Share this page
zuci, ai ta ce ba da gayya ta konata ba kuma yadda ake ta ririta al'amarin da na ga ciwon ai ba wani babban al'amari ba ne, lamarin mata ne kawai da ririta lamarin da bai kai ya kawo ba, yi shiru Y'ata share hawayenki. Kul na kara jin wani yayi magana da cewa za a kai batun nan ga hukuma kunar da bai wani tashi ba, ga yadda yayi baki kasan ai ba zai tashi ba, sannan kai Hafiz ka tuna akwai ranar da zamu tsaya a gaban Ubangiji, ka ji tsoron Allah kada son zuciya ya kai ka ya baro ka, kawai jikina yana bani haka kawai Lubna ba zata aikata kome ba." Kunya ce da bori tasa shi, kame-kame amma a cikin ranshi bai so haka ba yasan Baban Bauchi da za a bar shi sai ya mari Lubnah shi yanzu yadda zai bakanta mata rai yafi bukata akan wannan abin. Duk da an ce yau da gobe bai bar kome ba, Iyayena da dangi babu wanda ya hango mutuwar tsaye da nake yi saboda Ya Hafiz, Babu wanda ya yarda da cewa ina cutuwa, a'a kowa gani yake kamar ba cuta ba ce ni ce nake cutarsa saboda shi mutumin kirki ne, bayan shi ya shiga rigar mutanen kirki ne. Yayi ado da kwalliya a cikinsa, sannan babu wanda zai kalle shi ya ce mutumin banza ne. Amma bakin maciji ne sanye da tufafi yan adam, haka muka bar gidan, bayan an mana nasiha. Ni dai nasan cewa zuciyata ta gama mutuwa bani da wata amfani. A hankali gidan ya zame mini kamar hell fire, bani da kwanciyar hankali bani da sukuni, idan abin ya dame ni sai na rufe kaina a daki na ki fitowa, a hankali abubuwan suka ta tsanani domin kuwa na daina sayar da kome na daina yin kome, shi kanshi Ya Hafiz da ya fahimci bani da wani amfani sai ya cigaba da azabtar dani da abubuwan da zai saka na ji har na tsani zaman gidan, damuwa ya kara tsananta min domin ba wani abu ba ne su min gorin haihuwa. Bayan wata biyu kusan watan Mauludi, Ya Ado ya dawo, ni ya fara kira a lokacin babbar wayar hannuna na sayar domin Ya Hafiz ya zo ya saka ni a gaba yana son kudi haka na hada da wayar da sarkata ta gwal na bashi, kunsan me a duk lokacin da zai same ni yana bukatar wani abu tow ba irin yaudarar da baya min, haka zai zo da soyayya ya cutar da zuciyata, har yau ina da yakinin zai shiryu ya daina abun da yake min don na fara tunanin kamar shiga tsakaninmu aka yi. Cikin murmushi na ce mishi. "Barka da dawowa yasu Aunty Zakiya? Kun iso lafiya?" "Alhamdulillahi Auta nace ke zan fara kira ki san na dawo!" "Masha Allah sannu da hanya madalla!" Yadda muke wayar naki sake jiki da shi, ya sa shi kashe wayar da zai kira wani lokaci, tunda Ya Ado ya dawo Nigeria kullum zai kira ni, zamu gaisa daga nan zan yi shiru. Haka zai ta ja na da hira, har ya gaji ya kyale ni. A hankali abin sai ya zame min jiki, sannan ban kara yarda mun yi tashin hankali da wani abu cikin gidan ba, wani abu daya da na fahimta idan na kashe auren ma bani da wani amfani, haka yasa babu amfanin na gayawa kowa halin da nake ciki, sannan kwasar bakin ciki a wurin Ya Hafiz da danginsa kamar shafa ce ta alola. Haka yan uwansa zasu zo musamman Aunty Nana, haka zata yi ta min kome da gadara da iko iko, idan nayi magana zata ce gidan dan uwanta ne. Haka zan zuba musu idanu, kome zai wuce amma idan ban mutu ba zan sha kallo. Idan ka kalle ni bani da matsala sam, amma deep in side ina cikin wani irin mugun yanayi ne. Sai dai ba wanda ya san da haka sai wanda Allah ya jarabta da irin halin da nake ciki. * Yau Dan wake nayi shima dai nice nayi cefanen, musamman duk ranar da ya tashi rashin mutunci ni ce zan yi kome har na gidan, ya daina kawo abinci domin kuwa Karimah ta ce mishi ai idan aka kawo kayan abinci sayarwa nake sai dai idan ya tashi ya auno mudu idan ya gadama idan bai gadama ba zai ce na ranta mishi, yasan bani da kosisi. Haka zan ta kame kame har na hada abincin aci. Har lokacin Maman Na'ilah bata bani fuskar da zan tambaye ta kudin ba, abu daya take gaya min. "Duk ranar da zaki yi aikin alkhairi wa rayuwarki in sha Allah zan baki kudinki amma idan har wa Mijinki ne wallahi kwandala ba zan baki ba, karshe ma zance sharri kika min!". Murmushi nayi da yake tasan ba zan yi magana ba, shi yasa nima na barta. "Ke Yusrah kawo min kular Babanki na saka mishi abincinsa tun dazu sai magana nake kin ki kula ni!" Cikin rashin kunya ta ce min. " Eh din ba zan dauko ba ko dauko da kanki mana! Tunda bake kika haife ni ba. " Haushi yasa na zo na dauka na kuwa zungure kanta, ai kuwa ta fasa ihu. " Sai ki yi mara kunya kawai! " Na je na dauka ina mai komawa kitchen na zuba musu abincin. "Ina kika san zafin d'a ke kin san yadda wahalar daukar ciki da reno yake ne? Ina zaki sani bayan an lalata mahaifa da alluran family planner, kawai don ta ce ba zata ba sai ki saka min ita a gaba da fada idan fitsari banza ce kaza tayi mana!" Ka sake nayi ina kallon Karima tana gaya min magana akan nayiwa Yusrah fada taki dauko min kular da xan sakawa Ubanta abinci. Shigowa yayi yana faɗin. "Ya dai kaza uwa Yaya mai ya faru Agwagwata uwar albarka?" "Waye ban da juyar matarka da ita bata san haifa ba sai dai kashi a masai." Kumshe bakinsa yayi yana dariya mai sauti. "Yau kuma waye na samu da suna juya au lulu love ce!" Ya fada yana kallon yadda jikina yake rawa. "Ita mana ita dai da bata san ciwon kanta ba, wacce dad'i miji ya kaita aka ta zuba mata alluran hana ciki!" Cikin isgilanci ya ce mata. ."tow waye zai yarda ni ne bana son haihuwa da ita? Bayan nasan ba sonta nake ba kin san idan iyaye suka ga kana kula yarinya sai su dauka wani abu ne a tsakaninku, musamman idan Iyayen yarinyar suka gano cewa yarsu bata jin maganarsu sai naka!" "Ya Hafiz da bakinka kake fadar haka? Kada ka manta da mahaifina da naka Uwa daya Uba daya!" "And so what? Dube ki kitse ya taru a jikinki ke kanki ba zaki iya gudun minti goma ba, dube ki don Allah har kunya nake na ce ke matata ce, domin dariya zaa ayi min, balle kuma." Dariya yayi ta min yana fadar cewa.."wallahi matse matsinki wari suke balle kuma can kasar idan kika kwanta kamar an zuba kashi a bola!" Sai naji jikina yayi sanyi duk abinda zai gaya min naji ciwo ya san ni. "Ka sake ta mana Habibi wannan mai kama da dorinar ruwan tsoro take bani!" Dariya yayi sosai ya ce mata. "Karimcy ba zan iya sake ta ba, kai ko da na sake ta waye zai aure ta? Kada ki manta yadda take tafiya da kyar da kyar waye zai aure ta? Abin dariya nama na jan kare." A hankali na bar abin da nake na wuce daki, na zauna na fashe da wani irin kuka. Ina jin kamar zuciyata zata buga wallahi naji zafi amma ya zanyi, ina son ya Hafiz sosai ba wani abu bane fadar da yayi, shigowa dakin yayi ina zaune ya ce min. "Uban waye zai miki aikin da kika fara? Kin ga Lubnah bana son iskanci da renin wayo, wallahi zan tattaka ki, zaki fita ko sai na zane ki, ga ki katuwa amma kanki babu ƙwaƙwalwa!" Ba yau ya saba duka na ba, sannan ba yau ce zai daina ba. Tsoron dukan da yake fadar zai yi yasa na mike ina faɗin. "Kayi hakuri!" A duk lokacin da yazo ya fara wannan masifar ya tsani yayi magana nayi shiru, idan ban bashi hakuri ba marina zai ta yi. Har sai na bashi hakuri.... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI* Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu TARA Haka na fito na karasa aikin, ina kuka na gaji na gaji da abinda yake min, a hankali na gama na koma daki. Yanayin ba dad'i, ko nace ni ce bana jin dad'insa. Ana haka bikin yar gidan Aunty Hindatu da aka saka ana d'agawa ya taso saboda mijin ba a kasar yake ba, haka yasa aka saka bikin karshen wata June, tun daga kan kayan da zamu saka da kome Yayuna suka min, har lokacin Mama da Yadiko babu wanda yake shiga harkata tow ba ma damuwa suka yi da ni ba, idan bani na kira ba tow da babu wanda zai kira ni a cikinsu. Bikin Maamah yar Aunty Hindatu da za ayi ya saka na dan samu yanci, domin Ya Ado ya kira Ya Hafiz ya gaya masa batun bikin da niman alfarman nazo ayi kome da ni, yadda yasan halin Ya Ado bai da sauki yasa bai yi musu ba, shima Ya Ado zai zo da Yaransa. * Yau da wuri Umar ya bar muda lawan kasancewar mashin suke sayarwa shi a bangarenshi amma yana aiki da ma'aikatan shige da ficen jahar Bauchi. Yana kokarin hawa motar shi wani magidanci ya ce mishi. "Malam Umar ko?" "Eh nine lafiya?" "Hmm dama ina son na tambaye ka ne? Ya kuke da matar Alhaji Hafiz ne?" "Eh kanwata ce!" "Tow gaskiya ku sayi likkafanin da zaku lullubeta idan ta mutu, ni shawara da zan baka kenan idan kun so ku tsaya mata idan kun so ku barta ta cigaba da mutuwar tsaye!" Daga haka mutumin ya tsare abin hawa ya bar wurin. Da wannan tunanin ya iso gida, ya sami Maman Aunty matarshi ya bata labari. "Ba tuntuni ake gaya muku ba, sau nawa ina baki a gidan nan bayan mun gaisa zasu ce don Allah idan ina da yadda zan yi na kaiwa Lubnah ɗauki." Haka suka ta tattaunawa da fadar ko da zasu wani abu su Mama ba zasu bari ba, shi yasa kowa yake shakkar shiga rigimar. Haka suka yi ta tattaunawa a tsakanin al'amarin. * Haka bikin ya karaso aka fara hidimar biki babu ji babu gani, kullum xan je kuma Ya Sani shi yake kawo ni har gida, domin Ya Hafiz ya hana ni kwana. Ranar daurin aure ina ta shirin fita da yake ita ranar ta gama wuninta, tunda asuba nake aikin gidana har na gama da wuri Ya Hafiz ya tambayi Karimah ta ce ba zata ba, haka yasa na gama shirina da wuri, wurin karfe tara na fito ba sai ga Karima ba. " Zan je bikin fa! " " Tow don Allah ki hanzarta! " Na fada ina kallon agogon hannuna. Tunda Karimah ta shiga daki ta manta da ni sai da na kara mata magana wasa wasa bamu bar gidan ba dai karfe biyu da wani abu. Kamar nayi kuka da gayya tayi haka sai dariyar mugunta take min, Ni dai ban kula ta ba. Har muka isa gidan da ya cika da mutane. Muna shiga cikin gidan Aunty Hindatu ta watsa min harara tana faɗin. "Wai ke me yasa baki kome da jikinki? Kullum zaki zo sai kin makara." Zan amsa caran Karima ta ce musu.."jiki duk tarin kitse taya zata yi sauri? Ai kun san Habibi yana kokari ko?" Wani hade rai Aunty Innah tayi tana kallonta cikin haɗe giran sama da kasa ta ce mata.."An kasa dake ne?" Da sauri na cewa Aunty Innah.."Inna uwa maba da mama bata yi karya ba, jikin nan damuna yake ni kaina da ina da hanyar rage shi da na rage, gaskiya ta fada!" Duk da na gama aikin gidan da wuri ita ta makarar da mu. A hankali na wuce bayan na fadi haka na barta nan kunya da yadda sauran yan uwana da yan uwan Ya Hafiz suka mata ca, Mama tana jin su bata amsa ba amma kuma zuwa yanzu ta fara jin kamar akwai abinda suke ƙoƙarin aikatawa. Dakin Aunty Hindatu nayi na zauna can kuryan gadonta. Shigowa Aunty Nana tayi ta ce min. "Ke kullum aka yi magana sai ki nuna babu kome, Alhamdulillahi tunda ba kome amma ki sani Ubangiji yana madakata!" Ta fada min tana wani dauke kai Aunty Nana Yayar Ya Hafiz ce, kuma na hannun damanta uwa uba Karima kanwar Mijinta ne, murmushi nayi na de mata. "Kiyi hakuri wallahi ni ce na makarar damu kamar yadda ta faɗa!" Na fada mata kamar xan yi kuka. Tsaki tayi ta bar dakin Yaya Asabe da take alolan a ban daki ta fito tana faɗin.." Lubabatu ba zaki daina cutar da kanki ba?" Washe mata hakori nayi ina faɗin " ba kome fa" "da kome mana, na akanki aka fara aure ne Lubabatu meke faruwa a gidanki" dariya na fara mata, dariya irin wanda kana gani kasan ba lafiya ba, na ce mata.."ba kome wallahi!" Shiru tayi tana kallon yadda na koma na yi shiru. Ina murmushi. Ina zaune Aunty Hindatu ta kawo min kayan anko dinmu da su, na saka na fito ɗas da ni. Kowacce ta saka sarkan gwal dinta ni dai bani da shi sai wata fashion da na saka Aunty Munah ta ce min. "Lulu ina gwal ɗinki?" Da yake iya mune a dakin. Zare idanun nayi ina kallonsu. "Ina gwal ɗinki?" Aunty Innah ta kara jefa min tambayar bakina yana rawa nace musu. "Na sayar da shi?!" Wani katon salati suka saka tare da zaro idanu. "Karya kike munafuka gaya min gaskiya ko naci ubanki ina kika kai sarkokin gwal ɗinki!" Shiru nayi naki magana, shigowar Yadiko dakin ta ji suna sake tambaya ta ina na kai sarkan gwala-gwalai na. "Na sayar nace!" "Me kika yi da shi Lubabatuna." "Inji Goggo alti Yayarsu Baba mace ce mai fahimta da sanin ya kamata, tana da zurfin ilimin addini sosai. Ta ce gaya min. "Gaya min ina kika kai sarkokin gwal ɗinki!" Jikina ne ya dauki rawa. Nace musu. "Goggo na sayar!" Wani irin mari Mama ta kifa min sai da na ga haske, na rintsa idanuna bakina yana rawa nace mata. "Na sayar da su!" Shiru dakin ya ɗauka haka aka bar zancen amma ran Mama ya b'aci. "Kome kin sayar gidanki, kin sayar kome kin sayar shi yasa kudin Umaranki na shekara biyu na ce kada a baki don baki da hankali!" Ni dai ban ce musu kome ba. Bayan mun gama muka fito waje, muka bar Goggo Alti da Goggo Uwani sai Yadiko da Mama.. "Salamatu ina jan hankalinki da ki tashi akan Yarki, wallahi yarinyar nan tana bukatar wani a tare da ita, ni dai bana zargi amma yarinyar ko baki kika mata iya ka kenan." Haka muka sha hidimar bikin sannan aka shiga hadadar kai Amarya dama ban saka kaina ba, haka na shirya muka tattaro muka dawo gida ashe akwai buhun bala'in da yake jirana. Tunda muka shiga gidan Ya Hafiz yake Bala'i da fada zagi da cin mutuncina har sai da nayi kuka. "Ke gaki mai yan uwa har zasu tsare ta da magana suna gaya mata abinda ransu yaso, don na rufa miki asiri na zauna dake haka na kuma zauna da wannan fuskar naki mai kama da ta giwar zasu zagar min Mata wallahi sai na sake ki,.na rantse da Allah idan na sake ki ba zaki tab'a samun wanda zai aure ki ba wallahi billahi azmin, wannan tarin jikin naki mugu da shi kamar kashi." "Kayi hakuri!" "Hakurin Uban me kike ba ni? Bayan kaf duniya babu mummuna irinki, ga baki ga muni ga munin hali da na halitta, ina kallonki gani nake kamar zan mutu don takaici!" Kaina a sunkuye ya gama zagina na ce kuma ce mishi. "Kayi hakuri na gode sosai, Allah ya baka hakuri." "Don na rufa miki asiri ina zauna dake zaki ci mutumcin matata!" "Kayi hakuri ba zan kara ba!" "Kina nan tibi-tibi sai kace aladiya!" "Na gode sosai!" "In ba don ina kunya Mama da Baban Bauchi ba wallahi da na sake ki, domin ya gaya min duk ranar da na sake ki sai dai ki nime wani uban ba dai shi ba.". "Kayi hakuri ba zan kara ba." Na fito ina murmushi, abubuwa dayawa sun boya a bayan murmushi na, kuka da ihu sun boya a bayan fuskana, amma haka na share na manta da kamar ba ayi ba. A tunani na zancen ya kare, sai dai a wurin Karamcy bai kare ba, domin kuwa bori ta saka mishi a kan sai ya min duka shine zata huce. Ya rasa yadda zai yi da ita kuma yasan matuƙar ta fara fushin nan zai zame mishi tashin hankali, don haka ya fito ya tsaya bakin kofar dakina yana faɗin. "Ke Jaka fito ki bata hakuri!" Wani hakuri kuma? Kawai daurewa nayi na fito waje ya ce min muje ki durkusa ki bata hakuri.. "Ni dai gaskiya ba zan durkusa ba domin hakuri kan xan mata amma ban da durkusawa." Dama kamar jira yake kawai ya rufe ni da duka. Duka sosai sai da makota Baban Na'ilah da Na'ima tare da basu Boy suka shigo gidan dakyar ai kwace ni a hannunsa. Tunda na shiga dakina na rufe na kwana ina kuka. Washi gari naki fitowa na daura abin karyawa haka ya gama barazanarshi ya fita, yana fita nima na dauki hanya na nufi gidan. Ashe ina fita Karimah ta kira shi ta gaya masa gani nan na fita. Idan nace ban daku ba nayi karya, haka yasa na kwaso jiki na kawo ƙara, sai dai ban kai ga isa gidan ba Ya Hafiz ya kira Baba ya gaya mishi karya da gaskiya, ina isa gida Mama da Yadiko suka fatattake ni, akan na koma, don ba zan kashe musu aure ba, Baba yace musu duk wacce na zauna a wurinta a bakin aurenta, wannan ya bawa Ya Hafiz lasisin mai da ni jakarshi da zaran nayi laifi zai rufe ni da duka, wanda ya cusa min tsoro da tashin hankali, wannan dukar da zalinci yasa ni jin dole na rayu ko don na rabu da Ya Hafiz, na gaji. Kaf yayuna aka rasa wanda zai tsaya min, Maman Na'ilah kaɗai ta bani shawarar na fara niman zabin Allah, idan da alkhairi a zamanmu Allah ya shiga lamarin idan babu shawara daya ne, na kai shi kotu a raba auren domin idan aka cigaba da irin wannan zaman karshe daya zai iya rasa rayuwarsa. Haka na dukufa da azumi da addu'a sallah dare da sadaka. Sai da na shafe wata hudu cib har zuwa lokacin ba wai ina da nutsuwa bane, sai dai na ji n koma baya na saurari karatun Malam Albani Zaria, akan khulu'i, duk da zuciyata bata yarda da abinda nake nufi ba, amma ni a kaina na gaji, ni a karan kaina ina son na rabu da shi, ina son na bashi iska ko zai gane yadda nake ji, duk wannan lokacin Ya Hafiz bai tab'a nuna yayi nadamar abinda yake aikatawa ba, kai hatta Yaransa suka yi kuka da ni zai min dukar da dai na tsani kaina. Duk wannan abin da yake faruwa kowa yana jin takaici amma ba yadda suka iya tunda ni ban ga hanyar fita ba, bani da wata madogara, sannan ba ni da wata makama, haka yasa na zubawa sarautar Allah idanu. A cikin wannan ukubar na samu Maman Na'ilah da Na'ima na ce mata.. "Don Allah ina son kudin nan zan samu, idan ba xan samu ba ki barshi kawai!" "In sha Allah zaki samu yanzu ma kuwa!" Mikewa tayi ta shiga can cikin dakinta, ta janyo abu a kasan gadonta, ta ce min. "Lubnah shigo mana!" Mikawa nayi na shiga cikin dakin, ta ciro wata akwatin katako, ta fita tare da dauko wuka ta fasa kan akwatin katako, sai da ta fasa saman sannan ta saka hannu ta bude shi da kyau, kafin ta kalle ni tana faɗin. "Gashi nan ki zazzage shi!" Ƙasa kai hannuna nayi ita da kanta ta zazzage shi tas a gabana. Tow me zanyi da kudin nan?............... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI* Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu GOMA Wannan shine abinda na tambayi kaina me zanyi da kuɗin? A hankali na ji zuciyata bata amince min da abinda nake shirin ba nace mata. "Maman Na'ilah ki bar kudin tunda na ga yadda suke!" Na juya zan fita ta riko hannuna. "Me yasa kuma Lubnah?" Murmushi yake na mata. "Tow me zanyi da shi?" Yadda nayi maganar sai ita kanta abin ya dame ta, ta zata ko ina zarginta ne ta ce min. "Wallahi summa tallahi babu kwandala naki da na." "Har abada bana zarginki kuma ba zan tab'a zarginki ba, kawai bani da abinda zan yi da shi ne." Daga haka na bar gidan. Na dawo na samu Karimah da Yaranta da wata kawarta suna ta hira, yadda nayi sallama basu amsa ba haka nima ban ce musu uffan ba na wuce dakina, tunda na shiga na zauna bakiɗaya naji duniyar tayi min kunci, ko na rabu da Ya Hafiz Iyayena ba zasu tab'a karbana ba. Sai naji bakiɗaya duniyar ta juya min baya, bakiɗaya duniyar kamar ni daya ce mata amfani a cikinsu, haka nayi ta jin kamar zan mutu. Ina zaune a dakin naji sallamarshi, ban d'aga kai ba ya shigo yana faɗin. "Wani wacce irin iskanci ne da ba zaki yi abinci a gidan ba?" A da ina ina ya Hafiz zai sauya amma by now sai nake ganin kamar har abada ba zai sauya ba. "Bakya ji ina miki magana ne?" "Me kace?" Na faɗa ina kallonshi. Fita yayi daga dakin ina jin shi yana ta b'ab'atu, kiran sallah azhar yasa na fita nayi alwala na dawo dakin nayi sallah, can sai gashi da kaya niki-niki a leda har da kayan abinci ya saka a kofar dakina ya fita yayi ya shigo da abincin tunda na ga haka na fahimci wata ya shirya min, don haka ina zaune ya kawo min takeaway, kamar ba zan amsa ba na amsa na ajiye na ce mishi. "Nagode" na cigaba da addu'ar da nake, can bayan ya fita na shafa,. Sannan na ja ledar abinci ne mai kyau, dauka nayi na fara ci a lokacin ya fara shigo da kayan abincin, yana zubawa a bayan kofana. Ni dai ban ce mishi cikanka ba balle har ya dauka ko na damu da shi ne, zama yayi yana min murmushin mugunta, ban bi ta kanshi ba ya mike ya fita, haka na gama na fita da ledar da robar na kai waje, sannan na dawo dakina bayan na wanke bakina. Tunda na shigo naji kamar jikina yana sakewa a daddafe nayi sallah Asr, a wurin dai na cigaba da zama ko kwanciya nayi Allah shine masanin. Ashe kwanakina hudu me kyau a gadon asibiti, sai ranar na hudun na farka. Naga hannuna daure da abin karin ruwa, kamshin abin wanke asibiti ya tabbatar min da asibitin nake, a hankali na yi yunkurin mikewa zaune domin ina jin kamar maganar mutane sama sama, na ji kamar an mai da ni baya, bude idanu nayi a buge amma ban san waye a kaina ba can can naji ana cewa. "Koma ki kwanta!" Haka

Chapter 7 of 13