"Wash mami nagaji" tayi maganar tana kwantar da kanta a kafaɗan mamin da ta zauna kusa da ita.
Ture mata kai mamyn tayi "Abinda kika iya kenan"
Dariya twins suka fara yi mata, ita kuma ta ɓata fuska.
Katse su tayi da "halan baki ga baƙo ba?"
"Afuwan mamy wallahi ban kula ba, ina yini?” ta gaishe shi tana gyara zaman ta, Idonta bai faɗa ko ina ba sai kan Maryamah data ɗago tana kallonsu.
Cikin sauri budurwan tace "Wow, what's a beautiful creature" tayi maganar tana haɗe yatsanta manuni da babba waje ɗaya.
Maganar da tayi ce ta janyo hankalin twins daga gaida Malam Sale da suke, suka kalli inda take kallo, suma suka hada baki wajen cewa, "Wow mami tanada kyau, muna sonta"
Basu jira cewar mamyn nasu ba suka nufi inda take.
Itama kallonsu tayi tana ɗan riƙe hannunsu kaɗan, duk da bata saki jikinta ba, haka tayi ma budurwar murmushi tana faɗin "Inayini"
Zaro ido budurwar tayi tace "Kaini kike gaidawa" dariya ce ta ƙwace mata cike da mamakin an gaisuwar.
"Allah ya shirya ki Zuhyra, kuje ku cire unifoam" cewar mamyn tana kallon yaran nata.
Tashi tayi tana faɗin, "But mami who is she?" Tayi maganar tana nuna Maryamah.
Girgiza kai mamin tayi tace "Our new maid"
Yar ƙara Zuhura tayi tana ɗan tsalle "Wow mami kin biyani nikam" sama tayi da gudu, twins na binta a baya, girgiza kai mami tayi Allah ya shirya......
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋
BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️ & AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️
FULANI ❣️
08082101373
✨🦋RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
PAGE 1️⃣1️⃣
Ƴar dariya malam sale yayi ya amsa da "amin itadai ba ruwanta"
"Haka take bansan ranar da zatayi hankali ba"
Da haka suka dawo maganar da sukeyi sosai malam sale yayi mata godiya haɗi da addu’o’i, sannan ya kalli Maryamah yace, "Yar babanta kinji duk abinda hajiya tace?"
Jinjina masa kanta tayi.
"Ina fata zaki cigaba da nuna halayenki nagari ga mutanen nan kamar yanda nasan ki dasu?"
"Insha Allahu baba"
"Allah yayi ma rayuwarki albarka, ya ɗaga darajarki, Allah ya cika miki burikanki na alkhairi"
Da amin ta amsa kanta a ƙasa.
"Insha Allah zakiyi farin ciki, kedai ki tsare kanki da mutuncin kanki, banda kwaɗayin abun wani"
"Inshaa Allah"
Da haka ya miƙe "zan ɗan shiga cikin gari, In Allah ya kaimu gobe kafin na tafi, zan biyo ta nan muyi sallama"
Cikin marairaice murya tace "Baba ba'a nan zaka kwana ba?"
Murmushi yayi "ƴar shagwaɓan babanta, in miki ta bakin baban naki, ba nan zan kwana ba, akwai abinda zanyi a cikin garin, tunda gobe nake son juyawa saboda ba kasuwanci ya kawoni ba balle na kwana biyu a garin, na miki alƙawarin insha Allah, duk lokacin da na shigo garin zan ringa leƙowa mu gaisa"
"Shikenan baba Allah ya kaimu gobe" tayi maganar hawaye na zubo mata.
Hajiya tace "Kuka bayama ɗiyata wahala dai, da alama kodai da gaske yar shagwaɓan ce?"
Ƙasa tayi da kanta tana murmushi cikin jin kunya.
Bayan tafiyar malam sale, hajiya ta kira mai aikinta babbar cikinsu mai suna lami, "Iya lami,kije da ita ɗakinku a bata abinda ya kamata, Ina ganin ta zauna ɗakinki, shi wancan ɗakin sai a barwa su dije da Sahura"
Cike da ladabi, amsa da toh hajiya, muje tayi maganar tana yin gaba.
Kallonta hajiya tayi tace, "Maryamah, zaki iya zuwa ki huta, kunsha hanya, sai zuwa gobe zaki fara aikinki"
Da to ta amsa tayi mata godiya tabi bayan iya.
Sosai kalmar godiyan tayi wa hajiya daɗi a ranta ga dukkan alamu yarinyar ta samu tarbiyya mai kyau kuma da alama ba sai an sha wahala akanta ba, dan dagani bata da duhun kai tunda ba daga ƙauye ƙayau take ba.
★★★
Bayan tafiyar su, Zuhura ta sauko cikin kaya mara nauyi, riga da wando na wani yadi mai matuƙar tsada, kanta ba ɗankali amma tana rike da hulanta a hannu sabida tasan, ko giyan wake tasha, bazata sauka wurin mami ta zauna ba ɗankwali ba, yanzun tasha ranƙwashi, gashi in ta fara mita har a kwanta bacci tanayi "Bakwa gujewa kanku shaiɗanu kudai, ku dinga ɗaukan ɗabi’un yahudawa"
Haka ta sakko ta nufi dining area ta ɗebo abinci ɗan kaɗan a plate kamar wanda za a bawa yarinya, ta haɗo da ruwa da juice a cup, kusa da mami ta zauna, ganin bata ganta bane yasa ta tambayi "Mamy tana ina?''
"Wace?" Ta mayar mata da tambayar ta.
"Ayya mamy house helper ɗin da kikace an kawo mana"
Ganin yanda tayi mata magana kaman me shirin kuka ne yasa tace "Tana ciki wajen iya Lami"
"Mamy wajen masu aiki kuma?" Ɓata fuska tayi alamun hakan baiyi mata ba.
Ido mamy ta zura mata tana ganin ikon Allah "itama ba aiki tazo yi ba halan?"
"Shi tazoyi but she's different from them" tayi maganar tana ƙara ɓata fuska.
"Au Allah?" Ta ƙara tambayar ta cike da gatse.
"Allah mamy kema ai kinga ita she's special mai aiki" tayi maganar with full of excitement.
Mamee tace "Aa, nidai kam ban gani ba"
"Nidai mamy please a bata ɗaki ko cikin parlour ɗin nan, not at wajen masu aiki" tayi maganar hankalinta kwance, tana kai abinci bakinta.
"Bari dai ta kwana biyu muga yanayinta, ni kaina yarinyar ta kwanta min a rai tun kallon farko"
Cike da jin daɗi Zuhura tace "Yauwa mamy i love you" kiss ta hura mata, ta maida hankalinta kan abinci.
Girgiza kai kawai mamy tayi.
Suna zaune twins ma suka fito, duk sun canja kaya, abu na farko da suka fara shine tambayan mamy Ina aunty cutie.
Cike da mamaki mamy tace "Tofah wacece haka kuma?" Tayi maganar tana kama haɓa.
"The new maid" cewar fadil.
Mamy sosai tayi matuƙar mamaki Ikon Allah wai su yaran nan, daga ganin yarinya yau kowwa ya susuce a kanta, sonta suke koda yake ita kanta haka taji a ranta game da yarinyar.
Ganin yanda suka zuba mata ido alamun amsar ta suke jira ne yasa tace "She's in her room"
Har suna haɗa baki wajen tambayar "Which of the rooms?"
''Ɗakin iya Lami"
Kai tsaye suka juya zasuyi inda ɗakunan masu aikin yake, amma mamy ta kirasu tace su dawo, lokacin magrib yayi yanzun za'a fara kira, suyi maza su shiga toilet na rooms ɗin dake parlour, idan suyi alwallah su tafi masjid, in sun dawo sai suje su ganta.
A haka badan sun so ba suka tafi, sukayo alwallah suka wuce with full of excitement, kan cewa zasu je su faɗawa brothers nasu na part ɗin mommy cewa an kawo musu wata cutie aunty mai aiki.
Tashi mamee tayi ta wuce sama tana faɗin, Kema kiyi maza kigama kije kiyi sallah, time yayi, da haka ta haye sama.
Haka zuhura ta ɗan tsakuri abincin, tashi tayi takai plate ɗin kitchen saboda tarbiyyan da mamy tayi musu kenan, sanda ta shiga haka ta samu iya nata faman hada hadan tuwo, dan yau shi mamy tace ayi da dare. Sannu ta mata da aiki ta wuce ta aje plate din ta fita.
Bayan an idar da sallar isha, haka suka shigo gidan suna yan guje gujensu dasu dasu Adil da Aqeel waɗanda suka faɗawq sunyi new cute auntyn su shine fah suka zo ganinta.
Saukowan mamy kenan taji guje gujen su ana rige rigen zuwa ɗakin iya a gano aunty cutie, Mamy tace Kudai Allah ya shirye ku, ta nemi wuri ta zauna, A haka, itama Zuhura ta sauko, ko zama batayi ba ta kama hanyan shashen masu aikin su.
Mamy ce ta dakatar da ita "dawo ki zauna"
"Mamy please"
"Zasu fito yanzun dasu Fadil"
Bata rufe baki ba taji hayaniyan su sunko tasota, kowwa so yake yayi mata labari har da Fudail da magana ma bata dameshi ba, Ita kam sai murmushi take masu ta rasa wa zata amsa, haka suka fito falon.
Ganin mamyn a zaune ne yasa ta rusuna "sannu da hutawa hajiya"
kafin ta amsa har Fadil ya tari numfashin ta "Mamy zakina ce mata cutie?"
Murmushi kawai tayi, gefe da gefen kumatunta na lotsawa. Fudail yace "You look more beautiful in kikayi smiling cutie"
Wani murmushin ta ƙara, suka nemu wuri suka zauna a kasan carpet mai laushin tsiya.
Ɗago idonta tayi ta kalli Zuhura ta mata ɗan murmushi "Sannu"
Zuhura da ta cika tayi fam kam kin amsawa tayi.
Mamee ta kalleta tace, "Baby ke kam kin shigesu wallahi"
"Amman mamy kina gani ta kula kowa banda ni"
Zaro ido Maryamah tayi tana kallon Zuhuran.
Mamee tace Allah ya kyauta miki.
Haka suka zauna sunata mata hira, Ita kam hankalinta duk baya kansu sosai duk da taji matuƙar daɗi na yanda yaran suka amsheta da ma sauran yan gidan, amma tunaninta na kan takira babanta, wayan ta sanya caji ta barota dakin so hankalinta duk yana can.
Ganin har lokacin bata sake ba, mamee tace, "Oyo, Aqeel and Adeel ku je ku kwanta, dare yayi, Ta kalli su Fadil Kuma kuje kuyi shirin bacci, gobe akwai school, kubarta ta huta....."
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
🦋✨ RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋
BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️
FULANI ❣️
08082101373
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
PAGE 1️⃣2️⃣
Mamee bata kai ga rufe baki ba, wata budurwa ta buɗe kofan ta shigo kanta tsaye batare da sallama ba, ciki ciki tace "barka da dare mamy"
"Barka" ta amsa mata a taƙaice.
Inda su Adeel suke ta kalla "maza ku tashi mommy na kiran ku"
Ko kallo Maryamah bata isheta ba duk da ta ɗan kalleta a fusge, amma badai zata shaida ya take ba, tsakanin ita da zuhura babu wanda ya tanka wani a cikin su, haka ta tasa ƙeyansu suka fice.
Mamy sama ta nunawa su Fadil alamun su haye, sannan ta maida kallonta ga Maryamah Kije ki kwanta kinji, akwai gajiya tare dake, sai da safe.
"Toh Allah ya kaimu" Ta kalli Zuhura tace "Saida safe"
Zuhura kam zumɓuro mata baki tayi "Nifa ba ruwana dake,tunda wariya kike nuna min"
Murmushi tayi cikin rashin sakewa ta bata haƙuri.
Mamy ce ta katse zuhura dake shirin magana "yi tafiyarki abinki, ki tabbatar kinyi bacci, banda tunanin baba" ta ƙarasa maganar da murmushi a fuskar ta.
Sallama sukayi, kowa ya nufi makwancin sa amma su mamy parlour dake sama suka nufa, hira suka dasa ta tsakanin ƴa da uwa.
Koda taje ɗaki, ta samu iya Lami ta gama komai da zatayi har ta shige ɗaki, da sallamanta ta shiga tana mata sannu.
"Sannu ƴar nan sannu da baƙunta"
Murmushi ta mata kawai tayi kasa da kanta.
Iya tace "Da alama kinzo da ƙafar dama gidan nan, tunda naga yaran gidan sunayin ki, duk da daman nan ɓangaren basu da matsala, sukam ɗayan ɓangaren ne dai azabar duniya" iya tayi maganar cike da sigar son bada labari.
"Uhmmn" kawai tace ta wuce inda wayanta take caji, ta ɗauka cike da zumuɗi ta kunna wayan, dan so take tayi waya da babanta taji ya yake.
Bayan wayar ta kawo komai ya saitu daidai, ta fara kiran layin babanta, tanajin ringing ɗin amma a ƙagare take, Ka ɗauka babana tayi maganar ƙasa ƙasa tamkar me shirin sakin kuka.
Ai kuwa cikin sa'a ya ɗaga ɗin da sallama, tanajin ya ɗaga ta saki siririn kuka mai haɗe da dariya "Babana, baban Maryamah"ta kira sunan shi wasu hawayen na kara zubo mata.
Shima a nashi ɓangaren ajiyar zuciya ya sauke "Zinariyar babanta ce?"
Ɗaga kai tayi kamar yana ganinta "Zinariyar kace babana, ina matuƙar kewan ka babana"
Nima ina kewan zinariya ta, toh yakike ? ya kukaje? Ya kika samu sabon wurin?” Duk ya jera mata tambayoyin a lokaci ɗaya, yayi shiru alamun yana jiran ta amsa mishi duka.
Dariya ta saki cikin hawayen tace "Babana duka tambayoyin nan mani ni kaɗai"
Shima a nashi ɓangaren dariyan yayi yace "ɗiyar babanta, to ai na rasa me zance ne"
Murmushi take tayi "To baba duk lafiya lau alhamdulillah, wurin zama kuma, baba, gashi nan, shima alhamdulillah muna fatan dacewa"
"Allah yasa mun dace ɗin"
"Ameen, baban Maryamah, ya mutanen gidan, yasu Zainab da Muktar?”
"Duk suna nan lafiya lau, mutanen gida kam tunda na dawo ma ban koma ba sai zuwa ɗan anjima, tunda kuka sauka mukayi waya da Malam Sale, yake faɗamin kun sauka lafiya"
"Haka ne baba"
"Masha Allah ki kwanta kiyi bacci, kiyi addu'a kinji, sannan kiyi aiki da gaskiya, banda taɓa abin wani"
Inshaa Allah, da haka sukayi sallama cikin kewar juna.
Bayan ta gama magana dashi ne ta kira numbern Aisha itama cike da zumuɗi.
Aikam kamar mai jira Aisha ta ɗauka, dan tun ɗazun take trying ana ce mata switch off.
Tana ɗagawa ta fara mita "Shine kika barni inata jiran kiranki har hawan ruwana sai da ya tashi"
"Au haba, kice hawan ruwanki ne ya tashi"
"Ki bari kawai, duk motsina sai nace sahiba ana can yanzun, ko kin isa, ko har kin fara aikin, ko mutanen sunada mutunci?"
Dariya ce sosai ta ƙwace wa Maryamah jin a yanda tayi mata maganar "Gaskiya Allah ya yaye miki yanzun wannan tunanin duk ke kadai" ta faɗa tana wata dariyan.
Itama Ai'shan dariya tayi "Ke Allah gaba ɗaya hankalina da tunani na yana wajen ki"
A nan suka shashance suna hiransu cike da nishaɗi har sai da akayi masu warning sannan sukayi sallama.
Itakam, iya Lami ashe tana gefe ta buga tagumi tana kallonta, a ranta take jinjina girman kaunar da wannan uba da ƴar suke ma junan su, ga kuma wata ma da batasan ya suke da ita, ba amma dai tasan sunada kusanci mai girman gaske, gaskiya.
Juyowa tayi taga iya na kallonta ɗan saita kanta tayi, sannan ta shiga toilet saboda wanka takesonyi, kunsan mutuniyar ku da wanka kamar kwaɗo, ganin bata gane kan abun ba dan ko ɗazun da ta shiga, iya ce ta taran mata ruwa a buta tayi alwallah, ganin bata san yanda zatayi ba, kuma bata son tayi karambani, shiyasa ta fito ta nemi wuri ta zauna.
Iya ta kalleta tace "Ba wanka zakiyi ba?"
Ƙasa tayi da kanta "Shi zanyi"
"Naga kin nemi waje kin zauna"
Sai lokacin ta ɗago kanta kaman zatayi kuka tace mata "Bansan ya ake amfani da bayin ba"
Iya ta riƙe baki da mamaki "Ikon Allah ƴar nan shine kuma kika nemi waje kika zauna maimakon kiyi magana"
Shiru Maryamah tayi, tayi ƙasa da kanta.
Wannan yarinyar dai inajin miskila ce, maganar ma kamar akan dole take yinta,
haka nan tace, tashi muje in nuna miki yanda yake.
Godiya tayi mata, tare da bin bayanta.
Bayan sun shiga ta nuna mata duk yanda zatayi amfani da abubuwan banɗakin, sanann ta fito ta barta, ita kuma tayi wankanta tsaff ta fito, jikinta ɗaure da zani da ƙaramin hijab.
Bayan tayi shirin bacci ne ta nemi wuri ta rakuɓe saboda basan ya zasuyi ba, kuma bata son baba taga zakewar ta.
Saida baban tace, Ki kwanta mana, ai gadon zai ishemu.
Haka ta kwanta a ɗarare tayi addu’an bacci, da yake tanada bashin baccin jiya da bata samu tayi sossai ba saboda zullumin barin gida, ga kuma gajiyar hanya, kasancewar bata taɓa doguwar tafiya ba, tana kwanciya bacci yayi gaba da ita.
Asubah tagari Maryamahn babanta....
★★★★
Asubar fari ta farka, ita kanta tayi mamakin baccin da tayi dan batayi zaton zata samu bacci har haka ba, jin anata kiran sallah ne yasa ta shiga bayi dauro alwallah, tazo ta kabbara sallah tayi nafila, Tana zaune tana lazimi har akayi kira na biyu, ta tashi ta kabbara raka'atan fajr har ta kabbara sallar asbah, iya bata tashi ba, Sai bayan da ta sallame sallah sannan ta ɗan bubbuga gefen iya kanta tashi tayi sallah.
Tashi tayi tana salati tace, Har anyi sallah, yar nan.
Kanta ta gyaɗa mata.
Nayi ta shige bata jima ba ta fito ta ta kabbara sallah.
Bayan ta idar ne, Maryamah ta maida kallonta ga iya tace mata, "Ina kwana?"
Lafiya lau ta amsa mata tana fadin "Ya kwanan bakunta?"
"Alhamdulillah" Maryamah tace tana cigaba da lazimi, bayan ta gama tayi azkar sai ta fara karatun Qur'ani cikin zazzakar muryarta.
Iya ma tashi tayi ta tafi kitchen dan ta fara nata aikin.
Bayan Maryamah ta gama karatun, ta tashi ta nunke abun sallah ta fito, tayi hanyar dataga iya na yawan fitowa da shiga tana kyautata zaton nan ne kitchen ɗin.
Shiga tayi ta samesu su 3 sunata aiki kowa da abinda yakeyi, gaishe da sauran tayi, suka amsa duk suna binta da ido, suna mata kallon ƙurilla, abunda tafi komai tsana a rayuwarta kenan, kallo bata son shi ko kaɗan....
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋
BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️ & AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️
FULANI ❣️
08082101373
PAGE 1️⃣3️⃣
Ƙarasawa inda iya take, tayi tana tambayar ta "Iya mai zan taya ki da shi?"
"A'a keda zakije kiyi naki aikin yar nan, kije kawai ki fara naki aikin, babu yawa ai aikin"
"Bansan mai zanyi ba iya, tunda kinga jiya Hajiya bata faɗa min abinda zanyi ba, tadai ce shara da goge goge, to kuma bansan inda zan ringa sharewa"
Shiru Iyan tayi na ɗan lokaci kafin tace "toh tunda basu kai ga sakkowa ba, inaga koki fara gyara parlour na ƙasa kafin su sauko, sai kiji ina da ina zakiyi"
"Amma bansan inda kayan aikin suke ba ai"
Ajiye ludayin hannunta tayi "Eh kuma fa haka ne, muje na nuna miki inda suke"
Zuwa tayi ta ɗakko mata engine ɗin da keyin sharan da duk kayan buƙata, su mopping stick da sauran su.
Tsayawa tayi tana kallon abinda iya ta nuna mata, wai dashi zatayi shara ta tambayi kanta cike da mamaki.
"Ban iya amfani da wannan ba, in akwai tsintsiya a bani kawai sai inyi da ita"
"Ai parlour da ɗakunan nan sun miki girma, ace kiyi shara da tsintsiya wannan ɗin dai zaifi sauƙi, bari kiga yanda ake amfani dashi"
Nan Iya ta kunna mata, ta nuna mata. Da yake mai saurin ɗauke abuce, yasa tayi saurin fahimtar yanda ake amfani dashi, tayi ma iya godiya, ta fara aikin nata cike da kuzarinta.
Kafin karfe 7 ta gama gyara parlourn tsaff, tayi shara, tayi goge-goge. Tana cikin sanya turaren wuta da burner (kasancewar har shi Iya ta nuna mata yanda zatayi), taji saukowan mamy su Fadil na biye da ita.
Cike da murmushi da kuma jin daɗin ganin Maryaman na aiki tace "Kai Masha Allah, wai har kin tashi kin fara aiki kenan Maryamah?"
Da sauri ta tsugunna ƙasa "Ina kwana Hajiya"
Da lafiya ta amsa mata tace ta tashi daga tsugunnon da take haka, ya kwanan baƙon waje.
Da Alhamdulillah ta amsa tana ƙara yin ƙasa da kanta ganin irin kallon da take mata.
Cike da burgewa mamy take kallon ta dan ita dai haka nan yarinyan ta kwanta mata a rai, kuma da ƙari da tarbiyyar da ta kula yarinyar nada ita.
Cike da tsokana tace "Allah dai yasa baki kwana kina kuka ba"
Da murmushi a fuskarta bata amsa da a'a.
"Toh alhamdulillah, ashe har kin fara aikin ma, sannu kinji da ƙoƙari"
"Iya ce ta nuna mini inda zan fara, tace kafin ki sauko sai ki faɗa mini sauran wuraren"
"Aikam ta kyauta, yanzun sauran parlour sama da ɗakina, Zuhura ita ke gyara ɗakin ta dana su twins"
Fadil da Fudail ne suka hada baki wajen faɗin, "Morning cutie"
Murmushi tayi masu tace "Kun tashi lafiya?"
“Alhamdulillah.”
"Oya ku wuce kuyi breakfast" cewar mamy ganin suna shirin ƙara yin wata maganar.
Wucewa sukayi, lokacin ita ma Zuhura ta sauko.
Tana saukowa suka hada ido da Maryamah tace mata "Ina kwana?"
Kaman me jira ta bushe da dariya tace "Nifa wallahi kunya kike bani, in kika gaidani bafa wani girmarki nayi ba, kilan ma sai dai muyi age mate"
Murmushi kawai Maryamah ta mata.
Ita kuma Zuhura, da ta tabbatar Maryamah ba magana zatayi bane, yasa ta kalleta "ya kwanan ba kunta, hope dai kinyi bacci yanda ya dace?"
Aisha ce ta faɗo mata a rai, sanda Zuhura ke mata wannan tambayan, sai kawai tayi murmushi mai faɗi "eh alhamdulillah"
Mashaa Allah ta furta tana wucewa dining area inda su mamy suke, already har sun fara cin abincin su.
Sallama tayi dan tasan ƙa’idar mamy sannan tace mata,"Mamy good morning"
"Morning baby, how was your night?"
"Alhamdulillah"
"Mashaa Allah"
Nan suma, twins suka kalleta suna gaidata, amsawa tayi ta shafa kansu.
Kujera taja ta zauna ta fara serving kanta tea kawai ta had6a da chips.
Cikin natsuwa suka karya suka gama.
Bayan sun gama, dije mai aikinsu ta fito riƙe da lunch boxes nasu. Nan kowwa ya amshi nashi, sunawa mamyn su bye bye
"Bye ayi karatun and ayi addu’a kafin a fita"
★★★
Bayan tafiyan sune mamy ta dawo main parlour, ta samu Maryamah tace "Muje sama na nuna miki inda zaki gyara"
Bayan ta tabi suka hau saman, Ita sai yau ma ta ƙara kallon yanda benem yake, ita kam ai bata taɓa ganin bene irin wannan ba, duk da ta taɓa hawa bene sanda sukaje Katsina ita da Aisha da umma biki gidan yayan umman Aisha, Amma gaskiya ba irin wannan bane, wannan kam da banbanci da wancan, dan wannan ba ka cika gane cewa bene kake hawa ba saboda faɗin staircase ɗin, ga ƙarafunan gefen ma gwanin sha'awa.
Bata ƙara rikicewa ba saida suka isa saman, taga irin tsaruwar gurin,
ba ƙarya parlourn yayi masifar kyau, dan bata cuci kanta ba, haka ta saki ido ta hau kallon aljannar duniya, an zuba dukiya, ba ƙarya a wajen, duk da ba wani tarkace ne a parlourn ba, amma su kansu kujerun da aka ƙawata parlourn dasu abun kallo ne, Itadai ko a film bata taɓa ganinsu ba, duk da ba wani kallo take ba, haka tayi ta kalle kalle abinta.
Mamy ce ta katseta ta hanyar cewa ki fara da ɗakina, ta nuna mata corridor ɗin da ke ɗauke da ƙofofi kusan hudu, dama 2, hagu biyu,
"Ɗaki na karshe daga dama ne nawa, so shi kawai zaki gyara da toilet sai kuma nan"
Toh tace ta ɗauki kayan aikin ta nufi ɗakin.
Da shiganta ɗakin wani irin sassanyan ƙamshi ya bigi hancinta, ido ta lumshe tana furta Mashaa Allah ƙasa ƙasa.
Ɗakin ta karewa kallo ya haɗu, haka ta gyara shi tsaff, duk da daman sai kayi tunanin ma ba a kwanta a ciki ba, gaskiya ita da kanta ta jinjina tsaftar mamy, haka da ta shiga toilet ɗin, dole ta zuba ƙauyancinta son ranta tunda tasan ba me kallon ta daman mazewa kawai take, ta gama ƴan taɓe-taɓenta, ta wanke shi tsaff ta fito.
Sannu mamy tayi mata, tana shi mata albarka da ta shigo taga yanda ta gyara mata ɗakin kamar yanda takeso, ba buƙatar saita ƙara gyarawa ko tasa Zuhura tayi mata.
Parlour ta fita nan ma ta gyara shi, ta sanya turaren wuta, sannan taje ƙofar ɗakin mamy tayi knocking.
Izinin shiga ta bata dan haka ta shiga da sallama.
Zaune ta sameta a bakin gado, daga bakin ƙofa ta tsaya ta ɗan duƙa tace "Hajiya an gama sai kuma ina?"
"Shikenan kije ki huta"
Godiya ta mata tare da ja mata ƙofa ɗakin.
★★★
Bayan ta sauka ta tsaftace duk abinda tasan tayi amfani dashi, ta maidasu ma’ajinsu.
Saita koma kitchen wajen su iya, wannan karan ma dai still haka su dije suke binta da ido.
Sannun ku da aiki kawai tace masu, ba tare da ta tsaya sauraren amsansu ba, tayi gaba wajen da iya take.
Nan suka samu abinyi, daman ashe tun jiya suke gulmar ta, an kawo mai aiki kyakkyawa kuma ga dukkan alamu ta samu karɓuwa a qurin masu gidan, duk da sunsan daman mutanen basu da wulaƙanci, amma gani suke kamar sunfi nuna zumuɗin ta yaran gidan, kuma daga ganinta zatayi girman kai.
Sahura ce ta taɓe baki tace "ni wallahi gaba ɗaya ma batayi min ba,