Share this page
bincike ni tas kafin na karasa garesa saboda sau biyu ana kai masa hari a shekarar nan dan ma Allah yana tsare sa” “Gaskiya ne dole ba kowa za’a amince ya rabe saba shikenan ka kaini gidan naka zuwa gobe in shaa Allah sai in koma kano danni ko takan farouk bazan bi ba “ daga haka suka ci gaba da hirar su har md ya isa apartment dinshi dake nan maitama bayan ya ajje alamin ya wuce zuwa gidan mutumin da yake kira oga *** Saidai ban taki sa’a dan dakin da yake ne na shiga ban fahimci hakan ba saida naga wayoyin sa a saman gado ga kuma alamar gurin daya tashi nan gadon yadan yamutse zaro ido nayi saidai kafin in gama tunani naji an murda handle din dafe kirjina nayi ina rumtse ido a hankali ya shigo baima lura dani ba ya nufi gado ya zauna har yakai hannu saman wayarsa kawai yaga kamar mutum a tsaye da sauri ya kalleni nima lokacin na bude idanuna a harzuke yace “ ubanwa ya kawo ki dakina “ zanyi magana yace “ get out stupid kawai “ ya fada a tsawace bansan sanda na fashe mashi da kuka ba dan a razane nake wallahi duk ya juye tamkar ba yaya farouk din dana sani ba, tsaki yaja a karo na babu adadi yana kara jin tsana ta a zuciyar shi tamkar ya kashe ni ya huta ya rasa wata irin masifa ce wannan yace baya sona amma sun kwakwafa mai ni tsaki ya kara ja cikin hasala yace “ na rantse da allah idan baki fita ba saina shake ki kin mutu a gurin nan “ ai da gudu nayi kofa ina kuka wannan wata irin rayuwa ce haka na fito parlor na nemi kujera na zauna har sannan ina kuka da kuma tausayin kaina gashi ina ganin tsanar da yayi min a ido, na jima a haka har kusan 3 na rana gashi zuwa lokacin yunwa ta fara kwakwalata ta, ganin zaman bazaiyi min ba yasa na tashi dan inajin pad din jikina ta baci gashi ban canja da wuri ba tashin hankali ma ya hanani yin tunani mai kyau, gashi ko sau daya bamu tsaya a hanya ba saboda saurin da yaya muhammad yakeyi shima uzuri gareshi wai boss dinsa zai bar kasar, handbag dina na dauka na zaro pad da pant din dana sako a jikar saboda in mun tsaya a hanya in canja sai kuma bamu tsaya ba, leke leke na fara inda zan shiga daga cen gefen naga kamar toilet nufar gurin nayi sai gashi kuwa toilet dinne shiga nayi na gama kimtsa kaina har wanka saida nayi kafin na fito da kayan jikina saboda babu towel anan din trolley na na janyo na bude na ciro abaya black mai stones na koma toilet din na saka sannan na danji dadin jikina, sai kuma na fara tunanin inda zan saka kayana da suke zube a parlorn daki uku ne biyu a jere sai daya acen gefe sai kawai naji cewar na cen gefen zai fiye min zuwa nayi na bude naga komai set akwai a ciki gasu white and gold da alama ma shine nawa danya tsaru a ciki kuwa nayita saka kayana dan naga babu kura ko datti kuma dama nasan ba’a jima dayin jere ba, bayan na gama shirya kayana sai naji jikina yayi min tsami saboda gajiya sai kawai na shimfida bedsheet na haye gadon ko pillow ban nema ba, banjima ba kuwa bacci ya dauke ni danma da yunwa na kwanta, nice ban tashi ba sai bayan magrib sosai nayi mamakin bacci wanda yake cike da mafarkai marasa kyau bayan nayi addua da dan azkar din yamma na sauko daga gadon na shiga toilet nan na iske komai na amfani da kayan wanka kala kala, wani wankan nayi na fito da towel a jikina na nufi walldrop dina na dauki wasu riga da wando kamar na bacci masu tsantsi na saka sosai sukayi min kyau jikin mirror na tsaya na fesa turare kala kala wanda yaya amira ta kawo min a ciki harda favorite dina REXONA na kama gashina da yake a kunce yasha gyaran saloon din da muka je da maryam da islam na daure da ribbon saiya bada wani style na ponytail gashi dama ina da tsayin gashi barakallah har baya, sosai nayi kyau dukda banyi kwalliya ba kamar a sace ni a gudu, slippers na dauko cikin takalma na nasaka na fito cikin tsoro tsoro har addua nake allah yasa kada a mu hadu dashi inda naga alamar kitchen na nufa. Babu laifi akwai kayan abinci cikin cabinet (Loka)din indomie naga zatayi saukin dafawa dan haka na janyo guda biyu kanana na bude famfo na dauki ruwa a tukanya dan kadan, ashana na fara nema cen na hangota a wata loka na kunna gas din na dora bamma nemi su attarugu ba dan bana shan yaji amma na soya kwan dana gani saidai banga albasa ba har saida na gama ina neman ruwa a fridge din dana bude anan ne naga vegetables da yawa daga kasa harda albasar daga sama kuma nama ne yayi kankara da yawan shi daga tsakiya kuma ruwane faro, sakin baki nayi ganin wani aikin sai maza yanxu minene abin hada ruwa da su nama, juyawa nayi gurin Dan karamin fridge din dake gefe irin na hotels shi kuma cikinsa lemu ne kala kala dan haka sai na fiddo ruwan na maida cen saidai yayi kadan wasu basu shiga ba haka nan na maidasu wajen su ina tunanin yadda zan ware rana daya inyi aiki a kitchen din in gyara komai a muhallinsa, dukda bashi da kazanta kawai babu tsari ne ko kadan, daukar flat din indomie na nayi na fito nan ma banji motsin saba direct na wuce dakina acen naci na koshi nasha ruwa sai sannan hankali na ya koma kan yan gidanmu gashi banda wayar da zan kirasu, suma nasan sunyi kewa ta, ganin babu abinda zanyi yasa na fara tunanin ko in dafa masa abincin dare? Wata zuciyar tace “ koma kinyi ba lallai yaci ba “ dan haka nayi kwanciya ta ina tunanin rayuwar da zamuyi nida yayan nawa gashi dama ina da burin karatu dan haka zuwa safe zanyi magana dashi, ina nan har bacci ya dauke ni. Asuba ta gari najmah. Yaya farouk kuwa bayan ya kora najmah sai ya dafe goshinsa yanajin tabbas haduwa guri daya da wannan yarinyar ba karamin bala’i bane dole zai samo manufa amma bayajin zai iya zama da ita a wannan gidan daga nan ya mike ya zura jallabiyar sa ya dauki key din motarsa da wayoyin sa ya fita acen gidan wani abokin aikinsa ya kwana bai waiwayi gidan saba sai kusan 8 na dare ranar sunday kenan , parking yayi da mota ya fito yana tunanin hukuncin daya yanke akanta bude kofar yayi ya shiga a parlor ya iskeni inata zuwa ina dawowa duk hankali na ya tashi ganin shiru yau banji motsin saba har dakinsa na leka amma ban ganshi ba shine fa hankali na ya kasa kwanciya gashi babu waya hannu na balle in kirasa saidai ina jin ya shigo cikin sauri na matso inda yake inajin hawaye suna cikomin ido dan gani nake kamar zan rasa shi yadda na rasa amina da anisa a rayuwa ta, cikin raunin murya nace “ yaya farouk ina kaje tun jiya banji motsinka ba hankali na ya tashi wallahi allah yasa dai lafiya “ batare daya bani amsa ba ya raba ni ya wuce wani iri naji ganin ko kulani beyi ba yasa na kuma taryan sa ina marairaicewa nace “ kayi hakuri idan nayi maka wani laifi ne dan allah wallahi bani da burin daya wuce muyi rayuwa kamar kowasu ma’aurata in shaa Allah zaka sameni mai biyayya a gareka “ cikin gajiya da takaici ya kalleni ya fara magan cikin tsawa “ najma I hate u na tsaneki waike baki ganewa ne ni banasonki banason zama dake banason duk wata kulawar ki a gareni, ki hada kayanki zan canja miki gurin zama daidai dake amma ba’a nan ba na rasa wata irin nakasshiyar zuciya ce a jikinki da bazaki dinga ganin abubuwa a yadda suke ba “ tunda ya fara magana nakejin wani irin yanayi mai zafi yana ratsa duk kanin gabobi na shin menene laifi na? Shin ya zanyi yau mijina yana furta wannan kalaman a gareni na tsana? Maganar daya cigaba da fadi ne yasa na kure fuskarsa ina kallo amma zuciyata ta tsaya cak tamkar wadda ta daina aiki “ ni banason mace mai bin maza wadda ta gama bada kanta a banzace , banajin zan iya zama tare dake najma shiyasa zan nisantaki da tawa rayuwar “Wani kuka na fashe dashi ina dukawa a kasa cikin tsananin tukukin bakinciki wai nice yau yaya farouk yake fadin wannan mugayen kalaman a kaina wanda ko rantsuwa zanyi bazanyi kaffara ba ban taba yarda wani daba muharramina ya taba hannu naba da gangan balle takai in aikata sabon allah, cikin tashin hankali nace “ wayace maka ina bin maza yaya farouk wallahi ban taba ba ka yarda dani dan allah, banaso mu bari kiyayyar iyayen mu mata ta shafi aurenmu “ “ ohh kina nufin sharri za’ayi miki naji inma sharri ne ki tafi ki dauko kayanki muje in nuna miki inda ya kamace ki “ sosai nake kuka nama rasa yadda zance mishi banyi aune ba naji ya riko hannuna da karfi yaja ni tamkar kayan wanki har zuwa gaban motar sa bai sake ni ba gashi duk na fara gurjewa a kasa haka ya daga baya ya wurgani ciki ya shiga gaba ya tada motar, tafiya mukayi ta kusan minti 40 amma har sannan kuka nake jin komai nake a mafarki yau wace irin kaddara ce wannan? Ina zai kaini? Wace rayuwa zan gudanar anan din gurin danayi nesa da ahalina , a wani kauye muka tsaya daga gani mun fita ma daga cikin abuja ne dan dakaga kauyen kasan ta talakawa ne kuma tsakanin wani gidan da wani akwai tazara mai tarin yawa daidai kofar wani gida wanda ko gidanmu dake kano ya fishi kyau anan ya tsaya ya fito ya kuma kama hannu na ina kuka ya janyo ni yana zuwa ya hankada kyauran nan ya bude ya shiga dani, a tsakar gidan ya watsar dani yana jin kamar ya kashe ni ya huta gaba daya bayason ganina kusa dashi (tabbas sihiri gaskiyar mai shi mommy kin cuce mu) daki biyu ne kadai sai toilet a gidan suma dakunan duk sun farayo gaba saboda tsufa gashi katangun sun tsattsage kai dagani kasan yayi shekara da shekaru babu mutane wai yau nice zan zauna anan? Karewa gidan kallo nayi dukda darene amma akwai farin wata wani kukan na sanya ina rarrafowa na kama kafafunsa na rike tamkar za’a kwace min shi nace “ dan allah mijina ko sakina ne gara kayi da ka barni a wajen nan ka taimakawa kanwar ka dan allah “ hankada ni yayi na fadi amma cikin sauri na taso ina ci gaba da rokonsa ina kuka saidai ko tausayina baiji ba karshema ya juyo yace “ idan kika fita daga gidan nan allah ya isa ban yafe miki ba duniya da lahira “ daga haka ya fita ya barni anan kasa ina kuka mai hade da kara inajin sanda motarsa ta tashi na kara fashewa da wani kukan nafi minti 10 kafin na fara hakura da duk yadda rayuwa tazo min haka na mike jikina a mace ina tangadi dan rabonda inyi kuka haka tun mutuwar amina dan koda akace mana ga gawar anisa a lokacin munyi tawakkali kuma jikinmu yayi sanyi shiyasa saidai kukan zuci. TAWA RAYUWAR By maryama Page 15 Daki na farko na shiga ko kyaure bashi da akwai babu komai cikinsa sai uban kasa da datti babu ko fanka balle gulub na haske, wani abu na hadiye mai radadi haka na fito na shiga dayan nan ma dai hakan take saidai shi akwai wata yaloliyar katifa irinta yan boarding sai ledar tsakar daki, amma fa bangon duk a tsage yake sosai tsoro ya kamani na fashe da wani kuka wanda ko hawaye babu tsabar yadda nayi shi da yawa, anan kofar dakin na zauna ina tuna aunty na da islam da duk wani masoyina sosai nakejin rauni a cikin raina in takaice muku yadda naga rana haka naga dare a wannan kangon gidan da babu komai cikin sa sai bantsoro danma bakina da zuciyata basu rabu da addua ba.(😞) Sai da yaga ya rabu da ita kafin yaji hankalinsa ya kwanta gida ya koma yayi bacci cikin kwanciyar hankali tamkar wanda aka zarewa kaya a zuciya, da asuba yayi sallah ya koma bacci bayan karfe 8 ya tashi ya shirya anan ne ya tuna da waccen ballagazar a cewar sa dan haka yaga dacewar ya kai mata kayan abinci da kayan sawarta dan kada ma ya kara tunawa da rayuwar ta hakan yasa ya shiga dakin dayake kyautata zaton nata ne, trollen ta kusan guda hudu ya dauka da uban kayan data fara jerawa a walldrop ya cusa duk a motar ya fita da su a cen wani store ya tsaya ya sai mata shinkafa tiya 3 da gari mn kwaki tiya 3 dasu mai maggi sugar gishiri sai sabulu da abinda baza’a rasa ba harda tukunya da mangal sai gawayi shima marar yawa ya durasu duka mota ya dauki hanyar kauyen. Bayan ya tsaya ya fito ya shiga gidan da wasu kayan , a zaune nake nayi tagumi abin duniya ya isheni lokaci daya har nayi rama ga uban sauron daya cijeni a jiya ga rashin bacci ga ciwonkai inafama dashi saboda kukan dana sha a hankali na dago idanuna da suke kasa na kalle shi, yana sanye da suit black masu kyau cikin nutsuwa na kauda idona ina gaishesa saidai bai amsa niba ya ajje kayan ya fita yaci gaba da dauko su, ko babu komai naji dadin daya dauko min kayana, haka ya gama shigo min da komai ya juya zai fita nace masa…… “ yaya farouk dan allah kada ka barni anan komai zakayi min kayi amma dan allah ka daukeni daga nan ina jin tsoro “ bai juyo ba kuma bece komai ba cikin sanyi na taso daga kofar dakin nazo inda yake har gabansa na tsaya kaina a kasa nace “ nidin marainiya ce kum… kukane ya kwace min sosai nake rashin mahaifina tabbas inda yana raye da duk haka bata taso ba saboda baban mu abinda mukeso shine yake so, rabe ni yayi ya fita daga gidan ya barni a tsaye ina kuka nama kasa masa magana har ya tada motar sa yayi gaba anan na tsugunne ina kuka wanda har daga zuciyata yake fitowa ya zanyi? Waye zan fadawa halinda nake ciki? A hankali wata zuciya tace min ALLAH take naji wani karfi yana shigata na mike daga tsugunnen na tafi inda kayana suke ina tunanin ta ina zan fara aikin gidannan gashi ko tsintsiya babu a gidan. *** Mommy ce suka rako mama da jikar kayanta zuwa inda motar su take, cikin jin kewa mommy tace “ yanxu dai kin nace bazaki kara mana koda kwana daya ba “ dariya mama tayi tace “ haba ai sai abban afiya yaga rashin hankali na biki dai an gama kuma minene na zama ai nayi kokari ma , kawai dai komai kenan “ “ hmm ai shikenan allah ya tsare hanya tunda an barmin diyata anan kinga damuwar bazata yimin yawa ba “ Nan suma yaran sukayi mata bankwana ta bude mota ta shiga tana daga musu hannu , mommy ce tace “ af kinga na manta “ saita sunkuyo kanta jikin kunnen mama ta rada mata “mutuniyar ki nasan tana cen tana azabtuwa ai wallahi aikin malam tamkar yankan wuka haka yake gaskiya idan kika koma kada ki dade ki sake dawowa dan mu koma ya kuma mana wani aikin akan najmah “ wani zaro ido mama tayi tace “ bayan wanda akayi har wani kike bukatar kari? Kin manta yace da zaran yaci maganin nan bazai iya koda sha’awar taba balle ya kalle ta , tsana mai tsanani zata shiga tsakanin su kuma shine kike bukatar kari? Haba yaya zulfa ki barsu haka mana “ wani shekeke din kallo tayi mata tace “ cab ai inkinga na bar najma da uwarta haka to saidai mutuwa sukayi amma wallahi yanxu na fara “ Jinjina kai mama tayi tace “baki tunanin wannan tsanar ma dayayi mata zaisa ya kasheta kuma a daure danki a banza “ shiru mommy tayi tana tunani kafin ta sauke ajiyar zuciya sai kuma tace “ shikenan mu barsu haka “ daga haka mama taja motar ta sunata daga mata hannu, bayan sunga tafiyar ta sai suka juya cikin gidan afiya da amira suka shiga dakinsu, abida kuma tabi mommy daki amra kuma ta nufi dakinta. Afiya ce ta kalli amira ganin sunyi zasu tafi wani hotel akwai bakin da suke jiransu acen amma gashi ita ta zauna taki tashi ta hada kayanta “ amira lokaci yana ja fa ya kamata ki hada kayanki mu wuce kada dare yayi mommy ta kawo mana cikas ko ita ko abba “ girgiza kai amira tayi tace “ na fasa zuwa kawai kije “ kallonta tayi da dan shock tace “ wai miyasa kikayi sanyi ne amira? Yanxu fa ko kadan naga baki son harka komai sai kice inje inyi ke banda ke “ tsaki amira taja cikin kosawa da yawan tambayar da afiyar take mata koda yaushe idan hakan ta taso tace “ na gama magana afiya please I need rest “ daga haka ta haye gado ta rufe ido, afiya kuma abin tun yana bata mamaki yanxu ya daina tsoro yake bata, ko kadan amira yanxu bata zuwa hotels balle wani abu ya shiga tsakaninta da wani gaba daya ta canja ta zama shiru shiru kuma kowa yaga canjawar da tayi tun su mommy ba tambaya har sun hakura sun kyaleta, jikin afiya a sanyaye ta gama hada kayanta ta nufi kofa ko kallon amiran bata sake yi ba ta fita. *** Aunty ta shiga kewar najmar ta har saida islam da anna suka gane hakan , gashi tana yawan kuka a kwana biyun nan da tafiyar najma idan su islam sun tambayeta sai tace tausayi ne kawai haka dai suka hakura da tashin najma saidai kewar ta bata Sake su ba, maryam da umma suna kokarin zuwa a bangaren doctor ma yana zuwa ya duba jikin aunty , saidai abinda yake tada hankalin aunty bai wuce mummunan mafarkin da take yiba daga biki zuwa yau saidai bata fasa addua ba. *** Rashin tsintsiya ya hanani komai gashi banda makwafta sai acen bangaren kudu shima akwai nisa tsakanin mu tamkar a wani jeji haka nake ganin zama bai kamani ba yasa na tashi na dauko wannan mangal na zuba gawayi a ciki dan kadan allah yaso akwai ashana na saka leda na kyarta, na fiddo tukunyar daya kawo min da ita yar karama zan dora sai kuma na tuna babu ruwa wani tashin hankali ya ziyarce ni, sai yanxu na tuna fa, da sauri na mike na nufi bandakin inda yau da asuba fitsari ya kamani na shiga toilet din na iske babu ruwa ko taras karshe da dutsi nayi tsarki haka nan dai inajin kyankyamin kaina amma na hakura aciki ne naga wani katon botiki da randar gwauro ( roba katuwa mai giwa) Dan haka na dauko botikin na fito dan shi kansa toilet din abin kyama ne ga yana sosai, soron gidan na fito inajin ciwon ulcer na yana kokarin tashi saboda yunwa jiya banci abincin dare ba gashi yau ban karya ba, dube dube na fara ko allah zaisa inga wani yaro koma babbane in roke shi alfarma ya samomin ruwa amma shiru banga gittawar kowa ba dan haka a raina nace tabbas bazan kashe kaina ba akan allah ya isar da yaya farouk yayi min ba dan haka na fito bayan na yafa gyale saman kaya na, akwai tafiya tsakanina da makwaftana a haka na karasa kofar wani gida nayi knocking ganin shima ba wani babba bane, bayan minti biyu naji an bude, wata dattijuwa ce saidai fa fuskarta babu alamun rahma dan dagani ranta a mugun bace yake wani kallo ta bini dashi sai kuma a shake tace “ lafiya daga ina?” Murmushi nayi nace “ inna kinga gidana cen haka jiya aka kawoni nan gashi banda ruwa kuma bansan inda zan nemo ba dan allah ki taimaka min da boket daya da kuma Aron tsintsiya zanyi shara “ tsaki taja har saida naji mamaki sai kuma cikin hasala ta kwala kira “hajar hajar “ da sauri naga wata yarinya ta fito nan inda muke fuskarta jawur da alama kuka tasha nidai baki sake nake kallonsu Mugun kallo tayiwa hajar din tace “shegiyar yarinya mai mugun hali zoki wuce cen rijiya ki janyo wa wannan balarabiyar ruwa ni nayi mamakin ma hausar data kama bakinta wai kuma a rasa inda za’a kawota sai wannan jejin, mtss allah ya kyauta “ daga haka ta juya ciki ta barmu anan, sosai maganganun ta suka bani dariya amma na kanne sai kuma na maido da kallo na kan yarinyar wadda bata wuce 14 years ba hannu ta miko min in bata botikin saidai duk shatin bulala ne abin tausayi gata fara dan sai nake ga kamar muna yanayi da ita, murmushi nayi mata wanda yake dabi’a tace a mafi yawan lokuta nace “ in babu damuwa muje tare saboda gobe “ cikin sanyin murya tace “ toh aunty “ sosai naji dadin kirana aunty da tayi nan muka juya har mun fara tafiya innar ta takwala mana kira muka dawo tsintsiya ta mikamin a yatsine sai kuma ta wurgawa hajar din mugun kallo tayi kwafa, nidai abin nasu ya tsayamin daga gani yarinyar tana shan wahala ci gaba da tafiya mukayi saidai babu mai magana cikinmu tafiya mukayi ta kusan minti bakwai kafin mukazo bakin wata rijiya saidai akwai mutane amma basu da yawa wasu wanki sukeyi wasu kuma suna inuwa suna fira dukkansu yan mata ne kuma bazasu wuce 14 to 16 years ba , hajar dince ta wuce da botikin ta zura wata guga dake gefe tayi ta janyo ruwa har tausayi ta bani dukda nima abin tausayi ce ganin inda rayuwa ta kawo ni wai yau nice da gata na da komai amma auren yaya farouk bai amfane ni da komai ba saidai wani zafi da zuciyata takeyi tamkar ni ba yar uwarsa ba a hankali nake kara kalle unguwar da nake ciki wadda saidai a kirata da jeji kauyen abuja , unguwar gidajen talakawa ne da marasa shi kuma irin gida cen gida cen ne akwai yar tazara gashi kowa ka kalla uzurinsa yakeyi, ina cikin kalle kalle naji hajar tana cewa “ aunty na gama muje “ TAWA RAYUWAR By maryama Page 16 Ganin da nauyi yasa na kama mata dukda bataso hakan ba amma na nace muka kama mukayi hanyar gidana, bayan munje cikin mamaki tace “ aunty gidannan yayi kura bari in taimaka miki “ da to na amsa mata nan fa ta fara shara ni kuma na dora shinkafa jellof dukda babu vegetable saidai tasha maggi da mai kuma dana gama mukaci tare daga nan na dibi ruwa na shiga wankan tsarki dan period dina ya dauke ita kuma tahau goge ledar tsakar daki na bayan ta gama ta shigar min da trolleys dina sai lokacin na fito daga wanka ba laifi gidan tas, daki na shige na shafa mai nasaka riga marar nauyi zuwa sannan anyi sallah azahar sai mukayi alwala mukayi sallah anan ne nace taje gida kada innar ta ta neme ta, batayi musu ba kuwa ta tashi ta tafi bayan na bata turare body spray mai dadin kamshi, haka na danyi tilawa nayi addu’oi sai kuma na karasa kyara komai na daidaita kayan amfanin kitchen kuwa wannan dakin na saka su marar katifa ganin ruwan ya kare yasa nace ta zama bata kamani

Chapter 7 of 10