Share this page
yana geamin gaskiya ga saje daya tara baki mai kyau ga fari sosai da yayi. Sauke idanuna nayi kasa ina aro murmushi a saman fuskata shima murmushi yayi yana matsowa inda nake “ ahh amaryar mu ya kk ya muka same ki dafatan baki mance ni ba “ dariya nayi marar sauti nace “ haba yaya muhammad ya za’ayi in mance ka koka manta twins ake kiranka kaida yaya farouk “ Jinjina kai yayi yace “ kwarai kuwa ashe dai baki da mantuwa “ “ gaskiya bani da ita ina yini “ “Alhamdu lillah ya hidimar biki har jibi yini ko ?” “ eh wlh in shaa Allah “ “Tohm me kuka shirya mana ne dan na tambayi abokina yace in tambaye ki “ Yake nayi dan nasan kawai ya fadi hakan ne danya kwantar min da hankali nace “ babu abinda za’ayi ta bangare na gaskiya “ “ tohm shikenan yanxu ki lissafamin abinda kike so na bangaren bikin nan kamar su kwalliya kudin dinki da duk abinda ba’ayi ba “ Dukar da kaina nayi ina wasa da hannu na sai kuma na girgiza kai nace “ yaya Muhammad allah babu abinda zanyi dan ba wani shiri na tanadar wa bikin nan ba “ Kureni yayi da kallo cikin jin tausayi na dan tabbas yaya farouk ya sanar masa kiyayyar da yake min , kuma yayi iya bakin kokarinsa akan yaya farouk ya amshe ni hannu biyu amma abu yaci tura karshe ma kusan fada sukayi sai kawai ya nemi address din nan inda muka dawo sai yaga ashe gidan kaka ne ma shine fa ya taho yaji koda abinda nake bukata dan yasan babu abinda abokinsa yayi. TAWA RAYUWAR By maryama Page 12 Mota ya daga ya zaro wasu kudi a cikin ambulan kimanin dubu dari uku ya miko min yace “ amshi idan basu isa ba ga card dina akwai number na ki kirani “ da kallo nabi hannun sa dake dauke da kudin saikuma nace “a’a bazan iya karba ba yaya muhd na gode da kulawa amma kayi hakuri dan allah “ bata rai yayi yace “ wallahi idan baki amsa ba saina mugun bata miki rai aini yayan kine ba a matsayin abokin farouk zaki dinga kallo na ba “ ganin ransa bace yayi maganar yasa nasa hannu biyu na amsa saidai hannayen mune suka gogi juna wani mugun shock ya ziyarce mu a tare da sauri na amsa ina godiya duk cikin daburcewa shima cikin wani yanayi najin babu dadi yace “ shikenan kije gida sai anjima amma duk abinda kike bukata make sure kin kirani “ da to na amsa daga nan ya shige mota na daga masa hannu har saida naga tafiyar sa sannan na shige gida ina kara mamakin kudin da yayi lokaci daya haka dan ko zan yi rantsuwa bana kaffara ba yaya farouk ya bada kudin nan ba. Su islam sun dawo nan fa nayi musu bayani take suka hau murna harda aunty kuwa nan fa anna tace inama wai shi zan aura islam ma haka tayi ta tsinewa farouk inajin su nidai bance komai ba har suka gama, daga nan islam tace yanxu ta zama bata kama mu ba sai muje mu nemo miki lace da atampopi kuma mu bada dinki urgent sannan mu siyo abinda zaki bukata dan wallahi bazaki dinka waccen kayar lefen ba balle kisanya su a biki Haka muka dauki shawarar ta muka tafi kwari acen saida muka siyo kaya na fita kunya dukda ba wani masu tsada cen bane amma masu kyau ne da inganci muka bada dinki kuma nace suma su islam da anna harda aunty dake gida su zabi abinda suke so nan islam ta daukar musu dama munsan size din aunty anan muka bada dinki kafin muka juyo gida lokacin tuni anyi magrib. Muna dawowa muka iske amira tana zaune tasa aunty a gaba gefenta uban ledoji ne manya cike da kaya bamuyi mamakin ganinta ba dan idan akwai sabo mun saba da wannan halin nata nan dai muka gaisheta ta amsa mana sai kuma ta turo min wannan ledojin tace “ ga gudummawar ta nan “ baki sake muka bita da kallo gashi komai jiki a sanyaye takeyi tamkar an canza amiran da muka sani mai fada da hantarar mu. Ganin dai kallon da muke binta dashi yasa tace “ ba abin mamaki bane idan mutum ya canza halinsa ba ni ina duk wannan ne domin Allah amma bada wata manufa ba kuma ina rokon duk abinda nayi muku a baya ku yafe min “ nan ma wani kallon muka bita dashi amma haka nan nace mata “ mun gode allah ya saka da alkairi “ dan kada mu karyar mata da guiwa, islam ma godiya tayi harda anna itama aunty ma da ido ta nuna jin dadin ta daga nan islam ta hau daga kayan a dinke suke har kusan kala 10 lace ne manya da atampopi masu tsada kuma kamar ta gwadani komai cas yayi min daidai a hankali na dago nace “ yaya amira ya akayi kika san size dina “ murmushi tayi for the first time da take zuwa gidanmu tace “kedai secret ne “ nima murmushi nayi ganin yadda murmushi yayi mata kyau ashe dama kyakkyawa ce mugun hali ne yasa muninta fitowa na raya a zuciya ta, dayar ledar takalma ne masu tsini da jiki sai pant da bra sosai na sake mata godiya ina jinjina kokarinta nan fa aka shiga fira harda ita yaya amira sosai kasancewar ta a gurinmu ya faranta ranmu a hankali na dinga jin dama haka sauran yan uwanmu suke damu da mun huta. Ranar biki Yau ta kama alhamis kuma ranar yinin biki na amma kamar ba bikin mace ba dan gidan mu daga ni sai islam aunty da anna sai amira da maryam da umma mune kawai , a cikin kayan da amira ta kawo min na sanya daya daga ciki riga da siket wanda sukayi min kyau suka fiddo da ainihin hasken fata na, lokacin ina secondary school har akwai masu cemin balarabiya dan nafi kama dasu amma daga baya nace kaini fa jini muka hada da buzaye amma ni ba balarabiya bace daga nan na hana sunan, sosai nake da kyau mai sanyi wanda kallo guda idan kayi min zaka san tabbas ina dashi, zuwa yamma saiga dan gidan kawu hamza wato muhammad ya kawo kayan abinci inji babansu haka dai kawu’s dinmu sukayita shigowa da abin arziki mudai godiya ce iya tamu, itama matar kawu ishaq tazo tayi allah ya sanya alkairi ta kawomin wasu jugs masu kyau na tangaran da flats itace dama wani lokacin take mana kirki ,itama matar kawu hamza tazo a yatsine ta kawo mana wasu cups daga nan suka tafi yan unguwar mu ma sundan leqo ba kamar umma da maryam wadda tazo da kayan ta tace sai an gama biki zata tafi munji dadi sosai ita kuma amira tsoro ya hanata kwana dan bata son iyayenta su ganta a gidan mudai bamusan dalilin taba amma mun bar hakan akan tsanar da mommyn su tayi mana ne. Abinci aka dafa kowa yazo sai an bashi harda makoftan kaka da suka shigo mana allah ya sanya alkairi, aunty anna ce ta shirya ta cikin atampa mai kyau saidai tana daga kwance abin tausayi, kakane da dare ya kirani yace in fadawa auntyn mu tuni an min jeren kayan daki a abuja wannan aikin kawu hafiz ne dan haka zuwa gobe inji in masa godiya, tabbas nayi murna harda hawayen farinciki kuma kaunar mutumin ta nunku a raina haka na koma parlor na zaiyane wa yan gidanmu abinda kaka yace min duk sunyi farinciki amma banda aunty data lumshe idanunta kamar me bacci abin ya bani mamaki amma saina share nace maybe gajiyar hayaniya ce haka muka kusa raba dare muna hira kuma duk mafi yawa zancen hakuri ne anna take fada min akan aure sosai jikina yayi sanyi da muka ga dare yayi sai kowa ta kwanta babu jimawa bacci ya dauke ni. Washe gari ranar juma’a misalin karfe 9 na safe na cewa maryam ta rakani gidan kawu hafiz dan banaso ya fita daga gida inason masa godiya gashi karfe daya za’a daura aurena, bayan na fadawa aunty sai batace komai ba haka nan jiki a sanyaye na fito maryam tana bina a baya har muka kawo bakin titi muka tsaida napep dan muyi sauri dukda babu nisa tsakani , bayan mun shiga get din nan naga motarsa take nayi hamdala ganin bai fita ba Maryam tace “ ke ki lullube fuskarki nan fa gidan surikanki ne ko kin manta zuwa anjima zaki zama matar dansu “ ta kare maganar cikin shakiyan ci wani banzan kallo na jefa mata nace “ aini abba ubane bawai suriki ba keni bani guri in karasa “ na fadi ina fusge hannuna data rike tana dariya kasa kasa knocking mukayi jim kadan yar aikinsu ta bude mana nan muka shigo itama cikin mamaki take kallo na wai amaryar da za’a kawo ce tazo gidan surikanta? Oho musu nidai ban damu ba dan kawu ubane gare mu kuma bazan taba masa kallon suriki ba su kuma yan gidan ruwansu ta shanyo dasu karbe ni da kar su karbeni duk daya shima gogan da zai zauna dani bai damu dani ba balle kuma su, ai abin baya min ciwo inda sabo mun saba. Gidan tsit da alama basu tashi ba, muna nan mundan jima saiga karan saukowa daga bene banyi zaton abba ne ba sai ganinsa mukayi, ya sauko cikin shirin fita cikin fara’a yace “ ahh daughter kece da safiya haka “ “ eh abba ina kwana “ Maryam ma ta gaishesa ya amsa yana murmushi (lallai mutum mugun icce) ya gida ina auntyn ku ya hidima? Duk Alhamdu lillah na amsa masa daga nan na duka nayi godiyar abinda yayi min nan yace baiji dadi ba aini diya ce a gunsa amma har inzo wata godiya nan dai yayi min nasiha akan hakuri da juriya sannan yace yau idan aka daura aure gobe za’a tafi dani abuja acen gidan yaya farouk dan haka in shirya, aifa kamar an bude famfo sai kuka ganin dai da gaske zan rabu da aunty na da islam harma dasu maryam, daya gama min nasiha yace in tashi ya kaimu gida nan muka bishi har kofar gida ya ajje mu kamin ya juya. Jiki a sanyaye muka shiga gida danji nake kamar zanyi rabuwa ta har abada nida aunty na da islam gashi ana fadin abuja za’a kaini, islam ce ta kama hannuna muka zauna bakin gado da dakinmu cikin tausasa lafazi tace “ haba big sis menene na kuka kuma bayan kinsan idan aunty ta gani hankalinta zai tashi “ hannu tasa a fuskana ta gogemin hawayen dana shigo dasu tun daga gidan kawu hafiz “be a brave woman mana “ yake nayi na gyada mata kaina cikin karfafa zuciya ta nace “ shikenan na dena “ “ yauwa kokefa amaryar faruku “ dariya itada marayam suka saka ni kuma cikin fushi nace “ allah ya sauwaka kudena hadani da wannan mutumin mai bakar zuciya “ “ mundena “ suka hada baki gurin fada dan sunga banyi maganar da wasaba saidai kowaccen su tana kunshe dariyar tane gudin kada ta fito a samu matsala. Bayan karfe 1 aka daura aurena da yaya farouk FADIMATU AMIN DA ANGON TA FAROUK HAFIZ kan sadaki naira dubu dari cas daga nan akayi gaishe gaishe dan kuwa ango yazo da matsawar kawu hafiz, shima yaya muhammad yazo daga haka kowa ya watse , ni kuma a daidai lokacin da aka daura auren naji zuciyata ta buga da karfi gabana ya fadi take nayita adduar da duk tazo bakina….. 09063174122 TAWA RAYUWAR By maryama Page 13 #fate Islam ne da maryam suka fara tsokana ta da cewa “ an daura an daura ta zama matar aure” tsaki naja na mike daga dakin zan fita saiga amira ta shigo itama tana murna, bata fuska nayi cikin shagwaba nace “ harda ke yaya amira “ “Ehmana ai dole inyi farincikin shigowar ki cikin mu “ murmushi kawai nayi na raba ta na wuce inda na koma cen bayan dakunan kakan mu na nemi guri na zauna ina tunani kala kala a raina. Sama na daga kaina ina kare mata kallo dukda rana tayi tar hakan bai hanani janye idanuna ba ji nake inama yaya farouk zai kauna ce ni da duk wani abu dake hakki a kan mace gurin mijinta tabbas da , babu abinda zai hanani yi masa biyayya dukda nima basonshi nake ba amma zanyi hakuri in karbi rayuwa a yadda tazomin. Amma kash nasan bazan samu wannan ba, bazanyi muku karya ba deep down ina kaunar shi amma kuma yanda yake yimin yasa nake jin tsanar sa a wasu lokutan. Dama lokacin bana sallah dan haka ba tashi daga gurin ba saida akayi la’asar tuni inajin hayaniyar mutane wanda na tabbata yan wancen unguwar tamu ne da muka baro saboda muna zaman aminci dasu dukda ba shiga harkar juna muke ba saidai idan biki ya tashi suna da kokarin yi maka kara. Doguwar rigace ta safe dana yi wanka na saka ta lace wanda yayi min kyau navy blue haka na fito daga back yard din kamar yadda nayi tunani mutane ne kedan shigowa babu laifi dukda bamuyi taro da yawa ba , kuma naga ya’yan kawu ishaq dana kawu nassar su biyu sunzo nan muka gaisa sama sama dasu daga haka na shiga parlorn inda na iske wasu daga cikin mates dinmu tare da maryam ana ta hira nan muka gaisa kowacce tayi min allah ya sanya alkairi dama saboda irin haka jiya islam ta siyo lemu da biscuit dan mu rinka badawa sai gashi na iske maryam duk ta basu sosai sukaji dadi, suma wasu yan islamiyyar mu sunzo dukda maryam ce ke gaiyatar su suma an basu, aunty kuma daki anna suka maida ta dan tace kanta ciwo yake, amira da islam kuma sune suka tarbi familyn mu dukda wasun su sunyi mamakin ganin amira tsumu tsumu a cikin mu bayan sunsan bamu ga miciji, haka dai suka gumtse gulmar su. Dama bamu sa ran zuwan yan gidan kawu aliyu ba da yan gidan kawu hafiz kuma basu zo ba, da dare saiga kiran kaka da kawu aliyu dana je suka zaunar dani suka min nasiha mai ratsa jiki ta hakuri akan aure sannan kawu aliyu yace in rike maraici na koda mukan samu sabani da mijina inyi kokarin ganin na shawo kan abun dan kada in tada hankalin aunty na dake kwance komai sai anyi mata ga ciwon kirji kwana biyun nan da take fama dashi danma muna kula da bata maganinta wanda baba doctor ya kawo mata, sosai nasihar ta zauna mun kuma na kudiri zanyi iya kokari na inga yaya Farouk ya soni kodan zaman lafiyar ahalina, ina kukan rabuwa da duk ahalina har suka gama kafin kaka yace inje gobe da wuri gurin 8 na safe za’a tafi dani hakan ya kara tada hankali na fiye da tunanin mai karatu a raina nace “ da gaske zan bar aunty na da islam da maryam ga kuma anna data zame mana wani garkuwa itama?” Wani kuka ya kubuce min haka dai na taso na dawo nan parlor inda maryam suke aifa ganin kukan da nake yasa kuma kowaccen su harda amira fashewa da kuka haka suka rungume ni munfi minti 2 a haka har saida umman maryam ta fito daga dakin da aunty take kafin ta rike haba tace “ yauni me zan gani wata sabuwa inji yan caca “ sai lokacin muka saki juna kowacce tanajin zatayi kewa ta gashi abuja ba kamar kano ba balle ace kusan kullum suna cen, tausayin mune ya kama umma sai kuma tazo ta kama hannu na tajani zuwa dakin da muke kwana anan ta zauna ta zaunar dani, nasiha irin wacce uwa takewa yarta shine tayi min ta kuma nuna min inyi biyayya ga mijina sannan in rike sirrin shi kuma in kara hakuri mun jima sannan tace inje maryam ta tayani hada kayana dan taji muna labarin karfe 8 za’a tafi dani harna tashi saita maidoni ta tashi ta fita bayan minti biyu ta dawo hannunta dauke da leda baka nan ta daga tayimin bayanin yadda zanyi amfani dasu , ashe maganin mata ne dana sanyi kala kala kamar dai yadda anna tayi min, anan ta hada min wasu ta bani na shanye dukda cikina akwai yunwa haka nan na shanye ganin dai bataga alamar naci abinci ba yasa ta kira saddik a waya tace ya siyo mun maltina da madara bai jima ba ya shigo ya mikowa islam sakon itace ta kawo mana nan umma ta hada ta bani tace in shanye tas dama cikina da yunwa nan na shanye sannan tacewa islam a zubo min shinkafa jellop da wannan naman kazar da tace kada wanda yaci a ajje nawa ne, fita islam din tayi ta dauko ta dawo aka hadamin da shinkafa kadan na kuwa cinye tas har mamakin kaina nayi kodan ma tun safe rabona da abinci har na wani yi rama ta yini daya dukda banda wani kiba dama saidai diri. Safiyar assabar Tun bayan sallar asuba na shiga wanka jiki duk a sanyaye dan ma maryam tana kara karfafa min guiwa, cikin kayan da muka amso a sabon gari na dauko atampa a ciki wata mai golden pink da rashin yellow kadan tayi kyau sosai annace ta dama mana kunu ta soya doya nan ta tsare ni akan dole inci haka nan bakina babu taste nadan samu naci daga nan anna ta kamo hannuna zuwa dakin da aunty take tana nan a kwance kamar kullum idanunta akaina sanda muka shiga, wasu hawaye naji sun zubo min na tausayin ta bansan sanda naje na rungume ta ba ina kuka tabbas uwa ko ayaya take duniya ce, da ace babu ita tabbas bansan wani hali zamu shiga ba a hankali na kwantar da kaina saman kirjinta ina hawaye marar sauti itama hawaye ne kebin kuncinta dan tasan tabbas yanxu ne asalin jarrabawa zata kwankwasa kofar yar tata amma babu yadda zatayi dole ta karfafa mata guiwa kuma zata ci gaba dayi mata addua in shaa Allah komai yayi tsanani yana tare da sauki, tadai san hafiz ya gama cutar ta tako ina gashi babu dama ta sanarwa wani daga cikin ya’yan ta dan zai iya bibiyar rayuwar su kumaa yanxu su kadai suka rage mata a duniya, mun jima a haka har saida anna ta matso ta kamani tana cewa “ yanxu su al’amin zasu zo shida muhammad wai sune zasu tafi dake dan haka gara kije lokaci yana gudu duk abinda kikasan ba’a dauka ba gara a hada guri daya da zaran sunzo dai asaka a mota “ ban iya magana ba na mike batare dana kalli mahaifiya ta dan wani irin rauni nake ji kamar ince wa kaka su barni anan amma nasan bamai yiyuwa bane. *** “Wai kana nufin baku gane komai game da batan gawar anisa ba “ aka fada daga cen bangaren wani numfashi oga ya sauke mai zafi yace “ kwarai kuwa dan duk wanda ya dauke gawar tabbas yana bibiyar rayuwar mu amma muna iya kokarin mu zamu gano hakan nan kusa “ tsaki aka ja daga cen bangaren ba’asake cewa komai ba aka kashe wayar, shima oga tsaki yaja sai kuma ya tadawa yaransa hankali kancewa dole su binciko ko wanene yake da niyyar bata musu aiki. *** Misalin karfe 8:30 muka dauki hanyar abuja bayan nasha kuka kamar zan mutu ganin tabbas fa zan rabu da dangina haka islam ta rungume ni itada maryam suna kuka ita kuma amira bata zoba ranar umma ma tayi kuka itada anna sannan sun kara min nasiha sosai tamkar yar da suka haifa, aunty ma dakyar ta bude baki tayi min magana wadda da kyar ake ji tace “ kiyi hakuri FADIMATU kiyi hakuri ki yafe min, nice duk na ja miki hakan kiyi hakuri allah yana tare dake “ daga haka kuka yaci karfinta ni kuma kalaman tane suka tsayemin arai saidai ban wani maida hankali garesu ba nima na fashe da kuka daga haka suka riko ni su umma har mota wadda yaya muhammad yazo da ita sai al’amin kanin yaya Farouk dama kayana an zube su a katon booth din motar ina kuka da komai suka rufe motar haka yaya muhammad yaja, muka dauki hanya dan ko yar rakiya kaka ya hana a dauki kowa. Tafiya muka sha ta kusan 4 hours kafin muka iso cikin garin abuja direct asokoro muka nufa inda apartment din yaya Farouk yake, a daidai kofar gidan muka tsaya kafin al’amin ya bude min na fito har kofar. Kayana suka fara saukowa dasu sai kuma yaya muhammad daya ajje trolly na ya taho yayi knocking har kusan sau hudu kafin kit aka bude sosai gabana ya yanke ya fadi, yaya farouk ne tsaye da alama bacci yake dan yau weekend daga shi sai gajeren wando da single wani kallo ya bimu dashi kafin ya maido da idanunsa da suka dan canza kala zuwa kan muhammad yace “lafiya “ Tsaki muhammad yaja yace “ al’amin shiga da wannan kayan ciki dan allah inada gurin zuwa yanxu haka boss ne yake shirin barin kasar kuma ni zan kaisa airport “ ganin an bashi order yasa ya dauko ya nufo kofar zai shiga amma sai yaya farouk ya tarye kofar yana bina da kallon tsana wanda yake kara razana ni kuma wani tsoronsa yana kara shiga cikin zuciyata. Wani hankada sa yaya muhammad yayi cikin fushi yace “ wallahi kodai ka bari a shiga da kayan nan ko kuma in maka sanadin barin aiki a garin nan kai ko kunya bakaji farouk Meyasa kake abu kamar marar mafada tsss” yaja tsaki ya warci kayana yana shiga dasu a mamaki na farouk bai hana ba amma daga kallon da yake binmu dashi ransa yayi matukar baci, yana gamawa yace inzo in wuce ciki dama kamar jira nake na wuce da gudu dann tsoro nakeji ya kamani inajin sanda motar su ta tashi na kara idasa shigewa wani daki da banma san kona waye ba a cikin mu. Wata rayuwa kuke tunanin ma’auratan zasuyi? Shin waye ya dauke gawar anisa kuma menene manufar sa? Waye yasa aikin kashe su amina? Yaushe asirin kawu hafiz zai tonu? Menene dalilin amira na canjawa lokaci daya? Waye bokansu mommy yace zai baiyana? Mommy zata samu nasarar kashe najma kuwa? Wani buri ne mama take dashi akan auren afiya da farouk? Menene ya haddasa kiyayya tsakanin mommy da aunty da kuma umma da aunty? Kuci gaba da bina a sannu in shaa Allah komai zai warware. 09063174122 TAWA RAYUWAR By maryama Page 14 Yaya Muhammad ya kara jan tsaki yana dukan sitiyarin motar cikin takaici yace “Al-amin waiko farouk yana shaye shaye ne nifa Al amarinsa kamar wanda ya samu tabuwa a kai inba haka ba minene nakin aurensa da najma yarinyar da ko makaho ya taba yasan ta isa kodan kyanta a sota bayan tarin tarbiyya da iyayenta suka bata kai nifa in baya sonta ya barmin ita in aura dan wlh ba karamin tausayi take bani ba “ Al-amin da shima abin yayan nasa yake daure masa kai yace “ ai ba kai kadai ba yaya md ko nima haka take a gurina amma ina tunanin mommy ce take kara saka masa tsanar ta dan kasan ko kadan ba’a jituwa kuma ni har yau banga abinda aunty tayi mana ba na rashin kyautawa “ tsaki md (Muhammad kenan)ya kara ja a karo na ba adadi kafin yace “ yanxu bari in kaika apartment dina zanje wajen oga na kasan yau zaiyi tafiya shida Nigeria sai an gansa “ jinjina kai alamin yayi yace “ nifa so daya na taba ganinshi amma ji nayi inama in zama yaronsa ko driving dinsa in dingayi aida rayuwata ta haye dan wlh mutanen kano ko keyata bazasu dinga gani ba, da yanxu zaka taimaka min daka tafi dani munyi masa rakiya wlh ni ko ganinsa ne in kara “ dariya marar sauti md yayi sai kuma yace “ kasan yanayin tsaron ne ba’a bari kowa ya gansa dan koni da nake yaronsa ba haka kawai nake zuwa ba sai an

Chapter 6 of 10