gama jana’iza kafin su dawo daga makabarta wajen binne amina sukayi saurin fita itada mama ko waiwayen bayansu basuyi har saida suka tsaida napep kafin hankalinsu ya kwanta.
***
Doguwar tafiya sukayi har saida suka fita daga gari suka nufi kauyen da bokansu yake daga nan ma babbar tafiya ce kafin su isa duk sunyi likis sai bayan azzahar suka je, direct gurinsa suka nufa bayan sunyi al’adarsu ta shiga wurinsa kafin kowacce ya bata umarnin zama nan suka gaishesa ya amsa yana zare zaren idanu gashi ba wani girma garesu ba idanun kamar na yan china ga wata malafa daya kafa akai duk kuwa da ranar da akeyi sai uwar zufa yake narkawa kamar wanda yayiwa sarki karya ,babbar riga dake jikinsa kuwa bata da maraba da kalar kuli kuli duk dauda ta dafar da ita , gefensa kaskone sai a hannunsa dogon carbi mai dubu yanata ja yawa wani mutumin azziki!
Gyaran murya yayi yace “ ya ake ciki ? Dafatan kinji sakona?”
“Eh malam naji yanxu dai zuwan da mukayi inji ya ake ciki ne shin akwai abinda za’a iyayi akan maganar yaran nan? Dukda an kashe daya kuma an rasa daya acikinsu “
Murmushi yayi batare dayace komai ba har saida aka kusa minti biyu kafin yace “akwai abinda za’ayi a akansu amma ki sani wancen sihirin da aka musu na bakin jini tamkar mujiya yanxu ya kusa daina aiki kuma yana dainawa zai koma kan naki yayan, kuma shi a ka’idar sihirin da aka musu sau daya akewa mutum shi a rayuwar sa, yanxu saidai ayi musu wani amma bazai kai wancen tasiri da kuma karfi ba “
Wani zufa ya shiga keto mata tace “ to malam indai bazai koma kan ya’yana ba kawai ayi musu yadda kace dukda baikai wancen karfi ba nidai banason ganin walwalar su harda uwarsu kuwa “ mama dake gefe ta jinjina kai ganin duk muguntar ta yar uwarta tadameta ta shanye ko tausayin marayun ya’yan bataji gashi har daya ta mutu dayar kuma ba’asan wani hali take ciki ba ga halinda uwar take ciki na shanyewar barinjiki amma kiyayyar da take mata baisa ta tausaya musu ba (🥺💔mommy zuciyar ki bata da kyau) “ Shikenan zan kara musu aikin bakin jini su biyun da suka rage harma da mahaifiyar tasu , hakan yayi miki?” Ya tambaye ta da sauri ta gyada kai saiya dauko wani tsohon carbi mai dari duk yayi baki ga wani hayaki yana fitarwa ya miko mata yace dauki daya tak da sauri ta kai hannu ta dauki guda daya, bayan ya amshi wanda ta dauka din sai ya fara karanta wasu abubuwa na yan tsubbu yana gamawa carbin ya koma toka wani ja da baya yayi yana kara zare kananun idanunsa.
***
Muna nan a rakube nida islam da sauran mutane yan uwa da yan unguwa sai gashi an dawo daga makabarta ankai amina gidanta na gaskiya duk inka kallemu bazakaso ka kuma kallon mu ba dan munyi luhu luhu kamannin mu duk sun canza tsabar tashin hankali ga aunty acen asibiti an ma hanamu tafiya saboda jikinta baza’aso wani ya je inda takeba, baba doctor ne acen yake kula da ita shida sauran nurses din, nidai bana ma iya magana saidai bin mutane da ido suma mate dinmu duk sunzo sunyi mana gaisuwa saidai Maryam ce kawai take amsawa, zuwa azzahar saiga yaya Farouk yazo nan a tsaitsaye yayi mana gaisuwa ya fita danni ko kallonsa banyi ba kuma nasan abin yayi masa ciwo, shima yaya hassan dashi akayi jana’iza yayi kuka sosai abin tausayi dan harga allah yanason amina amma mutuwa tayi musu yankan kauna, yan sanda sunzo anyi binciken amma a banza ba’a samu komai ba kuma rahoto ya tabbatar maza uku sunyi raping dinta kuma daga baya aka murde wuyanta wannan lamarin yayi tsamari dan take aka dinga watsa rahoton abinda ya faru ga amina sannan kuma an nemi anisa an rasa kuma ansan tare aka daukesu .
Su kawu aliyu sunji mutuwar yarinya kuma hankalinsu ya tashi dan wannan kisan wulakanci ne kuma suna ganin alhakin mutuwar yarinyar ya rataya a wuyansu saboda basuyi kokari gurin neman su ba gashi basu san ya halin da anisa take cikiba, kaka ma yayi kukan mutuwar yarinyar sosai hakan yasa yace idan an gama zaman makoki yanason mu dawo gidansa da zama saboda nan din babu security ko kadan kuma ba’asan manufar kidnappers dinba zasu iya dawowa daga baya su kwashe mu ,da yake gidan yana da fadi sosai gidan kuma akwai boys quarter yace saimu zauna acen kuma kula da aunty za’a dauko yar dattijuwar da zata dinga kula da ita tunda komai sai anyi mata kuma ni aurar dani zasuyi islam kuma ita kadai bazata iya ba, wannan maganar da aka fada mana tasa mun kara shiga tashin hankali dan sai yanxu muka tabbatar munyi maraici ba karami ba rungume juna mukayi nida islam muka sanyawa su kaka kuka wanda ko muryar mu bata fita sosai.
Kawu ishaq ne ya goge kwallar dake idanunsa tunowa da yayi da danuwansu mutum mai hakuri da juriya ga sadaukarwa yau ga iyalinsa cikin jarrabawa mai tasiri a zuciya, hakuri ya fara bamu shima kawu aliyu jikinsa yayi matukar sanyi cikin lallashi yake bamu baki tare da nasiha da kuma yarda da kaddara , haka ma kawu nassar sosai ya mana nasiha kawu hafiz kam harda kukansa wai acewarsa ya tuno dan uwansa amin.
Mama rakiya ma tazo saidai bata wani zauna ba har ya’yanta kuwa sukayi tafiyarsu acewar ta gidan a matse yake gashi batajin dadi wai.
TAWA RAYUWAR
By maryama
Page 10
***
Su oga da sukayi kidnapping su amina hankalinsu ba karamin tashi yayi ba da suka sami labarin gawa daya kadai akayiwa sallah kenan wani ya gansu lokacin da suka ajje su amina? Idan hakane waye ya gansu, aidai mutum baya mutuwa ya dawo balle suce gawar da kanta ta tafi nan dai haka sukayita hasashen abubuwa amma sun kasa daukar guda daya a ciki saidai ogan ya hakikance wallahi kawai wanine ya gansu a lokacin kuma ya dauke anisa saboda wata manufa tashi, sunata jajantawa text ya shigo wa oga yana dagawa yaga ansa “ meyasa zaku nemi batamin aiki? To duk ku kuka da kanku dan matukar sunana ya fito a bakacin rayukanku, sannan inaso duk rintsi ku nemomin gawar anisa dan mutumin daya dauketa yana da wata manufa bayan wannan za’a iya bin rayuwar ku a koda yaushe kuyi taka tsantsan “ daga haka duk sukayi jugum suna jimami.
***
“ lafiya malam?” Cewar mommy ita da mama dan sunga tsoro a idanunsa sai suma jikinsu yayi sanyi , ajiyar zuciya ya sauke yace “ akwai matsala dan kuwa ya kusa bayyana “ da sauri mommy tace wane kenan “ tayi maganar tana zaro idanu “bayyanarsa shine zai haskaka tata tauraruwar a duniya baki daya dukda akwai tarin kalubale a gabanta ,saidai kafin nan zamu iya yin duk yadda zamuyi dan ganin basu hadu ba “
Cikin muzurai zatayi magana ya katseta da cewa “ ita wannan kyakkyawar wadda tafi kowa karfin tauraro “
Zuwa lokacin zufa ta gama feso ma su mommy harma da mama dan sun gane najma yake nufi amma dukda haka mommy tayi jarumta tace “ayi aikin da zai hanasu haduwa “
“Za’ayi kuwa saidai daga cikin kalubalen da zata fuskanta akwai auren danki, sai kuma shiga cikin dangin wancen mutumin saidai hakan bazai hana tauraruwarta haske ba kawai lokaci ne bayyi ba “ sosai hassada ta kama mommy saidai tayi shiru batace komai ba ga bakincikin cewar dole najma ta auri danta, wani kulli ya dauko ya miko mata yace “ karbi ki tabbatar danki yaci wannan a abinci tabbas za’ayi aurensu kuma zata dandani ukuba da azaba tsakaninta da mijinta, ku tashi ku bani waje “ ya karasa maganar da nuna musu hanya cikin sassarfa tace “abin sadaka fa “ kureta yayi da ido sai kuma yace “ zamu bukata anan gaba “ da to ta amsa kafin ta kara da cewa “malam waye zai bayyana a cikin rayuwar tata?” Cikin kosawa yace “ lokaci ne zai bayyana shi ku fice min “daga haka suka fito jiki a sabule jin dole dai sai tauraruwar ta haska kuma amma sunyi farincikin jin zata fuskanci kalubale a gidan farouk, daga nan mommy ta fara tsara yadda zata kashe najma batare data fita daga gidan Farouk ba dan batajin zuciyar ta zata iya daukar ganin ci gaban zuri’ar nusaiba dan kuwa duk wanda yaci tuwo da ita to miya yasha.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya yau har tsayin wata guda da mutuwar amina abubuwa marar sa dadi sunyi ta faruwa, daga ciki kuwa harda wata konanniyar gawa da aka yo mana text message akace ga gawar anisa nan muje mu dauka a wani kango wannan abu ya girgiza mu amma allah ya saka mana juriya daga mu har aunty dukda har sannan komai sai anyi mata saidai tayi ta binmu da ido, an sallameta kuma mun koma gidan kaka da zama sannan an samo mana wata dattijuwa mai kula da ita wadda muke kira anna, rayuwar gidan kaka ta tazo mana da sanyi dan yanxu har islam bazakace itace wannan mai surutunba da kuma karambani, saidai wani al’amari daya daure mana kai bai wuce ganin amira tana yawan ziyartar mu ba kuma idan tazo iyakaci bayan mun gaisa saita zauna tana kallon mu wani lokacin har kuka muke ganin tanayi saidai mun dauki hakan amatsayin mutuwar su amina ne yake taba ta, gashi takan kawo mana su chocolate harda abin amfani amma bamu taba sakin jiki da ita ba itama ba wani magana take mana ba bayan gaisawa wannan abin sosai yake tsaya min arai, a baya nasan tafi kowa tsanar mu amma kuma yanxu ba haka bane saidai ban taba tambayar ta dalilin sauyawar ba, sosai muke kula da aunty bawai iya anna kawai muke barwa aikin ba kuma maryam tana zuwa mana harma da umma sannan baba doctor yana kawo magani tana sha wanda ance idan tayi sa’a zata iya warke wa saidai ba lokaci daya ba, duk in nayi sallah saina saka yan uwana a addua ta samun rahma dukda ina kokontar gawar anisa kamar ba ita ba amma dai naja bakina nayi shiru gudin wasi wasi kuma banason tadawa aunty da islam hankali , kawu hafiz da sauran kawu naina suna zuwa sosai su duba aunty shima yaya hassan yana zuwa yana gaishe da aunty, haka rayuwa taci gaba da tafiya kuma zuwa lokacin bikinmu baifi sati uku ba kuma ni tun randa yaya farouk yaje yayi mana gaisuwa bai kara zuwa inda muke ba nima kuma ban damu ba dan nasan waye shi kawai burina aunty na ta samu lafiya kafin komai zai faru ya faru.
Kaka yasa an ajje mana duk abin bukata yau idan nayi girki gobe islam zatayi haka mukeyi, kullum nakan tashi misalin karfe 3:30 na dare in tashi islam itama haka zamuyi sallah mu roki ubangijin mu saukin rayuwa tare da hakuri da juriya akan jarrabawa da kuma lafiyar auntyn mu da kuma gafarar mahaifinmu da yan uwanmu.
Bangaren biki na babu wani abinda akeyi dan banajin ko an daura auren zan iya tafiya inbar aunty a cikin wannan yanayin, ni banma taba ganin biki kamar wannan ba ko irin anko babu wanda yayi mana magana balle azo kan wani gyara da amarya take samu dan bama tashi nake ba tunda wanda zanyi gyaran domin shi ba wani kauna ta yake ba.
Yau muna zaune a dan karamin parlon mu na boys quarter dake gidan kaka islam ta shigo hannunta rike da leda baka, zama tayi da bismillah a bakinta kafin tace “anna dama haka wannan kasuwar take nikam nayi dana sanin zuwa” Murmushi anna tayi tace “ bana fada miki ba kibarni inje amma kikayi kunnan uwar shegu kika tafi waike jaruma waya gayamiki barno gabas take “ dariya nima nayi dan kuwa akayi akayi islam kada taje kasuwar ta yanboda amma ta nace sai gashi tana fadin tayi dana sani “kai big sis “ cewar islam tana shagwabe fuska “ shine kema kike dariya? Aunty kin ganta ko “ ta kare maganar tana kallon aunty dake kwance kamar ko yaushe babu magana bata kuma iya sarrafa komanta saidai ta bika da ido , yanxun ma idonta ne ya motsa tamin kallon gargadi hakan yasa na gimtse bakina ina toshe dariya,
“ nidai ga kayan dana samo mana bari in dauko plate in juye mana amma saina fi kowa ci gaskiya “
“ hmm dama aike komai kece gaba gashi nan harkin fara tumbi “ nace mata daga haka ta sauye mana su rogo da dafaffiyar masara sai kullin su gyada dadai kayan makulashe na gargajiya.
Dukda muna cike da kewar yan uwanmu amma haka muke kokarin dannewa saboda tarin nasihar da anna take mana dan yanxu itace kusa damu sosai dukda su umma ma da maryam suna zuwa akai akai, saidai kowace sallah nakan wa kowa addua bama fashi, haka rayuwa taci gaba da tafiya ga jinyar aunty da koda yaushe muke nanike da ita kuma muke kokarin faranta mata rai saboda yanayin ciwonta.
Yau sauran sati daya biki kuma ayau ne muna zaune nida islam munsa aunty gaba kamar kullum anna kuma tana nan daga kofar parlon tana yanka mana lettuce na abincin rana mukaji sallama ta mutane da yawa, a tare muka amsa saiga mommy tana yatsina fuska tana kare mana kallo tasha wata doguwar riga ta lace wadda tasha stones kamar matar wani shugaba sai dage kai take a dole su masu kudi bayanta kanwar tace wato mama sai kuma abida da amra sai wasu matan da ban sani ba suna rike da akwatina nan anna tayi musu iso tana komawa daga gefen kujera kusada katifar da aunty take kai, shigowa sukayi kowacce tana mana kallon kaskanci da raini amma ko akanmu dan basu ne a gaban mu ba dagani har islam, gaishesu mukayi a jam’i amma banji sun amsa ba sai wannan matan da ban sani ba akwatina ne guda ukku yellow shar dasu nan suka ajje a tsakiyar parlon nidai juya kai na nayi dan nasan bazai wuce suce lefe na bane, kafin in gama tunani naji mama tana cewa anna “ ga lefen yar ku nan mu mungama namu saura kuma daurin aure rana ita yau “
Aunty da ido tabi su sai kuma ta sauke kallonta a kaina kafin ta lumshe idanunta wani dariya mommy tayi tace “nusaiba akwai magana a bakinki amma kuma kash hawan jini da ciwon zuciya sun cinye bakin balle ki maganta “ rumtse idanu nayi amma kuma sainayi ta hasbunallah a raina kafin nace “ jarrabawa ce bata wuce kan kowa ba “
TAWA RAYUWAR
By Maryama
Page 11
wani dan iskan kallo mommy tayiman kafin tayi kwafa tace “ badake nake ba nakasshiya da nusaiba nake ke tukunna banzo kanki ba “ “ kinji rashin kunya gatse gatse waike nan har kinyi baki ahhh lallai wato nusaiba ko tarbiyya baki bawa ya’yanki ba “ mama ta kare maganar da rike baki, abida da maganar najma ta mata ciwo itama ta budi baki zata maidawa najma amma mommy ta hana ta sannan tace “ baku fara ganin komai ba tukunna dan haka maida magana ba taku bane “ cikin zafi islam ta bude baki zatayi magana aunty ta mata wani mugun kallo dayasa ta fasa cewa komai tayi shiru, kallon tsana suke binmu dashi kafin mommy tayi murmushi tace “ hmm zaki maimaita abinda kika cemin yanxu akwai lokaci najma“ daga haka suka tashi suka tafi batare da mun sake tanka musu ba, rike baki anna tayi tace “ tab di gaskiya lamarin familyn nan naku najma akwai kallo yanxu suna nufin wannan ne lefen naki dan sun raina mutane duk tarin dukiya da allah yayi musu kuma ga tsantsar cin mutumci da sukewa mutane “
Murmushi islam tayi tace “ kyale matsiyata su abin duniya ya shayewa kai ai badan banaso in tada tarzoma ba dana maida musu magana “ nidai bance komai ba karshe ma ni na cigaba da yankan lettuce din da anna ta fara nan suka fara bude akwatinan wani ashar islam tayi tana kara daga kayan ganin duk roba ne sai cotton kanana basu fi biyar ba robar ma tayi goma dayan akwatin suka dauko suka bude takalma ne kala hudu masu saukin kudi sai jika biyu da hijab biyu sai kuma dayar akwatin tarkacen su sabulu ne kanana sai sarka biyu da kuma abinda baza’a rasa ba, aunty ma idanunta akan kayan ,nasan arzikin Farouk idan lefe na kirki zaimun saiya hada akwati ashirin kuma masu tsada amma kuma bazai yiba kuma mommyn ma bazata yiba wani kuka islam ta fashe dashi na takaici itama anna jiki a sanyaye ta koma gefe tayi tagumi, murmushi nayi wanda iyakacinsa lebe na tashi naje inda islam take na rungume ta ina bubbuga bayanta “ haba little sis menene haka dan allah komai fa yayi farko zaiyi karshe kiyi hakuri indai akan wannan abin ne komai zai wuce “
“ bazaki gane ba yaya najmah yanxu wani irin wulakanci ne haka? Ai ko basu duba zumunci ba zasu duba halinda muke ciki amma ace muna family nasu amma su kawo mana wannan abin a matsayin lefe kuma kamar yaya Farouk yana kallo su kawo abin nan “
“Shshhh ba damuwa ai sunyi kokari “ nace mata , wani fusge jikinta tayi daga nawa tana harara ta sai kuma tayi kwafa, nidai dariya nakeyi kasa kasa dan nasan magana ta ta qular da ita , aunty dai da ido take binmu daga mu har kayan kafin ta lumshe ido kamar mai bacci ko a bata furta ba dukda maganar tana mata wuya kuma a jirge takeyi dan bata fita sosai.
***
Bayan komawar su mommy gida nan suka zauna suna sheka dariyar mugunta dukda maganar da najma ta fada ya musu ciwo mama tace “ ai hakan shine daidai su matsiyatan banza masu kama da aljannu “ abida tace “ baki ga uwar tasu ba tanason magana amma ta kasa “ amra ta cabe zancen da cewa “ni ai allah naso ku dauki shawara ta kada akai musu komai amma hakan ma ya wadatar ba abinda yafi ban dariya kamar yellow trollyn nan “ nan fa suka kwashe da dariya harda rike ciki afiya da bata je ba saboda ita a dole kishi take harda fadowa daga kujera tana dariya , amira kuma dama tana daki bata fito ba amma tana jinsu nan ta saka bayan hannunta ta share hawayen dake zubar mata (🤔 wai minene ya canza amira haka?) Mommy ce tace aje a kirata nan abida ta shigo saidai tayi turis ganin kukan da yar uwarta takeyi daga tsayen ta kwala kiran mommyn su dama kamar jira suke suka taho mama tace “ lafiya amira meke damunki “
Girgiza kai tayi tace ba komai nan sukayi ta tambayar ta amma ta kafe cewar itafa kawai kanta yake ciwo badan sun yarda ba suka barta.
***
Umma ce mahaifiyar hassan tana zaune hakince saman kujera sai hassan wanda yake a kasa ya dukar da kansa banda musiba bata masa komai cen dai ta hadiye yawu kamin taci gaba da cewa “ wallahi ba tausayi ba idan mutuwa zasuyi baka isa kace zaka maido da maganar aurenka akan waccen yar iskar yarinyar ba wai ita islam kaini bari kaji na rantse ko cewa akayi ka sake zuwa gidan saina saba maka banda ma baka da hankali a gaban ka ubanka yaso ya koreni a lokacin da yana neman auren uwar su banda ma na shiga na fita da tuni yanxu wani labarin ake ba wannan ba dan haka kasan me kake ciki tashi ka bani waje “ tayi maganar da nuna masa kofa, jiki a sanyaye ya mike zuciyar sa na zafi dan ji yake tunda ya rasa amina to bazaiyi gangancin rasa islam ba, shidai tausayi suke bashi amma ko kadan umman sa bata kaunar hadin auren dan ita a boye tayi murna da mutuwar amina (subhanallah) har cewa take ba wani dauketa da akayi yawon ta zubar ta tafi karshe wani ya halaka ta a banza, haka dai tayi ta bin amina da sharri dukda bata duniyar amma bata yadda maganar taje kunnen mijin taba kawu aliyu dan tsaf zai sauwake mata akan hakan, gashi abinda yake cin zuciyar ta har gobe mijinta yana son nusaiba amma taki bashi hadin kan ya aureta shiyasa ya hakura, a bangaren aunty kuwa kawu hafiz ne yace indai shi bai sameta ba duk duniya babu mai aurenta kuma idan tayi aure to wallahi saiya kashe mijin hakan yasa ta hakura tunda kuruciyar ta harta manyan ta bata taba sha’awar auren ba.
Bayan fitar hassan umma ta bishi da harara tana kwafa ganin zai ballo mata ruwa ta rabu da alaqaqai amma yana niyyar tado wata , hamida ce tace lafiya umma naji kinata fada allah yasa ba wani abin yaya hassan yayi ba rausaya kai umma tayi tamkar kadangaruwa tace “ barni da banza kamashi nayi yana waya da abokinsa wai shi yanxu tunda amina ta rasu zai koma gun kanwar ta islam kiji fa “ bata fuska hamida tayi sai kuma ta tabe baki tace “hmm sudai sun rantse sai sun hada aure damu “
“Barni da shegun ai sunyi kadan na rantse “. Daga haka suka ci gaba da zagin su islam suna aibata su.
***
Anna ce yau taje kauye cen garinsu amma ba kwana tayi ba sakone ta amso muna zaune sai gata ta shigo bayan munyi mata sannu da zuwa ta miko min wata leda sannan tace in bude zata min bayani take na bude nan naga wasu jarkoki da wani ruwa a ciki sai kuma garin magani kala kala, bayani tashiga min ashe tsumi ne da kayan infection dana mata wanda kowacce amarya take sha idan aurenta ya kusa nan fa ta hada wasu ta dinga miko min inasha ni duk kunya ta isheni islam kuma banda dariya bata min komai, aunty kam fuskar ta alamun murmushi take amma idan ba ka kalleta sosai ba bazaka gane ba haka dai na yini ana banka min magunguna sosai kaunar anna ya kara shiga cikin ranmu ita kanta tana tausayin mu ganin babu mai tsaya mana babu mai jan mu a jiki a ciki kuwa harda kakan mu wanda gaisuwa take hadamu sai kuma yace ya jikin aunty shikenan daga haka muke tasowa mu dawo bangaren mu, to kwana biyun nan baya nan ya nufi gidan wani aminin shi dake abuja wai zai kwana biyu acen.
Yau saura kwana biyu a fara biki ina zaune ina ba aunty kunu da spoon tana shan rabi rabi yana dawowa sai ga mai gadin kaka wanda muke ce masa malam bayan na fito nan kofar bangaren mu na gaishe shi yake fadamin nayi bako a waje, kallon mamaki nayi masa nace a raina wata sabuwa inji yan caca.
Anan tsaye malam ya barni ina jinjina wanda yazo nema na, haka dai na koma ciki na canza hijab na fesa turare kafin na cewa aunty ana nema na a waje zanje da ido tayi min alama saina dawo dama lokacin islam da anna sun fita siyan kayan miya da abinda baza’a rasa ba saboda girkin biki duk da basuyi gayya ba har nima banyi ba saidai mutanen cen unguwar mu duk sunce zasu zo kuma gashi maryam tayi mana gayyar abokanmu na secondary nan dai na fito har zuwa kofar gate din gidan mu a jikin mota na ganshi tabbas na gane shi shine best friend din yaya Farouk dan idan ban mance ba acen baya idan mukaje gidan kawu hafiz muna ganin shi tare da yaya Farouk sosai amininshi ne amma daga baya sai muka dena ganin shi anan ne naji su amira suna firar ai degree ya tafi karowa a london kuma yanxu sunyi kudi familyn shi har ba’a ganinsu sosai daga nan ban kara jin labarin sa ba sai yau danake ganinshi a kofar gidanmu jikin katuwar motar sa tabbas ya canza sosai har yafi yaya Farouk komai na fannin kyau kudi da kuma wayewa, shidin dogone saidai yana da kira ta maza sosai maybe