Share this page
2 / 9
nace maka zanci abinci yau to ina mai tabbatar maka da cewa, ko abakina ba zai wuce ba” Malam Sale yace, “Subhanallah Malam Jafaru, wannan wane gagarumin tashin hankali ne kuwa?” Malam Jafaru yace, “Malam Sale ina cikin wani mummunan tashin hankali da masifa, bansam dame zan kira abun ba a taƙaice, Wato malam yau na tashi da mura, haka nan na daure na tafi wurin nema da yammanan sai na ji jikin na neman gagarata, sai na tatatra na taho gida, ashe rabon in ji tuggun da ake shirin haɗa ma marainiyar Allah ne amanar da aka mutu aka bar mun” Nan ya kwashe duk abunda yaji su Hajja da baba suna shirin aikata wa Maryamah. A take shima yaji hankalin shi yayi masifar tashi. Faɗi yake Malam, “Wane zamani muke cikin dan Allah? Miyasa son zuciya yayi yawa a cikin al’ummah? Kai, innalillahi wa inna ilaihi raji’un., Allah kayi mana maganin musiba ta fili data ɓoye, Yanzu ita Hajja wai har yau bata cire qiyayyar baiwar Allah nan a ranta ba, wadda tundaga zamanta har mutuwarta ba zata ce ga abunda tayi mata ba” "Allah shi kyauta eh lallai kana cikin tashin hankali mai tsananin gaske, Kamayi kokari, wallahi Allah ya kawo mana mafita ta alkhairi” Malam yace, “Ameen.” Shiru sukayi su duka, kowwa na nazari. Zuwa can Malam Sale yace, “To yanzu wane mataki kake ganin zaka ɗauka?” Shiru Malam Jafaru yayi sai zuwa can ya dago yace, “Malam Sale, gaba daya kaina ya kulle, na rasa wane kalar tunani zanyi, Allah ya sani, ina son yarinyata tayi karatu mai zurfi, ban san daɗin boko ba, mahaifiyarta bata san daɗin shi ba, Amma tunda ta samu cikin nan ta kwallafa rai akan abunda ke cikinta, inshaa Allah zai yi karatu mai zurfi ko Allah zai taimake ta sanadin karatun shi ya shiga har inda zai sadata da danginta, to ashe ko fuskar abunda zata haifa ɗin Allah ma bazai bata ikon gani ba” ya ƙarasa maganar cike da karyewar zuciya yana share hawaye. Haka ne inji Malam Sale domin ya rasa, mema zaice wa aminin nashi. Chan dai ya nisa yace “To yanzu ya kake ganin za a yi? Ni da inada babban yaro wallahi, da na aura Maryamah shi, ko dan a samu a cire yarinyan nan daga wannan ƙangin rayuwaer da take ciki, To amma yarona babba ma ita kanta Maryamah ta girme shi” "Hakane" Malam Jafaru ya fadi yana duƙar da kanshi ƙasa. Shiru ne ya biyo baya, sai zuwa can Malam Sale ya ɗago ya kalli Malam Jafaru yace, “Malam, ga wata shawara, amma ban san ko zarayi maka ba???? FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t 🦋✨ RANTSATSTSEN RABO 🦋✨ BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA SADAUKARWA GARE HALIMA HASHEEM(MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD(HABIBI) ♥️ FULANI ❣️ 08082101373 ✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨ RAGE 4️⃣ Cike da zumuɗi, malam Jafaru ya ɗago yana faɗin “Ah haba malam ni da daman neman shawaran ne ya kawoni gareka, ai kawai ka faɗamin i insha Allah zan yi aiki da ita nasan bazata cutar da maryamah ba” Shiru malam Sale yayi na ƴan sakonni, zuwa can yace, “To malam Jafaru shawarar dai tawa ba wata bace illa ina Alhaji Muhammadu da muke har kar kasuwancin dabbobi dashi, wanda nake kaima dabbobin kiwo yake ajesu a gidan gonar shi dake can Habuje?" Kallon shi yana jiran amsar tambaya dayayi masa idan ya gane wanda yake magana akai. “Eh! na’am nagane shi dai Alhajin dake baka zakka duk shekara, koh?” shima ya mayar mishi da tambayar shi. "Yauwa shifa" Bai jira cewar shi ba ya ɗora mishi da bayani. “Toh me ɗakin shi ta biyu zuwan da nayi, take ce mani dan Allah in cigita mata yarinya da zata ringa kama masu aikin gida, kasancewar wadda take masu yan aikace-aikacen aure zatayi, su kuma basu cika son tarkacen yan aiki ba, shine tace dan Allah in nemo mata wadda na yaba da hankalinta, Allah ya sani inda ace Halilu mace ne wallahi zan bata saboda nasan ɗiyata bazata taɓa wulakanta ba, kuma nasan zata samu kulawa dai-dai gwargwado. Inda ace uwargidan ce tace in nemo mata, Allah da a take zance mata babu, kuma bani da hanya, To kasancewar amaryar ce, kuma na yaba da haƙurin matar da yakanar ta, nace mata toh, gaskiya daman ɗiyar wajen ƙanwata nayi niyyar kai mata, dan har na yi magana da ita Hajaran nace mata zata bani gaje in kaita wurin aiki, kuma da ita da megidanta sun amince" “Amma in kana ganin cewa zaka iya bada Maryamah, sai ince ma ita gajen ta zauna gaba. In an samu wata damar sai a kaita" Shiru malam Jafaru yayi cikin tsannin baƙin ciki Allah ya sani, yana tsananin son ɗiyarsa domin itace sanyin idaniyar shi, kuma yasan malam sale bazai taɓa cutar dashi ko abinda ya haifa ba, yana ganin kamar gara ya bada ta, ta bar garin taje can inda su Hajjah da Zainu bazasu ganta ba, balle suyi tunanin cutar mishi da ita. Shiru ne ya biyo baya kowa na nazari a cikin ranshi, zuwa can malam Sale yace, “Amma in kana ganin bazaka iya ba, sai a kai masu gajen ita kuma Maryamah, sai mu nemo wata mafitar Amma dai a wannan gaɓar da muke ciki, tafiyar ta ina ganin kamar zaifi zama alheri, Kuma can inda zata, ina mai tabbatar maka da cewa wani me mugun nufi zaiyi wahalar samun daman yin kutse cikin wannan gidan saboda tsaro, domin sojoji ne ke tsaron unguwar gaba ɗaya, dama gidan kasancewar baban yaron gidan babban soja ne me babban muƙami, inshaa Allahu zata kasance cikin tsaro a can" Nannauyar ajiyar zuciya, malam Jafaru ya sauke tare da fadin "Bakomai malam Sale na amince, gara ta tafi can din, hankalina zaifi kwanciya akan kasancewar ta a nan, koda yanzun ta tsallake wannan gaɓar, bansan kuma me zasu ce zasuyi mata ba nan gaba" ★★★★ A can ɓangare gidan su Maryamah haka tayi sallan isha, bayan ta idar ta taci abinci, ta fita ta qara jan ruwa a rijiya ta shiga wanka kasancewar ta da son wanka kamar ƙwaɗo, bayan tayi wanka ta shirya cikin wata koɗaɗɗiyar rigar bacci, ta dan shafa turare, taja littafinta, ta kunna torchlight tana bitar karatunta kasancewar gaf suke da fara JSCE exams dinsu, wanda taciwa buri sosai, so take taci daga nan ta jona SS tana fatan ta samu damar yin karatu mai zurfi, tuna hakan a cikin ranta ne yasa ta lumshe dara-daran idonta wanda suke da yalwar gargasa. Tana nan kwance tana karatu, taji shigowan Hassu lokacin tara saura na dare, a ranta take ayyana yau da ɗan arziƙi an dawo da wuri, haka ta ringa jiyo kwarafniyar su da ita da uwar a tsakar gida, suna ƙirga kudin cinikin da sukayi da kuma wanda ta samu ƙari uwar nata shi, mata albarka cike da alfaharin kuɗin da ɗiyar tata take kawo mata bayan na tallar. Aranta tace, “Allah dai ya kyauta.” Shiru tayi tana tunanin, yau baba ko lafiya be dawo ba, kodai muran ce? Gashi ita ko yar rakani kashin nan bata da ita, balle ta kirashi taji lafiya. ★★★ Shi kam malam Jafaru yana can suna tattaunawa da malam Sale akan yadda tafiyan zai kasance da yaushe ya kamata suyi tafiyan ma. Malam Sale ke ce mishi gaskiya, shi da abunda ya tsara sai nan da sati biyu yake so yayi tafiyan, amma tunda haka ta taso, bari ya kira Hajiyan yaji ya za ayi. Nan malam Jafaru yace, “Eh, kirata dan Allah, dan ni wallahi kwana biyu ma in Maryamah ta kara a garin nan inajin jinina sai yayi hawanda da wahala ya sauka.” Malam Sale yace “Subhanallah, kadaina faɗin haka abokina, inshaa Allah ba abinda zai sameta sai alkhairi" “Allah ya tabbatar mana dashi.” ya amsa yana kallon shi ganin har ya danna kiran wayar. Cikin ikon Allah, malam ya samu Hajiyan a waya, Bayan sun gaisa, yake ce mata daman maganar yarinyar an sameta, amma nida nace sai nan da sati biyu zan taho" A take hajiyan tace, "Aa malam Sale nidai in dai yarinyan na da iyayenta sun shirya, ko gobe ko jibi ku taho zan ɗauki nauyin komi in Allah ya yarda" “To shikenan Hajiya Zamu taho ko zuwa jibi ne, domin yarinyan marainiya ce, mahaifiyarta ta rasu, toh tana ɗan fuskanta wasu ƙalubale ne, yasa baban duk son da yake mata ya haƙura, yace gara ta bar garin duk da kuwa yarinyan nakan zuwa makaranta, dan gaff suke ma da zana jarabawar fita daga karamar sakandire” Hajiya tace “Ashsha abu beyi daɗi ba Allah ya kyauta, inshaa Allah karatunta bazai gagara ba In kun shirya ɗin sai ku taho jibi yanzun, zan tura maka kudi, sai kuyi amfani da shi, Itama sai abata in tana bukatan wani abu ko shi mahaifin nata” “To Hajiya, amma su dukan su ba dan wani abu suke son aikin ba, sai dan neman mafita inaga kuɗin abun hawan ma ya isa” “Aa, duk da haka dai a basun ai haƙƙin su ne.” “Toh mun gode Allah ya ƙara girma” Amsa mishi tayi da “Ameen nima nagode, sai da safe” Bayan sun gama wayar ne, ya kalli malam Jafaru yace "Kadaiji yanda mukayi da ita" kasancewan a speaker ya sanya shi. “Eh, naji komai, nagode sosai da ƙoƙarinka, Allah ya saka da mafificin alkhairi, Allah ya jikan iyayemu, ya raya mana zuri'a, ya kuma cigaba da basu kariya akan komai" "Amin amin yanzun sai ka zauna, muci abinci, tunda alhamdulillah mafita ta samu, koh?" Ya faɗa yana murmushinsu na manya. Shima malam Jafaru murmushi yayi yace "Ka bari kawai malam sale, bazan iya misalta maka tashin hankalin dana shiga ba wallahi" "Akwai tashin hankali kam babba ma, Allah dai ya kyauta, su kuma Allah ya ganar dasu” "Ameen dai" A nan sukaci abincin suna dan taɓa hiran abun da ya shafi rayuwa da yanda son zuciya ke sanya mutane aikata ɓarna da yanda ƙasar ta lalace, bayan sun gama, malam ya karayi ma malam Jafaru godiya sannan ya tafi gida cike da tunani kala kala, duk da baya son rabuwa da ɗiyar shi, amma yana ganin kamar tafiyan ta sai yafi zamanta alkhairi, dan haka bashi da wani zaɓi. Da wannan tunanin ya isa gidan, Lokacin tara ta wuce sosai dan su kansu su Baba Zainu sun shiga ɗaki, ita da Hassu da su Zainab, kasan cewa a dakinta su suke zaune, saɓanin Maryamah da take ita kaɗai a ɗan karamin ɗakin da be kai nasu baban girma ba. Da sallama ya shiga gidan, wanda Maryamah tayi zaraf ta fito tana amsa sallaman baban nata. Sai lokacin hankalinta ya kwanta, Ta kalli baban nata cike da kauna ma tariya yawa tace "Baba, hankalina ya tashi najika shiru" Ta faɗa cike da yar shagwaɓa har da hawaye. Dan ita dai indai tana gaban babanta zakaga taɓara kala kala. Shima cikin tsanin ƙauna ya kalle ta yana murmushin karfin hali ya bata amsa "Yar shagwaɓan babanta, bakiyi bacci ba kenan? me kika tsaya jira?" Ƙasa tayi da kanta tana ɗan tura baki irin na shagwaɓaɓɓun yaran nan da suka samu kulawar mahaifinsu irin wadda bata keta shari'a ba. "Babana! baban Maryamah! Ina Maryamah taga bacci, bataga abincin ruhunta ba" kasancewan sunada kyakkyawan mu'amala ita da mahaifin nata, tunda ta tashi shi take gani taji sanyi a ranta, Shine uwar ta, shine ubanta, shine yaya kuma abokin hiranta, dan in tana hira da babanta, bazaka ce itace wadda magana ke wa wahala ba. Tana tuna memories nata da babanta sanda tana yarinya, ko irin lokacin zafi ne in babanta yayi shimfida a ƙofar gida karkashin bishiyan darbejiyan da suke dashi, tofa ita kuma zaka sameta kwance a akan cikin shi, kaff abokan babanta ba wanda besan ƙaunar dake tsakanin wannan uba da yar ba, wasu ma daga cikin su Maryamah babanta suke ce mata har yanzun daga cikinsu ma akwai malam Sale aminin babanta. Kama hannunta yayi ya shiga da ita dakin Hajjah yana bata amsar maganar ta cike da jin daɗi, "toh ai ga baban Maryamah nan ya dawo cikin ƙoshin lafiya, ya samu ƴar amanar shi itama tana lafiya" Ya ƙarasa yana sakin kyakkyawan murmushi akan dattijuwar fuskar shi, a duniya bashi da wani abun dake saka shi farin ciki bayan ganin yar marainiyar shi cikin walwala. Da shigansu, suka iske ta tana jan numfashi kamar rago. Kai kawai ya girgiza maganganun su na dazun suna dawo mishi a rai, yace, “Ashe tamayi bacci, to mu tafi sai da safe.” Suka fito yana mai ja mata ƙofan ɗakin. Daki ya shiga, ita kuma ta nufi kitchen zata kawo mishi abincin shi. Yace, "Zo, bar abincin nan a koshe nake, daga gidan Baban Sale nake can naci abinci" “To” Tana me bin bayan shi zuwa cikin ɗakin. Bayan sun zauna, ya kalle ta yana me kiran sunanta. Ɗago kanta tayi takai dubanta kan fuskar mahaifin nata kasancewan nepa sun kawo wuta da karfe 9, sai a lokacin taga damuwa kwance saman fuskar shi, dan ita in ma ba gizo idonta yake mata ba, sai taga kamar ya faɗa. A ɗan rikice tace, "Babana meyasa meka murance dai? To kona dafa maka ruwan zafi me kayan yaji?" Bata jira cewar shi ba ta miƙe. Hannunta ya kamo, yana mai girgiza mata kai "Dawo ki zauna magana zamuyi...... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t ✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨ BY RABIA'TU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM(MIEMIEN HABIBI)🤍 & AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️ FULANI ❣️ 08082101373 🦋✨ RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨ PAGE 5️⃣ Haka kawai taji gabanta ya faɗi zama tayi cikin sanyin jiki. Cikin sanyin murya tace "babana ina jinka" Shiru yayi yana tunanin ta ina zai fara mata bayanin da za ta fahimce shi, duk da ya san bai gaza a kanta ba wajen tarbiyyar da ya yi mata, amma ya san abin ba mai sauƙi ba ne rana tsaka ya zo mata da maganar tafiya aiki. Shirun data ji ya yi yawa ne yasa tace "Babana!" Tana ɗora hannun ta akan nashi. A jiyar zuciya ya sauke yana dawo daga dogon tunanin daya tafi, kallon ta yayi cike da tausayi ya fara mata magana cikin sigar rarrashi da fatan kuma tayiwa maganar shi kyakykyawar fahimta. "Ɗiyar baba kin san babanki mai sonki ne ko? Kuma kin san a duk duniyar nan duk wanda zai so ya ga farin cikinki da walwalarki bayan nine?" Cikin zaƙuwa da son jin abin da zai ce, ta ɗaga kai tana bashi amsa a ɗaɗare "Na sani babana, meyafaru?" Ɗauke kallon shi yayi daga kanta "Kiyi haƙuri Maryamah, ba ni da yadda zanyi ne shiyasa, wannan ce kawai mafita a halin da muke ciki" Cikin tashin hankali tace "Baba wane hali muke ciki? kuma menene ya faru?" Take idonta ya fara tara hawaye domin jin yanda gabanta ya tsananta faɗuwa, burinta kawai ta ji wane hali mahaifinta ke ciki. "Ki kwantar da hankalinki, ba wani abu ba ne gagarumi, kawai ina neman wata alfarma ne a wajen ki Idan da hali" ya faɗa yana yin ƙasa da kansa. Zuwa lokacin sosai hankalin ta ya tashi cikin ƙarfin hali tace "Baba ka fi ƙarfin komai a wajena domin kai ne duniyata, kai kaɗai gare ni, kai nake gani nake samun natsuwa a raina wallahi babana raina fansa ne a gare ka" Murmushi ya yi yace, "Allah ya yi miki albarka, ya kula min dake a duk inda kika tsinci kanki" “Ameen baba” "So nake ki shirya ki haɗa kayanki da duk abin da kika san zai miki amfani, da takardun makaranta gaba ɗaya ki haɗa su waje ɗaya,Idan Allah ya kaimu jibi da rai da lafiya, zaki bi babanki Sale zuwa garin Abuja, zaki koma can da zama kina kama wa matar ubangidansa aiki" Wata iriyar mummunar faɗuwar gaba da tsoro da firgici ne suka dirar mata lokaci ɗaya, kanta ta ɗago ta ɗora dararan idanuwanta kan mahaifinta a rikice tace "Amma baba" kuka ne ya sarƙeta dole ta haɗiye maganar ta, sosai hawaye yake zuba a fuskar ta tamkar an buɗe famfo. Hannunta ya kama ya riƙe yace "Maryamah yadda kika ji haka nake nufi, ki sani ba mu da wata mafita, wannan ce kawai mafitar mu, Idan na barki kika ƙara sati a garin nan, ban san girman abin da su Hajja za su aikata miki ba, Kuma idan na ɗauki mataki a kan Zainu, Hajja fa ba zan iya ɗaukar mataki a kanta ba, saboda uwata c mahaifiyata ce, ba ni da yadda zan yi da ita, Kuma duk ba ma wannan ba, idan har wani abu ya same ki Maryamah, zuciyata ba za ta taɓa ɗauka ba, ni na san mutuwa zan yi" Ya ƙara sa maganar hawaye shima suna wanke fuskarsa. Ba ta san sanda kuka ya kuɓuce mata ba, hannu ta saka ta toshe bakin ta dan hana kukan nata fitowa har ta janyo hankalin mutanen gidan duk da sunyi bacci, sosai take kuka har tana shiɗewa baban na dan bubbuga mata kafaɗa, sai da ta ɗan rage kukan ne. Yace "kiyi haƙuri bada son raina zaki tafi ba, amma abinda naji yau ya sanya ko kwana biyun da za ki yi a garin nan, wallahi a ɗarɗar zan yi, ba zan taɓa samun natsuwa da kwanciyar hankali ba sai na ga kin bar garin nan, Insha Allah mugun nufin Zainu sai dai ya koma kanta" Ya ƙara da cewa "Da'ace na san inda dangin mahaifiyarki suke, tabbas wannan karan da sai na sadaki da su, komai za su yi min zan ɗauka akan zaman ki a nan" Cikin shaƙaƙƙiyar muryar ta data sha kuka tace "Ba komai baba duk hukuncin da zaka yanke a kaina daidai ne, ka isa kayi, ka daina roƙona kai uba ne, ba za ka taɓa cutar da ɗiyar kaba, Na amince Allah yasa haka ya zama mafi alkhairi" "Ameen"yace yana mai sanya mata albarka. Kanta dake ƙasa ta ɗago tace "Baba to shikenan sai na haƙura da karatu, da shine burina?" Hawaye na ƙara cika idonta. Murmushi yayi ya kalleta duk da bai kai zuci ba yace, "Yanzu zuciyar babanki haka za ki je gidan mutane kina masu shagwaɓa? Kin girma fa" Ya ƙarasa da murmushi mai faɗi. Ita ma murmushi ta yi tace, "Har abada ni yarinya ce a gaban farin cikina, ba zan taɓa girma ba idan ina tare da kai" "A’a yanzu ma kin girma sannan maganar karatu, Insha Allah za ki yi har sai kin ce ya ishe ki" Cikin sauri ta kalle shi "Da gaske babana" Kanshi ya jinjina mata fuskarsa na yalwace da murmushi "Insha Allah" "Allah ya cika mana burikanmu na alkhairi, ya yi mana zaɓin alkhairi baban maryamah" “Ameen zinariyata, rayuwarki za ta cika da tarin albarka da ikon Allah, ki tashi kije ki kwanta dare yayi, kuma kada ki bari wani ya fuskanci cewa kina shirin balaguro, Insha Allah yadda suka so bamu mamaki, sai dai mumu basu da yardar Allah" "Allah ya yarda babana, sai da safe" Dariya ya yi yana girgiza kai, domin a duniya bai taɓa ganin abin da ya kasance abincin ruhinsa a jinsin ɗan Adam ba sama da wannan yarinyar. ★★★★ Ɗaki ta shiga zuciyarta fal da tunani, wai me baba yaji da ya rikice haka harya haƙura da ita yaga gara ta tafi wani wuri ta barshi, wurin da ita kanta ta san inda lafiya lafiya ne, to konan dacan ba zai bari ta je ba, tabbas biri yayi kama da mutum, sassaucin da ta gani a wajen mutanen gidan ba a banza ba, kwanciya tayi akan shimfidarta tana faɗin Allah Ya fisu, Addu’ar bacci ta yi ta kwanta da hannun dama, amma bacci ya gagari idonta, duk yanda taso bacci ya ɗauke ta abin ya gagara, juyi take tana tunanin can ɗin kuma wace irin rayuwa za ta je tayi Allah masani. Ba ta san sanda bacci ya ɗauke ta ba, kiran sallar asuba na farko ya tashe ta, ta tashi ta ɗauro alwala, ta zo ta yi nafila tana zaune tana lazimi har aka yi kira na biyu, ta tashi ta yi raka’atan fajr, daga nan ta yi sallar asuba, ta yi azkhar, ba ta ma tsaya karatun Alƙur’ani ba, Ta fita ta hau share tsakar gida, tana cikin sharan ne baba ya shigo gidan da casbaha a hannu. Dukawa ta yi ta gaisheshi, duk da ba wani sakewa a tare da ita, ya amsa yana ƙara bata haƙuri a hankali don kada mutanen gidan su ji. Tace, "Baba ka daina dan Allah" tana dan turo baki. Ya yi murmushi yace, "Na bari zinariya" Ita ma murmushi ta yi ta ci gaba da sharan, shi kuma ya kama hanyar ɗakin Hajja domin ya san har yanzu ba ta tashi ba, aikuwa yana zuwa ya sameta tana jan minshari, kanshi ya girgiza ya ƙarasa gareta yana ɗan taɓa ta tare da kiran sunan ta, "Hajja" Da ƙyar ta buɗe idonta tace, "Lafiya za a zo a hanani bacci?" kauda kai yayi yana jin rashin daɗin ɗabi’ar mahaifiyar tashi yace, "Hajja gari fa ya yi haske" “"o sai akayi me? mezan wa wani?" "Hajja sallah mana" cike da ƙosawa tace "To naji tashi ka bani wuri ai zanyi" Haka ya mike jikinshi ba ƙwari ya nufi ƙofa, bayan ya fito ya tsaya yana tambayar Maryamah ko za ta je makaranta yau. Tace ba ta tunanin zuwa. Yace, "A’a ya kamata ki je daga nan kiyi musu sallama" Kanta ta gyaɗa mishi. Yace ta shirya ta zo ta amsa kuɗin abin hawa. Ci gaba tayi da aikinta, bayan ta gama sharan gida ta haɗa wuta ta ɗora ruwan koko, rijiya ta nufa ta ja ruwa ta wanke kewaye, sanda ta gama ruwan kokon ya tafasa ta dama, ta maida na wankanta. 7:20 ta fito cikin shirin tafiya makaranta, a lokacin baba Zainu ta fito za ta yi alwala. Kallonta kawai ta yi ta ɗauke kai, yau yan miskilanci ne a kai, ba ta tunanin ko gaisuwa za ta samu. Ta nufi ɗakin mahaifinta da sallama ta shiga tace, "Baba na shirya" 300 ya ɗakko ya bata yace tayi abin hawa da kudin breakfast, godiya tayi mishi ta fita, bayan ta fito ta ga Zainab zaune a bakin ƙofa, alamar tashinta ke nan. Ta kalleta tace, Sai yanzu kika tashi?" Ba ta amsa ba saboda tsoron addarsu. Kawar da kai ta yi tana taɓa baki tace, "Ku hanzarta ku shirya ku wuce makaranta" Tace, "Toh" Daga nan itama ta fice daga gidan. A hanya suka haɗu da Aisha, kasancewar makaranta ɗaya suke. Gaisawa suka yi, daga nan Maryamah ba ta ƙara tankata ba, ganin haka yasa Aisha ta san kila tana cikin bacin rai, domin duk miskilancin Maryamah da ake faɗa ita ba ta mata, Bayan isarsu makaranta suka ci gaba da ɗaukar darasi, A lokacin break ne Aisha ta kasa haƙuri tace "Nikam Maryamah yau lafiyarki kuwa?" Kaman me jiran jin hakan take hawaye ya tsinke mata..... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t ✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨ BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA SADAUKARWA GAREKI HALIMA HASHEEM 🙌🏻 TARE DA KAI HABIBI NA AHMAD JAMIL AHMAD ♥️ FULANI ❣️ 08082101373 ✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋 PAGE 6️⃣ Cikin kuka tace mata "Aisha wai aikatau babana ya amince naje wani gari" Dafe ƙirji Aisha ta yi idanuwan ta

Chapter 2 of 9