Share this page
nan (wato kaka😂) ta inda ta shiga bata nan take fita ba ganin za’ayiwa yarta salhohuwa bayan bata ma fara cika burinta ba.(🤔) har tafi mommy zagewa daga nan dai suka gama kulla kitumurmurar da zasu aiwatar kafin sukayi sallama, mommy ta ajje wayar tana yin kwafa ganin tun ba’aje ko ina ba abubuwa zasu cabe musu bayan ita ko murmushi bakinciki takeyi idan nusaiba ko ya’yanta sukayi itace bata tashi daga gun ba Harsaida abba(kawu hafiz) yayi kiranta kafin ta nufi dakin nasa nata ta shan magani gefe daya ga zugar da yar uwarta ta gama mata yanxu, a haka ta tura kofar da sallama ta shiga yana zaune a gefen gado yana latsa waya, abba ba dogo bane irin mazan nan ne tsaka tsaki yana da jiki kadan kuma yana da hasken fata gashi mutum ne mai fara’a ga kowa Da son mutane , dagowa yayi ya mata kallo daya ya dauke kai nan ta zauna ta fara huci tana magana da fada akan hukuncin da kaka ya yanke itafa sam abin bai mata ba kuma tana da wadda zata ba farouk gara ma su sake zama dan bazata yadda a dannewa danta hakki ba baice komai ba harta karasa maganar ta kafin yace “kina nufin magana biyu zan saka baba yayi? “ ya jefa mata tambaya take ta diriri ce dan duk iskancin mutum yasan waye kaka inya fada baya canji nan fa tahau kame kame ganin dai ta kasa bashi amsa yasa ya saki murmushin dashi kadai ya barwa kansa sani sai mahaliccinsa kafin ya kama hannayenta yace “calm down zulfa wai meyasa kike tsaurara abune maganar hadin auren nan baba ya riga ya yanke dan haka inma kinada wani abu a zuciyarki game da haka gara tun wuri ki janye dan aure babu fashi in shaa Allah kuma ka da ki manta najmah fa yar uwar Farouk ce sannan bamu san abinda allah ya boye ba kinga gara kada kiyi shisshigi ki barwa Allah komai” yana gama fadin haka ya saketa ya mike a hankali ta bishi da kallo harya shige toilet ya barta tana tunanin menene a zuciyar mijin nata dan wani lokacin yana bata mamaki idan yana wani abun (kamar yaya fa?) *** “Me aka tattauna a gurin meeting din? “ zuru zuru mukayi nida amina rasa wanda zai fada mata akayi har tsawon minti biyu islam ce ta kalleni tace “aunty fa tana tambayar ku “ nan ma shiru ne sai hawayen da nake kokarin gogewa dukda a duhu ne amma akwai hasken farin wata hakan yasa aunty ta lura dani kafin ta juya gurin amina da itama hawayen ta shafe, babban dalilin kin gaya mata da mukayi munsan ciwon tane ya tashi koda bata fada ba gashi kuma bamusan wani hali zata shiga ba akan lamarin tunda komai a bude yake, mudin yan uwane amma kuma duniyar mu ta banbanta kuma kowa ya sani “ shikenan zan kira wanda na isa dasu sai su fadamin abinda aka tattauna “ jin abinda aunty ta fada yasa na fashe da kuka ina toshe bakina kafin da kyar na saddakas nace “aunty wai auren hadi za’a mana amina da yaya hassan ni kuma da yaya …” kasa fada nayi wani kukan yana kwace min na tausayin kaina , tunda na fara magana aunty take fadin Hasbunallahu wa ni’imal wakeel a zuciyar ta harna kai karshen magana ta saidai rashin fadin mahadin nawa yasa da kyar cikin karamar murya kamar mai tsoron a jita tace “ keda wa? “ amina ce tayi jan halin cewa “ itada yaya farouk “ sosai muka ga aunty ta zabura ta mike zaune hakan ya kara tada hankalin mu fiye da ko yaushe dan munyi tunanin sai hankalinta yafi tashi akan auren hassan da amina amma sai naga ba haka ba cikin sarewa islam tace “ aunty ko akwai matsala “ sai sannan ta lura da abinda tayi dan haka tayi kokarin ganin tayi calm down kafin tace “ babu komai allah ya sanya alkairi “ sosai kalaman ta suka bamu mamaki har saida na kasa hakuri nace “ kina nufin kin yadda a aurar damu ga makiyan mu aunty?” Girgiza kai tayi hawaye nabin kumatunta tace “ babu abinda zai faru da rayuwar ku sai Alkhairi ina mai horar ku da hakuri komai zai faru gareku ku sani allah shine yake yi kuma duk abinda ya tsara babu makawa saiya faru saidai amsar kaddarar mu yana kara mana kusanci da allah madaukakin sarki kuma duk abinda iyayen naku zasu yanke akanku bazan iya hanawa ba saboda karfin ikon da suke dashi “ta karasa maganar cikin sanyin jiki dana zuciya saidai ita kadai tasan mi take ji tamkar zuciyarta zata fado kasa tsabar ciwo, daga haka mukaga ta mike ta shige daki nan islam tayi ta tayamu jajantawa amma itama a tsorace take kada ace za’a hada ta da wani cikin yan uwan namu dan dama ba’afi wata daya ba kawu aliyu yazo yace mu fitar da maza su aurar damu tunda shekarun mu sunkai amma rashin tsayayyun samari yasa muka kasa har su kuma suka dauki wannan matakin muna nan zaune mun kusa ko minti 20 saiga aunty ta fito da hijab tayi kofar gida a hankali kamar mai rada tace “ ina zuwa kada wanda ta fita cikin ku “ daga haka bata bamu damar tambayar taba dukda munason tambayar, gashi batajin dadin jikinta amma haka muka saka ido harta fice, ina mamakin halin nan na mahaifiyar mu wani lokacin haka zata tashi ta fita batare da munsan ina take zuwa ba kokuma me takeyi ba kuma tun muna tambaya har mun gaji dan kullum amsar daya ce “ naje nasha iska ne ina bukatar keben cewa “ wannan shine amsar ta koda yaushe kuma bamu taba bin bayan taba dan mun yadda da auntyn mu bataza aikata abu marar kyau ba. -Ina aunty zataje? -wata irin kaddara ce take bibiyar rayuwar ahalin? TAWA RAYUWAR By maryama Page 3 #villain #pain Tana fita ta mika hanya da sauri har tana tuntube ta bayan layinsu tabi tayi kwana daga nan zuwa wata primary ba nisa anan ta rabe jikin wata bishiya mai duhu dukda tana jin jiki amma yau ji take gara ayi ta takare tsakanin ta dashi, dan bazata yadda ba ya dasa mata ciwo kuma yabi ya’yanta sunma ya kuntata musu ba, cikin duhun ta fara jin takun sa na izza da zalumci Hannunta na karkarwa saboda ciwon zuciyarta tasa ta shafe hawayen ta masu dumi kafin tayi magana taji yace” Auntyn yara kenan dama nasan zaki neme ni “ dukda halin da take ciki bai hana murmushi bayyana a fuskarta ba amma bana farinciki ba saidai akasin hakan kafin tace “nasan bazaka taba hada auren Farouk da najmah dan allah ba saidai dan wata manufarka ,zuwa nan badan in amsa bukatar kaba nazo saidan inji menene manufarka a game da ya’ta?” Murmushi kawu hafiz yayi kafin ya shafa gemunsa wanda baya rabuwa da gyara kafin yace “kin canka daidai kuwa akwai manufar danake son cimma kuma naga hakan bazai yiyuba sai idan na kara kaimi gurin kuntata miki sannan zan cinma manufata, duk cikin ya’yan ki naga babu wadda kike tsananin so sama da kowa kamar najmah kuma idan hasashena gaskiya ne babu wadda Farouk ya tsana a duniya sama da najmah badan kuma tayi masa komai ba hakan yasa nayi amfani da wannan damar wajen ganin na kaiki kasa “ ya karasa maganar yana yin kasa da hannunsa kafin yace “shiiii tamkar saukar jirgin sama nakeso in ganki nusaiba nayi alkawari na kara bazan taba barin ki kishaki iska mai dadi ba badai a wannan duniyar ba saidai wata idan akwai ta, saina karasa tarwatsa guntun farincikin ki dana ya’yanki, nine nan na kaiwa kaka zancen hadin aure dukda nasan zulfa (mommy) har sauran yarana basu kaunar ku, nasan bazaki iya kallon ana azabtar da yar ki ba a gidan miji hakan zaisa dole ki…..” kukan data fashe dashine ya sanya bai karasa maganar saba kafin yayi murmushi na tsantsan mugunta yace “ ki adana kukanki zai miki amfani a gaba “ tana kukan ta duka kan gwuiyoyinta kafin ta dago idanunta tana kallonsa sosai hasken farin watan ya haske mata shi har lokacin tana kallon tarin manufofi a cikin kwayar idanunsa “dan allah kayi hakuri hafiz na roke ka for the first time a rayuwata su najmah ya’yan kane dan allah kada kasa rayuwar su a hatsari wallahi babu san komai ba face maraici da yake dawainiya dasu, kada ka manta allah yana kallon mu minene ribarka idan ka zalumce mu bayan kasan ni bansan abinda kake magana akansa ba sau nawa zan fada maka kafin mutuwar Amin bai bani wata jika ba! Bayan haka ni na fada maka bazan iya auren mutum irin kaba amma miyasa kake duk wannan ?” A fusace yace “kada ki fadamin maganar banza nusaiba banzo nan dan ki roke ni ba, ko kimin wa’azi ba nazo ne inji inda kika kai wannan jikar yanxu shine burina auren ki kuma aina fadamiki na fasa koda kuwa kin amince amma fa dole zaki biya bashin abinda kika dauka, ” Girgiza kai take maganar ma neman gagarar ta take wato shi bazai gane ba kenan duk yadda take kokarin nuna masa hanya amma baya gani tun bayan mutuwar mijinta yake nemanta saita bashi jikar da amin ya bata kafin ya rasu ita kuma a iya tunaninta bai taba bata wani abu na sirri ba da dan uwansa yake fafutikar nema kusan shekara goma sha biyu kuma ta fahimtar dashi amma kamar mai kwakwalwar kifi dayaga ta nace ita batasan zancen wata jika ba shine fa yace to zai aure ta dukdan ya samu cikar burinshi akan abinda ita bata sani bama wato jikar da yake cewa kaninsa ya bata a ranar da zai mutu , ita kuma tace bata amince ba dan mugun mutumne a boye hakan yasa ya fara musguna mata tun karfinsa ko tausayinsu bayaji har yayi sanadin ciwon zuciyar ta, yaran tama ya hana suyi karatu bayan secondary da suka gama, a cikin ruwan sanyi yake gallaza mata amma bata taba bari ya’yanta sun sani ba kuma yana mata barazanar idan ta fada sai ya kashe ya’yanta saiya sanya an musu yankan rago hakan yasa taja baki ta tsuke, ko sana’a ta kafa saiyaga bayanta ta hanyar turawa a kwashe duk abin sana’ar ayi musu kaca kaca da guri sosai take shan wahala a rayuwar ta gashi ba halin komawa niger tunda dama marainiya ce saidai yan uwa idan kuma ta tafi wa zata barwa ya’yanta mata? Idan ta tafi dasu cen niger sun fimu tsadar rayuwa wannan ne yasa ta zauna ta rungumi ya’yanta duk abinda zai faru sai dai ya faru amma bazata iya aurensa ba maganar jika kuwa batasan da ita ba. “Allah yana tare da ya’ya na “ ta amsa masa, kafeta yayi da ido yana kallo na tsayin mintuna kafin yace “ shikenan mu zuba mu gani kada kiyi tunanin zan gyale anisa da islam suma zan waiwaye su “ kuka ta fashe dashi na tausayin kansu kafin tace “ kayi hakuri hafiz dan allah kada ka lalata rayuwar ya’yan zumun ka “ “Kinyi kuskure nusaiba amma kada ki damu lokaci yayi dazan nuna miki ba’a wasa da maciji ki tashi kike gida sannan ki rike jikar banaso amma tabbas zakiyi kukan da ko mutuwar iyayenki da mijinki bakiyi ba “ sosai take kuka a durkushe a gabansa amma ko digon tausayi bata bashi ba tun yana mugun Kwadayin abin da ciki yanzu har yaji bayama kaunar abun saidai seya koya mata hankali nakin basa da tayi “go nusaiba “ ya sake fada yana murmushi jin yadda abubuwa suke tafiya yadda yake so “I’m sorr…..” ta fada cike da yanayin dake nuna tsantsan gajiya shekara da shekaru , hannu tasa ta dafe zuciyar ta dake mata azababban ciwo tamkar ta faso kirji ta fito “dan allah ka dakatar da auren nan farouk baya son najmah and najmah rauni gareta fiye da sauran yan uwanta “ ta kara fada tanajin tabbas da akwai jikar nan a gurinta zata iya bashi dukda batasan menene a ciki ba kodan ta tseratar da ya’yanta Amma ta rasa da wani kalamai zata fada masa ya yarda da ita,ta gwammaci ta taushi ya’yanta suje suyi zaman auren a haka dan tabbas komai zai wuce tayi imani da hakan, mikewa tayi ta juya batare data sake kallonsa ba tayi hanyar gida shima motarsa dake cen gefe ya shige ya ja da gudu. Zuwanta gida taga har maryam ta kawo anisa haka nan ta karfafa kanta tare da boye ciwonta tayi ta tausar mu tana mana nasiha da kuma hakuri akan rayuwar aure, A ranar idan nace nayi bacci to kuwa tabbas barawo ne bama ni kadai ba hatta amina da islam balle kuma aunty datafi kowa shiga wani hali , a cikin daren sau biyu tana aman jini ba tare da sanin mu ba. *** Abuja Gidane madaidaici shi ba kato bane ba kuma karami bane komai is safe yayi kyau sosai ,saurayi ne ya fito daga gidan kafin ya saka lock ya fito harabar gidan inda motarsa take, yana da tsayi kadan kuma bashi da jiki sosai kyakkyawa ne ajin farko black beauty ga saje daya kayata cute face dinshi Farouk kenan saurayi dan shekara 30 a duniya matashi mai ji da kansa, shadda ce a jikinsa ash data yi masa bala’in kyau budewa yayi ya shiga motar ya tada direct wajen aiki ya nufa, a wani private company ya samu aiki shekara uku baya kuma companyn suna samun ci gaba sosai shiyasa duk ma’aikatan su suna shanawa a ciki kuwa harda Farouk gashi dama da babban kwali ya shiga, bayan an tashi aiki yaji wayarsa tana ringing dauka yayi yaga kakane ke kiransa a hankali ya saki murmushi kafin ya daga da sallama yakai kunne bayan sun gaisa kaka yace yana son ganinsa this weekend idan babu aiki sosai nan ya amsa masa da tohm zaizo in shaa Allah daga haka sukayi sallama. *** A gidan kawu aliyu ma tarzoma umma ta tada akan auren hassan da amina har saida kawu aliyu yace idan bata amince ba kuwa saidai tabar masa gida wannan furicin ya sake tunzurq umma daukar alwashin wallahi zasu sani daga aminar har uwarta, suma yan uwan sosai sukaji ciwon abinda baban yayi musu akan su amina shidai hassan baice wa kowa komai ba dan idan tashine bashi da matsala zai rike amina sosai da amana amma ya zaiyi da ummansa? Abin yafi karfinsa gaskiya badan sun soba suka bar maganar ganin kashedin da baban ya sake musu. *** Washe gari sosai jikin aunty ya rikice ganin lamarin yafi karfinmu, yasa na ruga zuwa gidan doctor ina kuka amma yana wajen aiki take mama halima matarsa ta kirasa nan yace mu hayo napep mu iskeshi a asibiti nan take muka wuce bayan munje aka shiga da ita, doctor ne yayi kokari sosai a wajen mu kuma reception muka dawo anan muka zamna kowa da tunanin da yake cin ransa amina ce tayi hankalin cewa mu kira kawu hafiz koshi ko kawu aliyu mu sanar musu da halin da ake ciki, nisawa nayi kafin nace “ai bamu zo da waya ba “ islam ce ta saka hannu cikin aljihun ta na kaftan ta fiddo wata yar keypad ta miko min, amsa nayi ina jinjina kokari irin na islam da har ta samu damar dauko waya kafin na shiga list (call logs) nan a sama naci karo da number kawu hafiz kamar yadda mukayi saving mamakine karara ya bayya a fuskana ganin shine karshen kira kuma ga date nan jiya akayi waya dashi, nidai a iya sanina bamu kirasa ba amma haka kawai na fusge tunanin na danna kiransa. Bugu biyu yq daga da sallama nan muka gaisa nake fada masa rashin lafiyar aunty, cikin tashin hankali yace min gashi nan zuwa daga haka mukayi sallama, a bangaren sa bayan na kirasa murmushi yayi yana ayyana yanxu wasan ya fara tsakaninsa da nusaiba kafin ya nufi toilet mommy tana masa tambayar lafiya? Amma bai amsa taba nan yayi wanka ya fito yasa kaya shadda riga da wando sai babbar rigarsu kafin ya dora hula ita dai mommy kallon ikon allah take tama kasa magana ganin sai sauri yake “kada ki damu nusaiba ce ba lafiya tana asibiti ki sanar da yan gidan harda kaka ma duk ki kirasu a waya “ da to ta amsa masa daga haka yasa kai ya fice nan taja tsaki tace ba shegen da zan fadawa taje ta mutu mana waye keda asara. Sunfi awa biyu kafin doctor haruna ya fito fuskar shi dauke da damuwa mikewa mukayi mu uku kowa cikin tashin hankali take da kyar ya janyo nutsuwa ya rufawa kansa kafin yace “ da sauki zamu ce amma sai mun riketa anan bayan haka kuma……..” shiru yayi ya kasa karasawa sosai yake tausayin yaran ganin faman da suke sha koda yaushe daga wannan sai wannan gashi baya ganin wani sauki tare da ciwon mahaifiyar tasu saboda damuwa tayi mata katutu allah ne kawai zai tsallakar da ita a wannan stage din, yana mamakin yadda take sawa kanta damuwa da yawa yanxu gashi nan ciwonta yana stage na karshe har suna ganin akwai chance na zata iya kamuwa da shanyewar barin jiki tunda harda hawan jini, kuka na fashe dashi ina toshe bakina Dan gani nake kawai mutuwa aunty zatayi ta barmu itama amina kukan take, duk taurin zuciya irin na islam itama kukan ta sanya kafin tace “ kuma me baba doctor?” (Sunan da suke kiranshi) kafin ya bamu amsa mukaji sallamar kawu hafiz a bayan mu. Islam ce taje ta rungume shi ta kara sanya kuka nan shima bayyi magana ba ya dinga shafa bayanta alamun tayi hakuri sun jima a haka kafin yacewa doctor suje suyi magana, nan kara kwantar mana da hankali kafin ya wuce yabi bayan doctor haruna mudai anan mukayi cirko cirko ga yunwa harta fara cinmu dan rabonda muci wani abu tun jiya gurin meeting da la’asar su kuma islam muna gab da dawowa sunci, ganin dai zamu karawa kanmu illa yasa na mike dama akwai kudi gurinmu tun wanda kawu aliyu ya bamu saboda cefane yanxu da zamu fito na dauko wasu saboda napep da hidimar asibiti dukda nasan doctor bazai amshi komai ba, fitowa nayi harabar asibitin ina kalle kalle ko zan samu inda ake siyar da wani abu in siyo mana, ji nayi an tabo ni ta baya da sauri na juya ganin waye… ⛹️⛹️ TAWA RAYUWAR By maryama Page 4 Maryam ce dauke da basket na abinci fuskarta dauke da murmushi, ajiyar zuciya nasauke sai kuma na harareta nace “ harkin tsorata ni wallahi “ dariya tayi “ sarkin yan tsoro ina zuwa haka “ “Hmm abin breakfast zan samo mana wallahi “ nuna min basket din Maryam tayi tace “ gashi inji umma tace a kawo dan haka mu koma ciki, yawwa ya jikin aunty “ “ da sauki za’ace Alhamdu lillah “ “Allah ya kara sauki “ “ amin “ na amsa mata kafin muka shige ciki wajen su amina har lokacin kawu bai fito ba nan dai nace kawai muci abincin dan nasan kowa a takure yake matuka, maryam ce ta zuba mana soyayyan kosai ne da yaji sai taliya sphagetti sai kunu a jug nan muka danci dukda ba wani zagewa mukayi ba saboda damuwa, dan ma maryam tana karfafa mana gwuiwa anan ne nake bata labarin auren da za’ayi mana itama dayake babu abinda bata sani ba a game damu sosai ta tashi hankalinta gashi tasan family dinmu ba kaunar mu suke ba balle mu rabe su. “ maryam ban taba tunanin za’a dinga neman kai dani ba kodan suna ganin mahaifinmu baya raye shiyasa yanxu baga su yaya amira nan ba ga amra ga abida gasu hanifa da amida duk ga ya’yan su kawu ishaq suma amma a rasa wanda za’ace za’awa auren dole sai mu? Sam babu adalci gashi makarantar ma sun hanamu jonawa balle ma ko aikine ka samu ka rufawa naka asiri ga rashin lafiyan aunty da anisa ba karamin tayar min da hankali take ba dan allah da wanne zanji “ na karasa maganar da kuka, jikin maryam ne ya kara sanyi dan tabbas tasan muna cikin jarrabawa saidai komai mukaddari ne, kafadata ta dafa sai kuma tasanya hannu ta shafe kwallar daya cika idanunta na tausayin mu gashi tasan najmah macece mai rauni fiye da yan uwanta sai kuma tace “ kiyi hakuri najmah in shaa Allah komai zai daidaita kuma shima nasan yaya Farouk dole zai amshi auren nan kinga daga nan zaki fara samun rayuwa mai kyau tunda duk yan uwanshi suna tsoransa “ “ bazaki gane ba bawai amsar auren bane matsala a’a bansan wani zama zanyi ba a karkashinsa kinsan mata ma basu gabansa balle kuma ni “ “Haka ne amma addua maganin komai ce “ Daga haka mun jima muna maganar saiga kawu da doctor sun fito nan kawu yayi mana sallama ya fiddo kudi ya bamu masu yawa yace za’a kawo abinci da sauran su dan kwantar da ita za’ayi daga nan ya tafi, maryam kuma ta kara gaishe da mahaifin nata tayi mana sallama tace zata dawo zuwa anjima yanxu aikin gida zatayi idan ta koma, harta juya nace “ idan kin koma kice anisa ta rufe gida ta taho “ islam ce tace “ ita da batajin dadi ki barta kawai a gida “ “toh shikenan Maryam kawai ki barta “ na fada mata. A gida kuwa mommy kin sanar musu tayi karshe saida kawu hafiz ya koma ya kira kowa a waya ya fada musu, dan mama rakiya tsaki taja tana tabe baki tace “ ruwanta ya rage bakinciki ne takeyi zamu aurar da yaran nan saidai ta mutu kuwa “ iyayen maza ne kawai sukace gasu nan ba’a jima ba kuma duk suka zo harda wasu daga cikin ya’yansu kamar su yaya hassan , yaya Najeeb yaya muhammad da dai sauran yayan kawu latif kuma duk wanda yazo saiya ajje mana wani abu matan sune dai babu wadda tazo balle ya’yansu mata, daga haka kowa ya jajanta saiya fita , shima kaka yazo dubiyar dukda har yanxun babu wanda aka bari ya shiga dakin da take idan ka dauke kawu hafiz shima nauyin kuka ya yiwa doctor dan so ake ta samu hutu sosai amma tunda ya shiga ya kara dagula lamarin aunty. Bayan duk sun tafi ne yaya hassan ya samu damar yima amina magana cikin kunya ta tashi suka koma gefe dan a yanxu mu kanmu burinmu shine ta samu soyayyar shi tun yanxu koda anyi auren abubuwa zasu zo mata da sauki, a hankali ya dago idanunsa yana kare mata kallo abin tashin hankalin nan yasa tayi rama kadan amma fatar ta mai dan duhu tana nan smooth da ita gashi tana da maganai idanu kenan ga cute bakinta, hancinta ma yana da tsayi she’s totally black beauty tsayinta ma medium ne tana sanye da riga doguwa sai hijab irin mai lafewa a jiki din nan har kana iya hangen shape dinta da lafaffen cikinta ajiyar zuciya ya sauke yana dauke idanunsa daga kanta itama cikin kunya ta kauda kanta basuyi wani dogon magana ba dan babu wata shakuwa tsakanin su tunda su tamkar bare suke a dangi daga haka ya ciro kudi ya bata amma taki amsa nan ya nuna bacin rai dole ta amsa tayi godiya kafin ya tafi sai ta koma wajen yan uwanta. Haka dai ranar ta kare mana sukuku duk munyi laushi da doctor yaga dare yayi sai yace kawai su tafi gida abar ni nikadai, hakan kuwa akayi bayan sun tafi na samu nurse ta barni na shiga dakin inda naga mahaifiyar tamu gaba daya kamannin ta sun sauya tayi wani haske sosai ga rama data bayyana a jikinta idanunta a rufe suke hannunta akwai cannula wadda aka cire mata karin ruwa dazu jikij gadon na karasa na kafeta da ido ganin har tsawo ma takara hannu na kai

Chapter 2 of 10