yayi ya ce mata. " Wani sati zamu tafi na gama shirina, zaki bi Hajiya da Yara zuwa Jama'are! " Ya fada yana fita daga part din, tabbas yayi shirme, amma yasan idan har ya samu hadin kan Lulu kome zai tafi yadda ya tsara.
Lokacin da ya koma, tana zaune akan abin sallah, hannunsa dauke da wata cadi yayi shiru cikin doguwar rigan jikinshi. Ya yi jugum kamar wanda yake ciwo, a yau daya na hango ramar da yayi kafin ya kalle ni cikin karfin hali ya ce min. " Kin idar ne? " Gyada mishi kai nayi ina kallonshi, domin duk ya bani tausayi sai na rasa me ke min dad'i na matsa kusa da shi na, daura kaina a kan gwiwarshi, shiru yayi kafin ya ce min. "Allah ya jarabce ni a kwanakin nan, duk yadda nake son nayi ƙoƙarin dauke kaina amma na kasa." Shiru yayi yana jan numfashi, ya kwantar da kanshi a jikin kujera yana haki. " Ya Hafiz me kake bukata? Ya Hafiz baka yarda xan iya kome akanka ba ne??"
Girgiza kai yayi yana faɗin, "Lubnah ba zaki iya ba, ni da nasan ba zaki iya tunda kwanankin baya yan uwanki sun bukaci mu rabu gara kawai na sallame ki, na kare rayuwata a gidan Yari, domin nasan karshe na a gidan Yari zan gama rayuwata!" Na kaɗu da jin zai kare rayuwarsa a gidan Yari, haka yasa na shiga damuwa nayi ta rarrashinsa da mishi alkawarin duk abinda yake so ya gaya min xan mishi.
Haka muka cigaba da zama har aka yi sallah isha ya tafi masallaci.
Hafiz
Fitar da yayi ba masallaci ya nufa ba, bangaren su Hajiya ya nufa, ya zauna domin sallah dai baya yinta, kome za ayi sai dai a yi amma idan akan sallah ne ba zai tab'a yin ta ba. Haka ya zauna ya yi shiru Hajiyarsa ta ce mishi. " Hafizu ka barmu cikin duhu meke faruwa ne? " Shafa kanshi yayi kafin ya ce mata. " Ba kome. " " Wani irin ba kome? Me ya faru? " " Wato Hajiya Yan uwan Lubnah suna son su raba mu. " Nan ya kwashe kome ya gaya mata, shiru yayi yana kallonsu. " Yanzu saboda haka ne ya dauko ni? " Girgiza kai yayi yana lashe busashen lips dinsa yana kallon kasa. " Ba saboda shi ba ne. " A hankali yayi shiru ba zai tab'a fada ba, ko zai mutu ne domin bai yarda da Hajiyarsu da Tijjani ba, kai hatta Karima bai yarda da ita ba, shi a duniya yafi yarda da Lubnah akan kowa.
Ana idar da sallah ya mike zai fita Karima ta ce mishi. "Bamu ci abincin dare ba!" "Baki da hannu ne, kin manta halin da nake ciki ne? Ita kanta ta rude balle ni ta san me zata dafa, ki shiga ki dafa muku. " Ya fita daga parlourn.
Parlourn Lubnah ya isa ya zauna yana kallon tv, sannan yana jin motsinta a kitchen. Yasan zata yi wani abu amma shi abinda yake bukata yafi karfin abinda zai ci,. Shiru shiru bata fito ba, sai ya fara tari kamar wanda ya kware.
Haka yasa na ji tarinsa na fito da sauri ina faɗin," sannu Yaya kwarewa ka yi? Bari na kawo maka ruwa! " Na koma kitchen na kawo mishi ruwa da sauri na bashi ya sha yana sauke wata irin ajiyar zuciya da nishi mai karfi, sai da ya tsinkar min da zuciya. Daura kanshi yayi akan kirjina yana ajiyar zuciya. "Luluna ina cikin tashin hankali, mutuncina da kimata zata zube. " " Ya Hafiz meke faruwa ne? Idan Baban Bauchi yaji ranshi zai b'aci" a wani zabure ya mike zaune yana kamkame ni," don Allah kada ki gaya mishi, Innalillahi wainnalihir rajoun, don Allah ki rufa min asiri wallahi idan ya ji zuciyata zata buga. " Kamar yaro me tsoro haka ya koma min, ina son Ya Hafiz son da bana yiwa kaina. Shima kuma yasan haka ina sonshi so na hakika, don haka ya kara gigicewa yana mata gungun kamar mai cutar farfadiya. Shafa bayanshi nake ina bashi hakuri da rarrashinsa.
" Ya Hafiz meke faruwa? " Shakuwa ya fara tare da buga kirjinsa, haka yasa na mike tare da kawo mishi ruwan da na ajiye a saman Centre table, na bashi ya sha. Jin kauri a kitchen yasa na wuce da sauri na sauke jallop din taliya da kifin da nayi na zubawa Hajiya sannan na zuba mishi na zuba nasu karima da Yaranta sai na Tijjani, na saka a katon tire, na fita da shi zuwa bangaren Karimah, koda na isa na samu suna ta hiran halin da Ya Hafiz yake ciki suna jajjantawa. " Yanzu idan har bai yi wani abu ba zai iya fuskantar fushin hukuma kenan Hajiya? " " Eh kai Yar nan, kuma kin ga ai fushin hukuma babban tashin hankali ne domin ba mamaki su wuce da shi gidan Yari! " Wato sune suke magana amma ni ce hantar cikina yake kad'awa, "Allah ya kyauta in sha Allah haka ba zai yiwu ba!" Na fada musu ina ajiye musu abincinsu. "Zai yiwu kai tunda baki haihu da shi ba, taya zaki fahimci halin da yake ciki, idan kika tuna halin da Uban Yaranki zai shiga kome kika mallaka zaku kashe shi a nan wurin, ki sani ba zance zan rabaki da Hafiz ba. Amma ina ganin lokaci yayi da ya kamata Hafiz ya hakura da ke domin ke ba matar rufin asiri ba ne? Tunda har ta kai ya saka wannan gidan a kasuwa." Dafe kirjina nayi cikin wani irin bugawa da yake kamar zuciyata zata dirko daga kirjina, "haba Hajiya me yasa zaki gaya mata? Me yasa zaki bari ta sani? Idan wani abu ne na amince zan fuskanci hukuma akan laifina gara na fusk." Rufe mishi baki nayi ina girgiza kai. " A'a don Allah kada ka ce haka, ba zaka sayar da gidan nan ba! "
" Au ka ji ba, saboda gidanta ne, gidan da Ubanta ya saya maku, da ace gidanka ne wani ya isa ya hana ne? " Maganganun Hajiya suka kara birkita min ƙwaƙwalwa sai kaina ya fara juyawa, na fita da gudu na nufi dakina.
Bayan fitar Lulu suka kwashe da dariya, Hafiz ya ce "mahaukaciyar banza yanzu zata dauko jikinta yana rawa. Amma kun taimaka min." Tijjani da ya cika bakinsa da abinci ya ce musu. "Amma maganar gaskiya, ya kamata ka kyale yarinyar nan, iya adalci ta maka tayi maka kome, idan ka cigaba da abinda kuke akwai lokacin da kome zai lalace wallahi." "Dalla yi min shiru, ba gara shi ba kai ina sai dai na rike ka na rike matarka." Inji Hajiya, "Kyale shi Hajiya ai yadda Lubnah take kaf duniya babu me iya juya ta sama da ni, sannan idan kana ganin zata iya rayuwa babu ni zan gaya mata a gabanka zaka ji me xata ce, kuyi shiru gata nan zuwa!"
A hankali na shigo parlourn ba kome a tare da ni, suka zuba min idanu. " Ya Hafiz ko zaka zo! " Shiru yayi kafin ya mike yana dafe kirjinsa da yake nuna min alamar yana mishi ciwo. " Don Allah riki ni, jiri nake ji." Haka na matsa jikinshi, muka fito har zuwa parlourna, ya zauna a dogon kujera ya kishingida yana lumshe idanunshi. Dakin na wuce na dauko kwatin yan kunayena,. Na ajiye mishi sannan na koma gefe na zauna. "Ban san me ya faru ba, amma ga shi ka. Biya abinda ake binka." Kallona yayi kafin ya dauke kai yana dafe kirjinsa. "Lubnah bar dukiyarki kada yan uwanki su ji, su kara himmar raba mu, ki barshi kawai Allah yana nan." "Kudin ne ba zai iya ba?" Hawaye ne ya zubo mishi ya ce min. "Wato wani ƙaddara ne ya fada min, a shagon Baban Bauchi. Gashi saura kwana uku na hada kudin." "Baban Bauchi bai sani ba ne?" Dafe kanshi yayi da hannu bibbiyu yana nishi. Ban san lokacin da na kara rudewa ba, na riko hannunshi tare da janyo shi jikina ina tab'a shi. "Ya Hafiz ko mu tafi asibiti ne? Innalillahi wainnalihir rajoun! Ya Hafiz lafiya?" Yadda ya mike min kamar gawa yasa na kara kidimewa, garin juyawa na ci tuntube da center table din parlona, ban damu da zafin ba amma har cikin raina na ji ciwon sai dai halin da Ya Hafiz yake ciki yasa na manta da ciwon da naci, sai na kasa gane kukan da xan yi na ciwon ne ko kuma na halin da ya Hafiz yake ciki ne? Bakiɗaya na shiga tashin hankali, ban san adadin soyayyar da nake yiwa ya Hafiz ba, haka yasa na kara birkice na rungume shi, ina kuka sosai, domin zuciyata ta karye ainun. Bana son naga abinda zai d'aga mishi hankali, a daren muka kai shi asibitin ni'ima aka bashi kulawar da ta dace har da karin ruwa, Tijjani muka bari a can asibitin muka dawo gida, Hajiya sai kuka take, tana shashekar duk sai naji na damu da kai, dakyar muka dawo tambari inda Unguwar yake, na tura kan motata zuwa cikin gidan, dama motar da yake hawa tawa ce, tunda ya sayar da tashi kwanakin baya ya dauki tawa yana amfani da shi.
Koda muka fito Hajiyarsu ta ce min. "Lubabatu dama nace ko." kallonta nayi ina son naji me zata ce, sai ta ce min. "Dama kada ki gayawa Iyayenki halin da ake ciki domin idan kika gaya musu abin ba zai yi dadi ba, idan babanku na Jama'are yayi cewa ga abinda ya faru. Ki zama mace mai rufawa Mijinta asiri haka zai saka Allah ya rufa miki ta yadda baki zata ba." Gyada kai nayi ina faɗin.. "in sha Allah Hajiyarmu!" Na fita daga motar na nufi cikin gidan, na rufe bangarena parlourn na zauna nayi ta tunani kafin na shiga na kwanta, karfe biyu da arba'in da biyar na farka sallah dare, ina yi ina gayawa Allah kuka ta da matsalata, nayi tawassali da sunayen Allah tsarkaka, Allah ba zai tab'a wulakantamu ba.
Ina zaune har aka yi sallah asuba, sannan na yi raka'atu fijir, ina idarwa na daura da sallah asuba, sannan na fita na fere doya na daura a wuta, sannan na daura ruwan tea, a hankali nake bin kome ina lissafin yadda xan shawo kan matsalar ya Hafiz, wurin karfe bakwai sai ga Tijjani yazo daukar mota zai je dauko shi, "kenan ba sai an saka muku abincin ba zaku dawo ?" "Eh!" Ya ce ya fita, kafin bakwai da rabi, na hada abincin Yusrah na kai mata, na tashe ta na mata wanka, sannan na shiryata tana ihu, sai ga Hajiya ta fito. " Wai me kike mata ne? " " Wanka na mata Hajiya zan shiryata ne! " " Wanka ko mugunta? Ke fa muguwa ce ba mamaki ruwan da zafi kika yi ta kona mara mutunci, ke baki haihu ba amma salon muguntarki yafi karfinki wallahi ki ji tsoron Allah! " Kwalla ne ya cika min idanu, na gama shiryata na kawo mata abin karyawanta, tana sha tana kukan rashin mutunci. " Ni tea din ya min zafi, yana kona min baki kaka yana kona min baki! " " Ai dama nasan muguwa zata kashe ki ne! " Hajiya ta fada tana daukar tea din ta kurba, sai zare idanun tayi tana faɗin. " Takwara ai ba wani zafi, yadda yayi sanyin nan ma kulle miki ciki zai yi! " Kamar nayi kuka haka na bata doya ta furza min a fuska. " Ni kin cika yaji! " Wani irin bakin ciki naji ya cika min rai, na ce mata.. "ayya Yusra me yasa kike min haka ne? Ki ci don Allah!" Kamar nayi kuka nayi maganar, sai tura baki tayi tana faɗin. "Ba zanci ba." "Ai ba dole ba ne sai ta ci a barta haka don Allah!" Haka na hakura na barta, na kuma wuce na barsu na kawowa su Hajiya nasu don ta fara min ihun ita yunwa take ji taliyar jiya bai rike ta ba.
Haka na kawo abin karyawan, tana ci tana faɗin. "Kin iya girki amma salon mugunta irin naki sai kin azabtar da mutane!" Kaina a sunkuye na barta na riko hannun Yusra na kai ta makaranta, har lokacin ban ga Karima ba, sai da na kaita makarantar na juyo zan dawo gida, na hango su Ya Hafiz, na zata zasu tsaya su dauke ni ne, a'a sai suka yi tafiyarsu. Haka ba karasa gidan a gajiya na shiga na hada mishi abin karyawa yana zaune a parlourna, sai da yayi wanka ya dawo ya zauna yana karyawa hajiyarsa ta shigo ita da Tijjani da Yasir da har lokacin bai yi wanka ba. "Lulu waye zai yiwa Yasir wanka ne ?" Ya Hafiz ya tambaye ni, "ni ce!" Na fada ina daukar yaron da ya fara tsalla ihu, haka yayi ta ihu har kaina ta fara wani irin juyawa, gashi ya cika kashi a pamper dinsa, haka na wanke na mishi wanka na fito na shirya shi, garin shirya Yaron nan na kara fama tuntube na, wani irin kuka ne ya so kwace min, haka na daure na kai shi waje na koma daki na shiga ban daki na fashe da kuka, don sai yanzu na lura da farcen kafana ya fashe, baka hawaye yake zuba min ina jin kamar na mutu da bakin ciki, haka na gasa kafar na fito nayi wanka, na shirya cikin material.
Bayan na saka kwalli da man baki na fito, na samu sauran abin karyawan nawa da yake kitchen Hajiya da Karima sun dauka sun cinye, kitchen din na koma na dafa indomie da kwai, na zauna a kitchen din naci, sannan na fito na samu suna ta magana. Shi kuma yana zaune yana jin su, can aka buga gidan na zata Almajirin da yake min aiki ne, na koma daki tare da dauko Hijab na saka sannan na fita na bude gidan, wasu magidanta ne guda biyu, suka shigo gidan. "Alhaji Hafiz yana nan?" "Eh yana cikin bari na mishi magana,!" Na fada tare da nufar cikin gidan, "tow mun gode" haka suka jira na koma parlourn na ce mishi. "Ya Hafiz kana da baki a waje" "sun iso kenan?" Ya fada yana yatsina fuska. "Yaya kasan likita ya ce kada ka saka damuwa a ranka domin zuciyarka tana dab da bugawa!"
Lumshe idanunshi yayi ya bude a kaina yana min alama da idanu wato naji dai. Sunkuyar da kai nayi ya fita, shi da Tijjani, Hajiya ta zauna tana ta zuba kwadayi tana bawa Karima labarin yadda ta sha wahala akan Ya Hafiz ni dai na wuce kitchen na wanke kayan da nayi amfani da shi, sai gashi ya shigo kitchen din, "Ina takardun gidan nan?" "Yana dakina!" "Ko zaki bani aron gidan na sayar idan na biya bashin da ake bina zan!" Rufe mishi bakinsa nayi da hannuna, ya sumbaci hannun yana cire bakinshi a hannun ya tako har jikin dogon deeper freeze na, ya haɗa ni da jikin freeze din ya shiga sumbatar goshina da manyan kumataina. Abu daya nake bukata a gare shi, shine soyayya amma na rasa ni dai a bangarena bai rasa soyayyar da nake mishi ba, haka ya gigita ni, daidai shigowar Karima kitchen din ta kawo kayan da suka ci abinci da shi, ganin halin da muke ciki yasa ta jan tsaki tayi waje, sake ni yayi ya ce min. "Maza dauko min na manta mun bar mutane a waje!" Haka na wuce dakin na dauko takardun bakiɗaya, na mika mishi kamar wacce aka katse min tunanina da lissafina haka ya amsa ya fita, ban kara ganinsa ba, sai karfe daya da ya dauko Yusra, suka shigo na zuba mata abinci tana ci sai ga Hajiya ta shigo dama tuwo nayi miyar shuwaka, na kawo mata abincinta, ta fara ci tana mita. "Kin san yadda na tsani shuwaka shine kika yi miyar fisabiilillahi gudawa zanyi!" "Ki yi hakuri Hajiya ban sani ba ne!" Na fada ina bata hakuri, na kara kallonshi na ce mishi. "Yaya Mama bata ji dadi ba, ina son na je na gaishe ta!"
"Daga nan ki gaya musu ya sayar miki da gidanki ko?" Inji Hajiya, girgiza kai nayi na ce mata. "Haba Hajiya wannan fa duk bata taso ba." Hayayyako min tayi kamar zata rufe ni da duka, "Hajiya ai ta gaya miki Mama bata da lafiya ne, ki kyale ta an jima ta je. Luluna ki shirya ki tafi kin ji idan na gama zan zo daukarki!" "Shi kenan na gode!"
*08130269641*
[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu
HUƊU
Wani irin dad'i ne ya lullube ni, na gyad'a mishi. Ina me da hawayen da suka fara cika min idanu, murmushi yayi ya ce min. "Tashi ki je ki fara mata abinda zaki kai mata!" Mikewa nayi ina ta godiya. Domin ya min abinda ban zata ba, haka na wuce dakina, na sauya kayan na fito ina zuwa na samu basu nan shi da Hajiyarsu, kitchen na wuce.
Hafiz
"Hajiya me yasa baki da hakuri ne? Kina irin wannan ba sai ta fara jin wani abu a ranta ba? Hajiya gaskiya ki daina min haka, kin ga yadda Allah ya taimaka asirina ya rufu akan wannan lamarin."
" Amma Hafiz kasan dole dai mu kula domin tunda yan uwanta suka fara zargin wani abu dole mu kara mikewa. " Murmushi yayi ya ce mata. " Hajiya ni ba kamar ki ba, a wurin Lubnah bana buƙatar boka ko Malam, idan na tsaya ga kaina ina alfahari da haka, don Allah kada ki saka mata magana a bakinta."
Shiru Hajiya tayi tana faɗin. " Tow shi kenan amma ka kula domin kuwa Malamin nan ya ce a cigaba da kulawa." " Na gaya miki ni ban yi wani aiki da abinda ya fada ba, ni kaina Aljanu ma tsorona suke." Daga haka ya bar gidan, duk sai Hajiya ta shiga damuwa, ta dauki wayarta ta kira Malaminta, ta gaya masa abin da yake faruwa. Shiru tayi kafin can ta ce mishi. " Toh bari na turo maka da kuɗin!"
*
Ina ta aiki gyara kayan miya sai gaKabiru almajirina, mikewa nayi ina faɗin. "Ka iso? Ko zaka fara da shara sai kazo ka sayo min kaza." Durkusawa yayi yana faɗin. " Ina kwana Aunty? Eh na iso shi kenan!" " Shi kenan kayi sharar ina jiranka!" Na cigaba da aikina ya shiga share filin gidan bakiɗaya, ni kuma na cigaba da aikina. " Kai Uban waye ya baka izinin shigowa?" Dariya Karimah tayi tana faɗin. " Hajiya ai almajirinta ne. " " Eh samun wuri!" Yana cikin sharar sai ga Ya Hafiz tare da Tijjani, suka shigo ganin Hajiya a filin gidan suka tsaya. " Hajiya lafiya? " " Ina lafiya ashe gidanka har yayi arahar da kowani kare da doki zasu shigo? " Kallon Kabiru yayi ya hade rai. " Idan bai shigo ya taya ta da aiki ba me kike so nayi? Ita wannan me ta iya? Kin ga Hajiya ban kira ki, ki zo ku rusa min gida kamar yadda kika rusa gidan Nuru ba, ba ruwanki na gaya miki!" Shiru tayi tana da wani sunkuyar da kai.
Ina gama hada abinda nake ya shigo. " Luluna sannu ko zaki zo ina son magana da ke?" " Tow "na fada wanke hannuna, a bakin kofar parlourn na ji muryan Kabiru na fito na same shi mika mishi atm dina nayi na ce mishi. " Kaji guda uku, zaka sayo sai kifi kilo biyu da rabi ka ga bani da lokaci ka dawo da sauri don Allah!" " Tow Aunty!" Ya saka kai ya fita, na bi bayan Ya Hafiz zuwa dakina. Ina shiga na same shi a tube, yasan ina da aiki me ya kawo irin wannan lamarin yanzu? Kamar nayi kuka na ce mishi.."Ya Hafiz ko!" "Hakkina nake so!" Yadda yayi min magana take ya koma Ya Hafiz din da na sani, kwabe kayan nayi na haura gadon, .kamar yadda na sani ko minti goma ba ayi ba ya fara nishi daga nan ya sauka ya saka kayansa ya fita, ni kuma na wuce ban daki nayi wanka na sauya kaya, ina fitowa na sami Hajiya da Karima a parlourn, sai wani irin kallo suke bina da shi. "Akuya tana haihuwa domin ana kwasar Yaranta zuwa kasuwa, ke kuma sai dai ki tsotse min Yaro, bakya gaba ba kya ba." Shiru nayi na wuce kitchen na wanke shinkafa na zuba karasa da pea da green beans da karas ,na daura akan wuta na juye ruwan zafi a kai. Na daidaita wutar ina jin kamar na hadiye zuciyata. Ina cikin aikin Kabiru ya yi sallama na fito na amshi kayan na wuce ciki suna parlourn suna cigaba da zagina. Abin karyawar da na hada mishi na kawo mishi, sannan na ce mishi.."ko xaka dawo an jima ban gama ba rana ba!" "Ba kome Aunty na gode!" Yayi sallama ya tafi ni kuma na cigaba da aikina wurin karfe biyu saura na zuba abincin yan gidan, sannan na shiga wanka na sauya shigata cikin wata lace peach colour na fito ina gyara daurin dan kwallina, kitchen din na shiga turus nayi cike da mamaki. Hajiya ce ta bude kular abincin da miyar da xan kaiwa Mama, ban ce mata cikanki ba na ce wuce inda na daura farfesun kifin na sauko a hankali, na dauko wata kula na juye shi a hankali, kamar wacce kwai ya fashewa haka ta saka kai ta fita. Bayan fitar ta na d'ago tare da isa wurin kular na kara gyarawa sannan na dauko sauran da na rage na karyawa na kara sannan na gama kome na saka a basket na fito, daidai isowar Kabiru na koma kitchen na dauko mishi nashi sai godiya yake ta min, bayan na sallame shi na dawo na shiga dakina, na tattara duk wani abina me daraja na boye shi, domin nasan ba a abin mamaki ba ne gobe na gani a jikin Aunty Nana ko Haulatu, haka yasa na rufe dakin da kome nawa, sannan na saka key ɗin a jakata na fito na bar gidan, don shi kan Ya Hafiz tun dazu ya sake fita da wasu mutane.
*Dutsen tashi*
Daidai gidan Marigayi Malam Idris anan gidanmu yake, kafin ka isa gidan Malam Idris, anan aka sauke ni da basket guda uku, kafin na samu napep a unguwarmu sai da na fito bakin titin tambari housing estate, na sha zama don ma Maman Ummi da zata fita ta rage min hanya zuwa bakin hanyar unguwarmu, na tsaya kafin na samu abin hawa, haka muka iso gidan.
Yaran unguwarmu yan matasan suka taso da sauri suna faɗin. "Lubnah barka da zuwa!" Murmushi nayi suka dauki kayan ina amsa musu. "Yawwa Amir kai ia girma haka? Lallai girman dan mutum, Jamal ka ne haka ka zama kato!" "Kai Aunty Lubnah ba wani katon da na zama, ga Waheed naj baki ga girmanshi ba sai ni! " Suka fada murmushi nayi muka isa kofar gidanmu me dauke da shagunan provision. " Lubancy ke ce daga sama haka? " Murmushi nayi na ce. " Eh Malam Anas ni ce! " Na wuce Yaran suna bina da kayan har cikin gidan, yadda muryata ya karad'e cikin gidan sai da kowa ya fito har da Aunty Innah dama tazo ne? Wani murmushi suka min na karasa har da Aunty Munah. " Aunty Munah yaushe a gari?" " Korata kike kenan? Ke dai mugun halinki na kin mutane yana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 13