An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
TAWA RAYUWAR
by maryama
#family
#drama
#heartbroke
#injustice
Bismillahir rahmanir rahim🤍
1
A duk lokacin da naji ana fadin komai me wucewa ne saidai inyi murmushi a raina badan na yadda cewar kaddarar dake tare dani wani lokaci zata wuce ba…Hakika kowani bawa baya wuce tasa kaddarar don kuwa tamkar rigar jikin mu haka take koda ka cire ta dole zaka nemi wata ka saka, don bazakayi yawo tsirara ba. Saidai kuma a lokacin da farin ciki yazo min a sannan ne na tabbatar da maganar cewa komai mai wucewa ne ,kada kuyi tsammanin rayuwata tamkar ta kowa take! Ni tawa ta banbanta dan kuwa ba kowani bawa bane zai iya jurar daukar kaddarar tawa , ina fatan zaku ci gaba da bin labari na mai ban al’ajabi tare da tausayi, cin amana, kunci da damuwa , zafin kai,soyayya mai tsafta da shiga rai…..
Babban parlor ne wanda ya kasance ba’a budesa a gidan kawun namu indai ba irin wannan ranar ba wadda muke family meeting a ciki ba, cike yake da dangin mu na bangaren mahaifina kowa ka gani dauke yake da matsananciyar damuwa dan kuwa babu wani mai farinciki a cikin mu idan ka dauke kakan mu da kawun nan mu, a kalla zamu kai hamsin da wani abu dan idan ka hademu muda iyayen mu bamu da wani yawa ,set din kujeru biyu ne a ciki da ash masu duhu da kuma brown kirar royal chairs wanda suka kawata parlon matuka babbar kujeran 3 seater kakan mune a kai wanda zai doshi a kalla shekaru 80 da wani abu sauran kujerun kuwa yayyan mahaifina ne da kanninsa a kai sai mu damuke yanmata da matan aure da yan samari da dai sauransu muna saman wani carpet lallausa kalar golden wanda ya kara bayyana kyawun dakin taron. ,kawu hafiz shine babban da a gurin kakan namu sai mabiyin sa kawu ishaq sannan kawu aliyu, kawu nassar sannan babana Al’amin sai autarsu mama rakiya.
Kawu hafiz ne bayan yaja dogon numfashi ya kalli wata yar budurwa dake gefen kujera tana ta sharar hawaye tana shassheka cikin kwantar da murya da lallashi yace “Aminatu kukan nan ya isa ya kamata kiyi hakuri hakan nan kinsan bazamu cutar dake ba a matsayin mu na iyayenki kuma ai Hassan dan uwankine dan haka banason in kara ganin kukanki kinji ina fatan zaku amshi wannan hadin da hannu biyu, kunga zumuncin mu zai kara karfafa koba haka ba? “ ya kare maganar da tambaya shima kawu ishaq ya karbe zancen da cewa “tabbas hakan yayi dan nasan hassan bazaka bani kunya ba aminatu bata da matsala kuma yar uwar kace dan haka ku rungumi juna in shaa Allah muma zamu taya ku addua tare da fatan zaman lafiya mai dorewa “
Hassan da har yanxu kansa yake duke a hankali ya dago ya dora idanunsa akan yarinyar da ake ikirarin an bashi bata da laifi black beauty ce yar duma duma saidai shi a saninsa ko kadan babu jituwa tsakanin ya’yan umman sa da ya’yan auntyn tashi dukda baisan menene mafarin abin ba , shi idan ta tashi za’abi baya da matsala da auren tunda duk wanda yasan ya’yan aunty ansan suna da tarbiyya tsantsa ga girmama na gaba amma idan ya tuna umma sai yaji auren yana neman fita a ransa, bangaren Aminatu kuwa sanin tsananin kiyayyar dake tsakanin dangin biyun yasa take jin da tana da iko da ta hana wannan auren itama a nata bangaren yaya hassan baida matsala amma yaya zatayi da yan uwansa? Mahaifiyar sa da duk wanda ya dangance su? Tuno Hakan yasa ta take zubarda hawaye batare da tayi kokarin tsaida su ba saidai dukda tashin hankalin da suke ciki saida sukaji ya karu sanadin maganar da tsoho mai ran karfe ya fadi “ hassan da aminatu mun gama da maganar ku yanxu ta NAJMAH da FAROUK zamu dasa dan so nake bikin naku duka kada ya wuce wata 2 in shaa Allah masu zuwa“ a zabure mafi yawan mutanen parlorn suka dago, a take naji tamkar a datsa min guduma a kai cikin gigicewa har bansan lokacin da bakina ya furta “KAKA dan girman Allah kada kace haka wallahi babu wata soyayya dake tsakanina da yaya farouk saidai tsantsan tsana dan allah kad…” dukan da mama atika ta kaimun ne ya sanyani kasa karasa maganar tawa take na fashe da kuka mai matukar ciwo bawai ina kukan dukan bane a’a ina kukane saboda wulakancin da yaya farouk yake mana dagashi har yan gidansu sam babu jituwa tsakaninmu ga tsantsar tsana da mahaifiyarsa mummy tayi mana wanda hakan ya kara sa muka janye jikinmu daga familyn mu tamkar bamu da kowa dukda a cikinsu akwai wanda suke janmu a jiki, , hakika banajin zan iya amincewa ayi hadin auren mu dan kuwa mudin mun banbanta shidin hagu ne ni kuma dama ce, cikin kuka na daga murya nace “dan allah kaka ka taimaka ni wallahi bana sonshi nayi maka alkawarin zan fiddo mijin aure amma dan allah kada ku hadani da yaya farouk” mama rakiya ce ta kara kawo hannu zata mazgeni kaka ya daga mata hannu yana fadin “ ya isa rakiya “ kafin yayi murmushi ganin duk wanda ya kalleni yasan bana cikin hayyacin na daga ni har aminatu da hassan dama shi yaya farouk bai samu damar zuwa taron ba dan haka baisan wainar da ake toyawa ba, a hankali wani kukan ya kara kubuce mun duk tausayin amina da nake sai naji ashe nice abar a tausaya wa dan kuwa yaya hassan bashi da wata matsala idan ka dauke ta yan gidansu shi kuwa yaya farouk shi kansa matsala ne balle aje ga mommyn shi ga kuma sisters dinsu , bansan me muka tsare musu ba daga ni har auntyn mu da duk yan gidan mu ma dan ko kadan bamu da farin jini agun dangin mu ko kuwa dan mu marayu ne shiyasa? Bayan hakan munfi kowa karamin karfi dan abban mu kafin ya rasu shagone garesa na provision kuma ba wani babba ba.
A cikin nutsuwa kaka ya ci gaba da mana nasiha tare da nuna mana ingancin auren gida kuma ya kara jaddada mana babu fashi sannan zai sami farouk din shima ya fada masa dan kuwa bayason abin ya dauki lokaci mai tsayi sannan kuma batun karatun mu bayan aure idan mazajen mu sunaso sai mu cigaba da yi daga nan aka tsaida 2 months in shaa Allah masu zuwa sai ayi biki yana kare jawabin sa kawu hafiz ya rufe taro da addua dake shine babba a cikin ya’yan kaka. Jiki a sabule yan uwanmu suka ringa fita wasu suna tausayin mu kamar ya’yan kawu nassar sauran kuwa banda harara da kwafa basa komai burinsu bai wuce a tashi su tafi gida ba dan kaiwa iyayen su gulma, Amina ce ta matso kusa dani fuskar ta shabe shabe da hawaye saidai babu yanda zamuyi kaka magana daya yakeyi baya biyu kuma munsan tunda ya furta wallahi sai anyi saidai mu mutu ko kuma wani iko na allah, maganar mama rakiya tasa na dago fuskata “ wato ke tatatta marar ta ido ana magana kina maidawa manya ko? To wallahi saidai ki bunne kanki daga ke har uwar taku mai neman ta rabamu daku saboda taga an barku a gunta wato ita isasshiya kum…” “ rakiya magana ta wuce fa ku kuma ku tashi ku wuce gida kafin dare yayi “ kawu aliyu yayi maganar yana kaiwa kofa shima, a hankali amina ta kamani har lokacin ban daina zubda hawaye ba muka fita batare da mun kalli kowa ba dake harabar gidan na kawu hafiz ba muka nufi get duk wanda ya kalle mu yasan muna wani hali more especially ni da bansan ya zan kare da yaya farouk ba gara ita aminatu da sauki ,hannu biyu nasa na dafe kaina dake barazanar rabewa biyu ga hajijiya dake neman kada ni, aminatu ce ta kalleni da idanunta luhu luhu tace “ najmah ki daure dan allah mu samu abin hawa kinga magriba tana karatowa ga halin da mukabar anisa kuma kinsan aunty ma ba lafiya gareta ba please ki daure “ gyada mata kai nayi ina cije lebe na na kasa sannu a hankali har na mike daga kan dakali (dabe) dake kofar gidan neighbor din kawun namu.
Sunana FADIMATU AMIN saidai ana kira na da najmah shekara ta 24 a duniya ya’yan mahaifiyar mu hudu Aminatu ce babba shekara biyu tsakanin mu sai ni sai islam da auta anisa duk baya wuce tazarar shekara biyu, mahaifin mu ya dade da rasuwa dan tun anisa tana yarinya yayi accident ya rasu.
Kaka asalin sunan sa Muhammad ishaq dan asalin kano ne anan yayi aure har allah ya azurta shi da yaya duk maza sai guda daya mace wato mama rakiya, na farkon su shine hafiz, isahq, aliyu ,nassar ,amin, da rakiya kuma kowanne yana da zuri’a kuma kowa anan kano yake da zama kuma a unguwa daya saidai mune kawai gidanmu yadanyi nisa da sauran, familyn mu suna da tsauri sosai kuma idan sukayi magana ta zauna kenan.
Yaya farouk dan kawu hafiz ne dama duk cikin ya’yan kaka babu mai kudinsa, ilimi, wayewa, da sauransu daga shi sai al’amin, amira, amra, abida duk ya’yan mommy ne, kuma duk allah bai hada jinin su damu ba dan idan baka sanmu ba bazakace yan uwa bane idan muka hadu saidai mazan bawai kiyayya suke gwada mana ba badai su shiga harkar mu kuma duk hudubar mommy ce saboda qin da take mana, kawu aliyu ma yayan sa hudu, ukku mata daya namiji Hassan, usaina, hanifa, hamida sai kawu ishaq shima ya’yansa ukku,abban mu yana da mu sai kuma kawu nassar mai ya’ya shidda hudu mata biyu maza sai mama rakiya ya’yanta biyu maza ukku mata itama anan kano take aure (duk a sannu zaku san yan uwan namu da halayan su) wannan shine takaitaccen tarihin mu a gajarce.
A hankali muke tafiya dagani har amina kowanne akwai abinda yake cimai zuciya bamu ankare ba naji an janyomin hijabi nayi baya kamar zan fadi allah ya taimake ni amina tayi saurin rikeni tana kallon Amra da abida sai hanifa da hamida ko waccensu tana jifarmu da mugun kallo tamkar zasu daba mana wuka su kashemu su huta, kara daidaita tsayuwa ta nayi idanuna da suka kumbura saboda kuka na kallesu dashi na budi baki inyi magana amra da take babba a cikinsu tace min “ki rubuta ki ajje matukar kika auri yayana wallahi saina tabbbatar da rayuwar ki ta lalace dan kuwa sai mun hadu mun azabtar da rayuwar ki bake kadai ba hadda ta wannan sakaran “ ta kare maganar tana nuna amina wadda magana ma ta kasa yi musu sai binsu da ido takeyi kamar yadda nima nayi shiru ina sauraren yaya amra “matsiyata masu bakin jini “ hanifa ta amshe zance, murmushi nayi wanda iya kacinsa lebe dan inda sabo mun saba da cin mutumcin yan uwan namu da basa mana kallon mutane nace “ai bani zaku tara ku fadawa ba sai kuje wajen iyayen ku da suka hada auren ku sanar musu ku….” Marin da hamida ta kaimun yasa na kasa ci gaba da maganar cikin zafin rai na kalleta da jajayen idanuna yarinyar da a haihuwa na girmeta amma shine ta iya daga hannu ta kaimun mari haka , saidai maimakon na rama saina tsinci kaina da mata murmushi nace”bashi kika dauka ko baki biyani ba tabbas wani zai amsarmin batare dana kara cewa komai ba na kama hannun amina dake kukan marin da sukamin na jata muka wuce, cikin daga murya abida tace “as as a kara gaba masu bakin hali ya’yan mace “ a tare suka tuntsure da dariya suna tafawa tare da ci gaba da fada mana maganganu marasa dadin ji wanda suka shafe mu da mahaifiyar mu saidai ko kadan bamu juyoba burinmu bai wuce mu bar layin gaba daya ba dan yanxu ba tsanar ya’yan kawu nan mu kadai nakeji ba harda ta kakanmu ma daya hada auren mu dasu.
-minene mahadin kiyayyar su Amina da danginsu?
-za’ayi auren kuwa?
-waye farouk?
TAWA RAYUWAR
By Maryama
Page 2
#the beginningđź’”
Da kyar muka samu abin hawa dake har an fara kiran magriba, adaidai kofar gidanmu aka ajje mu normal irin ginine na talakawa amma masu rufin asiri kofar gidan mu koface sai gefe wani dan shago karami inda baban mu kafin ya rasu yake zama, yanzu kuwa babu komai cikinsa aminatu ce ta kama ni dukda itama tana ji da nata al’amarin amma ni nafita shiga wani hali dan shigata cikin su amra tamkar nakai wa kura fida ne gefe daya ga mommy allah kadai yasan irin cakwakiyar da za’a yi, da sallama muka shiga saidai tun a soro nake jin kukan mahaifiyar tamu cikin tsananin firgici da gigicewa muka ruga izuwa ciki…
Farar dattijuwa ce wadda a shekaru bazata gaza 40
ba amma kamar wadda tayi 50 saboda yanayin tsufa daya fara bayya mata, kuka takeyi cikin halin rashin sanin abinyi saman cinyarta budurwa ce yar shekara 20 kakkafe kamar mai figar ruwa idanunta sun juye da alama bata cikin haiyacinta gefensu ma budurwa ce wadda tadanfi marar lafiya a girma itama kukan take, a wannan halin NAJMAH da aminatu suka iske su aunty wadda take mahaifiya garesu, da gudu najmah ta kama anisa tana jijjaga ta amma inaa bama tasan sunayi ba “ aunty mu kama ta ko gidan baba doctor ne mu kaita nasan yana gida yanxu “ amina tayi maganar tana matsan kwalla da tausayin kansu da kuma yar uwarsu wadda tunda aka haifeta take tare da wannan lalurar lokaci zuwa lokaci idan ciwonta ya tashi tamkar bazata rayu ba kuma sunje asibiti amma har sun gaji ga kuma karamin karfi danma kawu hafiz da kawu aliyu suna matukar taimakawa saidai yau da gobe sai allah amma har yanxu babu wani sauki tare da ciwon nata, da kyar amina tayi ta lallashe su suka riko ta najmah ta kama hannunta itama amina ta kama gefen daya ita kuma mahaifiyar tasu ta saka mata hijab dukda itama ba lafiya gareta ba tana fama da ciwon zuciya ne shiyasa ba’ason yawon tashin hankalin ta amma dole take dannewa dan su tasu kaddarar kenan, islam ce ta riko hannun auntyn tasu da take kokarin bin bayansu tana kuka abin tausayi, “kiyi hakuri mu jira su dawo nasan in shaa Allah komai zai zama tarihi a rayuwar mu aunty, zamuyi farinciki kamar yadda kowa yakeyi anisa ma zata tashi kamar kowa mudai mu cigaba da mata addua” kalaman islam ne suka dakatar da aunty daga kokarin da takeyi nason bin bayansu dan ganin halin da yar ta take ciki wasu hawaye masu tsananin zafi suka sulalo kumatunta saidai duk halin da take ciki ba karamin godiya take da allah ya azurta ta da ya’ya na gari gasu da hankali iya lafazi kuma a koyaushe burinsu kada tayi kuka burinsu su kwantar mata da hankali, murmushi mai ciwo ya subuce mata a sannu takai hannu jikin kirjinta jin yadda zuciyarta yake bugawa da karfi kamar zai faso kirjinta ta fito a hankali ta sulale a wajen saijin karar faduwar kawai islam dake duke taji wani kara ta fasa tayi kan auntyn tasu wadda suke jinta itace duniyarsu.
Bayan fitarsu direct neighbor dinsu suka shiga gidan doctor ne kuma yana matukar taimaka musu duk lalurar data same su shi yake tsaye har sai yaga da sauki cikin ikon allah, daga farkon shiga cikin gidan parlonsa yake da sallama suka shiga dawowarsa kenan daga masallaci yaji sallamansu iso yayi musu kafin suka shiga har sannan anisa a kame take sai idanunta dake bude gasu masha allah da girma anan carpet suka shimfideta shi kuma ya sauko daga kujera bayan sun gaisa yake tambayarsu ciwonne ya tashi eh suka amsa masa a hankali ya dafe goshinsa , dattijo ne amma ba cen ba yana da mata daya da ya’ya ukku sosai suka daukeshi yayansu dan idan lalurar su ta tashi kafin su kawu su kawo musu dauki shi zai fara, first aid box ya dauko acen kuryar dakinsa kafin ya dauko wata allura da idan ciwonta ya tashi yake mata nan ya hada da sauri kafin ya mata ita su najmah duk sunyi cirko cirko kana kallonsu basai an gayamaka irin tashin hankalin da suke fuskanta ba tun suna kananun yara har kawo girmansu, wani huci mai zafi na sauke mun fi minti 10 kafin mukaji anisa taja numfashi mai karfi ta sauke a sannu idanuwanta suka rufe bacci ya kwasheta na wahala sai a sannan muka ajje ajiyar zuciya murmushi ya kubuce mana harda shi doctor kafin ya kallemu yace “Alhamdu lillah yanxu saiku barta anan zuwa bayan isha sai maryam ta rako ta (diyarsa kenan best friend din najmah) da to muka amsa kafin mukayi masa godiya dukda munsan bayaso amma ya zama wajibi a garemu, batare damun shiga ciki ba muka fito daga gidan inajin sanda yake kwalawa matarsa kira wadda muke kiranta da umma.
Shigarmu gida wani tashin hankalin muka riska islam duke a wajen aunty tana mata fifita ga hawaye yana zuba a idanun auntyn mu gashi tanajin a jikinta ciwon tane ya tashi amma bata son ta kara tada hankalin mu, jiki a sabule muka zauna muka sata a tsakiya saidai ta kalli wannan ta kalli waccen gaba dayanmu mun kasa magana , cen ta budi baki da kyar tace “ kuje kuyi sallah “ dafe goshi nayi dan wallahi shaf na manta ko sallah bamuyi ba ta magrib harga isha tana kawo wa da sauri muka fara rige rige nida su islam bayan munyi ne nutsuwa tazo mana kafin aunty tace “ya jikin anisa “ aminatu ce ta amsa mata da sauki kafin tace bacci take sai doctor yace a barta maryam zata rako ta idan ta tashi daga nan ba wanda ya sake magana har lokaci mai tsayi kafin a bazata aunty ta jefo mana maganar da yasa muka fara ido ido nida amina sai yanxu ma muka tuna halin da muke ciki na aurar damu da kaka yake kokarin yi ga yan uwanmu.
***
Matar kawu hafiz mommy kenan itace ta fara riskar maganar hadin auren da za’awa danta wanda ta dauki son duniya ta aza masa wani irin lailayo ashar tayi ta sauke wa amira da amra da suke bata labarin kafin tace “ ai kuwa lokaci yayi da zan nunawa nusaiba (aunty) gaba daya rayuwarta a tafn hannuna take dan da’in hada zuri’a da ita gara in hada da karuwa mai zaman kanta wallahi bata isa ba duk wani asiri da tayi saidai ya koma mata amma badai zai kare akan dana ba “ ta kare maganar tana huci duk idanunta sunyi ja saboda tsananin bakinciki da tsanar nusaiba da yake dawainiya da ita (Niko nace ko menene sila?) “ mommy kada ki yadda haka nan sun gama tambadewa a titi yanxu kuma a makalawa danki ita bayan a idanun ki dai babu wani saurayi daya taba maganar zai aurensu saboda bakin jinin da suke dashi ga rashin mashinshini “ amra ta fadi tana tabe maki zuciyar ta fal hassada saboda kaf familyn su ba’a taba haihuwar kyawawa ba kamar yayan aunty more especially ma najmah duk ta fisu kyau na asalin buzaye dan auntyn su buzuwa ce daga niger babansu ya auro ta kuma duk yayan kamr ta sukeyi aminatu ce ma tayi kama da baban nasu dan ta dauko kiba amma ba mai muni ba kuma tayi dan duhun fatar sa, Amira ce tayi kwafa tace “ni kuwa idan akayi auren nan wallahi saita yi dana sanin shigowa cikinmu “ buge mata baki mommy tayi kafin tace “ a gidan uwarki za’ayi auren? Shegiya mai mugun baki “ turo baki gaba tayi tana bata fuska jin zafin ya ratsata har kwalwa, abida da take zaune ce ta dago ta kallesu kafin tayi murmushi tace “ ku kwantar da hankalin su dan kuwa idan akwai abinda Yaya farouk ya tsana to wannan shegiyar ce najmah, dakatawa tayi da magana tana murmushi dan duk ciki ta fisu wayo da mugunta ta karkashin kasa dukda kuwa itace karama kafin taci gaba Da cewa” har abada banajin zai sota kuwa dan tsakanin su babu jituwa tamkar haduwar rana da wata “ lumfa sawa tayi kamin tace “so you guys sai ku sanyaya zuciyarku bayan gaba da kiyayya babu komai kuma koshi bai dauki mataki a kanta ba mu zamu dauka wannan alkawari nane su da jin dadi har abada “ kwashewa da dariya sukayi gaba daya kafin mommyn tace “ hmm dukda haka nidai bazan bari yayi auren ba saboda babu lafiyayyen namijin da zaiga najmah a gidansa yace baiso taba “ daga nan suka cigaba da hada yadda zasuyi su hana auren kuma su musgunawa aunty da ya’yanta, bayan sun gama ne mommy ta tashi ta nufi dakinta ta dauki wayarta dake saman mirror kafin ta danna kiran wata number da akayi saving da mujahida bayan ringing uku aka daga nan take labartawa matar abinda ake ciki akan danta farouk da yar makiyar ta wato najma itama daga cen bangaren banda zagi da cin mutumci bata komai harda cewar har kotu ko human rights sai sunkai tsohon banzan dayakeso yayi hadin auren