Share this page
kalamansa gare shi masu zafi su ka dinga dawo masa da wata irin amsa kuwwa. Shi ya faɗe su amma yau yafi Abba Habibu jin zafinsu. Nadama da tulin dana-sani su ka sarƙafi zuciyarsa. Tabbas tun a jiya zuciyarsa ta shiga alhini da jin nauyin abubuwan da ya yi a baya. Amma a wannan sa'ar, da Habibu ya zo gabansa amma ko kusa fuskarsa bata nuna alamun zuciyarsa na ɓoyon baƙincikin sadaukarwar matarsa ba. Hasalima tuhumar kukan ƴarsa yake yi har yana shawartar ta da kada tayi abin da su da aka yiwa alfarma za su ji babu daɗi. Sai ya ji komai ya kwance masa. Babu sauran jin kai da ƙafafa. Shi Hayatu ya yarda ƙaddara bata fi ƙarfin kowa ba. Zaɓin yadda ɗan Adam zai tafiyar da halin da ya tsinci kansa shi ne ma'aunin dacewa. "Alhaji lafiya? Me ya faru kuma?" Firgigit Alh. Hayatu ya dubi su Hajiya dake tsaye da wasu cikin ƴaƴansa suna kallon shi. Kawar da kansa ya yi gefe bai cewa kowa uffan ba. Kallo guda Inna ta yiwa yaran nasu su ka fahimceta. Kafin wani lokaci dukkaninsu sun bar wajen. Masaukinsu Ahmad ya ce su zo su tafi saboda asibitin ba a jinya. Kamal kuma yana buƙatar hutu sosai tunda ko magana bai fara yi ba. Ya dai dawo hayyacinsa amma yana cikin magagin ciwo. "Mubina tare za mu tafi ki samu ki ɗan yi bacci ko yaya ne." Ya dubi Taj "ka zauna da Hamdi sai ku taho tare da su Alhaji." *** Tsaye a bakin gadon Yaya, Abba Habibu ne da wata nurse. Sharuɗɗan shiga ICU ɗin ta bashi wanda a ciki ta nanata masa banda ɗaga sauti cikin magana ko kuka. Ya tambayi ko zai iya taɓa ta tayi masa izini amma shi ma ba riƙo mai ƙarfi ba. Komawa tayi table ɗinta a can tsakiyar ɗakin ta barshi gefen da aka keɓewa Yaya. Abba Habibu ya daure sosai ya hana kansa kuka ko da a zuci. Gani yake da zarar ya karaya wani abu zai iya samunta. Hannunsa ya ɗora akan nata ya riƙe kamar zasu yi musabaha. "Ashe waliyya nake aure ban sani ba? Gaskiya ki tashi haka nan in kwashi tubarraki." Kamar daga sama yaji muryar Yaya tana magana a hankali sosai. Salati ne take yi da sauri-sauri cikin kiɗima. Abba Habibu ya ranƙwafo kansa su ka haɗa ido. Ai da ya tabbatar ta tashi da saurinsa ya juya zai fita domin ya kira nurse. Ita kuwa Yaya ta sake damƙar hannun tana mai jin tsoron kada ya fita ya barta. "Sannu. Nurse zan kira a zo a duba ki." A hankali ta rufe ido ta buɗe cikin nutsuwa. Sai a lokacin ta dawo hayyacinta. "Yaushe ka zo?" Kafin ya amsa ta kaɗa kai "kai ne ɗin dai ba gizo idanuna suke ba ko?" "Ni ne Jinjin. Yau na zo. Yaya kike ji a jikin naki? Ki bari na kira Nurse." Cikin ƙanƙanin lokaci likitoci biyu da nurse su ka tsaya akanta. Aka duba lafiyarta sosai su ka tabbatar cewa babu sauran matsala. In sha Allahu bata cikin haɗari. Sannan aka bata awa guda ta sake hutawa kafin a mayar da ita ɗaki. Wannan abu ya farantawa Abba Habibu rai sosai. Bayan fitar likitocin waɗanda su ka jima suna yabonta kafin su tafi, Yaya ta dubi Abba Habibu. Bayani ta so yi masa yace sam bai yarda tayi magana ba. "Ki bari sauƙi ya samu shine babban burina. Ina so dai ki saka a ranki cewa kin yi jihadi kuma ko kaɗan baki ɓata min rai ba." Lokaci na cika ko minti biyar ba a ƙara ba aka gangaro Yaya zuwa ɗakin da hukumar asibiti ta tanadar mata na musamman domin karramawa. VIP wing aka nufa da ita wanda sai an shiga lift an sake ƙara hawa uku akan inda su ke. Tun a ƙofar ICU ɗin Hamdi ta kama mata hannu tana biye dasu. Idanunta jazur duk ta fita hayyacinta amma a haka take ta murmushi saboda kada ta karyar mata da zuciya. Taj tsayawa yayi tare da Alhaji. Yana kallo su Hajiya su ka bi su a baya. "Ka bi su mana" cewar Alhaji gare shi. "Abin da ya hana ka bin su nima shi ya hana ni Alhaji." Ya kalli Alhajin da ɗan murmushi a fuskarsa "na san ba surukuta ce ta hana ka bin su ba." Alhaji ya numfasa yana bin hanyar da aka gangara gadon Yaya da kallo. Ya jinjina kai sannan ya zauna a kan kujerar. Taj ma kusa dashi ya zauna su ka kasance gefe da gefen juna sun jingina baya da bango. "Ɗan Adam ba ya gane cewa ba a bakin komai yake ba sai ya ga ikon Allah a inda yake tunanin wayo ko dabararsa sun ishe shi." Kallonsa Taj yayi yana sauraronsa da kunnuwan basira amma bai ce komai ba. Alhaji ya cigaba da magana. "Idan wani ya ce min ɗan cikina mace ma ba namiji ba zata ci abinci da sana'ar abinci wallahi zan ƙaryata Taj. I was so confident cewa Allah Ya lamunce min rayuwata akan tsarin da nake so. Ina da kuɗi kuma nayi muku tarbiyya daidai gwargwado. Fitintinun zamani da ake kuka dasu babu ko ɗaya a cikin gidana. Ƴaƴana duk inda su ka shiga ana alfahari dasu. Na zata..." muryarsa ta kama rawa "Taj na zata gobe na kamar yau zata cigaba da kasancewa muddin rai. Hmmm" Ya sauke ajiyar zuciya da ƙarfi. "Tajuddeen Hayatu sai ka zaɓi kitchen. Sana'ar da bayan ƙiyayyar da nake yi mata ban taɓa hango wani nawa cikinta ba. Kuma kamar da gayya sai ga ka da auren ƴar Habibu. Wato Taj da ace zan iya fito da zuciyata ka ga tsanar da na yiwa auren ku a dalilin Habibu, da ko da wasa ba za ka tunkare ni da maganar Hamdiyya ba." Taj ya yi kasaƙe yana jin furucin mahaifinsa dalla-dalla. "Subhanallah! Komai yana tafiya cikin tsari da ƙudurin Al-Hakimu. Ba don auren ku ba da babu abin da zai kawo mahaifiyar Hamdi inda muke ko da a asibitin nan take aiki. It's like everything happened for this day Taj. Allah Ya rubuta da ƙodar matar Habibu kuma surukarka Kamal zai cigaba da jan numfashi a duniya. Kuma duk tarin shekaruna sai a yanzu na gane wannan izinar." "Tsarki ya tabbata ga Sarkin da gyangyaɗi da bacci ba sa cikin siffofinSa." Taj ya faɗi cikin shauƙin alawar imani wadda zaƙinta yakan tashi a lokutan da bawa ya yaba wa sarautar Ubangijinsa, gatansa, majiɓincin lamuransa. Alhaji ya gyaɗa kai sai da raunin murya ya ce "Zuciyata ta cika da kokonton karɓuwar dukkan alkhairi na na baya." Wani irin kallo Taj ya yi masa ya ce "Alhaji me ya sa za ka yi wannan tunanin? Don Allah ka kyautatawa Allah zato." A gurguje Alhaji ya bawa Taj labarin abin da ya gama tunawa ɗazu akan zuwan Abba Habibu neman taimako wajensa a shekarun baya. "Ka san Annabi SAW ya gargaɗe mu da gujewa girman kai da illarsa akan ayyukan ladan mu." "Haka ne." Cewar Taj da sauri yana jiran yaji sauran abin da Alhaji zai ce. "Dole na daina yaudarar kaina idan ina son ganin daidai. Tabbas tuntuni na jima da ji a raina cewa Habibu ya tuba. A zuciyata ina muradin janyo shi jikina in inganta masa rayuwa. Amma a gefe guda ina tunanin makomar mutumcina a idon duniya. Ina ƙyamar a ce ina mu'amala da mutum irinsa." Muryarsa ta koma abin tausayi a yayinda yake cewa "kaga gabaɗaya fushin nawa ya zama ba don Allah ba. Girman kai ne kawai ya hana ni yin abin da ya dace ba wai don ban san ya dace ɗin ba. Tun girma da arziƙi ban nemi shiri da shi ba gashi yanzu dole in ƙanƙantar da kai a gaban sa tunda girman da arziƙin nasa ne. Kowa yaƙi sharar masallaci..." "Yaya Hayatu dai ba zai yi ta kasuwa ba!" Tare su ka juya da jin muryar Abba Habibu a gefen su. Abba Habibu ne tsaye shi da Hamdi. Ganin su ya sa su miƙewa su ma. Tun shigar su ɗaki, Yaya ta ce Hamdi ta koma su dawo tare da Taj. Ta hango shi yana ja da baya. Mama ta ce musu tana tunanin yana jin nauyin fuskantarta ne bayan ta gamu da lalura a dalilin ɗan uwansa. "Ai kuwa ba zan yarda da wannan tsirfar ba. Maza bi shi ki ce ina nemansa." Da ta fito sai ta manta a hawa na nawa su ka baro su. Ta koma tambaya shi ne Abba Habibu ya hana Umma da tayi yunƙurin rakota biyota. Ashe rabon za su ji maganganun su Alhaji ne. "Habibu..." Alhaji ya fara cewa da wata ƙaramar murya kamar ba shi ba. Sai dai Abba Habibu bai jira ya gama magana ba ya girgiza masa kai. "Ko me za ka ce don Allah ka bari indai ina da sauran mutumci ko yaya a idon ka. Ya wuce. Komai ya wuce in sha Allahu." "Ba za ka bari na baka haƙuri ba?" Lura yayi Taj ya yiwa Hamdi alama suna shirin barin wajen ya koma gare su "kada ku tafi." Abba Habibu ya tsaya tare da yaran nasu suna kallon Alhaji. "Ƙaddarar auren ku ita ta kawo mu wannan ranar saboda haka ina so ku shaida kuma ku taya ni bawa Habibu haƙurin dukkan wani abu na rashi daɗi komai girma ko ƙanƙanta da na taɓa yi masa." Da rashin jindaɗi Abba Habibu ya ce "Amma na ce ya wuce. Ban riƙe ka ba wallahi." "Kayya dai Habibu. Zuciya tana son mai kyautata mata ne. Abubuwan da nayi ko bakin ka bai faɗa ba na san dole rai ya sosu." Murmushi kawai Abba Habibu ya yi ya ƙara maimaita cewa komai ya wuce. Su ka koma ɗakin Yaya tare. Alhaji gabaɗaya ya kasa sakewa duk yadda Abba Habibu da Yaya su ka yi ta ƙoƙarin nuna babu komai. Hakan yasa su Hajiya tsangwamar kansu su ma. Tun abin yana burge Taj har dai ya ƙosa su bari haka nan. Alhaji yana ta maimaita ban haƙuri. Abba Habibu yana ƙoƙarin nuna komai ya wuce. Iyayen su mata kuma suna taya mazan su. "Alhaji da dai kun bar abin nan haka kun fara tunanin gaba. Misali kaga kai sai kayi fama da su Daddy (Yaya Babba) kafin su karɓi uzurinka na ƙin faɗa musu ciwon Happiness da wuri. " Ya juya ya kalli Abba Habibu "su Zee za su iya saurin fahimta idan ka kira su amma Inna Luba dai ban sani ba ko za ta yarda ba sayar da ƙodar Yaya kayi ba." Ya mayar da duban sa ga su Hajiya yana sosa tsakiyar kai "yau dai ya kamata ku kikkira naku ƴan uwan ku ma ko kuwa?" Ɗakin ya yi tsit. Taj ya harba bomb ya barsu da jiran tashin sa. Wayar da basu yi tunanin kira ba a tsukin kwanakin baya sai yanzu su ke tsoron abin da zai biyo baya. Tabbas ƴan uwan kowannen su za su ji babu daɗin ɓoye musu zancen nan ba. Da ya kula attention ɗin su ya samu don irin su Inna har an ɗauko waya sai cewa ya yi "amma dai kada ku kira yau domin tunda magriba ta wuce a gida dare ya riga ya yi. Zancen zai iya hana wasu bacci. Ga masu BP da ƴan rikicin tsufa." Mama dai hannu ta ɗaga za ta kai masa duka ya zille da sauri yana dariya. Su ma ɗin su na son yin dariyar amma babu hali. Zungurin da ya yi musu akan wayoyi masu mahimmanci da ya kamata su yi duk ya ɗaga musu hankula. "Zo mu tafi Hamdi. Its late and I am tired." "Haƙƙun! Sannu mai mata. Wato ta zo ku tafi ko? Kai babu ruwan ka tunda mu tayar mana da namu BP ɗin kuma za ka hana mu bacci ba." Umma ce tayi maganar tana harararsa sama da ƙasa. Dole kowa ya dara kuwa har Yaya akan gadon ta. Daga dai su ka yi sallama domin su ƙara raguwa. Abba Habibu kaɗai za a bari. Su Alhaji gabaɗayan su kuma su ka fito tare. Agogo ya nuna ƙarfe uku da kwata na dare. A muhalli uku bayin Allah suna kan abin sallah cikin ganawa da Ubangiji SWT. Abba Habibu na zaune hannuwa a sama bayan ya idar da nafila yana mai ƙasƙantar da kai cikin neman yardar Allah. Fatansa Yaya da Kamal su koma gida da ƙafafun su. Sai kuma ya miƙa dukkan al'amuransa, na iyalinsa da na dukkan wanda mu'amala ta haɗa su komai ƙanƙanta ga Allah SWT. A cikin ɗakin Alhaji ma shi kuka yake yi sosai yana roƙon gafarar Sarkin Sarakuna SWT. Hakan kuma take tsakanin Taj da Hamdi. Gajiyar da su ka kwaso bata hana su raya daren da sallah ba domin kyakkyawan fata akan gobe. A ɗakin Kamal, idanu ya buɗe tar cikin hayyacinsa. Tashin farko ya kai hannunsa ciki ya tabbatar akwai yanka alamun an yi masa aiki. Bai san lokacin da ya runtse idanunsa ba yana faɗin "Allahu Akbar. Allahu Akbar. Allahu Akbar" *** RAYUWA DA GIƁI 39 Batul Mamman💖 Allahumma Balighna Ramadan...AMEEN Saƙon ta'aziyya ga ƴar uwa kuma shugabar mu ta WOMEN OF WORDS wato Hassana (Sanah) Sulaiman Ismail Matazu bisa rashin mahafinta da tayi. Allah Ya jiƙan shi. Ya gafarta masa. Allah Ya sa ya huta. Ya baku dangana. Amin Idanun Salma tsilli-tsilli kamar an kasa gurjiya a faranti. Irin yanayin nan da akan samu a wajen munafukin da ƙaryarsa ta ƙare. Sam ta rasa gane me ma ya kamata tayi tun bayan mahaifinta ya sanar da ita baƙin labarin da a wajenta gara mutuwa sau dubu a kan shi. Wai an ɗaura aurenta da Alh. Usaini. "Kaiiiii. Wallahi ba zan yarda ba. Ni ba zan zauna da shi ba ko sama da ƙasa za ta haɗe. Taj nake so kuma shi zan..." Kaf taji saukar duka akan laɓɓanta. Dukan ya shige ta kuwa domin babu arziƙi tayi shiru sai zugi a bakin. "Wallahi Salwa idan na ƙara jin sunan Taj a bakin ki zan iya tsine miki. Shashashar banza wadda bata san ciwon kanta ba." Baki za ta buɗe ya juya bayan hannunsa a fusace zai kai mata mangara dole ta fasa yin maganar. "Ko mata sun ƙare kina tunanin Taj zai aure ki? Ke ko yana son ki ina mai tabbatar miki Alh. Hayatu ba mahaukaci bane. Ba zai taɓa amsar ki a matsayin suruka ba." "Na ji amma don Allah ka kashe auren nan. Ba zan iya zama da mushiriki ba" "Har kura za ta ce da kare maye? Ba ki ji kin bawa kan ki dariya ba Salwa?" Ya faɗi yana yi mata kallo irin na wadda ta rainawa kanta hankali. Tashi ya yi ya kalli ɗakin hotel ɗin yaji wani abu ya sake turnuƙe masa zuciya. Wato dai da gaske da bahaushe ya ce son zuciya, ɓacinta. Ko a tatsuniya shi bai taɓa jin an ɗaura aure a ɗakin hotel ba sai da shi da kansa ya karɓi sadakin ƴarsa. Yadda abin ya kasance ya fi kama da almara. * Ɗazu da azahar mahaifin Alh. Usaini ya je hotel ɗin da su ke shi da Salwa. He got the shock of his life lokacin da ƙanin Usaini ya ƙwanƙwasa ƙofar su ka ji muryarsa yana cewa. "Ƙar ki taɓa ƙofar nan. Kada ki buɗe." Ransa kuwa ya sosu fiye da tunani. Dama can barazana yayi a reception har aka rako su ɗakin. Saboda haka sai ya yi wa ma'aikacin hotel ɗin inkiya da hannu ya yi magana. "Yallaɓai baƙo ne da kai a ƙasa." Da sauri Alh. Usaini ya ce "kada ka bari ya hawo gani nan saukowa. Ƙanina ne. Dama mun yi waya na faɗa masa ya same ni a nan ɗin." Ya ɗaga yatsa ya gargaɗi Salwa "zan fita kuma na rantse da Allah idan ki ka min halin jakancin nan naki ki ka fito sai na ɓaɓɓalla ki. Wawiya kawai. Dalla can gafara in wuce." Ta murguɗa baki tana yatsine fuska "jaka tana can gidan jaki mai furfura." 'Yau kuma jakuna mu ka koma' Baban Alh. Usaini ya jinjina kai yana zancen zuci. Ran Alh. Usaini ya ƙara ɓaci sosai ya ɗaga hannu ya zabga mata mari. "Iyayena ki ke zagi Salwa? Iyayena?" Kumatu ta fara riƙewa ta ce "Ni ka mara?" Sai kuma ta cakumu wuyansa "wallahi ba ka doki banza ba. Yadda kake jin kana da gata nima ina da shi." "To gatan naki ya zo yanzu don uban mutum." Daga nan sai sautin duka da kukan Salwa da kuma maganganun Alh. Usaini. Baban ya nuna wa ma'aikacin hotel ɗin lallai ya buɗe kafin ayi kisan kai. Da yake tsoron afkuwar ɓarnar tafi yawa akan privacy ɗin costumer, dolensa ya buɗe. Su ka yi mummunan gamo. Tsananin fushi da ɓacin rai ya sa Alh. Usaini yiwa Salwa dukan biredi. Ita ma kuma ta samu nasarar jifansa da abubuwa don har goshi ta kumbura masa. Sandarewa ya yi a lokacin da idanun sa su ka sauka cikin na mahaifinsa da aka buɗe ƙofar ɗakin. Ya saki Salwa a gigice kamar wanda ya ɗauki garwashi ya kama rantse-rantse. "Wallahi biyo ni tayi Baba. Duk abin da ka ke zato ba haka bane. Sam ni ba na harkar mata." Ya sassauta murya sosai "Salwa faɗa masa gaskiya. Ai babu komai tsakanin mu ko?" Maimakon ta faɗi gaskiya sai ta zaɓi amfani da wannan damar. Zubewa tayi a ƙasa ta kama kuka. "Mene ne tsakanin ku?" Baban ya fara tambayarta sai ya fasa ya dubi wanda ya rako su "kwanan su nawa a nan?" "Kwana uku ne." "Shike nan. Kana iya tafiya." Bayan ya fita Baban Alh. Usaini ya buƙaci Salwa ta bashi numbar wani nata su yi magana. Tana jin haka idanunta su ka raina fata, ta kasa motsawa. Sai ya kalli ɗansa. Yana iya ganin tsananin tashin hankali a tare da shi. "Ka karɓar min numbar wanda zai zo ya karɓeta ta koma gida." Jikinsa na rawa ya tashi ya buɗe handbag ɗinta ya ciro wayarta. Wayar ma a kashe sai da ya kunna sannan ya bata don ta buɗe wayar. Jikinta ya yi la'asar don ta kula tsoron babansa yake yi shi ne ta ce "Ka bani abin da nake buƙata in tafi da kaina." "Ai baki isa ba. Wallahi gara a zo a ɗauke ki in san na rabu da ƙaya." Tsawa taji daga sama kafin ma ta sake yin gardama daga babansa "Ke! Bani number na ce yanzun nan. Ki tabbatar wadda za ki bani mai shiga ce." Da ka ta karanto masa numbar Babanta saboda Ahmad dai baya nan sannan bata ga alamun za su wanye lafiya ba idan tayi ƙarya. Waje ya fita da ya yi dialing numbar. Salwa ta matsa kusa da Alh. Usaini kafin ya dawo. "Kaga ka bani abin da nake nema na tafi tun kafin ya dawo. Ban san me yake shirin yi ba kuma ba na burin sani." "Hummm...kin makaro. Ƙaryar da ki ka yi masa da alama ke za ki kwana a ciki don na san dole ya kira baban ki a zo a ɗauke ki." Wajen rabin awa ya share yana wayar kafin ya dawo. Umarni ɗaya ya basu kafin ya fita. "Zan dawo gobe in sha Allah. Ina fata idan na zo na same ku tare. Idan ka bari ta tafi Usaini to ka tabbatar babu ni, babu kai wallahi." Yana gama magana su ka fice. Alh. Usaini ya ƙulle ƙofar ya dinga naushin bango kamar mahaukaci. Salwa jiki na ta tsuma ta ɗora hannuwanta akan kunnuwanta tana hawaye. Gabaɗaya a tsorace take kuma tayi imani motsin kirki idan tayi sai ya sake jibgarta. * Ko awa guda ƙwaƙƙwara Abban Salwa bai iya sake yi ba ya biyo hanyar Kano tare da ƙannenta. Saboda munin labarin da ya samu sai ya kasance ko murnar ganinta da aka yi bai yi ba. Mutumin da ya kira shi ya faɗa masa cewa ya same su da ɗansa su na rigima harda doke-doke. Shin yaushe lalacewarta ta kai haka ba tare da ya sani ba? Yanzu ya ƙara yarda duk wanda ya sayi rariya dole ya ga zubar ruwa. Cikin dalilai huɗu da Manzon Allah SAW ya hori musulmi da aure, guda ɗaya tal ya duba lokacin auren Mami wato kyau. Ƙwarai ta haifa masa kyawawan yara abin nunawa ta wannan fannin. Amma a halin yanzu hatta mazan ba wai ya sami yadda yake so bane daga gare su. Kawai dai ana cikin yanayin da babu gara ba daɗi. Takwas da arbain na dare a Kano tayi musu. Ko masauki bai nema ba ya kira Baban Alh. Usaini. Nan ya faɗa masa sunan hotel ɗin ya ce ya jira shi zai taho shi ma yanzu. Da su ka haɗu sun jima su na tattaunawa game da halin ɗan yau da abin da son zuciya ke kawowa. Baban Alh. Usaini shi ne ya kawo shawarar lallai a ɗaura musu aure. Wannan ne zai sa har ƴan baya ma su shiga taitayinsu. Matsanancin tsoron da ya kama Salwa da Alh. Usaini a yayinda iyayensu da ƴan uwan su su ka shigo ɗakin da su ke ba zai faɗu ba. Banda ƙannen Salwa biyu akwai wasu biyun na Alh. Usaini da Babansa ya taho tare da su. * "Aure???" Salwa da Alh. Usaini su ka yi tambayar da sun riga sun san amsarta ga iyayensu a lokaci guda. Kamar ba da mutane su ke ba. Babu wanda ya tanka musu. Sai ma Limamin Masallacin Khamsa Salawatin kusa da hotel ɗin da aka yi wa iso ya shigo ya zauna. Kafin wani lokaci ɗakin ya kasance babu masaka tsinke a dalilin mutanen da su ka shigo ganin ƙwaf. Labari ya bazu tun daga reception za a ɗaura aure. Sai ga mutane su na buɗe ɗakunan su suna tahowa kallo. Video kuwa harda masu yin live a social media handles ɗin su. Salwa sai wani ɗakin aka shigar da ita. Abu kamar almara. Aka ɗaura aure bisa sadaki naira dubu hamsin lakadan tsakanin Salwa hauka mai son ma so wani ƙoshin wahala da Alh. Usaini shugaban ƴan hassada da baƙinciki. Aure ne wanda iyaye su ka yi alƙawarin yin baki ga ƴaƴan nasu idan su ka kuskura su ka rabu. Bayan an watse ne Abban Salwa ya miƙa mata sadakinta a hannu. Shi ne take ta roƙo da magiyar ya yi haƙuri ya sa a sauwaƙe mata. "Aure an yi kenan in sha Allah. Daga nan in kun fita ku yanki daji ku fara bokanci ko bori tunda silar haɗuwar ku kenan." Kalaman sa sun yi mata zafi. Yanzu kuma bokanci yake kira mata kamar ba ƴar cikinsa ba? "Daddy ni ce kuma zan yi bokanci?^" "Meye a ciki? Boka mushiriki, mai zuwa wajen boka ma mushiriki abu na Ɗanjuma da Ɗanjummai." Su na ji su na gani iyayen su ka tattara su ka watse abin su bayan dogon gargaɗi akan dole su zauna tare. Su ka tafi tare inda Baban Alh. Usaini ya ce yau a gidansa za su kwana. Sannan gobe zai kira duk wanda ya dace ya san da auren domin su gabatar da junansu a gaban shaidu. Salwa kuka kamar ranta zai fita, Alh Usaini ko kallonta bai tsaya yi ba. Ya riga ya yi wa kansa alƙawarin zama da ita amma fa sai ta ɗanɗana kuɗarta. Son da yake yiwa kuɗin babansa bai kama ƙafar tsanar da ya yi mata ba. Ita ta ja masa komai. Ta saurari hukunci. *** Gaba na faɗuwa Taj ya kama ƙofar ɗakin Kamal. Hannun nasa har wani sanyi ya yi kamar ba a jikinsa ba saboda tararrabi. Bayan asuba su ka taho asibitin saboda kira da su ka samu akan tashinsa babu sauran magagin allura. Kowa ya kama shiri sai Alhaji ya ce su yi haƙuri a dinga tafiya in batches. "Kun gan mu unguwa guda idan mu ka cika musu wuri irin na jiya ba za su ji daɗi ba. Idan wasu su ka dawo sai wasu su tafi." Ba dai haka su ka so ba amma sun san tsarin nasa shi ne daidai. Nan ba a jinya ba kamar tamu ƙasar ba. Sannan babu damar zama idan ba layin ganin likita ba. Maimakon su yi ta zama a mota ana jiran juna gara kowa ya kintsa a cikin nutsuwa. Taj da Hamdi da iyayensu mata ne su ka fara tafiya tare da Alhaji. Idan sun gama sai Ahmad ya taho da wasu. A hanya aka dinga mayar da zancen yadda ƴan uwa da abokan arziƙi su ka ƙarbi zancen abin da ya faru da aka kikkira su a waya. Don tausayi, sosai an tausaya kuma an jajanta. Amma fa hatta waɗanda su ke matsayin ƙanne a garesu babu wanda bai nuna ɓacin rai akan shirun da

Chapter 42 of 46