Share this page
7 / 9
maganar a tsawace. Maimakon taji tsoronta, sai ta tsaya tana mata kallon ido cikin ido, dan haka nan taji matar batayi mata ba, kuma bata da kwarjini Sam a idonta, tace hajiya ce, tace a gyara ma yaranta zasu dawo. Cike da isa ta ƙara daka mata tsawa "Cire idonki cikin nawa yar matsiyata, kina kallon mutane cikin ido gidanku ba su baki tarbiyyan da ya dace bane halan?" Don ita kanta a nata ɓangaren ganin yarinyar, saida ya sanya mata mummunar faɗuwar gaba, kuma lokaci ɗaya taji ta mugun tsanar yarinyar, duk da bata san wacece ita ba, kuma bata tantance matsayinta ba a gurin waccan matar uwar yan kwashe-kwashe. Kauda kanta tayi gefe duk da taji zafin maganar matar, amma tunda rashin girmama na gaba da ita ba halinta bane, yasa ta ƙyaleta, dan ko su baba sai da taga zasu kasheta da azaba ta fara kwatar kanta a gurinsu, cire key ɗin tayi ta ƙara kallon hajiyar cikin ido, sannan ta ɗauke kai, tayi gaba ba tare da ta amsata ba. Hakan da tayi ya ƙara rura wutar tsanar da hajiyan taji tanayi mata duk da bata san wacece ita ba, fisgota wata zuciyan tace tayi, amma sai kuma taga ai ba girmanta bane, ta tsaya sa’insa da wannan kuchakar a compound ɗin gidan, ƙwafa tayi, zamu haɗe in har ta tabbata itace yar aikin da akace waccan matar ta kawo gidan, ta rantse da wanda ranta ke hannun shi, wannan karan sai yarinyar ta bar gidan, dan bazai yiwu ta dinga masu kwashe-kwashe ba, wataran ta kwaso wanda zai zamar musu jaraba. Part ɗinta ta wuce tana kwala ma ɗiyar ta kira mai suna Farha. Zaune ta same ta tana famman danna waya, hankalinta kwance kamar bataji uwar tana kiranta ba, ranta ne ya ƙara ɓaci akan wanda ta shigo da shi. tsawa ta daka mata "bakiji ina kiranki ba bane?" Ɗago idonta tayi daga danna wayar, itama cike da izza, wadda har taso tafi ta uwar tata "Lafiya?" Ta mayar mata da tambayar ta. Zama tayi kusa da ita "Kinsan kamannin yarinyar da akace Zeenatu ta dauko aiki?" Girgiza kanta tayi ta cigaba da danna wayan ta, sai zuwa can ta ɗago ta kalli uwar tace "Mom miye haɗina da ita da zan san kamanninta? Infact ni ban ma taɓa ganinta ba, kin manta Nabeela ce ta ganta tazo take faɗa maki?" Wani zazzafan huci mom ta sauke "Hmmmn wata useless yarinya na gani ta fito daga part ɗin su Haydar, kinsan inama yarinyar nan magana ta wuce ni ta barni tsaye" ta ƙara sa maganar cike da takaici. Ido Farha ta zaro cike da mamaki "Who the hell is she?" Mom tace "Ina zan sani dan ubanta? Aikam in itace mai aikin, gobe daddy ku na dawowa dole ta maidata inda ta daukot wallahi!!!! Ta ƙarasa maganarta ta cike da alwashi..... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t https://chat.whatsapp.com/DysmUMWo6dYJlLWGBPOMEI?mode=gi_t ✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋 BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️ FULANI ❣️ 08082101373 🦋✨ RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨ PAGE 1️⃣7️⃣ Koda ta shiga bata faɗawa mamy ga abinda yafaru ba kawai keys ɗin ta maida ma mamy tace sun gama sannu tayi mata tana sanya mata albarka tace taje ta huta kafin Zuhura ta dawo in sunyi azahar sai suyi aikin ko zuwa azahar ne. Ɗaki ta shiga daman a jigace take dan yau ba ƙarya ta aikatu gashi bata ma gama ba, tana shiga wanka ta farayi sanan ta zauna zaman breakfast time din 10:30 na safe flashing tama babantayan katsewa yayi ya kira ta dauka cike da shauki da kewa tace babana! Shima a can bangarenshi cike da kewar gudan jinin nashi yace diyar babanta kina lafiya, tace alhamdulillah sai tsananin kewar ka baba. Murmushi ya saki mai sauti yace to ai gani a waya, cikin yar shagwaɓan tace to ai kewar ta zahiri ce. Haka sukayi wayan cikin tsananin so da kauna irinta ɗa da mahaifi har sai da katin shi ya kare sukayi sallama. Bayan sun gama takwanta tunda taga akwai sauran time aikam bacci ya ɗauke ta, ba ita ta farka ba sai 1 iya ta shigo kusan sau biyu amma ta sameta tana bacci kuma bata tada ta ba tunda tasan yau kam tasha aiki a haka ma ba gamawa tayi ba. Tana farkawa sallah tayi ta fita kitchen ta fara shiga ta same su sun kacame sunata aiki kowa da abinda yakeyi a ranta take cewa ko mutune nawa ne zasuzo wannan uban kayan fulawa da akeyi(snacks). Sannu ta masu iya ta amsa su kam tsaki suka mata bata damu dasu ba dan batasu take ba, wurin iya ta karasa tace mata sannu da aiki iya, tace yauwa Maryamah kin tashi kenan, tace eh ashe bacci ne ya ɗauke ni ban sani ba me zan kama maku dashi naga kunata aiki, Iya tace a'a kibarshi ɗauki abincinki kici in kin gama sai kije wurin hajiya dan naji hajiya ƙarama (Zuhura) na neman ki sannan mutanen ki ma sunata zaryan nemanki dan ma hajiya ta hanasu tadaki da taji kina bacci ne. Murmushi tayi tace to bari naje in na dawo sai naci abincin, Iya tace a'a da dai kintsaya kinci saboda in kikaje be zama lallai ki dawo yanzun ba yau aiki garemu da yawa. Tace ai banajin yunwa kinga ina cine ma bayan na gama bacci ya ɗaukeni, haka ne sai kin dawo. Kitchen ɗin ta fita ta nufi parlour inda tana dosowa taji hayaniyan su da kamar ma ƙarin wasu mutanen, a nutse ta shiga da sallama gaba ɗaya hankalin mutanen parlourn ya dawo kanta yayinda su twins suka fara rige rigen zuwa wurinta suna faɗin oyoyo cutie itama hanayenta ta buɗe musu kaɗan duk da bata so ta zaƙe amma bai kamata ta share ƙaunar da yaran ke nuna mata ba, jikinta suka shiga cutie we miss you kansu ta shafa to ai gani kuma kunga weekend za a shiga zamuyi hira sosai. Sunajin haka suka fara tsallen murna, ɗago kanta tayi da murmushi taga yanda baƙuwar fuskan dake zaune kusa da mamy tana breastfeeding babyn ta wadda bata wuce 11 months ba,ta saki baki tana kallonta tana murmushi. Ƙasa tayi da kanta tace mata ina yini ta amsa cike da sakewa "Mashaa Allah daman kece cutie ɗin da su Fadil suka damemu da labarinta kenan tunda na iso abun mamakin wai har da Fudail" murmushi kawai tayi ita kuma waccan ta cigaba da "ah Mashaa Allah lallai kinci sunan cutie" ta kalli mamy tace "mamy ina kika samo kyakkyawan ɗiya sai ki bani itama kawai in zan koma mu tafi tare gaskiya" "Toh uwata aminatu dole zan baki ita mana tunda ina tsoronki ko kada ki min baki na lalace" Dariya duk sukayi "au nafa manta mamy yanzun zaki fara mita amma dai Allah nikam dama ki bani ita" Banza mamy tayi da ita dan bata ganin zata ƙara tanka mata ta maida kallon ta ga Maryamah tace "kinzo kucigaba da aikin ne?" "eh haj....." kafin ta ƙarasa Fudail yace "mamy not hajiya' Gaba ɗaya falon murmushi sukayi mamy tace "Maryamah haƙuri kawai zakiyi ki dena kiran hajiyan nan tunda su Fadil sun bani ke matsayin ɗiya" Itama murmushi tayi tace inshaa Allah mamee, mamee tace ko kefa, kallonta ta maida kan zuhura da tun ɗazun bata ce komai ba "hajiya fati a tashi a fara aiki koh?" Dariya duk sukayi Zuhura tace "yau kuma fati na koma mamy?" tace yo eh mana ai duk sunan ki ne. Tashi tayi "muje to may be daga nan zuwa asr mu gama tunda ba wani datti ne dasu ba" mamee tace "probably amma sai idan kun maida hankali baki tsaya zuba magana ba" "kai mamee" ta faɗi tana kumbura baki, aunty amnah dake zaune tace hali ai mamee ta sani. Ita kuma Zuhura ta ƙara tunzura baki tace mamee kinji aunty ba. Mamee tace ki tsaya shaida kada ki tafi kuyi abu5nda ya dace. Tashi sukayi tace ma Maryamah "cutie muje" itadai in sukace cutie ɗin nan sai taji abun wani banbarakwai haka tabi bayan ta su Fadil sukace zasu bita mamy tace bazasu ba in sunje bazasu barta tayi abinda ya dace ba. Haka suka fita ita da Zuhura tana ɗan yi mata hira kaɗan kaɗan ita kuma sai murmushi kawai dan batasan mi zata ce ba, ko da sukaje part ɗin daddy Zuhura ta sanya key ta bude suka shiga, part ɗin din shigen yanda ginin part din mamee yake shima haka yake, furniture's ɗin ne kawai suka babanta sai kitchen ɗin da yake dan ƙarami sannan kuma ƙasan 2 bedrooms ne kawai. Sama Zuhura tace su fara gyarawa suka dunguma sukayi sama, nan ma dai Maryamah tasha kallo amma tana kamewa dan kada Zuhura ta fuskanta haka ta ringa mazewa, ɗakin daddy suka fara shiga Zuhura tace tare zasuyi komi ita dai Maryamah binta kawai take, gado Zuhura ta fara gyarawa ita kuma Maryamah ta shiga toilet ta wanke shi fesss. Sanda ta gama ta fito itama Zuhura ta gama gyaran ɗakin tayi mopping ta canja bedsheet, turare ɗakin sukayi sannan suka fito suka gyara parlour sama daga nan sukayi ƙasa shima suka gyara shi tass in not less than an hour sun gama komai na part ɗin daddy, Zuhura nata zuba mata surutu dan surutun ta ma yafi aikin yawa. ★★★ Bayan sun gama part ɗin wanda taji anacewa shine babban yayan su suka nufa, suna tafiya Zuhura tace "to Allah yasa in mun gyara in ya dawo yace yayi dan shi yaya ba a mishi gwaninta ka gama wahala yazo ya ce baka iya komai ba" ta ƙarasa tana ɓata fuska. Jin yanda Zuhura ke mita yasa Maryamah jin fargaba akan aikin nashi batasan tace ma Zuhura to in beyi mashi ba ya yakeyi cikin low tone. "Hmmmn idan ya fara masifa ba hmmmn daga karshe sai ya gyara abinshi baya yarda ana gyara mishi part fah cewa yake wai duk bamu iyaba, babu abinda muka iya, but a haka ma wai ni yace idan nayi yana ɗanyi mishi akan nasu ya Farha da Husna na part ɗin mom, sukam yace ba abinda suka iya sai ciye ciye da lalaci wai mijin da ya aure su ya shiga uku da ƙazanta imagine fah" ta faɗi tana yar dariya. Itama Maryaman dariyan ne tayi kadan tace "amma dai yayan baya duka koh kamar in an mishi ba dai dai ba?" Dariya Zuhura tayi "ah haba baya duka but ya iya punishing mutane in such a way that zaka so ma ace dukanka yayi wallahi" tayi maganar tana ɓata fuska. murmushin yaƙe Maryamah tayi a ranta tana fadin inshaa Allah bazamu hadu ba balle har ya sanya ni abu nayi ba daidai ba. Suna isa nan ma Zuhura ta buɗe musu suka shiga Maryamah ba tasan lokacin da tace wow Mashaa Allah tana haɗe yatsunta wuri ɗaya tama manta ba ita kaɗai bane a wurin. Saida taji Zuhura tayi magana "so you like the part" dage mata gira tayi alamun tana jiran amsa. A take ta dawo hayyacinta cikin jin kunya tayi ƙasa da kanta. "Allah baki isa ba tunda muka taho nake miki surutu baki nuna labarina na burgeki ba and munzo nan Allah ya kamaki kika buɗe baki kikayi magana daga zuciyan ki yanzun dan nayi magana zaki wani ƙasa da kai wai kunya" Yar dariya tayi tace "kai wai daga zuciyana inji waye yace daga zuciya na na faɗi ban ma fa san na faɗi ba" tayi maganar a shagwaɓe ba tare data kula da hakan ba, dan ɗan sakewan nan da tayi da yanda Zuhura ke mata surutun sai tajita kamar tana tare da Sahiban ta. "Wow cutie so you're that cute idan kikayi smiling but why are you always frowning your face kina rage kyau Allah be smiling always" Murmushi mai faɗi tayi a ranta tana jinjina halin Zuhura dan Allah ji yanda ta saki jiki da ita kamar ba me aiki da wanda ake ma aiki ba, bata bata amsa ba tace "yanzun dai mamy tace kada ki tsareni da surutu dan haka muyi aikin mu" tayi maganar with a wide smile on her face. Zaro ido Zuhura tayi "cutie kema haka zaki ce" "a'a yi haƙuri zoki nuna min inda zan fara dashi" Parlour ne mai matsaƙaicin girma amma yayi matuƙar ƙayatuwa da tsaruwa fentin da cushions din dake ciki har curtains ɗin duka off white ne daga ganin yanayin tsaruwar wurin zaka san mamallakin gurin mai tsananin tsaff ta ne kuma ɗan gayu, dan komi a tsare yake kamar ɗakin mace ba wani tarkace ko hayaniya daga gefe akwai wani ɗan corridor wanda kana bin gurin zaka ga 2 bedrooms, a parlour ɗin kuma akwai ƙofa guda biyu ɗaya ɗan ƙaramin kitchen ne da ke ɗauke da jerin kayan tea kala daban daban da na coffee, ga kuma coffee maker a gefe sai standing gas cooker mai 4. Akwai wani dish drainer na company roveger wanda ke ɗauke da plates da cups masu kyau sosai......... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/DysmUMWo6dYJlLWGBPOMEI?mode=gi_t https://chat.whatsapp.com/DysmUMWo6dYJlLWGBPOMEI?mode=gi_t ✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨🦋 BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️ FULANI ❣️ 08082101373 🦋✨ RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋 PAGE 1️⃣8️⃣ Kitchen ɗin ta gyara tsaf, ta wanke cups ɗin da plates, har dish drainer ɗin sai da ta wanke sannan ta sake jerasu gwanin ban sha'awa, bayan ta share ko'ina tayi mopping sosai, komai tana yi da taka-tsantsan kada taje tayi ba daidai ba yazo yace a nemo ta, yayi punishing nata, tsaf ta gyara kitchen ɗin ya ɗauki ƙyalli, kalla tayi sosai a ranta tace, ita dai tasan duk yadda ya kai ga son liƙa ma mutane laifi, nan dai ya fita. Bata gama tunanin ba, Zuhura ta shigo, ganin yadda ta gyara kitchen ɗin sai kyalli yake, tace "wow cutie where did you learn all this?" Murmushi ta mata "ba ko ina" Haka suka fito Zuhura na zuzuta yadda gyaran kitchen ɗin yayi kyau duk masifan tsaftanyaya nasan dole zaiyi shiru wannan karan. Koda suka zo parlour itama Maryamah tace, "to ai aikin da kikayi ne ma abin ya yabawa, wallahi kin yi ƙoƙari sosai sannu da aiki" Murmushi tayi "Allah yasa yayi ma yaya kam" "Ah haba nasan ma zaiyi mishi" "Hmmmm ba kisan waye yaya ba shiyasa kiyi shiru kawai" Haka suka nufi bedroom ɗin suna buɗewa wani sassanyan ƙamshi ya bugi hancinta, dan ita kam, Zuhura she's used to it, ɗan lumshe ido tayi, amma wannan karan batace komi ba. Kallonta Zuhura tayi "ba kice komai ba, ko nan beyi miki ba?" Murmushi tayi "yayi sosai wallahi, kamar ɗakin mace" Wani makeken Italian bed ne wanda ya mamaye rabin ɗakin, daga gefe kuma closet ɗin shine ya cinye gaba ɗaya bango, sai kuma wani guri da taga yayi kamar corridor—wai ashe prayer corner ne, gaba ɗaya tsarin ɗakin nashi yayi mata, banda sassanyan ƙamshi da take ji har cikin ƙashi da ɓargonta. Ɗakin beyi wani datti ba yar kura ce ta an kwana biyu ba a shiga ba, ta faɗa ma Zuhura. Ita kuma tace "kinsan bai cika zama ba da yake yana ɗan taɓa business duk da ba wani sosai ba, dan yafi son aikin shi akan business ɗin, kinsan babban likitan jijiya ne da ake ji dashi a Nigeria, Neurosurgeon ne, and he's one of the best Neurosurgeon here in nigeria" Allah sarki, Maryamah tace, duk da ita bata son taji ance mutum likita ne, don gani take duk likita ɗan iska ne and he's exposed to mata shiya saka ita aikin samm be mata ba. Ɗakin suka fara gyarawa, bedsheet ɗin suka canja, suka ɗauko wani fine white bedsheet mai laushin gaske suka shimfiɗa, irin mai haɗe da duvet cover ɗin nan ne, suka sanya bedsheet ɗin, sai suka maida duvet cover ɗin suka ɗora, amma shi sai sukayi folding nashi into half of the bed, haka suka yi arranging mashi 4 pillows, a ranta tace kome yake da pillows har 4 a gado oho. Bayan sun yi tidying room ɗin yayi kyau sosai, suka kunna burner suka sanya turaren wuta, mixing Maryamah tace suyi dan taga cupboard da yake ɗauke da varieties na turaren wuta a ɗakin, and different brands, duk ba irin na ƙasan nan bane—irin na su companyn Al-haramain ne da Naseem, gasu nan dai kala-kala, shine tace ma Zuhura su gwada mixing kala huɗu suji wane kalan kamshi zai bada, hakan sukayi, and alhamdulillah ya basu feedback mai kyau kam, dan wani daɗaɗɗan kamshi ya bada wanda mutum zai kasa gane wane kala ne. Mirror ɗin shi suka je suka gyara, amaki ya kusan kashe Maryamah taga abu kamar an buɗe kamfanin turare, gasu nan kala-kala irin masu muggan tsada ɗin nan, Itama saima ta rasa bakin magana, taga duk yadda takai ga son ƙamshi akwai wanda ya takata a nan kenan, saima ta fara tunanin duk wannan turaren, to shi basa saka shi mura. Haka suka gyara gurin tsaf sukayi rearranging mashi kayan dake kan badubi gwanin ban sha'awa, toilet ne kawai ya rage masu, nan fa Zuhura ta noƙe tace Maryamah ta shiga ta gyara, kada taje tayi yazo yace tayi mishi ba dai-dai ba. Haka itama Maryamah ta shiga tana ɗar-ɗar, toshi wannan wane irin mutum ne wanda komai za'a mishi ba a burgeshi, haka ta fara wanke shi a natse, tanayi tana kaffa-kaffa. Ita dai fatanta ta gama lafiya, dan wallahi in ta mishi ɓarna gara ta bar gidan, wata zuciya tace, to in kin bar gidan kije ina? Ina kika sani a Abuja?. Tana ciki tana wanki, ita kuma Zuhura na bedroom ɗin tana ta faman ɗaukan hoto da videos, gaban mirror nashi tana videos irin mirror view ɗin nan. Tana cikin yi taji an banko ƙofar, an shigo "uban waye ya buɗe part ɗin nan?" Sanin ko suwaye suke shigowa yasa bata ko ɗago kai ta kallesu ba, ba kowa bace face Nadiya, ɗiyar kanwar mom wadda ake ta so a likawa yayansu, sai yar korenta Husnah, ɗiyar mom wadda suke kusan age mate da Zuhura amma ta bama Zuhura 3 months. Ko kallon inda suke batayi ba, ta cigaba da videos nata. Gabanta Nadiya tazo "you idiot, ba dake nake ba, bakiji nace uban me kikeyi a ɗakin mijina ba?" Wani sakaran kallo Zuhura ta mata "au haba ashe ɗakin mijinki ne? Sorry ai bansan an ɗaura auren naku ba, ko kuma may be dan ba'ayi mana shelar hakan bane oho" Sakare Nadiya tayi tana binta da kallo, tana jinjina rainin wayon yarinyar, ta daɗe da gane cewa yarinyar ta raina ta, sam bata ganin girmanta, koda ba ita yayanta zai aura ba, ai ta girme mata nesa ba kusa ba. Matsowa Husnah tayi gaban ta "to uwar rashin kunya ai ko baki girmama ta dan komai ba, kin girmamata dan kasancewar ta wadda yayanki zai aura" Banzan kallo ta aika mata "au Allah? To ai sai ku jira a ɗaura, bawai ta dinga faman zarya a tsakanin gidan iyayenta da gidan nashi iyayen ba, kai jama’a, su balama dai anyi asarar kunnuwa" tayi maganar tana ƙunshe dariya. Zaburowa Nadiya tayi cikin hargowwa "ke ƙaramar mara kunya ni kike zagi?" Hayaniyar su ce ta fito da Maryamah, wadda already ta riga ta gama, ta ringa jiyo hayaniya sama-sama kamar faɗa ake yi, shine ta fito taga Zuhura ita da wa kuma? Daidai lokacin da Nadiya ta matso kusa da Zuhura ta ɗaga hannu da niyyar kai mata mari kenan, Maryamah ta fito gaba ɗaya. Kallon juna sukayi ita da Nadiya da idanuwan su suka faɗa cikin na juna wanda a take gabansu suka ji ya mugun faɗuwa. Maƙalewa hannun nata yayi, ita bata kai shi ga fuskar Zuhura ba kuma bata sauke ba, sosai gabanta ke dokawa, ta aje idonta ƙyam akan Maryamah. Wanda itama Maryaman a nata ɓangaren hakan ce ta kasance, idonta cikin na Nadiyan take mata kallon tsakiyar ido. Juyawa gurin da Husnah ke tsaye tayi, ta kalle ta tace "who is she?" Ta faɗi tana maida kallonta ga Maryamah. Husnah ta kalleta a wulaƙance "maid i guess" ta bata amsa in a disgusting tone. "Maid?"ta ƙara tambaya cike da rashin fahimta. "Eh the new maid" ta ƙara bata amsa tana banka ma Maryamahn harara, saboda itama kanta sai yau ta ƙara kallon ta ta gane ma idonta kyaun da su Adeel suketa faɗin tanada shi, ashe ta ma fi yadda suke faɗi ɗin a fili, haka kawai itama taji batayi mata ba. Wata uwar tsawa Nadiya ta buga "and what the hell is she doing in my spouse room?" Dan gaba ɗaya yadda taga yarinyar ta firgitata don kyau da diri kam tabbas akwai su a gurin, a haka ma dan bata gama cika shekarun yammatancin ta ba, sosai taji tsanar yarinyar da wani mugun kishinta, saboda yarinyar ta haɗa komai da ake buƙata na mace ga wani sassanyan kyau mai fusgan mutane gareta. "Point of correction your fiance dai ko?" cewar Zuhura, bata jira cewar taba ta ɗora "tunda ai ba'a riga an ɗaura ba, abinda kuma takeyi a nan shine gyara ɗakin shi wanda kike kira mijin naki, domin nasan in ke aka bari da gyaran ba iyawa za kiyi ba" ta bata amsa hankalinta kwance..... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/DysmUMWo6dYJlLWGBPOMEI?mode=gi_t https://chat.whatsapp.com/JHxZP3j1IIr6O5UZj4Csq5?mode=gi_t ✨🦋 RANTSATTSEN RABO 🦋✨ BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️ & AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️ FULANI ❣️ 08082101373 ✨🦋 RANTSATTSEN RABO ✨🦋 PAGE 1️⃣9️⃣ Kauda tunanin ta tayi a ranta, ganin tuna ta ma ƙara ɓata mata rai yake bata san dalili ba, amma ita kam zata iya cewa bata taɓa jin irin wannan ƙin wata halitta a rayuwanta ba, gani take gaba ɗaya ma bata da mamora. Ajiyeta tayi a gefe, tama Aisha flashing sai kam ga kiranta ya biyo baya. Tana ɗaga wayan ta, ta fara "ayita kiran mutum, amma bazai dauka ba" Cikin dariya Maryamah tace "Aifa ke baki ba mara ɗa kunya" Dakatawa Aisha tayi da masifar "Ban gane ba" Cikin dariyar tace "Daman nace zansha masifa tunda naga tarin miss calls naki, sai gashi kina kira da abinda kika fara kenan" "Yanzu shedan da kika mini ma kenan?" "Ba wani shaida, halinki na faɗa ai" "Nagode sai anjima ma an fasa hiran" Cikin sauri ta katse ta "haba tawan" tana jiyo murmushin Aishan. "Ai indai yaudara ce, an barmiki kayan ki, duk wani mai sweet mouth bayanki zai biyo" Dariya sukayi gaba ɗaya, bayan sun tsagaita ne Aisha tace "ya garin shugaban ƙasan ne? " "Hmm gamu nan a cikin shi, har yau na kasa sabawa da garin sahiba" "Haka nan zaki cigaba da daurewa zaki saba, ya mutanen gidan suke?" "Hajiyan da nake tare da ita bata da matsala, damuwata masu aikinta guda biyu sukam bansan mena tare musu b, basu da aiki sai habaici da ƙananun maganganu" "Baki cimin uwar su ba?" "To uwar rashin haƙuri, meye amfanin faɗan nikam? Me lokacin su ma banda lokacin shi balle su ɗin da kansu" "Miskila kafi mahaukacin kare ban haushi" A'isha tayi maganar da murmushi a muryarta. Murmushi tayi kadan, tace zakiji dashi ke kam. Maryamah tace "yawwa sahiba wai kinsan mene?" "A'a meyafaru?" "Hmm na baki labari wani yayansu sune kinji yanda suke kuranta shi, amma in kinga wadda zai aura sai takaici ya kusan kasheki, dan gaba ɗaya sai kin raina ma ajin shi da komai ma da akace yanadashi" Cike da mamaki A'isha tace"Ikon Allah kinganshi ne da har kika gane macen bata dace da shiba?" "Ko ban ganshi ba yanda suke faɗin shi da tsarin shi, Allah nidai dana ganta na raina mishi, kuma Allah gani ɗaya na mata naji bana sonta samm a raina" Ta faɗa tana ɓata fuska. Dariya Aisha tayi "Yau naga ikon Allah toh waini shatutu, ina ruwanki dashi da matan da zai aura?" Jin Aisha na mata dariya ya sa a ƙugule tace "Au mahaukaciya ma kika

Chapter 7 of 9