suna kallona cikin tsantsar mamaki wai yau nice nayi jarumtar marin yaya amra nida duk zagin da suke mana da cin kashi ban taba tankawa ba tsabar hakuri da kauda kai abida ce tace “ zaku sani zakuga abinda zai faru wallahi bashi kuka dauka “ daga haka suka fice kowacce tana dafe gurinda aka fasa mata.
-wani mataki zasu dauka kuwa?
-ya batun jikar da kawu yake nema?
-minene a cikinta wai?
TAWA RAYUWAR
By maryama
Page 7
Sai sannan aunty ta juyo tahau mu da fada akan meyasa zamu biye musu kuma bayan yayyan mune har mu tsaya muna dambe dasu sannan ta juyo kaina tayi mun tas akan marin dayiwa amra a gabanta, nan dai ta hademu ta kara mana fada da kuma nasiha akan hakuri da juriya sosai ta kuma ce mu shirya zuwa gobe aje a basu hakuri kada abin ya zama babba, kowa a cikinmu zaro ido tayi wai muje mu basu hakuri har gida? Amma kuma bazamu iya musu da auntyn mu ba saidai kowaccen mu turo baki tayi har gara islam itace tayi karfin halin cewa “ su fa sukazo inda muke kuma suka takale mu da fada sannan muje mu basu hakuri? Ai sai su raina mu wallahi “
“ ohh bazaki jeba kenan?” Aunty ta tambaye ta kafin ta bata amsa aunty tacigaba da cewa “ dukawa wada aiba gajiya bane, kuma shi yaki dan zamba ne yanxu irin dukan da kuka musu sai yasa wata fitinar ta tashi amma idan mukaje kuka basu hakuri shikenan komai ya wuce, ni banaso inji ance ga abinda kukayi dan haka babu fashi in shaa Allah gobe zamu je daga nan har ziyara ma sai mu danyi “
Raurau islam tayi da ido amma babu halin musu dole taja bakinta tayi shiru, nima kuma banason tashin hankali shiyasa na goyawa aunty baya amma fa idan wata cikinsu tayi kokarin zagin ahalina wallahi bazan yarda ba saidai in kara marin yarinya, ai dama ba wani finmu sukayi ba balle mu zauna su taka mu a banza.
***
A pharmacy suka tsaya aka musu dressing saidai kowacce ta dauki alwashi mai tsanani akan su najma kuma tunda suka taho babu wacce tayi magana itama afiya da suka iske a mota tsaki kawai sukayi basu tanka mata ba dan acike suke da ita sun gyale tane sai sun isa gida, a wannan halin suka isa gida kowacce ta fito tana jan kafa, iyayen nasu suna parlor suna hira harda kawu hafiz daya dawo daga gurin aiki duk ido suka zubawa su amira mommy ce ta mike da sauri tana dafe kirji “ me zangani accident kukayi ne na shiga uku “
Ita kuma mama ganin yarta lafiya saita saki ajiyar zuciya tana hamdala amma cikin kissa itama ta nufe su tana tambayar lafiya
“Ba accident mukayi ba dukane “ cewar abida wani zagi mommy ta laulayo ta dirkawa abida tana fadin “ waye yakeson a sake haihuwar sa dazai dukan mun yara haka koshi ubanwaye a kasar nan ku fadamin nayi imani da allah saidai wani ba shi ba “
Amra ce cikin takaici tace “ aida kinji wanda ya dakemu inaga sai kin suma dan tsananin takaici amma babu komai nice zan dauki mataki babu ruwanku a ciki “
Amirace ta hankada amra amma cikin ikon allah bata fadi ba abin kujera ya tare ta wani huci take kamar zakanya tsabar an mata abinda tunda uwarta ta haifeta bata taba mata ba amma sai gashi kaskantattun yara sun musu dukan kawo wuka cikin bakinciki tace “na rantse da Allah kika kuma cewa kece zaki dauki mataki akansu babu abinda zai hanani shakeki ki mutu har lahira nice nan zan dauka zasuyi dana sanin da basu taba yi ba indai sunana ne amira hafiz “ duk abinda sukeyi iyayen baki sake suke kallonsu mommy ce ta kulu da shashancin da suke tace “wai bazaku fadamin wanene ya dake kuba zaku tsaya kuna min hauka “
Abida tayi murmushi mai ciwo tana dafe goshinta dake mata azaba tace “ islam, anisa da najma ne “ zaro ido mommy da mama sukayi da al’amin wanda ya shigo ya iske suna maganar amma kawu ko gezau beyi ba saima kauda kai dayayi yana ci gaba da danna wayarsa, mama ce tace “ meya kaiku gidan mayun nan ubanwa yace kuje musu gida aiga irinta nan a banza kunsha duka “
Amira ce tayi kwafa ta nuna afiya dake rabe jikin bangon parlorn tace “ wannan banzar ce tace mu kaita gidan waita bigewa najma warning akan yaya farouk haka muka dibi kafa muka bita amma dayake butulu ce ita a gaban ta aka mana duka karshema guduwa tayi mota ta zauna “ mommy ce ta kalli afiya ta girgiza kai ranta na kuna na sokancin yarinyar gata babba amma mai karamar kwalwa, mama kuma hararar ta tayi tace “ kin bani kunya afiya saboda allah kija su gidan mutane kuma kina gefe kina kallo a daki yan uwanki?” Itadai banda sunne kai batayi komai ba dan batajin zata tsaya a daki lafiyar jikinta a banza sudai da sukaji zasu iya(😂), nan fa ta inda mommy tashiga ba tanan take fita ba sai bala’i take da alwashin daukar fansa amma kawu ko ci kanku baice ba daga karshe ta furtima su daki kafin ta juyo kan al’amin dake bata hakuri yana fadin abu a hankali kuma ma ai ba’asan me su amiran sukayi ba nan ta shiga zaginsa dan dole yabar parlon yana dariya kasa kasa
Juyowa tayi kan kawu nan tahau masifa ganin yaki cewa komai, banza yayi da ita harta karasa surutun ta ganin ya manna mata hauka yasa ta tashi ta haye saman bene inda dakinta yake wayarta ta dauko ta danna kiran wata number wadda rabonda ta kira harta manta bayan an daga mutumin zai hau surutu ta katse shi da cewa ka duba message dinka zan tura maka address da komai inason a kwaso min yaran gidan amma incomplete building dina zaka kaisu daga haka ta kashe ta danna masa text message harda kudin da zata biya take yace done (😢 kaico su najma).
Bayan tafiyar ta kawu yabi bayanta da murmushi kafin ya shiga messages dinsa ya turawa wata number sako ya sender sai kuma ya shafa kansa yana tunanin yadda abubuwa suke tafiyar masa lafiya wani murmushin ya sake yace nusaiba u are done “ sai kuma ya fita, a bangaren amira ma ko sallar magrib bata damu da tayi ba ta kira wani tsohon saurayinta da suke cin duniyar su da tsinke ta fada masa abinda takeson yayi mata akan su najma har address ta bashi daga haka taji hankalinta yadan kwanta dan wallahi yadda tayi kuka da idonta suma sai sunyi, amra kuwa bata nemi kowa ba amma da kanta takeson daukar mataki kuma batason ko amira da abida su sani dan kada ma su fadawa mommy.
A gida kuma bayan aunty ta kara mana nasiha zuwa lokacin anyi sallah ta magrib sai duk muka tashi kowa yayi alwala mukayi sallah sannan muka ci gaba da aikin tuwan mu zuwa isha’i mun gama komai nan na zubo mana a faranti mukaci gaba dayan mu dama haka mukeyi, sallamar Maryam naji bayan ta shigo ta gaida aunty sannan ta mikomin kula tana murmushi “ minene a ciki “
Na tambaya “ anshi ki bude mana kinsan Yau na dawo daga gidan gwaggo acen nayi”
Tace min tana kara mikomin amsa nayi na bude nan naga alala ne cikin zumudi nace “ wow amma kin kyauta min kinsan bana gajiya da favorite dina dukda naci abinci amma wallahi saina kara “ dariya tayi tace “ kash bankawo da wuri ba amma babu komai aiga anie nan itama tanason alala “ dama kamar jira take anisa ta matso itama islam matsowa tayi banda amina da dama ba wani son alala gareta ba nan muka bajeta a flat gashi tasha manja da yaji ai bamu saurara mata ba saida muka cinye tas amma fa cikinmu kamar ya fashe itama aunty kadan taci tayi hamdala dan tun dazu gabanta yake faduwa batajin dadi saidai tana ta hasbunallahu wa ni’imal wakeel bayan mun gama muka hau labari aunty kam jinki kawai take dan jikinta sai kara sanyi yake tanajin kamar akwai abinda zai faru gareta mara kyau ganin karfe tara tayi yasa aunty tace wa maryam ta tafi gida dare yayi amma najmah da anisa su rakata , harsun tashi najma taji cikinta ya kulle dan haka tace “ ku jirani in shiga toilet dan allah “ da gudu ta dauki buta tayi toilet ganin haka yasa aunty tayi tsaki tace amina jeki dan allah ni banason fitar dare gashi umman maryam bataso ta dingayin dare kuma ma ai bai kamata ba “
Maryam ce tace “ allah aunty dare beyi sosai ba fa kawai dai..” tace tana toshe baki gudin kada tayi laifi, kwafa aunty tayi tace maza ku wuce “ da sauri suka nufi kofar gida inajin sanda Maryam take min saida safe amma inaaa gudawa kawai nake cikina ya baci sosai ga alala ga tuwo.
Har kofar gida suka rakata saida ta shiga kafin suka juyo suna tafe hankali kwance saidai wani irin burki da akaja a gabansu yasa kirjinsu bugawa kafin suyi wani yunkuri kattin maza tuni suka fito aka jasu cikin motar ko damar ihu basu samu ba dan ita amina tsabar tsorata tuni ta suma.
-a ganinku suwaye suka dauke su?
-hmm
️
TAWA RAYUWAR
By maryama
Page 8
Muna cikin gida muka ji tsayuwar mota da tashinta nan take aunty gabanta ya mugun faduwa har saida ta dafe kirjinta tana addua a fili “aunty lafiya “ fitowa ta kenan Daga toilet naga ta shiga wani irin yanayi islam ma tasowa tayi ta zauna gefenta tana fadin “ meke damunki ko ciwon ne zai tashi “ girgiza mana kai tayi tace “ ba ciwona bane kawai naji a jikina kamar babu lafiya ku bakuji tsayuwar mota ba? Kuma su amina naga sun dade ku tashi mu dubo su “ ta karasa maganar tana mikewa nan hankalin mu mukaji ya tashi duk bin bayanta mukayi dan islam ko hijab bata dauka ba sai dankwalinta data yafa, fita mukayi nan mukaga shiru unguwar tamu dama gashi babu wasu masu kudi saidai rufin asiri ko nepa ba ko ina suke dashi ba, gidan baba doctor mukaje nan aunty tayi knocking zuwa cen saddiq ya bude bayan mun gaisa aunty tace mishi wai su amina kwana zasuyi ne
Cikin mamaki yace “ai tuni sun juya ina jiyo sanda suka rako maryam suka juya “
Wani baya aunty tayi zata fadi mukayi saurin taryo ta wani karkarwa jikinta yahau yi cikin tsananin tashin hankali tace “ tabbas dama nasan ba lafiya ba ina suke yanxu wayyo allah na wayyo ni nusaiba ya allah ka dube mu da idan rahma innalillahi wa inna ilaihi rajiun “ ta fashe da kuka tana fincike rikon da muka mata, sosai muka shiga tashin hankali yanxu dauke su anie akayi ko kuwa me hakan yake nufi? wani kuka muka fashe dashi cikin damuwa muka bi bayan aunty dake zabga sauri batare da munsan ina zata je ba, ai saddiq da gudu ya shiga gidansu ya tado yan gidan harda baba doctor da umma, maryam kam kuka itama take jin yan uwanta wai an dauke su bayan yanxu yanxu suka rakota gida , kafin su umma su isa inda muke tuni aunty ta zube a kasa ko mu bamu samu taryo ta ba nan fa kowannan mu banda ihun kuka da kiran sunan allah bamu komai muna haka su saddik suka iske mu dan haka baba doctor yace aka ma aunty muje gida zuwa gobe da safe sai yaje ya shigar da rahoto na batan nasu, sannan yanxu shida saddiq zasu bi sahun motar su gani, duk dadai munsan danya kwantar mana da hankali yace haka amma ai tuni motar nasan tayi nisa ,nan fa mu biyar muka kinkime ta har cikin gida , a daki muka ajjeta amma fa cikin mu uku an rasa wanda za’a lallasa dani da islam da maryam dan tsabar rudanin da muka shiga, ai a daren su umma kasa komawa gida sukayi anan mukayi kwanan zaune kowa da tunanin da yakeyi.
Kafin safe baka iya gane kamannin mu sosai dan duk munyi luhu luhu bacci dai baiga idanun mu ba, hakurin duniya umma da baba doctor sun bamu amma inaaa bazamu iya hakura da kewar yan uwanmu ba gashi bamu san wani hali suke ciki ba kuma bamu san manufar wanda suka daukesu , allah sarki rayuwa.
Asubar fari baba doctor da saddik suka fita basu dawo ba har saida suka shigar da rahoto a police station na batan yan matan biyu , mu ma anan gida islam ta kira su kaka, kawu hafiz, kawu aliyu, kawu ishaq, kawu nasaar , amma bamu da number maman rakiya shiyasa bamu kirata ba kafin wani lokaci labarin batan su amina ya zagaya gaba daya dangi harda makwafta da kuma garin kano gaba daya indai mutum yana social media zai gani nan fa zuwa karfe tara saiga officers sunzo harda wasu yan jarida da kuma yan gidan radio aka hau mana tambaya, iya abinda ya faru muke ba kowa amsa amma har sannan aunty tunda ta farka ta kasa magana sai bin mutane da ido take kawai su kaka ma duk sunzo cikin tashin hankali nan fa aka fara zaga gari da neman su amina amma shiru kake ji.
Kawu aliyu ne ya kara lumfasawa ya dubi yan uwansa da mahaifinsa da suke kofar gidanmu dama sauran jama’a masu jimami na batan su amina “gaskiya akwai matsala baba kuma alamu sun nuna ko suwaye suka dauke yaran nan anjima ana fakon su sai jiya suka sami nasara gashi duk wata hanya anbi an toshe balle a samu kofar da za’a kamo bakin zaren “ kawu hafiz ne cikin alhini ya amshe zancen da cewa “ koma su waye bazasu samu nasara akan yaran nan ba in shaa Allah kuma ina tunanin saboda kudi suka dauke su amma koma minene zamu ji ai “ jinjina kai kaka yayi kafin yasa yatsa ya lakuce ruwan hawayen daya zubo musu yace “ muma muna da alhaki a wannan gabar saboda bamu basu wani tsaro ba bayan a cikinku kowa ya killace nasa ya’yan amma su munyi buris da rayuwar su wanda nasan inda amin yana raye bazai bar daya daga cikin iyalenku a nan ba su kadai “
“Hakane baba Allah dai yajikan amin amma ba karamin kyautatawa yan uwa ne dashi ba “ da Amin “ suka amsa kowa zuciyar sa cike da tunani kala kala.
A lokacin da aka dauki su amina take wani kato ya rufe fuskar anisa ganin ita bata suma ba, wani kango aka kai su nan fa kattin nan suka daure su a wani daki dake saman incomplete building din sai gaba nin asuba amina ta dawo hankalinta amma dayake a daure suke hannu da kafa baki da ido shiyasa basu samu damar koda motsi ba dukda suna jiyo maganar kattin dake cen gefe kamar parlor
Ogansu ne yace “kai wannan lamari nasu akwai cakwakiya nifa a jiya da dare na tsorata da ganin su rafta wai suma an turo su “ wani siriri a cikinsu ya cabe zancen da cewa “ sudai yaran nan sun shiga uku kowa farautar su yake kuma ma gashi naji ance jinin sune “ dayan maidan fadi yace “ hmm ni dama kawai su bani kwangilar yaran nan wallahi nasan yadda zan kare dasu “ wata dariyar shakiyanci sukayi nan dai suka ci gaba da maganar su amma ko kadan su anisa basu fahimci inda maganar su ta dosa ba.
Kwanan su biyu a gurin saidai a since bakinsu a basu abinci in kuma zasuyi fitsari a hakan idanunsu a rufe mazan suke raka su suyi wannan dalilin ya mugun jan hankalin kidnappers din dan haka ogan ya kira wanda suka bashi aiki yace sufa suna son matan nan ya za’ayi? Cikin rashin imani ba tare da tunanin komai ba aka ce an basu dama suyi abinda suke so dasu a ranar su anisa sun riski tashin hankalin da tunda mahaifiyar su ta haifesu basu taba gani ba ranar mazan nan sukayi raping nasu babu wani tausayi, saidai tun kan su gama ciwon anisa yayi sallama dan sosai ta kame musu idanunta da suka kumbura saboda kuka da bakinciki tuni sun firfito, saida kattin suka gama shagalinsu kafin suka lura da yanda anisar take, ita kuma amina hankalinta ne ya gushe (🥺💔) bama tasan me ake ciki ba balle ta fahimci ciwon yar uwar tata, tabbas rai biyun sunga jarrabawa a ranar , ganin anisa a wannan yanayin yasa hankalin kattin ya tashi ogan sune ya kira waya bayan an daga yake fada cewar dayar fa ta kakkafe musu ya za’ayi? Daga cen bangaren akace kawai tunda sun keta haddin yaran hakan ma kadai ya ishi yan gidansu dan haka a dauke su akaisu kofar gidan da cikin dare, oganne ya nisa yace “ nifa sai inga barinsu a raye akwai matsala tunda kafin muyi raping dinsu saida muka bude fuskar su kuma dukda darene ai sun ganmu tunda muna da touch kuma nasan sun haddace maganar mu, me zaisa mu yanke harshen su kawai?” Wata dariya akayi daga cen bangaren kafin akace to kawai ku saukaka musu ta hanyar kashe su mana “ duk muguntar ogan nasu saida ya zaro ido ganin duk abinda suka musu bai isaba sai sun kashe su tab wannan yaran sun tabo wa kansu bala’i batare daya sake magana ba ya kashe wayar yace “ an bamu order mu kashe su “ sauran biyun sukace to kafin nan bari mu kara shagali oga daga nan babu tausayi suka afkawa su amina saidai tun kafin su gama anisa rai yayi halinsa, amina ma suna gamawa siririn nan ya kama wuyan ta ya shake tun tana fadin sunan allah da dasasshiyar muryar ta har tayi shiru alamun ta mutu, ita ma anie da sukaga ta cika sai suka kinkimesu suka kai mota suna jiran 2 tayi na dare suje su yar dasu a kofar gidan.
Kwana yanxu na biyu ne da sace su anisa izuwa lokacin duk mun fidda rai daga ganinsu kuka kuma munyi har mun gode allah duk mun fige aunty kam ciwonta tuni ya tashi amma tace kada akaita asibiti abarta a gida tasan mutuwar tace tazo wannan kalmar idan ta fadi ji nake har tsakiyar kwalwa ta suma kawun nan mu suna iyakacin kokarinsu tare da yan sanda , su mommy ma sunzo sunyi jaje amma a tsaye sauran matan ma sunzo sun jajenta ma aunty, daga haka kowa ya tafi umma ce dai da maryam suka dawo nan da zama kuma baba doctor shine ya basu umarnin hakan dan kada abin yayiwa aunty biyu shima yaya hassan yazo har ya taho dasu kayan abinci da abinsha kuma kullum yana tare da officers ana bincike amma shiru kake ji shima har kuka saida yayi jin batan amina dan kuwa a kwanakin nan ya fada soyayyar ta, amma farouk baizo ba wai aiki yayi masa yawa inji mommy da tazo take fadi sosai abin ya matukar bata min rai saidai nadau alkawarin saiyaga rashin mutumci na dabai san inadashi ba.
-wa kuke tunanin yasa ayi aikin nan mu hade a comment section.
TAWA RAYUWAR
By maryama
Page 9
Ranar da za’a kawo mana gawar su amina ranar kowa jikinsa yayi sanyi dan wani faduwar gaba muka dinga ji aunty kuma jikinta ne ya rikice sosai harda aman jini amma yin duniya munyi akaita asibiti tace bataso abarta kawai ta mutu a haka, kowannen mu nida islam sukuku muke kamar wanda kwai ya fashewa a ciki, ga wani ciwonkai da nake fama dashi har magani nasha overdose amma a banza babu sauki sai gurin allah, dama bamuyin bacci amma a ranar gurin karfe 12 bacci ya dauke mu saidai aunty ce kawai batayi ba idanunta dai a rufe amma ba bacci take ba, daga nesa suka ajje motar su kafin suka dauko su amina a cikin sanda suka ajje su daidai kofar gidan kafin suka juya zuwa gurin motar su suka tafi.
Da asuba baba doctor da saddik sun fito sukaga kamar gawa a kofar gidansu aunty nan cikin tashin hankali suka nufi gurin, hasashensu kuwa ya zama gaskiya gawa ce amma ta amina cikin wani irin yanayi duk dauriyar doctor kuka ya sanya yana mai rungume yarinyar shima saddik kuka yasa kafin yace “ ko ina ita anisar allah yasa basu kasheta ba “ 🤔😳 nan fa baba doctor yace ya kamata su shiga da ita cikin gidan da kyar suka shiga da gawar amina dan tayi nauyi sosai dama abinka ga mai kiba.
Tashin hankali ba’a sanya masa rana
Duk mun fito yin alwala ta asuba mukaji an turo kofar gidan mu dama tunda abinnan ya faru ko rufewa bamayi, rayuwar duk ta fita daga ranmu nice na fara dago kai na kalli masu shigowa cikin mamakin bakin da mukayi da asuba wani zabura nayi na mike ina salati ganin kamar mutum a hannun su baba doctor hakan ya janyo hankalin islam da Maryam wanda harsun kabbara sallah take suka salamce aunty da umma ma da suke daki fitowa sukayi dukda jikin aunty babu kwari amma jinta tayi wani mayen karfi a take yazo mata da sauri ta nufi baba doctor da saddik da suka sunkuyar da kai hawaye nabin idanunsu duk kuwa tarin jarumta irinta maza, “ wanene wannan me yake faruwa doctor? Gawar wanene haka “ aunty tayi tambayar a burkuce umma ce tayi karfin halin kamata tana cewa “ kwantar da hankalin ki aunty muje ki samu guri ki zauna tukun “ wani murmushi na ciwo tayi tana girgiza kai gabanta yana dukan ukku ukku kafin ta juyo wajena ta warce fitilar dake hannuna ta dalle gawar da suke dauke da ita, me zamu gani Amina ce babu numfashi ko alamar rai tare da ita ga rigarta daga sama duk a yage cikin tashin hankali ta saki fitilar tana kwala kiran sunan allah da karfi muma wata razana mukayi babu wanda baiyi kara.ba cikin kaduwa, kafin kace me aunty tayi baya ta zube jini yana fitar mata ta baki da hanci ai rasa inda zamu nufa mukayi na dafe kaina ina kuka bakinciki, jin duniyar ta fita a kaina bansan sanda na zube a gurin ba na suma, baba doctor, saddik cikin tashin hankali abinda ke faruwa yasa suka ajje gawar amina saman sallaya da na shimfida nan umma tayi kan aunty tana kira amma inaa babu ko numfashi tare da ita, islam ce ta ruga kan gawar amina tana kuka na tashin hankali tama rasa ina zataje taji sanyi maryam ma kukan tashin hankali take duk ta tsorata jikinta banda karkarwa babu abinda yakeyi nan fa tun karan da aunty tayi yasa makwafta suka fara shigowa nan fa suka iske abinda ya girgiza su gashi kuma ance gawa daya ce ba’asan inda anisar take ba ga kuma halin da yan gidan suke ciki kuma kowa abinda yake daga masa hankali da kaga gawar amina kasan anyi mata fyade kafin rasuwarta shiyasa idan suka tuna babu anisa sai kowa jikinsa yayi masa sanyi .
Tundaga faduwar da aunty tayi ta samu paralyze wato shanyewar barin jiki tun kafin ayi jana’izar amina aka tafi da aunty asibiti acen ne suka tabbatar da haka su kaka kowa ya taho gidan dasu akayi jana’iza .
Lokacin da abinda ya faru ya riski dangin mu sun shiga tashin hankali ba karami ba ba kamar yan gidan kawu hafiz kowa jikinsa yayi matukar sanyi har bazaka iya banbance wanda ya saka aikin ba kuma sosai suka nuna tashin hankalinsu kuma duk sunje gidan mutuwar dukda babu wadda ta saki jikinta a cikinsu dama su afiya basu tafiba dasu akazo dalilin kin tafiyar su kuwa mommy tayi tayi da kawu yabar ta zuwa gidan bokansu amma ya hana dukda karyar rashin lafiyar da tayi masa na wani dan uwansu a kauye amma ya hana kamar dai yasan da abinda suke kullawa hakan yasa sai yau ta samu fitowa zuwa gidan rasuwar ana