ba take na zura hijab na fito da boket dina a hannu Anan fa na zage damtse nayita zarya ina ciko bokitin dukda yayi min nauyi amma ya zame min dole in daure saida naga randar gwauro na ta cika kafin na hakura zuwa sannan har an fara kiran la’asar sai kawai nayi alwala nayi sallah .
Garin kwaki na jika ina jin ciwon abinda yaya farouk yayi min haka dai badon ina sonshi ba naci mai da maggi ne kadai kayan girkin nawa yanxun sune na sakawa garin bayan na gama na fara tunanin inda zan samu pos a cikin account dina dan akwai ragowar kudin da yaya muhammad ya bani wanda naje nida islam na tura su a account din ashe kuwa zasu min rana ya zama dole in samu kayan miya da dan abinda baza’a rasa ba na girki in siyo saidai kuma in na tuna allah ya isar da yayi min sai inji wani iri, ji nayi fitar ta fita daga raina gara in bari idan yazo sai in nemi alfarma sai kawai na nemi guri nayi tagumi, nama yi tunanin hajar zata dawo amma naji shiru nasan innarta ba lallai ta barta ba dama.
Haka naci gaba da rayuwa a cikin wannan gidan cikin kadaici, kuntata, kewa, tare da zazzafan maraici ga shegen sauro da nake fama dashi kuma in dare yayi babu fitilar da zan haska balle inga haske inji dadi ko wutar nepa babu , duk abinda zanyi kafin magriba nakeyi dan idan duhu ya fara saidai in rufo kofar gidan in saka wani katon dutsi in tokare kofar sai in nufi toilet inyi fitsari in dauro alwala in shige daki da ruwana a cikin kofi koda zanji kishin ruwa, bana sake fitowa sai asuba a haka nayi kwana 5 cur cikin wannan yanayin marar misaltuwa kuma tun randa hajar ta tayani aiki bata sake zuwa ba dama naji a jikina innarta bazata barta ba dan daga gani itama cikin wahala take danma yarinyar bata da surutu ko kadan, shi kuwa yaya farouk bansa ka ran zai dawo ba saidai wani ikon na Allah ga bani da waya balle ko waya inyi inji yanda su aunty na suke haka nan nake danne zuciyata ina karbar TAWA KADDARAN koda nayi tunanin in tafi in koma kano sai wata zuciyar tace min “ kada ma ki fara me zaki fadawa su kaka ? Kice baya sonki ko kuma me? Bayan kinsan karshe kan aunty abin zai koma a dinga cewa ta kashe miki aure ga kuma itama ciwonta da bayason tashin hankali ko kadan tunda ciwon zuciyarta yana matakin karshe wanda abu kadan zai iyayin ajalinta “ idan ina wannan tunanin sai in fincike tunanin tafiya gida ince gara inyi hakuri in daure kodan farincikin mahaifiyata da yar uwata.
yauma kamar kullum na tashi nayi wanka na dora shinkafa wadda kullum dai itace daga ita sai gari, fara na dafa na saka mai da maggi na zauna na ci na koshi na wanke flat dina sauran abincin kuma a tukunya na barshi dan bani da cooler, kayan datti na na fiddo kala uku da sabulun daya sayomin bocket na dauko saidai ina duba robar ruwana naga ya kusa karewa dafe goshi nayi ina rumtse ido na tunowa da nayi da wahalar daukar ruwannan ga nisan dake tsakani na da rijiyar ai bansan sanda naji wasu hawaye sun fara min zarya ba.
Cikin bakinciki na wullar da boket din na fito tsakar gida na zauna ina kuka kawai ji nake rayuwar ta fara isata da wanne zanji dan allah , wani irin kaskanci ne wannan yaya farouk yakeso inyi gashi har yau banga ko keyar sa ba, kuka nasha sosai har saida kaina ya fara ciwo ganin dai babu sarki sai Allah yasa na hakura na tashi na koma inda nayi wurgi da boket dina na dauko na zura hijab na fito , fuskana tayi jawur saboda kuka, tafiya nakeyi cikin nutsuwa ta ina kare zafin rana da hannuna ganin ta dan fara zafi a haka harna karasa rijiyar ban wani iske mutane ba sosai dan haka bayan sannu da mukawa juna babu abinda ya kara hadamu na hau jan ruwa wanda ban tabayi ba a tarihin rayuwata ba sai yanxu da aure ya kawoni wajen nan, ina gama cikashi na dauko kayana dukda uban nauyin amma na daure na karaso dashi na sauye.
Haka nayi tayi har saida na cika roba ta sai kuma na dibo wani a botikin na taho anan ne nace bari in biya gidan innar hajar inji ko lafiya dan haka na ajje ruwana anan gefen hanya nayi knocking gidan cen saiga hajar ta bude wani murmushi muka sakarwa juna take naji damuwata kashi 60 ta tafi cikin murnar ganina tace “ aunty kece shigo “
“ a’a hajar wucewa zanyi nace kwana biyu banganki ba bari in biyo ko lafiya?”
“ lafiya lau muke nice dai kanwar ubanta bazan bari ta rabi wani ba, dan kada a hure mata kunne ehe “
Muka jiyo muryar innar daga bayan mu cikin sauri hajar ta matsa cen gefe tana sadda kai, kallo na namaido wajen innar na kirkiri murmushi na yafawa fuska ta nace “ ina yini inna ya gida “
“ ke nifa ba sunana inna ba gwaggo nake ehe in kin gama abinda ya kawo ki zaki iya tafiya “
Gyada kai nayi a zuciya ta nace “ another problem kenan wato kowa da tasa kaddarar “ a fili kuma nace “ zuwa nayi mu gaisa dama “
“To to na gode kwarai ai tunani na janye min yarinya zakiyi ki hure mata kunne kinsan yaran zamanin nan basu juri zuga ba “
“Haka ne shikenan bari in wuce sai anjima “ na fadi ina kallon hajar din da jikinta yayi sanyi matuka haka na juya inajin dama gwaggon ta bani ita in rike danaji dadi dan haka kawai nakejin kaunar yarinyar a raina.
Ruwana na dauka na tafi gida saidai ina zuwa shiga na hango wasu maza su ukku duk hankalinsu a kaina yake kuma daga gani irin marasa ji dinnan ne, haka kawai naji jikina yana bani ba alkhairi ba amma na daure na tura gidana ina addua, wanki na hau yi ina gamawa na shiga toilet na sake wanka na fito na saka riga da wando nayi sallar azahar, bayan na gama na kishingida take bacci ya dauke ni mai dadi nice ban tashi ba sai kusan rana zata fadi cikin sauri na zabura ganin ko la’asar banyi ba toilet na fada nayi alwala nayi sallah sannan na dauko tukunyar shinkafa ta na saka mai na ci dukda wani irin yanayi da nakeji a jikina marar dadi na fito na dauko ruwa a kofi na, daga nan na tafi kofar gida na saka dutsen nan babba na tokare kofar, in takaice muku shidai gidan ko sakata (kuba )babu , na tafi cikin dakin nayi sallah magrib na rufe kofar na koma gefen katifar nan wadda da ita da babu duk daya na zauna nayi tagumi ina tunanin ahali na wani irin kewa nakeji, ina bukatar koda dabba ce ta kasance dani amma banda wannan damar.
Wasu hawaye na goge duk iya tunani na banga abinda nayiwa yaya Farouk ba dazai saka min da haka ba, inama zai barni a wancen gidan koda a boys quarter ne tabbas da zan zauna kuma bazan fasa mishi biyayya ba da duk abinda yakeso, haka nayita kuka abin duniyar ya isheni saida na tabbatar lokacin sallah isha yayi kamin na tashi nayi bayan na gama na danyi tilawa ta alqur’ani sannan nayi bismillah na haye katifa ta ina lumshe idanuna da suka kara girma saboda ramar data fara bayyana a jikina, tunani na bai wuce ya zanyi in koma gidan yaya Farouk ba idan kuma bayason zamana acen to kawai zan koma kano komai zai faru ya faru , nasan mamana zata shiga damuwa amma gara ina kusa da ita akan inyita zama a wannan jejin.
A hankali naji kamar dirowar wani abu take kirjina ya buga ban kuma dawowa daidai ba na sakejin an diro ai bansan sanda na mike ba, gashi banda fitila again na karajin an diro haba tuni hawaye sunyi min sallama cikin rawar jiki na maqe a bayan kofar dakin gashi shima babu wani sakata haka nan nake rufewa jikina banda karkarwa babu abinda yakeyi addua kuwa duk wadda tazo bakina fadinta nakeyi cikin matsanancin tashin hankali, tafiya na faraji sai kuma magana kasa kasa saidai banajin me suke cewa.
***
Afiya a hotel ta kwana sai gabanin asuba ta dawo gida nan mai gadi ya bude mata ta shige dama sun saba haka dan suna biyanshi ita da amira harda amra mai zuwa club, cikin sanda ta shiga cikin gidan ta kofar baya ta sulale ta nufi dakin su saidai a mamakinta amira ce zaune a saman sallaya da hijab jikinta tana lazimi wani kallo amira tabi afiya dashi sai kuma taci gaba da abinda takeyi batare datayi magana ba, cikin mamaki afiya tace “ wai kina nufin kin musulumta “
Cikin harzuka amira tace “ dama ance miki ni kafura ce afiya? Ko ke kika fiddani daga addinin “
Dariyar rainin wayo afiya tayi sai kuma ta zage zip ta fiddo dollars ta hau lala su sannan tace “ hmm da alama shaikh din dayayi miki wa’azi babu kamarsa a duniya, nifa kina bani tsoro amira naga dai ko magajiyar shedanu bata kaiki shedanci ba a harkar bariki ciki ma kusan sau 3 kina zubarwa amma lokaci daya harkin hakura kin dena komai “
Wasu hawayen takaici suka ciko idanun amira amma tayi namijin kokari ta maidasu ta kalli afiya tayi murmushi mai dauke da manufofi tace “ ai nawa mai sauki ne tunda banda cuta kuma yanxu na tuba na koma ga allah ina alfahari da tuba na saboda ba irin na muzuru bane , shawara ta guda daya a gareki shine ki hakura haka nan kema ki tuba ga allah koda zaki samu rahmar sa “
Dariyar rainin wayo afiya tayi tace “ sannu ustaziyya thank you for the advice amma kinga shan magani na da neman kudina yamin rana tunda babu mai taba cewa ina dauke da cutar kanjamau “ daga haka ta shige toilet tanajin zafin maida mata magana da amira tayi ita kuma amira ta girgiza kai taci gaba da lazimi abinta.
Tun shigowar afiya kawu hafiz daya tashi zuwa toilet ya hangota sosai kanshi ya kulle game da lamarin amma dai ya bari zuwa gobe zai tuntube ta yaji inda take zuwa dan abin ya daure kanshi da yawa mamakin yarinyar ya kamashi
TAWA RAYUWAR
By maryama
Page 17
***
Dakin kayan abinci na suka shiga ashe harda yar wayarsu nokia sukaga bana ciki sai suka taho nawa dakin ko kunya basu jiba kuma zuwa lokacin na tabbatar ko taran dare batayi ba kawai abin unguwar shiru ne shiyasa, ji nayi sun turo kofar take hasashena ya tabbata dan nasan dama kilan yan fashi ne ko kidnappers wani kuka na sanya mai matukar karfi ina fadin “ kuyi hakuri karku kasheni dan allah wayyo aunty na …” da sauri wani cikinsu yazo ya rufe bakina da hannun sa suma sauran biyun suka fado dakin babbansu yace “ rufe mana baki ko mu fiddomiki ya’yan hanji yanxu “ cikin tsawa ya karasa maganar hakan yasa nayi shiru ina zare idanu kafin wanda ya fara shigowa yace “ gayu mu kwashe wannan akwatinan kawai mu kara gaba sannan inkina da kudi ki ma fiddo mana batare da mun taba lafiyar jikin kiba “
“ wlh banda komai bayan akwatinan nan “ na fada ina karkarwa, karamin su yaja tsaki ya fara daukar trollys din da aka kawo min lefe yana fitarwa dayan ma yana tayasa daidai da akwatina mai sutura ta saida suka dauke atakaice basu barni da komai ba sai kayan dake jikina da hijabin da nake lulluba dashi sai wata tsohuwar jikata tun ta islamiyya itama harsun dauka babban yace haba gayu wannan me zamuyi da ita kuma, hakan yasa suka yasar ta anan kasa, kafin suka juya suka fita, cikin wani irin yanayi na saukar da numfashi na da tun zuwansu yake barazanar daukewa a raina ina fadin alhamdu lillah tunda sata ce ma ta kawo su ba wani abu ba saidai ko minti biyar ba’ayi ba naji dawowar su, nan da nan na mike ina fadin “ kun rabani da komai nawa dan allah ku kyaleni haka ku rufamin asiri dan allah “ dariya sukayi dayan yace “ haka kyakkyawa ai barinki haka bai kamace muba ki bari cikin laluma muyi abinda zamuyi kawai “ jin manufarsu yasa wani irin bakin tashin hankali ya kara ziyarta ta nan fa muka fara kokowa amma ina karfin ba daya ba take naji sun fara kokarin kaini kasa wani mummunan tashin hankali ya bugi kwakwalwa ta tabbas inda za’a yankani a sannan baza’a samu jini ba, girgiza musu kai na fara cikin yanayin fitar hankali ganin suna kokarin rabani da kayana da karfi na cije hannun wanda ya rufe bakina na saki kara cikin saddakar wa tabbas tawa ta kare shikenan ni kuma irin tawa jarrabawar kenan, da aurena amma wasune zasu sanni ba miji na ba wani mari wanda na ciza ya kaimun amma cikin naci na dunga kai musu naushi cikin jin zafi babban su ya fara dukana irin dukan da akewa sa’a, take hawayena suka kafe gashi sunyi nasarar cire rigar dake jikina saidai jin karar tsayuwar mota yasa suka sakeni suka saurara dan suji wanene, karar turo kofar da akayi yasa a guje suka fito daga dakin saidai ganin babu yadda zasu iya hayawa yasa suka tsaya daga dan lungun soron, ana shigowa suka bugesa da sauri suka fita da gudun bala’i cikin tashin hankali yake bin kattin mazan da suka bigeshi suka fita a guje da sauri ya mike yayi cikin gidan yana haska waya a kwance ya iske ni a daki saman katifa jikana babu riga sai bra da dogon wando allah yasa yau banyi gangancin cire wa ba dayake wasu lokutan gaskiya ina kwana da ita musamman idan ba mai karfe bace, kuka na fashe dashi na tashi na nufesa ina fadin “ yaya farouk “ cikin muryar rauni matuka wani irin mari ya fesa min ya kuma kaimun wani jikinsa yana tsuma yace “ dama abinda kike aikatawa kenan a wannan gurin ma “ a razane na dago dukda marin dana sha hancina ya fashe yana jini na fara girgiza kai dan na kasa magana ma wani marin ya kuma kaimin ya saka kafa ya tade ni yahau jibga tamkar ya samu dabba kuka da ihu rantsuwa babu wanda banyi ba amma bai ko saurare ni ba , ga dukan dana sha a hannun azzaluman mutanen nan hawaye naga yana fitarwa yana nuna ni da yatsa amma ya kasa magana, jikina banda azabar karkarwa baya min komai bansan taya zan fahimtar dashi ba bansan waye zai fiddani ba a wannan sarkakiyar saidai tabbas nasan allah shine shaidata cikin mugun tsanata yace “ na tsaneki wallahi kuma allah saiya min sakayya a cikin zalumcin da kikamin kika kawomin kattin maza har gida kina a matsayin matar aure na banyafe miki ba allah ya isa tsakani na dake “ daga nan ya juya zai fita cikin daskarar da nayi tamkar kankara naji karan fitar sa take a haukace na rufa masa baya, nama kasa magana burina bai wuce ya fahimce ni ba burina bai wuce ya gane bani da laifi ba meyasa KADDARA zata min haka rigar sa na fusga cikin tashin hankali wanda baki bai isa ya fadi ba, hankada ni yayi take na bugu da bango amma bandamu da jinin da goshina yake yiba balle kuma in damu da karan danaji a cikin hannu na ba burina bai wuce mijina ya fahimce ni ba harya shiga mota na kama murfin motar ko fa riga babu a jikina danma dare ne kuma babu haske ko kadan unguwar kuka nakeyi da raina amma bakina ya kasa furta kalma ko guda, bansan me zai sanar da iyaye naba kuma bansan wani hali aunty na zata shiga ba cikin zafin nama ya fito ya kama kaina ya buga da jikin motar cikin tsananin azaba na sulale anan batare dana san inda kaina yake ba, kafata ya kama ya janyo ni zuwa soron gidan ya yasar dani ya juya ya tafi a hankali ya juya ya kalli kwalin indomien dayayi niyyar kawo min ganin cutarwar tayi yawa idan ya barni dasu gari ashe tsautsayi ne zai kawo sa yaganewa kansa abinda yafi karfin idanunsa wai najmah ce harda maza uku a gida wani irin dukan sitiyari yayi yana jin zafin zuciyar sa yana karuwa , take ya kira abba a waya cewar ya kama ni da maza uku a cikin gidansa shi saki na kawai zaiyi baiga amfanin auren mu ba bayan nidin mazinaciya ce sosai abba ya saki wani kayataccen murmushi na samun nasara amma bai yadda farouk yaji ba yace “ a’a farouk ban amince ka sauwakewa najma auren nan ba kawai ka shirya kazo kano zamuyi magana “ cikin mamaki farouk da idanunsa sukayi ja yace “ haba abba wai kaji me nace kuwa “
“Naji mana kazo inason ganinka ba maganar waya bace”cikin takaici Farouk yace to shikenan allah ya kaimu”
Azabar data ratsa kwakwalwata ce da zafin hasken rana ya dalle min fuskana dake jike da busasshen jini yasa na farka, a hankali na bude idanu na da suka min nauyi matuka akan kasar da nake kai na sauke idanuna sai kuma na fara yawo dashi inason tuno inda nake kuma meya faru dani, tabbas a soro nake kuma ko riga babu a jikina take abinda ya faru jiya da dare ya fara dawo min wani azababben kuka na fashe dashi cikin kunar zuciya saidai sam muryata bata fita saboda tsabar dasashewa yunkurin tashi nayi saidai jin wani ciwo da azaba mai radadi yasa na kwalla kara ina kiran sunan Allah cikin razani na maida dubana ga hannu na na hagu wanda yayi suntum ya kumbura wani firgita na kumayi gashi inajin kamar ba’a jiki naba, kuka na rushe dashi dukkan jikina yana tsananin karkarwa , nafi minti goma a wannan halin cikin tsananin bukatar taimakon wani amma babu kowa gareni cikin juriya da dauriya na fara kokarin mikewa amma kafafuna suka ki bani hadin kai dan su kansu basu iya rikeni, dayan hannu na marar ciwo ko kuma ince karaya dan da alamu itace shine na kai saman kai na dafe jin yana barazanar rabewa biyu , cikin jarumta da bansan ina da ita ba nayi wani nishi da karfi ina fincike jikina na mike tsaye da sunan allah a bakina kafin na farabin bango har zuwa cikin dakina a saman katifa na zauna na jingina inajin bugun zuciyata yana karuwa ga ciwo da takemin.
Ganin zaman ba zai yiyuba gashi banyi sallah ba ga ciwo aduk illahirin jikina yasa na sake mikewa a karo na biyu inajin wani mugun zazzabi yana nukurkusa ta, dan kwali na dake yashe a kasa. na dauka na yafa shi a kirjina na fito ina dingishi jin kafar ma ciwo takemin ba karami ba ga kullutu da nake jinsa a goshina inda yaya farouk ya bugani da jikin motarsa ga radadin dukan da kartin maza suka min ,ruwa na diba na nemi guri na zauna na fara gabatar da alwala harda inda jini ya bata min saida na saka ruwa na dauraye bayan na gama na tashi na nufi daki nayi sallah sannan na kai kuka na ga mahaliccin mu akan ya fitar dani daga wannan kullin, dan bansan ya zan fara taryan kawu’s dina da wannan maganar ba na tabbatar zuwa yanxu ya shaida musu abinda nayi gashi bansan wani hali aunty na zata shiga ba , wani kuka na fashe dashi mai radadi amma babu hawaye saidai zafi da ido na suke min tamkar yaji sai kuma zuciyata da takemin ciwo ga bugawarta ya sauya matuka , ya zanyi yanxu? Na tambayi zuciyata
***
“ ki fadamin meke fitar dake waje a irin wannan lokacin afiyah “ kawu hafiz ya kara maimata mata tambayar still fuskar sa a murtike ganin zata raina masa wayo , shiru tayi ta rasa yadda zata ce masa ganin karyar data shirga mishi baisa ya yarda da ita ba ganin dai bata da gaskiya kuma hasashensa yana neman tabbata sai kawai yayi murmushi ya taso daga kujeran da yake kai a cikin garden din yazo har inda take a kasa saman carpet ya zauna kusa da ita gab har saida gabanta ya fadi tadan ja baya cikin tsoro tana kallon abban.
Wani murmushin ya kuma yi yakai hannun sa saman nata yana kallon reaction dinta dukda ita yar duniya ce amma hakan saida ya razana ta dan wannan abba ne mijin yar mahaifiyarta ba kamar sauran tantiran da suka saba hulda da suba “ ki saki jikinki nima ina irin harkan da kikeyi kinji afiyah ta “ sororo tayi cikin mamaki zatayi magana ya hana hakan ta hanyar sanya dayan hannunsa saman bakinta yana wani zagaya wa ita jinta take tamkar a mafarki, “zan baki makudan kudade da zakiyi ta jin dadinki dasu amma fa daga yau bazaki sake fita ba saidai idan wajena zaki zo ni dinnan idan har kika rikeni bazaki nemi abu ki rasa ba “ gyada kai tayi tana kallon hannun su dake waje daya yana wasa da yatsunta daga nan ya mike yana cewa “ zan fita zuwa office amma karfe 12 ki sameni a star hotel daki mai number 21 koma ki kirani kawai saidai banason jira “ yana kaiwa nan ya fita ya barta da dumbin mamakin mutumin amma ba laifi zata ci abinda taci itama ta huta da zarya hotel a boye, tashi tayi tana tsallen murna ganin ga dama tazo mata tabbas zata dama amma a gefe daya tana tsoron maman ta ko mommy su sani more especially mommy dan tabbas saita kasheta wallahi saboda idan bata manta ba abban ya dade zai kara aure amma saita hana ta hanyar sihiri saidai kuma abinda mommyn bata sani ba shi abban bin mata a gurinsa ba komai bane, allah kadai yasan da iya mata nawa yake tare a waje.
***
TAWA RAYUWAR
By maryama
Page 18
Babban dakin da mukeyin taron family meeting ne yake dauke da yayyan mahaifina da kuma kaka na sai aunty wadda kaka ya tirsasa aka daukota a mota aka kawo ta gurin dukdan ayi komai akan idonta kuma taji da kunnenta abinda yar’ta ta aikata kowa ka kalla cikin tsananin damuwa yake banda kawu hafiz dake sakin guntun murmushi idan suka hada ido da aunty wadda take saman keken guragu, tundaga jan da fatar ta tayi zakasan ba karamin mummunan tashin hankali take ciki ba saidai juriya da tawakkali da kuma hakura da duniya baki daya yasa ta iya nutsuwa tana sauraron abinda kaka yake fadi cikin fushi
“Hakika nayi allah wadai da abinda yarki tayi sannan inaso ki sani na cire fadimatu daga cikin zuri’a ta “ a hankali aunty ta runtse jajayen idanunta kafin kaka yaci gaba da cewa “ kuma na hana farouk ya sauwake mata saboda inma ya rabu da ita bazan barta ta dawo gidana ba ko cikin zuri’a taba balle ta lalata rayuwar yar uwarta, dan haka dole ta zauna kuma duk hukuncin da farouk zai dauka wajen hukunta ta yaje ya dauka hakan shine daidai sannan ku kuma a cikin ku duk wanda yamin maganar hukuncin nan bayyi ba to Allah ya isa banyafe ba “ ya karasa maganar yana kallan kallon su abba dasu kawu aliyu sosai karshen jawabinsa ya girgiza su tabbas dole kowa ransa ya baci saboda abinda najma tayi amma hukuncin yayi tsauri dan hannun bazai rube ka yanke ka yarba.
Aunty ce da hawaye suka gangaro mata ta lumshe idanunta a karo na babu adadi kafin cikin jirgaggen bakinta ta fara maganar da bata fita sosai saboda lalurar ta tace “kayi hakuyi amma bazan iya yabuwa da ya’ta ba komai ta jama nan duniya ina canta dan haka jan dauke cu ita da ishlam in koma nijar “ wani murmushi kaka yayi kafin