Share this page
Kamal. Muryarsa kuma rawa take yi sosai. "Ban faɗawa kowa ba sai kai. Ina buƙatar ka zo mu yi shawara Ahmad. Zan iya rasa Kamal a kowacce daƙiƙa." "Kayi haƙuri. In sha Allahu zamu sami mafita. Gani nan zuwa." "Ka taho da Salwa." RAYUWA DA GIƁI 31 BATUL MAMMAN💖 YA HAKIMU gwanin Sarkin *** "Salwa kuma Alhaji? Wani abu tayi?" Ahmad ya yi tambayar ne saboda a tunaninsa ciwon Kamal kaɗai ya isa ya gigita Alhaji. Me zai sa ya tuna da Salwa har ya nemi a taho da ita a lokaci mai mahimmanci irin wannan? Gwiwa a sage ya tambaye shi "Laifi tayi ko?" "Kai dai ka taho min da ita." Yana bashi wannan amsar ya gane ko ma mene ne ba abin wasa bane tunda lalura mai girma kamar ciwon ƙodar Kamal bai hana shi nemanta ba. A kitchen ya same ta da himilin kwanuka kamar a gidan ake taron biki. Ko tausayi bata bashi ba don taurin kai da kafiya gami da son zuciyarta ne ya jawo mata. Abu guda ne dai. Ya sanyawa ransa sai ya bi kadin dukan da aka yi mata a cikin gidansa. Su Habitti ba a ci bulus ba. Muƙullin mota ya ɗauka ya ce da Zahra kiransa ake yi a gida game da bikin Taj ya fice. Da ya kira Salwa su tafi ba ƙaramin rawar jiki ta dinga yi ba. Bata san ina za su je ba amma hankalinta duk ya tashi. Tayi zaton ya canja shawara ne zai kai ta tasha ta koma gida. Ta dinga bashi haƙuri da magiya. Bata san damuwarsa ta ninka duk wani abu da ya shafeta ba. Ciwon Kamal ya ɗaga masa hankali sosai. Haƙurin da take bayarwa kamar ba shigarsa yake ba. Shi ne ta koma barazana "Yaya Ahmad kada ka ɓata kuɗinka. Ba zan tafi ba domin na tabbata Taj zai zo gareni da ƙafafunsa. Ko mun je Bauchi zan shigo wata motar na dawo." Ko ci kanki bai ce mata ba. Bashi da wannan lokacin. Ita kuwa bata sam ta shiga one chance ba sai da ta gane hanyar ina su ke bi. Ta zaro idanu da su ka ƙanƙance cikin kumburarriyar fuskarta. Ta kama ƙofa a tsorace tana kokawar buɗewa a titi. "Me za ka kaini ayi min? Yaya Ahmad buɗe min na fita." A haukace take dukan gilas tana neman yi masa ɓarna. Ya juyo ransa yana suya ya daka matsa tsawar da ta gigita ta. Saboda tsorata da tayi a lokacin da za a tambayeta sunanta da wuya ta faɗa farat ɗaya. "Salwa!!!" Laƙwas tayi a kan kujera har su ka isa. Su ka shiga falon tare ya sami gidan a cike fam. Zuciyarsa a take ta faɗo ƙasa daga ƙirjinsa saboda mummunan tunanin da ya zo masa. Allah Ya taimake shi su na ganinsa aka soma bashi labarin abin farincikin da aka wayi gari dashi a gidan. Idanunsa su ka sauka akan Kamal zaune a tsakiya. Wata irin ajiyar zuciya yayi mai ƙarfi sannan ya sami damar sakin ransa ya shiga cikinsu. Ko gaisawa basu gama yi ba Alhaji ya buɗe ƙofar ɓangarensa ya kira shi. "Ahmad kai fa nake jira." Da saurinsa ya tashi har yana tuntuɓe. Kamal ya sha jinin jikinsa. Ƴar hira da dauriyar da yake yi ya kasa jurewa. Ɗakinsa zai koma kawai kafin Alhaji ya neme shi. A hanyar fita ya yi kiciɓus da Salwa. Da yake bashi da masaniyar me yake faruwa sai bai canja mata ba. "Salwa? Ashe tare kuke ki ka tsaya a nan?" Ya kalli fuskarta "me ya same ki haka a fuska?" Yuuuu idanu su ka dawo kanta. Jiki a mace kamar magen da aka tsamo daga lamba two ta ƙarasa ciki tana raɓe raɓe. Ƴaƴan gidan dai babu sauyin fuska amma iyayensu ko kallonta basu yi. "Zamewa nayi." "Allah Ya sauwake" ya ce ya fita. Ita kuma ta ƙaraso aka gama yi mata sannu sannan ta matsa gaishe da su Inna. "Hajiya ina kwana?" Ta durƙusa a gabanta. "Lafiya" ita ce taƙaitaciyar amsar da ta samu ba tare da sakin fuska ba. A ranta tayi tsaki. Ai dai ba ita ce ta haifi Taj ba take wani sha mata kunu. Ko ita Innar bata fi ƙarfin a kai sunanta gaban malam ya ƙulle mata baki ba. Nan gaba ma wajen malamin Ummi za ta je domin da alama zai fi na Mami iya aiki. Muskutawa tayi ta ƙara matsowa ciki. "Mama..." Mama bata jira ta gama gaisuwar ba ta tashi abinta tana duban Amma. "Uhmmm, Jamila duba ki ga me Taj da Hamdiyya suke yi a ɗakin nan har yanzu shiru." Jin furucinta yasa gaban Salwa ya faɗi, ya sake faɗuwa. Baki ya kama rawa kamar mazari ya ji kiɗa. Dama ga fuska a kumbure. Sai tayi wani irin yanayi mara kyau duk suna gani. Umma tayi dariya "kema dai Mama da rigima kike. Ba kya ko tsoron me za a buɗe a tarar? Sabon aure basa son sa ido fa. In ba haka ba kuwa sai aji kunya." Inna tashi tayi zumbur ta bar musu wajen. Su ka dinga dariya banda Amma da bata gane manufarsu ba. "Takwara me ki ka mayar min da ɗa ne? Ki ka sani ko bacci ya samu tana yi?" "Sai ya zauna korar mata sauro ko?" In ji Hajiya. Umma da Mama sai shewa harda tafawa. Ƴaƴan na gani amma su ma basu san me ake yi ba. Ita dai Amma tashi tayi ta barsu suna kallon suman zaunen Salwa a fakaice. Ta zubawa ƙofar ɗakin Inna da Amma ta nufa ido tana jiran ganin da gaske Hamdi za ta fito daga ciki ko yaya? In tana ciki me ya kawota gidan da sassafe? Ko dai ita ma murnar ta zo taya shi? Ai kuwa da an kira iyayenta marasa kamun kai. Me zai hana su jira ido na ganin ido? Don baƙin naci an biyo shi har gida a lokaci irin wannan da yake buƙatar ahalinsa. * Duk da ba komai Amma ta ji ba amma iya maganganun da su ka shiga kunnuwanta sun fahimtar da ita me yake faruwa. Akwai wani abu da Alhaji ya yiwa mahaifin Hamdi. Jikinta kuwa ya yi sanyi sai dai wayewa da sanin yau da gobe yasa ta je musu da fuskar rashin sani. Bayan ta gama ɗorawa Taj laifin hana Hamdi zuwa cin abinci, sai ta shiga ta riƙo hannunta. "Sai da na shigo nake jin ashe jiya rigimar babanku ta haɗa dake." Hamdi ta sunkuyar da kai kawai tana murmushi "Zo ki ci abinci in kai ki gida in kuma bada haƙuri kada ace ba za a bamu ke anjima ba." Sake yin ƙasa Hamdi tayi da kanta cike da kunya. Balle da Taj ya ce shi zai kai ta. Ya ce da Amma "Akwai maganar da za mu yi da ita." "Fita idona Taj." Ta harare shi. "Please mana Ammata." "Don ƙaniyarka ka san irin bikin da ake ta yiwa Hamdi a falo?" "Ni kuma?" Hamdi ta fito da idanu. Amma kuwa sai dariya ta sami damar tsokanarta domin a yanayin fuskokinsu ba za ta so su fita ba. Gidan akwai manya da masu experience da yawa. Yanzun nan za a harbo jirginsu a gane da matsala. "Harda masu cewa ko a biyo ku da abincin nan idan ya so sai muje mu karɓo miki kayanki a gida." "Ya Rabbi, to ya zan yi? Ko kada na fita?" Kai da ganin idanunta da jin muryarta ka san hankalinta ya nausa da nisa. Kunya, tsoro da jin nauyi sun cika mata ciki. Da Taj ya dubeta sai da yaji kamar ya kamota a gaban Amma ya ɓoyeta cikin jikinsa. She looked so cute and innocent kamar ba bakinta bane ya gama zaro masa zantuka ɗazu. "Wasa take yi miki. Ko Amma?" Ya rage murya shi ma ɗin ba son jin wata magana babba yake yi a bakin ƴan gidan nasu ba. Dariya Amma tayi musu. Tana yi musu fatan alkhairi a zamansu. Sun dace sosai da juna. Sweet young Hamdiyya and Charming Happy Taj. Za ta cigaba da sanya musu ido a fakaice ta gani ko za su shirya ba tare da tsoma bakin manya ba tunda ta kula basa so a sani. Idan basu daidaita ba sai ta shiga tsakani kafin ƙaramar magana ta zama babba. Hamdi ce ƙarshen fitowa daga ɗakin bayan Amma da Taj. Salwa ta kasa ɓoye baƙinciki da kishinta a fili. Wata irin zabura ma tayi daga zaune. Numfashinta ya nemi yankewa. A zatonta turaren jiya sake janyo ɓaraka zai yi tsakaninsu. Me Hamdi take a gidan? Wata zuciyar ta kwaɓeta da sauri. Ko dai har an sami matsalar? Maybe shi ne aka turo su gida sulhu. Munafukar dariya tayi a zuci. Ta miƙe tsaye domin ta nunawa kowa matsayinta a wajen Taj. Kashe murya tayi tana kwarkwasa. "Ya Taj" Ai fa ta zo gidan yawa. Idanu sun fi goma a kanta. Hamdi wani malolon abu taji ya mata karan tsaye a wuya. Faɗi take tana nanatawa In sha Allahu ba za ta sake kiransa da Ya Taj ba. Sunan ko daɗi babu ashe, bata sani ba sai yau. Taj kuwa Hamdi kawai ya kalla tayi kamar bata jinsu. Murmushi ma take yi abinta da ƴan uwansa suke ta nuna mamakinsu akan kwanan da tayi basu sani ba. Aka dinga yiwa ƴan kwanan ɗakin Inna surutu. Su ka ce ita ta sanya su yin shiru saboda kada su tashi Hamdin da hayaniyarsu. Shi da ya san akan tsini yake ba zai yi kuskuren sake ɓata mata rai ba. Kawar da kansa ya yi kamar bai ji ba. Yana gudun me zai faru idan ya amsa. Ta sake shaƙa har wuya. Abinci ƴan uwansa su ka kawo wa Hamsi shi ne ya samu ya fita wajen Kamal. Amma ta karanci duk motsinsu. Me yake faruwa ne wanda bata sani ba? Zama bai ganta ba. Ɗakin Mama ta shige inda Inna ta shiga ta zauna jin abubuwan da bata san da su ba. Mamaki mabayyani ta nuna akan wannan sabon al'amari. "Ashe yarinyar nan bata da wayo ban sani ba? Ana soyayya dole ne?" "Gabaɗaya ta ɓata rawarta da tsalle. Halin da uwarta ta so nuna mana a gidan nan shi ne ita ma take son gwadawa." Umma kallon Mama tayi da mamaki "kada ki ce min asiri ne ya koreta, don na tabbata ko ita ce autar mata akan ƴan biye biye tsaf Alhaji zai nuna mata ƙofar gida." Hajiya ta murmusa "ai har yau bai san mun san ainihin me ya dinga faruwa ba. Bayan wani asirin ma a gabanmu take yi kawai don ta san ta ɗaure mana baki. Ai ke dai anyi abu fa a gidan nan. Allah kada Ya maimaita mana kawai." "Amin. Don dai kam ko Taj ya rasa mace in sha Allahu babu shi babu wannan yarinyar." Cewar Mama. Hirar shekarun baya su ka koma yi. Inna ta sake kaɗuwa da jin wace ce Mami. Ashe zama bai ganta ba kuwa. Dole ta dage ta nesanta Taj da Hamdi daga Salwa. * "Yaya haka Ahmad? Ni da na kira ka mu san abin yi sai ka kama kuka?" Ahmad bai san cewa duk bayanin da yaji a waya bai kama ƙafar wanda ya ji yanzu ba. Ƙodar duka biyu Kamal ya rasa kuma wai cikin su ashirin da bakwai babu wanda tasa za ta yi. Idan babu mai taimakon Kamal a cikinsu daidai yake da babu Kamal ɗin. "Alhaji bayaninka fa yana nufin duk yawanmu ba za mu amfane shi ba tunda babu jinin wanda ya dace dashi." "Haka su ka yi min bayani da likitan." "Anya ba ya faɗa bane kawai saboda baya son takura kowa?" Ahmad ya yi tambayar da basu san amsarta ba. Alhaji sai ya shiga tunani. Tabbas kowa a gidansa ya yi fice akan wata halayya. Indai ana batun sadaukarwa to Kamaluddin ɗinsa shi ne na farko. Wuyarta ka nema zai baka ko shi ne abu na ƙarshe a tare dashi. Ba abin mamaki bane in ya zamo yaƙi yarda a cire ƙodar kowa a dasa masa. Wannan tunanin kaɗai ya haskaka zuciyar Alhaji. Zai nemi Kubra ta haɗa shi da likitan da ya dace a Aminu Kano Teaching Hospital. All hope is not yet lost. Sun tattauna yadda za su yi idan aka yi rashin sa'a da gaske babu wanda jinin nasa ya yi daidai. Alhaji ya sanyawa ransa daga yau zuwa sati in ba a dace ba za su bar ƙasar. Ɗan lokacin ma ya bari ne saboda su sami damar yin booking ɗin asibitoci a ƙasashen waje. Duk wanda aka sami appointment da wuri, shi za su je. Baya son su fara tafiya a can ma ace ƙodar ake buƙata dole kuma babu mai bayarwa. Da su ka gama ne Ahmad ya ce "maganar Salwa..." "Yauwa..." ya tashi "mu je ƙasan. Wani rami nake son toshewa kafin ya zama ƙofa." Gaban Ahmad faɗuwa ya yi "Alhaji ka sami labarin tana son Taj ne? Nayi mata faɗa. Ko a hanyarmu..." "Bana fatan abin da zai sa na ci zarafin jininka Ahmad. Amma tabbas idan Salwa ta cigaba a turbar da ta ɗauka to lallai za ta fuskanci fushina." Hankalinsa ƙara tashi ya yi. Me kuma tayi? Bai sami amsarsa ba sai da su ka shiga mota ya matsa mata da tambaya saboda abin da Alhajin ya yi ya bawa kowa mamaki. Hamdi ya nema suna saukowa. Amma ta ce masa ya yi sa'a kuwa domin yanzun nan suke shirin fita ita da Hajiya da Na'ima wadda ke bin Hajiyayye za su kai ta gida. "Da kun koma kun ɗaukota kuwa" cewar Alhaji yana shafa kan ƙananun jikokinsa "ni na kawota. Idan ba a jira na mayar da ita ba sai a nemi izini na kafin a kaita gida." "Mun kusa yin laifi ashe. To Allah Ya bada haƙuri" in ji Umma. Gabansa Amma ta kawo Hamdi. Ta durƙusa ta gaishe shi kai a sunkuye. Yadda ya amsa mata da sakin fuska har Inna sai da ta jinjina lamarin. "Ni dai ba zan bar magana a cikina ba." Amma tayi maganar da ta janyo hankalin kowa gareta "da mun san aurenki ne zai dawo da Taj gidan nan Hamdiyya ai da ranar da ya fita zai dawo. Sannunki Hamdiyya tauraruwar Tajuddin." Dariya aka kama yi. Ita kuwa ta cigaba da cewa "Allah kuwa da gaske nake. Ji fa irin fara'ar da kake yi mata Yaya Hayatu. Irin ka yi na'am ɗinnan da auren hands down." Hararar ƙanwar tasa ya yi ya ce "A'a hands up." Yaran kuwa me zasu yi banda dariya. Da kowa ya nutsu ne Alhaji ya ce ina Salwa. Tana daga gefe ta kawo wuya da abubuwan da ake yi a falon. Tasowa tayi kamar ƙwai ya fashe mata a ciki. Tayi zaton magana zai yi mata a gabansu sai ya ƙara gaba ta bishi. Kowa na gani amma ba a san me yake cewa ba. "Kin ga matar Taj ko?" Shiru tayi da farko. Ya nanata tambayar da wata irin murya mai cikar kwarjini. "Kin ga Hamdiyya matar Taj ko?" "Eh" ta gyaɗa kai da sauri. "Kin kuma fahimci me yasa na nuna miki ita ko?" Nan ma eh ta ce ba tare da jiran ya kuma tambaya ba. "To kada na ji, kada na gani Salwa." Ya juya mata baya "ki je Ahmad ya mayar dake gida." * "Yarinyar nan ya nuna min" ita ce amsar Salwa ga Ahmad da ya kusan kai mata duka akan ƙin amsa masa tambayar me Alhaji ya ce mata da farko. "Wace yarinya?" Ciki-ciki ta ce "matar Ya Taj." "You are the least of my problems Salwa so ko ki buɗe baki ki bani amsa ko ki riƙe abinki duk ke ta shafa." Ahmad ya faɗi da faɗa-faɗa. Yadda su ka yi ta faɗa masa. Ya kalleta yana mai taɓe baki. "Kina gab da yin nadama mara amfani idan baki dawo daga rakiyar zuciya ba. Duk wanda ya bari tasa ta mulki tunaninsa da wuya yake cin riba. Dubi yadda gabaɗaya ki ka sauya akan wannan obsession ɗin naki. Kin zubar da mutumcinki ana ta takawa a banza." Ci kanka bata ce masa ba. Yana magana ma Ummi take turawa text tana neman inda za su haɗu yau. Ta riga tayi nisa bata jin kira. Burinta kawai Taj ya so ta ko iyayensa basa so kuwa sai sun yi aure. *** GIDAN TAJ DA HAMDI (Sponsored by annurifoods, nafsbedding and meensincense) Jeren gidan amarya ba mai yawa bane ta ɓangaren gidan Abba Habibu. Inna tayi rawar gani da nunawa fiye da tunaninsu. Ta cika gidan da komai na buƙatar amarya da ango. Sai dai kuma duk da haka Abba da Yaya basu fasa yin nasu ba. Makusantansu ma sun nuna bajinta ba kaɗan ba. Kayan zaƙi na gara irinsu dubulan, alkaki, nakiya, gireba, bakilawa da cincin Ƴar Ficika da muƙarrabansa ne su ka yi. Abin ka da tsofaffin takari, nasu ya sha bamban sosai da wanda aka saba. Iyaa kuwa gidan ƙanwarta taje a hotoro aka rakata wajen wata ƙwararriya a harkar kayan kaɗi da abubuwan abincin gargajiya. Samira Muhammad kenan, mai Annurfoods. Mace mai faram faram da iya mu'amala. Tun abin da ya haɗa Ummi da Hamdi a makaranta Iyaa take neman hanyoyin daɗa wanke iyalinta duk da su Yaya basu canja musu fuska ba. Bayan gudunmawar kuɗi da su ka bayar shi ne ta haɗo wannan. Da ta kawo kayan Yaya kasa rufe baki tayi. Wanda ta haɗawa amarya dole ta ajiye domin babu yadda za a kai Hamdi ba tare da kayan annurfoods ba. Garin kuka da kuɓewa masu kyau a madaidaitan bokiti. Sai daddawa wadda ana haɗa kayan Anti Labiba ta ce ita dai ayi haƙuri sai ta ɗiba saboda daɗin ƙamshinta. Babu warin nan mai hawa kai mutum ya rasa inda zai yi da ransa. Sai nau'in yaji daban daban. Jan yaji mai tafarnuwa da wanda babu, na daddawa da kuma na ƙuliƙuli. Niƙaƙƙiya da kuma markaɗaɗɗiyar gyaɗa (gari da paste), garin ɗanwake, garin kunu wanda yaji duka kayan haɗi da kuma soyayyen man shanu mai daɗin ƙamshi. (Samira Muhammad 08039183880, instagram @annurfoods.ng) "Altine wannan kaya basu yi yawa ba?" Faɗin Yaya tana jin kamar tayi kuka saboda karamcin da ake ta nuna musu. "Ina abin yake Jinjin?" "Haba dai, wannan yafi ƙarfin a bi shi da kalmar ina abin yake. Ke dai Allah Ya biyaki da mafificin alkhairi." Iyaa ta ce "amin Ya Allah." Sajida aka damƙawa kayan a hannunta da umarnin idan sun je gidan tunda da wuri za su fita kafin a kai amarya ta saka komai a inda ya dace. Ana haka su Amma su ka yi sallama. Allah Yasa sauran safiya ce. Babu baƙin fuska a gidan. Aka sauke su a falo. Hajiya ta fara da bawa Yaya haƙurin tafiya da Hamdi da Alhaji ya yi. Don ta rufa masa asiri ma ta ƙara da cewa yayi haka ne kawai don ya kula suna cikin damuwar ciwon Taj. Yaya tayi murmushi. Gashi dai an shigo gidan amma hannun Hamdi yana cikin na Amma a gefen Hajiya tayi mata riƙo na ƴar da ake ji da ita. "Wallahi babu komai. Da nan da can duk ɗaya ne." "Kin sami labarin Alhaji ya yiwa Taj izinin komawa gida?" Amma ta yi tambayar saboda ita fa a yanzu wannan yafi bikin ma a wajenta. "Ƙwarai kuwa..." sannan Yaya ta taya su murna. Cikin mutumci aka gama komai. Za su fita Amma da bata iya shiru ta ce da Yaya don Allah wane irin turare ne aka saka a ɗakin yake fitar da ƙamshin da su ke ji tun shigowarsu? Hajiya girgiza kai ta kama tana murmushi. Amma bata iya baƙunta ba. Sai dai idan bata ga fuska ba. Ta gode mata dai saboda ita ɗin ma surukuta ce ta hanata tambaya tun shigowarsu. Daɗin ƙamshin ba daga nan ba. Bayan kujera Yaya ta nuna musu. Inda aka ajiye turarukan wuta a cikin bokitai an rurrufe bakunansu da salatif. "Ko kunnawa ba'ayi ba. Na gidan ƴarku ne." Tashi Hamdi tayi ta bar falon. Yaya ta ƙwalawa Zee kira. Tana shigowa ta ce ta ɗauko a buɗe musu su gani. "Haba Maman Hamdi? Don Allah kada a buɗe. Ƙamshin ne ya yi min daɗi na kasa barwa cikina" Amma ta faɗi da sauri. "Ni dai ban ga komai a ciki ba. Nan kuke ta cewa an zama ɗaya" cewar Yaya tana kama guda ɗaya "in sun je gidan yanzu ma buɗewa zasu yi su zuzzuba a rufe sauran." Da ƙyar su Hajiya su ka hanata buɗe musu. Bayan tafiyarsu ta sanya a ranta lallai za ta sayi wani ta aika musu. Zuciyarta kuwa fari ƙal don daɗi. Duk da ana ta yaba ƙamshin a gidan tayi zaton na ganin ido ne kawai. Sai yanzu da waɗanda basu san dashi ba su ka yi magana ta kuma gaskatawa. Matar Halliru maƙobcinsu Hairat ce ta dinga zuzuta kyau da ingancin turarukan wata ƴar garinsu Bauchi. Da farko Yaya har cewa tayi duk turarukan Kano ace sai ta nemi na wani gari? Matar Halliru taƙi haƙura domin ta san me za su rasa idan ba a saya ba kamar na lokacin bikin Sajida. Na wajenta da basu da yawa ta kawo. Zee ta kunna da yamma. Sai da kowa ya fito tsakar gida ranar. Washe gari Yaya ta karɓi numbar Amina (08036387204, instagram @meens_incense). Ta kira su ka yi ciniki akan farashin da idan ka karɓi turaren ma sai ka ce sadaka kawai aka baka. Da turarukan su ka iso kasa rufe baki tayi don murna. Ta dai ɓoyesu kafin Hamdi ta dawo gida ranar saboda ko za ayi mata faɗa sai ta kunna. Soyayyarta da ƙamshi ta daban ce. Ga dai turaruka kala kala, kwalaccam ɗinta kuwa abar duƙan ƙirji ce (I mean it, the scent simply calms the heart), sai kuma humra irin wađanda sai hancin da yaci karo dasu ne kawai zai gane. Haka aka tattara komai aka zuba a mota domin kammala gyare gyare kafin zuwan amarya. *** Banɗaki Ummi ta shiga da waya ta turawa Alh. Usaini saƙo cewa jiya ma Salwa ta sake shafawa Taj turaren nan. Kuma da alama anyi nasara domin ta sami labari a daren aka kai shi asibiti. Daga maganar da taji Baba Maje da Iyaa suna yi bayan wayarsa da Abba Habibu da safen ta fahimci ba rashin lafiya bace kawai ta kama shi. Salwa kuma ta tabbatar mata a text. Ita Iyaa da wuri ta tafi gidan bikin. Ta barsu in sun gama girki da gyaran gida sai su biyota kafin dai a fita da amarya. Yana karantawa ya kirata. Da ta ɗauka tsoro ya bata da taji ya fashe da wata irin dariya mara daɗin ji. Da jindaɗi ya ce "Ƙarshen wannan ɗan daudun ya zo." "A'a fa, ba ɗan daudu bane" Ummi taji ba za ta iya shiru ba. Ko makaho ya shafa Taj ba zai kira shi ɗan daudu ba, balle mai ido. Idon ma irin nata mai son abu mai kyau. "Ummi kenan. Wai me ya hanaki cewa ayi aikin da za ki sami soyayyarsa maimakon wannan sakaryar Salwan?" "Bana ra'ayin namijin da kowa ke rububi." Tana ji Alh. Usaini ya yi dariyar rashin yarda. Tunanin Taj ya so ta bai zo kanta ba saboda tayi nata binciken akan waye shi. Labarin mahaifinsa kaɗai ya isheta dalilin mayar da kwaɗayinta. Sannan ta san cewa ko ana muzuru ana shaho a yadda Baba Maje yake ganin darajar Abban Hamdi, da wuya ta gaske a barta ta aure shi. Ita kuwa abin da take ji a kansa ba na irin mu'amalarta da banzayen samarinta bane. Ya girmi hakan. Shi yasa kawai taga babu mafita sama da rusa shi. Ita da Hamdi kowa zero. Mafi munin hassada kenan. "Ki tabbatar kin je kai amarya kuma kin bibiyi me suke ciki na ƴan kwanakin nan. Kin san na faɗa miki aikinsa a hankali yake ci." "Bana son yin abin da zai sa a zargeni. Ba wani shiri muke da Hamdi ba kuma kowa ya sani." "Sai ki san yadda za ki yi." Ya ɗaga mata murya kamar wata ƴarsa. Bai san bashi da wani kwarjini a idonta ba. Yana shiru ta ce "Ban gane ba? Wannan abu fa duk kai ne da riba. Idan ka damu ka sa malamin da ya yi maka aiki akan Taj ɗin ya tura aljanu su binciko maka mana. Mtseww" Wayarta ta kashe ta sake buga tsaki. "Aikin banza. Ni za ka ɗagawa mur..." Haɗiye maganar tayi cikin tashin hankali saboda haɗa ido da tayi da Siyama. Ita kuma cikin sauri da ta karanci fuskar Ummin sai ta kama ɗaɗɗaga ƙafa. "Fitsari, fito don Allah." Fitowar Ummi tayi tana wasiwasin Siyama taji wayar da tayi ko kuwa. Gaba na faɗuwa Siyama ta dakata a bakin ƙofa ta nemi mafita don kaɗan daga aikin Ummi tayi mata

Chapter 33 of 46