Share this page
cike take da duk wani abu da yake muradi a wurin mace. Ga ƙarin kwarjini da nutsuwa da yake da yaƙinin tana da su daga yanayin tafiyarta. Wayar da yake son ɗauka tuni ya manta da ita har ta katse. Kamar ana ingiza shi ya bi ta. Idanunta a rufe lokacin da ya hangota. Ta sanya hannu ta rufe kunne tana karanto abin da ta haddace. Sannu a hankali ya dinga takowa gabanta har ya rage babu nisan kirki a tsakaninsu. Ƙamshin da Hamdi taji yana ta kusanto ta ne ya hanata buɗe ido. A zuciyarta ta gama tsorata don an saba faɗin akwai ƙwanƙwamai a bayan Admin block. Wai ba a ganinsu sai dare. To me ya fito dasu da hantsin nan lokacin da ake ta kai kawo a makarantar? Taj na jin yadda ta ja numfashi ta kasa saukewa da ya matso. Ya saki murmushi. "Buɗe idonki." Hamdi ta tsuke baki don in ta sami wuri akwai tsiwa. To yau dai aljanu za ta nunawa bata tsoronsu don kada su maketa a banza. Ta sha jin labarin idan baka nuna tsoronsu ba, ba sa yiwa mutum komai. "Anƙi ɗin. Tsakanina da aljani nan gani nan bari. Na riƙe Ayatul Kursiyyu." Dariya Taj ya yi a hankali ya a jin wani irin abu na bin jikinsa. "Ni ba mai cutarwa bane so you can open your eyes." Ido ɗaya ta ɗan buɗe a hankali ta tabbatar mutum ne sannan ta buɗe ɗayan. A lokaci guda idanuwansu su ka sarƙe cikin na juna sai dai Hamdi bata iya zurfafa kallon ba ta kawar da kai. Babu abin da zai sa ta iya jurewa kallon idanun mutumin dake gabanta masu kaifi da su ka tsareta. A zuciyarta kuwa sai da ta kira sunan Allah saboda tunda take bata taɓa ganin wani namiji taji ina ma ace....ba sai a kan wanda yake gabanta. A daidai lokacin su ka ji sanarwa ta sipika. "Bayan wannan gajeriyar diramar da za ayi mana mai taken Ilimi a Karkara, za mu saurari speech daga bakin overall student ɗin makarantar nan Hamdiyya Habib." Wani haɗaɗɗen ruɗani Taj ya gani a idanun yarinyar gabansa. Da haka ya gane ita ce aka ambaci sunanta. Takardar hannunta yaga ta kalla kamar za ta yi kuka. "Kin taɓa ganina?" "A'a." "Good. Ki yi imagining ni ne duka mutanen wurin can sai ki yi speech ɗin naki na ji." Kamar ta ce a'a sai dai ta gyara tsayuwarta. Ta rufe ido. "Open your eyes and think of ..." ya kalleta "Wa ki ka fi so a duniya?" "Iyayena." "To ni ne su. Ki sa a ranki su kaɗai ne a wurin." Sallama tayi da rawar murya ta soma da gabatar da kanta amma ta kasa faɗin sunanta ma. Sai komawa baya take yi. Taj ya karɓi takardar ya dunƙuleta a cikin hannunsa bayan ya karanta a gurguje. "Bayan godiya ga school da iyayenki za ki bawa students shawarar karatu. Do you realy need a paper to say all that?" Hamdi ta ƙifta idanu "no." "Then say what you truly want to say from your heart. You will be fine in sha Allah." Haka kawai magana da shi ta sanya mata wata irin nutsuwa. Ta tattare doguwar rigarta sama kaɗan ta dube shi da murmushi a fuskarta. "Thank you." Ya so sake cewa wani abu amma tunawa da ya yi tana buƙatar nutsuwa kafin ta iya yin abin da ke gabanta sai ya barta ta tafi. Ya raya a zuciyarsa idan an gama taron zai nemeta. RAYUWA DA GIƁI 10 Batul Mamman💖 *** Numfashi ta sake saukewa a hankali bayan ta karɓi loudspeaker ɗin sannan ta rufe ido ta buɗe da sunan Allah. Da ido ta lalubo Taj wanda har ga Allah tayi matuƙar mamaki da ta iya gano shi a cikin mutane. Bata sani ba ko hakan yana da alaƙa da sahun gaba da ya dawo ya tsaya a jikin ƙarfen canopy bayan kusan kowa a zaune yake. Ya yi mata murmushi gami da gyaɗa kai kamar mai bata damar yin magana. Mantawa tayi da kowa da komai ta yi taƙaitaccen speech ɗinta mai ma'ana wanda kalmominsa su ka dinga zuwa kamar daga sama. Wuri kuwa ya kaure da tafi. Ɗalibai ƴan ajinsu su ka dinga kiran sunanta da ƙarfi suna tafi. Haka kawai tauraruwarta ta ƙara haske a idanunsu tun bayan da ta kare martabar iyayenta. Idanunta lokaci lokaci su na kan Taj har ta gama. Tana addu'ar gamawa taga Taj ya kalli wayarsa sai ya kara a kunne ya bar wajen. Za ta sauka aka dakatar da ita. Mai Girma hakimin Gabasawa da kansa ne zai bata kyaututukan da aka tanada dominta. Wani ƙayataccen kwando ne aka saka komai aka lulluɓe da ledar ado aka ɗaure. Ya miƙa mata aka yi musu hoto tare sannan ya ce tasa kyautar ita ce kujerar Makka a Hajjin shekara mai zuwa in sha Allah. "Allahu Akbar" Malamin da yake MC ya faɗi, sai ɗalibai da iyayen yara su ma su ka amsa. Murna a wajen Hamdi kuwa ba a cewa komai. Ta sauko daga stage ɗin idanunta cike da ƙwallar zallan farinciki. Wurin da su Sajida su ke zaune ta nufa da sauri. Banda Sajida da Zee harda ƴaƴan ƴan uwan Abbansu mata tsararrakinsu. Halifa ma ya baro ɓangaren maza aka yi murnar tare da shi. "Hamdi ina kayanki? Yaya ta ce kada mu yarda mu wuce ƙarfe biyu nan." Halifa ya ƙara da cewa "ana can ana haɗa miki ..." Kafin ya gama magana Zee ta dage ta doke masa ƙeya. "To fesal uban zance." Hannu Hamdi tasa ta saƙalo kafaɗarsa tana dariya "rabu da ita Halifa. Idan ka faɗa min me ake yi zan bar maka duk ragowar provision ɗina." Da sauri Zee ta riga shi faɗa. "Walimar ƴan gida za ayi miki" "Kin dai ji kunya wallahi. Da kayan ƙwalama za a sayeki cikin sauƙi" cewar Sajida tana taɓe baki. Kayan nata ta nuna musu su ka haɗu da cousins ɗin nasu aka kwaso cikin ƙanƙanin lokaci. Ta koma cikin ƴan uwanta ɗalibai aka yi hotuna harda malamai da musayar lambobin waya. Wasu harda kuka sosai. Ita dai bata yi ba don sabon da tayi da abokan karatun nata na iya lokacin jarabawa ne. Kewar rayuwar makaranta tafi damunta. Duk abin da take yi hankalinta yana komawa ga tunanin ina mutumin nan na ɗazu. Ta gaji da juyawa ko za ta gan shi Allah bai yi ba. Ga Sajida ta damu su tafi don ita za a yiwa faɗa idan su ka ɓata lokaci. Haka ta tafi zuciyarta tana begen sake ganin sa. * Wayar Amma ce ta sake shigowa, ita ce dalilin da yasa ya bar wajen. Kuka take yi wanda ya matuƙar tayar masa da hankali. Ta sanar dashi surukarta Hajjo ta ce lallai ta zaɓi tsakanin aure da aiki amma ba za ta haɗa biyu ba. Mijinta shekarsa huɗu da ritaya ya koma gida gabađaya. "Wai zaman me nake yi a nan. Taji an ce kai ma ka dawo." "Ba ki faɗa mata ba daɗewa zan yi ba?" "Nayi mata bayani duk taƙi ji. Yanzu don Allah 7 months to my retirement sai nayi resigning? An yi min adalci kenan?" Ta maza ya yi bai nuna mata damuwarsa ba ya dinga rarrashinta. Da ƙyar ta haƙura bayan ya yi mata alƙawarin zuwa Abuja ya sami Hajjo a gidan mijin Amma ɗin inda take zama da amaryarsa da yaransa. Yana dawowa cikin ƴan uwansa Firdaus ta janye shi tana ta nunawa ƙawayenta Uncle Taj. Daga hoto ɗaya sai da aka yi yafi goma. Masu ƙyasawa da yawa su ka kasa ɓoyewa. Shi dai ya biye mata ne kawai saboda ko a cikin jikokin gidan ita ce ƴar gaban goshinsa. Indai ana hutu tana yawan kiransa. Ana hoton da hayaniyar amma idanunsa yarinyar nan Hamdiyya Habib su ke nema. Da bai ganta zuciyarsa bata kawo komai ba tunda yana da yaƙinin Firdaus ba za ta kasa saninta ba. Bai san Hamdi bata da ƙawa ba. In ka cire sunanta ko sunan unguwarsu babu wadda ta sani. *** Washegari jirgin ƙarfe bakwai ya bi zuwa Abuja. Idan buƙata ta biya so yake ya dawo a ranar don yanzu ya matsu ya koma wurin Amma. Da yake tun dare ya sanar da Daddy mijin nata cewa yana tafe, yana isa direba ya zo ya ɗauke shi. Iyalan gidan ba baƙinsa bane tunda su na yawan kai ziyara America har Hajjo. Ƴan mata uku ne ƴaƴan kishiyar Amma da ake kira Anti. Su ma duka sun saba da shi. Dama tun zuwansa yana son tahowa Abujan su gaisa amma aiki ya hana. Tarba mai kyau ya samu daga Antin da ƴaƴanta. Sai da ya ci abinci ya ƙoshi sannan aka yi masa ido ɗakin Hajjo. A hakimce kan kujera ya sameta ta kashingiɗa tana danna remote. "Wannan zuwan na san na Jamila ne ba don neman albarkar tsofaffi ba." Taj ta sosa ƙeya "tuba nake Hajjo tawa ni kaɗai." Ƴar tsohuwar ta yatsina fuska "bana son daɗin baki. Ai da uwarka Jamila ce a gidan nan ba za ka saka aiki a gaba ka kasa zuwa ba." Anisa babbar ƴar Anti ta nuna rashin jindaɗin wannan furuci "abin kuma harda zagi Hajjo?" "Fita ko ban guri ai ba kiranki nayi ba." "Ya Taj na biyo." Hajjo ta haɗe fuska tana neman abin duka "Duk gidan nan babu wanda ya isa ya yi min iko da ɗaki saboda haka get out." Taj da Anisa su ka saka dariya. Ita tana cewa "yeeyyyy, Hajjo ta tuno zama cikin turawa." "Zan zagi babanki wallahi. Zo ki fice." Kafaɗa Anisa ta noƙe ai kuwa Hajjo ta bita da daƙuwa hannu bibbiyu. "Na iyayenki su uku." Alamun rashin jindaɗi Anisa ta nuna wanda Taj ya lura. Da ka ya yi mata ishara ta fita daga ɗakin. "Hajjo sai ki yi ta zagar mana iyaye saboda Allah? Kinga bata jidaɗi ba daga ɗan yin wasa da kakarta." Lura tayi shima kamar bai jidaɗin ba sai kuma ta saki fuska. Ita a dole Taj ne kaɗai jikanta namiji na wajen babban ɗanta. Tunda ya koma hannun Amma bata taɓa canja masa ba. Saboda tun asali dama kakarsa wadda ta haifi Alhaji da ita ƙawaye ne da su ka yi ƴan matanci tare. Ita ta fara zayyano masa ƙorafinta akan zaman Amma ita kaɗai a gida ga mijinta a wata uwa duniyar. "Saura bai fi sati uku ba na koma in sha Allahu. Kuma zan zauna har tayi ritayar. Ai na san zamana ne sharaɗin da yasa ki ka yarda ta cigaba da aikin." Hajjo ta ƙara sakin fuskarta saboda Taj akwai iya tsara zance. "Ka san ita mace bata tsufa da buƙatar kulawa. Yau ko ƙwan fitila ne ya mutu wata idan babu namiji a gidan sai dai ta zauna a duhu." Haƙuri ya sake bata da yaga ya samo kanta kuma ya yi mata bayanin gininsa da ya yi nisa. "Shi uban taurin kan har yanzu baku daidaita bane?" Dariya Taj ya yi. Kamar ba ita ta nuna ta daina ƴan mintuna ƙadan baya ba. "An dawo kansa kuma?" Ko a jikinta ta ce "Ai Hayatun ne akwai wuyar sha'ani sai ka rantse ni na haife shi. Don ita babar tasu haka take ba cas ba as." "Ahhhh. Ni fa Hajjo zan tashi wallahi. Harda kakata kuma." Yadda ya ɓata fuska sai da tayi dariya. Daga nan aka kashe maganar dawowar Amma. Sai kuma ta sako zancen da yake cin ranta. Dama can ba dawowar Amman bace a gabanta. Tafi kowa sanin halinta tunda a gabansu ta tashi. Ita ce ma ta haɗa auren nata da ɗanta. Da gangan ta tayar mata da hankali yanzu kawai don Taj ɗin yazo. Don tayi imanin indai yaji ba zai ƙasa a gwiwa ba zai zo neman sulhu. "Tajo." Babu yadda ya iya. Dole yake amsa sunan nan da baya son a faɗi indai daga bakinta ne. "Nace wai me zai hana ka nemi ƙanwarka Anisa ku daidaita? Karatunta sai gudu yake har an shiga aji huɗu a jami'ar nan." Gabansa yaji ya faɗi. Duk kirkin Hajjo kowa ya san rigimammiya ce ta buga misali. Yanzun nan sai ta yiwa mutum dabaibayin da zai sarƙe wuyansa bai sani ba. Ƙofa ya kalla tana gama maganar "Hajjo daina faɗa kada ta zata gaske ne ta soma jin haushina don na tabbatar ba za ta rasa masoyi ba." Shan kunu tayi harda yi masa daƙuwa. "Ƙaniyarka Tajo." Ya sunkuyar da kai yana sauraron sababinta. "Da akwai wanin ai ka san ni ba mai yiwa jikoki shisshigi bace. Sannan na tabbata da daga cikin Jamila ta fito ba ma za ka ce komai ba." Hankalinsa tashi ya yi ya miƙe tsaye yana ɗan tausar kafaɗarta. "Allah Ya huci zuciyarki. Ba haka nake nufi ba." "Za ka yi mata maganar ko na kirata yanzu?" Gani ya yi za ta rushe masa ginin da bai fara saka tubali ba akan yarinyar nan Hamdiyya. Shi yasa da saurinsa ya ce ta bari shi zai yi. "Alƙawari fa za ka yi min." "In sha Allahu zan yi mata magana." Tana jin haka ta washe baki hankali kwance. A ranar da washegari da zai taho bata sake tada wata rigimar ba. Daddy kawai ta kira ta ce masa tayi mai wuyar. Ya fara shiri don ba za ta zuba ido ya bar ƴan mata a gabansa babu aure ba. Da yaji waye zaɓin da ta yiwa Anisa sai taga ya fita farinciki. Kuma da murnarsa ya kira Amma ya faɗa mata. Sai ta nuna masa ta fishi jindaɗi domin ita ba butulu bace. Duk wata gudunmawa da ta dace financially da morally ya bata wajen kulawa da cikar burin Taj. *** Rayuwa ta fara tsanani ga iyalin Abba. Da yake mutum ne mai sakarwa iyali aji daɗi da abin da Allah Ya hore masa, yanzu da ajiyar ta soma ƙasa sai suke ƙuntata. Yawancin samunsa in ka cire buƙatun gida to anyi amfani dasu wajen tarin kayan ɗaki da yake yiwa ƴan matansa. Komai na mutum uku yake saya. Yaya bata san yiwa ƴaƴa komai ba ta wannan fannin don bata sana'ar komai. Tun da ƙuruciya babu irin nacin da bata yi ba amma sam yaƙi yarda tayi saboda a cewarsa ta gama aikinta da ta aure shi. Nan kuwa yana tausayin lafiyarta ne. A ganinsa rashin imani ne zai sa ya sanya rai da ta dinga neman kuɗi a yanayin da take ciki. Gashi dama bai tsira daga dariya da surutun mutane ba. Idan ya bari tana shiga jama'a da sunan sana'a babu mamaki a karyar mata zuciya da zancen lalurarta. Shi yasa ya yiwa tufkar hanci da wurwuri. Sauƙinsu ɗaya yanzu a gidan shi ne kitson da Sajida take yi. Hamdi kuma satinta biyu da dawowa gida Anti Labiban Abuja da ta zo Kano ta roƙi alfarmar tafiya da ita idan za ta koma. Kowa ya san miskilancin Hamdi idan ta so. Suna ta zaton za ta ƙi. Sai gashi da kanta ta amince za ta bita. Weekend na zagayowa kuwa su ka tafi. * Abin haushi da takaici da Taj ya tambayi Firdaus game da yarinyar da ta kasance overall a makarantarsu wai bata san komai a kanta ba. "Ba ƙawarki bace?" "Hamdiyya ai bata da ƙawa ko ɗaya. Sai da case ɗin babanta ya tashi ne ma ta ɗan sake da mutane." Interest ya nuna na son jin me ya faru da baban nata. Firdaus kuwa ta zage ta kora masa jawabi tiryan tiryan. Har hukuncin da makaranta ta ɗauka akan ƙawayen Ummi tunda ita an cireta. Tana gama jawabin ta tashi tayi gaba abinta. Ta bar shi da shiga ruɗani da mamaki. Ba kuma komai bane ya sanya haka illa tuna sunan mahaifin Hamdi da kuma sana'arsa da Firdaus ta faɗa. Tunani barkatai ya shiga yi game da yadda aka haihu a ragaya. Indai shi ne Habibun da Alhaji yake ƙyamar ya yi koyi da halayyarsa to yaya aka yi ya yi aure? Me ya faru da rayuwarsa? Kuma wace irin rayuwa yake yi yanzu? Tabbas zai so sani. Shi Tajuddin zai so ƙwarai ya shiga cikin rayuwarsa ba don ƴarsa kaɗai da ta tarwatsa masa zuciya ba. Wasu burika ne suka mamaye zuciyarsa wanda zai so ya cimma in har shi ne wanda Alhaji ya sani ɗin. Kwana biyar kacal su ka ɗauka shi da Kamal wurin neman Habibu Simagade na Soron ɗinki. Sai gashi an kai su har ƙofar gidansa. Mutumin da ya rako su magidanci ne amma har su ka isa hirarsa akansa bata wuce alkhairinsa da kyakkyawar tarbiyar ahalinsa ba. "Ai wato banda ance kowa da ƙaddararsa da in kaga wani aka ce maka zai sami sauyin rayuwa sai ka ƙaryata." "Me yasa ka ce haka?" Kamal da Taj bai ɓoyewa komai ba illa son Hamdi ya tambayi mutumin. Shi kuwa ya daina tafiya tare da binsu da kallon rashin yarda. Sannan ya nuna Taj. "Ka ce min kai sana'ar girki kake yi. Ɗan uwanka kuma kasuwanci." "Haka ne." Da faɗa-faɗa ya cigaba da magana "zamanin yanzu ai babu yarda a tsakanin mutane. Da naji aikin naka na zata taimakon Habibu ka zo yi. Shi yasa ma zan kai ku gidan." Taj ya yi murmushi "sana'ar girki yake kenan?" "Watannin baya ba. Kafin ƴan hassada su sako shi a gaba su ka ƙwace wurin da yake haya. Banda haka ko garau garau Habibu ya dafa maka wallahi sai ka ji bambanci." Duk surutun mutumin nan bai ƙara yarda ya đara daga inda yake tsaye ba yana jiran su faɗa masa gaskiya ko su waye su sai ga Abba ya fito. Daga yanayin tafiyarsa da kamanni da ya gani da Hamdi Taj ya gane shi. Kafin ya iso wurin da su ke ya tsaya ya fi sau huɗu yana gaisawa da mutane. Wannan abu ya sake burge Taj sosai har bai san lokacin da haƙoransa su ka bayyana da farincikin da ya shiga ba. RAYUWA DA GIƁI 11 Batul Mamman💖 Yadda ya gaisa da kowa da zai wuce haka ya tsaya su ka yi musabaha da wanda ya rako su. Sannan ya ɗagawa Taj da Kamal hannu yana ɗan ranƙwafawa kamar yadda ya gaisa da sauran mutanen da su ka gani. "Ƴan samari barkanku dai. Ya sanyi sanyi? Ya ayyuka? To Allah Ya yi jagora." Ya dubi mutumin da da ya yi mu su rakiyar ya ce "na barku lafiya." "Dakata Mal. Habibu. Waɗannan fa kai su ke nema." Tsayuwa ya yi ya sake kallonsu sai dai bai tuna taɓa haɗuwa dasu ba. "To Allah dai Yasa lafiya" ya ce muryarsa na raguwa saboda rashin sanin ko ba da alkhairi su ka zo ba. Kamal ne ya amsa masa "lafiya ƙalau." Sannan ya gabatar da kansa da Taj. Jin cewa Taj chef ne kuma a yanzu haka ginin restaurant yake sai Abba ya sami kansa da daina saurin zuwa uzurin da ya fito dashi. Zancen bai wuce fita nema ba dama. "Dama nayi tunanin maganar ba za ta wuce ta ɗaukarka aiki ba. Shi yasa na rako su. Bari na wuce." Abba ya yi masa godiya sosai sannan ya nunawa su Taj gidansa. "Ko mu ƙarasa daga soro mu zauna?" A duk lokacin da ya yi magana sai Kamal yaji zuciyarsa ta karye. Allah Ya sani a yau ya daina ganin baƙin Alhajinsu. Tabbas da wannan rayuwar Taj ya faɗawa da shi ma sai ya yi kuka ba iyayensu ba. Ta yaya zuciya za ta jidaɗin ganin namijin da ya cika a halitta yana irin wannan muryar? Don ma bai san lanƙwasar jikin da sauƙi yanzu ba. Gidan su ka bi shi. Daga soron ya ɗaga murya yana ta kiran sunan Zee amma sai da ya yi kamar sau biyar su ka ga ƴar budurwa ta fito a guje. Don shi Kamal ji ya yi kamar ya taya shi kiran saboda muryar ba ta tashi yadda ya dace. "Abba yi haƙuri ban ji ba ne." Mutanen da ta gani tare dashi ne yasa ta saurin komawa da baya don bata fito da lulluɓi ba. Ta bayan ƙofa ta gaishe su. Su duka biyun yadda tayi ɗin ya burge su sosai. "Tabarma za ki kawo da ruwa." Bata jima ba ta dawo da hijabi a jikinta ta shimfiɗa tabarmar. Abba ya sake gaisawa dasu sannan ya buƙaci jin neman da su ke yi masa. "Kamar yadda ɗan uwana ya faɗa maka gidan abinci nake ginawa. To sai na sami labarinka a wajen mutane. Duk da ba haka ake so ba ance ka rasa wurin sana'arka." "Eh. Amma yanzu ma haka wani waje zan je dubawa. Idan mun daidaita sai na kama haya." Babu wani dogon tunani ko shawara Taj ya ce "hayar kafi so ko za ka iya aiki tare dani?" "Kai da baka gama gini ba Happy? Zai yi ta jira ne har lokacin?" Kamal ya yi saurin katse shi. "Me ya kawo ku wurina tsakani da Allah?" Abba ya tambaya da sakin fuska. "Aiki nake so mu yi tare amma wurin nawa da saura kamar yadda ya faɗa maka. Ina so nayi recruiting ma'aikata da wuri kafin na gama ginin." Kamal da ya yi zaton ganinsa kawai su ka zo yi sai yaji hankalinsa bai kwanta ba. Me yasa Taj yake neman abin da zai ƙara nesanta shi da Alhaji? Ina shi ina aiki da wannan mutumin daga jin ance baya aiki? Abba ya ƙare musu kallo sai ya yi murmushi. Da alama shawararsu bata zo ɗaya ba don yaga irin kallon da Kamal yake yiwa Taj. "Samari nagode amma ina mai baku haƙuri. Ina da mata da ƴaƴa huɗu. Zama haka a yanzu ma yana damuna balle kuma na wasu watanni. Sannan ina da ma'aikata biyar da har yanzu dani su ka dogara." Kuɗi Taj ya ciro daga aljihunsa da sauri. "Zan fara baka albashi tun yanzu kafin mu fara aikin." "Happy!" Taj ya yi biris da Kamal. Shi kuwa bai barshi ba ya dubi Abba da kyau. "Kayi haƙuri don Allah. Bari mu tafi." Taj ya ɓata fuska "Da gaske nake ina son aiki da shi Happiness." Abba sai ya nuna kamar bai ji haushi ba. Yana ƴar dariya ya yi musu godiya kawai ya tashi. Kamal kuma haƙuri ya yi ta bashi sannan ya janye Taj su ka tafi. A mota kuwa kafin su isa gidan Ahmad anyi faɗa kaca-kaca. "So kake Alhaji ya mutu da baƙincikin ka ko me? Kai yanzu rayuwarka tana yi maka daɗi?" "Kai baka ji komai ba da aka ce bashi da aiki yanzu?" "Sai ka taimaka masa da kuɗi." Kamal ya ce har zuciyarsa. "Are you serious? Yanzu da aiki da kuɗi wanne ya fi?" Da wannan cacar bakin su ka koma gidan. Don takaici Kamal ko shiga bai yi ba. A waje ya sauke shi ya tafi. "Masifaffe." Taj ya furta yana harar motar. * Ikon Allah Zahra ta gani yau tun dawowar Salwa gida. Kwananta shida a Bauchi da aka yi musu gajeren hutum mid-semester. Abin da aka bayar da kwana goma har weekend ya kama shabiyu, a daddafe tayi shida ta dawo. Ƙarya ma ta yiwa mamansu wai field work za su je. Da yake Agricultural Extention take karantawa. Nan kuwa kewar Taj ce ta isheta har tana neman zautar da tunaninta. Abin baƙinciki kuma shi ne tunda ta tafi ko sau ɗaya bai kirata ba. Ita ce ma da ta gaji tayi masa waya harda ɗan ƙorafi. "Idan mutum yaje gida baya son damu Salwa. Tunda ba daɗewa za ki yi ba gara duka time ɗin ki ya zama na family." Ji tayi kamar ya faɗa mata magana. Ta daure ta ce "Ba ka cikin family ɗina kenan?" "In ji wa? Idan kin dawo zan baki wayata ki gani a yanzu zan chanja yadda nayi saving sunanki." Zuciyarta ta harba da wani irin farinciki ta ce "me za ka saka?" "Ƙanwata Salwa. Yadda nake saving sunan ƴan gidanmu. Manyan kuma ina saka musu Yayata" Kuma bai barta ta gama jin haushin hakan ba kamar shi ys kira ya ce "bari na barki ki huta haka. Sai da safe." Azahar a Kano tayi mata. Tana zuwa gidan ko hutawa bata yi ba ta karɓi girkin dare. Zahra tana ta faɗa mata ta jira ayi la'asar amma ta ce gara tayi da wuri tunda tuwo ne. Daga nan ta haɗa juice ɗin abarba, mangwaro da ɗanyar citta saboda ta kula Taj yafi son fresh fruit juice. Da su ta taho tun daga Bauchi. Bayan tayi sallar la'asar ta shiga ɗakin Taj. Yana ƙullewa idan zai fita amma baya taɓa zare key ɗin. A cewarsa tunda masu gidan suna da kaya a ciki me yiwuwa za su buƙaci shiga idan baya nan. "Salwa me ki ke nema a nan?" Zahra ta taho da sauri da taji alamun buɗe ƙofar. Tsintsiya ta sameta tana gyarawa ɗauri. Tana ganinta tayi murmushi. "Anti Zahra gyara ɗakin zan yi." Curiosity yasa Zahra ta ɗan leƙa. Baya buƙatar wani gyara na a zo a gani. "Yana gyarawa. Ki fito don yayanki

Chapter 8 of 46