Share this page
ba. "Indai mijinki ne to ki manta da matsayinsa ki kama abinki a hannu. Na san komai da ƴan uwana su ke ɓoyewa game da sharaɗin da Alhaji ya bawa mahaifinki. Ni kuma in Allah Yaso Ya yarda kin shigo kenan. Allah ba zai bawa kowa damar ganin ƙarshen auren ba ballantana su cigaba da ɗora zarginsu. Hatta ƴan uwanki ina yi musu fatan samun nasarar zaman gidajensu. Abu ƙanƙani ne zai faru a ɗorawa babanku laifi. Idan kuwa ta ɓangarenki ne to da uba da miji duka a kunnuwanki za ki ji ana cin zarafinsu." Darasi mai girma Inna ta ɗora mata, saɓanin su Hajiya da aikin da su ka bata ne mai girman. Akan shekarunta taji kamar an ƙara mata ashirin saboda yadda take ganin ba za ta iya ba. Amma kuma ta sami ƙwarin gwiwa sosai. "Taj yana son ki. Ki sa ya ƙara ƙaunarki Hamdi. Ki hana zuciyarsa sakat ta yadda aurenku ba zai sami tangarɗa daga yinsa ba don Allah." Bayan ta gama ɗaukar karatun mai girma sannan Inna ta kira Firdaus ta ce su koma falo. A can aka cigaba da hira wadda ita dai amsarta bata wuce murmushi sai eh ko a'a. Tunanin da aka barta dashi yafi ƙarfinta. Abu guda ta fahimta shi ne matan gidan duka basa son auren nan ya mutu. Gashi Abbanta ya tsorata da barazanar Alhaji yana ta yi mata tuni. Cikin dabara aka sa Firdaus ta tambayeta size ɗin da taƙi turawa Taj. Da ƙyar ita ma ɗin ta sanar da ita. Sannan cikin ƙanen Taj wata ta aunata gwajin riga da siket da na doguwar riga. Sai gashi kafin magrib ta soma sakewa dasu. Naƙasun da aka samu bai wuce na rashin shigowar Kamal ko Salwa ba. Sannan ko sau ɗaya Taj bai kirata ba. Ta shaƙa tayi fam tana jiran ya tsikareta ta fashe. Ita ma Anti Zahra har fargabar zuwan Ahmad ɗaukarsu take yi. Ta san shi sarai. Laifinta zai fara gani kafin ya saukewa ƙanwar tasa kwandon masifa. *** Ikon Allah Taj da Kamal su ka gani yayinda Salwa ta soma kuka tun a bakin gate wai Taj yana wulaƙanta ta. Aka yi ta rarrashinta taƙi shiru saboda makirci. A dole Kamal ya ce ta shiga motar. Shi ne su ka tafi Happy Taj. Office ɗin Kamal dake cikin boutique ɗinsa su ka shiga. Ta sami wuri ta zauna tana goge ƙwalla. "Salwa tunda ku ke da Taj ya taɓa cewa yana son ki?" Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta. Taj yaji a duniya yanzu babu abin da ya tsana kamar mace ta dinga wasa da yatsunta. Tsaki ya ja ta dubi Kamal. "Kana ganin abin da yake yi min? Meye laifina don na ce ina son shi? Ba fa cewa nayi ya saki yarinyar da ya aura ba." "Ki dinga gyara kalamanki akan matata. Sannan kin fi kowa sanin cewa ba zan juyo ba. Ba yaudararki nayi ba so don't give me that crap wai in haɗaku." "Haɗamu ma bai taso ba tunda Alhaji ya ce..." "A wurin wa ki ka ji wannan maganar?" Ya tambayeta muryarsa a sama. "A wurin Yaya mana." Ta bashi amsa tana tura baki. Kallonsu Kamal ya yi don bai gane komai ba ya ce "wace magana ce Happy?" A taƙaice Taj ya yi masa bayanin da bai yi ba saboda rashin lafiyarsa. "Bana jin Yaya zai faɗa mata." Kamal ya faɗi yana kallonta "a ina ki ka ji?" Rigimar da Mami ta ce ta haddasa tsakanin Taj da duk wanda zai goyi bayan yaƙi aurenta ta tuna. Ta kuwa taɓe baki cike da raini. "Ina ruwanka? Kai dai burinka ba ya saki Hamdi ka aura ba?" Duka su biyu zabura su ka yi cikin ɓacin rai. "Salwa!" Kamal ya yi mata tsawar da a tunaninta ba zai taɓa iyawa ba saboda yafi Taj sanyin hali. "Ki kiyayeni wallahi." "Idan naƙi fa? Ya Kamal na fa san kana son yarinyar nan. Ko ba abin da ya kwantar da kai ba kenan? Me yasa baka taɓa yin wani ciwon allergy ba sai da Ya Taj ya aureta? Wallahi zan iya dafa izu sittin baka da wani allergy." "Kinga Salwa, kalleni nan" Taj ya yi mata magana yana cijewa don ta riga ta kai shi matakin da yake son taɓa lafiyarta. Wani abu da bai taɓa yi ba ko da wasa. Idanunta a bushe ta kalle shi. Bai san bata tunkari wannan rigimar ba sai da ta shirya mata daga gida. "Ina jin ka" "Zo ki tafi kafin wani cikinmu ya yi miki rauni." "Please Taj kada ka biye mata. Ka bar zancen raunin nan kada wani ma yaji." Kamal ya yi maganar da kana gani za ka gane yadda yake ƙoƙarin danne ɓacin ransa. "Za ka aureni Ya Taj. Allah kuwa..." Kawai ta sa kai ta fita. Bayan tafiyarta Kamal ya zo zai yi masa rantsuwar zancenta ƙarya ne Taj ya dakatar dashi. "Idan kana tunanin na yarda da zancenta har ina buƙatar ka wanke kanka to gaskiya akwai matsala tsakaninmu." Murmushi Kamal ya yi "Allah Ya huci zuciyarka." "Amma wane irin ciwo gareka Happiness?" Koda Kamal ya juya ya kalli Taj sai yaga babu alamun wasa a tare dashi. Allah Ya taimake shi ya fara ajiye magungunan allergy su antihistamine saboda rana irin wannan. Durowar magungunan ya buɗe ya fiddosu duka. "Ka ce baka yarda da zancenta ba." "Daga cikin addu'ar da nake yawan yi mana harda kada Allah Ya haɗamu son abu guda da mutum biyu basa tarayya a kansa. Zancen ciwo kuwa ai rantsuwa tayi. Tunda tana sa gaba gabas zancenta zai iya zama gaskiya." Ɗaya bayan ɗaya yabi magungunan ya dudduba. Pain relievers ne da wanda su ka danganci kwantar da abin da ya shafi allergy. "Allah Ya baka lafiya Happiness." "Amin." *** Tafiyar minti biyar a mota za ta kai mutum wani babban mall da ya yi shura a titin kafin a gina Happy Taj. Ƴan Kano da son sabon abu na yayi kusan kowa ka taɓa zai ce maka ya yi siyayya a Glory Mall. Wurin shaƙe yake da kaya na alfarma. Sannan akwai snacks irinsu shawarma, small chops, popcorn, ice cream da sauransu. Har event centre garesu a ciki. Wurin mallakar wani hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ya damƙawa babban ɗansa alhakin kula da shi. Kuma a shekara biyu da rabin farko uban ya yi alfahari da ɗansa. Ciniki ake yi na bugawa a jarida. Komai ya soma taɓarɓare musu cikin abin da bai fi sati guda da buɗe Happy Taj ba. Idan kaya ake so boutique ɗin Kamal yana da na kowanne jinsi manya da yara. Abin da ya shafi abinci kuwa harda wanda mutane basu sani ba akwai a ɓangaren Taj. Kamar wasa su ka dinga tunanin ko irin abin nan ne na ɗokin sabon waje. Idan an kwana biyu abu zai koma normal. Sai aka yi rashin sa'a kasuwa da gaske take damawa da su Taj cikin albarkar Allah. Haka kawai mutane su ka fara janye jiki. Ciniki ya yi wani irin ja da baya mara daɗi. Alh. Usaini ya shiga gagarumar matsala da mahaifinsa. Inda rashin tawakkali yasa uban ya taso shi a gaba da muggan kalamai da tsoratarwa. Indai ciniki bai daidaita ba to ya kwana da sanin zai karɓe mall ɗinsa ne ya bawa wani daban cikin ƴaƴansa. Wannan abu ya yi matuƙar tayar masa da hankali. Ya shiga faɗi tashin hanyar dawo da martabar mall ɗinsu amma abu yaci tura. Har an kai wasu masu kai musu kaya sun fara janye jiki. A irin wannan yanayin na neman hanya kowacce iri ce Allah Ya haɗa Alh. Usaini da Ummi. Cutar hassada tayi mata lulluɓi tun daga kai har tafin ƙafa a lokacin da taji labarin auren Hamdi da mamallakin Happy Taj. Ranar harda kuka sai da tayi. Zuciyarta a cunkushe tana fama da takaicin yadda ƴar ɗan daudu ta sami miji irin Taj. Ta taɓa zuwa wajen da wani saurayinta. Yadda taga Taj ta san wadda ta fita ma bata isa ta aure shi ba, balle kuma Hamdin da bata kama ƙafarta a gayu da rufin asiri ba. Wani abin kayan haushin kuma jan kunne da gargaɗin iyayenta da yayanta akan ƙanwar Hamdi da ya aura. Ko kallon banza ta yiwa Zee ya yi alƙawarin canja mata kamanni. Ranar da ta haɗu da Alh. Usaini, cikin jin zafin auren Hamdi ta fito ds niyyar zuwa Happy Taj ta ɓata ta a gaban Taj. Sai da ta iso kuma ta rasa me ya kawo mata tsoro ta kasa ƙarasawa. Haka kawai ƙafafunta su ka kaita Glory mall. Ta je wurin snacks ta sayi meatpie da lemo ta sami wuri tana ci. Amma hankalinta gabaɗaya yana kan ginin Happy Taj. "Ki tafi can mana idan nan bai yi miki ba." Kallonsa Ummi tayi za ta faɗi baƙar sai ta adana. Mutumin zai yi shekara arba'in da biyar. Ya sha shadda ƴar ubansu da ɗinki na alhazawan birni. Ga ƙamshi na waɗanda naira ta tsaga jikinsu ta zauna da kyau. Murmushi tayi masa "ba kallon son zuwa nake ba. Fatan abin da zai zo ya tayar da wurin gabaɗaya koda gobara ce nake yi." Ta kashe masa ido. "Ko zan san dalili?" Amsarta tasa ya sami interest akanta. "Kaji daɗin kaini gaba? Allah Ya kiyaye." Ta tashi tsaye. "Ko kusa. Nima burina kenan.." ya kashe mata ido yadda tayi masa. "Dalili?" "Sun kashe min kasuwar mall ɗina mana." Zama ta koma tayi "nan wurinka ne?" "Eh. Amma yana fuskantar barazanar rufewa saboda su." Dariyar mugunta Ummi tayi a zuci. Daga ranar su ka ƙulla ita da Alh. Usaini. Suna neman hanyar da za su nakasa Taj domin su gurgunta masa sana'a. A wannan rana ta asabar da Salwa ta fito daga Happy Taj cikin ɓacin rai, ta faɗa Glory Mall saboda akwai mai POS daga bakin gate ɗinsu. Tana jiran mutumin ya idar daga sallar la'sar a gefen ƴar container ɗinsa take waya da Mami. A ciki take zayyane mata duk fa abin da ta ce tayi ta gwada amma ƙarshe Taj yaci mutumcinta. "Ni dai Mami da kin barni naje masa a yadda nake. Na tabbata idan ina kwantar da kai zai dube ni." Zaginta Mamin tayi ta ce mata kuma ta kwantar da hankalinta. Ta sanar da mahaifinsu ya ce zai kira Alhajin su yi magana. Tana da yaƙinin yadda Alhaji yake ragawa Salwa don mutumcin babanta da yake gani nw. Duk taurin kansa ba zai ƙi tayin ƴa ba. Musamman tunda ba son wadda Taj ɗin ya aura yake yi ba. "Kin nuna musu kin san baya son auren?" "Eh, kuma ban faɗa musu cewa waya naji Yaya Ahmad yana yi da matan gidansu yana sanar dasu ba. Har wani cewa yake su yi wani abu kada a raba Taj da wadda yake so. Ni ko oho." "Ki daina yin komai. Da kansu za su nemi ki idan babanki ya yi masa magana." Wayarta duka a kunnuwan Ummi da Alh. Usaini waɗanda su ka yiwa juna wani irin kallo gami da murmushi. Tana gama wayar Ummi ta matsa kusa da ita su ka gaisa. Sai ta nuna kamar ita ma mai POS ɗin take jira. Abin ka da mata in an haɗu. Hira a taɓa nan a taɓa can sai gashi sun yi exchanging number. Bayan Salwa ta ciri kuɗin ne ta fito Kamal ya kirata. Babu ja in ja ta faɗa masa inda take. Shi ne su ka ɗauketa don darajar Ahmad kawai. A hanya harda basu haƙuri wai ranta ne ya ɓaci. Babu wanda ya kulata a cikinsu har su ka isa gidan. Taj ya yi zamansa a mota. "Happiness ka turo min ita in kaita gida kafin magrib." Salwa bata ce musu komai ba tayi wucewarta ciki. Ganin Kamal bai shigo ba ta tsaya ta goga hoda da lipgloss kafin ta shiga ciki. Hayaniyar mutan gidan taji daga ɗan korido ɗin da ake ajiye takalma kafin a shiga falon. Ta ƙara yin tsaki. Bata san za ta ƙi mutanen nan ba sai da taga yadda aka dinga kai kawo akan zuwan Hamdi. Yanzu kuma da alama hirar ma da ita suke yi. Sallama tayi ta shiga da wani irin farinciki a fuskarta. Bata sha wahalar haɗa ido da Hamdi ba don ita ma ɗin sallamar tasa ta ɗaga kai ta kalli ƙofa. Murmushin nasara ta sakar mata. Hamdi ta mayar mata. Daga ita har Taj ɗin sai ta fanshe wannan ɓacin ran da su ka sa ta wuni cikinsa. "Salwa ina ki ka je?" Ɗan firgita tayi domin kuwa Ahmad ne ya yi tambayar da kakkausar murya. "Da Ya Taj muka fita. Cewa ya yi na raka shi Happy Taj. Shi ne mu kaje harda Ya Kamal" "Bangane ba? Ya zai kawo matarsa kuma ya yi wani wajen. To da izinin wa ma ki ka fita?" Kafin ta bawa Yaya Zulaiha amsa Kamal ya shigo. Sai ta canja akalar tambayar. "Ko dai soyayya ku ke da Kamal?" Da wani irin sauri ya ce "Allah Ya kiyaye. Ina da wadda nake so." Jama'ar falon su ka kama ihun murna. Harda masu cewa ko a dakatar da bikin Taj saboda dama indai da amana tare ya kamata su yi aure. Wannan amsa ta Kamal ta ɓakanta ran Salwa. Yadda ya faɗa tamkar wata abar ƙyama. Ahmad kansa sai da yaji babu daɗi. Anti Zahra ta kallesu su biyun. Idan Salwa ta cigaba da zama dasu za a iya samun matsala tsakaninsa da ƴan uwansa. Ko me za ta yi ita ma jininsa ce. "Ku tashi mu tafi" ya ce da Anti Zahra, bana son Magariba tayi min. "Kai Ahmad, kamar kana dawa? Don Allah ka zauna." "Ai mun gaisa da ƙanwar tawa ko?" Ya yiwa Hamdi murmushi. "An kusa kira Yaya. So kake Ya Taj ya yi sallah shi kaɗai?" Bishir ya ce. Fin ƙarfi aka yiwa Ahmad. So yake kawai su shiga mota ya gamu da Salwa. A dole ya bi ƙannensa waje su ka tare cikin motar Taj abin tausayi suna hira. Aka sake tashi yin sallah. Hamdi ta koma ɗakin Mama. Salwa sai ta faki ido ta bi bayanta. Su Mama suna ɗakin Umma ana ta shirye shirye. "Washhh. Wannan zirga zirga Ya Taj duk ya tara min gajiya." Ƙin kulata Hamdi tayi. Kowa yaci tuwo da ita ai miya ya sha. Darajar inda su ke yanzu yasa ta kama kanta. Amma ramuwa kam zata yi gwargadon abin da aka yi mata! *** Gayya guda aka rako Hamdi bakin gate da sha tara ta arziƙi. Har ta dinga jin wani iri saboda bata kawo musu komai ba. Yawancin kowa a bayan mota ya ajiye kyautarsa. Banda likitar gidan. Yaya Kubra a hannu ta damƙa mata wata baƙar pepper bag da aka rubuta Scentmania a jiki. Ƙamshi a take ya cika gaban motar tun ba a buɗe ba. Ya haɗe da sanyin AC sai ya bada wani irin ni'imtaccen yanayi. "Zamu yi waya in miki bayanin turarukan kinji. Mun kuma gode da wannan ziyara." "Nima nagode sosai. Allah Ya saka muku da alkhairi." Suna ta ɗagawa juna hannu aka rabu a mutumce. Daga nan kuma motar ta koma ta kurame. Taga ta zubawa idanu tana kallon gilmawar ababen hawa da fitilunsu. Taj ya kalleta yafi a ƙirga ya tabbatar da gaske shi ne bata son kulawa. Murmushi ya yi. Ya taɓa wayarsa wanda Hamdi ta gani da wutsiyar ido amma ta share. "Hello, Salwa..." Iya abin da taji ya ce kenan ta juya a fusace su ka haɗa ido. Wayar a gefe ya ajiyeta. Babu kuma wani abu da zai nuna mata wayar yake yi. Dariyar kamata ya fara sai yaga babu fuska sam. Ta tsuke baki kawai ta sake juyawa. Har wani numfashi mai nauyi ya kula tana saukewa. Gabaɗaya sai yaji ya kasa sukuni. Dama ya san za ta ji haushi. Amma ya yi zaton za ta jira bayani daga gare shi. "Mrs Happy" Shiru. "Hamdi" sunan nan har tafin ƙafarta take jinsa idan ya faɗa amma ko motsi bata yi ba. "Please ki juyo.." nan ma biris tayi dashi " to kada ki ga laifina duk abin da ya biyo baya." Gyaran murya taji ya fara ta taɓe baki. Wato zai fara yi mata daɗin bakin maza da take ji ....katse mata zancen zucin ya yi. "Dil ne yeh kaha hain dil se (my heart has said this to your heart)" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Banda waƙar India don Allah. Wallahi kunya ma nake ji. Bana son namiji yana..." "Mohabbat ho gayi hai tumse (I have fallen in love with you)" "Na shiga uku" Hamdi ta sanya hannuwanta biyu ta toshe kunnuwanta "ka bari don Allah zan saurareka." "Meri jaan, mere dilbar (my life, my love)." "Ya Taj wasa nake. Ba ma fushi nayi ba..." "Mere aitbaar karlo (have faith in me)" "Happyyy" ta faɗi kamar tayi kuka wai yau ita ce miji yake yiwa waƙar india. "Jitna beqarar hoon main (how much restless I am)" Titi yake kallo abinsa yana sakin baiti. Ta rasa yadda zata yi dashi. Kawai sai ta kai hannuwanta ta cupping fuskarsa wanda ya sanya shi ɗauke wuta na wucin gadi. "Allah na haƙura." Ta fada a hankali. Gefen titi ya gangara da motar ya ɗaga handbrake tare da canja giya zuwa 'P'. Ya juyo su ka haɗa ido har lokacin bata cire hannuwanta daga fuskarsa ba. Shan kunu ya yi "Ki barni in ƙarasa. Ba ke nake yiwa ba." Ita kuma ta marairaice masa "Don Allah kayi haƙuri to sai na fita." Ƙwayar idanunta yake kallo sai ta rufe idon. "Can I have that kiss now?" Zame hannuwanta ta soma yi daga fuskarsa ya janyota gabaɗaya. Garin ya ɗorata a cinyarsa handbrake ya sauka. Motar ta ɗan yi gaba amma ba da sauri ba saboda giyar da ya canja. Rungume shi tayi ƙamƙam tana salati ta sanya fuskarta a tsakiyar ƙirjin shi. "Wayyo Allah Abbana...Yaya..." Bata san lokacin da ya sake tsayar da motar ba. Hannunsa đaya kawai taji a ƙasan haɓarta ya ɗago kanta sama. "Salwa bata da matsayi ko kaɗan a wajena kinji." Kai ta gyaɗa a hankali. "Fitar da muka yi ba abin da kike tunani bane. Happiness ne yake ƙoƙarin fahimtar da ita ta haƙura." "Ai na yarda." "Akwai waƙa da ta dace da irin wannan yanayin." Ya ɗage gira. "Kada kayi don Allah." "Ke dai???" "Bana so." Ta turo baki. "Hamdi." "Na'am." Ta ce tana mai jin nauyinsa don yaƙi sakinta balle ta koma mazauninta. "I love you." Ƙasa ta so yi da fuskarta don kunyar yanzu tafi ko yaushe. Sai dai Taj yaci alwashin yau sai ya rage wani abu a kunyar nan ya tafi dashi gida. Shammatarta ya yi kamar zai yi magana taji saukar leɓensa akan nata. He was so gentle amma ya kashe mata jiki har ta sake narkewa a jikinsa bata sani ba. Rungumeta yayi a haka kanta a gefen kafaɗarsa kamar mai bacci. Shi kuwa wani irin contentment ya samu ds nutsuwa a zuciyarsa. Basu yi aune ba su ka ji ana ƙwanƙwasa gilas ḍin motar. Mutanen dake waje suna cewa ko lalacewa tayi ko kuma mai ita wani abu ya same shi. Kamar ƙifta ido Hamdi ta koma wurinta tana raba idanu. Taj ya kalli mutanen ya ga da wuya su fahimci matarsa ce idan su ka gan shi da mace. Kawai sai ya canja giya ya yi gaba. Shi da Hamdi su ka haɗa ido su ka kama dariya. _Uwargida....I see you! SonSo Sis Juwairiyya_ RAYUWA DA GIƁI 23 Batul Mamman Har su ka ƙarasa gida idan sun kalli juna sai sun yi murmushi. Abin da ya ɗaurewa Hamdi kai shi ne yadda Taj har wani kawar da kai gefe yake irin na masu jin kunya. To ai ita ma kunyar take ji. Kuma ita ya dace ta dinga yin haka. Sai gashi kafin tayi yake yi. Gajiya tayi lokacin sun iso layinsu ta kalle shi. "Wai mene ne?" Gefe ya kaɗa kai yana wani rufe ido "Awwnnnnn, ni ki daina tambayata. Kin fi ni sanin ko mene ne." Murmushin fuskar Hamdi ɗaukewa yayi. Ta soma harararsa. "Banda waƙa kuma harda irin haka kake yi?" "Irin yaya?" Ya tambaya kamar bai gane manufarta ba. "Meye wani awwnnn don Allah?" Hannu ya kai ya shafa kumatunta "Saboda ina son ganin wannan hararar da juya idanun naki. You always look cute." Murmushi ta soma yi ya kuwa sake cewa "awwnnnn" yana dafa saitin zuciyarsa. Wannan karon dariya tayi. Irin dariyar da bai taɓa gani daga gareta ba. Zuciyarta tayi fari kamar auduga. "Kin san wani abu? Zo mu shiga ciki kafin haƙurin Abba ya ƙare." Bakin ƙofar gidansu ta kalla. Ai kuwa Abbanta ne yake ɗan leƙowa. Bai yi zaton za su yi dare ba. Kuma sun iso ɗin ma taƙi fitowa. Shi ne ya kasa sukuni. Kada fa ta biyewa Taj al'amari ya kwaɓe a gaba. "Zan kira ki idan naje gida. I hope ba da wuri ki ke bacci ba." Bata iya bashi amsa ba da ta hango inuwar Abban da gaske. Kamar an tsikareta ta fito da sauri. Tana hango shi ya koma cikin gida ta bi bayansa. Taj ya yi murmushi kawai. Ya juya baya zai yi ribas ya yi arba da ledojin da ƴan uwansa su ka ajiye mata. Parking ya gyara ya ɗebi yadda hannuwansa za su iya ɗauka ya je ƙofar gidan yana sallama. Caraf yaji Abba yana yiwa Hamdi faɗan kada ta manta da maganarsu. Shi ba zai iya ja da Alh. Hayatu ba. Jin sallamarsa yasa shi yin shiru. Hamdi kuma ta ruga ciki da sauri. "Taj baka tafi ba?" Ya fito waje. "Saƙonta ne ta manta." Ya nuna ledojin hannunsa. "Harda wahala haka?" "Ƙanwarsu su ka yiwa. Bari na shigar mata dasu." Taj ya wuce ciki kafin Abban ya ce shi zai karɓa. Hakan zai zama raini ma. A tsakar gidan ya sake sallama, Yaya ta amsa da yi masa izinin shiga falon. Akan kujera ya ajiye ledojin ya ce da saura. Ta saki baki har yaje ya dawo. Lokacin ita da Abba ne a falon. Waɗanda ya dawo dasu har sun fi na farkon yawa. "Mene ne haka Taj? Daga zuwa gaishe su kuma sai ka haɗota da wannan kayan?" "Babu ruwana Yaya. Ƴan uwanta ne su ka bata." Yaya dai bata jidaɗi ba. Ta san kwaɗayi ba halin Hamdi bane to amma za a iya fassara ta dashi ga wanda bai santa ba in yaga kayan. Da dai bata karɓa ba. Kiranta tayi ta dawo falon da sauri don kiran ta san na faɗa ne. Kaya dama ta tafi cirewa. Wata free doguwar riga ta saka da hula a kanta. "Me yasa ki ka karɓo kayan nan Hamdi? Tarbiyyar gidan nan kenan?" Durƙusawa Hamdi tayi a gaban kujerar da ya zube kayan tana ƙare musu kallo. Ita kanta bata san sun kai haka ba. "Allah Yaya ba roƙa nayi ba. Ba ma a hannuna su ka bani ba." Kusa da ita Taj ya dawo ya zauna a ƙasa ya fara sauko da kayan gabansu. "Yaya yanzu abin hannun ƴan uwana kike faɗa a kai? Kin san da roƙa tayi nima ba zan yarda mu taho dasu ba ko?" Yaya ta ce "Kada ka kare mata. Ai ta san irin abin da ya dace da wanda bai dace ba." Hamdi ta sunkuyar da kai ta ce "Ki yi haƙuri." "Ni ya kamata na bata haƙuri. Na zata mun zama ɗaya ne ko ban aureki ba shi yasa ban ɗauki karɓar kayan a matsayin laifi ba." Ya yi wani iri da fuska yadda za a tausaya masa "a zatona na kai matsayin da zan iya tambayar Halifa da yake ƙarami abu idan ina so. Na ɗauka hakan ne a wajenku ku ma. Kuskuren daga gareni ne. Ki yi haƙuri." Yaya dariya ta kama yi. Abba kuwa ya girgiza kai don dama ya san za a rina. "Anya Taj ba ɓatan kai kayi na zaɓen aiki ba? Da lauya ka dace. Yanzu Fisabilillah wannan marairaicewar duk don nayi maganar karɓar kaya ne?" Da rashin jindaɗi kamar gaske ya ce "To Yaya abin hannun ƴan gidanmu ai baya cikin wanda za a yi mata faɗa a kai ko?" "Baya ciki. Magana ma dai ta wuce." Ya kalli Abba dake yi musu dariya da Hamdi da kana ganinta ka san taji daɗin ceton da ya yi mata a hannun Yaya. "Gara dai na baki haƙuri kuma nan gaba duk mu kiyaye." "Nace magana ta wuce Taj." "Mungode. In sha Allah zan yi musu magana su ma kada su sake..." "Ya Rabbi. Taj a bar maganar nan. Ni na fara kuma na janye." Yaya ta faɗi da ta rasa yadda za tayi dashi ya yi shiru. Tashi ma tayi tace musu sai da safe. In ta biyewa Taj sai ta koma basu haƙuri tana tumami a ƙasa. Ai kuwa su ka sanya dariya harda shi uban gayyar. Yaya da Abba na miƙewa ya ɗaga hannunsa yana kallon Hamdi. Bata kula da cewa basu gama fita ba ta tafa dashi a

Chapter 22 of 46