Share this page
na kara komawa na kwanta tare da lumshe idanuna, ban kara budewa ba sai washi gari da misalin karfe biyu na rana naji Muryan Ya Ado, a hankali na kara mike jikina duk ciwo yake min. "Sannu Lubnah!" Inji Umma Kanwar Mama wacce take aure a azare, lumshe idanuna nayi na kara budewa akanta, ta mike da sauri ta shiga ƙoƙarin taimaka min na zauna ina sauke wani irin numfashi kamar mai cutar asthma. Kallona Ya Ado yayi a hankali ya ce min. "Ina ke miki ciwo?" Girgiza kai nayi alamar babu. "Sannu ko." Ya ce min haka ta rike hannuna muka tafi ban daki ta haɗa min ruwan wanka nayi da ruwa me zafi, sannan na hada da alwala na fito na zauna a bakin gadon fita Ya Ado yayi ya bamu damar sauya kayana. Bayan na sauya na gabatar da salolin da suke kaina, ina idarwa Umma ta zuba min tea me zafi a daidai shigowar Ya Ado da Ya Umar, sai Albashir da Ya Tahir, Ya Sani, ba Ya Ubaidullahi da Ya Mustapha, suna shigowa Aunty Hindatu da Aunty Innah suka shigo, zama suka yi akan kafet, ina cin abinci a hankali. Hiransu suke na abin da ya shafe su bayan na gama na shiga ban daki na wanke hannuna da bakina. "Barista ina ga mu bar maganar nan sai anyi la'asar ko kada mu fara mu katse saura minti goma a shiga sallah! " Inji Ya Tahir, "Ok Malam muje ko!" Kallonsu nayi suma kallona suke yi. " Kina son wani abu ne Auta? " Inji Ya Sani, " A'a bana son kome!" Nayi shiru suma basu fita ba Ya Umar ya ce min.." kina son tambayar wani abu ne?" Yadda yayi min maganar a tausashe yasa na ce mishi. " Me ya faru na ganni a nan?" " Baki da lafiya ne!" Kallonsu nayi kafin na ce musu. " Na fara hauka ko? " Idanuna ya cika da kwalla, fita suka yi na hango tausayi a idanunsu, a for the first time da na hango yarda da aminci a tattare da su, bayan fitarsu Aunty Hindatu ta mike tare da alwala tazo tayi sallah, Umma ma haka, nima a zaune nayi sallah saboda yadda nake jin jiri. Tunda na idar da sallah nayi shiru, maganar gaskiya ko addu'a a yanzu na rasa ta me zanyi, ta rokon Allah ya saka ya Hafiz ya sake ni ne ko ta nimawa kaina mafita ne, shigowar Yan mazan ne yasa ni kallonsu, tare da Yadiko wacce take tsakiyarsu, shigowa suka yi Umma ta ce mata. "Ina Yaya Salamatu? Yau kwanaki biyar yarinyar nan tana asibiti bata leko ba? Wallahi zan kira Inna na gaya mata tunda ita bata tsoron Allah a haka zata kashe Yarta." Sai a lokacin na kalle su naga yadda Yadiko take zabga min harara. "Yaushe kika fara shaye-shaye Lubnah meye amfanin wannan abin kunyar da kika aikata?" "Yadiko a dai bi kome a hankali kada azo ana danasani!" Inji Ya Tahir wanda ya kasance dan Yadikon ne na fari. Juyawa tayi a fusace ta fara faɗa. Wani irin kara kaina ya fara na dafe kan ina ƙoƙarin jin kamar ana buga min abu a cikin kwakwalwata. Rike ni Aunty Innah tayi tana faɗin. "Duba min alluran da yake cikin farin kwalba da sauri!" Ba musu Aunty Hindatu ta mika mata, ta ce mata.. "fasa min!" Haka ta bude bakin, sannan ta mika mata, ita kuma ta rike ni domin wani irin jijjiga na fara kamar ana fifigar jijiyar kaina, shiru Yadiko tayi ganin yadda nake jijjiga ga jinin da yake zuba ta hancina, abin ya razanata, dama haka lamarin ya ke. Alluran aka min sannan suka yi tare tare aka daura ni gadon tare da daure min hannuna, barci me nauyi ya dauke ni. Hindatu. "Kai wallahi karya ne Lulu bata san amfanin kwayar da ta sha ba, da ta sani ba zata shiga wannan yanayin ba, imma an jima ana bata tana sha." Cikin fada Yadiko ta rufe Hindatu. Tahir ya ce mata." Yadiko lokaci yayi da ya dace ku san waye yake auren Lubnah kun ga haka muke yiwa Yaran wasu? Me yasa sai ita? Me yasa a duk lokacin da tazo da bukatar a saurare ta ba a bata damar ta fadi abinda yake ranta? Yadiko lokaci yayi da zaku cire kanku, ku kyale mu da Mijinku ya isa haka ya isa haka. Idan da Munah ko Raliya ne a cikin wannan yanayin hakan zaki hana mu magana? Duk lokacin da aka yi abu Lubnah ce mai laifi me yasa ko sau daya kun tab'a tambayarta meke faruwa? " " Amma ka ga yadda muka samu kayan maye da abin hana daukar ciki? " Murmushi yayi ya ce mata. " Waye bai san Hafiz ba? An gaya miki bakiɗayanmu basu san halinsa ba ne? A cikinmu ya tashi fa, a lokacin da Uwarsa ta watsar da shi Abba ya janyo shi jiki saboda nakasar Baban Jama'are, Yadiko ni nan Hafiz ban gaya miki ba ne, Hafiz shine yayi sanadin da na bar shagon Abba, shi yayi dalilin da kowa cikin mu ya bar shagon Abba muka dauki abinda ya mana. Yadiko lokaci ya kure da zamu kyale wannan lamarin." Yadda suka tsaya akan maganar yasa Yadiko tayi shiru ai al'amarin matukar ba kai ya fadawa ba, tow tabbas ba zaka fahimci yadda abin yake ba. Sai da lokacin Sallah yayi suka tafi masallaci, su Aunty Hindatu suka yi sallah har da Yadikon bayan sun idar, suka ci abinci suka ajiyewa yan mazan, lokacin da suka iso an kawo na gidan Ya Umar da Ya Tahir haka suka hadu suka ci, sai karfe tara suka bar asibitin suka kai Yadiko gida. Hafiz Bakiɗaya hankalinsa yayi azabar tashi, domin ya hango kwabarsa zata yi ruwa, yasan matuƙar ya rabu da Lulu tow ba makawa duk abinda yake zai fito fili haka yasa shi kiran Baba Malam suka gaisa ya ce mishi.. "Alhaji ka ga sun dauke min matata, bayan ina sonta don Allah ka saka baki su bani matata wallahi ina sonta zan turo maka da kuɗin mai a saka a mota a kawo ka kaji alhajina." "Shi kenan in sha Allah zan tawo gobe!" Godiya yayi ta mishi yana kara gode mishi. A hankali ya ajiye wayar yana kallon Karimah da take zaune a gabanshi ta hade rai. "Baby Karimcy kada ki damu ai!" "Ya isa haka!" Ta fada tana kokarin mikewa ya janyo ta suka fada wata duniya na daban. *** Kiran sallah farko akan kunne na aka yi shi, na tashi nayi raka'atu fijir, ina cikin sallah Aunty Innah ta shigo, murmushi tayi ta shafa kaina ta wuce ban daki tayi alwala ta zo ta gabatar da sallah nafila, a hankali ta ajiye min wata waya a gefena. "Ki duba akwai Alqur'ani a ciki zaki iya saurarenshi, ga airbon ki hada da shi kada maganar wani ya kara saka ki cikin tashin hankali har ki razana, domin condition dinki yana da matuƙar hatsari kin ji." Gyada mata kai nayi, har ta haɗa min abin karyawa da magani na sha sannan ta koma wurin aikinta. Sai karfe bakwai ta shigo lokacin ta gama zata koma gida. "Zan koma na huta an jima zan dawo bakiɗaya kin ji kina son wani abu ne?" "Duk abinda kika kawo min zanci " murmushi tayi ta shafa kaina tana me rungume ni a jikinta. Tana bubuga bayana. "Ki yi hakuri kin ji kome zai wuce wata rana zaki ga kamar mafarki ne kin ji ko?" Murmushi nayi mata nace mata.."Nagode!" Haka ta mana sallama ta tafi, wurin karfe takwas sai ga Mama da Abba, tsoron ganinsu yasa na rikice ina mai niman hanyar da zan gudu ban daki, amma ba hali shigowar Ya Ado da yaga yadda jikina yake kerma ya zo inda make ya zauna tare da kwantar da kaina a kafad'arshi. "Shiiiiii!" Yake furtawa a hankali, yana matse hannuna rintsa idanuna nayi hawaye na zuba min, a hankali a kafad'arshi. "Tow Yar gata, yar kwai ko nace yar gwal!" "Hajiya Shehu idan kana son tayi aman ƙwaƙwalwarta sai ka gyara wuri ka zauna domin ina ga haka ya dace da ku kai da Yaya Salamatu;" jin haka yasa shi kallon Umma ya ce mata. "Aminatu amma kin san abinda tayi bai dace ba?" "Ai rashin dacewar yasa zance maka kai ka tab'a tambayarta me yake faruwa a rayuwar aurenta? Yanzu yar gurin kishiyata da muka aurar bariya a lokacin ƙaƙa ina cewa saboda ita na fari ce uwar ta watsar da batunda mijin nan yayi ta cutarta ba a sani ba karshe sai da ya dauko mata lalura yarinyar nan ta rasu a wurin haihuwa bayan ciwo ya cinye ta ita da abin cikin ina lokacin da yar take kawo karar koranta muke? Sauyin Lubnah yayi yawa. Shirunta cuta ce ga rayuwarta ko ku shiga lamarin ko kuma muna nan daku zaayi kukan mutuwarta. Da yake Allah ya bata wani mugun jiki ne da baya bayyana tashin hankali da wata ce ta kare tas sai kashi da hakora rakwacan! " Kasancewar Umma Aminatu abokiyar wasarshi ce ita kanta Mama Abokiyar wasan Abba ne domin su Ya'yan mace, shi kuma ɗan namiji. Haka yasa ta hana shi magana kuma akwai mutuntawa a tsakaninsu domin Mijinta da ya rasu aminin Abba ne, cikin nuna damuwa ta ce mishi. "Nasan da Madaki yana raye da shi zai dauki lamarin Lubnah da muhimmanci, gaskiya abin ba dad'i duk da har yau bata ce mana uffan ba, shiru idan yayi shiru mace idan ta tashi mutuwa aman jini take yi saboda lokacin da ya dace tayi magana an rufe mata bakinta." Ambaton Madaki yasa Abba ya juya yana faɗin." Kai anan zaka lalace ba zaka koma aikinka ba!" "Zan koma ina son na ga yadda al'amarin zai kasance ne!" Juyawa Abba yayi ya zuba masa idanu kafin ya harare shi. "Kada ka sake ka lalata mata aure domin ba zan dauki haka a matsayin kuskure ba." Shi dai bai ce kome ba har ya janye ni a jikinsa ya rako Abba da yake Mama zata zauna da ni. Har ya dawo ya samu ina karyawa, ban yi magana ba, amsar nashi abun karyawa yayi yana waya da Aunty Zakiya har da mika min na gaishe ta daga haka nayi shiru na cigaba da karyawa. Mama ta fara magana a hankali. "Shi rayuwar aure dan hakuri ne." "Ai kuwa idan irin na Lubnah ne kabari ne wurin zamanta kawai domin daga alamu kun fifita zumuncin uban yaron akan Yarku!" Jin haka Mama ta rufe Umma da Fada itama Umma ta hau sama suka rikito ashe itama yar bala'i ce, daukar airbon din nayi na saka a kunne na, na fara ƙoƙarin kunna karatun Alkur'ani, sannan ba kure karar, yadda ba zan tab'a jin muryansu ba. Haka ce ta faru kuwa, sai abin ya zo min da sauki har suka gama hayaniyarsu ban san me ya faru ba don Ya Ado yana gefena har barci ya dauke ni. Gyara min kwanciya yayi, bai kashe karatun ba ya cigaba da yi. Karfe daya na rana na farko a lokacin wai Mama ta tafi da na tambayi Umma Aminatu sai tabe baki tayi wai tana faɗin.. "taga ni da lauya munki bin bayan shegen Yaron nan shine ta yi zuciya Allah yasa ta daka da kafa har Dutsen tanshi idan tana da zuciya." Wanka nayi nazo na gabatar da sallah, ina addu'a Ya Hafiz da Baba Malam suna shigowa, wani irin bugawa kirjina yayi wanda ban san lokacin da hawaye ya zubo min ba. Gaishe Baba Malam Umma Aminatu tayi tana kallon Hafiz da yake kallona cikin jin dadi. "Kaso daga gidanka a wuce da ita dungulbi ko?" Take ya gyara fuskarshi yana kallon Baba Malam.. "yanzu ba wannan ba yaushe da a sallame ta ne ta koma dakinta. Na kashe wannan maganar domin na samu Usmanun na gaya mishi na kashe zancen nan har abada a bashi matarsa Allah ya taya shi riko! " Kaina a kasa har aka turo kofar yana kara jaddadawa an kashe maganar, Ya Umar ya ce mishi. " Magana dai bata mutu ba, sai yq gaya mana inda ya kai mata da duk abinda ta mallaka. " " Umaru ina magana kana magana da nuna min abinda na isa da shi!" Gyara tsayuwa Ya Hafiz yayi yana kallona, kafin ya ce musu. " Gata nan ku tambaye ta yadda tayi da dukiyarta? Har shaidu ina da shi, yarinyar nan Alhaji nayi hakuri da ita yarinyar da ta bada jinginar gidanta kawai don a bata kwaya ta sha, meye ne ban mata ba? Kayan sawanta ta haɗa ta sayar kome nata ta sayar wallahi na rantse da wanda rayuwata take hannunsa yarinyar nan ba karamin bashi ta cillani ba, Alhaji kasan yadda nake kaunar Lubnah amma ni yanzu idan yan uwanta suka ce ba zata zauna da ni ba, zan iya hakura da ita ba gaji! " Yadda na kafe ya Hafiz da idanun yasa ji wani abu me daci ya cika min wuyana. Ban san yadda aka yi duk soyayyar da nake yiwa Ya Hazif ya dawo kiyayya ba, shin dama ba soyayya ba ce to idan ba soyayya ba ce mece ce nayi mishi? A sanina dai na kaunace shi, nayi mishi biyayya na wulakanta kaina na boye kaɗan daga cikin miyagun halayenshi, kura mishi idanu nayi ban iya magana ba, haka akayi ta rikici ni dai har lokacin ban ce kome ba, kuma bana son na ce kome, haka suka tafi ashe bayan barin asibitin babban rigima aka yi da Baba Malam wanda ya tilasta Abba cewa daga asibiti idan aka sallame ni a wuce da ni gidan Mijina. Ba zan mutu ba sai naga karshen Ya Hafiz haka yasa koda na warke aka sallame ni ban cewa kome daga abinda yake faruwa ba, haka suka yi ta bina akan na musamman abinda ya fada karya ne nace musu A'a ai gaskiya ya faɗa, wannan abin da nayi ya fusata yan uwana, haka suka mai da ni dakina, tunda na fahimci an gyara min dakin an saka min sabin kayan dakin, sai na tsaya a kaina da zuciyata dole na kwaci kaina a hannun Ya Hafiz, amma ta ya? Shine ta hanyar shigar da shi kotu amma kuma idan na kai zancen kotu ya familyna zasu dauki al'amarin, sai na kara jin na shiga wani irin damuwa mai danne zuciya. Hankalina yayi azabar tashi. Bani da hanyar da zan iya yakince Ya Hafiz a rayuwata sai na ji bani da wani kwarin gwiwa, tunda na dawo kuwa iskanci da cin zarafi sai da yafi na baya, gori kuwa ina shan shi, tun ina dauke kai har ta kai da idan na rama sai ya dake ni, haka yasa na kara shiga wani irin kuncin rayuwa, domin kuwa Ya Hafiz ya saka Abba haramtawa kowa zuwa inda nake, haka yasa babu wnada ya san halin da nake ciki, sau biyu ina faduwa a ban daki. Haka zan farka na ganni dauke da karin ruwa. Faduwar da nayi na biyu ranar Maman Boy ta shigo ta ga na fadi suka kama ni suka kai ni daki, suka yi ta min fifita dama ya dake ni kenan ya fita shine na fadi, itama Karimah ta fita abinta. "Har ga Allah lokaci yayi da zaki samawa kanki Yanci idan kika kai shi kotu kudin wanke muni zaki biya!" Shiru nayi ina nazarin maganar, bayan fitarsu. Ina kwance na kira Ya Ado. "Ya Ado!" Amsa min yayi kafin ya ce min.. "na'am Auta!" "Ya Ado idan nace zan rabu da Ya Hafiz Abba zai hana ni wurin zama!" "Are You ready!" *Wannan littafin na kudi ne* *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI* Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu SHA ƊAYA. Kamar yana gabana na gyad'a kai ina jan hancina. "Lubabatu kin shirya rabuwa da Hafiz ko baki shirya ba?" Sai na ji tambayar ya zo min a wani irin rude, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, na rasa meke min dad'i shin mai yayi zafi da zan kashe auren. " Abba zai kore ni!" Ina jin yadda ya sauke numfashi ya ce min. " You're not ready!" Ya kashe wayar. Haka na cigaba da kuka na rasa yadda zan saka kaina, haka na wuni suku-suku har dare yayi ban daura abinci ba, ko da Ya Hafiz ya dawo ganin babu alamar na daura aninci sai bai ce kome ba, ya fita ya sayo abinci ni kuma ko kallo bai ishe ni ba, ina da sauran kayan tea shi na sha na kwanta. Tun daga lokacin wani irin kunci da kasala ya shige ni, a daddafe nake ibada da alamarun gidan wanda ya dauki idanun ya zuba min, ina kiyaye lafiyata domin duk bayan sati biyu ina zuwa ganin likita wanda su Mama ba su sani ba, haka muka ci gaba da zama, ba ana haka Azizat matar Ya Tahir ta haihu, kiri kiri ya hana ni, zuwa. Nima kuma ban damu ba, ana gobe suna Ya Tahir ya zo gidan da kanshi, ya same shi tunda ya ga Ya Tahir yayi ta kame kame. "Nace ai ta je ita ce!" "Ko dai kai ne baka yarda ta je ba, Hafiz mun fa san halinka!" " Wallahi Attahiru ba haka ba ne, kasan yanayin ne yanxu tana zuwa ta ga su Inna da Hindatu, zasu zuga ta ai." Murmushi Ya Tahir yayi ya ce mishi. " Yaushe zaku bar gidan nan an kusan shekara biyu kenan a gidan nan?" Shiru yayi yana kame kame kafin ya ce mishi. " Ai dama wancan gidan ban san lokacin da ta sayar da shi ba! " Fitowa nayi daga cikin dakina na zuba mishi idanu. Na kasa magana kawai sai ya rude. " Lulu!" Juyawa nayi na koma dakin, na kwanta. Wacce irin kiyayya ya Hafiz yake nuna min ne? Me nayi mishi da baya gudun jogana min laifi ko mi kankantarsa? "Auta! " Tashi nayi da kyar na leka wajen. Mika min kudi Ya Tahir yayi yana faɗin. " Nasan you are broke, gashi ki rage na abin zuwa gobe suna. " Kallon kudin nayi nace mishi. " Ina da kudi Ya Abba ya turo min shekaranjiya, Ya Almu ma ya turo Ya Sani ya ce idan nazo gobe zai bani sabon waya ya ishe ni." Ina son naga reaction din Ya Hafiz kuwa Allah bai kunyata ni, sai ga eyes ball dinsa kamar zasu fado kasa kuma maganar gaskiya babu wnada ya bani kudin so nake na ga yadda zai yi, "oya karba nima ga nawa!" Inji Ya Tahir ya juya yana faɗin. "Ina jiranki fa gobe da wuri domin akwai liyyafa kin san wannan ne farkon samun Ya mace a gidana, kuma ina son nayi surprise dinki ne!" Murmushi nayi na fito ina rako shi, juyowa yayi ya riko hannuna har kofar gidan wurin da ya ajiye motarshi, ina murmushi ko ba kome nayi farin ciki, nauyin da nake ji a raina ya ragu, a kofar gidan su Maman Na'ilah suka zo wucewa sai rike baki suka yi suna faɗin. "Kunga autar Yadiko da Mama!" Murmushi nayi ina mai gaishe su, Yaransu da yake bana rabuwa da su, suna yawan shigo min haka yasa suka tawo wurina da gudu, Ya Tahir ya saka hannu a aljahun ya ciro kudi ya bawa Yaran, iyayen suka yi ta godiya tare da ni. Bayan tafiyarsu ya kalle ni. "Allah ya hadaki da mutane kirki!" Gyada kai nayi, ban ce kome ba daga haka ya kalle ni. "Auta you are suffering." D'ago kai nayi ina kallonshi, murmushi nayi nace mishi. "Abba yace duk lokacin da na kashe Aurena na nime wani uban!" Yadda nayi maganar a sanyayye, sannan na d'ago kai ina murmushi, murmushi yayi min ya ce min. "Mu ai muna raye ba zamu tab'a barin haka ya faru ba." Shiga mota yayi yana d'aga min hannu, murmushi yayi min tare da jan motar ya bar kofar gidan, na juya ashe ya Hafiz yana tsaye, shiru nayi ashe shi yasa ya janyo ni kofar gida, kuma wani abu maganar kudin nan bai bar ranshi ba, ina isa bakin kofar ya mika min hannu. "Wata nawa baki biya kudin haya ba!" Kallonshi nayi a hankali na ce mishi. "Ai kayi sanadin da aka hana ni sana'ar balle kace na biya kudin haya!" Bai ce min kome ba sai da ya shiga cikin gidan ya wani taka min kafa sai da kashin kafar naji yadda yayi kara ya ce min. "Sannu ba da gayya ba ne!" Yadda nayi zafin kamar an zare min raina haka nake jin ciwon haka nayi ta takawa har cikin dakina wanda ya ragani isa yayi maza ya dauki wayata yayi ta saka number check balance, amma bai ga kome sai wasu yan iska dari biyar da dubu daya, da yake account biyu ne da ni. Haka ya gama dube dube a wayar tunda dama keypad ce, haushi ya kama shi ya wurga min wayar na dauki abina ina me ninke hijab dina, ganin sa gaske naki kula shi. Sai ya daddume ni ya shiga ƙoƙarin kwace kuɗin ni kuwa naki, gani zai zai cutar da ni na gantsara mishi cizo wanda ya saka shi kara tare da shake min wuya kamar zai kashe ni. Sai da ya ga na fara fita hayacina sannan ya sake ni. Dakyar nake sauke numfashi, sannan ya kwashe kudin ya watsa min dubu biyar yayi gaba abinsa. Hawaye ne ya zuba min in sha Allah na fita na fita kenan. Ina kwance a wurin har aka kira sallah Magariba kafin na lallaba shiga ban daki nayi tsarki na zo nayi alwala na shiga dakin nayi sallah ina zaune. A wurin har aka kira sallah isha na mike na gabatar tare da shafa'i da wutir, sannan na kwanta a wurin, idan na kyale ya Hafiz wata rana zai kashe ni. Kwarai na gano kiyayya a cikin idanunshi. Dama tun can Ya Hafiz bai sona ne? Idan har haka ne tow meye amfanin zaman da shi. Haka na kwana washi gari na shirya zuwa gidan suna, sai da na biya gidan Maman Na'ilah na amshi jakar kudin nan, bayan na cire mata itama kudin da ban saj nawa bane, na juya na fita tana ta min godiya, daga nan gidan Aunty Hindatu na fara zuwa ita tana unguwar Federal locals ne, nan na fara zuwa, tana ganina ta fara tambayata. "Auta lafiya?" "Lafiya kenan!" Na shiga na zauna Mijinta Alhaji Mas'ud ya fito cikin shirin zuwa kasuwa. "Matar roba kece a gidanmu!"gyada nayi, "Kiyi hakuri har kika kwanta ban samu zuwa ba na tafi umara ne amma ita wannan matar karfen bata gaya min ba sai da na dawo!" "Na gode Angon bogi!" Murmushi yayi ya ce min. "Tow ayi min addu'a zan tafi kasuwa!" "Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya!" Muka fada ya fita Aunty Hindatu ta bishi har waje sai da ya fita ta dawo tana kallon yadda nake a takure wuri guda. " Lafiya Lu'lu'a!? " Kaina a sunkuye na ce mata. " Na shirya rabu da shi!" Wani irin sujada tayi tare da ambaton Allah, ta rike hannuna. " Da gaske! " Hawaye na zuba min na ce mata. " Eh! " Na gyada kaina ina cizon bakina. Wato ban tab'a jin kwarin gwiwa ba irin na yau sai da ta kira conference call bakiɗaya aka hadu ina jin su, tambaya daya suka yi min na shirya rabuwa da Hafiz Ali Umar Jama'are? Na ce musu eh ma shirya. Aunty Hindatu ta gaya musu na zo da kudi, da yadda za ayi da kuɗin. Murmushi Ya Ado yayi ya ce shi kenan. " Baby girl get ready muna bayanki! " Haka muka gama muka tafi gidan sunan amma bamu tafi lokaci

Chapter 8 of 13