Share this page
guda kowa da tafiyarsu, lokacin da muka isa gidan kowacce daban daban ya shiga. Anan muka samu ana ta liyyafar, ina isowa Ya Tahir ya riko hannuna ya kai ni wurin abokansa abin mamaki har da Ya Hafiz a wurin wato don jaraba ya biyo ni, irin kallon da yake min na tuhuma da zargi yasa ni dauke kai, babyn aka kawo min Ya Tahir ya ce min. "Ga takwara na miki!" Kurawa yarinyar idanu nayi hawaye na zuba taruwa a idanuna, na d'ago kai ina kallonshi hawaye na zuba min, wannan na gudu wannan na koro wannan, kasa magana nayi ina kallonshi. "Takwara na miki!" A hankali nake shashekar kuka ina me rungume yarinayr har cikin raina nake jin kaunar yarinyar. Haka Yan uwana suka taru ana ta taya ni murna ban haihu ba amma yan uwana sun min kara domin duk abinda ya dace nayi sai gashi sun yi min kome har da kayan barkatu. Soyayyar da yan uwana suke min ya wuce tunanin mutum. Haka na tashi na tafi wurin uwar jaririyan nayi ta kuka, ita kan dariya tayi min. "Lulu Allah ya sani nafi ki farin cikin saka sunan Yarinyar nan, kuma taki ce har abada!" Haka nayi ta kuka a wurin kukan da na kasa yi shine nake yi ina yi ina kallon yarinyar, yadda nake kuka Aunty Hindatu ta ce a kyale ni, nayi kukan dama tun tuni ake son nayi ban yi ba, sai nayi har kaina ya fara ciwo, suka kai ni dakin Ya Tahir na kwanta, barci ya dauke ni mai karfi. Sai wurin karfe biyu na farka zan yi sallah na ga bakona, ita mai jegon ta bani sabon pant da ledar pad, na gyara jikina na fita wurin yan uwa da ake ta hidimar bikin sunan, Aunty Hindatu bata gayawa sauran dangi ba, iyamu yan daki daya da dakin Yadiko aka san da zancen. Wurin karfe shida nayi sallama na wuce gidan Aunty Hindatu. Itama can ta dawo, ta fito min da kaya kala uku domin gobe da sassafe zan wuce Kaduna wurin Ya Almu. Hafiz Karfe takwas ya dawo, koda ya shigo ya g kofar dakin Lubnah a rufe tsaki yayi, yana tambayar Karimah. "Yarinyar nan bata dawo ba ne?" "Ba ka bani sandar kiwonta ba fa!" "Ikon Allah!" Ya ce daga nan bai kara magana ba, haka har zuwa karfe tara na dawo babu labarin Lubnah, bai damu ba yasan yadda zai ji da ita gobe.. don haka yake shirya yadda zai cika Baban Bauchi. ** Washi gari. Asalin tashar Kaduna aka kai ni, wanda yake hanyar Jos, daga nan Aunty Hindatu bata bar wurin ba sai da ta ga motar ya tashi, sannan ta dawo gida. Dama wayata na bari a wurinta, ta bani wani tsohon wayarta da layin duk tsoho ne, amma tana amfani da shi. Haka yasa na kwantar da hankalina don ko na tafi da wayar Ya Hafiz zai iya amfani da kiran na dawo. Karfe biyar biyu na rana na iso Kaduna, Ya Almu yazo ya dauke ni. "Auta sannu da ƙoƙari, sannu Ubangiji yasa karshen wahalarki kenan!" "Amin Ya Allah!" Na fada a hankali, muka wuce gidansu da yake base na Sojojin sama. Muna isa Matarshi Aunt Saliha,ta tarbe ni. Ina zata saka ni ina zata ajiye ni. Don farin ciki da jin dadi. Haka nayi ta jin kamar alfarma aka min. Nayi wanka aka bani abinci naci kaɗan, sai kuma na fara jin kamar nayi wani kuskure. Wurin karfe uku Aunty Hindatu ta kira shi tana gaya mishi yadda Ya Hafiz ya rikice yana bin gida gida yana niman inda nake. Shiru nayi da Ya Almu yake gaya min yadda hankalin Ya Hafiz ya tashi ya rasa yadda zai cusa ranshi har Jama'are aka bincika ko ina can. Gashi yau aka yi wani hatsari a hanyar Jama'aren hankalinsa yayi mugun tashi. Sai jikina ya fara rawa na kasa zama ko na zauna zan tashi tsaye. Rike hannuna Aunty Saliha tayi tana faɗin. "Ki saka a ranki, zaki iya yaki da kanki idan kika koma kofar da zaki sake samu ki gudu ma ba zaki samu ba, ki nutsu ki gaya Allah kukanki, Hafiz ba shi bane karshen rayuwarki, kina da naki rayuwar ki sa ranki, zaki rayu!" Kuka na saka mata har ina shashekar kuka. "Zan koma kawai ya sake ni." "Yes muna tare dake, shi zai bukaci haka a yanzu kuwa kina komawa daga shi har su Abba ba zasu baki damar kare kanki ba, ina magana a matsayin daya daga cikin matan da suke yaƙi da matan da suke da irin matsalolinki ne, kada soyayyar da kike ji yayi tasiri a ranki, kwarai zaki koma amma dole muna buƙatar nutsuwarki." Dakyar ta shawo kaina nayi hakuri tare da rarrashina muka bar zancen Ya Hafiz ba a kara zancensa ba, kawai so suke nayi farin ciki. Kuma na yarda amma na kasa farin cikin. Yaron mai sunan Abba ana kiranshi Zunnur, ya dawo daga wurin Yayarta shi ɗaya Allah ya basu har yanzu dai basu kara sun wani ba koda yake yan boko ne Original masu hakoran Abcd. Sai dare da na shimfida hakarkarina na kwanta sai wasu abubuwan suka yi ta dawo min. *** *Mafari tushen kome* 2015- June/July JIBWIS Bauchi state. Yau ake bikin Yaye mu, kasancewar mun gama Jss3, zamu faɗa aji hudu na Senior secondry School. Wani abu guda uku yake tattare da wannan ranar yanayi uku yanayin da ba zan iya mantawa da shi ba. Sunana Lubabatu Usman Umar Jama'are, wacce ake kira Lubnah Shehu Usman Jama'are, Abbanmu haifaffen garin Jama'are ne na jahar Bauchi. Iyayena bakiɗayansu yan Jama'are ne, a unguwar kofar Fada. Gidansu Abba yana da tarihi domin suna cikin Kingmaker idan za ayi nadin sarauta a fada. Yan uwa da sauran dangi suna can. Abba wanda shine da na biyu a cikin gidansu Alhaji Umar Madaki yana cikin amintattun sarki kuma wanda ake damawa dasu a fadar, wato Kakanmu wanda muke kira da Baba Malam. Abba da Mama auren zumunta ne aka musu har zuwa yau Mama bata taɓa yaji ko wani abu ba, haka Yadiko wacce itama bata taɓa yaji ba itama yar kanwar Hajiyarsu Abba ne, Abba yayi karatun boko tun daga barewa College zuwa ABU zaria, akan ce kowani mutum da inda bakin rabonsa yake shi Abba ya karanci hada makamashi ne, amma yana gama bautar ƙasa ya kama kasuwanci, dama tun yana aji uku aka mishi aure da Mama, tana shiga ta haife Ya Ado, bata rufe shekara ba ta haifi Aunty Hindatu, sannan ta haifi Ya Umar, shima shekararsa daya da rabi ta haifi Aunty Innah, sai a lokacin Abba ya auro Yadiko sanin cewa dukkansu yan uwan juna ne sai suka zubar da kishi suka rungumi juna, itama Yadiko ta haifi Ya Tahir, bai cika shekara ba aka. haifi Aunty Munah wato aunty Maimunatu. A lokacin Baba Ali yana tare da Matarshi Hajiya Asiya yar garin Gyembu, wacce suka haihu tare da Yadiko tana goyon Ya Hafiz, kwatsam Abba ya tattara iyalinsa ya dawo Bauchi saboda ya samu aiki kuma ga kasuwanci, sai abin ya zo mishi da sauki ga aiki ga kasuwanci, Hajiya ganin yadda Abba yake ta gaba, abin ya d'aga mata hankali domin Baba Ali malamin secondry School ne, sai ta rena mishi tana ganin kamar gazawarsa ce ta haifar masa rashin arzikin har dan uwansa ya fishi, Bayan Baba Ali akwai Goggo Larai da Goggo Uwani, sai goggo talatuwa, su biyu maza sai Babarsu Goggo Alti. Abba wanda ake kiranshi Baban Bauchi bai taba zama ya manta yan uwansa ba, domin ko zuwan shi aikin hajji tare da Baba Malam da Goggo Alti suka je, lokacin duniya na kwance........ *Wannan book din paid na kudi* *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI* Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu *Littafin nan na kudi ne akan 1500* *1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 16 12 40 my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641 Posting Arewapen da Telegram SHA BIYU Shekara na dawowa ya biyawa Baban Jama'are, da Goggo Uwani da Goggo Takatuwa, suka tafi a lokacin ta Kano ake tafiya haka yasa a can suka tashi. Ko a Bauchi unguwar da Abba ya fara zama a ibrahim bako, haka ya zauna a lokacin yana aiki a ma'aikatan albarkatun kasa, sai da suka shafe shekaru goma sha biyar, lokacin an haifi Ya Almu da Ya Abba su kan tagwaye ne, Yadiko ta haife su Ya Almus shine Babba, Sai Aunty Raliyah tana aure a Jos, sai kuma Ya sani,da dan lokaci ya ja sannan aka haife ni, na samu gata a wurin Yayuna. Dakinmu bakiɗaya mu Biyar ne, Ya Ado, Aunty Hindatu Ya Umaru, Aunty Innah nice na biyar, dakin Yadiko kuwa akwia, Ya Tahir, Aunty Munah, Ya Almu da Abba, sai aunty Raliyah da Sani, bakiɗaya gidanmu Allah ya albarkaci iyayenmu da mu biyar ne. Haka muka taso cikin wani irin so da gata, ni dai ban san sanadin da Ya Hafiz ya dawo gidanmu ba, amma ma taso na ganshi a cikin gidanmu, kuma abin al'ajabi a dakinku, wato Ya Hafiz kyakkyawa ne tun ina Yarinyar na yi crushing dinsa, kuma bana kaunar na ga wata ta kula shi, Ya Hafiz bai da yawan magana, duk da lokacin da na fara wayo yayuna mata Aunty Raliya ce bata yi aure ba, domin duk yaran gidanmu suna fara jami'a a gida ne su karasa a gidan mazajensu. Haka yasa ita Aunty Raliya ba a Bauchi take karatu ba, a BUK ta karanci karatun jarida. Tana cikin karatun ta hadu da Alhaji Bilya suka yi aure, ni sai bana ce ba amma a wannan lokacin muka fara shakuwa dabYa Hafiz, domin kuwa an hanani zuwa bikin nayi ta rigima har na hakura. Idan na ce muku mun shaku tow ina nufin mun yi wani irin shakuwa da duk wanda ya ga yadda muke sai ya ji sha'awarmu, da farko Yayuna maza suna zuwa shagunan Abba, amma daga baya suka shiga barin shagunan daya bayan ɗaya. Na farko yar rigima ake tsakaninsu a shagon daga baya sai su bar zuwa shagon kuma dama kowannensu yana da abin yi, Ya Ado dama lauya ne, tuni ya samu aiki a Abuja ya koma abinsa sannan ya haɗa da kasuwanci domin abin ya same musu jiki. Ya Umar shima yana aiki da ma'aikatan shige da fice a nan Bauchi, kuma yana da wani shago da suke shigo da mashina, sai Ya Tahir, malamin makaranta ne Tatari Ali Polytehnin, yana sana'ar fitar da tsabar abinci. Ya Almu da Ya Abba, shi Almu sojan sama ne yana garin Kaduna, sai ya Abba da yake sojan kasa yana Maiduguri. Ya Sani dai ya gama karatu yana da shagon da yake kula da su na sayar da generator, Yayuna mata kuwa Aunty Hindatu tana aiki a babban Kotun majastir na nan Bauchi ita ce magatakarda. Sai Aunty Innah tana aiki a babban asibitin Bauchi babban nurse. Domin degree biyu gare ta, MBS. Duk yan gidanmu babu cimma zaune, kowa akan kafarshi yake Abba ya ji haushina yadda duk Yayuna suka ki zama a tare da shi, don haka ya kama Ya Hafiz ya daura shi akan kasuwancinsa, ban ce muna da kudi ba, amma muna da wani irin rufin asiri da duk wanda ya ganmu tow ya san mun fi karfin a wulakanta mu, wannan lokacin ni daya ce mace sai yar rikon gidanmu Jalilah yar gidan Goggo talatuwa, Babanta Yayan Yadiko ne. Abban ya Hafiz wato baban Jama'are ya hadu da hatsari wanda yayi sanadin da ya rasa ƙafarsa daya, haka yasa ya daina aiki Abba ya bude masa shago aka zuba kayan kudi, Hajiya Asiyah idan mace muku matar nan ayin kyau domin kaf yan gidan wato iyayenmu babu wacce ta kamo ta kyau, bafilatana ne amma irin masu burin nan. Duk da yan Gyembu ne sai dai mazauna Jama'are ne, yadda yayi burin Baban Jama'are ya kasance abin bai zo mata yadda yake ba, amma tayi making wasu abubuwan wanda daga cikinsu wofatar da Ya Hafiz, wanda haka yasa Abba ya dauke shi, Ya Hafiz ko nace yan gidansu basu son karatu, both mazan da matan. Da yake Allah yana yankarsu da tsada dakyar yan matan suka gama secondry School, su kuma mazan dama watsarwa suke su kama abinda zasu iya. Shagon da Abba ya budewa Baban Jama'are kuwa, Yaran da Uwar ne suka ruguza kome, Abba ya kara cika shagon suka sake lalatawa, ganin za ayi na uku Baban Jama'are ya ce a barshi haka shi dai zai koma noma, haka da yayi ya b'atawa Hajiya Asiya rai, Baban Jama'are mutumin kirki ne, haka yasa koda ya koma noman rani da damina, idan. Amfani yayi haka zai cika ya kawowa dan uwansa, shi kuma Abba sai ya mishi hanya yana cire amfanin gona ya haɗa shi da masu saya har da saya mishi motar da zata na wannan jigilar da shi, da yake yana da kafar roba da yake amfani da shi, Allah ya dafa masa kuma ya tsaya da kafarshi amma a haka Hajiya Asiya gani take bai kai Abba ba, shi kuma haka bai dame shi ba. Domin mutum ne mai yarda da Allah. Ya Hafiz shine Babba, Aunty Nana Asma'u ita ce take binsa Sai Ahmad Tijjani, yake bin Aunty Nana, sai Babangida, yake bin Tijjani, sai Yahanasu, kafin Firdausi. Ita Aunty Nana tana auren wani dan siyasa a can azare, sai Yahanasu itama wani dan abokin Abba take aure suna River State, sai Firdausi da take tsalle tsalle taki zaman auren domin Allah ya mata ruwan kyau. Ya Hafiz yadda bai samu soyayyar mahaifiyarsa ba domin kuwa bata janyo shi a jiki ba, sai da ya zama mutum, nan ta fara nunawa ita fa danta ne, babu wanda ya damu shima a lokacin bai da uwa sama da Mama da Yadiko, domin yana da gaskiya da rikon amana, duk inda Abba yake shiga Ya Hafiz ya sani duk inda Abba yake niman kudi Ya Hafiz ya sani. Kome na Abba ya sani kuma haka yasa shi kara samun yarda har da na dangi domin idan ba Abba bane ya ce yayi wani abu ba zai tab'a yi ba. Shima Abba yana ganin kamar dan uwansa ne a tare da shi, domin kaf halin Baban Jama'are Ya Hafiz ya kwashe bai bar kome ba. * Haka na taso da wani mahaukaciyar kaunar Ya Hafiz da fari ni doguwa ce, sannan a yanayin yan gidanmu bamu da irin jikin nan da zaka ga mutum kato, a'a muna da yanayi jikin fulanin Jama'are, sannan gidanmu yanayin kowa daban, yanayin dakin Mama mu fatarmu tana da dan duhu, yayinda dakin Yadiko Fatarsu take da haske, haka yasa idan ka gan mu zaka yi ta mamakin yanayinmu. Wannan shine labarin dangina da gidanmu. 2015- June/July. A karo na uku na lashe musabakar Alqur'ani, na fara shiga tun ina jss 1, sannan wancan satin mun Quiz and prize, na kasa a garin Abuja wanda na wakilci makarantarmu, tare da rakiyar Yayuna. Allah ya zuba min rawan kai surutu uwa Uba tsokana da son ayi da ni, gashi yau mun yi bye bye da Jss3. A lokacin ina fama da tashen balaga, wayyo kusan kwaila da rawan kai, haka muka shiga makaranta mu hudu team dinmu, nice a gabansu na juya ina kallonsu ina musu bayanin yadda Abuja yake, sai ji nayi kamar nayi kawo da mutum. Na tafi kamar xan fadi, na ji an tare ni. Da yanayin wata gaurayayyen hausa mai mix da fulatancin da ta kama harshe tare da wani guntun fashion English aka ce min, "opps i hope baka ji ciwo ba!" Sai ce min sannu yake, da wani irin murya me sanyi. A hankali na matsa ina faɗin. "Ba kome!" Na riko hannun Rumana muka yi gaba sai juyawa suke suna kallonsa, ni kuwa naki juyawa don bana ce ga yanayinsa ba sai dai yadda gabana yake faduwa yasa na yi saurin janye su muka shiga cikin Makarantar. Bikin yaye dalibai yayi kyau domin nima naci lamban yabo kala uku, a cikin kuwa har da kyautar kudin da na samu, saboda zama na daya da anyi a ko ina. A wannan ranar mai cike da tarihi har Makarantar Ya Hafiz ya zo ya dauke ni a ranar da ya fara sayan mashin dinsa Simba, tun muna Jss1 kawayena suka san da zancen Ya Hafiz. Rumah Rabi'u Mai shanu, Hafsah Faruq Babaji, Nafisa Sadi Gital, sai ni Lubabatu Shehu Umar Jama'are, sau dayawa cewa ake sunana yayi tsawo ni kuwa ban tab'a ganin tsawonsa ba. Wani lokaci shafin ƙaddara tana budewa a rayuwarmu, ba tare da mun sani ba. Idan da ace wani abun mun rike tow ba makawa da ba zamu manta da shi ba. Haka muka sha hutu, sannan muka dawo. A lokacin na dawo da wani irin yanayi na ciwon mara na al'ada. Sati na biyu da dawowa, da yake ban yi al'adar da wuri ba sai da na shiga aji na hudu, sannan ranar ita ce ranar da na fara, ciwon ciki kamar zan mutu, zufa nake yi tare da jin wani irin zazzaɓi ya rufe ni, ga ciwon ciki kamar xan yi amai. Sabon malamin Chemistry da aka kawo mana ya shigo ya fara kiran sunan kowa sannan shi zai zame mana Form master dinmu, a hankali ya fara kiran sunayen mu, har ya zo kaina ya kira sau biyu ban iya d'ago kai ba, sai da ya kara kiran na uku Ruma ta ce mishi. "Sir tunda tazo gata nan bata da lafiya!" A dan hanzari ya kalle da wurin da ta nuna, a hankali ya karasa wurin ya ɗan taɓa desk ɗin a hankali na d'ago kai kafin ya tambaye ni na sheka mishi amai a jikinsa bakiɗaya, sai a lokacin na zaro idanu ina kallonshi. "Sorry how are you feeling now?" Shine tambayar da yayi min, kasa magana nayi ina rike da cikina. Shiru yayi na wani lokaci kafin ya mike ya fita can sai ga yan ss3 sun shigo tare da shi har ya sauya kayan, wata jamfa ce a jikinsa golden yellow, yana shigowa ya ga yadda suke ta irin kyamar tabani. " Me kuke yi haka? " Takawa yayi yana kallon yadda suke son taba ni don ni kaina nasan a i mess up, duk aka rasa dabarar da za ayi min sai gashi an buga break, yan class suka fita a dudduke na mike, dawowa bayana yayi zai magana yadda zasu rike ni ya ga hatta hijab dina ya baci da jini! " Look koma ki zauna!" Haka na koma na zauna ina jin wani irin ciwo ya ce yan matan. " Ku tsaya ina zuwa!" Haka ya fita can sai gashi tare da Malama Malika ta Jss3, dauke da sabon hijab dal a hannunta ta sallami yan matan sannan ta ce min.. "Lubnah sannu ko!" Gyada kai nayi, ta bani hijab din na saka, sannan ta dauki wancan ta saka a leda, ta riko hannuna muka fita waje, motar Principle aka saka ni, muka wuce gida, ban san ya aka yi ba sai da nayi sati sannan na dawo lokaci na warware, Ya Hafiz yake kawo ni. Tun daga lokacin Malamin nan ya saka min idanun, sannan shi ya rubuta min note akan duk ranar biyar ga wata, matukar ba jarabawa ba ne ba'a bukatar nazo makaranta idan kuma nazo, na fara zuwa clinic na makarantar na amshi magani da sanatery pad ni sai ya shiga sani jin kunya haka kawai zai saka ni jin na zama yar iska, akwai wani program da kamfanin Always suka yi a lokacin, tabbas sun bamu kyautar pad din, haka na ga mutumin nan yana kallona. Ni tun a wurin nayi kyauta da shi domin na tsani yadda yake bina da idanu. Sau biyu na taba kallonsa, idan na Ganshi bana iya d'aga kai na kalle shi domin zubi yake min da gardawan almajirai. A gefe guda soyayyarmu da Ya Hafiz kamar mu cinye kanmu, haka yasa yan gidanmu suke ta ganin ina gama secondry School za'a aurar da ni, ban damu ba. Amma kuma zuwa lokacin da muka shiga ss2 mutumin nan ya fara damuna, don ya saka min idanu yadda ni ban zata ba, sannan duk wani abu nawa yana jin sa ne a bakin Ruma ita kuma sai Allah ya daura mata sonshi da ni, ita tayi ta ziga ni har na fara kula shi, amma ba a makarantar ba a gidan Aunty Inna, domin a lokacin Aunty Hindatu tana tare da Ya Hafiz, Nafisa Sadi Gital kuwa cewa tayi na ci kuɗinsa kawai don mun lura wallahi kamar bai da wayo, duk abinda zance ina so zai bani, kuma bai taɓa jin zafin cire kudi, Yaran Aunty Innah kuwa wani irin kashe musu kudi yake domin ni a wurinsa na taɓa ganin wasu chocolate. Amir dan Aunty Innah ya cika shekara biyu, nake gaya mishi ai sati na zagayowa sai ga tarkace har da Cake, lokacin Blackberry sai wane da wane ina fama da wata yar Nokia da Ya Hafiz ya kure a daka ya saya min, sai ga Malam Bilal ya kawo min sabuwa dal, ai kuwa Aunty Innah yana kara zuwa ta mai da mishi ya ce shi me zai yi da shi, dukkanmu kallon mai fama da albashi muke masa, bana sonshi domin Ya Hafiz ya cika min raina da soyayyarshi. Lokacin da muka shiga Ss3 ya gabatar da kanshi a wurin Abba, maganar gaskiya Abba ya amince da shi amma lokacin da ya tambaye ni, kai tsaye na ce ni fa Ya Hafiz nake so, shima kuma Ya Hafiz din ya amince ni yake so, haka da ya kara dawowa Abba ya bashi hakuri tare da gaya mishi an tsayar min da miji domin ya tambayar da yayi min na gaya mishi gaskiya. Koda na je makaranta na samu sakon yana min fatan alkhairi, Malam Hamza Adam ya kira ni office dinsa ya min.. "Lubabatu gaya min me yasa bakya son Malam Bilal?" Shiru nayi ya rasa yadda zai saka ranshi.. "kin san waye kika yi rejected dinsa kuwa? Kin san waye shi? " Kasa kasa nace mishi. " Kayan lambu ne da zan tsaya dai ya nuna zan zabe shi. Ni ina da wnada nake so!" " Wanda kike so kin san waye shi? " " Dan uwana ne fa! " Na fada ina ɗauke kai daga kallonshi. " Shi kenan Allah ya baku zaman lafiya!" Daga haka na mike na bar mishi office din. Kafin mu gama makaranta na ji labarin wai ai ɗan masu arziki ne, Malam Hamza ya gayyace shi bikin Yaye dalibai shine ya zo. A bakin Ruma naji wacce ta ce min ya bar min sako a wurinta. " Ki rike na baki sakon da ya bani! " Tayi ta mamaki. Haka muka gama makaranta na manta da shi domin ya cikin lissafina, a 2017 muka gama har da Jamb, na kuwa cika ATBU, ba laifi point dina ya ja, suka bani business administration, a shekarar da na fara a wannan shekarar Ya Hafiz ya kawo lefena da sadakina har dubu hamsin, duk da a lokacin sadaki yafi haka amma ba yanke mishi ba, Dangina kowa ya goyi bayan auren Yayuna maza da mata kowa yana san barka, haka yasa bikin ya zama irin na yar gatan

Chapter 9 of 13