Share this page
kira ya sanar da su shawarar da ya yanke. Su ka yi na'am da farinciki. Yaya Babba ya shiga gaba su ka haɗu da ƴan uwan Hajiya, wani abokin Alh. Hayatu da ƴan uwa shaƙiƙan sauran matan mutum ɗaiɗai sai gidan Kawun Mubina. Shi ma kafin zuwan nasu ya riga ya faɗawa duk wanda ya kamata. Ana idar da sallar la'asar wanda ya yi daidai da magrib a birnin Jeddah aka ɗaura auren a masallacin unguwa. Asibitin gabaɗaya ya kaure da murna. Ma'aikatansu waɗanda su ka san Kamal da Yaya su ma duka sun taya su murna sosai. RAYUWA DA GIƁI 40 ƘARSHE Batul Mamman💖 Allahumma Balighna Ramadan...AMEEN A can hotel Mubina ba ƙaramar takura ta shiga ba. Aure dai an ɗaura amma kamar yadda ta ce babu kowa nata sai dangin miji. Duk sai ta koma abar tausayi. Yaya Kubra ta lura da haka sai su ka yi magana da Yaya Hajiyayye, aka kama mata ɗaki daban domin kwana biyun da su ka yi ɗakunan da su ka kama na group ne masu gado hurhuɗu. "Hamdiyya ki koma wajenta ki tayata zama. Idan kuna buƙatar wani abu ki mana magana. Na san ba za ta sake da mu ba yanzu kuma sai a hankali." Hamdi tayi murmushi harda rufe fuska da tafukan hannu "nima dama kunyar taku nake ji har yanzu." Yaya Kubra ta harareta da wasa "Ehhh lallai, wallahi ki ka sake cewa kina jin kunyarmu sai na yi mi ki handsfree a gaban Alhaji." "Tsegumta min mana likita. Me ki ka gani? Tajo ya yi ajiya ko? Oh ni uwar babana. Aure ko wata biyu ba a yi ba. Dama na san za a rina. Taj ko kaɗan bai yi kama da salihai ba. Hararar da take yiwa Hamdi komawa tayi kan Yaya Hajiyayye. "Ke fa daɗina da ke sakin zance wallahi. Don Allah kina yi kina tauna magana kafin ki furzar. Me ya kawo batun salihanci tsakanin mata da miji banda abin ki?" "Raini ya jima da shiga tsakaninmu dama Kubra. Gara ki kwaye min baya a gaban...." ta waiga babu Hamdi babu dalilinta. Can ta hangota ta kusa ƙure korido tana ta zuba sauri kamar ta kifa. Ita da Kubra su ka haɗa ido su ka kwashe da dariya. Faɗan da ba su ƙarasa ba kenan. * Ƙarfe tara da rabi Umma ta shiga ɗakin su Mubina. Hamdi kaɗai ta samu ta kashingiɗe akan abin sallah. Umman na shiga ta tashi zaune. Umma tayi murmushi "ƙanwar Ango ina amaryar yayanki?" "Tana banɗaki" ta amsa mata ita ma tana murmushin. "Ai gara tayi wank..." Caraf Mubina ta katse Umma daga cikin toilet ɗin da rawar murya. Tsoro muraran ya bayyana a tare da ita. "Ba wanka nake yi ba. Alwala zan yi na fito." "Ai ba laifi ki ka yi ba Mubina. Ki yi wankan ki shirya a nutse Alhaji ya ce ni da Hajiyayye mu raka ki asibitin." "Na'am? Asibiti kuma" Ta buɗe ƙofar ta fito a firgice. Idanunta zuru-zuru sai ɓare-ɓare take yi. Mubina akwai ruɗewa sai a lokacin hakan ya bayyana. Hamdi ta kalli Mubina sai taji wani tausayinta ya tsirga mata. Shi fa aure kwarjini gare shi na daban. Gashi dai da ƙafarta ta taho ƙasar amma yau ɗaya duk ta sauya saboda alhini. Umma zama tayi akan gado ta yafito Mubina da hannu. "Mene ne amfanin aure idan mace bata kasance tare da mijinta ba Mubina? Asibitin da kansu su ka ce sun yarje miki zama tare da shi tunda ke likita ce sannan sabon aure." "Umma ni dai don Allah" sai kawai ta fashe da kuka. Umma ta tashi tsam ta rungume ta. "Kamal ɗin ne ba kya so?" Mubina ta girgiza kai. "Aure a irin wannan yanayin ko? Ba haka aka saba ba na sani, amma faruwarsa a hakan ya sa naku ya zama special." Ba kunya Mubina ta ɓare baki "ni dai Mamana, Umma don Allah wajen Mamana zan tafi." Ɗago kanta Umma tayi ta ce "Tamɓali! Mubina? Shekararki nawa ne?" Mubina ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana kuka tana murmushi lokaci guda. "Na fahimce ki" Umma ta sake yin murmushi "ƙarasa abin da ki ke yi ki kwanta" Ta juya za ta fita Mubina ta kira ta kai a ƙasa saboda nauyinta da take ji. "Umma ba za ku yi fushi ba?" "Haba dai. Mubina ba na jin Kamal zai taɓa samun soyayya irin wadda ki ke yi masa. Kin haɗu da shi a halin ciwo kin so shi. Sannan a lokacin da dukkan wata ƙofa ta ƙulle sai Allah Ya yi amfani da ƙudurinki na biyo shi domin..." muryarta ta karye "ku yi sallama sai Ya kawo mafita. Hamdiyya kina ganin akwai..." ta juya ko sama ko ƙasa babu Hamdi sai kawai ta kama dariya "wannan ƙanwar taki ta san yakamata sosai Mubina. A duk lokacin da take jin ana buƙatar keɓewa cikin magana sai ki ga ta bar wajen da dabara." "Nima na kula Umma." "Idan ku ka rayu tamkar ƴan uwa tare da sauran yaran namu da matar Ahmad haƙiƙa kun gama yi mana komai." "In sha Allahu." "To amarya sai da safe." Umma ta fita fuskarta babu komai sai annashuwa. Mubina kuwa wata ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi ta faɗa kan gado. Yanzu da Umma ba mai fahimta bace kawai sai a wuce da ita asibiti tinƙis-tinƙis. Gobe kuma a dinga zuwa dubiya ana ganinta a ɗakin Kamal. Ai da kunya! 'Kamal' ta maimaita sunan a zuciyarta. Yanzu fa wai ya zama mijinta. Wani juyi tayi na farinciki tana ƙara yiwa Allah godiya. * Hamdi na fita ɗakinsu da Taj ta wuce da niyyar ta ɗauko kayan baccinta ta dawo wajen Mubina. She was just smiling idan ta tuna yadda ta baro Mubinan. Tana ji a jikinta Umma ba za ta matsanta mata ba. Nata key ɗin ta saka ta buɗe ɗakin. Tana shiga taji anyi sama da ita. Ta buɗe baki za ta yi ihu Taj ya sauketa ya jingina bayanta da ƙofar ɗakin. Ya tare mata hanyar wucewa. "Kina yi su Alhaji za su zo kinga sai mu taru mu yi musu bayanin me ya firgita mu." Ta harare shi "abin da ya firgita ni dai." "Da na sani ma a toilet na ɓuya sai kin fi tsorata." Hango irin tsoron da za ta ji tayi ta yi murmushi "da kuwa mai raba ka da yayana sai Allah." "Kinga ki kiyaye ni da zancen yayanki ɗan kalen dangi. Yana can gadon asibiti me zai iya? Taj will do what Taj wants." Ya ƙare magana girarsa ɗaya a sama. Kai ta girgiza "Gobe idan mun je ka maimaita abin da ka ce yanzu in koma gefe in sha kallo." "You are looking for my trouble fa, and I will give it to you har sai kin ce ya isa." Dariya ya bata ta kama ƙugu da hannu guda. "Bring it on." Janyota ya yi su ka nufi 3 sitter ɗin ɗakin su ka zauna. Ta ɗora kanta a ƙirjinsa shi kuma ya sake rungumeta. "Ƴar caras matar Tajuddeen." Ya kira ta affectionately. "Uhmmm." Ta amsa muryarta can ƙasa-ƙasa. Kasancewarsu tare ya saukar mata da nutsuwa fiye da kullum a yau. Jikin Yaya yana ta ƙara kyau. Sai yanzu ta sami damar appreciating zuwa ƙasa mai tsarki a dalilinsa. "Yau ban ce miki ina son ki ba Hamdi na. I love you." "Ni ɗin kake so ko ƴar caras?" Ta tambaye shi bayan ta zauna su na fuskantar juna. "Why do you ask?" Baki ta tura kafin ta ce "Tun ina yarinya ake cewa jiki zan yi idan nayi aure. Wai ƙirar mu ɗaya da ƴaƴan Anti Zinatu." "Ƙira kuma sai ka ce wata mota?" "To dai ance zan yi ƙiba. Kai kuma har wani ƴar caras kake cewa. Kada na fashe nan gaba na daina burge ka." Damuwa sosai yake iya gani tare da ita. Ya yi dariya ya kuma zolayarta. "Ki fashe kamar wata kwalba?" "Happy manaaaa" ta buga ƙafa a ƙasa. He hugged her tightly sannan ya yi magana a hankali. "Ko me za a ce mi ki, ko me ki ka zama a gaba Hamdiyya ki sani cewa Taj is your home. You can be anything as long as Hamdin Abba Habibu ce ina son abata. Hamdi ƴar tsinke" ya fara ƙirge da yatsansa "Hamdi ƴar doguwa, Hamdi ƴar gajera, Hamdi ƴar lukuta, Hamdi mai tumbi, Hamdi shafi mulera..." Yana kaiwa nan wata wawuyar cakuma yaji ta kai masa tana rigima ya kwashe da dariya. "Wai ina faɗa ne don ki san cewa ke nake so ba jikinki ba." Daga nan ya lallaɓa abarsa su ka kwanta. Sai shabiyu saura Hamdi ta farka firgigit kamar an tsunkule ta. "Mubina tana jira na mu kwana tare. Ya Subhanallah." Ta tashi tana neman hijabi. Sai da ta saka tukunna Taj ya ce "to amara ƙirjin biki dawo ki kwanta. Amarya tana wajen Angonta." "Anya kuwa? Ban ga alamun za ta tafi ba." Ta faɗa masa iya abin da ta gani da Umma taje ɗakin. Taj ya soma dariyar mugunta. Hamdi tun tana mamaki har ta koma kusa da shi tana jiran ya faɗa mata me ya kawo dariyar. "Kaza gashin Najeriya" ya ce da ƙyar dariya na cin sa. "Ban gane ba fa." "Yayanki..." dariyar harda ƙwalla. Hamdi ta kama baki "yau ina ganin ikon Allah." Da ƙyar ya saisaita kansa "ana cewa an ɗaura auren nan yayanki ɗan kalen dangi ya sa ni fita neman kaza. Wai bai dace amarya ta zo babu wani abu da zai tuna mata al'adar gida ba." Yana kallonta ya cigaba da cewa "kin dai sanni da faɗin gaskiya ko Hamdi na...to haka na aje kunya a gefe na nuna masa rashin fa'idar nemo kazar nan saboda kada amarya ta fassara shi yana kwance magashiyan." Ya sake yin dariya. "Ba ka da kirki fa" ita ma ta soma dariya don ta hango inda zancen zai dire. "Rawar kai irin ta ango sabon shiga ya ce bai yarda ba. Babe, tun la'asar nake neman kaza don ya ce dole na nemo gashin Najeriya mai ɗan ƙuli-ƙuli da yaji. Kuma bai yarda na tambayi su Bishir ba duk da sun fi ni sanin gari wai kada a raina shi. To cut the story short naji a jikina. Wurin ana layi haka nayi ta zama har na samo." "Shi ne kake yi masa dariya?" Ita ma fa dariyar take yi. "Sai da yasa na dawo na ɗauko masa aron kayana. Ga ciwo ga wahala amma haka ya dage na saka masa shadda harda hula. A table ɗin gefen gadon na jera masa kazar amarci, juice, youghurt da biryani. Kaiiiii, wa zai cirewa Happiness kayan nan? Ko dai in kira shi ne? Ba za su yi daɗin bacci ba." Hamdi dariya, Taj dariya. Sai sun yi kamar sun gama da sun haɗa ido sai a sake daga farko. "Harda turaren angwanci yasa na nemo masa mai mugun tsada ya feshe jikinsa." Hamdi ta goge ƙwallar dariya da yatsa "Ni damuwata akwai fridge a ɗakin?" "Fridge kuma? Akwai." "Yauwa dama don kada kazar ta buga." Su ka sake tuntsirewa da wata dariyar that was just contagious. Da mutum zai shigo ɗakin dole ya taya su. After 1am Taj ya raka Hamdi ƙofar ɗakin Mubina. Ta shiga ta sameta tana sallah. They just smiled at each other sannan Hamdi ta ɗauro alwala ta zo ta tayar a kusa da ita. *** Yau dukkanninsu su ka tafi asibitin domin daga nan za su wuce su shiga jirgin ƙasa zuwa birnin Madina. Hajiya dai ta ce da Abba Habibu babu inda za ta har sai Yaya ta fara tashi da kanta. Anyi-anyi da ita ta tafi saboda akwai kulawa sosai a asibitin amma ta rufe ido ta ce su ƙyaleta. Alhaji ya goya mata baya tunda shi ma ba tafiya zai yi ba. Kamal kuma za a bar masa Abba da amaryarsa. Duk wannan zancen kafin su fito aka gama yinsa. Alhaji ya ce da Mubina idan tafi son fara yin Umrarta a nutse cikin ƴan uwa babu damuwa. Sai kawai ta duƙar da kai. Mama ta fassara masa da cewa ta amince da zaman ne. Kuma hakan yake a zuciyarta. Tun asuba mahaifiyarta ta kira ta su ka yi magana akan yin abin da ya kamata. Wasu lokutan mutum ya kan ajiye kunya da tsammanin al'ada ya yi abin da ya dace da halin da yake ciki. Daga ɗakin Yaya su ka rankaya ɗakin Kamal. Ango ya dinga cika yana batsewa. Taj ne kaɗai ya san dawan garin. Ya yi ƙoƙari sosai bai yi dariya ya tona masa asiri ba. Sun fara yi masa sallama a zaton sa harda Mubina a tafiyar sai ya kaɗa baki ya ce, "Mubina matso mu yi sallama, sannan ga kazar ki nan ki tafi da ita." "Innalillahiiii...." ta tattaro numfashi kafin ta dire "wa inna ilaihi raji'un." Ji tayi kamar ya tsomata a cikin ruwan sanyi saboda kunya. Ɗaki ya yi tsit kamar ruwa ya cinye su na wucin gadi. "Ku fita mu tafi. Kamal, Allah Ya ƙara sauƙi." Ahmad ya yi ta maza ya kawo ƙarshen kallon-kallon da ake yi. Ai kamar jira su ke yi su ka fita a layi ko waige babu. Mubina ko motsi ta kasa yi. "Da alama anaesthesia bata sake shi ba har yanzu doctor. Lamarin Happiness sai kin haɗa da haƙuri. " cewar Taj. Kowa ya watse. Babu mutum guda da ya kalli Mubina ko ya yi murmushi ko da ƙasa-ƙasa ne kuwa. Ba su isa ba ne. Duk barkwancin yayyensu sun san Yaya Kubra ko Yaya Hajiyayye ce ba za ta ɗaga mata ƙafa ba. Sun san wasan da ya kamata su shiga da wanda bai dace ba. "Ashe haka ka ke Kamal?" Ta faɗi baki buɗe don har yanzu tana mamakin wannan magana. Ya juya mata ƙeya "Me na yi?" "Babu komai." Ta rage murya tana magana a hankali amma yadda zai ji "dama Taj ya ce na lallaɓa ka da sauran allura a jikin ka." Ta sami wuri ta zauna akan kujera ta juya masa baya ita ma. Ɗakin ya koma shiru. Da ya ga babu Sarki sai Allah sai ya sauko. Yana magana abin tausayi. "Jiya ba ki kyauta min ba. I waited." "Shi ne yasa ka bani kunya a gaban ƴan uwanka?" Briefly ya labarta mata yadda jiya ta kasance a wajensa. Mubina ta dinga girgiza kai ita a dole ya bata tausayi. Ya gane sarai abin nata harda tsokana. "Kar ki yi min dariya." That was it! Magiyarsa tamkar zuga ta koma a gareta. Dariya ta kufce mata ta kare baki ta yi. Kamal samun kansa ya yi da zuba mata idanu kamar haɗuwar farko. She looked so cute tana wannan dariyar. Ya ji zuciyarsa tana neman cika masa ƙirji saboda farincikin da ya samu daga abin da take yi yanzu. Da ta gama dariyar tashi tayi ta dudduba ɗakin bata ga alamun nama ba. "Ka saka min rai kuma ni ban ga kazar ba." "Laifin naki kenan." "Me kuma ya na yi?" "Na zama abin tsokana dai da alama. To ki kwantar da hankalin ki domin kema kin shiga one chance yadda na shiga jiya." Ƴar dariyar da take yi ta daina babu shiri ta dawo kujerar gefen gadon ta zauna. Kamal ya sosa ƙeya. "Ba na faɗa miki sai da na sa Happy ya canja min kaya ba?" "Yesss" "Kaya dai har sai da su Alhaji su ka shigo yi min sai da safe su ka ganni da su, na kasa cirewa. Shi da Abba Habibu ne su ka cire min. It took more than 10 minutes saboda su na tsoron fama min ɗinki." "Ya Rahman" Mubina kanta sai da taji kunya. "Da su ka gama ne Alhaji ya ce sai na biya ladan wahalar da jikin girma. A gabana su ka cinye naman nan. Harda cewa ranar da za ki tare zai biya mu." Ya ɗan cije baki "Saboda Allah me zai sa ya yi min zancen tariya? Don na ɗan yi kwalliya shikenan sai a fassara ni? Ko ni na kawo fitina duniya ai dole in jira nayi healing ko?" "Ni dai na shiga uku." "Wallahi kin shiga. Kazar amarci surukan ki maza sun cinye. An barwa ƴaƴa tarihi." Kamar za ta yi kuka ta ce "to ni yanzu yaya zan yi?" Kamal ya ware hannuwansa yana kallon cikin idanunta. "You can start by giving me that first halal hug." Bata san abin da zai ce ba kenan da ba za ta zauna a kurkusa yadda kunyarsa za ta kama ta da yawa haka ba. "Idan ka warke kayi da kan ka." Ta faɗa a ciki-ciki. "Mubina" ya tsare ta da ido. "Na'am." "Now please." Magiya ce ko umarni? Ita dai bata gane ba. Abin da ta fahimta kawai shi ne zuciyarta tana muradin yin abin da mamallakinta yake so. She gave him the warmest hug. Zuciya da gangan jiki su ka sami kyakkyawar nutsuwa. A lokacin da Kamal yake tunanin Mubina ta gama biyansa da alkhairi, she brushed his lips lightly da nata. Tsokana ta so yi, reshe sai ya juye da mujiya. Happiness got his happiness and he wasn't willing to let go easily. Kamal da Mubina Allah Ya ƙara lafiya da zaman lafiya! *** Wani irin kuka Inna Luba ta fasa daga ɗaki mai firgitarwa. Malam da yake ririta ta tun jin Yaya ta tafi Saudiyya ya fito daga banɗaki da zariyar wando a hannu. "Luba me ya faru? Mutuwa aka yi?" Inna Luba kuka kawai take yi babu ƙaƙƙautawa. Amarya duk jarabarta jikinta ya ɗan yi sanyi. Shi yasa bata faɗi magana mara daɗi ba da ta fito. Banda haka da tuni ta fara domin tsufa bai rage mata komai ba. Da ƙyar Malam ya samu cikin kuka Inna Luba ta faɗa masa wayar da aka kira ta daga Kano. "Surukar Abdulƙadir ce ta kira yanzu wai za ta yi min jaje." "Waye kuma Abdulƙadir?" "Ƙanin Habibu mana." "To, sata aka yi ko gobara wani cikinsu ya yi?" Amarya ta tambaya tana jin haushin tsurkun da ta fito kuma da alama labarin ba zai ƙayatar da ita ba. "Yarinyar nan ce..." Malam ya dafa bango jiki na rawa. Sai ka rantse bai taɓa nunawa Yaya ƙyama ba. Ya marairaice sosai gwanin ban tausayi. "Lubabatu bar zancen nan haka. Zuciyata ba za ta iya ɗaukar zancen mara daɗi akan gudan jini na ba." "Wannan kam dole sai ka ji. Wai anyi mata aiki an cire mata ƙoda guda ɗaya an dasawa wani yaro." Da wani irin zafin nama Malam ya zabura kamar ba tsohon da yake taku da ƙyar ba saboda ciwon ƙafa. "Me???" Yadda taji ta maimaita. Dama su kan gaisa a waya da ita a matsayin surukai. Ashe duk gargaɗin ds Abdulƙadir ya yiwa matar tasa akan ɓoye zancen sai da ta sanarwa ƴan gidansu kaf. Ita kuwa Mamansu da bata san ɓoye zancen ake yi ba ta kira Inna Luba domin ta jajanta mata. Jinjin ta bayar da ƙoda an dasawa wani ɗan balarabe a Makka. "Jar uba! Kin ga kira Ɗandaudun nan ki haɗa mu kawai. " Baba Malam ya nuna kansa yana jijjiga jiki "Ni za a ha'inta? Ɗiyar tawa za a feɗe daga zuwa ibada? Dama can ban yarda yana da kuɗin kai Jinjin Saudiyya ba. Matsiyaci mai tafiyar mata. Ina yi masa kallon wanda ko ƙuda ba zai iya kashewa ba ashe ja'irin ƙodar ɗiyata zai sayar. Allah Ya isa Habibu!" To Inna Luba dai babu bakin kare Abba Habibu domin kuwa bata san gaskiyar me yake faruwa ba. Ana haka gida ya kaure da tsine-tsine da zagin bawan Allah Abba Habibu sai ga wani ɗan saurayi cikin jikokin Amarya. Inna Luba ta miƙa masa wayarta ko zama bai yi ba. "Ya'u maza lalubo min lambar Sajida ka kira." Ya'u ya yi abin da ta ce ba tare da tambayar komai ba duk da mamakin da ya cika masa zuciya. Kiran na shiga ya miƙa mata wayar sai dai kafin ta ankara Malam ya karɓe ya manna a kunne yana masifa. "Maza-maza ki yiwa ubaki waya ki ce ya kira ni yanzun nan." "Baba Malam me a ka faɗa muku?" Sajida ta fahimci ba lafiya ba "don Allah ka tsaya nayi maka bayani." "Ƴal ƙwal uba har ki na da bayanin da za ki mani? Me ya hana ki neman mu kafin yanzu tunda da alama kin san komi" ya yi ƙwafa "wato kun haɗa kai da baban ku za a kawo muku kuɗin jini ku wanki biyar ku tsoma biyar, ni da na san zafin haihuwarta kuma a barni da kukan rashin ɗiyata. To wallahi ba ku isa ba. Nemo shi ki ce masa lallai a mayar mata da ƙodarta." Sajida ta sake kwantar da murya "Baba Malam ka yi haƙuri. Ba abin da ka ke tunani bane. Yaya taimako tayi da ceton rai." "Da ƙodarta? Ke Sajada, kada ki raina min wayau mana don kawai kin ga ina rayuwa a ƙauye. Tun Kaka da Kakanni ban taɓa jin an cire sassan jikin wani an dasawa wani ba. Zancen nan bai yi kama da wanda hankali zai ɗauka ba." Haƙurin ta sake bashi ya ji haushi ya surfa mata zagi daidai wa daida. Ya ce kuma ta saka a ranta cewa Yaya na dawowa zai maka Abba Habibu a kotu a raba auren su. Jin haka Inna Luba ta karɓe wayarta ta ce da Sajida tayi maza ta nemi Abbansu. "Idan bai kira ni ba to nima zan bi shawarar Malam." Ta katse kiran. Hankalin Sajida ya tashi sosai. Ranar kwanan su Taj biyu da tafiya Madina ta kira ta sanar da Abba Habibu yadda su ka yi da su Baba Malam. Murnar sauƙin da su Yaya ke samu sai ta koma ciki domin kuwa nasa hankalin ba ƙaramin tashi yayi ba. Alh. Hayatu ya yi Allah wadai da halin surutun wasu mutanen. "Wani lokacin sai ka yi tunanin akwai masu ɗokin zama ƴan yaɗa labari mara daɗi. Suna rawar jikin zama farkon waɗanda za a ji mummunan labari daga bakinsu. Banda haka wane irin rashin nazari ne zai sa a kira tsohuwa a tayar mata da hankali irin haka?" "Yanzu ta ina zan fara? Ta yaya zan yi musu bayanin da za su fahimta?" Abba Habibu cikin damuwa, Yaya kuma tana ta kuka. Tausayinsu ya kama Hajiya, musamman da ta tuna rayuwar ɗanta ce ta janyo mu su. Jikin kowa yayi sanyi. Sun kira su Inna Luba amma ko kusa Baba Malam bai bata wayar ba. Shi kaɗai ya dinga faɗa kai ka rantse tunda Yaya ta taso bai taɓa juya mata baya ba. Maganganunsa duka ana ji domin faɗa yake yi iya ƙarfinsa. Har cewa Yaya ya yi ta tabbatar ta karɓi takardarta kafin su dawo. Hajiya dai sai da tayi kuka mai isarta. Yanayin ɗakin ya koma wani abu daban a tsukin lokacin. Ana haka sai ga kiran tawagar Madina. Dama kullum sai sun kira an gaisa. Hajiya na karɓa ta ce a bawa Yaya Kubra wayar. Sai da ta fara gargaɗinta akan kada maganar da za su yi ta fita musamman zuwa kunnen Hamdi sannan ta tambayeta shawara. "Ke ce likita Kubra. Me ya kamata mu yi? Ta ina za mu ɓullo mu su ta yadda za su fahimci girman taimakon da Yaya tayi har ma su yaba mata?" "Hajiya turo min numbar da zan same su." "Bari na karɓa sai na turo miki. Amma don Allah ki kiyaye." Kallo su ka bita da shi har ta tura numbar sannan tace musu su duka babu mai ilimin da zai iya yin bayanin da su Inna ba za su ɗauka son zuciya ba. "Mu bata dama tunda ɓangaren aikinta ne. Na san Kubra, za ta yi abin da ya dace." * Gidan Baba Malam fa babu lafiya. Inna Luba kwanciya tayi zazzaɓi ya rufe ta yayinda maƙota su ke ta zaraf-zaraftu a ƙofar gidan ana ta zuwa jaje da ganin ƙwaf. Amarya ce ta fice fit ta fesawa waɗanda ta san za su tayata yaɗawa. Kafin wani lokaci gari ya ɗauka. Abin ne da mamaki ace mutum ya bayar da ƙoda sukutum kuma yana nan da rai. Waya na ringing Inna Luba ta tashi da sauri ta ɗauka. Yaya Kubra ta gaishe ta a ladabce sannan ta buƙaci Innar ta haɗa ta da matashi ko matashiya idan akwai a kusa. "Yarinya ko me za ki ce ki faɗa min kawai." "Don Allah ki yi min wannan alfarmar Inna. Ki taimaka." Ba don ta so ba ta fito tsakar gidan. Cikin sa'a tayi kiciɓis da Ya'u. Har yanzu bai koma gidansu ba tunda ya san me yake faruwa. Rigimar kakarsa Amarya da Inna Luba ba sabgarsa bace. Yana ɗasawa da kowa a gidan. "Inna kina buƙatar wani abu ne?" Ya matso kusa da ita da sauri. "Gashi" ta bashi wayar ta koma cikin ɗakinta. Ya'u ya saka waya a kunne ya ce "hyalo?" Kai tsaye Yaya Kubra ta bijiro masa da buƙatarta bayan ta gabatar da kanta kuma taji daga ɓangarensa. Yadda take magana kaɗai ya yi masa kwarjini don jikinsa

Chapter 44 of 46