shi ba sai yanzu?"
"Aure ka ce, halattacciyar alaƙa. Kuma da kake zancen ban san dashi ba ai ba laifinsa bane. Na yarda da tarbiyar da mu ka bawa ƴaƴanmu. Yaron nan bai taɓa yin wani abu gaba gaɗi kamar mara mafaɗi ba. Tunda har kai ne ka jagoranci ɗaurin auren na tabbata ba a hanya ka tsinci zancen ba."
"Haka ne" ya ce da wani irin disbelief. Wai yau Abu ce take kallon idanunsa tana faɗa masa maganganu irin waɗannan.
"Na kuma jima da sanin cewa duk abin da zai yi yana turo maka saƙo ya sanar da kai."
Bai yi mamakin yadda aka yi ta sani ba
"Shi ya faɗa miki ko?"
"A wayarka na gani."
"Bincike kike min?" Ya ɗaga murya.
"Ni na nuna mata" Mama ta bashi amsa ita ma yau da nata ƙwarin gwiwar.
Inna ta dube shi bayan ya gama yiwa Mama nata kallon za ki gamu dani ɗin.
"Abu guda nake nema daga gareka. IZINI. Duk wani abu da ya kama na bikin nan wanda zai fitar dani ko ƴan uwana..." ta nuna su Hajiya "daga gida ina roƙon ka sahale mana. Sannan ranakun taron su ma ka barmu mu je. A gidan nan kai amarya ne kaɗai uwa bata zuwa. Amma komai tare muke yi ka sani. Ko sisi ba na nema a wajenka. Alhamdulillah ina da abin hannuna na fitar da ɗana kunya."
"Ɗanki? Wai yau Abu kin sha wani abu ne?" Alhaji ya ma kasa yi mata faɗa saboda ta shayar dashi mamakin da bai taɓa zato ba.
"Ɗana Tajuddin ba. Wanda a kansa na fara sanin daɗin zama uwa. Yaron da tsabar taurin kai irin nasa ya laƙaba min suna Inna tun da sauran ƙuruciyata." ta faɗi cikin tuna baya da tasowar zazzafar ƙwalla "a wajen yi maka biyayya da son kyautatawa na dinga danne haƙƙinsa dake wuyana. To amma daga yau in sha Allahu an gama. Ba zan bari wata aƙida mara tushe tasa ya rayu da fushin iyaye biyu har ma rayuwar tasa ta kasa albarka ba."
Tana gama magana ta tashi za ta fita don hawayen da take yi ya hanata cigaba da faɗa masa irin damuwar da ta jima tana dannewa a zuciyarta.
"Zainab."
Dakatawa tayi ta juyo su ka haɗa ido da Alhaji.
"Ban yi miki izinin fita yin duka buƙatun da ki ka nema ba. Haka ma ku" ya kalli inda su Hajiya ke zaune suna murmushin jindaɗin wannan abu.
Inna ta goge hawayenta ta kalle shi.
"Samun izinin shi ne kaɗai abin da zai sa na yafe maka rabani da ɗana da kayi sama da shekara goma alhalin ba Allah Ya saɓawa ba."
Ficewa tayi ko kallon inda yake bata sake yi ba. Umma da Mama su ka bi ta. Hajiya da ta ɗan jinkirta tashi kallonsa tayi.
"Tura ce ta kai bango Alhaji. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan baka sassautawa Abu ba to wannan fito na fito ɗin yana nufin ta gaji da aurenka. Muma kuma ƙofa ta buɗe mana na daina shanye mulkin mallakar da kake mana. Ah to."
"Wai ni Gambo anya ba sauya ku aka yi ba?" Ya faɗi da gaske.
Hajiya tayi dariya "ai na faɗa maka tura ce ta kai bango. Ka bar gani na shiru shiru. Wallahi da Kamal ka yiwa abin da kake yiwa Taj da gidan nan ba zai ɗaukemu ba. Ita kanta Abu har gulmar yakana irin tata muke yi da su A'i. Akan korar Taj da kayi kuma ta cigaba da zaman gidan nan akwai yayunta biyu da su ka fita harkarta. Kafi kowa sanin tana da gata. Mace tilo cikin maza shida! Babu yadda su Alh. Lurwanu basu yi ba akan za su ɗauko Taj daga wajen Jamila taƙi. Kawai don ta faranta maka. Amma kullum sakayyar da kake yi mata ba mai daɗi bace."
Ita ma ficewarta tayi ta barshi da tulin tunani da fargaba. Ba zai yaudari kansa ba. Tsoro ya mamaye shi da abin da ya faru yanzu. Idan ya matsa matansa za su iya barinsa babu waige. Idan kuma yayi sakaci gidan zai fi ƙarfinsa. Abu ɗaya ya rage. Ya dinga cizawa yana busawa. A yau dai dole ya busa don yana cizawar Abunsa za ta ɓalle. Matar da zuciya ta kasa tsufa daga yi mata soyayya tamkar yau ya aurota.
RAYUWA DA GIƁI 18
Batul Mamman💖
***
Snacks lodi guda jere akan trays Zahra da Salwa su ka dinga shiga dasu falo. Komai da zafinsa saboda yanzu aka soya. Sai sassanyan zoɓo da kunun aya sun sha ƙanƙara a cikin jugs.
"Zahra mun tayar dake tsaye ba notice ko? Da ba ki wahalar da kan ki ba. Yanzu mu ke shirin watsewa." Cewar Ya Zulaiha.
Zahra tayi murmushi "ko yaya dai ya kamata ku ci. Abinci na so ɗorawa sai Salwa ta bani shawarar sayen frozen snacks daga Happy Taj."
Zahra ta nuna Salwa ta sha mayafi "kin ganta nan tana dawowa ko zama bata yi ba ta hau suya. Da kun tafi ma sai an bi ku dashi har gida."
Kowa dariya ya yi banda Ahmad da ya maka mata harara. Sai kuma Kamal da Taj da su ka kalli juna. Kamal ya yi dariyar tsokana don ya san ran Taj bai so ba.
Ya Hajiyayye tana shan zoɓo ta ce "Mungode sosai. Sai ku fara shiri ku ma. Baƙon gidanku ya yi aure yau."
Kallon neman ba'asi Zahra ta yiwa Ahmad. Shi kuwa Salwa da ta tsaya cak yake kallo. Rawar kanta da baya so tayi yawa. Amma duk da haka sai yaji tausayinta ya tsirgs masa kafin ya iya bawa matarsa amsa.
"Taj aka ɗaurawa aure bayan sallar juma'a."
Ita ma Zahran da yake ta gama harbo jirgin Salwa sai da gabanta ya faɗi. Ta waiga gefenta da sauri amma bata ga Salwan ba.
Ashe Ahmad na ambaton auren Taj ta bar wajen a guje.
"Me ya sami Salwa?" Wajen mutum uku su ka tambaya a tare.
Zahra sai ta faɗi abin da ya fara zuwa bakinta "ai kuwa samosa ta bari akan wuta."
Da sauri tabi bayanta har ɗaki. Da shigar Salwan ta banko ƙofar da sauri ta murɗa muƙulli. Kan gado ta faɗa ta riƙe ƙirji. Kukan da take tunanin yi yaƙi zuwa. Sai ajiyar zuciya kawai da wani irin zafi a ƙirji.
"Ana wata ga wata" Zahra ta faɗi tana juyawa.
Ahmad ta gani a bayanta. Fuskar nan tasa babu salama. Tare gabansa tayi kafin ya fara buga ƙofar.
"Don Allah ka barta taji da abu ɗaya."
"Wane irin rashin aji ne wannan Zahra? Ke haka kika yi?"
Bayansa ta kalla "Rage muryarka don Allah kada a ji."
Kamar bai ji me ta ce ba ya cigaba da faɗa.
"Duk ta bi ta dami kanta akan wanda bai ma san tana yi ba. Da ta san da yadda yayi wannan auren ma sai ta godewa Allah. Na riga na faɗa mata da wuya Alhaji ya yarda ɗansa ya auri ƴar Mami."
Tura shi Zahra tayi don maganganun ta tabbata za su ƙarawa Salwa zafi akan abin da take ji. Duk soyayyar da bata sami haɗin kan zuciyar da take muradi ba, abar a tausayawa ce. Lokacin da tayi ta dakon son Ahmad ta sha wuya. Allah ne Ya taimaketa ashe shima yana sonta. Ranar da ya faɗa mata sai da tayi sadaka mai kyau saboda farinciki.
Ƙanana cikin matan ne su ka wanke duk abin da su ka ɓata sannan aka gyara falon kafin su tafi. Zahra ta so su bari domin dai ƴan uwan mijin nata in baka yi bani wuri ne. Kowacce tana ji da boko da gayu. Don ko kina gama secondary aka aurar dake to fa Alhaji zai yi da wajewa da mijin. Ƴarsa dole tayi karatu kamar yadda ya yi. Aiki ko kasuwanci ko zaman gida kuma zaɓin mijin ne idan ta gama.
Yadda su ka zo haka su ka tattara su ka tafi gida domin ganawa da iyayensu. Taj kawai aka bari ya shige ɗakinsa ya kwanta. Addu'a kawai yake yi Allah Ya basu ikon yi masa uzuri kada laifinsa ya yi yawa. Zuwa Abuja already ya kama shi. Ya ma ƙudurce a ransa ba zai ɗauki wayar Amma ba ko ta kira. Gara su haɗu kawai ayi ta ido da ido.
Abin farinciki shi ne irin tarbar da iyayen su ka yiwa zancen.
"Nan da ku ka taho a ayari kun zo yi mana kwarjini ne? Alhaji ya riga ku fasa ƙwan. Har mun fara shirin biki." Umma ta faɗi tana dariya.
Kamal ya ce "Tunda baku yi fushi ba mu ai Alhamdulillah."
Kafin su watse Hajiyayye ta sake tado maganar lefe bayan iyayen sun tashi.
"Bishir kai zan bawa aikin buɗe mana sabon group a whatsapp. Sai a sake maganar a gaban waɗanda basu zo yau ba. Kada ka sako mana Taj dai kaji ko?"
Murmushi ya yi akan maganarta taƙarshe
"Zan kiyaye. Yanzu mece ce shawararki yadda idan na buɗe kawai zan rubuta inda aka kwana sai kowa ya faɗi ra'ayinsa." Kowa ya yi na'am suna saurarenta.
"A nawa ganin ko sisi kada Taj ya kashe da sunan lefe. Na sani cikin gidan nan babu wanda bai mori arziƙin Taj ba tun baya gari. Mu da ƴaƴanmu kullum cikin hidima yake damu. To lokaci ya yi da za a ramawa kura aniyarta. So nake ayi lefe na kece raini amma babu kuɗin ango. Ya ji da muhalli da sauran abubuwan da su ka sauwaƙa kawai."
Abinka da gidan yawa. Amincewar tasu kaɗai sai da ta kawo amsa kuwwa a falon. Wai a haka ma don mata sun fi yawa. Sun tsayar da shawarar yadda Bishir zai tsara jawabin. Sai kuma a bawa kowa damar faɗin me zai kawo daidai ƙarfi.
Wasu don zumuɗi tun kafin a tashi su ka fara faɗin nasu. Haɗin kansu gwanin ban sha'awa. Ɗakin Mama yafi kusa da inda suke zaune saboda haka taji duk abin da su ke cewa. A zuciyarta ta raya lallai wannan zaman lafiya da ƙullewar zumunci tsakanin matan gida da ƴaƴa shi ne mafi girman arziƙin Alhaji. Ba don haka ba da tuni gidan yafi ƙarfin duk wani zafin rai da tsare girarsa.
***
Yawan mutane ƴan Allah Ya sanya alkhairi a gidan ya mantar da Abba damuwar da ya tsinci kansa ɗazu a dalilin Alhaji. Murna ake taya shi da zuciya ɗaya. Cikin hikima ta Allah ya aurar da duka ƴaƴansa ba tare da tsumi ko dabararsa ba.
Amaren ne ma dai Sajida ce kawai take walwala. Zee kuka, Hamdi kuwa ba a cewa komai. Tana can ɗakin Halifa ta rufe ƙofa tana fama da ciwon kai saboda uban tunani. Dukan ne goma da ɗari ba ma ashirin ba. Ita ta sani sarai cewa haɗuwar farko ta kamu da son Taj. Irin son nan mai shigar farat ɗaya. A haɗuwarsu ta biyu lokacin ta tabbatar da gaske zuciyarta take. Sai gashi haɗuwa ta uku da ya dace su yi musayar zuƙata ya zo ba a yadda take so ba. Tarin ƙaunar da take masa take ta bi iska saboda sana'arsa. Kuma don abin haushi bai tsaya a nan ba shi ne harda sake dulmiya mata uba cikin sana'ar da tafi tsana. Me namiji zai yi da girki don Allah? Ita mace da tun ƙuruciya ake horata da ayyukan gidan miji da girki ake farawa. Komai manya za su ce game da aure da maganar ɗa'ami suke farawa ko su ƙare. Sai dai kaji ana kiran tsafta, iya kwalliya, ladabi da biyayya...sannan uwa uba girki. Shi fa girkin nan sai an ƙara masa UWA UBA saboda mahimmancinsa. Shi ne zai zo ya koya har ma ya fita iyawa. Don tayi imani girkinsa da nata zai sha bambam. Ya riga ya ƙwace abin tinƙahon da taƙamar. To ita me za ta yi? Shara da wanke-wanke?
Muskutawa tayi tana sauke numfashi da ta tuna rashin kunyar da tayi masa rannan da irin abubuwan da ya ce mata shima. Ba shiri ta tashi ta zauna tana sakin murmushi.
"Da kansa ma zai sakeni tunda ba sona yake ba." Ta faɗawa zuciyarta.
Da wannan tunanin taji wani irin kuzari na shigarta. Tunda Sajida tayi aure ai nata ba dole bane. Salin alin za su rabu. Haka kawai ba za ta iya rayuwar uba girki, miji girki ba. Duniya ma sai tayi mata dariya. Abin da tafi gudu da ƙi ace shi ne a tare da ita muddin rai? Inaaaa!
Kamar ba ita ba ta fito tsakar gida. Ana ta taron yinin Sajida. Ita da Zee taji ana cewa tunda ko kamu ba ayi musu ba, za a jira mazajensu su faɗi lokacin da su ke so su tare. A zuci tayi dariyar sai dai su kai Zee ita kaɗai. Sai ta kalli Zee ɗin. Idanunta luhu luhu sun kumbura. Tayi zuru zuru ba a buƙatar likita wurin gane bata da lafiya. Tausayin ƙanwar ya kama ta. Gashi tana ganin wannan auren mai raba shi sai Allah. Irin amincin gidajen nasu biyu da soyayyar da aka ce Baballe na yiwa Zee bata hango mata fitowa ba.
Da su ka shiga ɗaki, dafa ta tayi cikin rarrashi ta ce "Allah Sarki Zee. Allah Ya sanya soyayyar Baballe a ranki. Na kula yana da mutumci da sanin darajar mutane."
Zee ta sake fashewa da kuka "kema kin ga babu alamun auren nan zai rabu ko? Yaya zan yi?"
"Ki kwantar da hankalinki. Bawa bai isa ya ƙetare ƙaddararsa ba. Wani ba ya auren matar wani. Yanayin yadda aka yi auren kaɗai ya ishe ki ishara."
Kasaƙe Zee tayi tana sauraron nasihar Hamdi kafin tayi magana.
"Ke baki da matsala kenan da auren? Kodayake me zai sa ki ƙi Taj? Nima ba don abin da Ummi ta yiwa Abba a school ɗinku ba da na haƙura." Wayarta ta miƙawa Hamdi "kin gani. Tun ɗazu yake ta turo min message."
Saƙonnin har guda shida duk abu guda biyu su ke ɗauke da shi. Na farko haƙuri Baballe yake bata akan rashin sanar da ita da neman yardarta. Na biyu kuma yana jaddada mata ba auren alfarma bane tsakaninsu. Sonta yake. Kuma yana fata za ta bashi dama ya koyar da ita son shi ita ma.
Murmushi sosai Hamdi tayi. Bata taɓa sanin soyayya za ta burgeta ba a zahiri sai yanzu. Da alama Baballe zai yi saurin siye zuciyar Zee ta ce a ranta. Tsarin kalaman sun taho da rarrashin da mai karatu zai ji a jikinsa. Ai dole ma ta rabu da Taj. Ko don rashin irin wannan text ɗin na Zee da wayar da Safwan ya yiwa Sajida ɗazu yana ƙara bata haƙurin abin da ya faru.
"Allah Zee kada ki tada hankali da yawa. Na san irin auren nan babu daɗi. Amma ki godewa Allah da mai sonki aka haɗaki. Kuma kina ganin yadda Abba da Yaya ke ta murna. Yawan kukan zai sa su ji babu daɗi."
Sajida ce ta shiga ɗakin a lokacin. Ta kalli ƙannen nata tana murmushi.
"Su Hamdi malaman aure. Irin wannan huɗuba haka? Ko dai dama soyayya ku ke da Ya Taj bamu sani ba?"
Idanun Hamdi hango mata Taj su ka yi a gaban tukunya sai taji tsigar jikinta na tashi. Wannan aure ba da ita ba. Ba dai za ta iya labartawa ƴan uwanta niyyarta bane saboda kada yanzun nan su kaita gaban iyayensu.
"Gani nayi an riga an ɗaura. Gara mu haƙura kawai. Kukan ciwo zai sa mata."
"Da gaskiyarki. Amma ni ke ce damuwata. Jiya da baki san da naki auren ba sam baki da damuwa sai tamu. Yau kuma an ɗaura naga kin yi saurin haƙura kamar ba ke ce ki ka suma ba ɗazu... Don Allah mene ne tsakaninki da shi?"
Da Sajida da tayi tambayar, da Zee idanu su ka zuba mata. Tana son gilla musu ƙarya amma ta rasa wadda za ta fi dacewa. Allah ne Ya taimaketa ƴan matan danginsu su ka shigo ɗakin ana tsokanar amare. A dalilin Abba dukkaninsu basu da wasu ƙawayen kurkusa da su ke shawara dasu. Su ne dai ƙawayen juna sai cousins ɗinsu.
Gabanin Magriba da baƙi su ka sarara ne Hamdi ta shige ƙuryar ɗakinta da wayar Sajida da tata a hannu. Numbar Taj ta kwafa ta gama karanto addu'o'in neman nasara ta kira shi.
***
"Happy kana ganin ka kyauta kuwa? Duk fa irin yadda Yaya ya damu da mu ita ma Salwa jininsa ce."
Kamal ne yake yi masa wannan tambayar a yayinda yake shiryawa zai je ɗaukan Abba su je wurin Alhaji. Yadi ne ya saka mara nauyi ruwan bula mai kyau. Rigar tasa kaɗan ya rage ta ƙarasa gwiwa. Hannunta kuma ya ɗan zarce gwiwar hannu kaɗan. Aikin wuyan da aljihu da aka yi ruwan madara ba mai yawa bane. Hula ya ɗora a kansa lokaci guda ya zama kamar ba shi ba. Ya yi kyau sosai. Sai da ya gama fesa turare sannan ya juya ya fuskanci Kamal.
"Ya kake so nayi da ita? Me ma nayi mata? Banda na bi shawararka ka san Allah da ko text ɗin da take yawan yi min ba zan kula ba."
"Na sani. Amma yanzu da ta shige ɗaki tun ɗazu ya dace ka kirata ka ɗan rarrasheta."
Taj ya ware idanu "in yi me? So ka ke tayi zaton aurenta zan yi? Gaskiya Happiness ka rage sauƙin kai. Zai iya kai ka ya baro."
"To ko Yayan ka ɗan yiwa magana mana. Sharewa kamar baka san komai ba fa ba daidai bane. Please." Kamal ya ce da damuwa. Baya son rigima irin wannan ta cikin gida. Su duka ƙannen Ahmad ne. Amma ana iya samun dalilin da zai sa Ahmad ɗin ya zaɓi ɓangare guda ya ƙuntatawa ɗayan.
"Yanzu dai bani key mu je. In na dawo zan yi masa magana in sha Allah."
Da murmushi Kamal ya ce "ko kai fa." Sai kuma ya sako wani zancen "Goben dai za ka tafi Abuja?"
"In sha Allahu. In Amma ta tsine min tas za ta bini. Gara naje na daidaita da uwata."
"Ba ka yi fushi ba dai da na ce ba zani ba ko?" Kamal ya faɗi yana sosa ƙeya.
Ƙwafa Taj ya yi "Kaf ɗinku na san zaman da nake da ku. In matan suna da mazaje ai ku za ku iya zuwa. Amma har Naja da Rukky dake Abuja duk sun zame wai babu mai zuwa rakani."
"Naja fa ta ce za ta turo a ɗaukoka daga airport."
"Wannan ma laifi zai zama a wajen Amma. Cewa za ta yi wato har na fara neman ƴan uwana na barta."
"Allah Ya fito da kai lafiya. Daga nan zan taya ka addu'a. In kaje dai ka gaishe da Anisa." Yana dariya ya yi maganar.
Wata kwafar Taj yayi don ya san tsokanarsa yake. Shi ya tuƙa motar. Suna hanya yaji wayarsa tana ta ringing. Idan kiran ya katse a sake binsa da wani. Bai ɗauka ba sai da ya tsaya a danja kafin a bada hannu. Baƙuwar lamba ya gani. Kira har huɗu a jere dole ya bi.
Hamdi na ganin sunansa da hasken waya ko ringing bata fara ba ta ɗauka.
"Assalam alaikum wa rahmatullah" ta faɗi da ladabin da ya bawa Taj mamaki. Shi da ya sa rai da tsiwa da rashin kunya. Har ya gama tanadin yadda zai ɓullo mata. Sai gashi tana yi masa gaisuwa irin wannan. Haka kawai zuciyarsa ta hana shi soma murna. Gara yaji da me ta zo. Hamdi ce fa. Wadda ta faɗa masa ƙiri ƙiri bata son sana'arsa.
Basarwa ya yi ya ce "Wa alaikum salam. Wa ke magana?"
"Ya Taj ni ce. Hamdi ce. Don Allah magana nake so mu yi" Ta wani ƙara sauke murya ita a dole mutuniyar kirki.
"Ina tuƙi yanzu. Idan na tsaya zan kira ki in sha Allah." Duk da idan ya so zai iya sanya earpod ɗinsa ya amsa wayar, jikinsa ya bashi dalilinta na nemansa. Shi yasa ya katse mata hanzari.
"To babu komai. Nagode. Nagode. Zan jira ka don Allah."
Jira ya yi ta kashe wayar kafin ya soma dariya. Ya labartawa Kamal rigimarsu ta ranar buɗe Happy Taj da kuma randa ya koma gidan.
"To dai mata sai da lallaɓawa. In kana son shawo kanta sai ka ajiye taka rigimar."
"Ashe ba za mu daidaita ba. Kallo ɗaya nayi mata na gane rigimammiya ce. Tana yi min zan rama don gidan abin ta zo."
Da takaici Kamal ya kalle shi "Kai Happy. Matarka ce fa kuma yarinya ba abokiyar faɗa ba. Ko ina sai ka nuna hali ne?"
"Take takenta kamar cewa za ta yi na saketa. Haka jikina yake bani. Ni kuma wallahi sonta nake kamar babu sauran mata a duniya." Ya ƙare magana yana kanne ido.
Shi ma Kamal da shaƙiyanci ya ce "Shege...mutumin ya fola tsundum. Allah Yasa kada Alhaji ya kawo cikas dai kafin mu kwashi ƴaƴan love."
"Za ka yi bayani. Bari dai hankalina ya dawo jikina in mun shirya da Amma. Ko da duka ne sai ka fađa min sunan budurwarka. In kuma babu sai muje wajen Baba Malam (yayan Inna) ayi maka ruƙiyya. In ma wata jinnu ce ta ƙyasa ayi waje da ita."
"Aljana sai dai a kanka. Ni kam ƙalau nake."
"To in ba tsoro ba ka faɗa min. Idan kuma kasa ka aka yi ne gara na sani. Sai na baka tips na shawo kan ƴan mata. Ka san mu masu auren nan komai mun sani."
"Daga ɗaurawa? Ka rufa mana asiri dai kada ƴar mutane ta tare da ciki."
"Sai kace wani namamajo" Taj ya sha kunu.
"Da meye?"
Da irin wannan faɗan nasu na wasa su ka isa gidan Abba. Idan ka kallesu sau ɗaya dole ka ƙara. Alhaji ya tara arziƙi a gidansa. Ba mazan ba, ba matan ba. Shi kan shi ya san wannan.
Waya Taj ya yiwa Abba bayan sun fito daga motar. Ba a jima ba kuwa ya fito da shirinsa harda babbar riga.
"Ko shigo ciki ku gaisa da mutan gidan mana. Dama can an zama ɗaya balle kuma yanzu. Kuma mazajen ƴan uwanta ma sun zo. Sai ku san juna ko." Ya nuna ƙofar yana murmushi.
Bayansa su ka bi Taj yana sunne kai shi a dole ya shiga gidan surukai. Kamal ya faki ido ya ɗauke shi a hoto ya adana domin duk ranar da ya bashi haushi ya tura group ɗinsu na gida.
*
Hamdi na zaune da waya a hannu tana jiran kiran Taj a ɗakin Halifa ita kaɗai. Falonsu kuma Safwan ne da abokansa biyu. Sai kuma Baballe da iyayensa. Ga Yaya da amare Sajida da Zee. Tsakar gidan kuwa ƴan uwa ne na kurkusa su ke ta aikin kayan miya na girkin gobe saboda sun san dole a sake zuwa kafin ƴan ɗaukar Sajida su zo. Musamman waɗanda basu ji auren Hamdi da Zee da wuri ba.
Abba ya shiga falon da sallama aka amsa. Taj da Kamal su ma su ka yi. Yaya jan mayafi ta ƙara yi. Bakinta har kunne. Duk yadda take son nuna kunyar surukai abu ya gagara. Allah Ya gatance mata a lokacin da bata yi zato ba.
Musabaha su ka yi da duka mazan. Sannan su ka gaisa da Iyaa da Yaya. Abba ya sake gabatar musu da juna.
"Safwan ai ka san Taj ko?"
Safwan ya yi murmushi "sosai Abba. Tun kafin ya dawo ma ta haɗa mu. Abokina ne ko in ce ɗan uwa ma."
Sajida ta sunne kai tana murmushi. Safwan ɗin dama ɗan ayi ne na gaske.
"To ina jin duka dai Baballe ne baku sani ba. Sunansa Abubakar kuma ɗan amini na ne."
Baballe ya taso ya sake basu hannu.
"Ni ne dai ɗan autanku. Ina fata zamu yi zumunci mai ɗorewa."
Iyaa taji daɗin yadda ɗan nata ya yi. Sai da ta yi dariya da Safwan da Taj su ka ce sun ɗauki girman. Aka ɗan yi raha sannan Baba Maje ya juya dama da hagu.
"Ina Hamdiyya ne? Mijinta ya zo ba za ta leƙo su gaisa ba?"
"Yi maza ki kirata Zee." Iyaa ta faɗi ganin Yaya ta sunkuyar da kai.
A ɗakin Halifan ta sameta. Ta rasa gane zaman me take yi ita kaɗai bayan ta nuna musu ita bata da damuwar auren.
"Ki zo ku gaisa da Ya Taj. Amma ki yi sauri don fita za su yi da Abba."
Kafin Zee ta gama magana ta fice da ƙaton hijabin da tayi sallar magariba. Falon ta shiga da sallama. Idanunta Taj su ke nema. Shi ma kuma ƙofar yake kallo. Su ka haɗa ido ta kasa yakice nata.
Tabbas Taj ne mafarkinta, amsar addu'arta kuma zaɓin zuciyarta. A wannan ɗan taƙaitaccen kallon makaman yaƙin neman sakin su ka fara saukowa ƙasa da kansu. Buɗar bakin Inna Luba da shigarta falon kenan sai cewa tayi.
"Mu dai Tajo idan mun zo ɗakin amarya ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 46