada ina jin wani irin tsoro yana cika ni, ina saka kafana a waje naji kamar an kwashe min karfina haka na cigaba da tafiya har cikin gidan a dan barandar da zata kai ni cikin gidan anan na hango Ya Hafiz tsaye, wani irin bugawa zuciyata tayi naji kamar na juya da gudu. Kanshi a sunkuye da alamu waya yake cikin farin ciki da nutsuwa, kamar ance ya d'ago kai sai a kaina. Ji nayi kamar zan takowa yayi nima na fara yin baya ji nayi an janyo ni baya. Sai da na sake wata irin ajiyar zuciya da

Chapter 10 of 13