Share this page
na tuba ta faɗi a zuci. "Hamdi?" Ya ɗan matsa hannun. "Kai na yiwa" murmushi ya soma yi ta ƙara da cewa "amma dai Yaya ce ta tilasta min nayi." "Allah Ya biya Ya mafificin alkhairi. Now can I ki..." Bata bari ya gama magana ba ta sanya hannu ta toshe masa baki. "Kaga fa Ya Kamal ya fito." Ta kalli gate ɗin a firgice. Dariya ta bashi ya cire hannun nata ya riƙe shi da ɗaya hannun. "Idan ya ƙaraso sai na ce ya tayani roƙonki. Kinga fa a waje za ki barni for God knows how long." Kamal har ya ƙaraso. Ƙwanƙwasa gilas ya yi ta ɓangaren Taj. Shi kuma ya zuge gilas ɗin ƙasa. "Happiness taƙi yi min sallama kamar bata san iyakata nan ba. In ta shiga ciki sai sanda suka ga damar sako min ita." Sunkuyar da kai tayi don har lokacin hannuwanta suna cikin nasa. Tana ja yana sake riƙewa. Kamal dariya yayi kawai "Mrs Happy haka za mu yi dake?" "Shi za ka zaɓa?" "Da me kike tunani? Ya zaɓeki a kaina?" "Naga wai ni ce ƙarama" tayi kicin kicin da fuska. A take Kamal ya canja sheƙa. "Happy buɗe mata. In ka kaita gida sai ku yi sallamar a can." "To wallahi tayi alƙawari a gabanka" Taj ya sha kunu da ya yi maganar. "Ki yi mu shiga kinji. Su Umma ke su ke jira." "Nayi." Ta faɗa don idanun ƴan uwan su biyu sun hanata sakat. Sama Taj ya yi da gilas ɗin ya kai hannunta guda bakinsa ya sumbata. Hamdi ta rasa inda za ta tsoma ranta don kunya. "Gidanmu ba irin wanda ki ka saba bane Hamdi. Duk inda ake da yawa komai is possible. Don Allah idan an ɓata miki rai ki fara faɗa min kafin su Abba. Zan baki haƙuri a madadin ko waye. Kin ji?" Murmushi tayi har zuci. Ta ɗan matsa hannunsa dake cikin nata sannan ta fita. Kamal na buɗe gate da su ka shiga ciki taji wata murya da ta so ta gane tana yi masa magana. "Ya Kamal basu iso bane?" Hamdi ta bi inda ya kalla da ido. Budurwa ta gani tayi kwalliya ta fitar hankali. Tayi kyau tamkar wata amarya. "Salwa? Saukar yaushe?" Ya ce babu wani jindaɗi a tare da tambayar. "Ɗazun nan na iso. Ina zuwa gidan kuma naga Anti Zahra za ta taho wai yau amaryar Ya Taj za ta zo gaishe da su Hajiya." "Gata ku gaisa." Ya faɗi yana kallon yadda shigarta gabaɗaya ta saɓawa sanin da ya yi mata a baya. "Sannu amarya." Ta ce tana yin gaba "bari naje na taya Ya Taj hira kafin ku fito." Kashewa Hamdi ido tayi wanda Kamal bai lura ba. Ta wuce su ta buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ta fita. Komai ya nemi tsayawa Hamdi da ta tuna yadda su ka yi a waya. Sai da Kamal ya kirata sau biyu taji ta bi bayansa tana tunanin hanyar da zata bi ta nunawa Salwa tayi kuskuren shiga gonarta. RAYUWA DA GIƁI 22 Batul Mamman💖 This page is sponsored by _Scentmania_ by Sana. A Kano take, amma ƙamshi babu ruwansa da gari ko ƙasa. Wuyarta ciniki ya faɗa. Za ku sami undiluted oil perfumes ɗinku a duk inda ku ke. Bayin Allah babu cika baki. Talla ne daga abin da na gani, na gwada kuma na amince dashi. Gashi babu ruwanki da jiran sai asusunki ya cika ya tumbatsa kafin ki shiga jerin mata masu aji. Da dubu biyar ma za ki haɗa kwalabe daban daban ki gigita waɗanda ya halatta su ji ƙamshin jikinki da yawan tambayar wane irin turare ne wannan. Scentmania by Sana, na Naana Hauwa'u queen of oil perfumes. Domin neman ƙarin bayani a tuntuɓeta a wannan layin 07065525409. Ko sakan 30 ba ayi ba tsakanin fitar Salwa da shigarsu ciki Taj ya turo gate ɗin. Kamal ya yi mamakin ganinsa tsaye daga waje. Shi kuwa yafito shi kawai yake da hannu. Cewa Hamdi ya yi ta ɗan jira shi. Ko kallon Taj ɗin bata yi ba domin ranta a ɓace yake. Bata son yanayin da take jin zuciyarta a ciki. So take ko dai taga dawowar Salwa ciki ko kuma ita tayi hanyar gidansu. Kafin Kamal ya ƙarasa gate ɗin sai ga Firdaus. Ƴar wajen Yaya Hajiyayye wadda su ka gama FGC tare da Hamdi. "Anti Hamdiyya Habib Umar" ta kirata da ƙarfi cikin murna. Tana rufe baki sauran jikokin su ka firfito suna yi mata oyoyo. Abin ya bata mamaki don gaskiya idan ta ce ta sa rai da tarba mai kyau daga zuwanta tayi ƙarya. Ƙaruwa mamakin nata ya yi da Firdaus ta rungumeta. "Wai ashe matar Uncle Taj ce ke ban sani ba duk zamanmu a school. Ai da ko ruwa wallahi ba za ki ɗebo ba. Uncle Taj is my favourite." Hamdi tayi murmushi kawai tana mai jin kunya. Firdaus ta ja hannunta su ka shiga ciki. Anti Zahra ta taso da sauri. "Ke matsa min. Ƙanwata ce. Ni zan kaiwa su Hajiya ita." "To duk gidan nan dai idan aka cire Happiness kowa ya san nice ta gaban goshin Happy. So please allow me..." wata ƙanwarsu ta janyeta "sannu da zuwa Sis" "Meye haka jama'a? Ba babba babu yaro?" Umma tayi magana daga ƙofar ɗakinta. Kowa sai ya sami nutsuwa "Za ku barta ta zauna ne ko kuwa sai kun gama tsorata ta da wannan hayaniyar?" Sai a lokacin wata mai yawan murmushi ta zaunar da Hamdi akan kujera. Sai dai tana zaman ta zame jikinta ta koma ƙasa. Akayi akayi sam taƙi komawa kujerar. Ga mayafi ta sa ta rufe fiye da rabin fuskarta. A haka ta gaishesu. Umma da su Hajiya su ka fito su ma. Cike da kunya da ladabi ta gaishesu tamkar iyayenta. Aka tambayeta mutanen gida ta ce suna gaishesu. Bakin Inna kasa rufuwa yayi. Surukar tata tayi mata ta ko ina. Fargabarta ma ta ganin wata halayya da za ta nuna nakasun tarbiyya a tattare da zuri'ar Abba Habibu ta ɓace ɓat. Filin gabatarwa aka shiga inda Bishir ya nuna mata iyayensu da sunayensu. Sannan yabi ƴan uwansa ɗaya bayan ɗaya su ma. Haddacewar dai sai a hankali. A wajen ya nuna mata mata goma sha biyar. Sauran sun yi nisa. Ga jikoki gari guda. Su kaɗai sun ishi juna gayya. "Za a saka ki a family group. A hankali duk za ki gane mu." Yaya Kubra ta faɗi. Tana cikin waɗanda Hamdi ta riƙe sunansu saboda kana kallonta kaga ƴar gayu ajin ƙarshe. Gashi ance likita ce. Ta lura dai duka gidan akwai wata kamanceceniya da ko baka san su ba za ka iya danganta su da juna. Kai ta gyaɗa har lokacin ta kasa buɗe fuskarta da kyau. Hira ce ta ɓarke kowa da irin tambayar da yake yi mata. "A kawo abinci kafin ku cika mata kunne don Allah." "Hajiya ai so muke ta buɗe bakinta." "Baki zai buɗe ne babu abinci?" Mama ta fatattaki jikokin ta ce su tashi su fara ɗauko kwanuka. "Yau bamu ci komai ba muna jiran amaryarmu. Me za ki ci?" Wadda tayi maganar ta fara buɗe food flask. Akwai fried rice wadda taji kayan haɗi da hanta, tuwon shinkafa da miyar agushi, waina (masa), coleslaw, pepper chicken, farfesun kayan ciki da kuma nau'ikan lemo na kwali da ruwan roba. Abu kamar taro, kodayake taron ne tunda yawa garesu. Kai a ƙasa ta ce "Na ƙoshi." "Kada na sake jin zancen ƙoshin nan Hamdiyya. Don Allah ki saki jiki don a gida kike. Girkin yau dukkaninmu uwayenki sai da muka saka hannu." Umma tayi magana tana hararar ƴaƴan nasu "daga cewa za ki zo gaishemu duk su ka baro gidajensu saboda fitina. Ai gashi nan kun cika mata ido ta kasa sakewa." Dariya aka yi. Aka gama ajiye tarin kayan abinci kamar na biki sannan aka shiga zuzzubawa. Hamdi ta lura kusan sa'anni ake haɗawa a tray guda. Firdaus ta nace a haɗasu a tray guda amma fir aunties ɗinta su ka ƙi. Wai matar aure ba sa'arta bace. Basu san ita babu yadda za ayi ta ci abinci da kowa a zuwan farko ba. Kuma ƙila na ƙarshe. "Idan ba za ki iya ci su ba a zubo mana tare." Wani irin shiru falon ya yi na wucin gadi kowa na kallon Inna kamar ba ita tayi maganar ba. Kafin kuma su kwashe da dariya suna hailing ɗinta. Harda masu karambanin ɗauko plate za su zuba musu. Da wani irin sauri Hamdi ta matsa tray mafi kusa da ita harda gyara murya ta ce "Bismillahir Rahmanir Rahim." Waɗanda basu yi dariya da farko ba ma sai da su ka yi yanzu. Cikin ruwan sanyi Inna tayi musu maganinta. Inna ma murmushi tayi. Abinci ya yi daɗi. Ba don gidan surukai bane tabbas cin da Hamdi zata yi sai yafi wanda tayi na baƙunta. Su na ci ana kiran sallar la'asar. Ɗakin Mama aka ce a kai ta tayi sallah a can. Suna tafiya da Firdaus ne ta tambayi Salwa. Don duk abin da ake hankalinta bai bar kallon ƙofa ba. "Gidan nan kowa nada kirki Firdaus. Da ina shigowa na haɗu da wata ƴar uwar taku ma a bakin gate mu ka gaisa. Naga kamar ta tafi." "Kai anya kuwa. Kowa na nan fa." Ba don bata riƙe sunan ba ta ce "sunanta Salma ina jin." "Salwa ko?" Sai kuma ta kalli matan dake zaune ta ce "Ina Anti Salwa ne? Sai yanzu na lura bata nan." Cigiyarta aka fara yi ana kiran Anti Zahra ko ta san inda ta tafi saboda bata cewa kowa za ta fita ba. Ita dai jikinta sanyi ma ya yi. Dama tun a gida da ta rangaɗa wannan uwar kwalliyar hankalinta bai kwanta ba. "To ku kira ta mana. An duba banɗakuna? Ko bacci ya ɗauketa a wani ɗakin?" Cewar Hajiya. Hamdi ta tabbata ko ma mene ne babu hannun ƴan gidan nan, duba da yadda su ka shiga ruɗanin ina ta shiga. Firdaus ta ce musu ai Hamdi ta ce taga fitarta. "Tambayata sunan wadda su ka gaisa a waje tayi shi ne na kula ita ce bata nan." "Da shirin fita ki ka ganta?" Anti Zahra ta tambayi Hamdi. Murmushi tayi don tambayar da take jira kenan dama. "A'a, cewa tayi za ta je wajen shi..." Yaya Hajiyayye ta ce "shi wa?" "Ke kuma komai sai anyi miki gwari gwari ne? Taj take nufi ko Hamdiyya?" Yaya Zulaiha ta tambayeta. Ta sake yin murmushi kawai. Kunyar inda take ba za ta sa ta bari Salwa ta sami biyan buƙata ba. Tayi kaɗan! A yadda tazo mata da raini da isa shi yasa za ta hana ruwa gudu matsawar da igiyar Taj a kanta. Ko sun rabu Salwa ta aure shi ba za ta ce ita ce sila har taji daɗi ba. "Ku kira min ita. Ko Kamal. Ta dawo ciki" Anti Zahra ta faɗi hankalinta a tashe. Yadda tayi yasa kowa kallonta da ayar tambaya. Sai ta wayance wai taga Salwan daga tafiya ta dawo ko abinci bata ci ba su ka fito. Nan kuwa tsoronta kada taje tayi abin da zai zubar musu da mutumci. Domin duk abin da Salwa za ta yi dole a danganta ta da Ahmad. Ita kuwa bata son abin da zai taɓa mutumcin mijinta akan wata shirmen soyayyar da babu aji a ciki. Kamal ɗin aka kira ya ce sun fita da ita da Taj amma ba jimawa za su dawo. "Ya za ku fita da ita babu wanda ya sani?" Umma da ta kira wayar ta tambaye shi. "Gamu nan Umma. Mun kusa gida ba in sha Allahu." Sallah aka tafi yi. Wasu kuma suna ta aikin kwashe kwanuka. Masu aikin gidan dai za su aikatu da wanke wanke. Don ma ba da plate suke ci ba, haɗawa ake yi. Hamdi ta đauro alwala ta tada sallarta a inda aka shimfiɗa mata abin sallah. Shigarta ta kamala ta burge Mama. Taƙi jinin lokacin sallah ya yiwa mata a waje su dinga aron mayafi ko hijabi saboda nasu bai dace da tsayuwa gaban Allah ba. A ganinta rashin daraja addini ne yake sa mata fita da suturar da ba za ta musu sallah ba. Su kansu sun san hakan bai dace da tarbiyya da ma ɗa'a ga addini ba. Da ta idar sake gaishe da Mama tayi bayan ita ma ta idar. "Hamdiyya ina son mu yi magana. Matso kinji." Gaban Hamdi ya ɗan faɗi. Ko faɗa mata zata yi ta fara shirin zama bazawara? "Ina fata kin san komai game da Taj yanzu da alaƙarsa da mahaifinsa?" "Na sani" ta amsa kai a ƙasa. Mama ta numfasa ta ce "Kullum burinmu shi ne ƙila idan ya tashi aure su daidaita. Sai Allah Ya ƙaddara masa aurenki. Wannan ma ya ishi mai hankali tunani." Ta kamo hannunta ta riƙe "a halin yanzu mutumci da martabar mahaifinki da ta mijinki suna hannunki Hamdiyya. Hali da ɗabi'ar da za ki nuna mana ita za ta tabbatar da ɗorewar rigimar Alhaji ko kashe gobarar da ta tashi babu gaira babu dalili." Jin an taɓo Abbanta ne yasa ƙwalla cika mata ido. Wani ɓangare na zuciyarta yana ƙara tunatar da ita laifin mahaifinsu ne da su ke fuskantar wannan abu daga ita har shi. Yayinda wani ɓangaren kuma yake kare Abba a matsayin đan Adam ma'asumi wanda ya cancanci duniya tayi masa uzuri idan ya bayyana tubansa. Da ƙaramar murya ta ce "Me ya kamata na yi?" "Na san ke yarinya ce amma tunda na ganki naji bani ds haufi akan zaɓin da Allah Ya yiwa Taj." Mama ta faɗi tana yi mata murmushi "Alhaji yana son mutane jajirtattu. In kin kula yaran gidan nan kowa baki gare shi. To ƙuruciya su ke samun wannan ƙwarin gwiwa ta rashin gazawa daga gare shi. Saboda haka kada ki yarda ki zama sokuwa. Ko laifi aka yi miki yafi son ki gwada ƙwatarwa kanki ƴanci. Sai abin yafi ƙarfinki ya amince ki nemi wani. Abu na biyu kuma ki kasance a kodayaushe cikin nuna hali na kyakkyawar tarbiyya. Zan so ya gani kuma ya shaida cewa ƴaƴan Habibun da yake ganin ya kauce hanya ya sun cika ƴaƴa ta kowacce fuska. Na ƙarshe kuma ki so mahaifinki da mijinki. Ki nuna masa ke kina ƙaunarsu dasu da sana'ar da Allah bai haramta musu ba. Kina alfahari dasu kuma hakan bai rageki da zama ƴar da shi ko wani zai kasa ƙauna a matsayin suruka ba." A rayuwa akan ce wanin hanin daga Allah baiwa ne. Hamdi ta fahimci haka a yau. A shekaru irin nata ko ma fi wata ba za ta gane mene ne ainihin abin da Mama take so ba. Saboda duka maganar a ɗan dunƙule take fita. Amma yau da gobe saboda tashi a gaban Abba yasa ta gane. Magana da iya zuba zance a wajen cikakken ɗan daudu yana daga cikin alamomin da ake ganesu ma. Ya rage nasa ne nesa ba kusa ba da ya gane yana daga cikin abubuwan dake saurin saka a gane tsohuwar rayuwarsa. A taƙaice Mama so take ita Hamdi ta saye zuciyar Alhaji da halaye masu kyau ta yadda zai gane Habibun da ya raina bai gaza ba wurin tarbiyyar ƴaƴansa. Sannan sana'ar Taj bata cikin dalilan da mutum zai yi fushi da ɗansa. Godiya tayi mata da alƙawarin kamantawa da yardar Allah. "In kin kula gidan nan babu ƴan ubanci tsakanin ƴaƴanmu. Duk da Alhaji ne ya ɗora mu akan turbar zaman lafiya to amma fa akwai ƙoƙari matuƙa daga Hajiya. Daga cikin irin zaman ne alhakin kula da kuma tarbiyar ƴaƴa maza ta dawo hannuna. Ba don Allah Ya tsare ba da tuni a sanadiyar korar Taj komai ya rikice mana. Ni kaina ina ɗorawa kaina laifi domin kuwa ni na ƙarfafa masa gwiwar girki. Fatana da raina da lafiyata in ga lokacin da Alhaji zai shigo da Taj ya damƙawa mahaifiyarsa." Kowane gida akwai nasu kalar damuwar. Tana ganin kamar duk duniya sun fi kowa sai gashi gidan da tun shigowarta komai na jama'ar ciki yake burgeta su ma da nasu. Ɗakin Umma, Mama ta kaita. A nan ma babu kowa sai Umman ita kaɗai zaune akan abin sallah. Suna shiga Mama ta fita ta barta. Umma ta ɗaga hannuwa tana addu'a, Hamdi sai ta ɗaga ita ma har Umma ta kammala ta ce Amin. Umma ta zolayeta da cewa "Wato kin ji ina roƙa muku ƴan bibbiyu sau biyu a shekara shi ne ki ke ta cewa amin ko?" Kunya kamar ta nutse "Allah ban san ita kike yi ba." "Janye Amin ɗin za ki yi?" "Eh" Hamdi ta faɗi da sauri, kunya duk ta ishe ta. "Yanzu addu'ar tawa ce ba kya so?" Sake daburcewa tayi ta ce "A'a ban janye ba. Yi haƙuri don Allah" Umma tayi dariya sosai. "Wasa nake miki kinji Hamdiyya. Zo ki zauna." Ita ma kamar Mama da yi mata bayani akan gidansu babu ɓaraka ts fannin zamantakewa ta fara. Sai abin da ba a rasawa na zaman tare. Ko a cikin ƴaƴa tunda ba a raba siblings da ƴan rigingimunsu. Amma dai duk inda aka je aka dawo su ɗin tsintsiya ne masu maɗauri guda. "Hamdiyya don Allah ki riƙe mijinki riƙon da Allah Ya umarci bayinSa kinji. Ki bawa maraɗa kunya." "In sha Allahu Umma." "Na tambaye shi ya min rantsuwar ba taimako da rufin asiri kaɗai ya so yiwa mahaifinki ba. Auren yake so kuma ke ya zaɓa a matsayin abokiyar rayuwa. Saboda haka don Allah ki ji, ki ƙi ji. Ki gani, ki ƙi gani. Babu wata rayuwar auren da take ɗari bisa ɗari. Amma indai kun riƙe juna amana za a sami nutsuwa da rahamar da Allah Ya sanya a cikin aure." Wani tunani ne ya ɗarsu a zuciyar Hamdi da Umma ta kaita ɗakin Hajiya. Shin matan gidan nan sun san shirin da mijinsu yake yi a kanta na raba aurenta da Taj ne? Amsar a bakin Hajiyan ta samo ta ba tare da ta tambaya ba. Ita ma kamar ƴan uwanta zancen da ta fara akan zaman lafiyar iyalinsu ne. Shekaru arba'in da ɗoriya suna gina ƴaƴansu akan turba mai ɓullewa. Ba za su taɓa maraba da abin da zai kawo rabuwar kai tsakaninsu ba. "Nayi imanin kin ji daga bakin mahaifinki cewa Alhaji ya bashi wata uku ya san yadda ya yi Taj ya sake ki. Haka ne?" Taurin zuciya irin na Hamdi sai ta kasa kuka. Idanunta ne kawai su ka yi jazur kamar gauta. Ta gyaɗa a hankali. Hajiya ta dafa kafaɗarta da kulawa "Inna ce kaɗai cikinmu bata sani ba sai kuma ƴan uwanku da shi Taj ɗin. Ko kin faɗa masa?" "A'a." "Da kyau. Don Allah ki bar zancen a cikinki. Abin da nake so shi ne ki ginawa kanki matsugunin da babu wanda ya isa ya rabaki da shi. Kina ganin yadda ƴan uwansa su ka karɓeki hannu bibbiyu. Innarsa da danginta kuwa ..." ta kasa ƙarasawa. Haƙiƙa wannan karon akan Taj yayyen Inna da ƙannenta da su ke duk maza sai ɓarin kuɗi suke yi. Takanas babban wan ya turo matarsa ta sanar da Hajiya cewa su za su yi komai na bikin. Kayan gida da Inna ta ce za ta yiwa Hamdi duk an ɗauke musu. Lefen da ƴan uwansa ke haɗawa kawai aka bar musu. Shi ma kuma akwai gudunmawa gagaruma daga garesu. Yadda Taj yake kyautatawa a gidansu da dangin babansa haka su ma can yake yi musu. Ita dai Hamdi zuciyarta tsinkewa ta sake yi. Bata yi ƙasa a gwiwa ba ta ce "Hajiya maganar mahaifi ba abar wasa bace. Musamman shi da suke da wannan matsalar." "Hamdiyya addu'a nake so ki yi. Ki roƙi Allah ki kuma yi taki bajintar saboda muddin Taj ya fara sakin aure a tsukin lokaci irin wannan wallahi sunansa zai ɓaci. Alhaji bai san wannan hukuncin duka gidan nan zai shafa ba. Za a ce da gaske tunda ubansa ya kore shi ba mutumin arziƙi bane. Sannan ina mai tabbatar miki Innarsa ba za ta zauna ba. Don wannan karon a shirye take. Dama can wa'adin zaman ne bai ƙare ba amma da tabi ta ƴan uwanta da ta daɗe a gida." "Subhanallahi" Hamdi ta faɗi cike da tsoro. "Ƙwarai kuwa. Idan Inna ta tafi kuma Mama...Haj. A'i da ki yi sallah a ɗakinta ma tafiya za ta yi. Saboda kullum gani take laifinta ne Taj ya tashi da son girki." Ya dubi Hamdi da kyau "a yadda ki ka fuskanci gidan nan kina ganin ni da Umma za mu zauna? In kuma duka mu ka tafi yaya makomar shekarun da muka ɓata muna gina ƴaƴanmu akan soyayyar juna da zumunci?" Murya na rawa Hamdi ta ce "Hajiya aikin ya yi min nauyi." "Ke fa mace ce. Kada ki bari na kuma jin wannan kalmar ta gazawa." "Abbana...Yaya ma tana da lalura. Waye zai mutunta abin da zan yi?" "Ubangijin da Ya tayar dake a cikin zuri'arsu, Ya kuma kawoki cikin tamu, Shi zai dafa miki." "To amma ta yaya zan yi abin da aka yi shekaru ba a samu ba?" Har a lokacin zuciyarta ta kasa ganin me su ke so taƙamaimai. "Mace na juya miji Hamdiyya. Mu dai namu ina jin a kan shi aka ƙare kafiya da taurin kai" Hajiya ta faɗi tana dariya. Hamdi ma murmushi tayi. "Duk ya bi ya ɓata mana yara da halin. Sai dai kawai na wani yafi na wani. Tunda Taj ya hana shigo masa gida ba iyalin Taj ba ina ganin yau da gobe yana ganinki da kyawawan halayenki zai gane ɗansa da baban naki da yake ƙi basu ragu da komai ba akan sana'arsu. Allah Yasa kin fahimceni." "Na gane Hajiya. Amma..." "Za ki iya Hamdiyya. Wallahi ina jiye mana ranar da Abu za ta botsare a gidan nan. Mai haƙuri bai iya fushi ba. Komai na zaman lafiyarmu zai tashi a banza. Ƴaƴa ashirin da takwas idan kansu ya rabu yaya zamu yi?" Yau dai bata sani ba kuka ya kamata tayi ko dariya. Duk inda ta shiga magana ɗaya su ke yi mata. Ina ita ina ɗaukar wannan nauyin? Alhajin da ya raina mahaifinta bata jin za ta taɓa yi masa abin da zai burge shi har ya yafewa wani. Hajiya tashi tayi ta ce mata su je ɗakin Inna. Sun sameta da yawancin ƴan matan jikokin nasu. Zolayarta su ke son rai tana biye musu. "Ku zo ku fita." Hajiya ta nuna musu ƙofa. Babu wadda tayi gardama sai Hayat ɗin Ahmad da ya dage ba zai fita ba. "Ƙyale shi Hajiya" Inna ta kalli Hamdi tayi murmushi "iyayenki na san duka sun gama yi miki nasiha. Nawa kawai tuni ne akan ki riƙe maganganunsu domin su ne iyayen Taj. Sai Amma dake Abuja. Ya taɓa haɗaku kuwa?" "A'a" Hamdi ta bata amsa "Ai ta ce tana tafe jibi. Ita ma ba za ta bari su yi haɗuwar wajen biki ba tunda an riga an ɗaura." Ta nunawa Hamdi kujera "Zauna ba a rasa abin faɗa miki ba. Sai dai in kuma kara ce ba za ki yiwa Mama ba." Cewar Hajiya ga Inna. Bayan ta fita Hamdi taji kunyar da tafi ta sauran ɗakunan. Innar Taj tana da wani irin kwarjini da cika ido. "Kina da zaɓin kalar kayan ɗakin da ki ke so?" Tambayar a bazata ta zo mata. Ta ɗaga kai daga sunkuyon da tayi. "A'a." "Taso ki gani" Inna ta nuna mata waje kusa da ita akan makeken gadonta da tun shigowar Hamdi take santinsa a zuciyarta. Kasa tashi tayi sai da Inna ta maimaita maganar tare da umarnin lallai ta taso. A ɗofane ta zauna. Inna ta buɗe catalogue ta ɗora mata a cinya. "Buɗe ki zaɓi wanda ya yi miki. Sai kuma ki zaɓarwa mijinki." Yawu ta haɗiya. Jikinta har wani rawa yake tana jin sanyi sanyi na ratsa ƙasusuwanta. Wannan fa ita ta haifi Taj. Da Yaya za ta ga zaman da tayi kusa da ita irin wannan ƙarshenta sai ta ɓallata. "Hamdi" Ita kaɗai ta kirata da sunan da ake kiranta a gida. Wannan yasa taji ranta ya đan sake. Inna ta cigaba da magana "kin shiga ɗakuna uku na surukai. Nan kuma ɗakin na mamanki ne. Don Allah ki ɗaukeni a matsayinta domin hakan ne kaɗai zai bani damar yi miki riƙon ƴar cikina." Cikin rashin jindaɗi Hamdi ta ce "Ki yi haƙuri." "Ba fushi nayi ba. So nake ki ajiye komai ki saurareni da kyau." Hamdi ta miƙa mata hankalinta kacokan. Inna ta fara da yiwa Abba da Yaya addu'a da su ka haifi matar da ta auri Taj. Saboda ta jima tana tsoron kada aurensa ya tashi iyayen ƴar su fasa saboda korarsa da mahaifins ya yi. Abu na biyu kuwa fito mata tayi a mutum. So take Hamdi ta amsa sunanta na matar Taj ba tare da taji ɗar a zuciyarta

Chapter 21 of 46