duka a waje tace "na shiga uku aikatau kuma maryamah? baban dai kuma da kansa? Anya kuwa?" Gaba ɗaya ita dai ta kasa yarda
Cikin sanyin murya ta bata amsa "wallahi Aisha baba da kansa, amma yace min dalili mai girma ne ya sa zai haƙura ya barni tafiya, saboda tafiyata ita ce alkhairi a garemu ni da shi"
Yanzu maryamah yace baya fatan ki ƙara ko kwana uku a garin nan saboda tsoron abin da zai biyo baya"
“Bansan meyaji ba, amma tabbas jikina ya bani ƙila labarin wani tuggun suke haɗa min wanda yaji har ya ɗaga hankalinsa, Allah ne ya kawo shi har ya ji, shine dalilin da yasa ya samu baba Malam Sale da maganar, ya ba shi shawarar ya tafi dani wurin matar ubangidansa"
Ita kanta Aisha hawaye take ɗaukewa da yatsunta cikin muryar kukan itama ta bata amsa "Amma kwata-kwata ba Allah a zukatan mutanen nan, Insha Allah mugun nufinsu sai dai ya koma kansu, ni kaina sahiba tun da na ji wannan magana na gagara ki tafi, in Allah ya yarda rayuwarki za ta canja a can, sai sunji daman ace basu kitsa miki mugun abuba, da ikon Allah da baƙin cikinki zasu mutu ƴan wahala" Ta faɗi hakan tana ƙara kumbura, kasancewarta ita ma mafaɗaciya ce kamar ƙawarta, duk da ita ƙawar cikin ruwan sanyi take faɗa, amma maganar zafi take sosai.
"Hakane sahiba nima danaji haka nace wa babana gara na tafi, sai dai zan yi kewarku" tana faɗar hakan hawaye na ƙara zubowa a kuncinta.
Ƴar dariya Aisha ta yi tana share hawayen fuskarta tace "Mene ne yar shagwaɓan babanta?"
Dukan wasa ta kai mata tana cewa, "Duk fa na kewanku ne" share hawayen fuskarta tayi itama.
Bayan sun dan natsu, Aisha ta kalleta "Toh yanzu yaushe za ki tafi?"
"Gobe school ce nazo mu yi sallama da sauran yan class"
"Others like Uncle Muhammad?" A'isha ta tambaye ta tana dariya.
Ɓata rai Maryamah ta yi tana shan kunu tace "Ke kika sanshi, but me I know his existence?" Ta mayar mata da tambayar ta tana taɓe baki
"Really?" Aisha ta faɗa tana dariya.
Ita ma Maryamah murmushi ta yi tace, "Yeah" Daga nan sauran yan class suka dawo, aka ci gaba da karatu har aka tashi, da aka tashi ne Aisha ta yi saurin cewa yan class ɗinsu, "Dan Allah kada ku fita, Maryamah tazo yi mana sallama ne saboda zata koma gun dangin mamanta da zama"
Da mugun sauri Maryamah ta ɗago ta kalli Aisha, ita kuma ta kashe mata ido ɗaya tana murmushi tare da ɗaga mata kai alamar eh haka za a ce. Murmushi Maryamah ta yi ta girgiza kai ƙasa-ƙasa tace, "Allah ya shirya minke sahiba ki daina ƙarya" Da haka taje gaban class ɗin tana cewa, "Eh, kamar yadda kuka ji, gobe Insha Allah zan bar garin nan, dalilin ma da yasa nazo muyi sallama kenan, don Allah a yafe wa juna"
Wasu sun ji rashin daɗin tafiyarta, yayin da waɗanda suke mata hassada a kan baiwar ƙwaƙwalwa da Allah ya bata a fannin karatu suka ce, Umma ta gaida Ashsha haka, dai suka rabu suna kewar juna, duk da ba shiga hidimarsu take ba, amma they still mean a lot to her, three years no be small thing.
A hanyarsu ta dawowa gida ma haka suka yi ta jajen tafiyarta.
Cikin sanyin murya Aisha ta kalleta tace, "Best dagaske tafiya zakiyi ki barni?"
"Hmmmn!" kawai Maryamah tace, don ba taso ta buɗe baki, dan ita kaɗai tasan irin baƙin cikin da take ji da ɓacin rai a kan wannan tafiyar, dauriya kawai take yi.
Shiru suka yi kowa da abinda yake ranshi ganin yanda idanun maryamah sukayi ja ne yasa A'isha riƙe hannunta a hankali tace "Khairan Insha Allah"
Ganin sunzo inda zasu rabu ne yasa maryamah kara riƙe hannun A'isha dayake cikin nata.
"Karki damu zanje gida, anjima zan shigo na tayaki haɗa kaya"
Cikin murmushin yaƙe maryamah ta kalleta tace, "Yau kuma kece za ki zo gidanmu?"
Itama murmushin ta ƙaƙalo "Ki bari kawai ai ranar dole sai dole, amma Allah ya sani na tsani ganin baƙar fuskar matar gidanku, ga munin fuska ga na zuciya, kai tirrrrr" ta ƙarasa tana sakin yar dariya.
Rabuwa suka yi, kowa ya kama hanyar gidansu, ran Maryamah a jagule ta shiga gida, domin dariyarta da murmushin ta na ƙarfin hali ne da son ƙarfafa kanta, Bataso rauninta ya fito har Aisha ma ta shiga damuwa sosai.
Kamar wadda akayi wa dole ta buɗe baki ta yi sallama ciki-ciki, domin yau zuciyarta a sama take, da ba don sanin muhimmancin sallamar ba wallahi da baza tayiba.
Zaune ta samesu suna magana da Hajja da Baba Zainu, amma da suka gan ta sai suka yi shiru, ba ta kalli inda suke ba, ta shige ɗaki domin yau jinta take dai-dai da su, Ganin ba ta tankasu ba yasa Hajja ta fara masifar da ta saba tana cewa, "Shegiya, kin shigo kin same mu amma kallo ba mu isheki ba? To wallahi ni dai in kika mani jafaru kika yiwa, tunda ko banza ni na haifi abina, yar malafar uba"
Baba Zainu kam sai cewa tayi, "Ke ma dai Hajja, in ta gaishe mu ai munada ƙima a idonta, Ai halinta halin uwarta, kaff baƙin halin uwarta ta kwaso, ba ta rage komai ba sai ma ƙari datayi"
Sosai zuciyarta take zafi jin yanda suke aibata umminta wadda tun da ta haifeta ma ko fuskarta ba ta kalla ba ta koma ga Mahaliccinta, amma wai ita za su zaga ta dalilinta, duk da yanda zuciyar take azalzalar ta haka ta danne dan tayi alwashin yau ba za ta kula su ba balle su ƙara fadin maganganun banza a kan mahaifiyarta.
Uniform ɗinta ta cire, ta ɗauki soson wankanta da sabulu ta fita. Nan ma tari batai musu ba, fuskarta a ɗinke taja ruwa ta shige bayi, ta barsu da halinsu, duk da tana jin basu fasa ba ai bata ta da mahaifiyar ta ba.....
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋
BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)&❤️ TARE DA KAI HABIBI NA AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️
FULANI ❣️
08082101373
✨🦋RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
PAGE7️⃣
Bayan fitowar tawanka ta shige ɗaki tana jin su, har lokacin basu dena zagi da aibata ta ba, a ranta ta ayyana aiki ya same ku kukam, haka ta shirya cikin kaya masu sauƙin nauyi, dan tana da jin zafi, duk da bata da wani jiki sosai, amma Allah yayita da mugun jin zafi, zama tayi ta fara haɗa kayanta, dan yau ko takan abinci bata bi ba domin she’s not in the mood, kuma cikinta a cinkushe yake, dan ko tace zata ci abinci ma tasan ba shiga zaiyi ba, zuciyarta a kuntace take.
Jakar kayanta ta jawo ta fara zuba kayan a ciki, kasancewar tana da wadatar sutura, saboda babanta na matuƙar ƙoƙari wajen yi mata ɗinki da siya mata kayan gwanjo, kayanta sun kai kusan kala goma sha biyar, a haka ma dan ita ba mai daɗewa da sutura ba ce, tana samun wasu take bada wasu, bata jima ba ta jerasu tsaf cikin jaka.
Tana gama haɗa kayan ta ɗakko litattafanta na makaranta suma ta haɗasu waje ɗaya, tana cikin haɗawa ne ta ji sallamar Aisha a tsakar gidan.
Fitowa tayi tana amsa mata "Ashe da gaske kike zakizo" ta faɗa cikin sakewa kaɗan.
Taɓe baki tayi ta bata amsa "Ai kin koya mini rashin saɓa alƙawari"
Kallon Hajja tayi tace, "Hajja ina yini" domin ta ci darajar kasancewarta kakar Maryamah, ko dan baba zata gaidata.
A ɗage ta amsa mata da lafiya, tana kauda kai gefe, saboda ita a rayuwarta bata ƙaunar taga wani ya raɓi Maryamah, dan ita fa a duniya bataƙi ace Maryamah ta zama mujiya ba, ya kasance kowa yana gudunta, amma hakan bai samu ba, dan Maryamah ba mai sakewa ba ce da jama'a, duk da haka kuma tana da farin jinin mutane, kawai dai baƙin miskilancinta da wulaƙanci da shegen girman kai (amma fa inji su Hajja ) shine yake hanata mu'amala da mutane.
★★★★
Ɗaki suka shige Aisha na cewa "Kai ashe ma har kin gama, ina ta sauri"
Hmmmnn kawai tace mata ba tare data bata amsa ba.
"Danaje gida na samu ummanmu na masa da kuli, shine fa na tsaya na taho miki da ita, tunda nasan mutuniyar ki ce sosai" ta faɗa da murmushi sosai a fuskar ta, so take ta saka maryamah farin ciki, bata sonta cikin wannan damuwar.
Nanma dai hmmnn ɗin kawai tace.
Harta cire rai da zata bata amsa taji muryarta ƙasa ƙasa tana bata amsa.
"A'isha bakina ɗaci yake, bazan iya ciba"
Bata rufe baki ba itama ta tari numfashin ta "wallahi sai kinci, ni zaki watsawa ƙasa a ido inyi dakon abu tun daga gida kizo kiƙici? Ah haba, ai wallahi baki isa ba"
Murmushi tayi naji jarababbiya"
Itama murmushin tayi "Yauwa to koke fa yanzun naga sahibata a tare dani"
Maryamah tace "Toh dawa kike gani?"
"Someone else" yanda A'ishahn ta bata amsa ne yasa duk suka yi dariya.
Fita tayi ta wanke hannun ta zata fara ci, Aisha ma tashi tayi ta wanke hannu ta sauko zata ɗauki wainar.
Da sauri Maryamah ta ɗauke tana cewa "Ban gane ba malama, menene haka? kema kin san baki isa ba, kici taki a gida kizo kice zakici tawa?" Ta ƙare maganar tana zabga mata harara.
Bata bata amsa ba sai ƙoƙarin ƙwata da take a hannun ta, sosai suke kokawar ƙwatar wainar, Aisha ta dage sai taci, itama maryamah tana batazaci mata ba, ai tasan tatace ita kaɗai, ummanta ta bada a kawo mata.
Sosai zukatansu suka samu nishaɗi, wanda Aisha tana sane ta aikata hakan, dan tasan abinda zai faru kenan, Zuwa can ta zauna tana sauke numfashi, wadda ta ɗauka ta saka a baki tace, "aidaman nace sai na ci"
Maryamah ƙasa ƙasa ta kalleta tace "My kawai"
Hmmm
"Ki fito kanki tsaye kice min mayya, bawai my ba"
Sosai Maryamah ta ji daɗin zuwan Aisha, ko banza ta rage mata wani nauyin zuciya.
Haka suka yi ta hira. Bayan ta gama ci ta wanke hannu ta dawo, nan suka cigaba da haɗa kayan har aka kira la’asar. Suka fita sukayi alwala, anan taga su Zainab tace su yi maza su yi sallah su kama hanyar Islamiyya, ita yau bazata ba.
Ba yaran bama, har baba da Hajja sun yi mamakin jin wai yau ita ce bazata Islamiyya ba, a yadda take ƴar allazi makaranta, Da toh Addah Zainab ta amsa ta tashi tana shirin alwala. Ita kuma Maryamah ta shige ɗaki ta bar su, baba na binta da ido, kuma ba damar bin ba’asin abin da ya hanata zuwa makarantar, tunda sun sanba wannan mutuncin a tsakaninsu.
Itakam haka suka zauna ana ta hiran bankwana da Aisha har aka kira magrib, sai bayan sunyi sallar magrib ne suka fito zata raka Aisha, lokacin matan gidan sun shiga ɗaki.
A ƙofar gida suka haɗu da baba zai shigo, nan Aisha ta tsugunna har ƙasa ta gaida shi, Ya amsa yana faɗin, "Aisha, anzo bankwana da ƙawar taki ne?"
"Eh baba"
Ganin yanda ta amsa ne yasa shi cewa "Toh duk muyi haƙuri, haka Allah ya tsara, dama Allah ya rigada ya tsara cewa zata tafi wani waje daban tabar mu" "Hakane baba"
Maryamah ya kalla "kiyi maza ki rakata ki dawo"
"Toh babana" Da haka suka wuce.
★★★★
Sai da ta rakata har gida, don tana so tayi wa ummansu sallama, sanda suka shiga sun samu umma ta idar da sallah. Maryamah ta shiga cikin nutsuwa tana gaida umman.
Amsa mata tayi haɗi da cewa "Maryamah idonki kenam?"
Sunnar da kai ƙasa tayi tana murmushi tace "Umma kiyi haƙuri"
Itama umma murmushi tayi tace, "Anya kuwa zan iya wannan haƙurin?"
"Zaki iya Allah umma, ai uwa bata fushi da ɗiyarta"
"Ai fa kin iya daɗin baki" inji umma.
"Aa fa ummana"
"To aishikenan, na haƙura" cewar umma.
Gyara zama tayi kallon maryamah tayi ta kira sunan ta da muryar dake nuna duk maganar da zata mata ne muhimmanci ce.
"Maryamah ashe kuma abinda yafaru kenan ɗazun Aisha ta dawo take faɗa min" Hawaye ne suka cika idonta tace, "Eh wallahi umma" ƙoƙarin maida hawayen idonta take amman ina saida suka zubo akan fuskar ta.
"Kiyi haƙuri ki ɗauki hakan a matsayin ƙaddararki kinji, ni kaina bansan meyasa ba, tunda Aisha ta faɗa min naji a raina kamar hakan alkhairi ne a gareki, wallahi ko kaɗan banji ina fargabar tafiyanki ba, hasalima ni daɗin hakan naji, da ikon Allah wannan tafiyar sai mun ce gara da akayi ta"
Shiru tayi tana ƙoƙarin danne tausayin maryamahn dayake taso mata jin yanda take ta sauke ajiyar zuciya, ga hawaye tamkar an buɗe famfo haka suke zarya akan kumatun ta.
"Ki kwantar da hankalinki, sannan in kinje ki riƙe mutuncinki, ki kama kanki ki kama mutuncin kanki, kada abin wani ya burgeki, ban sanki da kwaɗayi ba, don Allah ki cigaba da hakan, karki bari halin ki ko guda ɗaya ta canza.
"In sha Allah umma" ta bata amsa tana goge hawayen dayake zubo mata.
Itama Aisha na gefe tana matse nata hawayen.
Ɗorawa tayi daga inda ta tsaya "ki kuma dage da addu’a, in kuma kin fara makaranta kamar yadda muke sanya rai, dan girman Allah ki tsaya ki yi abinda ya dace da rayuwarki, banda shashanci, duk da nasan ba halinki bane, ba ruwanki da rayuwar yaran masu kuɗi, ki riƙe maraicinki da talaucinki, sannan ki iya talaucinki, kada kuma ki wulaƙanta kanki a wajen kowa ta hanyar nuna son abin hannun wani"
Jinjina kanta tayi cikin kuka tace "Nagode sosai umma, Allah ya ƙara girma, haƙiƙa ke ɗin uwace wadda har ɗan wani ta maida nata, In sha Allah bazan baku kunya ba, zan yi amfani da dukkan nasiharki gareni, nagode, nagode" bata ƙara sa maganar ba kuka ya kuɓce mata.
Tsam Aisha ta taso ta rungumeta suka cigaba da kukan tare, ita kanta umma ƙarfin hali kawai take yi amman sosai take tausayin maryamahn.
Cikin ƙarfin hali tace "K
kaji shashanci to meye abin kuka, sai kace waɗanda in suka rabu sun rabu kenan. Ke da ya kamata ki ƙarfafa mata guiwa ma, zaki zauna kuna kuka tare"
Share hawayensu suka yi suka lallashi junansu.
Daga nan ta miƙe tace, "Umma bari naje gida dare yayi, sai da safe nagode Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana"
Umma tace "Maryamah, godiyanki ta isa haka, keda Aisha duk ɗaya kuke a wajena abinda zan yi wa Aisha shi zanyi miki, koba dan abotar dake tsakaninku da Aisha ba, ko dan zaman mutuncin da mukayi da mahaifiyarki, tunda Allah ya sa suka zo garin nan, mun yi mutunci da ita har zuwa ranar da ta bar duniya, Allah ya jiƙanta, mace mai matuƙar mutunci da yakana, ga haƙuri da gudun zuciya, Kuje kawai, dare yayi Allah ya yi miki albarka, ya tsareki da tsarewarsa"
Ameen duk suka haɗa baki suka amsa. Aisha na binta don ta ɗan taka mata…..
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋✨
BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)&❤️ AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️
FULANI ❣️
08082101373
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
PAGE 8️⃣
A hanya ma haka suke ji tamkar kar su rabu amma ba yanda suka iya sunzo daidai inda ba nisa daga nan zuwa gidansu Maryamah da kuma ita Aishan
Dakatawa sukayi da tafiya suka riƙe hannun juna.
A'isha ce ta kalleta tace "Sahiba ji nake kamar na biki mu tafi tare"
Murmushi tayi "kinjita kamar gaske"
yar dariya tayi "Allah da gaske"
Ganin A'ishan tayi kalar tausayi ne yasa ta fara mata magana cikin sigar tsoakana "Ba wani abu kika sani ma, koda naje ƙura ta lafa na gudo in dawo gida, ko in naga mutanen gidan basu da kirki wallahi guduwa zanyi dan ba yanda za ayi na tsaya a wulaƙantani, ke kinsan ma zuciyata bazata dauka ba"
Yanda maryaman tayi magana ne yasa tayi dariya "Sauran kije kina musu girman kai da wulakanci in miki ta bakin Hajjah"
Kusan a tare suka saki dariya "saifa abinda suka gani, nidai bazan ɗauki wulaƙanci ba, duk kuɗin mutum atohhhh"
"Insha Allah ma mutanen kirki ne zakiji dadin zama a cikinsu"
"Allah yasa kije gida kawai gobe kafin mutafi ko kinje school zan biki can in kara ganinki"
"Tabb ai wallahi gobe babu inda zani sai naga tashin motan ku dan har tasha zan biku"
Murmushi Maryamah tayi tana jinjina girman ƙaunar da Aisha ke mata, itafa zata iya sadaukar da komai saboda ita kuma tun suna yara suka tashi haka suna masu tsananin ƙaunar junansu, saboda Aisha take surutu, kasancewar ta bakin ta baya shiru, koba kayi niyyar magana ba saita saka ka kayi dolen ka, kuma saboda ita ta koyi buɗe baki ta mayar da magana in su Hajjah sun mata abu, wanda da ko kasheta zasuyi akan abun da batayi ba bazata bud6e baki ta kare kanta ba sai dai in an gama jibgarta ta shiga daki taci kuka ta gode Allah, Aisha ce in a mata take maidawa bayan sun keɓe su biyu kuma tayi ta mata bala'i akan ita bazata iya taɓuka komai ba, a haka a haka har itama ta fara maidawa daga kawaye har yan gida ya zamana ba ayi mata tayi shiru kamar da, daga baya kuma sai ya zama ƙawaye na shakkar yi mata saboda wani lokacin fuskanta kawai in mutum ya kalla yaga yanda take ɗinke ta sai yaji shakkan yi mata magana bare rashin mutunci, su Hajjah ne dai har yanzun suke fafatawa amma suma kaso 70 cikin 100 ya ragu na abunda suke mata da sbd sun san bazata ɗauka ba.
Haka sukayi sallama, kowwa ta kama hanyar gidansu a ransu sunajin matukar kewan junansu tun kafin ma su rabu.
Washegari, asubar fari, haka ta tashi sukuku duk bata da kuzari tafita tayo uzurinta ta ɗauro alwalah, nafila tayi ta zauna tana istigfari har akayi kira na biyu, tashi tayi tai raka'atan Fajr ta ɗora da sallar Asbah, bayan ta idar tayi duk abubuwan da ta sabayi na ibada dukda bata cikin yanayi mai kyau ranar, ko ayyukan da takeyi na gida bata samu daman yinsu ba. Haka ta zauna ta rafka uban tagumi, ita batama san tunanin me ya kamata tayi ba.
Ita kuwa Baba Zainu tana can, ta saki hanɗa da ganɗa tana ta sharar bacci sai uban Munshari take saki kamar wata bujimar saniya, tana tunanin baiwarta na can na mata aikin gida kamar yanda ta saba. Daman sallah sai 7 da wani abu take tashi tanayinta daga ita har yaranta, balle hassu da ba kullum take kwana a gidan ba, wani lokacin sai ace ta kwana gidan ubanta ne.
Sai ƙarfe 7 da minti shabiyar ta tashi, haka ta fito tsakar gidan tana faman mutsikka ido tana sakin hamma da miƙa, Idonta be sauka akan ko ina ba sai wurin murhu taga ba alamar ma anje wurin tun jiya. Kallon tsakar gidan tayi taga ba a share ba komai nanan yanda ta barshi jiya.
Cike da takaici tace "Kenan yau wannan yar iskar yarinyar ba Abinda tayi a gidan" Kasancewar tasan ko batayin ba, bata da yanda zatayi da ita tunda yanzun ba kamar da bane, da in batayi ba zata kamata ta jiba kuma ta sanya ta tayin dole koda bata so, sanin babu abinda zata iya akaine yasa kawai taje ta rarumi buta ta fada bayi, bayan tayo uzurinta tafito aka batsaltsala Alwallah aka shige ɗaki.
Faka-faka ta bubbuga sallah tayo waje dan tasan yaran yau sai sun makara kuma waccan shegiyar ɗiyar da ubanta bazasu bari tace kada suje ba, lokacin da take kiciniyar hura wuta, su kuma yaran suka tashi.
Ganin sai lokacin ma ake hura wuta sukace "Babarmu, yau zamusha dukan latti"
Ashar ta ɗura musu tana me daka masu tsawa akan su ɓace mata da gani dan a matukar fusace take da abunda Maryamah tayi yau, naƙin aikin gidan kuma tasan ba yanda za ayi tayi ma yarinyan magana.
Itakam Maryamah tana zaune bata ma san lokaci yaja ba ta faɗa duniyar tunani har sai da taga hasken rana ya hudo ta cikin ɗakin, yaye labulen dakin tayi tana kallon hasken ranar da yake haskaka fuskanta amma zuciyanta cike da duhu, tanaji kamar duniya ta juya mata baya in har ta tafi tabar babanta.
"Anya zan iya barin garin nan kuwa, inda na tashi tun yarinta har kawo yau, uwa uba kuma ran danafi ƙauna sama da komai a duk faɗin duniyar nan yana cikin shi wato mahaifina?!" Ta tambayi kanta cikin shakkar barin garin, amma wata zuciyarta na faɗa mata "Maryamah dole kibar garin nan kobadan kanki ba kodan kwanciyar hankalin mahaifinki, saboda halin da zuciyan mahaifinki take cikin na tsoron abunda ka iya faruwa da rayuwanki a dalilin zaman ki a garin" Wannan zuciyar nata itace ta bata ƙwarin guiwa kan cewa zata bar garin don mahaifinta da gobenta da kuma ilimin da take kwaɗayin samu, zata tafi amma ita kanta tasan zuciyanta tana tare da babanta a ko ina domin tana matuƙar ƙaunar shi sama da komai da kowwa shi ɗin duniyarta ne!!!.
Haka ta fito tsakar gidan tana
ƙarewa yaran da suke zaune suna shan koko kallo, da saurinsu har suna hada baki wajen faɗin "Addah ina kwana"
Lafiya lau ta amsa musu ta ɗora da kuyi hakuri yau na jawo maku makara, bansan time ya tafi haka ba.
Yaran take faɗawa saboda a ganinta sune dolenta, amma uwar yaran ce ta bata amsa.
wadda daman tun fitowarta take watsa mata harara da faɗan "Muguwa da baki fito kinyi musu abun karin ba ninayi, sauƙinta ma Allah ya wadatani da hannu da kuma lafiyan da zan musu ɗin" ta ƙarashe tana buga uban tsaki.
Kawar da kai Maryamah tayi saboda bata da lokacin maganganunta, ta barta ma taji da abinda ke ɗawainiya da rayuwanta mana.
Saboda kawai ta ƙara ƙular da ita tace
"Baba ina kwana" bata jira cewar taba ta wuce ɗakin babanta.
Kaman yanda tayi tsammani kuwa yaji tana zazzaga mata masifa.
Itakam ko gajiya batayi abinda ke