Share this page
da tayi. Cikin jin nauyi ta zauna a kusa da yayarta ta ɗan dafa ta. "Ki yi haƙuri. Kawai gani nayi kina ta wahala da matar da ba wani mutumci ne da ita ba." Da sauri Zahra ta kalli hanyar ɗakin Salwa inda Mami take kwance yanzu. Ilham ta gane tana tsoron kada Mamin taji ne. Sai dai ita ko a jikinta. Mami ta sirewa kowa a gidansu saboda ire-iren rashin mutumcin da ta dinga yiwa Zahra. A haka ma don ba gari ɗaya suke ba. "Na rasa me yasa Mama tace ki cigaba da kula da matar nan bayan ƴar cikinta ma ta gudu. Shima kuma Daddyn Hayat yayi tafiyarsa ya barki." Ta taɓe baki "kada ki ji haushina amma Allah na tuba wace Umra zai tafi alhalin ya bar mahaifiyarsa a wannan halin?" Zahra ta girgiza kai "Ilham indai kin gaji ki tafi kawai." Ilham ta sami waje ta zauna a kusa da yayarta. Jikinta yana bata akwai wata gagarumar matsalar a gefe wadda tasa dole Ahmad yayi nisa da gida a yanayin da ake ciki. "Yaya Zahra me yake faruwa ne don Allah? Ban kai matsayin da za ki faɗa min damuwarki ba?" Sai da Ilham ta zubar da hawaye kamar yadda Zahra take yi bayan ta sami amsar tambayarta. Cikin kuka ta sanar da ita abin da yake faruwa a gidan surukinta. Tayi mata bayanin tsaka mai wuya da Ahmad yake ciki wanda indai bata tausaya masa ba, bai kamata ta ƙara masa damuwa ba. Ga Maminsa a wannan yanayi. Ta sami labarin an saki su Salwa a wajen Ahmad amma har yau bata dawo ba. A gefe guda kuma ga Kamal a kwance, sun samu da ƙyar jiya anyi masa transplant amma daga nan ba za ta ɗorar da komai ba. "Amma Yaya Zahra su da suke da yawa don dai shi kaɗai ya dawo saboda mahaifiyarsa ai bai kamata ya zama laifi ba." "Alhaji ko sunan Mami baya son ji. Kuma kinga abubuwan da Salwa ta janyo musu. I know he feels responsible shiyasa na tabbata nauyin faɗa masa yake ji. Sannan komai na gidansu shi yake sakawa a matsayinsa na babban ɗansa namiji. Wannan ma zai iya contributing." Cewar Zahra a sanyaye. Ilham ta jinjina kai a hankali sai kuma ta kama dariya tana cewa "lallai aure ibada ne. Duk takurar da kike ciki amma kina auna komai ta fuska daban daban da yadda zai yi affecting mijinki." Ta murmusa "na ɗauki wani gagarumin darasi. Na san dole yana alfahari dake" Zahra tayi murmushi "za ki cigaba da tayani zama?" Ilham ta zumɓura baki ta koma ta kwanta akan kujera alamun dai ta fasa tafiyar. Zahra kuwa ta daddage ta kai mata duka a ƙafa sai da tayi ihu. "Me nayi miki kuma?" Ta tambaya tana murza ƙafar. "Tayar min da hankali mana. Wai ni kike yiwa barazanar komawa gida ƴar rainin hankali." Ilham ta tuntsire da dariya "sai ga Yaya Zahra an kwantar da kai ana marairaice murya." Wani dukan Zahra ta kai mata ta miƙe babu shiri ta gudu. A cikin ɗaki, Mami ke kukan zuci ita kaɗai. Ga ƴan uwa, ga ƴaƴa amma babu kowa a kusa da ita! *** A wulaƙance Alh. Usaini yake duban Salwa. Tana durƙushe a gabansa ta fita kamaninta saboda tsabar naci. Shi ko ganinta baya son yi saboda yadda yake jin haushinta. Makauniyar soyayyarta ta janyo tonuwar asirinsa da lalacewar aikinsu gami da korar da mahaifinsa yayi masa. Da azal ta hau shi kuma ranar da aka sako su a titi ya ganta tana tafe tana jan ƙafa. Ya tsaya rage mata hanya da manufa guda...ci mata mutumci akan asarar da ta janyo masa. Sai aka yi rashin sa'a ashe ƙarfen ƙafa ya kwaso. Wani hotel ya tafi da ita yana ayyana azabar da zai gana mata. Ashe ita za ta gana masa. Salwa ta nace lallai sai ya kaita wajen malaminsa. Tana da tabbacin za ta sami kan Taj tunda ta shaida da idanunta yadda wancan maganin ya birkita masa lissafi. Ba don iyaye sun shigo ciki ba da yanzu ƙarshenta an fara shirye shiryen rufe Happy Taj. "Zan yi maka biyayya Alh. Usaini. Duk abin da kake so zan baka banda mutumcina." Murmushi ƙayatacce ta saki sannan ta ɗora da cewa "Taj nake tanadarwa kaina." Wani kallon banza yayi mata yana ɗage hanci kamar tsohuwa zata tsallake lambatu "Wai ke wawiyar ina ce? Ana so dole ne? Banda masifa irin taki waye ma yake ta soyayya yanzu? Life is all about money, money and more money." "Ba za ka gane ba. Wallahi ni Taj ne rayuwata. Idan ban aure shi ba zan iya rasa raina." "Ƙaryar banza. Me ya hana ki mutuwa tuntuni?" Ya ɗan sassauta murya "kinga ki zo ki tafi gidanku don Allah. Hotel ɗinnan sun hana ni fita saboda ke. Naje checking out ance sai mun fito tare don kada na bar musu liability." "Ka taimaka ka haɗamu. Nayi maka alƙawarin ba za ka ƙara jin ko da suna na ba." Wani baƙinciki ya tokare masa wuya. Ya tashi kamar zai kai mata duka sai ya fasa. Baya son janyowa kansa wata sabuwar rigimar. "Wayyo Allah na. Salwa ki tafi kada na illata lafiyarki." "Zan jure. Wallahi ko me zaka yi min zan jure. Ka taimaka min." A hasale ya zauna. Magana da mahaukaci ɓata lokaci ne. Ba don Allah Yasa mata basa gabansa ba da tuni sunan Salwa sorry. Ita ko tsoro bata ji ba take zaune da shi a hotel a ɗaki guda. Safe, rana da dare duka zancen ɗaya ne. Idan yana so tayi shiru sai dai in yana waya. To gashi ta ƙare masa. Duk wani wanda zai roƙar masa mahaifinsa ya yafe masa ya zare hannu a kansa. A halin yanzu bashi da tudun dafawa. Wannan ma yana daga cikin abubuwan da suka kashe masa gwiwar yi mata wani abu. Tunani da damuwarsa sun shallake ƙaramar lalurar Salwa ta son maso wani. Abin da bai sani ba shi ne akwai wata ƙanwar kakarsa ta wajen uwa da ta saka baki akan maganarsa. Ga tsufa ga lalurar ƙafa amma a haka tasa aka kaita gaban mahaifinsa har gida ta bashi haƙuri a madadinsa. Ganin girmanta yasa shi yafe masa. Bayan ta tafi ya saka aka binciko masa inda ɗan nasa yake. Bayan nan aka tabbatar masa da cewa tunda ya shiga hotel ɗin bai fita ba. Abin ka da ɗa da mahaifi. Sai ya tashi da kansa yace ƙanin Usainin ya kai shi. RAYUWA DA GIƁI 38 Batul Mamman💖 Nagode da karamcin ku. SonSo *** Addu'a kam babu irin wadda bakunan ƴaƴan Alh. Hayatu ba su yiwa Yaya ba ta samun lafiya cikin ibadarsu. Hamdi ta zauna ta dinga yi wa Allah SWT kirari tana faɗin buƙatarta. Da ƙyar ta iya baro masallacin saboda shauƙin kasancewa a waje mafi tsarki kuma inda take da tabbacin karɓuwar addu'arta. Sai bayan isha su ka koma Jedda. Ana yi musu tayin tafiya masauki amma kowa ya ce sai sun ga isowar Abba Habibu. Ahmad da yake tracking tafiyarsu ya sami bayanin tsaiko da aka samu da su ka tsaya transit a Egypt sakamakon hazo da ya lulluɓe garin. Haka su ka kasance jugum-jugum ana ta tasbihi a zuci da fatar baki. A can Bauchi kuma mahaifin Salwa bai san me yake faruwa ba sai da Ahmad ya kira shi a waya. Keɓewa ya yi daga ƴan uwansa ya sami wuri ya kira shi. Abban nata bai ɓoye masa rashin jindaɗinsa ba kuwa. "Haba Ahmad. Kai da nake yabon hankalinka, ta yaya za ka bari har a kwashi waɗannan kwanaki kafin ka sanar dani?" Ahmad bai yi mamaki ba. Dole ko wane ne yaji babu daɗi. Shi yasa ya zauna yayi masa bayanin dukkan abin da yake faruwa da gidansu. Baban Salwa ya jajanta masa ya kuma yi masa uzuri. Musamman da yace ya dakata ne daman yana jiran ganin ko zata dawo, kada yayi saurin tayar masa da hankali. "Babu komai. Zan nemeta a waya. Idan ban samu ba ma akwai wani ɗan ƙanwata da zai iya yi min tracing ɗin layinta." "Allah Yasa a dace. Nima zan cigaba da kiranta." Suna tsakar sallama Baban Salwa ya dakatar da Ahmad ya yi masa nasiha mai ratsa zuciya. "Ana canja abokin zama amma kaga iyaye? Iyayen ma musamman uwa, sai dai haƙuri kawai. Na san kana ƙoƙari kuma kana haƙurin amma ka ƙara domin neman albarka ba don ita Mamin taku ba." Ɗacin abubuwan da Mami ta aikata waɗanda suka kawo su wannan lokaci ya dawo masa amma basu bari ya ƙi amsar shawarar ba. "In sha Allahu. Nagode" Da haka suka yi sallama. Ahmad ya koma cikin ƴan uwansa a inda suka taru suna jiran isowar Abba Habibu. *** Daga lokacin da Abba Habibu ya sauka daga jirgi zuwa yanzu da yake fitowa da ƴar jakarsa a hannu, gabansa ya faɗi sau ba adadi. Tunani iya tunani yayi amma ya kasa samun abu guda da zai iya cewa shi ne yake jin ya sami Yaya. Haka ya fito da sassarfa yana jan addu'o'i daban daban. Yana sako ƙafarsa waje ya ɗaga kai yana waige-waige. Abokin Ahmad ya sanar da shi cewa Alh. Hayatu zai turo a ɗauke shi. Shi yasa yake baza idanu ko zai hango guda cikin yaran nasa. Sai dai abin mamaki maimakon ƴaƴan, Alh. Hayatu ya gani da kansa yana tunkaro shi. Wani irin abu mai zafi yaji ya tsirga masa daga tsakiyar kai har tafin ƙafa. Ƙafar ta zaɓi wannan lokacin taƙi motsawa kwata-kwata ma. Yana gani Alh. Hayatu ya cigaba da nufo shi amma ya kasa ɗaga ko da ɗan yatsa har ya iso gaban shi ya tsaya. Da rawar murya Abba Habibu ya ce "Tun a waya na ce da Ahmad ya faɗa min gaskiya yace min da ranta." Alh. Hayatu ya gyaɗa kai da sauri "da ranta Habibu. Iyalin ka tana nan da rai." "To me ya same ta? Ni na san gagarumar matsala ce kaɗai za ta sa ka zo tarba ta a nan." Abba Habibu ya furta helplessly. Alh. Hayatu kasa magana ya yi, sai wata uwar kunya da ta mamaye shi. Abba Habibu bai yi ƙarya ba. Haka nan me zai kawo shi tarbarsa? Mutumin da yake ƙyama yau a dalilin matarsa yana yi masa kallon mafi girman daraja a cikin mutanen da yake tare da su. Kafaɗar Abba Habibu ya dafa ya nuno masa motar dake jiran su "Zo mu tafi Habibu." "Kayya da dai ka faɗa min me zan tarar da nafi samun nutsuwa." Ya kalli Alh. Hayatu da yanayi da yasa dole ya ƙara jin tausayinsa. "Ganin ka a nan da tausasa kalaman ka a gareni sun fi faɗar min da gaba fiye da wayar da Ahmad yayi min jiya. Don Allah ina zamu je? Ko dai da gaske ne an kama ta cikin masu nakasar dake taho wa bara?" Ba a nan Alh. Hayatu ya so sanar da shi ba. A wannan yanayin na tsananin firgici da yake gani a wajen Abba Habibu bai dace ya tsorata shi ba. Gudun tarwatsa labarin a bakin yara shi ne musabbabin tahowarsa. Sai dai kuma har ƙasan zuciyarsa shi ya san babu wani lokaci da ya dace ayi breaking mummunan labari ga makusancin wanda abu ya shafa. Ana faɗa ne kawai idan dama ta samu tare da addu'ar haƙuri da tawakkali. Ba tare da jan rai ko kwaskwarima ba ya sanar da shi gaskiya. "Ƙoda ta bawa Kamal. Tana kwance a asibiti yanzu haka muna jiran farfaɗowarta." Ko cikakken sakan Abba Habibu bai ɗauka ba wajen fahimtar kalaman Alh. Hayatu. Sun yi masa dirar aradu mai ƙarfi. Ga wasu irin tambayoyi suna tsaruwa a kansa cikin karo da juna wurin son fara fitowa. Amma duk da haka sai ya kasa furta ko ɗaya a dalilin tunawa da wayar da Yaya tayi masa tana neman izini. "Yaya jikin Kamal ɗin?" Mamakin wannan tambaya Alh. Hayatu ya yi kafin ya iya cewa da sauƙi a hankali. "To mu je" Abba Habibu ya ɗaga ƙafa yana mai danne tsananin tsoron da ya taso masa. Sai da suka shiga mota Alh. Hayatu ya kasa daurewa ya ce "Ba ka tambaye ni lafiyarta ba?" "Ka manta ka ce min ana jiran farfaɗowarta?" "Haka ne." Ya faɗi yana jinjina kai "to amma ba ka tambayeni komai ba?" "Za ta bani amsa da kanta idan ta tashi in sha Allahu." Abba Habibu ya jingina bayansa da kujera cikin yaƙini. A yayin da wani ɗaci ɗaci ya dinga taso masa na tsoro sai ya dinga faɗin "Hasbunallahu wa ni'imal Wakeel". Ba su ƙara magana ba har su ka isa asibitin. Abba Habibu yana tafiya ne tamkar a mafarki. Yadda aka yi ya iso ƙofar ICU ɗin abu ne da ko an saka masa wuƙa ba zai iya faɗa ba. Bai ma san lokacin da Hamdi ta iso ba sai ji ya yi ta faɗa jikinsa tana kuka. Iyalin Alh. Hayatu kuwa gaishe shi su ke ta yi ya dinga amsawa da sakin fuska. Za ka rantse baya cikin mummunan tashin hankali mara misaltuwa. Sun yi mamakin hakan ƙwarai da gaske. Mafi ƙarancin abin da su ka yi zato shi ne yi blaming ɗin Alhajinsu ya ce laifinsa ne matarsa take kwance a wannan yanayi. Shi dai Abba Habibu bai ma yi la'akari da kallon kallo da su ke yi ba. A lokacin Dr. Hadifi ya iso, Alhaji ya matsa kusa da shi domin nemawa Abba Habibu izinin shiga wajen Yaya. Suna magana a gefe Abba Habibu ya ɗago Hamdi daga jikinsa ya kalleta a cikin ido ya girgiza kai. Bai yi mata magana ba a lokacin sai ya ja ta gefe ɗan nesa da sauran. "A gabansu ki ke wannan kukan Hamdi? So ki ke su yi zaton kina baƙincikin sadaukarwar mahaifiyarki ga ɗan uwansu?" "A'a" ta girgiza kai da sauri. "Haka za su yi zato idan ba ki yi shiru ba mana." Hannuwansa riƙe da nata ya rarrashe ta " Don Allah kada ki sa su ji a ransu kamar sun yi wa kowa laifi. Wallahi da izini na ta bayar." "Abba da izinin ka?" A gurguje ya faɗa mata wayar da su ka yi sannan ya cigaba da cewa "farinciki da nutsuwar zuciyar da zamu nuna musu shi ne zai yi nuni da cewa mun girmama wannan kyakkyawan aiki da tayi." Duk wannan bayanin da Abba Habibu yake yiwa Hamdi ashe a kunnuwan Alh. Hayatu, Hajiya da Taj yayi. Sun biyo bayan su ne a zaton su faɗa zai yiwa Hamdin. Hamdi ta sanya ƙasan hijabinta ta goge idanunta. Cikin muryar kuka ta ce "Abba ina tausayinta ne kawai. Ga yanayinta ga ciwo. Gani nake kamar shi yasa ita bata tashi ba." A wannan halin ya ƙirƙiri ƴar raha domin kwantarwa ƴarsa da hankali. "Kada ki raina min mata mana Hamdi. Ta haife ku ku huɗu rigis sannan ki dinga tunanin wannan zai bata wahala? Ko an faɗa miki kowa ma rago ne irin ku?" "Kai Abba..." ta faɗi tayi murmushi akan kumburarriyar fuskarta dake jiƙe da hawaye. Hajiya bata san lokacin da tsananin tausayi da girmansu yasa ta sake fashewa da kuka ba. Hakan ya bayyana musu cewa ba su kaɗai bane. Ta rungume Hamdi tana rarrashinta amma kuma ita ma ɗin kukan take yi sosai. Alh. Hayatu ya kira Abba Habibu ya kai shi gaban Dr. Hadifi. Nan da nan aka shiga ciki da shi. Aka bashi riga da dukkanin kayan kariya ga mara lafiya domin kada a shiga da baƙuwar cuta. Sai da ya shirya tsaf aka bashi damar ƙarasawa gaban Yaya. Sannan Alh. Hayatu ya matsa gefe yana kallon what it truly means to be a great person. Kuɗi, mulki, lafiya, mazantaka da suna do not make a man. Habibu Umar Simagade ya nuna masa haka daga airport zuwa yanzu. Kuma duka abubuwan da yake taƙama dasu a yau ba su hana shi jin nauyi da kunyar wanda ya raina a baya ba. Zuciyarsa ta karaya matuƙa da ya tuna wani shuɗaɗɗen lokaci da Abba Habibu ya zo neman taimako wajen sa a kasuwa. Akan ce idan maye ya manta, uwar ɗa ba za ta manta ba. To shi dai da kansa mayen bai manta ba. *** SHEKARUN BAYA Abba Habibu ne yake tafiya a cikin kwanonin tsakiyar Kantin Kwari da gammo a kansa wanda ya ɗorawa madaidaiciyar cooler. Kayan jikinsa jamfa ce da wando kuma gwargwadon iyawarsa yana ta kamanta taku irin na maza, sai dai ko kusa baya iyawa. Tafiyar tasa tafi kama da rangwaɗa irin ta ƴan matan dake ji da kansu. Nauyin kayan da ya ɗauko ko kaɗan bai ɓoye yanayinsa na ɗan daudu ba. Da kwatance saboda daɗewa da sababbin gine-gine a kasuwar ya gano jerin shagunan Alh. Hayatu. Cikin farinciki ya shiga da sallama daidai lokacin da yaran shagon su ke ganiyar ciniki da wasu kwastomomi. Alh. Hayatu kuma yana magana a gefe guda da ƴan mazan ƴaƴansa su uku. Dukkaninsu sanye su ke da shadda wagambari tana ɗaukar ido. Ahmad, Kamal da Taj. Kamar kowacce Juma'a, Alhaji ya tura an ɗauko masa su daga gida bayan sun dawo daga makaranta domin zuwa masallaci. Alhaji na ganin Abba Habibu yaji tamkar an ɗauke masa wutar jikinsa. Sam baya son abin da zai haɗa su waje guda saboda yadda yake ƙyamarsa. Idan ya tuna Habibun da ya sani, ya kalli wannan sai yaji wani irin takaici. Da ƙyar ya amsa sallamar da yayi. Kuma gabaɗaya ya tsargu da kallon su da mutanen cikin shagon su ka kama yi. Yana ji a jikinsa yau shi zai zama jigon gulmar cikin kasuwar. Fuska cike da fara'a da jindaɗi Abba Habibu ya miƙa hannu zai dafa kan Ahmad yana cewa "girman ɗan mutum ba wuya. Yaya Hayatu haka Ahmad ya girma?" Ya kalli su Taj "waɗannan ƙannensa ne?" Kafin hannunsa ya taɓa Ahmad tuni Alh. Hayatu ya janye ɗansa gefe ya kuma bi shi da kallon me-ya-kawo-ka? Abba Habibu ya ɗan rissina gami da miƙa masa hannu sai dai haka ya koma da abinsa da bai mayar da musabahar ba. Still with a smiling face ya gaishe shi ya kuma tambaye shi lafiyar iyali. "Ƙalau! Aiko ka aka yi ne?" Alh. Hayatu ya tambaya a ƙagauce. "Dama magana na ke so mu yi" Abba Habibu ya bashi amsa da sanyin jiki. Attitude ɗin da yake yi masa yasa shi shan jinin jikinsa. Shi ɗin ba baƙon da ake maraba da zuwansa bane. Wata kusurwa a cikin shagon Alh. Hayatu ya ja shi maimakon su keɓe a office. Yadda mutane suke yanzun nan zai iya jin an yi masa muguwar fassara. Cikin jin nauyi Abba Habibu ya keta billensa ya roƙe shi akan ya taimakawa rayuwarsa. "Wallahi ban iya komai ba sai girki. Na fara koyon ɗinki amma saboda zama sai naji ba zan iya ba tunda na saba da kai komo. Ni kuma ba karatu na gama ba balle na nemi aiki." "Me ka ke so?" "Ba na son zama cima zaune. Idan da hali ko yaron shago ka ɗauk..." Ko direwa bai yi ba Alh. Hayatu ya hau shi da faɗa. "A'a...kada ma ka yaudari kan ka. Ta yaya zan bari mutumcina ya zube a wajen sana'ata saboda kai? Ban gaya maka zaka yi nadamar wannan hanyar da ka ɗauka ba?" "Ka faɗa Yaya Hayatu. Ba kai ba ma. Kowa ya faɗa kuma na gani." Idanuwansa su ka ciko da ƙwalla. Hakan ya sake ɓatawa Alh. Hayatu rai. Namiji har namiji amma mai saurin kuka. Tirrr da daudanci wallahi ya ayyana a ransa. "Habibu ka san ban iya munafurci ba ko? To ba za ka zauna min a shago ba. Ana girmama ni a wajen nan." Abba Habibu ya yi murmushi "nima kaina ina ƙyamar yadda rayuwa ta kasance min amma wallahi girki kaɗai nayi a cikinta. Duk sauran shiriritar da kake tunani ban taɓa yi ba. Kuskurena biyu ne. Na farko da nayi tunanin dole sai na koma mace zan sami damar yin girkin da nake so. Na biyu kuma da na bari son girkin ya rinjayi zuciyata zuwa ga saɓon Allah." Ya haɗa hannuwansa biyu "na tuba ga Ubangijina Yaya Hayatu. Ko zan mutu ina yawo a titi ba zan ƙara daudu ba. Tafiya, magana da wannan karya jikin ma don dai na rasa yadda zanyi na daina ne. Don Allah Ka taimaka min ko da jari ne." Zuciyar Alh. Hayatu ta fara karaya da zantukan Abba Habibu a wannan lokaci. Yanayin tamke fuskarsa ma ya sassauta. A lokaci guda yaji makamansa sun fara ƙarewa. Ya ja gwauron numfashi ya sauke. "Ba zan iya zama da kai a kasuwa ba Habibu amma in sha Allahu zan taimaka maka." Ya sami kujera ya zauna sannan ya dube shi "Yanzu idan na baka jari wace sana'a za ka yi?" Murna, nutsuwar zuciya, ɗoki da girmamawa ga Alh. Hayatu su ka taru su ka mamaye zuciyar Abba Habibu. Bakinsa har yana rawa don tsabar farinciki. "Girki!" Alh. Hayatu yaji wani irin haushi da takaici sun lulluɓe shi. Girkin dai zai koma wa? "Sana'ar abinci zan cigaba da yi domin a nan nake da ido. Kada na dulmiya kuɗin a inda zai salwata saboda rashin sabo. Ko yaya ka gani?" Ɗaga murya ya yi "Baka shirya gyara rayuwarka ba Habibu. Ka zo ka fita. Fita na ce!!!" Ka nuna masa waje. Abba Habibu ya waiga hagu da dama a rikice don bai san me ya sake tunzura Alh. Hayatu ba. "Yaya Hayatu..." ya soma kiran shi da sigar magiya. A yadda Alh. Hayatu yake ɗaga murya yanzu da yaran shagon nasa, kwastomomi da mutanen dake haraba kowa ya dawo da hankali garesu. "Girkin ba shi ya kawo ka wannan mummunan matsayin na ɗan daudu ba? Shi ne za ka kalli tsabar idona ka ce min idan na baka jari shi za ka cigaba da yi. Anya Habibu kana da hankali kuwa?" "Shi ne kaɗai nake ganin zan yi ba tare da mutane sun guji mu'amala dani ba. Yanzun nan fa kace min ba za ka iya zaman shago dani ba. Kana ganin akwai sana'ar da zan yi a saya a wannan zamanin namu da ake ƙyanƙyamin masu rayuwa irin tawa? Abincin mu ne kawai na san ba a gudu." "Habibu ka fita na ce. Kuma ko a hanya ka ganni kada ka kuskura kayi gangancin nuna ka taɓa sani na. Aikin banza." Jiki a sanyaye Abba Habibu ya ya juya zai fita. Idanuwan dake kallonsa sun fi ashirin. Nan take zuciyarsa ta sake raunana. Ƙwalla ta cika masa idanu taf sai dai bai bari ta sauko ba. A wulaƙance Alh. Hayatu ya kalli cooler ɗin da ya shigo da ita. Ya sa ƙafa ya zungureta. "Dawo ka yi mantuwa." Murmushin yaƙe Abba Habibu ya yi "dama kawo maka nayi a bawa yara." "A bawa yara? Me?" Ya sake tambaya yana taɓe fuska. "Zabi ne aka soya" Katse shi yayi da sauri "Allah Ya kiyaye jini na su ci girkin ɗan daudu wallahi. Ba ma tare da yunwa Habibu. Ka kwashe kazantarka." Abba Habibu ya kalli kular ya koma ya kalli mutane suna ta ƙananun maganganu a gefensa. Jikinsa yaji duk ya mutu kamar anyi masa duka. Wannan kular ya tabbatar a yadda yake jin kansa ba iya ɗauka zai yi ba. Ƙwaƙƙwaran motsi idan yayi zai iya yin hawayen da Alh. Hayatu zai sake aibata shi a kansu. Rago zai kira shi. "Don Allah ko a nan ne ka bayar." "Ai ba ni ba, wanda ya raɓe ni ma yafi ƙarfin cin abin hannunka." Ya kalli biyu cikin yaransa "ku ɗauka a kaiwa karnuka tunda ba ya so." Jin haka Abba Hayatu ya koma ya ɗauki kular kafin su taɓa. Mahaifiyarsa ce ta dafa sai dai baya jin Alh. Hayatu yana buƙatar dogon bayani irin wannan. Da ya fita bai sake waigowa ba. * In ya tuna, shi da Abba Habibu basu sake haɗuwa ba sai da maganar auren Taj da Hamdi ta taso sai yaji a ransa tamkar Abba Habibu yayi nasara a kansa har sau biyu. Na farko izzarsa ta kife a ƙasa a yayinda ɗansa mafi soyuwa a gare shi ya zaɓi girkin da ya tsani gani a wajen ɗa namiji a matsayin sana'a. It was as if karma came knocking and laughing at him lokaci guda. Na biyu kuma shi ne yadda ƙaddara ta sake haɗa ɗan nasa da yar Habibu. Abu kamar almara. Idan ya ce bai yi tunanin ko asirice masa ɗa Abba Habibu yayi ba tabbas yayi ƙarya. A karon farko zazzafar ƙwalla ta dinga kwaranya daga idanun Alh. Hayatu. After all these years, abar ikon Abba Habibu ce ta zama silar warakar gudan jininsa. Yau idan Kamal ya cigaba da rayuwa, Allah ne Ya yi ikonSa amma matar Habibu ce sila. Habibun da yake ganin bai cika mutum ba. Wasu cikin

Chapter 41 of 46