Share this page
6 / 9
kallo ɗaya nayi mata naji na tsaneta" Dije tace "Hmmn ke kike faɗima wani naji" Haka sukayita yi da ita, wanda ita batama san sunayi ba. Kusa da Iya Lami taje tana faɗin "Iya, nagama sai kuma me" Iya tace, "Kije kawai kiyi wanka, sai kici abinci ki huta kafin anjima in za ayi ma Hajiya wani aikin, ki wuce da abincinki kuma" ta faɗa tana nuna mata inda ta aje mata abincin. "Nagode sosai iya" Murmushi Iya tayi a fili a ranta kuma tana yaba tarbiyyan yarinyar da natsuwanta, duk da dai daga ganinta zatayi miskilanci..... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t ✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨🦋 BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️ FULANI ❣️ 08082101373 PAGE 1️⃣4️⃣ Ɗaki ta wuce tana shiga babanta ta fara kira Suka gaisa, tambayar ta yayi sabon waje, jin zatayi mishi kuka, yace ta bari zai kirata anjima, Duk da haka saida ta share ɗan guntun hawaye sannan ta tashi ta shiga wanka. Bayan tayi wankan ta zauna ta shirya sannan tayi zaman yin karin kumallo, bata wani ci sosai ba duk da abubuwan sun yi daɗi kuma wasu ma yau ta fara cin su, haka ta tashi ta maida sauran kitchen. "Badai har kin ci ba?" Cewar iya ganin ta dawo da kusan rabin abincin. "Eh Iya naƙoshi alhamdulillah" "Toh ai bakici da yawa ba, ko ba ki sonsu ne a baki wani abun?" "A'a nagode ya isheni" Aishikenam daga haka ta ci gaba da aikin ta. Kallon iya tayi tace "Maizan taya ku dashi?" "Ai da kinje kin huta kin sha aiki" "A'a, ai zaman ba daɗi ne" tayi maganar cikin sanyinta. "Haka ne, kuma to ga kayan lambu can ki wanke, sai ki gyara su" Amsa tayi tana nufan inda kayan suke, ta ɗauka ta nufi famfon da ta gani cikin kitchen (sink), kunnawa tayi ta wanke su tsaff, sannan ta nemi waje ta zauna ta fara aikinta cike da tsabta, duk abinda take iya na hankalce da ita kuma ta yaba ma tsaftarta. Haka ta gyarasu, ta yanka su gwanin ban sha’awa, suna cikin aikin ne, mamy ta kira iya a landline ɗin kitchen ɗin tace ta turo mata maryamah. Bayan iya ta aje wayar tace, mata ta aje abinda take, taje hajiya na kiranta. To tace, ta wanke hannunta tana nufan ƙofar fita daga kitchen ɗin, yayinda su dije da Sahura suka bita da ido suna magana ƙasa-kasa da gani dai gulmanta suke yi. Girgiza kai iya tayi tana jiran azo gabar da zatayi masu magana, dan taga kamar zasu hade ma yarinyar kai. ★★★ Da sallaman ta ta shiga parlour, ta samu hajiya da malam Sale zaune, cikin hanzari ta ƙarasa gare shi tana faɗaɗa murmushin fuskanta, dan ganin shi take kamar wani ƙani ko yayan mahaifinta. Shima da murmushi a fuskar shi yake tsokanar ta cike da jin daɗin ganin ta "inyee kaga maryaamah babanta" Wani murmushin ta ƙara saki tana ƙasa da kanta, kusa da ƙafarshi ta zauna "Baba ashe kaine kazo ina yini?" "Lafiya lau, alhamdulillah, Maryamah ya baƙunta?" Alhamdulillah kawai tace mishi. "Nasan ai kunyi waya da babanki ko?" "Eh yace ma zai ƙara kirana" "Da kyau daman zuwa nayi muyi sallama, yau zan wuce gida" Sosai ta ɓata fuska "ayya baba tun yau" taff idonta ya ciko da hawaye. Mamy dake gefe tace, "Kedai Allah yayi miki arhar hawaye" Ƴar dariya malam yayi yace "ai indai Maryamah ce, zaki gaji da gani, dan farin ciki ma ita kuka take mishi" Da haka ya mike "Toh hajiya ni zan tafi, duk halin da ake ciki sai a sanar dani ta waya, gata nan in tayi ba daidai ba a tsawatar mata dan Allah" Cike da dattako ta bashi amsa "Bakomi wallahi ni nama yaba da natsuwanta wallahi tun jiya, Sannan maganar makaranta, ina ganin zamu bari first term sai a akaita, tunda kaga yanzun muna 3rd term ne, kuma ba a da6de da shiga ba, Idan yaso sai a saman mata JSCE certificate, sai ta jona SS1 kawai" "Shikenan ba laifi hakan ma mun gode, Allah ya ƙara girma" Kuɗi ta bashi tace yayi kuɗin mota, sannan in ya koma sunyi magana da mahaifin Maryamah, sai su faɗi a inda ya kamata a ringa sanya mata kuɗin aikin. Tohm inshaa Allah zaiji da haka ya fita yana ƙara mata godiya, Ita kuma Maryamah tana biye dashi. Saida suka fita farfajiyar gidan, sannan ya tsaya ya juyo yana kallon ta, tsaya daga nan ba sai ta kaishi da nisa ba, gidan nada faɗi, kada ta dawo ta rasa inda zata shiga. Kallonta yayi yace, “To Maryamah, kinga inda rayuwa ta kawo ki, ina fatan kiyi amfani da damarki ta hanya mai kyau, ki zauna da kowa da zuciya ɗaya, sannan ki kauda kanki daga duk abinda be kasance naki ba, sanan banda rawar kai duk da daman ban sanki da ita ba, sanann ki tsare mutuncin ki kinji, koh kuma ki cigaba da muraja’ar karatunki, nasan in Allah ya yarda, hajiya duka zata sanya ki islamiyya da boko" "Inshaa Allahu baba zanyi amfani da duk shawaran da ka bani, bazakaji wani labari mara daɗi ba daga gareni, zanyi abun6da ya dace" tayi maganar tana share hawaye. "Yauwa ki kwantar da hankalinki, kinji koh, kidena ƴan koke-koken da kike kisa a ranki, dan kwanciyar hankalin mahaifinki kema zaki kwantar da hankalinki a nan har ki cimma nasararki ta rayuwa" "Inshaa Allah baba nagode, Allah ya kiyaye hanya ya kaika gida lafiya" Ameen ya amsa yana miƙo mata kuɗi cikin envelope. "A'a, ba abinda zanyi dasu ai" "Ki riƙe saboda tsaron lalura" Bata son musu da shi shiyasa ta amsa tayi mishi godiya. Albarka ya kuma saka mata. Haka suka rabu ta juyo ta koma cikin gidan, shi kuma ya kama hanya driver zai kaishi ta sha. Koda ta shiga bata samu mamy a parlour ba, sai kawai ta nufi ɗaki ta ajiye kuɗin hannunta, ta kama hanya ta koma kitchen. Da sallama ta shiga tayi musu sannu da aiki. Tsaki su sahura suka ja mata kasancewan Iya ta fita backyard na part ɗin tana wani abu. Ganin haka sai bata bi ta kansu ba, ta nemi waje ta zauna tana jiran iya ta dawo, tana nan zaune, tana jinsu suna habaici, bata tanka masu ba saboda ita dai bataga abinda tayi masu ba daga zuwanta jiya-jija. Suna cikin haka, Iya ta shigo, sai duk sukayi shiru. Iya tace "Maryamah har kin dawo?" "Eh" daga haka taja bakinta ta tsuke, ba tare da ta faɗi dalilin kiran da akayi mata ba, wanda su Sahura suka zuba kunne suna jiran suji, Ita kam kamar ta sani, sai bata faɗa ba, daman can tana da zurfin ciki, bata da yawan magana, sai in tana tare da babanta ko sahibar ta. Haka suka cigaba da aikin Iya na bata yan abubuwa masu sauƙi, saboda tasan ba abinda aka ɗauke ta tayi ba, wanda hakan ma ba ƙaramin baƙin jini ya ƙara jawo mata ba, wajen su dije suna ganin kamar Iyan na fifitata ne kan su, dan dai basu samu damar faɗawa wa Iyan ba. Bayan an gama komai su sahura suka ɗauka suka jera a dining, wanda daman kula da table ɗin na ɗaya daga cikin aikin su, sannan suka fitar da nasu, dana sauran masu aikin part ɗin maza da kuma security dake gate, duk da su acikin albashinsu ake fitar masu da kuɗin abinci, amma mamy tace a ringayi da su ana basu. Hakan kuma ya jawo suke matuƙar ganin girmanta fiye da matar ɗayan apartment ɗin, wanda kuma ya ƙara jawo mata mummunar tsana a gurin abokiyar zaman nata, dan tana kallon hakan a matsayin munafunci da kinibibi. Bayan sun gama komai, d6aki suka tafi da abincin su. Ita Maryamah ta ɗauki nata dana Iya su kuma su Sahura suka ɗauki nasu, suka nufi nasu kofan, a haka ma saida Sahura ta bangaji Maryamah, dan ita tafi jin tsana da ƙyashin Maryaman akan dije, sabida ita Sahura irin mutanen nan ne masu so su zama sune na farko, ko a guri suna so afi yabon su akan kowa, wanda zuwan Maryamah daga jiya zuwa yau taga kamar ita Maryamah ce zata samu duk wanna abubuwan da taso, ace ita ce keda su. Sannan uwa-uba baiwar kyan da taga Allah yayi ma Maryamah, wanda yanzun babu ne ya ɓoye shi, amma tasan nan da wata biyu zuwa uku, yaro6nyar zata iya sajewa da yan gidan a ringa ganin kamar itama yar gidan ce, abinda bazata taba fata ba kenan, wata tazo daga bayan su ta fisu samun shiga, sannan gashi da alama yarinyar bata da irin duhun kan da sukazo dashi, dansu sunfi shekara kafin su fara gane kan komai. Girgiza kai kawai Maryamah tayi a ranta tana ayyana tofah! nanma ashe akwai wani ƙalubalen, amma a zuciyar ta tana jin nasu mai sauƙi ne tunda ba zaman su take ba akan nasu Baba Zainu, tuna hakan ne yasa ta faɗin Allah sarki koya suka ƙare? Oho, koya Hajja zatayi in ta dawo taji tabar garin? Allah sarki, Zainab da Muktar ina kewan ku. Ɗaki ta wuce ta ajiye ma Iya nata abincin, itama ta ajiye nata, ta shiga ta ɗauro alwallah tazo ta kabbara sallar azahar kasancewan lokacinta yayi, bayan ta idar, ne tadan tsakuri abincin, da ita bata saba da wannan cimar ba, Kishingiɗa tayi daga nan bacci ya ɗauke ta saboda har lokacin da gajiyar tafiya a tare da ita, ga kuma yau ta sha aiki, ba laifi......... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_thttps://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t ✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨ BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️ & AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️ FULANI ❣️ 08082101373 PAGE 1️⃣5️⃣ CHARANCHI Tashin hankali na gidan duniya, malam jafaru ya shige shi, sanda ya koma gida, ya samu Hajjah nata surfa bala'i, ta inda shiga bata nan take fita ba, tace saboda ya rainata zai ɗauki yarinya, yace ya bar gari da ita, to gidan ubanwa ya kaita? duk inda ya kaita ya je ya dawo da ita, haka ta dinga uwar masifa, ta maƙi tsayawa ta saurare shi gaba ɗaya. Da yaga abun bana ƙarewa bane, sai ya fita ya je gidan kawun Hajjan, wanda shi kaɗai ya rage mata, kuma tasan yafita masifa, sannan ko bata so haka take jin maganar shi, da yaje ya same shi ya faɗa mashi abinda yake tafe dashi da kuma dalilin shi na barin garin da maryamah. Nanfa kawu lawalli ya fusata, "muje gidan na sameta, ashe Ramatu bata da hankali har yanzun ban sani ba, ache da ita za'ayi ma jikarta wannan mugun ƙullin kai, tirrr da halin Ramatu" faɗa yake haɗi da mamaki duka a lokaci ɗaya. "Baba ni so nake kawai ka tsawatar mata akan cewar da tayi, sai na maido Maryamah ko ta tsine mani albarka" yayi maganar cike da takaicin abin da mahaifiyar tashi tayi mishi da shi da ɗiyar shi. "Shikenan kaje zanzo gidan yanzun" Bayan tafiyan Malam Jafaru, ne Kawu Lawwali yabi bayan shi. Yana zuwa a ƙofar gida ya sameshi dan shi har ga Allah zullumin shiga gidan yake, bai samu ƙwarin guiwar shiga ba saida Kawu ya iso, yayi mishi jagora, suka shiga da sallama, har Hajjah ta fara masifa, amma ganin wanda ke bayanshi ya sanyata haɗiye abinda tayi niyyar cewa. Ita kanta Zainu tasha jinin jikinta don tasan Kawu Lawwali tsaff zai zagesu, ita da Hajjan da take goya mata baya, dan Kawu cikakken bakatsine ne, ya zagesu ya kuma tsine su tass. Tabarma Hajjah ta shimfida tana faɗin, "Kawu kaine tafe?" Yace "Eh, nine tafe, tunda kin uzzura ma ɗanki kin sashi dole ya isko ni a gida ya min bayani, anya kuwa Ramatu ashe bazakiyi hankali ba?" Ya faɗi yana karkatar da hula, wanda tasan da taja magana tayi tsayi ƙarshe, zai zageta ne tass a gaban ɗanta da suruka, shi ba abinda ya dameshi. Shiru tayi tana hararar baba dake gefe, karaf a idon Kawu, aikuwa ya fara sababi "Ai ni ya kamata ki harara ba shiba Ramatu, ko kuma ki tashi ki rufeni da duka" "Kayi haƙuri Kawu" "Duk ba wannan ba, Jafaru yazo kuma ya faɗa min duk abinda yafaru, ni na amince da hukuncin shi, dan haka ni nace a can yarinya zata zauna, kuma kada in karajin an tada zancen, In kuma ba haka ba, rayuka zasu ɓaci aci, ke kinsan halina" "Shi kenan Kawu, anbar maganar baza a kara tada ta ba" "Tom dai yafi miki" Da haka yayi masu sallama, Malam Jafaru ya rakashi yana godiya, shi kuma yace dashi duk lokacin da ta kara tada maganar, yaje yaa sameshi, in yazo sai ta gwammaci ta haƙuran kamar yanda ya bukata a farko. Da haka ya samu magana ta mutu, amma Hajjah na fushi dashi bata dai ce mishi komi ba. ★★★★ Bacci sossai Maryamah tayi, dan har kusan 4, sannan ta tashi tayi sallah. Iya ta tambaya koda abinda za'ayi. Amsa ta bata da a'a bakomai, dan yau ma Hajjah tace ba sai an ɗora girkin dare ba. Toh tace daga haka ta ɗakko littafinta na makaranta tana bita, har 5 tana nan zaune, Aisha ma ta kira, sun gaisa har suka gaisa da Umma, ta ƙara mata nasiha akan ta kwantar da hankalinta, Ita tama rasa abinda zatayi, saboda ta saba inda gida ne, da yanzun tana islamiyya, dan tana dawowa boko ƙarfe 2 tayi abinda zatayi, 4 ta tafi islamiyya, sai kuma 6. Tunanin gida ta dingayi, a haka ma sai da taji tana kewan masifan Baba Zainu da Hajjah Tana nan zaune, taji an shigo ɗakin da sallama, ɗagowa tayi tana amsawa, taga Fudail ne da Fadil, ashe har sun dawo, shine suna cire uniform sukayo gurinta. Da murmushi a fuskarta tare su "Yammakaranta an dawo?" "Mun dawo cutie, Shine bakizo kince mana oyoyo ba" "Eyya kuyi haƙuri to gobe zanzo nayi maku, ai kunga bansan time ɗin da kuke dawowa ba" Fadil yace "5 muke tashi sanda zamuzo gida 5:30, saboda akwai ɗan nisa, kuma kinga yamma in tayi Abuja akwai hold up" Murmushi tayi "A'a aini bansan Abuja ba, kaga bazansan akwai hold up ba" Suma duk murmushi sukayi suna cewa "Kizo muje main parlour please" suka faɗa suna haɗe hannunsu waje ɗaya. "A'a kuje dai ai kunzo mun gaisa" Ƙara haɗe hannayen su sukayi "Please please" Fadil ya kamo hannunta, wai ta miƙe yana please Da haka suka rinjayeta tace shikenan, muje to. Haka suka sanyata a tsakiya suka fito ɗakin, a bakin ƙofa suka samu su Sahura suna masu laɓe, ɗauke kai yaran sukayi, duk da basu da raini, amma Samm sudai Dije da Sahura basuyi masu ba, musamman Fudail da yake miskili shi daman ba kowa yake birge shi ba Shi ya sanya ita kanta Mamy tayi mamaki da taga har dashi cikin masu ɗokin Maryamah. Wuce su sukayi da yake itama Maryamah gwana ce wurin shariya, suka nufi parlour. Anan suka samu Mamy zaune tana waya, bayan ta katse tace mata, "Barka da yamma Hajjah" Tana duƙawa ƙasa. Fadil yayi saurin cewa, "Mamy not Hajjah" Murmushi tayi kawai. Mamy tace "Toh kinji abinda Fadil yace?" "Tom inshaa Allah mamy" Zama sukayi, suka sanyata a tsakiya suna mata surutun makaranta. Ita Mamy ma mamaki, Fudail ke bata yaron da beda yarda, amma shine ya saki jiki da Maryamah da ya sani jiya jiyan nan. A haka Zuhura ta sauko, tana sanya riga da wando irin yan Turkish din nan, masu taushi da ɗaukar ido, kanta sanye da hula ta cusa gashinta ciki. Bayan ta sauko ne ta nemo guri ta zauna kusa da Mamy "wash Mamy na gaji" Banza tayi da ita, dan ita kam laziness ɗin Zuhura na bata mamaki, Ji Maryamah tun safe take aiki har kitchen, tana sane, sai da taje ta kama wa su Iya aiki bayan ta gama nata. Kallon Mamy Zuhura tayi tana tura baki tace "Mamy nace na gaji" Banzan kallo Mamy ta watsa mata tace "To sannu uwata" Jin hakan sai Zuhura ta kama kanta, Ita fa Mamy abu kaɗan ta faɗa maka, baƙar magana. Juyawa tayi ta kalli Maryamah, ita kuma tace Sannu da dawowa. Yau kam bata tsaya neman dalili ba ta amsata. Dining area ta wuce tana faɗin "Yau kuma mai muka samu a nan" buɗe warmers ɗin tayi taga duk ba abinda yayi mata, ita Mamy sai tayi ta sanyawa ana masu abinci mai nauyi, rufewa tayi kawai, ta haɗa cornflakes ta cika madara, ta dawo parlour ta zauna, ta d6auki duka kafafunta ta hau dasu kan kujera. Kallon abinda ta haɗo Mamy tayi tace, “Duk kukan yunwan abinda zakici kenan?" "Eh Mamee, ni bana cin abinda akayi" Mamy ta ɗage kafaɗa tace "nah you sabi" kawai ta cigaba da abinda take. Ita kam Maryamah tana can twins sunata zuba mata surutu, Suna nan zaune su Adeel da Aqeel suka shigo da gudunsu, suna zuwa suma dai kan Maryamah sukayi. Mamee tace "kekam kinga ta kanki Maryamah, yaran nan bazasu barki ba" Murmushi tayi tace "Ai bakomai Mamy ai yara ne" "Aikam dai dan dukkusan sa’anni ne, tunda su twins da Adeel 40 days ne tsakanin su yanzun suna 8, sai Aqeel ne karami dake da 6 yanzun" "Mashaa Allah, Allah yayi wa rayuwarsu albarka" Mamy ta amsa da Amin......... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t 🦋✨ RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨ BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️ FULANI ❣️ 08082101373 PAGE 1️⃣6️⃣ Ana kiran magrib mamy tace su tashi suje suyi alwallah su wuce masjid, idan aka dawo kuma yau baza'ayi hira ba saboda gobe zasuyi aiki sossai da maryamah, za'a gyara part ɗin daddy dana su Sadeek tunda jibi asabar ake sanya ran zasu dawo daga umrah. Sunajin ance daddy zai dawo, suka fara tsallen murna da gudu suka haura sama dan yin shirin masallaci. Bayan tafiyan su mamy ta kalli maryamah tace "kamar yanda kikaji gobe insha Allahu Alhaji zai dawo da shi da sauran yaran mazan gidan nan, dan haka kiyi bacci da wuri, aiki garemu sosai daga gobe" "inshaa Allah" Zuhura ce tace "Mamy tabar gyaran part ɗin Abba dana yaya sai na dawo na tayata mu gyara" "Hakan na yayi babu wani abu" Watsewa sukayi, kowa ya kama gaban shi suka nufi yin sallah. Bayan ta shige iya tayi wa sannu da hutawa. Amsawa tayi tare da tambayar ta, ta dawo. Kanta ta gyaɗa mata. Bayan sunyi magrib da isha'i, tana zaune kan prayer mat, Iya tace yau bazakije ki taya mutanenki hira bane. "Yau hajiya tace musu ai baza'a yi hira ba saboda gobe zamuyi aiki sosai, tace megidan da yaran gidan maza zasu dawo" "Ƙwarai kuwa anyi haka, gobe kam akwai aiki, kinsan yaran su 5 ne manya maza, Ita hajiya nan tanada biyu, ita kuma uwargidan tanada uku" "Allah sarki" kawai tace dan bata san mai kuma zata ce ba. Iya ta cigaba da faɗin, "Fatana ki samu karɓuwa kamar yanda kika samu a gurin ƙananun yaran, koda yake babban nema mai wahalan sha’ani, duk da ba magana yake ba bashi da hayani, amma dai yaran gidan na matuƙar tsoron shi da kuma girmama shi sosai, gaskiya dan zance bayan Alhaji to shine mai zartar da hukunci, kuma duk abinda ya yanke shi kenan, shiyasa dole sai kinyi takatsantsan" "Inshaa Allah Iya nagode sosai, Allah ya kara girma" Da fargabar dawowar sauran yaran gidan maza, ta kwana tana tunanin ko ya zasu kaya, itadai Allah ya sani bata son wulaƙanci, amma dai zata ci gaba da addu'a. ★★★ Yau ma kamar jiya haka ta tashi tayi sallah da azkhar ta karanta shafi ɗaya kawai saboda tasan yau sunada aiki, gashi tana so ta fara da wuri, Iya ta gaida kawai ta ɗauki hijab ɗin da take aiki dashi ta sanya, ta ninke wanda tayi sallah dashi ta fita main parlour na gidan ta fara aikinta. 6:30 har ta gama gyaran parlourn ƙasa, ta haura sama ta fara gyarawa, Shima 7 ta gama ta sanya room freshener da turaren wuta. Tana cikin sakin curtains ɗin, mamy ta fito, duƙawa tayi ta gaisheta, ta amsa tana faɗin, Wai har kin fara aikin kenan. "Eh, na gama da ƙasan nace bari na fara nan kafin ki tashi" "Mashaa Allah, sannu da ƙoƙari" tayi mata sannun cike da jin daɗi. Amsawa tayi da yawwa kanta a ƙasa. Ɗakin su Fadil mamy ta wuce tana so taga in sun shirya dan time na tafiya, Ita kuma Maryamah ta nufi ɗakin mamy ta gyara mata. Koda ta gama gyaran ta fita har yaran sun gama breakfast, sun wuce school da Zuhura. A ƙasa ta samu mamy tana zaune a parlour tsugunnawa tayi tace "Mamy na gama sai ina za kuma ayi?" Albarka ta sanya mata "Inaga za'a fara da part ɗin su sadeek ne, kuje dasu sahura su kama miki kowa ya gyara ɗaki daya, guda huɗu ne, daga nan idan kun gama zuwa anjima in baby ta dawo sai ku gyara na Alhaji da na babban yayansu" Harta miƙe mamy tace ta jira su sahuran suzo. Waya ta ɗaga ta kirasu akan su sameta a main parlour, cikin ƙasa da minti 5 suka ƙaraso, amma ganin Maryamah already a wurin ya ɓata ransu dan sunso ace su kaɗai ta kira, Ce masu tayi su haɗu da Maryamah, suje su gyara part ɗin su Sadeek, da to suka amsa suna miƙewa gaba daya. Kallon maryamah tayi "kijira na kawo miki keys ɗin part ɗin da ɗakunan su" Sama hajiya ta haura inda tabar su sunata hararar Maryamah da ƙananun maganganu. Ita dai bata bi ta kansu ba, haka suka wuce kowa da mugun nufi a ranshi. Bayan tafiyar su mamy ta sakko ta bata keys ɗin, ganin bata ga su sahura bane yasa ta tambaye ta suna ina. Sunyi gaba kawai tace mata. "Ok idan kika fita part ɗin nan ta gefen hagu, zaki ga wani part ba ginin bene ba, zakiga ƙofa ta kasu biyu ta hagun ita ne ta part ɗin su Faruk, shi na yayansu anjima zaku gyara da Zuhura.” Data fita a bakin ƙofar part ɗin da mamy tace mata nasu Sadeek ne taga su sahura suna tsaye sun cika fam… tana zuwa suka hau masifa, wai ta shanya su. Ita dai cikanku bata ce masu ba, taje jikin ƙofar ta sanya key ɗaya ta fara gwadawa tana so taga wanda zai buɗe a cikin su. Koda ta samu na ƙofar murzawa tayi ta buɗe ta shiga, tana zare sauran keys ɗin ta shiga dasu. Bin bayanta sukayi suna sakin tsaki, da suka shiga nan ma ƙara gwada keys ɗin tayi har ta gane na ɗakunan ɗaki 4 ne a ciki, biyu hagu biyu dama, duk buɗe su tayi, ta kalli su Dije da suka nemi kujeru, suka zauna kamar ɗakin uwar su akuyar kulle ta samu sake. "Bismillah, zamu iya farawa" Sunajin haka suka yo mata caaa da masifa "Toh uwar iya ai da yake kinfimu sanin abinda ya kamata" "Allah ya baku hakuri" ta katse su tana shiga ɗakin dake farko, tana shiga ta fara gyarawa duk da ba wani datti yayi ba, amma ya ɗanyi ƙura kaɗan, tsaff ta gyara shi cikin ƙanƙanin lokaci, ta canja bedsheets, ta wanke toilet, sai ta sanya room freshener ta kullo ɗaki. Parlour ta dawo nan ma ta gyara, time ɗin su ba wanda ya gama gyara ɗakin da ya shiga har ta gama gyaran parlourn, basu fito ba aranta tace, Komai suke oho. Su kam ashe suna sane suka ƙi fitowa suka barta da aikin. Ɗayan ɗakin ta shiga kawai ta gyara dan bata ga amfanin tsayawa jiran su ba. Suna jin shiganta dayan ɗakin sai gasu sun fito, daman sun gama kawai basa so su fito ne su gyar, koda suka fito basu tsaya jiranta ba, tafiyan su sukayi hankali kwance. Bayan ta gama ta fito taga basa nan, rufo ɗakunan tayi ta fito, tana cikin rufe part ɗin ne wata hamshaƙiyar mata ta ƙaraso wajen cike da izza, da ganinta zatayi rashin mutunci, duk da ba a shaidan mutum daga ganin farko, bata san dalili ba amma sai taji samm matar batayi mata ba. Ƙarasowa wajen tayi "Ke ubanwa, yace ki buɗe gurin nan" tayi

Chapter 6 of 9