Share this page
ki diba musu tsaraba nan, akwai wasu a dakin Karimah bari na kawo sai ki hada musu." Ya tashi ya fita, can sai gashi dauke da jaka cike da fruit, ya kawo musu da Naira dubu goma a ciki wai su yi kudin abin hawa, Aunty Innah ce ta kawo su a motarta, bayan fitarsa da ya ce musu bari ya tafi muda lawan akwai kayan da aka kawo zai je ya duba, ya fita Aunty Innah ta kalle ni yadda nayi shiru. "Tunanin me kike yi?" Ta ciro kuɗin da yake cikin jakar ta ajiye min a gefena. "Mu yan uwanki muna jiranki duk lokacin da kika shirya ba zamu kashe miki aurenki ba!" Tana gama fadar haka suka mike tare da barin kayan ma bakiɗaya basu dauka ba, domin tun kafin su fita Karimah ta fita da Yaranta, aka bar ni a gidan ni daya tal. *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI* Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu BAKWAI Zama nayi ina nazarin makomar rayuwata, me nayi na kuskure? Duk da ina son Ya Hafiz amma ban san me yasa yake jin dadin daura min laifi ba, shi ya hana ni gayawa mutane, yanzu yazo yana faɗin ni ce me yasa yake min haka ne? Me yasa tow? Dama soyayya tana zama kiyayya ne? Ina cikin wannan tunanin Baban Bauchi ya kira ni, wato Abbanmu yayi ta min fada yana faɗin nayi haka ne don ba lalata zumuncin da yake tsakaninsa da ɗan dan uwansa, wallahi ban isa ba. Haka ya gama fadar shi nace mishi yayi hakuri. A hankali kuka ya zo min can kuma na fara dariya kamar mahaukaciya, domin haka ne kawai zai saka ni jin dadi. Tunda na fahimci dariyata tafi kuka saka ni nishadi, na saka a raina na daina kuka akan Ya Hafiz, zan yi dariya. Aunty Hindatu ta zo ita da Ya Sani suka ga gidan, babu wanda yayi magana har suka fita. A ranar Aunty Hindatu ta kira Ya Ado ta gaya masa. Murmushi yayi yana faɗin. "Hindatu dadina dake baki da hakuri, mutane biyar suke da iko akan wannan lamarin Baban Bauchi, Baban Jama'are, baba malam, sai ita Lubnah idan ta ce bata yi duk inda nake zan kwana a Bauchi, amma fa sai ita da kanta ta ji a ranta bata yi duk abinda zamu yi ba yadda muka iya.". "Amma kasan ya sayar mata da gidanta na Tambari?" "Tow ya za ayi tsakanin mata da miji sai Allah idan ita ta bashi fa!" "Ado kasan sai Lulu bata da hankalin da zata bashi gida ya sayar ko? " " Tow waye ya sani kin ga idan tana bukatar wani abu ayi magana batun gida dama ai an saya mata ne domin su huta da Yawon gidan haya tunda ya sayar ya sayi wani." " Amma ai a getto area ne! " " Ba gashi ta zauna har na wata guda ba ta gaya miki ne?" Shiru tayi ya cigaba da magana. " Baba da Mama sune suka involved din rayuwar Lubnah, idan da zasu tsaya mata Lubna zata samu yanci amma fa sai taso idan bata so ba, kuwa koda su zasu shiga ba zata matukar bata bada hadin kai ba. Babu yadda zamu karshe sai dai shara'a tayi aiki kanmu haka magatakarda kin manta da dokar ce. " " Ba dokar na manta ba, na hango tashin hankali da bukatar taimako, bata bukatar kome amma kuma idanunta yana kukan tsoron da niman taimako, wallahi Lulu da ka sani ba ita ba ce a gabanmu" Dakyar ya shawo kanta Ya Sani ya ce mata, "Ni dai na rasa me shegen Yaron nan yayiwa Abba ne da baya kaunar laifinsa, ki ga yadda Lulu ta koma don Allah? Ko ni da nake zukar wiwi wallahi ban ga dalilin dariyar da take ba, ki ga yadda take abu kamar wacce take cikin tashin hankali." Kwafa yayi suka cigaba da tafiya, *** Ko Ya Hafiz ya ji abinda yake faruwa ne, yadda Yayuna suka fusata, sai gashi ya tafi har Jama'are wurin Kakanmu, suka tawo tare yadda mutumin nan yake da mugun hali na tsane na bude idanun na ganshi, domin shima ya taka rawar lalata min duk lissafina, haka yayi ta fada da nuna kada ya ji kada ya gani domin yaji labarin ana son a kashe auren Lubnah da Hafiz, idan suka kashe auren waye zai aure ni? Sannan ga misali a gabansu Jalilah tunda aurenta ya mutu waye ya zo da sunan zai aure ta, kada ya ji kada ya gani. Abin da basu sani ba ita Jalilah Ya Hafiz take so kamar tayi hauka, duk aurenta uku da tayi ta kasa zama a gidan aurenta ne domin tana da yakinin wata rana ya Hafiz xai dawo gare ta. Haka abin ya cigaba da tafiya ba dad'i, a lokacin Ya Hafiz ya tsiro da wani hali shi da Matarshi. Abinda suke mun ba kome ba ne, sai nuna min da suke ni rayuwata bata da amfani, domin ido da ido ya ce min. "Lubnah baki da amfani a rayuwata, amfaninki kalilan ne, idan aka cire amfanin rashin amfanin yafi yawa, kin ga wallahi ko bukatarki na dabi'ar da namiji bana ji, ke kanka dube ki, yanzu ace na sake ki waye zai aure ki? Wallahi babu namijin da zai tab'a sha'awar aurenki domin baki da wani abin burgewa mace sai kace saniyar huɗa! " Ire-iren waɗannan maganar da yake gaya min ya haifa min da wani irin yanayi. Yana yawan gaya min cewa a yanzu dangi ma basu bukata na, babu wanda ya damu da ni, itama Hindatu don kudina da yake hannunta ne, idan babu ba zata kara kula ni ba,haka muka cigaba da jin kamar ba ni da wata amfani a rayuwar Ya Hafiz. Tunda ban haihu da shi ba, bani da wani abun da zai burge kowa. Ni kaina nasan be zama dole wani ya bukaci ni a rayuwarsa ba. A hankali na dinga jin kamar ni din ba kowa ba ce bani da sauran amfani. A haka watan azumi ya karato, ba zata Baba yayi mana, ya biya mana umara ni da Yayuna. Sai dai me? Ya Hafiz najin haka yayi ta kunci da bakin rai tare da rigima da fitina kala-kala, karshe dai ban san yadda aka kare ba Baba ya ce ya cire sunana a cikin masu tafiya yayi replace da Jalilah. Wani irin bugawa zuciyata tayi kamar zata fito, a hankali na kama dariya ina jin kamar ni daya ce bani da amfani a duniyar nan, haka watan azumin nan suka yi shi a can ni ina gida, a lokacin na kara koyan yadda xan bawa kaina nishadi. Sai na fara tunanin sana'a bayan sallah, wanda shima a wunin sallah ya ce ba zan je ba. A Jama'are zamu yi sallah, nan ma na amince muka tafi. Muna dawowa nazo da madaran kuka. Na fara sayar da kankara da Pure water, ta nan bai hana ni ba. Sai dai ya daina bani kudin cefane. A hankali na kara har da zobo da kunun aya da fresh milk. Haka su Aunty Hindatu da Aunty Innah suka zo min gidan, wuni da Yaransu nayi ta hidima gashi bana iya zama idan nayi baki abu ba abu ba sai dariya. Haka suka yi ta kuka a daki, wunin da basu yi ba kenan. Wani abin da na fahimta shine Ubangiji ya saka albarka a kayan ruwa, domin lokacin sallah layya, nayi ciniki har na ji tsoro, ana kawo min ruwan pure water har gida ake sauke min rabin mota, a lokacin da Ya Umar yazo gidan ya dauke karamin firji din a ranar aka kawo min babba deep freezer, wnada nake zuba jakan pure water ashirin ga kayan sanyina a gefe. Yadda kudi suke shiga da fita yasa Ya Hafiz ya fara tashin hankali na fara kudi xan rena shi, idan nayi abinci bana saka nama a wadace ai da can ba haka nake ba, nayi ta bashi hakuri ashe zai zare min tallafi da yake ne, domin ya daina kawo abinci gidan. Haka dai na kara tsayawa a tsaye sai Allah ya yaye mun dariyar da nake, sai dai duk niman da nake ina bawa Ya Hafiz ne domin bayan na cefane da nake yi kudin kusan shi nake bawa. Maman Na'ilah ita ce ta tambaye ni aron kudi, na ji tsoro ban iya bata ba. Karshe kamar wacce ta matse ni na gaya mata ai kudin wurinsa yake, zuba min idanun tayi kafin ta ce min. "Lubnah da hankalinki kuwa?" Shiru nayi kafin ta cigaba da cewa.. "wacce irin soyayya kike yiwa mijin nan naki ne? Kin san mun san kece kike dauke da hidimar gidan?" "Ba kome ai dan uwana ne." "Na ji ba wannan ba, daga yau zaki na kawo dubu uku akwai adashe da muke yi zaki shiga ai zaman tare ta wuce haka, ga yayarki nan wata siririya muna haduwa a asibiti ba karamin taimako take min ba, don Allah ki na kawo kudin! " " In sha Allah!" Na fada tun daga ranar ban yarda na kai mata ba, domin kamar wanda aka gayawa Ya Hafiz, kullum sai ya kirga abinda nayi yasan na kudin da yake ciki, idan ya dawo zai tambaye ni. Haka zan dauki kudin cinikin na bashi na mishi lissafin abinda aka kashe, ita Matarshi bata kome ni ce dai akansu, haka dai muka ta mikewa abin ba dad'i, kwatsam aka tashi wani biki, Aunty Innah ta kawo min aikin Kunun aya da zobo, domin suma ina bayarwa a kai musu har gida, a lokacin aikin zai min yawa na shiga gidansu Maman Na'ilah na roka su zo su tayani. Haka muka yi aikin dasu. Sannan ka zo aka dauka, washi gari muka sake yi sai da muka yi kwanaki uku muna aikin kafin aka kawo mana kudin aikin naira dubu hamsin, na dauki 20k na basu talatin, Maman da tazo ta kwace ashirin din ta tafi da shi, ban san me yasa matar nan take min karan tsaye ba, amma naji haushi, wasa wasa sai ga Mamansu Na'ima ta saka ni a gaba da amsar kudina ko ina so ko bana so zata dauka, haka muka yi ta fama da ita daga baya da kaina nake tura mata kudin ma, ta daina zuwa. Ban san manufarta ba amma tabbas ta wani gefen tayi min abinda jinina suka gaza min. Haka watan azumi ya kara zuwa, ita ta bani shawarar na ajiye kayan zaƙi na koma sayar da ƙanƙara. Ba sai ya Hafiz yayi tsaye ya ce bai yarda ba. Sai dai idan zan sayi generator, na ce mishi. "Ya Hafiz tow ka ba Ni a cikin kudin wurinka mana!" Ai kamar ya rufe ni da duka. "Ba zan bayar bada wutar gidana kike amfani." A lokacin na rasa yadda xan yi ina jin kunyar amsar kudin wurin Maman Na'ilah, sai na kira Ya Sani na tambaye shi nawa ne kudin generator? Tunda sune suke sayarwa. Ashe nayi wayar a kusa da Ya Albashir, sai cewa yayi me zanyi da shi? Na gaya mishi gaskiya washi gari sai ga Mikano daidai da zata dauki freeze na har da karin freeza. Nayi ta godiya aka turo masu aiki suka min aikin tsaf na sauka akan wutar gidan Ya Hafiz shima dai ai yana morar generator tunda kowa yasan watan azumi a lokacin nepa suka tadda iskancinsu, ga lokacin ana wani irin agazarin rana. Duk yadda xan fada farin cikin da nake ciki, kamar na boye ne. Ganin duk yadda zai ɓullo min ina toshe hanyar don bana son muna rigima, ba sai ya tsiro da fitinar cewa sai dai na kama haya dakin da nake ina biyan kudin wata wata da ruwan da nake tarawa a wajen shima ina biya. Haka na amince na ce nawa xan biya? " " Duk wata dubu goma! " Shiru nayi kafin na ce mishi.." tow Ya Hafiz ba ragi ne? " " Sai dai ku fitar min da kayanki a gidana!" " Shi kenan! " Haka na amince ai ba wani abu ne, haka nayi ta niman kudi ya Hafiz yana amsa da sunan nashi, da sallah yayi nayi musu ɗinkin sallah don ya ce min hakkina ne nayi musu tunda ai ina samu, nayi mishi nayiwa Yaranshi da matarshi da Yan'uwansa na tura har Jama'are aka kai musu, har da Baban Jama'are nayiwa Baba Malam ne ko da wasa ban mishi ba, ai kuwa na sha zagi ya kira Baba ya gaya mishi, Hafiz ya bani kudi nayi musu kayan sallah amma naki, haka Ya Hafiz ya fada. Sannan ya kara da cewa har su Mama da Yadiko nayiwa, amma a kuɗina a lokacin sai da na kwashe kome nawa na sayar har da dan kunnen gwal dina, tow bani da kudin ina sana'a kudin na hannunsa. Bayan sallah ina cikin azumi sitta shawal, na fara sauraron karatun Malam Albani Zaria, akan khulu'i wanda ban tab'a jin kalmar ba sai yau. Ba dai na kara nutsuwa ina sauraren dalilan da suke kawowa ayi shi.. *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI* Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu PAID BOOK TAKWAS Wato akwai wani abinda hankalinmu baya kai sai wani dalili mai girma ya shato shi cikin rayuwarmu, ban tab'a nazari akan khulu'i ba, amma kuma me yasa na damu? Me yasa nake son sani akanshi? Kawai sai naji abin bai min na cigaba da nazari akai ba, kawai zan cigaba da zama da fahimtar iyayena. A bangaren Ya Hafiz kuwa nadan wata rana zai dawo yadda muke zai kaunace ni sama da baya, amma kuwa zai yi haka. Bayan sallah da sati uku. Weekend Ina aikin hada zobo na dauke tukunyar fresh milk, koda yake ya jima da na sauke amma da yake yana da wuyar sha'anin, sai na ta saka idanun akanshi saboda Yaran nan da zarar na sauke tukunyar fresh milk sun ta kara kaina akai kenan, har sai na hada na basu. Hankalina yana kan zobo wanda nake ta saurin haɗawa. Sai naji an tab'a murfin tukunyar, da sauri na juya Yusrah ce rike da kofi ta bude tukunyar fresh milk din zata har ta saka kofin ta dibo da yake na juya mata baya, a matuƙar razane na kalle ta ina faɗin. "Gaskiya Yusrah bakya jin magana maza rufe min ki mai da kafin na zo wurin." "Ba zan mai da ba." Ta fada tana kallon cikin kwayar idanuna, abin da ya bani haushi da takaici yanzu ta kone Iyayenta su ce na konata. Mikewa da zan yi kuwa ta kwasa da gudu ai kuwa sai gashi ta taka ledar Bevimix ta zame bakiɗaya fresh milk din ya kware a gefen kirjinta, abinka da zafi sai kuwa ta fasa ihu wanda yayi daidai shigowar Mahaifinta da fitowar Uwarta a dakin, wani irin bugawa zuciyata tayi na tsaya cak kafin na karasa da sauri nace mata. "Kin ga abinda nake gaya miki ko?" Na yi maza na shiga daki na dauko kamun da aka niko min zan yi kunu na sha na watsa mata a kirjinta bayan na cire mata rigar, bakiɗaya iyayen babu wanda ya ce min ci kaina. Haka na zaunar da ita na cire mata rigar ba wani tashi wurin ba, amma yadda take kuka da ihu yasa Uban ya karaso ya bangaje ni sai da na fadi, sannan ya dauki yar ya fita da ita, wasa wasa basu dawo ba har dare habaici da cin mutumci babu wanda Karimah bata min ba, ni dai bance mata uffan ba, wajen karfe biyar Mama ta kira ni. "Kin kyauta Lubnah wacce irin kishi ne haka yake damunki?" Bata ba ni damar magana ba. "Saboda kishi zaki kyale yarinya kamar Yusra ta kona kanta?" Ni dai ƙasa magana nayi har sai da Mama ta ce min. "Saboda mugun nufinki Allah ya hana ki haihuwa domin da ya baki da Yaranki zasu dauki mugun halinki!" Komawa daki nayi na zauna shiru. Haka Baban Bauchi ya kira ni ya ce sai ya ga wanda ya isa min, wasa wasa sai ga al'amarin ya girma yadda ban zata ba, yusrah kwantar da ita aka yi a gadon asibiti. Sannan wacce take gudun Mama ce. A wannan lokacin na ji duniyar ta min zafi, kaf duniya mutum daya ce ta fahimce ni Aunty Hindatu, dole na bawa Aunty Hindatu special respect a duniyata, ita kaɗai sai Ya Ado suka fahimci abin domin abin ya faru da kwana biyu Baban Bauchi ya zo har gida ya saka aka kwashe kayan sana'ar aka fita da su. A wannan lokacin Ya Hafiz ya zata ni yayiwa mugunta. Ya zata ni ya rusa tabbas ya Hafiz ya rusa ni, sai da na kusan zarewa domin babu wnada ya saurare ni, kowa ya juya min baya sai Aunty Hindatu da ita ɗaya ce take rarrashina, kwana Yusrah biyar a gadon asibiti Hajiya da Baban Jama'are suka iso a ranar Karimah ta dauki matakin da Baban Bauchi ya goya mata baya. Ina zaune wurin karfe biyu na rana aka yi sallama a gidan, fitowa nayi ina amsa sallamar. Yan sanda ne mata biyu suka shigo. "Sannunku da zuwa!" Yadda nayi magana a matuƙar tsorace. "Kece Lubabatu Usman Umar Jama'are?" Jikina ne ya dauki rawa. "Eh nice!" "Ok ko zaki zo muje office din Yan sanda!" Ji nayi kamar ina yawo a saman iska. "Akan me zan bi ku Office dinku bayan ban yi kome ba?" "Eh tow idan muka je zaki ji abinda ya faru!" "Tow bari na kira mijina;" na shiga kiran Ya Hafiz amma bai dauka ba, haka nayi ta kiran Yan uwana har Baban Bauchi na kira Babu wanda ya dauka, sake magana suka yi na fito ko su shigo dakin. Haka na fito a sanyayye da hijab har kasa. Ina kara kiran Aunty Hindatu. Daidai na shiga bayan motar. Dauka tayi tana faɗin "Auta yi hakuri bana kusa ne!" "Aunty Yan sanda sun zo zasu tafi da ni!" "Akan me?" "Ban sani ba Aunty! Don Allah ki zo!" "Shi kenan gani nan zuwa!" Haka ya kashe wayar muka Office din Yan sanda da yake dutsen tanshi, anan na samu Karimah ashe shirinta kenan ita da Uwanta da iyayenta, muka shiga suka amshi wayata da kome suka tura ni cell suka ki min magana, ina zaune wata yar sanda ta shigo ta d'aga hannu tayi ta kifa min mari, yan uwan Karimah suna faɗin. " Saboda kishi ne ita Allah bai bata haihuwa, koda yake ta kashe mahaifarta da maganin hana daukar ciki shine bari ta kashe yar kishiyarta, Allah ya sa yarinyar ta auna arziki!" An tozarta ni, an ci mutuncina haka na kasa ko kuka sai sunkuyar da kai da nayi idanuna bana gani. Muryan Ya Hafiz da naji yana ta fada a waje. " Akan me zaki shigo da hukuma cikin maganar? Ko an gaya miki ban san yadda zan yi ba ne? Gaskiya kin bata min rai yanzu da wani idanun xan kalli iyayenmu?" Yadda Ya Hafiz yayi ruwa yayi makarbiya yasa ni shiga rud'ani amma ai ya ga kirana. Fada sosai yayiwa Karimah, Aunty Hindatu da Ya Umar da Ya Albashir suka karbi belina, haka na fito kamar wacce ruwa ya mata duka, fuskana ya dan kumbura saboda marin da yar sanda tayi min. A hankali nake takawa har wurin motar Ya Hafiz da ya nuna shi xan bi na je nayi wanka. Haka muka bar office din zuwa gida, a hanya yake cewa. " Kin san ina sonki, sannan abinda ya faru nasan bakida laifi Yusrah ta gaya min, amma kuma ita mahaifiyarta ba zata ji dadi ba idan na nuna baki da laifi don haka ki amshi laifinki ta haka ne kawai zaki wanke kanki kowa zai gane cewa bada wata manufa kika yi ba!" " Ya Hafiz me yasa?" Na tambaye shi, " Me yasa ka zabi kuntatta min? Me nayi maka da yake damunka har haka? A sanina ban maka wani abu ba? A sanina ban cutar da kai ba, ina saka ran wata rana zamu koma kamar baya kamar farko-farkon aurenmu, Ya Hafiz duk irin shirun da nayi na cancanci haka daga gare ka?" Shiru yayi da alamar maganar ya ratsa shi kenan. " Ka saka kowa ya tsane ni, ka saka kowa yana jin haushina, idan abu ya faru ba zaka gaya musu gaskiya ba sai ka bar maganar a daura min laifi me yasa sai ni? Ya Hafiz rabon da ka nemi ni a shimfidar aurenmu shekara kusan guda dawowarmu zango na gaji wallahi na gaji ka sawwake min nima na gaji!" Na fada ina kuka domin sai yanzu nake jin kamar bakina ya buɗe. " Ko na sake ki ai baki da wanda zai aure ki? Lubnah ki kalli kanki da kyau har abada babu namijin da zai tab'a jin sha'awarki, Lubnah na ajiye ki ne domin kowa yasan ina ƙoƙari da mugun halinki, ke har kina da bakin da zaki gaya min magana? Bayan na rufa miki asiri ne, jaka me kama da alade kalle babu abinda wani zai gani na burgewa a tare da ke kazama wawuya, kuma daga hau sai na hana ki farin ciki." Haka muka isa yana zagina da cin mutuncina har nayi wanka kai karewar masifa kofar ban dakin ya shigo yana cin zarafina. Haka na gama na shirya muka tafi cikin gidan inda Yusrah take da iyayenmu, anan ya min barazanar matukar nayi magana sai ya sake Baban Bauchi wato Babanmu ya tsine min shi kuma ya sake ni domin ba zai zauna da tsinanniya ba. Lokacin da muka isa gidan Baban Jama'are yana nan haka Hajiya ma, sai Iyayena da yan uwana. Tunda na zauna aka bude taron da Addu'a. Aka rufe ni da fada babu wnada ya ji yadda kome ya faru haka na sunkuyar da kaina ina jin Baban Bauchi yana faɗin. " Munafuka ban da kishi da munafunci me kika ajiye ace har degree gare ki ya zama na banza. Sai bakar kishi tow da abinda kike takama da shi na kwashe dama yana gaya min tunda kika fara sana'a kika sauya bakya jin maganarshi, kin yi sabi iyaye masu daura miki mugun abu akanki wallahi kin ji kunya." " Amma Baba ya kamata a ji me ya faru? " Inji Aunty Hindatu, da take wani irin cirra, juyawa yayi a fusace ya zabga mata harara, ya rufe ta da fada da cewa ai ita take zuga ni, haushi ya sa ta bar parlourn ma don bakin ciki haka Baba Malam ya amshi fadar yayi ya ce min. "Yanzu kin kyauta abin da kika aikata? Da Asiya kike kishi ko da Uwar Asiyah? Yanzu ban da mun fi karfin yarinyar nan ina sai dai kotu ta shiga lamarin nan?" "Malam wallahi ban san cewa haka dai faru ba,.Malam na rantse da Allah ban yi haka domin kona yusrah ba yayi hakuri ba da gayya ba ne!" Zuba min idanu Malam yayi yana faɗin.."Allah ya kyauta amma ina amfanin kishi irin naki? Akan ki aka fara kishiya ne?" Cikin shashekar kuka na ce mishi. "Wallahi ban san zata shiga ban dakin ba, ka yarda da ni!" "Kai yanzu Hafiz me ka gani?" Juyawa yayi ya kalli Baban Bauchi wato mahaifina ya ce mishi. "Duk abinda Baban Bauchi ya ce ai shi kenan!" "A'a Hafizillah kada ka cutar da kanka, na ga ƙoƙarin zaman da ka yi da Lubnah idan ba zaka iya da mugun halinta ba sakota na gaji da kullum ana abu daya a cikin shekaru goma kullum Lubna tana saka ni magana." "A'a Usman, Lubna ko bata auri Hafiz ba, akwai alakar jini balle kuma alaka ce da ta haɗa da ta

Chapter 6 of 13