maidani kenan? sai an jima" ta faɗi tana kashe wayan, dan ji tayi yanzun har Aishan ma da shi yayan nasu da bata sani ba da wadda zai aura ɗin duka haushi suke bata.
La'asar taji an kira ta tashi tayi alwalah ta kabbara sallah, ta kusan idar wa Iya itama ta shigo ta ɗauro alwalah, bayan ta idar ta tsaya tana kallon Iya a ranta, tace tsohuwar na nada son addini"
Bayan baban ta idar ne Maryamah ta gaidata, ita kuma ta amsa tana tambayar"har kun gama aikin?"
"Eh wallahi mun gama aikin yayi mana sauri, kuma parts ɗin ma duka biyun basu da datti sossai"
"Ai da yake na Alhaji be daɗe bayanan ba, shima na Alhaji ƙarami baza a samu datti ba, gaskiya saboda hajiya na bakin ƙoƙarin ta gurin ganin an shiga an gyara duk bayan kwanaki, bari nakoma kitchen ayyukan da yawa, gashi gobe inajin ƙilan gidan ya cika bayan su Alhaji sun dawo, kinsan ahalinsu basu da yawa sosai amma sunada ƙoƙarin zumunci gaskiya dan yan uwa ne masu matuƙar ƙaunar juna"
"Allah sarki toh Iya idan akwai abinda zan kama maki dashi na biyo ki mana?"
"A'a ƴar nan ai kinsha aiki ki huta kawai"
"Ina so inga yanda ake abubuwan yan gayu, ina so na koya nima"
"To shikenan tashi muje a hankali zaki iya ai tunda kina so"
Kitchen suka nufa, lokacin su Sahura, sunata faman suyan kaji, dan sun gama snacks ɗin sai kajin da dambun nama, Hajiya tace ayi ma Alhaji da son dinta, daman sune sarakan cin shi, dan duk gidan sunfi amfani da shi, da suka shiga bata biye ma halin su sahura ba tayi musu sannun da aiki.
tsaki sukaja dan har ga Allah sun tsani su buɗe ido su ganta a cikin gidan, dan gani suke nan gaba kaɗan sai ta fisu fada a gidan, dan sun tsani yanda yaran gidan suka sake da ita, sai kace ita ta rigasu zuwa, bayan sun rigata
Kallon su Iya cike da ɓacin rai "Wai ku lafiyan ku kuwa? Yarinyar nan tunda tazo gidan nan take binku, amma kullum da kalan wulaƙancin da kuke mata, Waɗanda take zaman su ma basu takurata ba, sai ku da kuke cin arziqi tare da ita, ya kamata ku gyara, idan kuma ba haka ba zan samu hajiya na sanar da ita, in yaso ita sai tasan matakin da ya kamata ta ɗauka tunda mu duka zamanta mukeyi"
Haka Iya tayi masu tass sai bayan ta gama musu faɗan ta tambaye su meyayi saura a aikin.
"Dambun naman su Alhaji ne da babban yaya, daga nan sai abincin dare, shi kuma hajiya tace ba sai anyi ba, a barshi tunda yau aiki yayi yawa"
Kallon Maryamah, Iya tayi tace "Kin iya danbum nama?"
"Eh na iya"
"Bismillah inaga kiyi shi ga naman nan, akwai na rago da zakiyi ma Alhaji ƙarami dashi, sai kuma akwai na kaza wanda Alhaji za'ayi wa shi"
Amsawa tayi da toh ta nemi turmi ta tambaya dakawa za'ayi.
Ayi na dakan yafi daɗi iya tabata amsa.
Zama tayi ta ware tsokar duk ta cireta daga jikin ƙashin kasancewan an dafa shi ya dahu luguf, dakan ma bata sha wahala ba, dan daman ya dagargaje, Kayan miya ta jajjaga tarugu da tattasai, sai ta yanka albasa wadatacciya, ta daka kayan ƙamshi su citta da su kanun fari, haka ta ware sauran spices ɗin suma da duk abinda zata buƙata.
Iya ta kalla tace "iya wane kalan suya za'ayi, na cikin mai ko wanda ake sanya mai kaɗan?”
"Wanne kike ganin zaifi a ciki?"
"Duk sunada kyau, amma na cikin mai yana ɗan jimawa ana amfani dashi, be lalace ba, matsalansa idan akayi in ba a tsane man jiki sosai ba saurin tayar da ulcer yakeyi"
"Inaga ayi suyan cikin man dan bama mu taɓa gwada shi ba, in yaso sai a tsane man sosai.”
Aikin ta fara cike da kuzari da ƙwarewa, kafin kace me gaba ɗaya kitchen ɗin ya baɗe da ƙamshi saboda spices da dambun naman yaji.
Sosai Iya ta dinga yabawa cike da tsokana tace "Kike cewa kina so ki koyi abincin ƴan gayu, bayan gashi nan ƙamshin abinda kikeyi yama disashe namu ƙamshi"
Murmushi tayi "Iya ai ina kan koya ne ban wani iyaba sosai"
Suna cikin magana ne, Zuhura ta shigo tana magana "iya yau me muka samu haka ne, duk ya baɗe mana hanci da ƙamshi? Turusss tayi ganin Maryamah gaban gas tanata aikin dambun nama, Kada dai cutie ce ke mana wannan horon, ba Iya ba"
Dariya Iya tayi aikam dai Maryamah ce.
Cikin sauri ta ƙarasa inda Maryamah ke tsame dambun daga cikin mai, "Like seriously, cutie kece kikayi wannan aikin? Jira ma dai waike, komai kin iya tayi mata tambayar with full of suprise.
Murmushi tayi "A'a fah, yanzun nan na koya wajen Iya"
Iya tace "Kidai faɗi gaskiya"
Plate Zuhura ta ɗauka zata zuba dambun naman dan miyanta duk ya gama tsinkewa.
Maryamah ce ta katse mata hanzari "ai sai an tsaneshi idan ba haka ba maiko bazai bari kiji daɗin ci ba"
"Eh kuma fah haka ne, buh lemme test small" Ta ɗiba tana kaiwa baki.
Lumshe ido tayi tana bada sound din hmmn, tana girgiza kai irin na wanda daɗi ya kaimawa "Hmmn what a yummy and delicious dambun nama" fito da harshen ta tayi tana lashe gefen lips nata inda ya ɗan zuba.
Murmushi Iya tayi "Babyn mamy kodai a sanya miki waigi ne?"
"Allah Iya ban taɓacin dambun nama mai daɗin wannan ba, upon all the danbum nama I ever ate in mah entire life"
Rarraba ido iya ta fara can tace "kedai kika san me kikace, ni kinsan ba gane wannan Yaren nake ba, amma ni kaina tun kafin naci ganin yanda take haɗashi nasan zaiyi dadi kam"
"Aikam ya masifar yi wallahi iya kici kiji"
Ita dai Maryamah tana gefe tana jinsu, kuma ko banza taji daɗin yanda suka yabi ƙoƙarin ta, tissue ta ɗauka irin na cikin kwallin nan, ta zuba ma Zuhura akai. Bayan ta ɗora shi a kan plate tace "gashi tissue ɗin ma zai ƙara taimakawa wurin rage maiƙon jiki"
Godiya Zuhura ta mata ta fita tana ci.
Zuhura na zuwa parlour dashi aunty Amnah tace "Wow, wannan danbum yayi kyau sosai a ido, make am test am"
Zuhura na dariya tace "Saima kinci zaki tabbatar wallahi cutie ce tayi shi"
Su Fadil da suke wasa da babyn aunty Amnah, jin ance cutie tayi, sukace zasuci suma.
Nan fa Zuhura tace, bazasu cinye mata ba, suje kitchen ɗin su anso mana.
Aunty Amnah ma da taci taji How sweet it is, sai cewa tayi itama bari taje ta zubo.
Mamy dake gefe tace "kunsan fah na daddy kune da yayanku"
Haɗa baki suka yi wajen cewa mamy please"
Allah ya bada sa'a daga haka ta tsuke bakin ta.
Kitchen aunty Amnah ta wuce "Cutie wato abun yar wariyar launin fata ne koh? Shine kika ware Zuhura, kika bata, kika hanamu?"
Bakinta ta rufe da hannu "Laaa aunty Allah a'a, itama yanzun ta shigo ta gani, shine tace tana so fah ta ɗiba"
"Ai kin kyauta"
"Afuwan aunty, bari a sanya miki naki"
Sai gasu Fadil da gudu suna "Cutie zamuci please"
Sahura da dije kam sakin baki sukai suna kallon ikon Allah, wato haka yarinyar nan ta samu shiga dai a gurin yan gidan har wani suna suke kiranta da shi.
Sahura tace "Hmmn, dole mu zauna dan bazai yiwu ba wallahi"
Ko ta kansu aunty bata biba Iya kawai tayi ma sannu da aiki saboda ita dai samm yaran basu mata ba.
Plates ta nema, duk ta zuba masu, ta hada masu da fork.
Thanks suka ce mata suna fita daga kitchen ɗin.
Sahura data kasa haƙuri tace "yau muna ganin iyayi ke baiwar Allah daga zuwa sai ki zaƙe kibi ki shige ma yan gida, to wallahi masu kuɗi dai ba'ayi mausu shishshigi aikin banza kawai"
Share su tayi bata ce masu komai ba, dan tanaji da miskilanci, kuma ita har yanzun bata ga dalilin da zai sanya ta biye masu ba.
Mamy ce ta shigo "Cutie shine kika bama kowa, ko ki tuna dani koh? To nagode"
Cikin sauri tace "Kiyi haƙuri mamy, banyi tunanin kina parlour bane ai"tun bata karasa mata bayani ba ta ɗau plate tana zuba mata.
"Aida ni har nayi zuciya nace bazanci ba"
"Kiyi haƙuri mamy kici" tayi maganar tana miƙa mata plate ɗin haɗi da marairaice fuska.
Karɓa tayi "shikenan nagode, sannun ku da ƙoƙari, kunata shan aiki"
Kan Iya ta maida kallon ta "gobe inaga ba sai anyi breakfast ba, kawai ki barsu kowa yasha tea, sai ku fara aikin girkin da wuri, dan jirgin 12 su Alhaji zasu sauka. So nasan sai yayi azahar zai shigo cikin gida, kafin lokacin nakeso a gama komai dan Allah"
"Sai fruit juice da nake so a haɗa wa "Son kinsan baya san company made yafi son natural juice, ban sani ba shi ko yau zaku haɗa shi ko sai goben, Inajin shiɗin ma saidai ke kiyi, iya kinsan son, ba kowa ke abu yanaci ba, Idan kuma daughter ta iya sai ki bata tayi" ta ƙarasa tana maida kallonta kan Maryamah.
Ba iya su dijee ba, har ita kanta Maryamah jin sunan tayi wani iri da Hajiyan ta kirata da shi.
Itakam hajiya shauƙin ka6unar ɗiyar da takeji ne yake sanya, take manta matsayinta a gidan, Allah ya sani tana son yarinyar, kuma tanada plan sosai a kanta, fatanta Allah yasa komai ya tafi mata yanda ya dace, ba tare da samun tangarɗa ba.
Ƙasa Maryamah tayi da kanta, ganin har lokacin hajiyan bata ɗauke idonta akanta ba, "Insha Allah zan gwada, nasan bazai gagara ba"
"Yauwa da kyau ɗiyata Allah yayi muku albarka"
Ƙasa ƙasa ta amsa da Amin.
Kan iya ta maida kallon ta "goben sai ki bata duk abinda ya dace ɗin"
Insha Allah iya ta amsa mata.
Allah ya taimaka daga haka ta fita daga kitchen ɗin ɗauke da plate ɗin danbum namanta.
Bayan fitar ta, su sahura suka ƙara shaƙa har suna haɗa baki, gurin cewa Hmm, uhmm, yau muke ganin abu a gidan nan.
Dije tace "anya kuwa ba sanya hannu a lamarin nan?"
"Kemadai kyace amma dai ai ba girin irin ba tayi mai" cewar sahura tana zuba mata harara.
Iya tace "Allah ya shirye ku ya rabaku da hassada, domin ita hassada taki ce, kunayi mata zakuga tana ƙara haɓaka kowa da kuke gani, arziƙin shi yake ci bame cin arziƙin wani"
"Kodai dai da rana ɗaya kada ki biye musu, kinji?" Tayi maganar idonta kan maryamah.
Inshaa Allah, Iya, nagode....
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/JHxZP3j1IIr6O5UZj4Csq5?mode=gi_t
https://chat.whatsapp.com/JHxZP3j1IIr6O5UZj4Csq5?mode=gi_t
✨🦋 RANTSATTSEN RABO ✨ 🦋
BY RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️
FULANI ❣️
08082101373
✨🦋 RANTSATTSEN RABO 🦋 ✨
PAGE2️⃣0️⃣
Washegari ma da aiki tashi, Ita dai Maryamah shara tayi da goge-goge, sai wuraren 11 ta shiga kitchen gurin su Iya, tana shiga Iya tace ta ɗauki cup ta haɗa tea taje ta tasha, idan ta karya sai ta zo ta haɗa ma Alhaji ƙarami lemon da hajiya tace ta hada mishi.
"Iya ki kawo kawai nayi yanzu ai bana jin yunwa"
"A'a kije kici abinci kiyi wanka sai kizo ki haɗa dan Alhaji ƙarami idan ya sameki a haka, akace mishi ke kika haɗa abinda zai ci tabbas bazaici ba, yanada tsantseni duk tsaftar mutum ba kowacce ke gamsar dashi ba"
Toh kawai tace ta juya tana jinjina iyayin bawan Allah nan, ita kam zata so ta ganshi, haka nan kuma sai takejin tsoron haɗuwar su har tana insha Allah ma ni bazamu taɓa haɗuwa ba, kada yayi min masifa, ta faɗi tana ɗan tura baki.
Tana shiga da wanka ta fara dan daman jikin ya isheta, bayan ta fito ta shirya cikin wata doguwar rigan atampha, taje kanta tayi wanda duk ya dameta, tana son a ɗan ɗaure mata shi, amma bata san ya zatayi ba, amman tabari idan Iya ta shigo zata tambayeta inda ake musu kitso, ƙaramin hijab ta ɗauka wanda ya kai mata guiwa ta sanya tafita, ta samu Iya a kitchen.
Iya tace, "Har kinyi wanka?" "Eh yanzun tea kawai zan sha sai inzo in haɗa abinda hajiya tace a haɗa yau"
"To shikenan ki gama saina nuna miki abubuwan da zaki buƙata"
Tea ɗin ta haɗa ta zauna a kitchen ɗin tana sha a hankali, cike da nutsuwa.
Su Dije suna gefe suna gulmar wai ta cika iyayi har sahura, na cewa "wannan da ace ubanta yafi haka kudi, daza aga wulakanci da taƙama, Ita komai nata cikin isa da izza takeyi, amma na banza tunda basu da kosisi, karshe ma an ƙare a aikatau"
Dije ta care dacewa "yanzun haka ubanta fah mugun matsiyaci ne, amma tazo tana mana feleƙe"
Miƙewa tayi ta ƙarasa gaban su, dan tanaji tabbas yau anzo gaɓar da zata tanka masu, tunda suka sanya mahaifinta a cikin shirmen su.
Koda ta ƙarasa gaban su, diriricewa sukayi domin wani kwarjini na musamman sukaga yarinyar ta masu.
Kallan su tayi tsaff a tsanake, sannan dakyar ta buɗe bakinta kamar bata son yin magana "a da nasa a raina komai zakuce baku kai matsayin da zan tanka muku ba, amma a yau kuma ayanzun sainaga cewar kun isa gaɓar da dole nayi maku magana wadda koda ita kadai nabarku ta isheku, abinda nake so ku sani shine, Maryamah da mahaifinta ba matsiyata bane, Infact bama mu haɗa hanya da tsiya ba, domin rufin asirin Allah dai dai gwargwado munada shi, tunda a tsawon rayuwata ba ataba ɗora tukunya ƙasa da sau 3 ba a gidanmu, kunga kam in babu ne ta rashin ci zaisa na fito nema to tabbas bana tare dashi, In kuma na fito hakika na tabbata mara godiyar Allah"
"Sai abu na biyu kuma, sutura itama ba sai na faɗa muku ba, tunda koda nazo gidan nan ba a cikin wulaƙantacciyar shiga kuka ganni ba, wanda har inda yanzun take kayan da mahaifina yayi man ne a jikina, bana uban wani ba, kuma ina so ku sani duk talaucin mahaifina, yanada wadatar zucin da abun wani da abun duniya duka basu tsone mishi ido ba, hakan yasa ya tashi, bame kwaɗayin abun duniya ba"
Shiru tayi tana maida numfashi.
"Daga yau idan zakuyi shashancinku, ina so ya tsaya akan Maryamah, In kuma kukace zaku saka Mahaifin Maryamah a shirmen ku, tabbas zaku gane shayi ruwa ne, dan billahillazee sai na manta da tazarar shekarun dake tsakaninmu na muku abinda har ku kwanta dama bazaku manta dani ba, Ina dau6kan komai amma bana daukan wulaƙanci da cin mutunci, Kuma da kuka ga kunayi, ina share ku inasawa a raina ne cewan ku ai baku isa ku wulaƙantani ba"
"Da ace wadanda nake ma aiki ne suke min haka ko kwana ɗaya bazanyi ba a gidan su, dan ni ba wulaƙantacciya bace kuma bana ɗaukan shi daga gun kowa, amma kasancewar naga kune kuma ba wasu kayan gabas bane, sai nake ɗaukan abinda kukeyi a matsayin shirme"
"Daga rana irin ta yau sai kusan yanda zaku mu'amalance ni dan shirun da kukaga, ina maku bawai dan ina tsoron ku bane, bakusan dalilin zuwana aiki ba dan haka ba zaman ku nake ba ku kama mutuncin kanku tun kafin nayi maku abinda zakuyi dana sani mara amfani Useless human being"
Dogon tsaki taja musu tabar inda suke zuwa gurin da ta tashi, tana jiran su tankata yau ta nunamasu asalin colour nata.
Mamy datazo zata shiga kitchen ɗin tun sanda Dije take maganar ta ta karshe, ta tsaya ganin Maryamah ta nufi inda suke, dan ita da batama fahimci da waye suke ba, taji daɗin gargaɗin da yarinyar ta masu, takuma nuna tasan darajar iyayenta, tasan koda zasu kara mata wani abu, badai yanzun ba, juyawa tayi tabar kitchen ɗin, dan daman zuwa tayi taga in sun gama aikin nasu, dan yanzun za a tafi airport tarban su daddy, A ranta take tunanin kenan matsama yarinyar suke, har taki yau sun mata wanda ta kasa haƙuri ta tanka masu, tabar maganar a ranta da niyya, zata sanya musu ido in suka cigaba, zata ɗauki mataki a kansu.
Ita kam Maryamah cikin natsuwa ta koma ta cigaba da shan tea ɗin ta.
Iya tace mata "Kinyi daidai kin nuna kinsan darajar iyayen ki." Ta kalli su Dije "Kunga abinda nake faɗa muku akan ku ja girman ku kunƙi, gashi yanzun har ya kai ga ƙaramar yarinya ta zauna ta sille ku tass, Kuma in har haka tacigaba da faruwa, bansan kuma mezai iya faruwa ba, dan haka dan Allah tun wuri ku kama girman ku"
Banza sukayi da ita, zuciyar su tana tafasa, domin iya cin fuska yarinyar ta masu, abin mamaki kuma yau ɗaya sai sukaga ta rikiɗe masu ta koma kalar tsiwa, dan gani suke duk da rashin maganar ta, zatayi masifa, shakkar tanka mata sukaji, dan gudun rashin kunyar da zata iya ƙarayi masu, amma a ransu sun sa bata yi a banza ba, zata gane bata da wayau.
Itakam bayan ta gama shan tea ɗin ta, ta ɗauraye cup ɗin.
Iya ta fito mata da fruit ɗin da zatayi fruit juice, ta nuna mata juicer da yanda ake amfani da ita, godiya tayi mata ta fara aikinta cikin natsuwa.
Pineapple ta wanke da apple ta yanka su, sai kuma coconut itama ta fasata da wani engine da iya ta nuna mata na fasa kwakwa da yanda akeyi, Itama yankata tayi, ta hade su tayi blending gaba ɗaya, ta tace su ta wanke na'ana'a da ginger suma tayi blending, tace su tayi akan wancan ruwan fruit ɗin da ta tace flavour ta sanya mai ƙamshin Pineapple and coconut, ta nemi tambulan mai masifan kyau garai-garai ta zuba a ciki.
"Iya bansan ya yanayin son zaƙin shi yake ba, amma duk da haka bari na ɗan saka cokali biyu na sugar, idann yasha beyi ba sai a ƙara"
"Bema son zaƙi sosai"
Ta bata amsa.
Bayan ta gama wannan, ta yanka sauran fruit ɗin, tayi fruit salad ta sanya condensed milk bata juya ba, kawai ta kaishi fridge. A haka tace, in sunzo sai a sanya powdered milk sai a juya gaba daya.
Iya ta tambaya ko akwai aya, tace eh, baza a rasa ba. Tace to ta bata. Iya batama tsaya tanbayan ta ba, tunda taga aikin da tayi, ba tare da ance ga ainayin abinda ake so tayi ba, amma tayi shi daidai koma ace fiye da yanda ake buƙata, shiyasa kawai ta yarda da koma me zatayi to shima zaiyi amfani.
Bata ayar tayi, tace ko akwai sauran abinda kike so, tace eh, in akwai dabino, ina so, tunda naga ga kwakwa nan. Iya tace akwai sosai, kam ta nuna mata cupboard ɗin da ake ajiye dabino. Shima ɗiba tayi, yanda zai isheta ta jikashi kafin ta gama gyaran, ayan tasan ya danyi taushi.
Surfa ayan tayi, sama sama ta wanke, ta rage, sai ta barta cikin ruwan. Ta koma kan dabino, shima ta wanke, ta bare ta cire kwallayen, haɗashi tayi da ayar ta ɗauki kwakwar duk ta zuba tayi blending nasu, ta tace ruwan kuma ta kawo flavour na aya amma na ruwa ta zuba, ta sanya peak milk, ta ruwa ta kawo condensed milk, ƴar daidai, ta haɗa ta juya, ɗanɗanawa tayi, taji zaƙin ya mata, duk da ba wani cika son zaƙi tayi ba sosai.
Iya ta kalla dake naga aikin itama cike da girmamawa tace "dan Allah kisha kiji zaƙin yayi kuwa, ni bana ganewa tunda ba son shi nake ba"
Sha tayi kaman yanda ta buƙata "Uhmmn uhmm charkwaɗi ɗiyar nan, yo ai kin iya hidimar kitchen, kikace kina so ki koya, ni ban ma taɓa ganin kunun aya irin haka ba wallahi yayi masifar daɗi, yau kam ai kin sallami Alhaji ƙarami"
Murmushi tayi kawai ba tare da tace komai ba, wani glass jug Iya ta bata mai girma da faɗi ta zuba a ciki, sai da ta cikashi taff shima ta kaishi fridge tana cewa in mukaji shigowar su sai a fasa kankara a zuba a cikin su duka.
"Hakan yayu ba laifi sannu da ƙoƙari kinji Allah yayi albarka"
Amin ta amsa cike da jin daɗin albarkar da iyan ke yawa saka mata.
Hanyae fita tayi Iya ta dakatar da ita "waɗan nan sauran da kika bari kuma fah, naga duk sai da kika rage saura"
"Naku ne keda su" tayi maganar ta fuska ba walwala, dan ji take ta gama sakar masu fuska kenan har abada.
"Dawo ki ɗibi naki sai kibar mana sauran"
Kai ta girgiza tun kafin ma iyan ta ƙarasa "Naƙoshi Iya kawai kuyi amfani dashi"
"Ai baza ayi haka ba taya zakayi abu kice kuma ke bazakaci ba, jiya ma ina gani dambun naman da kikayi baki kai ko ɗaya bakinki ba, Kuma da kika gama namu kawai kika bari, kikayi packaging sauran, sai da dare da na faɗa ma hajiya, shine ta bada naki, gashi can ki zo ki ɗibi waɗannan abubuwan, sai ki hada dashi, ai haƙƙin ki ne"
Bata son yawan musu shi ya sa ta dawo kawai ta ɗibi kaɗan tace ya isheta ta gode.
★★★★
Ɗaki ta shiga ta aje kayan a kan bedside drawer, ta wuce toilet alwala tayi tana fitowa ta tada sallah, dan already azahar tayi saboda 1 ma ta ɗan gota, tana raka'ar ƙarshe taji diran motoci a gidan, koda ta idar bata tashi daga inda take ba, tunda taga ta gama abinda duk ya kamata ace tayi, gashi ranta a ɓace yake na abinda yafaru tsakaninta dasu Sahura, bata taba sanya lamarinsu a kai ba saboda bata da lokacin su, amma indai suka kara sanya babanta a haukan su, zata tabbatar masu da shayi ruwa ne tayi kwafa.
Ƙarfe 2 da ƴan mintuna duk suka hallara a parlourn daddy bayan sunyi wanka sun canja kaya, waya mamy ta ɗauka ta kira iya tace su zo su kawo kayan abincin babban parlourn daddy.
Tana nan ciki Iya ta shigo da saurinta tana "Tashi maza Maryamah muje mu jera kayan abinci a sashen Alhaji, daga nan muyi masu sannu da zuwa"
Dummm!!! taji gabanta ya faɗi dan ita Allah ya sani bata shirya haɗuwa da sauran yan gidan ba uwa uba, kuma wannan yayan nasu batasan dalili ba, amma tanajin shakkar haɗuwa dashi.
Ɗago kai tayi batasan ta ɓata fuska ba tayi magana a narke "Iya yanzun nima sai naje" tura ɗan karamin lips dinta gaba tayi wanda hakan ya zamar mata daɓi'a a duk lokacin da takejin shagwaɓa, Ita tama manta da Iya take magana.
"Yau kuma shagwaɓa za ama iya ai"
tanajin haka, sai kuma taji kunya tayi ƙasa da kai tana miƙewa.
Kitchen ɗin tabi Iya sukaje, Iya ta nuna mata katon tray da ake dauke da plate da spoons tace ta dauka, suje yayinda ita kuma Iya ta ɗauki wasu tsadaddun food warmers masu kyan gaske, suma su sahura duk sun dauka, wasu warmers din suka fita dasu suka nufi part ɗin Alhaji kasancewar a can za su zauna gaba ɗaya a ci abincin.
Bata san dalili ba amma gabanta mugun faɗuwa yake, dauriya kawai take suna zuwa zasu shiga parlourn, suka samu iyayen takalma gasu nan designers na different companies, amma duk da haka akwai wani d6aya da kyan shi ya fita daban, a kuma inda aka aje, shima daban ne, dan yana daga gefe palm slippers ne irin na maza, Kaɗan ta kalle shi ta ɗauke kanta, suka kutsa kai bakin su ɗauke da sallama....
Gobe kam ayi ɗiyar baba achadu haƙuri babu update🙌
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/JHxZP3j1IIr6O5UZj4Csq5?mode=gi_t
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A