ba Maryamah mamaki, ita bakinta da kanta baya mata ciwo matar nan kullum in ta fara masifa tun safe har dare, kai ita kam kodan kunnuwata su huta ma taji ta amince da barin gidan nan, haba ayita abu ɗaya kaman cin ƙwan makauniya.
Da wannan tunanin ta ƙarasa ƙofar ɗakin babanta tayi sallama, bata shiga ba sai da taji ya amsa yace "Shigo Maryamah"
Shiga tayi da wata gajeriyar sallama a bakinta, zama tayi kusa dashi tace "Ina kwana baba"
"Lafiya Ya kwanan fargaba?"
Ɗan murmushi tayi tace "Ai banyi ba baba"
"Anya kuwa? Idon nan naki ya nuna har kuka kinyi"
wasu hawayen ke shirin zubo mata, tana mai ƙarajin soyayya da tausayin babanta a ranta domin tasan shi kanshi ƙarfin hali yakeyi, a zuciyar ta take jinjina soyayyar mahaifin nata, shidai daban yake daga shigowar ta ya gane cewan har lokacin tana cikin dmauwa, har ma da kukan data kusan kwana tanayi, ita ko waccan baƙar matar da alama ba abunda ta fahimta, saima tuhumar ta da take akan taƙi ta fita ta mata bautan da ta saba ba tare da uzuri ba.
Haka ta zauna sukayi yar maganar da zasuyi.
"Nasan bakici abinci ba?" Ya tambaye ta yana kallon fuskar ta.
"A'a baba naƙoshi"
Murmushi yayi ya miƙa mata nashi "ga nawa nan kici babarku nasan bai zama lallai ta baki ba saboda yau baki fito kin mata aiki ba"
Cike da tausayin shi tace "A'a baba kaci nina ƙoshi"
"Karki damu kici ni yau da azumi ma na tashi na neman Allah, yasa inda zaki ya zamar miki alherin rayuwa duniya da lahira"
Cike da jin daɗi ta amsa da "Ameen babana"
Badab ranta naso ba saidan ta faranta ran mahaifin nata, ta ɗan tsakuri ɗumamen kaɗan ta kora da ruwan koko.
Bayan ta gama, baba ya kalle ta yace "Har yau baki tambayeni dalilin da yasa nace kibar gari ba?"
Ƙasa tayi da kanta tace "Ka isa ne babana, kuma ko wane hukunci ka yanke akan zinariyarka daidai ne, ita ɗin me biyayya ce gareka" Murmushi yayi yana me ƙarajin tsananin ƙaunar ɗiyar tashi da kuma tausayinta mai girman gaske akan biyayyar ta gareshi, rauni ne ke mamaye zuciyan shi amma yana ƙoƙarin karfafa ta.
Yace "Nagode ma Allah da wannan baiwar da yayi mani ta yarinya, ma tsananin biyayya gareni, Ina rokon Allah kema ya baki waɗanda zasuyi miki biyayya kamar yanda kike min Allah ya shiga cikin al’amarinki, ya kula min dake"
A zuciyarta ta amsa da amin.
Ya ciga ba da cewa, "Allah yasa inda zakije ya kasance kinsamu rayuwa wadda baki samu ba a nan, ki dage da addu’a, ki riqe mutuncinki, ki kama kanki, Inshaa Allah zakiyi rayuwa wadda tafi wadda kikeyi a nan, a jikina nake jin inda zaki rayuwarki zata inganta kamar yanda nake mafarki da fata"
"Allah yasa babana, amma zuciyata zata kasance cikin kewan abunda tafi ƙauna da muradi"
Murmushi yayi yace "Da taji tana muradin babanta ta kirashi a waya, shiɗin zai kasance mai karfafa mata guiwa har ta cimma nasara a rayuwa..."
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️ & AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI) ♥️
FULANI ❣️
08082101373
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
PAGE 9️⃣
Kasancewar baya son hankalin zainu ya dawo kansu balle taji ko da kaɗan ne daga shirin su, duk da ma komai yazo ƙarshe, amma so yake ya shayar da su mamaki daga ita har Hajjah, domin so yake sai sun fito zata tafi kawai suji labari, dan yasan lokacin zasu tabbatar da ya shammace su, Shi ya sa yace mata ta tashi taje ta cigaba da shiryawa, shi zai je wurin Malam Sale yaji tafiyar tana nan karfe goma ɗin ko kuwa, dan shi hankalin shi ba zai kwanta ba sai ya tabbatar da ta bar garin.
Da toh ta amsa mishi ta miƙe suka fito kusan tare.
Dogon tsaki Baba Zainu taja cike da masifa tace "Aini ba za'a burgeni ba sai naga ka maidata ciki sannan zan tabbatar da girman son da kake mata, aikin banza kawai"
Girgiza kanshi yayi ya ficewar shi ya barta tana ɓaɓatu ita kaɗai domin Hajjah har lokacin bata fito ɗaki ba.
Itama ma Maryamah hanyar ɗakin ta tayi, dan da gaske take yau bata da lokacin matar, in kuma ta buɗe bakinta akan ta tofa abunda zai fito daga bakinta ita kanta sai tayi danasanin tankawa balle kuma ita baban, cire kayan jikinta tayi ta ɗaura zani ta fito zata shiga wanka, amma yanda ta samu bayin takaici sai da ya kusan sakata kuka, domin kaca-kaca haka yayi saboda yau batayi sammakon wankewa ba kuma ba za'a samu wani ko Zainab ta sanya ruwa ta kora dattin ciki ba, saida ta tsaya ta wanke bayin tass sannan ta shiga wankan, Bayan ta fito ta shirya cikin atamfarta ta sallah mai sauƙin kuɗi, kasancewar su masu rangwamen ƙarfi, amma duk da haka babanta na iya bakin ƙoƙarin shi wurin yi mata sutura, saboda yace ai macece ita kuma mace sai da sutura domin sutura ita ce mutum, haka ta shirya tsaf abunta kuma tayi masifar kyau duk da damuwar dake cin ranta, a hakan be hana kyawunta fitowa ba. fuskarta tayi fayau, kwalli ta shafa ta sanya man leɓe kasancewar bata mu’amala da hoda.
Tana cikin shirin ta jiyo sallamar Aisha a tsakar gida, inda kuma ta jiyo muryar Baba Zainu tana cewa "wai zaryar uban me ake mana a cikin gida tun jiya? Ni fa munafurci ne, bana so tunda ai ba zuwa kike ba da ko yanzun wani munafuncin ake ƙullawa yasa kiketa faman yi mana zarya"
Ƙaramin tsaki Aisha taja tayi wucewarta ɗakin Maryamah.
"Kinwa uwar ki buntalo tsaki bani ba, shegiyar yarinya mai kama da shaiɗanu"
Hayaniyar tace ta fito da Hajjah tana faɗin "Ke kam Zainu baki taɓa bari mutum ya rintsa, yanzun gidan ke kaɗai ma sai kin yi hayaniya, dan nasan dai yara sun tafi makaranta haka waccan kafurar ma yar allazee boko"
"Ina fa ta tafi? yau bansan munafurcin daya hanata zuwa makarantar da take jin ta kamar ɗakin uwarta ba, shine waccan shegiyar yarinyar ta wajen buntalo ta zo ita kuma tana nata rashin tarbiyya, kin san ba tarbiyya gareta ba daga nace wai zaryar me take mana a gida tun jiya, shine yarinyar nan ta kalle ni ta buga tsaki"
★★★
Aisha kam da shigarta Maryamah ta tareta da "uwar ƴan ɗaukar magana, gashinan kin jawo ma ummana zagi da farar safiya"
"Ke kyale karyar can tayi tayi, aita saba, ko bance komai ba sai tayi, shiyasa ma nayi mata tsakin dan tayi da hujja"
"Aikin kyauta da kika jawo magana"
Zama sukayi suna gaisawa.
"Ƙarfe nawa ne tafiyar?" "Toh baba dai yace jiya Baba Sale yace mishi ƙarfe goma amma yaje yaji abunda zai ce"
"Ai goma ta kusa" ƙara kallon Maryamah tayi tace "sahiba Allah gara ma kibar gidan nan ko kunnuwanki su huta da jin mugun alƙaba’in matar can"
“Hmmn kibari kawai sahiba, ni kaina abunda nace kenan ɗazun da ta fara" ta bata amsa tana ɓata fuska.
Suna ciki sukaji maganar Hajjah tana fadin "ni bari na shiga barka gidan azumi, jikanyarta ta haihu, daman cewa nayi in bari sai ɗagawar hantsi.
A dawo lafiya Baba Zainu ta mata tana ci gaba da aikin da take, dan yau awara take son yi tunda Hassu tace yau zata dawo, daman gidan babanta taje ta kwana biyu.
Bayan fitar baba ko minti ashirin batayi ba baba ya shigo gidan da sallama.
Banza baba Zainu tayi dashi dan a ciki take dashi.
Shima bebi ta kanta ba ya karasa ƙofar ɗakin Maryamah yana faɗin, "Zainariya in kin shirya ki fito mu tafi, Malam Sale na jiranmu"
Ai kamar da baba yake tayi saurin sakin abunda take ta juyo gaba ɗaya hankalinta na a akanshi, shi kuma yayi kamar besan da wanzuwarta ba. Mamaki be isa kasheta ba sai da taga Maryamah ta fito da jaka ta kuma sanya kayan sallarta alamar garin dai zata bari, gaba ɗaya ta ma rasa me zata ce, ƙoƙari take ta kamo bakin zaren amma ta kasa.
Bayan fitowar Maryamah da Aisha ne Aishan tana tsugunna ta gaida baba, ya amsa yace "kinzo yima ƴar uwarki rakiya kenan?"
"Eh baba"
Gaba ɗaya fa Baba Zainu ta shiga duhu, to wai me malam yake nufi ne? Yarinyar nan garin zata bari ko kuwa wani wuri zata ta dawo? Bata kai ƙarshen tunaninta ba taji muryar Malam na magana kaman ya shiga zuciyar ta.
"Toh Zainu, Maryamah zata bar miki gidan yau dai saiki sakata ki wala, dan naga kamar ta tare miki iskan shaƙa, sannan abinda nake so ki sani shine, shi sharri ɗan aike ne, yanda ya tafi haka zai dawo wa meshi, kuma ɗa dakike gani na kowwa ne ba ki san mejin ƙanki ba,ƙila ita da kike gani a wulaƙance ita ce zata ja ki zuwa gaba, kuma kin matuƙar bani mamaki akan abunda naji kuna shiryawa, nina riƙe taki ƴar da amana amma ke kin gagara riƙe tawa, ke kenan kullum cikin neman hanyar da zata tozarta, toh da izinin Allah Maryamah ba zata taɓa kauce hanya ba, kuma a duk inda take addu’ata tana tare da ita, zata tafi zata barmiki gidan kici uwar da zakici da shi"
Yana gama faɗin haka ya sanya hannu ya ɗauki jakar Maryamah yace "ku shige mu je"
Ko zarafin magana be bata ba, toh ta ina ma zata iya magana bayan tayi freezing, atoh tayi freezing mana gaba ɗaya ta daskare , abubuwa ne suka taru suka haɗe mata, na farko barin da Maryamah zatayi ma garin ba tare da ta cika burinta ba, na biyu yanda aka shammaceta akan tafiyan, sai kuma na ƙarshe wanda shi yafi komai, wato maganganun da Malam ya fada mata.
A haka suka tafi suka barta ba cikin hayyacinta ba.
Suna fita sukaga Malam Sale tsaye yana jiransu, su duka biyun suka tsugunna har ƙasa suka gaida shi, ya amsa haɗi da cewa Ah ƴan uwan juna anzo sallama ne, kasancewar duk inda ya gansu haka yake ce masu domin sun riga da sun zama ƴan uwa tun haihuwarsu.
Rankayawa sukayi suka nufi titi suka tsaida mai ɗan sahu da zai kai su tasha, Suna cikin tafiyan ne Malam Jafaru ya ciro wayar shi daga aljihu yace "Maryamah bari na baki wannan wayar, ni in Allah ya buɗe sai na siya wata"
Zatayi magana Malam Sale ya rigata "A'a ka bari kafin mu isa tasha sai a tsaya a siyan mata tata itama, saboda kaga nace maka Hajiya ta turo da kuɗin mota kuma abunda ta turo dashi zai isa a siyan mata, har kaima a baka wani abu ka rike a hannunka"
"Wai saida ta turo ɗin? Ni fa wallahi ba dan kuɗi nake son tafiyan Maryamah ba" cewan Malam Jafaru.
Shima Malam Sale yace "Toh tunda ta turo ai ba za a maida mata ba" Da haka yace ma mai ɗan sahun, dan Allah in sun je bakin tasha ya tsaya wurin shagon wayoyin nan.
Da isarsu wurin aka tsaya suka fito, da zasu shiga ta kalli Malam Sale kamar zatayi kuka tace "Baba dan Allah a siya da Aisha, in kuma kuɗin ba zasu isa ba a siyan mata ita, ni inna je in ina son magana da ku sai in ara waya na kiraku"
Cikin sauri Malam Sale yace "A'a zasu isama in Allah ya yarda, ai dubu hamsin ta turo Hajiyan" Haka suka shiga aka zabar masu wayoyin keypad guda biyu aka faɗa musu kuɗin suka biya, haka suka tsaya aka siya layi aka yi masu register, sim din be zama set ba suka tafi amma su duka sun rubuta lambar junan su a paper. Ita Maryamah daman ta haddace ta babanta duk da ba wayan kiran shi gareta ba a lokacin.
Da isar su tasha sauran mutum huɗu ake jira motar Katsina ta cika, kasancewar ita zasu hau domin daga Charanci ba a samun motar Abuja direct, dole sai kaje Katsina.
Haka suka shiga gaba ɗayan su, Ita batama yi tunanin su baba zasu raka su har Katsina ba, amma taga sun shiga motar ai a take farin ciki ya kama ta, cike da jin daɗi tace "Baba har can zaku kaini?"
Yace "Kwarai kuwa har sai mun ga tashin motar ku" Ai tuni hawayen farin ciki suka zubo mata, tasa bayan hannu ta goge su tana faɗin, "Nagode babana" Kukan ya isa haka, kin san kinada ciwon ido" yana magana yana share mata sauran hawayen.
Bayan isarsu Katsina haka suka ƙara shiga wani ɗan sahu ya kaisu KTSTA inda zasu hau motar Abuja, duk da ƙaramar mota zasu hau ba KSTA din ba, amma a can anfi samun motoci masu aminci. Da sukaje din ma can cikin sa’a mutum biyu ake jira, ai fa suna zuwa aka ce su shiga.
Ita kam Maryamah ganin da gaske fa daga nan zasu rabu da babanta yasa ta fara hawaye, yana rarrashinta da ƙyar ya samu ya lallasheta ta haƙura, nasihar ma da yaso ƙara yi mata kasawa yayi saboda gaba ɗaya ta karya mishi zuciya. Haka suka riƙe juna da Aisha suna rizgar kuka sai da ƙyar aka ɓanɓare su a jikin juna.
Gaba ɗaya hankalin mutane ya dawo kansu.
Shi kanshi Malam sale zuciyar sa ta karye yana tunanin rabuwar uba da ɗiyar shi ga kuma aminan juna, sanin kanshine juriya kawai Malam jafaru yakeyi…...
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️
FULANI
08082101373
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
PAGE 🔟
Haka suka rabu cikin tsananin kewar juna, amma ba yanda zasuyi sai fatan hakan ya zamar masu alkhairi gaba daya.
Cikin mota ma Maryamah tun tana kuka har bacci ya dauke ta, haka sukayita tafiya cikin aminci, bata farka ba har sai da suka shiga garin Abuja lokacin da suka isa la'asar sakaliya.
Da zuwan su suka samu driver na jiransu, kasancewar koda suka zo Suleja, Malam Jafaru sunyi waya da Hajiya shine ta turo wanda zai dauke su. Kalle-kalle Maryamah ta dingayi, duk da bata da duhun kai irin na kauyawa, amma dai ita ko cikin Katsina zata iya ƙirga sau nawa taje.
Haka suka shiga lafiyayyar motan da akazo daukan su, da ita a ranta tana jinjina kyau da tsaruwar garin, amma zuciyanta duk tana wurin babanta, gaba ɗaya tunaninta nacan tare dashi, rayuwa kenan ganin yau itace ta tafi wani gari ta bar babanta, wasu siraran hawayene suka ziraro mata.
Haka suka nufi ɗaya daga cikin manyan unguwannin garin na Abuja, unguwar Asokoro, wadda tana ɗaya daga cikin manyan unguwannin masu kuɗin Abuja wadda sai wanda yaci ya tada kai zaka gani a irin waɗannan unguwanin, Yakubu Gowon Crescent taga an rubuta sunan street ɗin da suka shiga inda yake kusa da Aso Villa.
Unguwa ce mai matuƙar tsaro, kasancewar tana kusa da villa sannan komai nasu a tsare yake, suna da takatsantsan wurin shige da fice na unguwar, gaban wani tamfatsetsen gida suka tsaya, horn sukayi aka wangale masu get motar ta silala cikin farfajiyar gidan wanda yake tamfatsetse mai ɗauke da wasu manyan motoci masu numfashi a rumfunan guda biyu da suke ta gefe da gefe na gidan.
Gida ne ba muna gida ba, ƙaton gida wanda misalta girman gidan ma ɓata lokaci ne, yana ɗauke da part 4, part 2 dukansu upstairs ne, sai kuma part biyu da suke flat, amma suma ɗaya yafi ɗaya girma.
Part ɗin da yake ta hannun hagun su me benen suka nufa bayan driver ya adana motan a mazauninta, fitowa tayi tana ƙarewa gidan kallo, gabanta taji tana faɗuwa tana, Anya kuwa gidan nan ba gidan yankan kai bane? Sai kuma wata zuciyan tace mata, kinsan dai har abada Baba Sale bazai taba cutar dake ba.
Jikinta a sanyaye ta fito, driver ya fito mata ta jakarta Baba Sale zai ɗauka, tayi saurin kai hannu "A'a Baba ka bari, zan ɗauka" Haka ta dauka, shi kuma Malam Sale ya sake kiran Hajiyan yana sanar mata da isowar su, mai aikinta ta aika akan taje tashigo dasu, wadda tazo tayi masu jagora zuwa cikin gidan suna biye da ita.
Da isar su kofar gidan, mai aikin ta danna wani abu a bakin ƙofar, saiga ƙofar ta buɗe suka shiga da sallama.
Palour ne mai matuƙar girma da ke ɗauke da kujeru saiti biyu, akwai ƙofofi barkatai a ciki wanda ita dai Maryamah bazatace gashi ko ƙofofin menene ba, daga gefe, ta hannun dama akwai dining area wanda yake ɗauke da ƙaton dining table mai cin kujeru 10, sai ta gefen hannun hagu kuma ɗauke take da staircase wanda zai sadaka da saman wanda Maryamah bazatace ga yanda yake ba, amma shi kanshi staircase din abun kallo ne, dan kai tsaye bazakace ga da abunda akayi shi ba. Gashi irin mai faɗin nan ne wanda bazai ba mutum wahala ba wurin hawan shi saman, kuma akwai baranda wadda ke d5auke da ƙarafuna masu tsananin kyau kamar dai ginin gidajen India.
Da sallama suka shiga, suka samu wata hamshakiyar mata zaune akan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun da sukaiwa palourn ƙawanya, tana zaune cikin ado, tana danna wayarta ƙirar Samsung latest one, ɗago wa tayi tana amsa sallaman su, fuskarta cike da murmushi "lale Marhabun da Malam Sale, kun ƙara so kenan" tayi maganar tana ɗago idanuwanta daga kan wayar, wanda basu sauka akan kowwa ba sai kam Maryamah, shock taji ta shiga ta kalleta sossai, taji wani yanayi na shiganta akan yarinya, kuma lokaci ɗaya taji yarinyan ta kwanta mata a rai.
"Bismillah Malam Sale ku zauna" ta faɗa tana ƙara kallon Maryamah.
Waje malam Sale ya samu zai zauna a ƙasa.
Da sauri tace "A'a dan Allah haba Malam dan girman Allah ka hau kujera mana"
Haka Malam Sale ya hau kujera, Maryamah ta zauna a ƙasa kusa da kafarshi.
Gaisawa suka shiga yi da Malam Saleh cike da girmama juna.
Maryamah cikin muryanta mai daɗin saurare ta gaida Hajiya duk da muryan ta dashe saboda kukan data sha, Hajiya ta amsa tana mai maida kallonta gareta tace "Malam Sale wannan anya mai aiki ka kawo min ko ɗiya gata nan, Mashaa Allah"
Hakanan taka sa ɗauke idonta akan yarinya wadda kanta yake a ƙasa tana sauraren su.
Murmushi yayi yace "Todai Hajiya gadai tanan duk wanda kika zaba"
Kayan abinci mai aikinta ta fara jera musu Hajiya tace "Bismillah kuci abinci sai muyi magana"
Malam yace "A'a zamu fara sallah dai, akwai Azahar da La'asar a kanmu, a hanya suka riskemu"
"Eh lallai kam gara kuje kuyi kam dan ita kanta Asr ɗin lokacinta yaja tunda gashi har 5 ta ɗan gota"
Haka Malam ya tashi ya fita farfajiyan gidan, ya nufi inda ɗakin drivers din gidan da sauran masu aikinsu maza suke, inda wurin su yake ta can baya, yaje yayi sallah, kasancenwan ya saba dasu.
Itama Maryamah, haka Hajiya ta saka mai aikinta ta tafi da ita zuwa ɗakin su, tayi sallah sai ta kai mata abincinta can taci kafin Malam Sale ya kintsa ya shigo, sannan ta umarci mai aikin da in ta kai Maryamah ta turo ɗayar mai aikin ta kaima Malam Sale nashi can inda yake sbd zaifi sakewa a can.
★★★★
A can kuwa gida Charanchi, Baba Zainu bata dawo daidai ba sai da ta ɗauki wani lokaci mai ɗan tsayi sannan ta dawo hayyacinta, aikam da mugun gudunta tayi waje wanda ko mayafi bata tsaya ɗauka ba, haka ta doshi kofar gidan, tana zuwa zaure, sukayi karo da Hajjah.
"Lafiyar ki kuwa Zainu?" Hajja ta tambaye ta a tsoro ce.
Haba ai kamar abunda take jira kenan, ta ɓarke da kukan baƙin ciki "Shi kenan Hajjah, burinmu ya ruguje"
Cikin rashin fahimta, Hajjah tace "Bangane ba, mekike nufi da burinmu ya ruguje? shige muje gidan muyi magana, kin kama hanya kin fito kamar wata mahaukaciya"
Haka suka shiga gidan, Hajjah nacewa "meyafaru yasa duk kika wani firgice kamar wadda ta warke daga hauka?"
"Hmmm Hajjah Malam ya shammace mu gaba ɗaya ya ruguza mana tsari"
"Me shi Jafarun yayi kuma?" Ta jefa mata tambaya cikin rashin fahimta.
"Hajjah ya ɗauke yar shi ya bar garin da ita, kuma duk yasan shirin mu akan ta"
zaman daɓaro Hajjah tayi "ke bansan hauka ya ɗauke ta ya kaita ina tace?"
"Hajjah ban san inda ya kaita ba, nan da ya tsaya ya ƙare min tanadi tass, sannan ya tasa ɗiyar shi a gaba, yace ta bar mani gidan inci uwar da zanci dashi" Sallallami Hajjah ta fara tana "Wai shi Jafarun?"
"Shifa Hajjah"
Hajjah tace "Eh lallai kam ya nuna mini shi ya haifi abar shi, amma ki barni dashi, zaizo ya sameni duk inda ya kaita sai ya dawo da ita, wato ya nuna ban isa dashi ba, ina gidan ko ya faɗa mini zai bar garin da yarinyar, tsabar ya nuna mini ban isa ba koh aikam zai dawo ya sameni"
★★★
Abuja
Bayan sunci abinci sun natsa, Hajiya tasa aka kira mata su, nan suka sameta zaune inda suka barta, wata sabuwar gaisuwar sukayi.
"Malam naji daɗin cika alƙawarin da kayi min wallahi, kuma gashi ka kawo mini irin yarinyar da na keso, fatana dai ace ta iya ayyukan gida yanda ya kamata"
"Inshaa Allah bazaki samu matsala da ita ba, yarinya ce mai matuƙar ƙwazo da zafin nama, ɗiyar aminina ce, mahaifiyarta ta rasu tun tana jinjira ranar da ta haifeta, ita kuma ta koma ga Mahaliccinta"
Cikin jimami Hajiya tace "Allah ya sanyaya makwancinta"
Haɗa baki sukayi wajen amsawa da Ameen, Maryamah na share hawayen da suka zubo mata.
"Kiyi hakuri Maryamah, rayuwa ta gaji haka
kinji" cewar Hajiya.
Jinjina kanta tayi.
Bayan nan, Hajiya taja numfashi tace Toh Malam Sale, aikin Maryamah a gidan nan shara ne da goge-goge, saboda banajin daɗin na waɗannan da sukeyi, gani nake kamar basu iya ba, ita wadda takeyi da ta koma garinsu ne"
Malam yace "ba wani abu, inshaa Allah bazai gagara ba, zata iya"
Hajiya tace "alhamdulillah, sai kuma maganar kuɗi za'a ringa bata dubu hamsin a wata"
"Ba laifi Hajiya Allah ya ƙara girma, ya ƙara arziki mai albarka"
"Amin ya Allah"
Wajen ne ya ɗauki shiru, zuwa can Malam Sale ya katse shirun masu dacewa "Hajiya alfarmar dai da muke nema dani da mahaifin yarinyar shine, dan girman Allah a samu wata makarantar gwamnati ko kuma irinta mai ƙaramin karfi, sai a sanyata, Idan yaso shi albashin nata sai a ringa biya mata kuɗin makarantar dasu"
Murmushi tayi "Maganar karatunta ba wani abu bane, inshaa Allah za'a nemi makaranta a sata kamar yanda nayi alƙawari, sannan bama sai an taɓa kuɗinta ba, abin bazai gagara ba inshaa Allah"
Cikin tsananin farin ciki, Malam Sale ya hau yi mata godiya, itama Maryamah tace, "Allah ya saka da alkhairi, ya kara girma Hajiya"
murmushi tayi tace, "Bakomi ai yiwa kai ne shi ɗa na kowa ne"
Suna cikin magana ne, aka buɗe ƙofar aka shigo da sallama, matashiyar budurwa ce, zatayi sa'a ɗaya da Maryamah ta shigo, sai yara biyu maza biye da ita duk da uniform a jikinsu.