Share this page
dai ko ke?" Yake na mata ban ce kome ba. Haka ta fita, ina zaune a wurin na gaji gyara parlourn na fara tare da shirya kome a inda yake, ina aiki aka kira wayata, dauka nayi Ya Ado ne, mutanen Lagos dauka nayi ina murmushi na ce mishi.. "Barista ya aiki?" "Auta" "na'am!" Na amsa mishi a hankali, "Hindatu ta kira ni, akan wani batu ya abin yake?" Tsintar kaina nayi da cewa.. "kawai zato take amma wallahi ba kome!" "Auta gaya min idan baki gaya min ba wa zaki gayawa? Kada ki daka ta su Abba kin ji!" "Ba kome wallahi!" Na fada ina lashe bakina. "Auta gaya min gaskiya meke damunki?" "Nima haihuwa nake son nayi na ga Yarana koda zasu na min kukan banza ne?" Murmushi yayi ya ce min. "Shi kenan Allah zai kawo kin ji, sannan zan tafi wani course Canada idan na samu dama zan turo ki tafi kin ji sai a duba lafiyarki." "Yaushe zaka dawo?" "Shekara daya da rabi ne, kin ji kiyi hakuri ba zan jima ba! " " Allah ya bada sa'a ya bada abinda aka fita nima!" " Amin Ya Allah! Kin ki aikin gwamnati ko?" Murmushi nayi kawai, ya ce min.." Gashi nan zan turo miki jari sai ki fara wani abu ko za a dace! " " Allah ya saka da alkhairi! " Na mishi godiya, ya kashe wayar, can nayi shiru ƙaran shigowar sako na ga ina dubawa na ga Naira dubu dari biyar ya turo min. Kiranshi nayi ya katse ya kira ni. "Kada ki damu ki fara wani abu, Lulu kada ki gayawa Mijinki, ki sami Hindatu ko Inna ki gaya musu, zasu fi baki shawarar da ya dace kin ji." "Na gode sosai! Allah ya kara lafiya da nisan kwana, na gode!" Amin yayi ta amsawa, bayan na gama na kira Aunty Hindatu, na gaya mata a take ta saka na tura mata dubu dari hudu ta ce min, zata gayawa Mama da Abba, ta bar min dubu dari sannan ta gaya min kada na tab'a fadar dubu dari biyar ya turo min, kawai na ce dari ne, kamar yadda ta tsara min haka nayi shiru ta kira Abba ya gaya mishi, ina cikin girki ba sai ga Ya Hafiz ba kamar an wurgo shi, a razane na kalle shi. "Ina kudin da Adamu ya tura miki?" Dama na goge alert din farko, ya amshi wayar yana ta dubawa ya ga dubu dari ta opay dina, kallona yayi irin kallon kurilla nan. "Yanzu ke mi zaki yi da kuɗi?" "Sana'a?" Na fada ina kallon kasa, tura dubu saba'in yahi ya bar min dubu talatin," zan ajiye miki, kada ki gayawa Hindatu dai na karba!, yawwa ki bawa Karimcy dubu goma, nima ki bani ladar ajiya!...... 08130269641 *Mai_Dambu* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI* Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu BIYU Nasan haka zai faru, sai na tura mishi tare da ita matar nashi. Tow me zance? Na hanata ya min rashin mutunci. Yana ganin na tura mata ya ce min. "Ke matar arziki ce, duk wanda ya zauna da ke sai ya ci daga arzikinki, shi yasa na tsani wani ya shiga min rayuwarki domin Allah ya gani ina sonki ina son zama da ke!" Gyada kai nayi ina aikin hada abincin rana, yana fita na cigaba da abinda nake a cikin dubu dari biyar ba don Aunty Hindatu ta amsa ba, tabbas da na tashi babu kosisi. A duk lokacin da na samu kuɗi haka yake min, ni kuwa kamar wacce yake wankewa bana iya mishi musu, a yanzu ma nasan sai ya bididigin ya ji nawa aka turo min, Ya Hafiz dai. Ina cikin wanke busashen kifi sai ga Matarshi. "Ashe kyauta muka samu Hajiyata, to mun gode mu ga dubu goma amma nasan yafi haka ko darling ne ya karba? Ina ta son na gaya miki." "Nima dubu goma suka rage min!" Na fada daga haka nayi shiru, jin yadda na fada babu wanda a cikin maganata yasa tayi shiru, sannan ta kuma ja bakinta bata kara magana ba, ta bar parlourn ban san me yasa suka mai dani haka ba! Koda yake ni ce na mai da kaina haka. Zan iya cewa a duniya duk yadda Ya Hafiz xai ce koda wuta ne zan iya bin sa ciki domin ina sonshi. Kuma zan iya kome domin shi, don na taso da wata mahaukaciyar kaunarshi ne. Shi yasa duk abinda zai min bana tab'a fushi ko nayi ma Baba zai saka dole na sauko. Ina gama hada abincin, Almajirin da yake min aiki ya buga kofar gidan, na je na bude ina faɗin. "Kabiru sai yanzu zaka zo? Kasan kana zuwa sayo min kayan lambu?" "Aunty kiyi hakuri, na zo Alhaji ya ce ba kya nan." Shiru nayi kafin na ce mishi. "Ok shigo ba ka kudin alyahun da zaka sayo min!" "Tow Aunty!" Ban san me yasa Ya Hafiz yake min haka sai dai duk lokacin da yayi min wani abu, na fushi ina jin haka amma bana iya maida abin. Kamar yadda aka saba na tura Kabiru ya tafi min aika, don bana son Yaran su dawo ban gama ba, ya ji haushina. Shi kuma Kabiru ya fara shara da yan aikace-aikace da yake min. Bayan mun gama na saka mishi abincinsa sannan yayi min sallama ya fita wurin karfe daya saura, ina ganin fitarshi na rufe kofar party dina nayi wanka, na shirya cikin doguwar riga. Sannan na dan yi kwalliya sama-sama. Domin nasan ko ya gani dariya zai ta min, haka na gama shiryawa na gabatar da sallah azhar, ina addu'a ya iso na je na bude mishi, kallona yayi kafin ya wuce na ce mishi. "Barka da zuwa, ya kasuwa?" Bai ce amsa min ba, ya wuce abinsa ya nufi daya daga cikin sofa na parlourn ya zauna yana hararan parlourn. "Na kawo maka abinci?" "Kin ga na miki kama da wanda yunwa ya koro?" Shiru nayi ya kara daka min tsawa. "Nace kin ga yunwa a jikina?" "A'a kayi hakuri!" "Hakurin Uban me kike ba ni ne? Akan me kike bani hakuri ne? Munafuka annamimiya?" Shiru nayi na koma gefe ban kara motsi ba, domin zuciyata wata irin tsinkewa take. "Nawa Adamu ya baki?" Bakina yana rawa nace mishi. "Dubu dari.." "me kika ce?" "Dubu dari biyar!" Na fada muryana yana rawa, murmushi yayi ya mika min wayata da take kujeran parlourn ya ce min. "Maza ki kira Hindatu ta dawo da kudin nan ko na miki dan bura uban duka, kuma na sake ki." Jikina yana rawa na amsa, ya ce min. "Wallahi ko nutsu ki yi waya da ita. Kuma ki nuna kece kike bukatar kudin ba ni ba!" Gyada kai nayi nayi na kira ta, a hankali ta dauki wayar tana faɗin. "Auta lafiya kuwa?" Murmushin yake nayi idanuna yana cika da kwalla na ce mata. "Aunty ki dawo min da kudin nan zan." "Hafiz ne ko? Ki gaya mishi kudi naci ko uban waye zai kira ya kira amma ya sani ya daina ci da guminki, sai an jima little girl!" " Ni dai ko turo min idan ba so kike gobe ki samu gawata a gidan ba Ni dai ki tura mishi don Allah! Idan har da gaske kina kaunata! " Na fada kamar zan yi kuka, shiru tayi kafin ta kashe wayar, zubawa wayar idanu nayi kamar ina son hango ta cikin wayar. " Lallai Hindatu tana nima na da magana. " Ya fada yana kwafa tare da hararan inda nake, wayarshi hannunsa ya ciro. Sannan ya kira Malam Baba. " Don Allah kada ka gayawa kowa zata dawo da kuɗin." Watsa min harara yayi kafin ya cigaba da kiran wayar har aka dauka. "Dattijo! " Daga can bangaren aka amsa mishi da." Na'am!" " Dattijo na gaji da wannan auren, bakiɗaya yan uwan Lubnah sun saka min idanu! " Kamar zan fashe da kuka haka nake rokonshi. Murmushi yayi yana faɗin. " Dattijo, kamar ni har sai Adamu ya zartas da hukunci a cikin gidana ban isa na sani ba? Gaskiya na gaji zan sako musu yar uwarsu. Tunda basu fahimci irin abinda nake yi ba, ban san me yake faɗa mishi ba, amma naga yadda yake gyada kai, can ya koma bashi labarin kome kafin ya daura da cewa. "Dattijo ni me zan yi da tsiyarta dama wai na adana mata ne tunda me take nima ta rasa, amma tunda abin har ya kai haka, shi kenan ai ba yau Adamu da Hindatu suke shiga min rayuwar gidana da iyalina ba, dattijo kasan yadda nake zaune da ita, kasan halin da nake ciki da ita, ban da ni waye zai zauna da ita a haka mace babu ciki ba sai dai ci baya." Ji nayi kamar zan mutu, yadda yake gaya min maganar kamar wanda na aikata mishi wani laifi, yana gama wayar ya mike yana faɗin.. "Na baki nan da kwana uku ki karbo kudin nan ko kuma wallahi sai kin bar gidan nan na gaya miki!" Daga haka ya fita, na rasa yadda zan yi da rayuwata. Yana fita na dafe kaina, na rasa meke min dad'i. Wayata ce tayi ƙara na duba Aunty Inna ce, ina dauka na ji kwalla ya cika min idanu. "Auta me Hindatu take gaya min?" Kuka ne ya kwace min na kasa bata labarin abinda ya faru. "Kina nufin a dauki kudin a bashi?" Kamar tana gabana na gyad'a mata kai ina faɗin "eh!" "Bakya tunanin da matsala kudinki ne fa, wai ma tsaya waye ya gaya mishi kin samu kudin?" "Ban sani ba wallahi iya na wurina ya amsa saura dubu bakwai!" "A cikin dubu darin da yake hannunki?" Shashekar kuka na ja, ta ce min. "Anya Hafiz ba asiri ya miki ba? Ai shi kenan zan mata magana ta turo miki kuɗinki sai ki bashi." A yadda tayi magana kamar ranta ne ya b'aci, kashe wayar tayi. Haka na zauna a parlourn har zuwa wani lokaci kafin na mike na wuce dakina, na wanke fuskana sannan na fito, na samu Yasir ya dauki remote dina yana dokawa da kasa, "Yasir bari kada ka bata min!" Na amsa da gudu ya fita yana ihu, ban kula ba na shiga kitchen na zubo musu abinci, ina dawowa parlourn Ya Hafiz suna shigowa da shi da Karimcy. "Uban me ta mishi Yusrah?" "Rankwashinsa tayi!" Ta fada tana me kallona, takowa gabana Uwarsu tayi ta amshi abincin ta ajiye sannan ta d'aga hannu zata mare ni ya ce mata. " Kyale ta! Bashi taci ko ta biya ko kuma ta ji a jikinta." Daga haka suka juya suka bar parlourn har da Yaran. Zama na cigaba da yi har lokacin sallah yayi na tashi nayi sallah, na zauna a cikin uwar dakina ban fito ba, abincin da nayi shi zamu ci har dare tunda gidan ba lafiya gara na dumama da dare, ina zaune can wurin karfe biyar na yamma Husnah ta kira ni, dauka nayi muka gaisa ta ce min. " Auta me ya hadi ki da Ya Hafiz kuma?" " Babu kome! " Shiru tayi kafin ta ce min. " Hala baki leka Whatsp ba ko?" "Eh bani da data ne amma zan leka yanzu!" "Gaskiya abin ba dad'i, sannan idan kin san akwai wani abu don Allah ki warware domin dai ba dad'i ayi ta rigima akanki kullum !" "Na gode in sha Allah zan yi yadda kike ce!" Na kashe wayar, ta banki na sayi kati na saka account dina sannan na sayi data, na bude Whatsp dina, a hankali na ga sako yana ta shigowa kasancewar na jima ban bude ba, sako ne dayawa, kamar wanda aka wurgo shi ya fado min daki, kallonshi nake shima ni yake kallo, tsoro da tashin hankali suka ziyarci zuciyata da fuskana, hadiye yawun tsoro nayi, zuwa yayi ya zauna a hankali ya cigaba da kallona. Amsar wayata yayi yana faɗin. "Luluna, ki yi hakuri maganar kudin nan a barshi Hindatu ta rike kuɗin kawai ai zaifi kyau ta rike miki kuɗinki ko? Yanzu haka Baban Jama'are zai kira, domin Hindatu ta kira shi ta gaya mishi. Don Allah baby girl kada ki kunya ta ni, kada ki kara d'ago tashin hankali akan wanda aka yi kin ji, ki gaya mishi cewa ai mun sassanta kanmu. " Gyada kai nayi ina kallonshi cike da tsoro, wayar ce tayi ƙara ya saka a kunne yana faɗin. " Gata nan! " Ya mika min wayar, kamar wacce aka danne min ciwon da nake ji, na amsa wayar muka gaisa da Baban Jama'are. " Lafiya lau Babana!" Na fada ina kame-kamen me zance, a na shi bangaren ya ce min.." Ummina gaya min me ke faruwa ne? " Murmushi nayi na ce mishi. " Babana babu kome ai mun daidaita kanmu." Murmushi yayi yana faɗin. " Ummina nasan waye Hafiz na san me yake so na san abinda baya so, na san halinsa ciki da waje. Gaya min me yake faruwa? " " Babu kome babana, wallahi mun daidaita kanmu;" " Idan dai da wani abu ki gaya min kin ji ko? Allah ya muku albarka, Hindatu ta ce Adamu ya baki kuɗi, amma Hafiz ya amshe sannan wanda yake hannunta ma yana harinsu. " Kallonshi nayi naga yadda ya wani razana, irin yadda nake tsoronshi haka yake tsoron na bude bakina," A'a Babana, ba magana makamancin haka, sannan ai kudin ni ce na ce ta turo min na bashi ya rike min!" Na fada ina kallon yadda yake gumi. " A'a Hindatu ta rike miki kudinki dai, ba batun ya rike miki ta ce ta baki dari kudin yana nan ko yayi amsa! " Kafin nayi magana ya nuna min alamar na fada cewa kudin yana wurina bai amsa ba, haka na faɗa ajiyar zuciya ya sauke har Baban Jama'are ya gama min tambayoyi sannan ya katse kiran ko magana bai yi da shi ba, wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana na kalle shi, fauce wayar yayi yana tsaki. "Babu babbar munafuka irin Hindatu na tsane ta!" Daga haka ya fita a dakin tana mita, nasan Ya Hafiz duk abinda ya saka a gaban sai ya cimma nasara akansa. Duba what'sp nayi bayan fitarsa, ashe rigima ake tsakaninsa da Aunty Hindatu, yadda yake mararaicewa yana bata hakuri tare da nuna shi na fi karfin kudin da ake magana a kai awurinsa, don Allah kada ra kara hada shi da mahaifinsa, idan don yana kula da dukiyar Baban Bauchi yasa take haka zai bar shagon yasan ba suna yin haka don ni ba ne suna yi ne domin yana rike da duk wani dukiyar baban Bauchi ne, amma in sha Allah zai janye hannunsa, Lubna dai Matarsa ce kaf duniya babu wanda ya isa ya raba mu, sannan shi dai ya so Lubnah kuma yana zaune da Lubnah yadda yake girmama lubnah kaf duniya babu wnada yake haka, sannan idan har tana ganin kaunar da yake yiwa lubnah ba don Allah bane, tayi duk abinda za tayi. Wato idan ka ga yadda yake magana cikin nutsuwa da kaskantar da kai zaka rantse da Allah, ya Hafiz na musamman ne, koda yake shi din ai dama can na musamman ne. Sai ya bawa Kowa tausayi har Yaya Umar da yake Maiduguri ya cewa Aunty Hindatu." Don Allah ki bar maganar nan haka!" Haka ya Amaar ya ce mata, a kashe zancen duk kannenta maza da mata sai suka shiga kare Ya Hafiz, murmushi takaici tayi ta zabga Left a group din, dama Aunty Hindatu akwai zuciya a kusa. Daga wannan ranar ban kara samun matsala da shi ba, ranar bayan kwana biyu na kira Aunty Hindatu na gaishe ta dakyar take amsa min. "Aunty Hindu!" "Kada ki kira ni haka, ki je can ki cigaba da abinda kike yi!" "Ki yi hakuri ba zan kara ba!" Na fada kamar xan yi kuka. "Ya isa haka, meke damunki?" "Ba kome kawai na kira na gaishe ki ne!" "Allah sarki auta ta fara hankali. Ko kina son kudi ne?" "Akwai sauran dubu tara ba sai kin turo min ba!" "A cikin dubu darin ne ya rage saura tara?" Shiru nayi ina tuna katobarar da nayi. "Nayi amfani da shi ne!" "Allah ya kyauta, Baban Bauchi ma ya kusan rabon Zakka ai ina ga yana bamu bana umara zamu tafi har dake ko?" "Allah ya amince!" Na fada a hankali domin nasan matukar Ya Hafiz yasan da batun kuma Matarshi ba zata ba, ba zai tab'a barina na leka ko da kofar gida ne. "Ya kika yi shiru?" "Ba kome kawai ina nazarin yadda zan ga dakin Ka'aba!" Murmushi tayi tana faɗin. "Kin yi waya da Mama ne?" "A'a ban yi ba!" "Bata jin dadi fa, tana fama da mura." "Wayyo Allah Ubangiji ya bata lafiya! Me xan mata Aunty Hindu!" "Ki mata farfesu da kayan kamshi!" Murmushi nayi na ce mata. "Aunty Hindu ya nusaiba?!" Dariya tayi tana faɗin. "Tana lafiya ai ta kusan zuwa gida haihuwa!" "Allah ya kawo ta!" Nusaiba yar aunty Hindu ce da aka yi aurenta, kuma yar dakina ce. Daga haka muka yi sallama, mikewa nayi na nufi kitchen na bude frij na duba nama, zabuwa ce guda biyu ta rage min, ajiyar zuciya na sauke idan na je gidan zan so ganawa da Baban Bauchi. Ko don a tura Mubarak gidan gona kawo min kaji. Murmushi nayi, fitowa nayi na zauna a parlourn. Shigowa Yusrah tayi tana faɗin.. "Lulu zanci abinci!" Tashi nayi na nufi kitchen na zuba mata alale da nayi, sannan na fito na ajiye mata, ta fara ci ina kallon tv. Ni dai shirun Ya Hafiz nasan bata lafiya ba, idan kuwa ta lafiya ce tow zaka samu akwai shirin da yake yi, don haka ina zaune ya shigo da sallama. Kallonshi nayi ina amsa mishi. "Barka da dawowa, ya kasuwar?" "Alhamdulillahi!" Ya zauna a dame, dakinshi na wuce na ajiye mishi jakarshi, sannan na dawo na hada mishi abinci, koda na kawo na ajiye mishi, kallona yayi ya ce min. "Luluna ina cikin tashin hankali!" "Lafiya?" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce min.. "bari na duba Karima na zo!" Haka ya tashi tare da Yusrah sun jima kafin suka dawo tare da Matarshi, a lokacin da suka dawo abun ya bani mamaki domin dukkansu kuka suke sharshar. "Hafiz lafiya?" Girgiza kai yayi yana faɗin. "Lulu ki rufa ki min asiri, Lulu." Sai hawaye, bakiɗaya sai jikina yayi azabar sanyi bani manta lokacin aurensa da Karima haka ce ta faru yazo yana kuka da tashin hankali, ya Hafiz idan yana cikin tashin hankali bai da nutsuwa, ban san me ya faru ba, amma duk abinda zai girgiza shi yayi kuka nafi shi gudun abun. Bakiɗaya sai na shiga tashin hankali, yadda yazo ya zauna tare da daura kanshi a kan cinyata, sai jikina ya ɗauki rawa, tambayar duniyar nan nayi mishi amma bai ce min cikanki ba sai ce min yake na rufa mishi asiri. "Na rufa maka asiri me ta faru?" Kuka Karima ta saka ni ma sai na fashe da kuka, aka rasa me rarrashin wani, har wurin karfe shida sai ga Hajiya, Mahaifiyarshi da kaninsa Tijjani suka zo, nasan a wurina zata sauka duk da bani da wani daraja a wurinta amma nasan wurina ne, shi kuma Tijjani zai sauka a BQ tunda akwai dakuna biyu a bayan. Yadda Hajiya ta ganshi yana kuka yasa ta shiga tashin hankali, nan na kara yarda da cewa ita uwa akan danta ba ruwanta ba abinda ba zata aikata ba. Tana shigowa matar nan ta zube akan gwiwarta, Tirkashi duk abinda zai saka Hajiya Asiya wacce Yaranta suke kiranta da Hajiya, ta saukar da kanta ta roke ka, tow wallahi ba karamin al'amari ba ne, domin nasan Hajiya mace ce mai d'agawa da izza, mace ce mai matukar ji da kanta sannan tana da wani irin girman kai wanda nake da yakinin Ya Hafiz a wurinta ya gada, rike kafana tayi tana faɗin. "Yar nan ki amince ki rufa masa asiri don Allah ki rufa masa asiri wallahi kaf duniya bayan ke babu wanda zai iya rufa masa asiri!" Duk sai na rude, tun fil azal haka Allah ya halicce ni da saurin rudewa, ko fada ya Hafiz yake take nake shiga tashin hankali, shi yasa bana son abin da zai kawo tashin hankali a tsakaninmu, bakiɗaya na shiga tsoro na ce mata. "Hajiya don Allah tashi ki zauna a sama ni zan sauka! " Girgiza kai tayi tana kuka. " Yar nan Hafizu yana cikin tashin hankali kece kawai zaki fitar da shi. " Wani abu ne me nauyi ya danne min zuciyata, na zuba musu idanu. "Me kuke so Hajiya?" "Me muke so? Tambaya kike me muke so? Bama ki ce zaki rufa mishi asiri ba? Ai na gaya maka Lubnah bata kaunarka, amma ka ki ka yarda gashi tana nunawa kamar abin bai dame ta ba." Sai ta rufe ni da fada, cikin jin haushi ya mike tare da daka mata tsawa. "Me kike zo yi? Kin zo ki kara birkita min ita ne? Kin san halin da nake ciki kuwa? Idan kika rud'a min ita ya kike so nayi? Luluna ya isa!" Ya rungume ni yana shafa kaina. Kallon Hajiyarsu yayi ya nuna mata kofa ba ita ba har Tijjani da Karima. Suna fita ya zauna tare shafa kaina yana faɗin. "Ki yi hakuri, ki yi hakuri." Me Ya Hafiz yake so a gare ni da yake bani hakuri haka..... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI* Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu UKU Bani mantawa shekaru biyar da suka wuce haka ya suka saka ni a gaba da irin wannan niman alfarman, kaina ya daure a lokacin na amince kome ya faru wanda har yau nake ji kamar da ban amince ba, babu abinda zai faru. Koda yake ai zanen ƙaddarata ce, "Ya Hafiz me kake bukata?" Na tambaye shi, sharce hawayensa yayi kafin ya ce min. "Ba kome pretty!" Sai naji sunan ya zo min wani irin banbarakwai, saboda rabona da Ya Hafiz ya kira ni da wannan sunan tun farkon aurenmu ludayina yana kan dawwo ba yanzu da nafi kamar da katifa huta ba. "Hmm me kake bukata?" Zama yayi ya kwantar da kaina a kafad'arshi, yaushe ya Hafiz ya zama haka? Tow akwai abinda yake bukata. "Zan gaya miki muje ki yi sallah." Ya fada yana jan hancinsa. Haka na mike na nufi dakina, shima ya fita zuwa bangaren Karimah. Hafiz "Hajiya ni ban kirawo ki nan, ki kara min matsala ba. Kin san irin halin da nake ciki? Yarinyar nan lallabata zan yi na rufawa kaina asiri, idan ba haka ba wallahi sai dai na kare a gidan Yari, kin san ban ajiye ba ban bada ajiya ba, sannan shi wancan Mijinki ba shi ne da shi. Don Allah ki ajiye kiyayyar da kike mata, nima hakuri nake da ita kada ki sake ki kara mata wani maganar banza!" Cikin kaskantar da kai ta ce mishi. " Ya kake so nayi? Kasan bana son ganka cikin tashin hankali, amma ka gaya min yadda zan bita, ai duk abinda kace shi za ayi Alhaji karami!" Zama yayi da kyau ya ce musu. " Nan da sati idan ta amince zan sayar da gidan nan, abinda ya rage zan sayi wani karami a tudun salamanu, bana son danginta da ita kanta su san abin da yake faruwa, ina son kafin haka na tafi Umara da ita, domin yadda kome zai tafi. " " Umara kuma? Taya Umara kuma? " Inji Karimcy, kallon an kusan fita Masallaci

Chapter 2 of 13