har rawa yake wajen amsa mata.
"Aiki ka ke yi ko karatu?"
"Aiki ne. Ina koyarwa a wata pravet a nan kusa da mu."
"Masha Allah. Mal. Ya'u nawa ne albashin ka tsakani da Allah?"
"Et fife (8,500) ne." Ya amsa mata cikin basarwa. Ba ya so tayi tunanin shi ɗin cima zaune ne.
"To zan baka dubu ashirin a yau in sha Allah idan buƙata ta ta biya."
Gigicewa yayi sosai yana ta doka murmushi ba ji ba gani. Ta gama da shi da tunaninsa kaf.
"Me ki ke so nayi?"
"So nake ka samo min waya mai yin bidiyo call na whatsapp."
"Shike nan?" Ya tambayeta da mamaki.
"Ƙwarai kuwa. Idan an samo ka bani lambar in saka data domin wayar za ta iya ɗaukar lokaci."
Ya'u baki har kunne don farinciki ya ce "wayata tana yi sai dai bani da data sannan wassof ɗin ma ya yi ispiya."
"Wannan layin?"
"Eh."
Cikin minti biyar Ya'u yaga 25G. Gani yayi abin kamar wani mafarki da zai iya tashi kodayaushe. Shi da ya saba saka datar naira ɗari zuwa ɗari biyu sa'i da lokaci ina zai kai wannan? Ya yi updating komai da sauri sannan da kansa ya kira. Dr. Kubra Hayatu tayi masa wani irin kwarjini. Ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta sannan ya kaiwa Inna Luba wayar. Kafin a fara jawabi Baba Malam da Amarya suma sun hallara. Ya'u yana gefe Yaya Kubra ta zauna tayi mu su gwari-gwari game da ciwon Kamal, zuwan Yaya asibitin, bayar da ƙodar da ma zuwan Abba Habibu.
Inna Luba tayi kuka babu adadi ba. Muryarta duk ta dashe.
"Yanzu ƴar nan kina da tabbacin rayuwar yarinyar nan ba za ta tawaya ba?"
"In sha Allahu babu abin da zai biyo baya sai tarin alkhairi. Addu'a da kulawa kawai take buƙata."
Baba Malam kuwa cewa ya yi "Idan gudan ƙodar ta sami matsala fa?"
Yaya Kubra ta jinjina tambayar don ta san da wuya a rasa mai yi.
"Komai na Allah ne Baba. Addu'a da kulawa kaɗai za ku iya yiwa Yaya. Sanin gobe kuma sai Allah maɗaukakin Sarki. Abu guda nayi imani da shi, Allah ba Ya taɓa barin wanda Ya fawwala Masa al'amuransa ya taɓe. Mu kyautatawa Allah zato, in sha Allahu babu nadama a cikin sadaukarwar Yaya."
"Allah Ya sa ƴar nan. Allah Ya dawo mana da ita lafiya."
Yaya Kubra ta tausayawa Inna Luba matuƙa.
"Inna na san Yaya a ƙalla za ta yi wata a ƙasar nan kafin ta sami sahalewar shiga jirgi daga hukumar lafiya. Saboda haka ki fara haɗa jaka. Zan yi magana da ƙannena ma za mu ji yadda za ayi a samar mi ki passport da visa."
"Allahu Akbar. Ni ɗin?" Ta kalli Baba Malam "wai Saudiyya zan tafi. Ikon Allah. Allah Buwayi gagara misali. Ni dai Lubabatun ko wata ƴar nan?"
Yaya Kubra ta sha dariya kafin su gama waya. Tana kuma ankare da fuskar Baba Malam. Yaƙe kawai yake yi.
Alhaji ta kira ta tura masa lambar Ya'u ta ce ya kira ya haɗa su Yaya da Innarta. Haka kuwa aka yi. Sun ji daɗin ganin juna. An dai sha koke-koke da addu'o'i. Har Kamal sai da su ka gaisa da shi. Ya yi musu godiya sosai da alƙawarin zuwa har gida idan ya dawo in sha Allah.
***
Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah SWT. Yau kimanin sati uku kenan da yiwa Kamal dashen ƙoda. Sauƙi ya samu sosai domin duka an sallamo su daga asibiti. Likitoci dai sun hana su barin ƙasar domin suna buƙatar kulawa sosai har na tsahon wata biyu zuwa uku.
"Ina ganin gara na kama mana gida kawai. Zaman hotel ba zai yiwu ba" Alh. Ya ce da matansa suna zaune duka su huɗun tare da shi a ɗakin hotel.
Inna ta ce "Hakan ma shawara ce, amma kafin nan ya kamata a san masu zama don a kama ɗan daidai. Sauran yaran nan su zo su koma gida haka nan."
"Kamar kin shiga zuciyata akan raguwar nan. Mata sun baro mazajensu sun tare a asibiti ayi ta hayaniya kullum" cewar Mama.
"Kamawa fa tayi." Umma mai ɗan sauƙin ta ce tana murmushi.
"Tunda dai suna samun lafiya mu kanmu sai mu ragu. Ko kuwa Alhaji?"
"Wannan shawarar ku ce. Ni dai ƙafata-ƙafar Habibu da iyalinsa." Ya gyara zama yana sauraron su.
Hajiya aka bawa dama. Ta zauna ta gama lissafinta ƴan uwanta su ka yi na'am. Umma za a bari tare da Bishir. Sai kuma Taj da Hamdi saboda zamanta kusa da Yaya yana da mahimmanci. Mubina ma babu inda za ta je. Sauran kuwa Alhaji ya ce da kansa zai faɗa musu su shirya nan da kwana uku su za su tafi. Sannan akwai wanda zai nema a samar mu su gida.
"Dr. Hadifi ya ce yana son ganin mu ni da Habibu. Idan mun dawo zan yi magana da su."
*
Bakin Abba Habibu ya kasa rufuwa bayan fitar Dr. Hadifi daga ofishinsa inda ya barsu su yi shawara kafin a bashi amsar batun da ya zo da shi.
"Habibu ba ce wani abu mana."
Abba Habibu ya girgiza kai "wallahi bani da abin cewa. Ni dai abin ya yi min girma. Anya zan karɓa kuwa?"
Alh. Hayatu ya ce "me zai hana? Roƙa kayi?" Ya yi gyaran murya "ba ka ganin kamar wata dama ce daga Allah SWT?"
"Har na isa a bani abu makamancin wannan?"
"Kada ka yi saɓo mana. Kowane bawa da arziƙinsa Allah Ya ke halittarsa. Kuma rabon mutum baya taɓa wuce shi. Ko dai ka je da ƙafarka ko ya biyo ka har inda kake."
"Haka ne. Allah Ya zaɓa mana abin da yafi alkhairi."
"Amin amma don Allah ka yi shawara mai kyau."
Abba Habibu ya yi murmushi "Zan yi istihara in Allah Ya yarda."
*
Zuwa yamma kowa yaji abin alkhairin da ya sami Abba Habibu. Dr. Hadifi ya yi masa kyautar gidan abinci sukutum a nan cikin birnin Jeddah. Tsohon ginin na Kawunsa ne ya saya ashe zai yi masa amfani. Abinnda Yaya tayi ya burge shi matuƙa, sai kuma ya tuna a hirarsu Abba Habibu ya ce ya taɓa sana'ar abinci a nan.
A hoto ya nuna musu gidan. Kusan komai na kayan aiki akwai, gyaran da za a yi kaɗan ne sai kayan abinci da za a tanada. Yayi masa alƙawarin yi musu igama shi da Yaya da duka ƴaƴansu. Sannan zai yi masa gyare gyare da kuma zubin kayan abinci na farko kafin ciniki ya kankama.
"Ku buɗe Nigerian restaurant wanda yake serving abincin ku na gargajiya." Ita ce shawarar da ya bashi.
Kamar haɗin baki duka shawararzu guda. Ya karɓa. To dai ya karɓa ɗin ranar da ragowar masu tafiya za su wuce. Ba su tafi ba sai da su ka je aka ga waje aka sanya albarka.
A gida ma ƴan uwa da su Zee anata murna da rawar jiki.
"Ki bar tunanin tafiya dai kina da aure. A daure a koyi larabci saboda idan na dawo zai yiwu na daina jin Hausa."
"To nima ai ba yanzu za ayi biki ba sai na kai level 4."
Daga cikin ɗaki Anti Zinatu ta ɗago murya "to uwar iya. Ke da yanzu ki ke jarabawar gama sakandire kike kiran level 4 saboda sallamamme ne ya aure ki? To bari iyayen naki su dawo naji ko da yawunsu ki ke wannan saɓon mai girma. In baki yi wasa ba wallahi ranar asabar zan ce da Baballen ya zo ku tafi."
Hankalin Zee tashi yayi tana neman yin kuka. Halifa kuwa dariya harda ƙyaƙyatawa.
***
Godiya da kyautatawar da Ahmad ya yi wa Zahra ba a cewa komai. He truly appreciated kulawar da ta bawa Mami duk da irin zaman da su ka yi a baya. Da ya fito daga wajen Mamin ne ya yi mata zancen Salwa.
"Babanta ne ya damu wai naje naga gidanta."
"Hakan ne ya kamata dama. Ba fa a canjawa tuwo suna."
"Ina ki ka baro amala da fufu? Ko duk ba ƴan uwan juna bane?"
Tayi dariya "ba zan yi musu da kai ba. Don Allah ka ɗauki matsayinka na babba ka wakilce kowa ka je ka ganta. Babu mamaki ma kaga ta sauya. Aure ai ba wasan yara bane."
"Allah ko? Shekararki nawa ne a ciki tuna min."
"Lokaci ɗaya mu ka yi da kai." Ta zolaye shi.
*
Da yamma Ahmad ya kira Salwa ba don ya so ba. Ita kuwa da azama ta ɗauka don ta fidda ran sake ji daga gare shi. Gashi tana jin kunyar zuwa gidansa. Alh. Usaini har gorin dangi yayi mata. Bata yi shawara da kowa ba ta kira Anti Zabba'u. Ai kuwa ranar taga tashin hankali. Irin haukan da su ka yi a gidan Ahmad su ka kwatanta a nan. Alh. Usaini ya zo ya gani ya ci musu mutumci la'ada waje daga su har ita. Banda Mami ta jawo musu ai da yanzu dangi sai sum ture na uwa da uba. Kai ba don abin da tayi ba hatta iyalin Alh. Hayatu sai sun fitar da ita kunya.
Purewater ta ɗauko guda ɗaya ta sako akan plate ta zo ta ajiye a gaban Ahmad. Ya bi ta da kallo ita da ruwan ya watsar.
"Ɗauke abin ki ba ruwa na zo sha ba."
Kunyar taji ta ce "Ko na fita na siyo maka mai sanyi? Ko zoɓo?"
"Zauna."
Zaman tayi tana godiya ga Allah da bai nemi hakan ba don ko sisi bata ajiye ba. Sadakinta ma ta nema ta rasa a cikin gidan. Ta san wanda ya ɗauka amma a yanzu tsoron tada maganar take yi.
Ahmad ya sami damar ƙare mata kallo daga sama har ƙasa. Abin tsoro. Auren da bai fi wata guda ba duk ta ƙare tayi baƙi sai idanu a cikin loko kamar mujiya da haƙora gayau. Falon da ta ajiye shi babba ne irin wanda kowacce amarya za ta yi farinciki da mallakarsa. Fitilu na alfarma, POP ceiling da dukkan wani abu da zai sa ace gida ya haɗu akwai shi. Abin da babu shi ne funiture da electronics. Kuma da alama har cikin ɗakuna da kitchen haka abin yake. Shima a yanzu akan tabarma yake zaune. Ɗakin kwananta ma tabarmar ce. A cikin ɗakin Alh. Usaini kuma katifar maigadi ya ɗauko bayan mahaifinsa ya kira maigadin ya ce ya bar aikin gidan.
"Salwa wannan rayuwar ce ashe take jiranki shi yasa ki ka kasa kwantar da hankalinki akan rashin samun biyan buƙatar zuciyarki ko?"
Ta ina za ta fara faɗa masa tayi nadama amma a lokaci irin wannan da bata da amfani? Yanzu ta gane cewa idan so cuta ne da gaske haƙuri magani ne. Da ta haƙura da Taj da tuni Mami ma bata gamu da hatsarin nan ba. Everything would have been fine. Rayuwar gidan Alh. Usaini babu daɗi ko kaɗan. Har yanzu bata gabansa, hakan bai dame ta ba kamar yadda ta zame masa wajen huce haushi idan ya fita bai samo komai ba. Mahaifinsa bai barshi da komai ba sai gidan nan albarkacin auren da ya yi. Duk inda yake ajiya a banki ya sa an rufe masa da dogon gargaɗi akan kada ya kuskura ya tada maganar.
"Na san irin wadaƙar da kayi min da dukiyata. Idan zan bi kayana na tabbata baka da kuɗin biyana saboda haka magana ta mutu a tsakaninmu. Duk ranar da ka dawo mutum ni kuma nayi maka alƙawarin dawo maka da komai naka. Idan ba haka ba kuwa sai dai ka jira gado in na riga ka."
Yanzu rayuwarsa ta koma bibiyar abokai da tsofaffin yaransa yana maula. Wataran a dace wataran kuma a wulaƙanta shi. Da ya gaji ne ma ya goranta mata rashin gara da kayan ɗaki. Ita kuma saboda ɗanyen kai ta kira Anti Zabba'u. Ranar anyi sa'a ƙanwarsa ta zaga ta bayan idon iyayensu ta aiko masa da kaji da jallof ɗin shinkafa ta gaske. Kafin ya dawo daga wajen abokinsa sun cinye tas. Ita kanta Salwa bata ko ɗanɗana ba. Tana ta magiyar kar su taɓa aka rasa mai sauraronta ma. Ɗan uwa aka ce rabin jiki. Ahmad ya tausaya mata sosai. Kayan ɗaki da electronics babu abin da bai tanadar mata ba amma ta watsa masa ƙasa a ido.
Suna zaune ya danne fushinsa yana ta yi mata nasiha tana ta kuks sai ga Alh. Usaini. Takalman namiji kawai ya gani ya yi jifa da ledar hannunsa ya zare belt ya afka musu. Salwa na ganin shi ta tashi ta tsaya a gaban Ahmad ta bubbuɗe hannuwa da ƙafafu ta kare shi. Ai kuwa belt ta sauka a jikinta ta gantsare don azaba. Ya sake ɗagawa karo na biyu Ahmad ya miƙe. Kwarjini da cikar mutumtakarsa su ka sanya Alh. Usaini yin laƙwas kamar dafaffen alayyahu.
Ahmad ya riƙe belt ɗin tare da hannunsa ya nuna masa Salwa.
"Duk abin da za ka yi, musamman wanda ya shafi mu'amala da mutane kaji tsoron Allah. Da kai da ita da gurɓatacciyar rayuwarku ku ka haɗu amma hakan ba yana nufin da ita za ku ƙare har ƙarshen rayuwa ba in kun so."
Ficewa yayi ko waige babu. A waje yaci karo da ledar da Alh. Usaini ya yar. Taliya ce leda ɗaya sau mai, maggi da kayan miya na naira ɗari biyu. Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Yanzu Salwa ake ciyarwa a haka? Lallai kowa yaƙi sharar masallaci zai yi ta kasuwa.
Ya koma gida cike da damuwa. Ya kira Abban Salwa akan maganar kayan ɗaki ya ce ya rabu da ita. Darasi yake so ta koya a cikin auren nan. Hujjojin da ya bashi duka ya gamsu da su. Duk da haka washegari ya tura ƴar ƙurƙura gidan shaƙare da kayan abinci.
"Idan da kuɗi a wayarka don Allah ka bani aro na kira Yaya Ahmad nayi masa godiya."
Tsaki ya banka mata ya tashi ya fita da sauri ya bi bayan mai ƙurƙurar nan da gudu. Sai da ya kusa ƙarshen layi ya tsaya. Yana faman haki ya ce ya taimaka masa da numbar wayar wanda ya aiko shi. Mutumin ya karanto masa ya kwafa. Da numfashinsa ya daidaita ya kira shi.
"Dama godiya na kira nayi maka."
"Ku dai ku ji tsoron Allah daga kai har Salwa. Rayuwar da kuke ciki Allah Ya azurta masoyanku da fin ƙarfinta. Cikin minti guda za a iya canja komai ma rayuwarku amma Allah bai bayar da iko ba. Hakan kaɗai ya isa ya zame muku izina. Allah Ya kyauta."
Tunawa yayi da wani kalamin da yaji daga bakin Abban Salwa wanda shi kuma Baban Alh. Usaini ne ya faɗa masa a lokacin da ya nemi shawararsa game da makomar rayuwar yaran nasu.
"Yunwa, ƙishi da rashin kayan more rayuwa zai sa su yi laushi harma ka ga nadama nan ba da jimawa ba a tare da su. Biyewa wannan ba ƙaramin ganganci bane. Yunwa ta ishi kowane shege darasi. Yanzun nan za ka ga mutum ya shiga taitayinsa. To amma fa ƙoshi shi kuma yana fito da ɗan iska cikin mutane. Da zarar tumbi ya ɗauka sai kowane rashin daraja ya biyo baya indai mutum ba nagari bane. Shin Alhaji ba ka ganin yadda almajirai su ke rashin mutumci a unguwa idan abinci ya wadace su? Wani fa a ƙofar gidanka zai zubar da abinci ya ce ka bashi gaya ko babu nama."
Abban Salwa ya gyaɗa kai "wannan gaskiya ne."
"Ina son Usaini amma nafi son gyaruwarsa. Idan mu ka yi saurin karaya akan su to ka sani komawarsu gidan jiya abu ne mai sauƙi. Irinsu bayan addu'a da nasiha dole a bari su gane cewa kyautatawa ce daga Allah privileges ɗin da su ke samu ba wai dolensu bane don sun isa. Suna buƙatar duniya tayi musu atishawar ƴan tsaki!"
Abu ne mai wuya iyaye su iya ɗauke kai idan ƴaƴansu su ka shiga irin wannan yanayin to amma fa wani lokacin dole a tauna tsakuwa don aya taji tsoro.
***
"Zancen Port Harcout naji tana yi a waya wallahi. Don Allah kayi wani abu kafin ta ƙarasa shiga duniya mu shiga uku."
Iyaa ke wannan maganar da Baba Maje tana kuka sosai. Sababbin tsare-tsare Baba Maje ya kawo cikin gidan bayan fitowar Ummi daga police station. An karɓe babbar wayarta sannan ba a barinta ta fita ko ƙofar gida. Ƙawayenta tun daga soro ake sallamarsu. Dangi kuma aka sami abin so. Kowa ya buɗe baki a gidan biki ko suna zancenta ake yi ana aibata halinta. Isassu ma har gidasu ke zuwa su faɗi maganganu son ran su. Yarinya a cikin gidansu ta zama mujiya. Tsangwama ta ko'ina fuskantarta take yi.
Watarana Iyaa ta fita sai tayi mantuwa. Ta dawo za ta wuce ɗakinta sai taji Ummin tana waya tana faɗawa wanda su ke magana ya saya mata ticket ɗin luxurious bus za ta fito nan da kwana huɗu. Iyaa ta sulale ta fice bata bari ta san da zuwanta ba. Sai dare ta sami Baba Maje ta faɗa masa.
"Ummi tamkar ba jinin mu ba. Yarinya sai azabar taurin kai da son zuciya. Duk abin da yake faruwa bata saduda ba" Tana kuka tayi maganar.
"Kada ki yi furucin da zai kai ki ga nadama akan Ummi. Ni dai na fahimci hanyoyin da muka ɓullo ba za su haifi ɗa mai ido ba. Ina kuma tsoron ace jini na ta shiga duniya."
"To yanzu meye abin yi?"
"Aure zan yi mata."
"Da wa? A dangin mu wa za ka tursasa ya bari ɗansa ya aureta?"
"Kofur Ɗanliti zai auri Ummi" Baba Maje ya faɗi da wani sense of relief.
Iyaa tayi shiru kafin daga bisani ta ce "haka ne."
"Ko kina da wata shawarar? Irin wannan auren ba shi mu ke yi mata sha'awa ba tsakani da Allah."
Magana su ke yi ƙasa-ƙasa cikin alhini gwanin ban tausayi.
Iyaa ta numfasa "yanzu za ayi ta aibata auren ana yamaɗiɗi da mu a cikin dangi da unguwa idan aka ga mijin da ta aura. Wasu ma su ce Allah Ya ƙara pi."
"Sai mu toshe kunnuwanmu tunda ba a canjawa tuwo suna. Mune dai iyayen Ummi duk inda za a je a dawo."
"Amma kana ganin za ta zauna? Mutum irin Kofur ɗinnan yana da abin riƙe mata sama da guda?"
Shima kansa Baba Maje ba wai son zaɓin nasa yake yi ɗari bisa ɗari ba. Da babu ne dai gara babu daɗi.
"Haka za mu haƙura don sau dubu gara ace abinci ne bata da shi a gidan miji da dai ta shiga duniya. Indai da rai da lafiya ba zan bari yunwa ta kama ta ba alfarmar Annabi SAW."
"Wahala za ta ƙaru a kan ka. Ba gara mu nemi wata dabarar ba?"
"Ummi bata jin magana kema kin sani. Kuma wannan shawarar da na yanke ba rashin so bane ya janyo. Ban san yaya lahira take ba amma a iya abin da Allah Ya hore min in ji a duniya game da iyalina, sai nake ganin ko aljanna na samu ba zan ji daɗinta ba idan wani cikinku bai riskeni ba a can. Ina tausayin makomar ƴata idan ba ta yiwa kanta karatun ta nutsu ba." Kawai sai ya soma hawaye.
Kusa da shi Iyaa ta koma su ka riƙe hannu suna kuka mai ratsa zuciya.
"Bawa baya sanin matsayin ibadarsa sai ya koma ga Allah. Kuma muna yi ne cikin kyautata zato da cikar yaƙini to amma bamu san baɗini ba. Yaya kike ji za ta kasance ace duka gidana babu wanda ya dace balle ya ceci sauran? Ai ance ana bawa salihan bayi ceto ko? Shi yasa na damu sosai."
"Kafin ma a kai ga lahira ba ka ganin kamar iyalin Habibu sun ja baya da mu? Ka duba fa hatta aikin da aka yiwa Jinjin sai Baballe ne ya ji a wajen Zinatu."
"Kai anya kuwa? Kada mu ɗauki haƙƙinsu." Baba Maje ya faɗi duk da yafi yarda da zancenta.
A sanyaye ta ce "nima bani da tabbas, hasashe ne kawai duba da abubuwan da su ka faru. Ka san Allah da Siyama ce ta auri yaron da ya fito daga irin gidan nan namu sai na sa an sako min ita. Zan ji tsoron kada Ummi ta cutar da ita."
"Kamar kin shiga zuciyata. Ina ta tunanin ko dai in sa ya sauwaƙe mata. Ƙila sun kasa faɗa mana ne saboda kawaici."
"Allah Yasa bai taɓa musu ƴa ba. Ka san yaran yanzu da mugun rashin haƙuri."
"Zan tuntuɓe shi. Tunda auren dama ba na soyayya bane. Zumunci mu ka so ƙullawa kuma da alama ba zai yiwu ba."
Wani abu Ummi taji ya wuce mata mai ɗaci. Ta juya a hankali ta koma ɗakinsu. Ɗazu ta ga fitar Iyaa sai ta zargi ko ta ji wayar ds tayi. Shi ne ta biyo ta da Babansu ya dawo. Jikinta ɓari ya dinga yi har ta isa ta faɗa kan gado. Da yake zuciyar ta jima babu tunanin komai sama da son kai, hassada da sharholiyar duniya, sai ta kasa kuka. Ta kuma rasa addu'ar da ya dace tayi. Haushin kanta kawai take ji da takaicin jin wayarta da Iyaa tayi.
*
Kofur Ɗanliti har gida ya zo neman auren Ummi bayan fitowarta da kwana ɗaya. Ta zauna ta sille shi da rashin albarka iri-iri. Baba Maje sai ya bashi haƙuri ba don komai ba kuwa shi ne yadda yake gudun me zai je ya dawo. Ummi idanunta a buɗe suke. Kada tayi wa Ɗanliti abin da auren zai zo ya mutu da wuri. To amma da alama zai iya riƙonta duk botsarewarta. Haka dai yake gani amma bashi da tabbas. Saboda haka bayan shawararsu da Iyaa, sai ya kira shi su ka yi magana.
"Me yasa kake son auren Ummi duk da ka san wani abu cikin halayenta?"
Ɗanliti ya yi murmushi da confidence "ina sonta ne Baba."
"Me yasa kake son mace irinta?"
"Haɗi daga Allah. Kuma da naji laifinta sai na tuna da tawa samartakar." Gyara zama ya yi domin jindaɗin abin da zai faɗa.
"Baba ni fa tsohon ɗan daba ne."
Kallon Baba Maje yayi yana jiran ganin tsoro ko firgici sai yaga babu ko ɗaya. Neman ƙarin bayani kaɗai yake iya gani. Ɗanliti sai ya yi masa tun kafin ya tambaya.
"Nayi dabanci da shaye-shaye sannan na taɓa tsibbu." Baba Maje yaji hankalinsa ya tashi amma kuma a yanzu dai bashi da wani zaɓi.
"Abubuwa ne da na san za ka sami labarinsu idan ka tashi bincike a kaina shi yasa nake faɗa maka. Na riga na tuba tuntuni ina aiki kamar yadda ka sani."
Wata zuciyar tana ƙwanƙwasarsa akan ya fasa yayinda wata take tuna masa da me zai iya faruwa idan Ummi ta shiga uwa duniya.
"Na baka amanarta. Don Allah idan ka ga abin yafi ƙarfinka ka dawo da ita gida. Bana son a kai ƙadamin da za ta gudu domin yanzu ma iƙirarin da take kenan." Yanayinsa ya nuna tsantsar damuwarsa "ba na son zama abin nuni da kwantace ace ƴata ta shiga duniya."
"Ba za ta shiga ba da yardar Allah. In Allah Ya so sai kayi alfahari da bani ita."
Da daddare a ranar ya faɗa mata shirinsa a kanta bata ce komai ba. Abin ya bashi mamaki sosai. Haka dai yana ta tsoron kada a wayi gari ta gudu kafin auren amma yaji shiru. A fuska da baɗini bata son auren amma ta rasa gane me yasa ta kasa kataɓus. Auren tubabben ɗan tsubba zata yi bata sani ba. Surkulle da siddabaru babu wanda bai iya ba, kuma babu wanda bai shirya yi ba a kanta domin ya samu ta zauna dashi. Ko bayan zuwansa na farko ba wai haƙura ya yi ba, shiri ya tafi sakewa.
Ƴan uwan Baba Maje da ya neme su akan bikin sun yi murna ƙwarai. Ashe kowa na tsoron kada ya roƙi alfarmar haɗata da nasa ɗan saboda mugun halinta. A ranar da ya kamata ta gudu, a ranar aka shafa fatiha tsakaninta da Kofur Ɗanliti.
***
BAYAN WATA UKU
Taj da Kamal sun duƙufa aikin gyara ko ace jeren sabon gidan Abba Habibu da Yaya. Hawa na uku kuma na ƙarshe a ginin gidan abincin da aka bashi ya mayar gida. Ko sisi basu bari ya kashe cikin kuɗin da Dr. Hadifi ya ba shi ba. Iyalin Alh. Hayatu musamman Kamal su ne suka yi komai.
An sallamo su daga asibiti jiki ya yi kyau sosai. Duk da haka Taj ya hana shi ayyukan ƙarfi. Shi da Abba su ke ta kai komo. Abba Habibu da Alh. Hayatu kuma sun fita ana ƙarasa cike-ciken takardun shaidar mallaka da sanya hannun hukumomin da su ka dace.
A can gidan da Alh. Hayatu ya kama kuma Inna Luba da Baba Malam (Alhaji ne ya biya masa) sun iso kwana biyu da su ka wuce. Su Amma da Yaya Babba ma duk sun
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 46