Share this page
nan har yau baki sauya ba." Murmushi nayi na koma inda Yadiko take alola na durkusa har kasa na gaishe ta. "Da fatan da izininshi kika fito? " Gyada kai nayi ina kallon kasa. " Tow sai ki gama ki koma da wuri don unguwarki da nisa!" " Haba Yadiko daga zuwa kamar mai ɗaukar wuta sai a fara mata maganar ta gama ta koma! " Inji Aunty Munah, daga can dakin aka ce mata. " Ai baki ga kome ba, sannan yadiko ta mata da kauna tsaya ki ga yadda Mama zata mata. " Inji Ya Sani da yake dakin yana cin abinci. Ya fito dauke da plat din abinci, " dube ta kamar Bakuwa" ya fada yana mita. " Aunty xamu tafi sai mun kara shigowa. " " Ku tsaya mana! " Na fada ina buɗe jakata na dauko dubu daya na mika musu. " Ban san zan ganku ba, ban saya muku tsara ba;" " a'a yayi yawa mun gode ko Waheed! " "Maza karba kafin na saka ki wanke gidan! " Inji Ya Sani, karba suka yi tare da fita da gudu suna godiya. " Mama tana ciki? " " Eh! " A hankali na ja kafa na nufi parlournta zuciyata tana wani irin tsalle. A hankali na shiga parlourn tana addu'a, ga Aunty Hindatu da take ta fama da laptop dinta. "Yar renin hankali tun yaushe na gaya miki bata da lafiya!" Zama nayi a gefenta, tare da daura kaina a kafadarta. "Am soweer." Na fada ina wasa da yatsuna. Shafa addu'ar muka yi abinda ya fito a bakin Mama yafi kome dukana.. "Me ya kawo ki? Da izinin waye kika tawo? Bayan ko yau sai da Mijinki ya gaya mana baya gari idan ya dawo zaku zo tare." Wani irin abu ne ya tsaya min a rai, yaushe Ya Hafiz yayi tafiya, amma sai na yi shiru ban ce mata kome ba. Ta kara da cewa. "Ya gaya mana Tijani zai kawo Hajiya Asiya an jima Asibiti kuma ya kamata ace kina gidan." Yadda Mama take shiga ba nan take fita ba, sai naji zuciyata tana wani irin ciwo kamar kaikayi. Ni dai kamar yadda aka saba kaina a sunkuye, wayar Mama ne yayi kara ta dauka tana faɗin. "Na'am Alhaji gata nan tazo!" Ta mika min wayar. Yadda ya balbale ni da fada yasa nayi shiru kamar yana gabana ya cigaba da cewa. "Kin san Abokiyar zamanki bata gari, sannan ta bar miki Yarinyarta taya zaki kai yarinyar makota? Ke wacce irin mahaukaciya ce? Don Allah bai baki haihuwa ba sai ki na wulakanta mishi Yarshi? Wai ma da izinin waye kike fito? Ga Hajiya Asiya can da Tijjani sun je gidan ba kowa, ke a rayuwarki idan baki saka mu magana ba, bakya jin dadi ne?" baba yana yin nashi a waya, ta yadda yake shiga ba nan yake fita ba, haka Mama tana yin tana kamar ta rufe ni da duka. Nasan cewa duk lokacin da zan zo matuƙar ba shi zai kawo ni ba, tow na rantse da Allah kamar yar riko haka nake komawa amma idan ya kawo ni kowa yayi ta ririta ni. Aunty Hindatu na ta kasa jure fadar Mama ta ce mata. " Mama dai, ya kamata ku fahimci Lulu ba zata fito don kanta ba, sannan taya zata fito a ce! " "Gafara can, an gaya miki bamu san yadda kike hure mata kunne ba ne? Ko an ce miki bamu san yaddA kika mata wayo kina rabata da kuɗinta, me yaron nan ya rage ta da shi? Ko an gaya miki ban san me nake yi ba ne? Wallahi Hindatu idan baki daina shiga rayuwar Lubnah da gidan aurenta ba na rantse da Allah sai na miki Allah ya isa, kuma ki zauna yanzu su Hajiya Asiya zasu tawo ku koma gida Wallahi, ina zaman lafiya da Mijina ba zaku kashe min aure ba ke da Yan uwanki! " Cikin fushi Aunty Hindatu ta shiga hada kayanta Ya Sani daga waje da Aunty Munah, suka shiga kananun magana, yadda Ya Sani yake mita yasa Yadiko ta dirko musu kamar zata rufe shi da duka, har tana faɗin. "Idan wani ya kara shiga rayuwar auren Lubabatu sai na mishi Allah ya isa, tunda burinku shine ku kashe mana aure, idan da kuna da hankali tausarta zaku yi ba ku tsaya kai da fata bata yin kuskure, tun kafin ta iso muka san cewa gaban kanta tayi, haba me yasa Lubabatu take haka ne? Yaron nan yana girmama ki amma ke kin dage sai kin zubar da mutuncinki." Kiri-kiri suka hade kai suka min tas Aunty Munah da haushi ya mata itama barin musu gidan tayi ta nufi gidan Ya Umar da yake makama jahun, Ya Sani ma haka ya bar gidan babu shiri, ni daya kamar mayya haka suka yi ta fada bayan sun gama, kuma suka sauko tare da min nasiha, har Yadiko ta shigo da abincin da na kawo suka ci da Mama, ni dai kaina yana kasa har lokacin ban d'ago kai ba, sannan ban ce musu cikanku ba. Kai mai karatu wannan sai ya zame maka sabo amma a wurina ba sabon abu bane, da na san haka zai faru da Hajiya tace na fasa zuwa da na fasa. Kiran Sallah la'asar ya saka na mike zuwa ban dakin Mama nayi alola na fito na gabatar da sallah la'asar. Bayan na idar ina zaune sai ga Hajiya da Yusrah, tana zuwa da gudu ta fada jikina tana faɗin. "Lulu shine kika tafi kika bar ni." "Yusrah babu Mama sai Lulu ba uwaki ba ce?" D'ago kai yarinyar tayi ta ce mata. "Allah ya kiyaye ta zama Uwata, ko Hajiya " wani diriricewa Hajiya tayi Tijjani ya daka mata tsawa, yana faɗin. "Kun ga yarinya mara tarbiyya, Lubnah haka kike tarbiyyar Yarki!" Ni dai bance musu kome ba, ina jin suka gaisa da su Mama da Yadiko, sannan aka zubo musu abinci suka ci sosai.. har a lokacin mamaki bai daina kamani ba yadda suka tawo da tsaraba niki -niki, suka bawa su Mama da Yadiko, yadda Hajiya take wani tarerayata, abin sai yafi kome bani tsoro tabbas Hajiya idan suka saka mu jariri zasu cije shi ya mutu har lahira. Duk uban abincin da na saka musu amma anan da aka kawo musu abinci sai da suka ci kamar ba mutane ba, har zuwa lokacin idanun Hajiya yana kan kular abincin, sai da Yadiko ta zuba mata hankalinta ya kwanta tana ci tana murmushin, a hankali na tashi na koma dakin Mama na kwanta, wayata ta ce tayi ƙara na ɗauka tare da kallon screen din wayar, shine dauka nayi a sanyayye ya ce min. "Da fatan kin sami kowa lafiya!" Murmushi nayi nace mishi. "Suna lafiya!" Sai yayi shiru. "Luluna ki yi hakuri wallahi nayi haka." "Wani abu ne ya faru kake bani hakuri?" Shiru yayi yana jina kafin ya ce min. "Sai kin zo gida zan miki bayani!" "Wani bayani babu abinda ya faru, don Allah ka daina damuwa akan haka." Daga haka na kashe wayar, na kwanta duk da haka sai da ya kira ni ina gani naki dauka har na kwanta kaina azabar ciwo yake, da yake mun san cewa barcin yamma babu kyau amma saboda yadda kaina yake ciwo yasa na kwanta. Karfe shida da wani abu ba ji kiran sallah, sai lokacin na lura da yadda aka lullube ni da mayafi. A hankali ba bude idanuna da suka min nauyi, na dafe goshina ina jin kamar kaina zai rabe gida biyu. Zama nayi ina dafe da kan har Mama ta shigo dakin. "Baki da lafiya ne?" D'ago kai nayi ina murmushi na ce mata. "Lafiya lau!" Na mike da kyar na nufi ban daki na yi alola na fito, na gabatar da sallah, itama sallah na samu tana yi ina idarwa na zauna a wurin shiru sai da ta shafa addu'a sannan ta ce min. "Me yasa kika fito ba da izninsa ba?" "Ba kome!" Shiru tayi tana kallon yadda nayi shiru. "Kina son Abbanku ya sake ni ne?" Girgiza kai nayi, sannan ta cigaba da min nasiha tare da fada domin babu wani abu me kama da rarrashi a cikin kalma ta don gaya min take zan kashe mata aure ne, tunda nasan cewa akan Hafiz Baban Bauchi bai da hakuri, ni dai ban ce mata cikanki ba har ta gama maganarta sannan ta fita, bayan isha na isa parlourn Abba na gaishe shi, ashe Ya Hafiz ya iso sai lissafi yake tare da gaya mishi abubu yan da ya faru a tafiyar da wasu dalilai da yasa aka samu matsala. Yadda Baban Bauchi ya yarda da Ya Hafiz kaf Yayuna maza da mata babu wanda ya yarda shi haka, durkusawa nayi na gaida Baba yaƙi amsa min, sai da Ya Hafiz ya ce mishi. "Baba tana gaishe ka!" "Ba zan amsa mata ba, akan me zan amsa mata bayan ta fito ba da izininka ba, tasan irin masifar da take shirin kawo min idan da yau mutuwa nayi da Allah zai saka Mala'iku su d'aga ni su ce ga abinda Yarka take yi!" Nan dai Ya Hafiz yayi ta rarrashinsa da kalmai masu dad'i, sannan ya kara da cewa. "Matukar kina son na kaunace ki Lubabatu ki bi Mijinki sau da kafa, don baki san irin asarar da kika janyo mishi ba ne ke da Hindatu itama zan kira Mijinta na ja mishi kunne tunda ku Yahudawa baku san yadda zaku bi aurenku sau da kafa ba. Kuma zan kira Addu'a da Umar da Tahir na ja musu kunne kada wani ya kara tura miki kosisi tunda ba zaman aure zaki yi ba." Yadda Baban Bauchi yake shiga yake fita sai ka rantse da Allah wani abu na aikata, wannan shine burin Ya Hafiz duk ranar da zan zo matuƙar bai mishi ba koda kuwa ya amince tow sai na fuskanci tashin hankali a cikin gidanmu. Ni kuwa kamar wacce ake watsawa ruwan zafi haka nake jin maganar su kamar danyen guba, nasan Iyaye suna kaunar Yaransu akan kansu amma ni nawa Iyayen sun zaɓi abinda za a fada a kansu sama da rayuwata, yadda ya gama fadar ya daka min tsawa akan na roki Ya Hafiz, har a lokacin idanuna wani irin zafi suke min, kaina a sunkuye na ce mishi. "Ya Hafiz ka yafe min." Muryana tana rawa, "Wallahi na yafe miki,matukar ni zan d'aga miki kafa ki shiga aljanna wallahi na d'aga miki ki shiga Allah na yarda da Lubnah Allah ka yarda da Lubnah!" Wannan yar draman da yayi a gaban Babanmu sai ga Baba yana irin farin ciki domin shi dai yaga yadda Ya Hafiz yake kaunata, Ya Hafiz ya ce mishi. "Baban Bauchi ka amsa gaisuwar Princess don Allah!" Cikin murmushi irin na manya ya ce mishi. "Na rasa ganewa Hafiz yadda kake kaunar Lubnah baka hango laifinta. " " Mace ta gari ce, tana da kirki da mutunci. Ba iya soyayya ya bani ita ba, Allah ya yarda da ita ne ya bani ita. " Yadda Ya Hafiz yake faɗan kalaman yabo yasa Baba ya kuma juyowa yayi min nasiha, da nuna min yadda Ya Hafiz yake kaunata kaf duniya babu namijin da zai min irin wannan soyayyar da yake min na rike mijina domin kaf duniya babu me min irin son da yake min......... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI* Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu BIYAR Tabbas Ya Hafiz yana kaunata, amma kuma me yasa yake min haka? Me yasa sai mun gama kome da shi yake juya min laifin? Ina ga ko yadda ya musu bayani ba haka suka dauka ba, amma zan tambaye shi ko nice ban fahimci yadda suke ganin laifina akan fitowa da nayi ba tare da izininsa ba, domin a sanima da izininsa na fito zuwa gidanmu, a hankali na fito daga dakin Babanmu, a bakin kofar muka hadu da Jalilah yar rikon Yadiko ce, amma yar uwarmu ce sosai, sai dai Jalilah ni da ita bama ga maciji saboda kawai kowa da abinda yake tsammani a tare da shi. Ni dai ban san me na mata ba, amma tare muka taso, zuwa yanzu dai auren Jalilah uku, tana zawarci sannan yan uwarmu ce na kusa sosai domin Mahaifinta kanin Baba ne, mahaifiyarta kanwar Yadiko, a sanina Jalilah kawar Ya Hafiz ce, kuma kawar Matarsa domin tun aurensu suke tare. Kallo daya tayi min ta dauke kai, nima na dauke kai kamar ban san tana wurin ba. Dakin Yadiko na nufa na ce mata. "Yadiko zamu tafi!" "Tow Allah ya kiyaye hanya, sannan ki daina fitowa ba tare da izinin Mijinki, baki san kin girma ba ne." Ni dai bance mata cin kanki ba, har ta gama magana na wuce dakin Mama na hada kayana. Ina hada kayana sai ga Ya Umar ya shigo da sallama, murmushi nayi na zauna. Sai da ya fara gaida Baban Bauchi da Yadiko, sannan ya shigo ya samu su Hajiyarsu Ya Hafiz ana ta surfa abinci, kallona yayi yana murmushi ya ce min. "Auta shi ne baki karaso makama ba?" Murmushi nayi na ce mishi. "Ina wuni Ya Umar!" "Lafiya lau!" Kafin ya rufe baki Mama ta tab'e baki ta ce mishi. "Ai fitowa tayi ba da izinin Mijinta ba!" Kallona yayi yana murmushi ya ce mata. "Tsakanin da Allah auta ta wuce sai ta nime izinin zata zo gida nan, kada ki manta Hafiz dai a gidan nan ya taso haihuwarshi ce ba ayi ba, sannan na biyu idan Auta ta tawo babu izininsa meye ribarta? Kayyasa Mama Hafiz da Lubnah dukkansu Yaran gidan nan, kuna nazari kafin yanke hukunci gudun kada a tsaya a gefe guda!" Da yake sunan Ya Umar sunan Baba Malam ne wato Kakanmu bata iya ko d'aga mishi murya ta ce mishi. "Mai sunan Baba Malam!" "Mama maganar Allah nake gaya miki kafin Hafiz ya auri Lulu mu ne muka fara auren Yaran wasu, yanzu saboda yadda Habibah ta samu wuri wallahi idan zata fita sau dari bai wuce ta gaya min sau biyu ba, mu Yaran wasu muka musu adalci sai mu namu ne ba zasu samu adalci ba? Mama ita yarinya ce bakiɗaya shekaru tara ake nima da aurenta idan kuka tsannanta mata bata da inda ya wuce nan ku sani shi Hafiz namiji ne, hmm kayya. Lulu kina son wnai abu ne? " Da zumudi na mika mishi takardan da nazo da shi. Budewa yayi sannan ya ce min. " Ok akwai ma a gidan nan kamar jiya aka yanka abokina dan liti zai zo ya saya. Fita yayi ina jin yadda Yadiko take gaya mishi abin da ya faru, itama nan gaya mata gaskiya yayi ya saka Ya Sani ya cire min kajin, duk wannan abin da ake Hajiya kunya ce ta kamata bata iya magana ba, sai sunkuyar da kai itama Mama sanin cewa Ya Umar ya daure ta da jijiyarta yasa bata yi magana ba, a can parlourn Baba naji yadda Ya Hafiz yake faɗa shi da Ya Umar, koda yake Ya Umar ya gaya mishi magana daya ya ce mishi. "Ka gama duk abinda zaka yi, wa'adin Allah gaskiya ce, ni da kai mun san kome! " Ba sai Ya Hafiz ya fusata ba, ya mike tare da sallama yana faɗin. " Na hakura da Lubnah tunda ban muku adalci ba! " Nan Baban Bauchi ya dirkowa Ya Umar fada yake kamar zai cire bakinsa, har da cewa. " Idan kuka kashe mata aurenta ko bayan raina ne ban yafe muku ba. " Murmushi Ya Umar yayi ya ce musu. "Ni ba zan kashe mata aure ba, ai ita mace baka ce mata kaso aurenta ki zo mu zauna wannan wani lamari ne da Allah yake shirya faruwansa! Ka yi hakuri Baba idan na ɓata maka rai!" Ko amsa masa sallama Baba be yi ba ya bar gidan, haka Baba ya zauna da Ya Hafiz yayi ta bashi hakuri, har da kiran Hajiya ya bata hakuri wai ta bawa Ya Hafiz hakuri. Abin bai yi dad'i ba, domin haka muka baro gidan zuciyata ba dad'i. Kaina a sunkuye a cikin motar. "Ban da rashin mutunci irin na Yaran Salamatu don an rufa muku asiri an yi muku alfarmar auren yarku sai ku saka min d'a a gaba? Wallahi kun yi asarar!" Haka Hajiya take fada, shi dai bai ce kome ba, zuwawa yanzu ya fara jin wani irin yanayi a tattare da shi, "Hajiya don Allah ki mana shiru!" Yadda yayi magana a karfafe zaka ɗauka ba ita ta haife shi ba, jin yadda ya daka mata tsawa yasa ni na sha jinin jikina na koma gefe da jikin kofar, har muka iso Tambari, na bude motar na fita tare da ɗaukar kayan da nazo da shi, kaya sosai aka hada min Mama da Yadiko wai kada na tashi hankalina. Bayan na shigar da kome na wuce zuwa part dina na saka kome a muhallinsa, sannan na wuce zuwa kitchen na daura ruwan zafin na zuba a flast, kafin na fito a kujeran Parlour na hango shi. "Zo nan!" Ya ce min, na taka a hankali jikina yana rawa domin nasan irin wannan kiran babu alkhairi a cikinsa. Durkusawa nayi a gefen kafarshi ina me sunkuyar da kaina. Shiru ne ya ratsa parlourn kafin ya ce min. "Me kika gayawa Umar?" D'ago kai nayi da sauri ya tsinka min mari, sai da naji wani irin shuuu a kunnena, bakiɗaya kaina ya fara min irin wannan ciwon da yake min tare da juyawa. Rike fuskana nayi da kaina. "Tambayarki nake!" Tsoro da tashin hankali, ya hana ni magana kara rufe fuskana nake ina girgiza kai. "Tambayarki nake?" Ya kara zuba min wani irin gigitaccen mari da yasa ni zama da duwawuna, nace mishi. "Wallahi ban fadi kome ba, ka yarda da ni." Na fada ina fashewa da kuka, haka yasa take ya kyale ni, ya bar parlourn anan na cigaba da kuka har dare ya raba na wuce daki na kwanta, haka nayi kuka har na godewa Allah, kwanciyar da nayi har na fara barci ya shigo ya bani wata magani na amsa na sha, ko minti goma ba ayi ba na fara jin kaina yana wani irin juyawa a hankali na kwanta. Daga nan ban kara sanin me ya faru ba, sai da asuban fari na tashi na shiga wanka, bayan nayi wanka na fito duk yadda naso na tuna mai ya faru na kasa, sallah nafilla nayi na wuce zuwa kitchen, ja daura abinda zan daura sannan na fito zuwa dakin nayi , bayan na idar na koma na fara aikin abin karyawa karfe bakwai saura na nufi bangarensu, na taso Yusrah amma yarinayr nan tayi ta min ihu har da wani abu kamar tana dambe da ni, ihun da take min da kuma yadda nake jin wani abu me karfi a kaina yasa na daka mata tsawa. "Don Allah tsaya na miki wanka!" Wannan abin na mata yarinyar nan ta fasa ihu, sai ga kowa ya shigo ban dakin, ba tare da wani bincike ba ya Hafiz ya rufe ni da duka, kamar zai kashe ni, saboda karfin azabar duka zubewa nayi akan gwiwata hancina yana zuba da jini. "Tashi ki mata wanka!" Ƙasa tashi nayi ina kife a wurin, koda ya d'ago ni, sai komawa nayi na kwanta sharaf kamar an jika tsuma, abinda ya saka hankalinsa ya tashi amma saboda rashin imani ya ce min. "Wallahi idan baki tashi ba, na taso sai na kara taka ki, jaka juya wacce bata san darajar haihuwa ba" "Gara ka gaya mata dai, ban da rashin mutunci ki saka yarinya a gaba da azaba, ke ina danginki gani suke ana cutar da ke!" Sai dai duk abinda suke yi bai saka na motsa ba, anan suka fahimci fa babu numfashi a jikina, abinda ya firgita su har Tijjani ya shigo yana faɗin. "Yanzu kana ganin daidai ne abin da ka yi? Kana tsammanin yadda Umar yake kallon idanunka zai kyale ka ne idan ya ji abinda ya faru? Kana abu kamar mahaukaci yarinyar nan kana amfani da ita yadda bai dace ba, ba fa Ubanta baya sonta ba ne a'a alfarma ya maka saboda Abbanmu, ka sake aka gano yadda kake azabtar da ita wallahi ka ji na gaya maka, ba ruwan kowa da kai ne ka fara waye ne ya fara. Kuna ganinsa zai kashe musu yar mutane bayan kace jiya ka mare ta, yau kuma ka kara rufe ta da duka. Ji yadda take sume ni dai ina shaye-shaye amma wallahi na fi karfin dukar mace kamar yadda kake yin nan ai abin ya koma jahilci kuma!", daga haka ya fita zai gashi da ruwan gora mai sanyi yana zuwa ya samu fuskata ya zuba min, ajiyar zuciya na sauke ya ce min.." tashi ki koma part dinki, Yarinyar idan baza du shirya yarsu ba, to su barta ko na kira Baban Jama'are yau wallahi na gaji da iskancinka Hafiz na gaji da muguntarka idan kayi wasa sai na gayawa Abbanmu! " Sanin cewa dan shaye-shaye ne bai da mutunci zai aikata. Dakyar na tashi na nufi hanyar fita, tunda na shiga parlourna, rufewa nayi na kwanta a saman kujeran parlourn nayi ta kuka ina jin kamar zuciyata zata buga, na rasa gano laifin da nayiwa Ya Hafiz. Zuwan Kabiru na bude mishi kofa nayi na zuba mishi abinci nace ya je yau ba aiki. "Aunty me ya same ki?" "Ba kome!" Shiru yayi kafin ya ce min. "Aunty ki yi hakuri kin ji, akwai abinda nake son na kawo miki idan kin amince sai na kowa miki!" Gyada mishi kai nayi nace mishi. "Na gode sosai!" Juyawa yayi ya tafi ni kuma na koma daki nayi wanka na kwanta, buga kofar parlourn da aka yi yasa na fito, na buɗe.. "wani irin abu kazan-kaza ne? Uban waye zai bamu abinci muguwa azaluma ke wacce irin dabba ce. Amma kin iya sakawa wancan dan iskar Yaron ke jaka wawuya wacce iyayenta suke niman kai da ita." Ni dai tunda ya fara fada na koma jikin bango na makale ban kara sakewa ba. Har ya gama ya bar parlourn, kitchen din na wuce na hada abin karyawan bakiɗaya na kai musu. Anan Hajiya ma ta rufe ni da zagi cin mutumci da gorin rashin haihuwa, sai na ji ba zan iya kuka a gabansu ba na fito na dawo dakina, ina zama wayata tana kara wacce take saman center table, dauka nayi fada Baban Bauchi ya rufe ni da shi, har da cewa wallahi na sake na kashe Aurena sai dai na nimo wani uban ba shi ba, yana kashe wayar Mama ta kira ni itama ta min tas har da barazanar zata tsine min,tana gamawa. Ya Umar ya kira ni yana tambayata mai ya faru? Murmushi nayi na ce mishi ba kome. Duk yadda yaso yaji me ta faru nace ba kome wallahi. Haka wunin ranar ban saka kome a bakina ba, washi gari Hajiya suka bar Bauchi amma ta ce zata dawo kwanan don tafiyar ya zame mata dole ne kuma domin danta tayi shi. Sannan tafiyar kusan nice na tura musu kudin mota domin tana zaune ranar Ya Umar ya tura min dubu hamsin ya ce na rike a hannuna, don haka ta cewa danta a kan idanuna. "Yayanta ya bata kudi ban san ko nawa ba ne." "Shine bakar munafuka bata gaya min ba." Fisgar wayar yayi yana faɗin. " Mai mugun hali! " Ya fada bayan ya tura dubu arba'in ya bar min dubu goma shima a take ya turawa Matarshi biyar ya bar min biyar, ya je ya cire musu kudin ya basu dubu sha biyar ya rike ashirin

Chapter 4 of 13