Share this page
yace “idan har zakiyi jayyaya da hukuncin dana yanke to kuwa zan karbi islam in baiwa hafiz ko aliyu rikonta sannan keda ita har abada na yanke alakarku kuma zan bawa farouk ita a matsayin najmah ita kuma najma saiki tafi da ita kinga kin rabamu da qaya “ cikin tashin hankali hawaye suke zuba a idanunta jin abinda kaka yake fadi saidai sam bazata iya bari rayuwar islam ta tarwatse ba kamar yadda suka tarwatsa mata rayuwar najma dole zata karbi abinda kaka ya fadi saidai tasan tabbas yarta bata aikata wannan mummunan abin da suke magana akaiba tasan wacece najmah tasan abinda zata iya aikatawa, kawai ita dai familyn Amin sun cuceta sun cuci zuri’ar ta ga karfin iko da suke nunawa akan ya’yanta ko ta ina sun mata illa ba kamar hafiz da duk duniya bata da makiyi irinsa. “Shirun ki yana nuna kin hakura da tafiya kenan? Cewar kaka saidai bata bashi amsa ba , kawu latif kawu ishaq da kawu aliyu ko wanne baiji dadin hukuncin baba ba Amma jin Allah ya isar da yayi yasa duk suka sauke kawunan su kowa yanajin rashin kyautawa akan irin wannan tsatstsauran hukuncin saidai babu yadda suka iya, daga haka kaka yace kowa ya tashi ya tafi hukuncinsa babu fashi cikin sanyin jiki suka fara mikewa kafin kawu hafiz yayiwa anna magana da take cen jikin flowers a zaune itada islam danko shiga gidan kawu hafiz din basuyi ba bakinsu nan cikin gate, amma amira tazo sun gaisa tayi tayi dasu akan su karasa ciki suka kiya karshe ta hakura dama fita zatayi dan haka ta musu sallama ta fita…magana yayi musu akan suzo su dauki aunty zai maidasu gida. *** Ranar dai ko abinci ban iya girkawa ba danba tashi nake ba balle kuma halin da nake ciki duk mai imani zai tausaya min inya ganni zazzabin daya rufeni ya haddasa min karkarwar jiki tamkar ana kakkaryamin kashina haka nakeji nasan izuwa yanxu labari na ya bazu a cikin dangina dan nasan farouk bazai taba rufamin asiriba, saidai wannan bashine a gabana ba burina kada aunty na taji balle ciwonta ya tashi yayi sanadinta idan hakan ta faru banajin zan iya yafewa kaina dan gara ka ni in mutu inbar aunty na ko addua zatamin amma bansan ya zanyi ba idan itace ta mutu ta barni ba, sallah kadai ke tada ni inyi in koma yaloliyar katifa ta in kwanta a cikin wannan halin na kwana saidai sam babu tsoron komai a raina a yanxu, banajin tsoron dawowar mutanen nan dan zuciya ta tabushe fatana ma bai wuce su dawo ince su kashe ni ba in huta, sai kuma nayi istigfar ganin ina neman kauce hanya tunda kaddara ce bata wuce kan kowa ba( wani lokacin muna kuskure gaskiya sai kaji mutum ba damar allah ya jarrabesa sai kaga ya kasa amsan jarrabaawar bayan Allah da kansa a cikin littafinsa Alqur’ani mai girma yace layukallifullahu nafsan illah wust’aha Allah baya dorawa mutum abinda yasan bazai dauka ba Dan haka mu kiyaye mu dinga hakuri da juriya akan kowace kaddara). Haka na wani gari cikin galabaita danko idanuna na kasa budewa ga hannuna dake matukar zogi a kumbure sallah ma ta asuba sai a daddafe nayi da kyar anan zaune daga nan dai bansake sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi na a ganni kwance a tsakar gida kan sallaya gefena hajar ce duk damuwa ta mamaye fuskar ta sai kuma wani dattijo da yake nan saitin kaina wanda ba wani tsoho bane kawai babu ce ta saka shi yamutsewa da alama. Cikin hazari nayi kokarin tashi amma ya dakatar dani yana fadin “ sannu baiwar Allah ya jikan naki kadaki tsorata ni mai magani ne na gargajiya acen nake daga gabashin ku wannan yarinyar yayi maganar yana nuna hajar yaci gaba da cewa itace tazo inda nake tana kuka tace mun inzo inga halinda da auntyn ta take ciki to da banyi niyyar shigowa ba saidai ganin kukan nata da kuma yadda take wassafa min ta ganki kamar wadda tayi hatsari yasa nace bari in shigo shine fa na iske ki a wannan halin amma yanxu cikin ikon Allah na gyara miki targaden dake hannun ki na kuma shafa miki magani a jikin ciwon goshinki Alhamdu lillah ya kikeji yanxu “ ya kare maganar da murmushi, sai sannan na sauke idanuna daga kallonsa na juya kaina ina kallon hajar dake tsaye itama tanajin dadin farkawata a hankali na sakin mata murmushi ina kara jin sonta a raina kafin kuma na yamutsa fuska jin zafin har yanxu yana ratsani saidai ba kamar jiya ba cikin jinjina kai nacewa mutumin “ Alhamdu lillah da sauki sosai Na gode sosai malam Allah ya saka maka da alkhairi “ da amin suka amsa min kafin nacewa hajar “na gode miki yar uwata “ murmushi tayi tana sakin ajiyar zuciya haka mukayi jigum dukda ina mamakin ya akayi hajar ta taimaka min bayan ni kadaice a gidan kamar ta sanin abinda ke raina tace min “ gwaggo ce ta aikeni dibar ruwa abin nima kwana biyu ban fito ba shine nace bari in zagaya ki in gaisheki saidai nazo nayita sallama shiru kuma naga dai gidan a bude balle ince ko bakinan sai kuma nadan jira inji ko zaki amsa amma shiru sai kawai nace bari in dubaki ko lafiya shine ina shigowa na ganki a yashe a kasa kofar daki ga hannunki a kumbure ga kamannin ki kamar sun sauya min shine na dinga kiranki cikin kuka amma shiru gashi naga alamar kamar dai barayine suka shigo danko kayanki ban gani ba wannan ne yasa na ruga zuwa gidan malam na taho dashi dan nasan tabbas ba lafiya ba “ malam ne ya amshe zancen da cewa “Allah dai ya miki albarka hajar kinyi kokari yanxu ke saiki dan watsa ruwa ga magunguna na hausa kowanne nayiwa hajar bayani sai ki dinga sha kina shafawa Kuma ki nemi abinci kici dan galabaitar nan hada yunwa Allah ya kara sauki bari inje “ nan na sake masa godiya cikin jin dadi yacemun babu komai bayan kwana biyu hajar ta rakoni ya kara duba hannun daga haka ya sabi jakarsa kamar ta wanzamai ya fita. Bayan fitar sa hajar ta tashi ta kunna mangal ta doramin abinci kamar dai yadda kullum baya wuce shinkafa haka ta dora ta dafa min nidai har sannan ina kwance dan jikina babu karfi bayan ta gama ne ta kamani na tashi ta zubamin na fara ci a hankali da lafiyayyen hannuna itama nace ta zuba taci, bayan mun gama nasha ruwa ta bani maganin da zansha badan naso ba nasha dan banason magani daga nan ta doramin ruwan wanka na shiga nayi izuwa lokacin tuni anyi la’asar bayan na fito na dauro alwala nazo nayi sallolin da ake bina a zaune daga nan nace hajar tace gida kada a nemeta dan nasan zan iya ja mata a gurin gwaggo haka badan taso ba ta tafi gida, ni kuma na tashi na dauki sallayar da nake kai na shige dakin da nake kwana saidai a bakin kofa na tsaya ina karewa ko ina kallo duk wasu kayana da komai nawa babu a dakin daga ledan dakin sai katifa ta sai kuma tsohuwar jikar islamiyya ta, a hankali na fara takawa harna isa inda take ainahinta kalar yellow ce amma tsabar dadewa da tayi yasa har wani fari fari take ni sai yanxu ma na tuna ashe da ATM dina da katin da yaya md ya bani wanda ke dauke da number wayar sa suna ciki, hannu nasa na dauko ta kafin na zage zip dinta da yake daga sama, littattafaina ne guda 2 a ciki na islamiyya wanda tuni muka gama haddace su arba’una hadith ne dana al’arabiyya wanda yake dauke da haruffan yaran larabci sai kuma wata yar madaidaiciyar bakar jika sai atm dina da card din yaya md, cikin nutsuwa na fiddo jakar nan ina juyata a hannu na mai lafiya tabbas tana da nauyi kamar wani dutse ne a ciki mamaki ya kamani ina tunanin me ya kawo ta cikin kayana, samun guri nayi na zauna ina ta tunani a raina saidai tuna wasu shekaru da suka shude da nayi yasa na kara zubawa jakar idanuna cikin wani irin yanayi a fili nace “ ai jakar nan babane yayi ajiyar ta cikin ta islamiyya ta a ranar da zai rasu “ cikin zurfin tunani na fara tuna shekarun baya a ranar da babana zai bar duniya ranar juma’a da misalin karfe 10 na safiya ranar bamuje makarantar boko ba saboda ana good friday esther monday……. Wace irin jakace wannan kuma minene a ciki? Yaya rayuwar najmah zai kasance? Kaka yayi daidai kuwa hukuncin daya yanke? TAWA RAYUWAR By maryama 19 *** Tun bayan dawowarsu gida ciwon aunty ya kuma tashi wanda yayi sanadin islam ta kira baba doctor , bayan yazo yaga jikin nata ya kara rikicewa dan haka yace kawai su tafi asibiti zamansu a gida zai iyayin sanadinta cikin kidimewa suka wuce asibitin tare nan aka shiga da aunty emergency dan wani irin jan numfashi take wanda saida aka saka mata oxygen kafin aka mata alluran bacci da kyar bayan tasha wahala bacci ya dauketa ganin haka yasa baba doctor shida abokin aikinsa suka fito daga dakin kowanne yana sharce gumin da yake goshinsa islam ce dake kuka har sannan ta nufesa tana fadin “ baba doctor ya jikin nata zan iya shiga in ganta? Dan allah ya take “ ta karasa maganar cikin sanya kuka, wata tsawa baba doctor yayi mata wadda tunda suke bai taba musu ba yace “ idan karshenta kukeson gani ai shikenan saiku cigaba da bata mata rai saidai ku sani a yanayin ciwonta ni kaina yafi karfina amma har yanxu bazaku iyayin abinda zai dinga kwantar da hankalin taba kullum jininta a sama yake ban maga amfanin zaman ku kusa da ita ba “ ya karasa maganar yana kallon Anna da islam da sukayi mutuwar tsaye jin maganganunsa, A hankali islam ta sulale ta zauna dabas a kasa tana kiran sunayen Allah tabbas idan akace babu aunty yau ina zataje taji dadi menene yake daga hankalin mahaifiyar tasu? Ta tambayi zuciyarta saidai bata da amsa Sam, cikin dacin rai baba doctor ya juya zai tafi office dinsa anna tayi saurin bin bayansa tana fadin “ Tabbas yayan mijinta shine matsalarta “cikin wani irin yanayi baba doctor ya juyo ya zubawa anna ido wadda ita kanta hawayene cike a kwarmin idanunta najin tausayin aunty, saidai lokaci yayi da zatayi jihadi ta hanyar binciko shaidanun ayyukan shi danta nunawa duniya wanene shi, gabas da yamma kudu da arewa baba doctor ya kalle ya tabbatar da cewar babu wanda hankalinsa yake kansu kafin yayi mata signal data biyo shi…..(🤔) *** Yau kimanin kwana biyu batare da afiya ta kwana a gida ba kuma hakan ko ajikinta dan yanxu sun dinke tsab itada abba saidai abinda ke damun afiya shine bataso abba yasan tana dauke da ciwo dan ba karamin kashe mata kudi yake ba a wannan kwana biyun, hankalinsa a kwance ko tunanin mutuwa bayayi balle hisabi kuma baya tunanin yayan sa mata. A bangaren mommy kuwa bata damu da duk matan da zaibi ba matukar bazai kawo mata wata cikin gidan taba shikenan, yau tunda asuba farouk ya kamo hanya ya taho saboda kiran da abba ya kara masa kan lallai ya dawo yazo suyi magana ya kuma fada masa abinda kaka ya yanke danshi a nashi bangaren bai shirya farouk ya rabu da najma ba ai ba’a fara komai bama a cewarsa (🤔) bayan mai gadi ya bude masa gate ya gangara da motarsa yayi parking ya fito cikin kananin kaya wanda babu laifi sunyi masa kyau sai dai sam baida kyakkyawar zuciya haka ya nufi bangarensa wanda tun kafin ya koma abuja a nan yake , shiga yayi ya iske duk gurin yayi datti gashi yasan ko masu aikin ba lallai sunzo ba hakan yasa yaja tsaki ya wuce saman kujera 1 seater ya zauna yana faman sakin huci na tsanar najmah gashi an masa fin karfi ance bazai sake taba bayan ya kamata da maza har uku a gidansa wace irin rayuwa ce wannan? Shidai sun cucesa kuma bazai yafe musu ba har kakan nasa kuwa, wani tsakin ya kara saki cikin dacin rai yadan kishingida kafin gari ya ida washewa yaje bangaren abban. Saida yaga kusan karfe 9 kafin ya tashi ya shige toilet yadan watsa ruwa ya fito ya nemi riga jallabiya milk ya saka ya fesa turare kafin ya fito ya nufi bangaren abban nasa, da sallama ya shiga parlorn saidai babu kowa alamu sun nuna bai fito ba har yanxu kwafa yayi yanajin tsanar kowama a ransa kafin ya fiddo waya ya danna kiransa bayan tayi ringing abba ya daga yana fadin hello “Gani a parlorn ka abba” “Ok I’m coming “ Ya katse wayar batare dayace komai ba bayan yan mintina sai gashi ya fito cikin shirin sa da alama tuni ya tashi ma , gaishesa farouk yayi ya amsa masa yana tambayar sa aikinsa “ “Alhamdu lillah abba “ “Madallah” Bayan yan sakanni farouk yace “ abba kace kana nema na kuma dan Allah inason ku janye maganar cewa wai kada in rabu da wannan yarinyar hakan ba karamin cutata akayi ba “ gwauran numfashi abba ya sauke yace “ai zaka iya daukan duk wani hukunci akanta ka ladaftar da ita ta gane cewa tayi kuskure ba dole saika rabu da ita ba bansan ko ka gane hausa taba “ “ bangane ba abba “ Murmushi abba yayi yace “ yaro yaro ne yanxu kana nufin bazaka dauki fansar abinda tayi maka ba ai idan ka rabu da ita taci riba kai kuma ka kaskanta amma idan kayi ramuwar gayya lokacin zuciyar ka zata huce ga abinda tayi maka “ Dago kansa yayi cikin mamakin furucin abban nasa yana kallonshi amma saiya kasa magana zuciyarsa cike da wasi wasi shidai a iya saninsa abba ba karamin kaunar su najma yake nunawa yana yiba amma kuma a ayau furucinsa yasha bam bam da abinda suke gani….. dan a baya koda mommy tana aibata aunty tare da ya’yanta shi yake shigar musu yana nuna bacin ransa akan mahaifiyar tasa amma kuma zuciyar sa ta kasa yarda yadda a yanxu abba yake irin waddannan maganganun tamkar yana yinsu ne akan wani babban makiyin sa. Kafadarsa abba ya dafa har sannan murmushi bai rabu da fuskar saba yace “ duk tunanin da zakayi kayi, amma ka sani bantaba son zuri’ar AMIN ba kuma har abada bazan so su ba” wata zabura farouk yayi cikin kidemewa ya koma da baya yana kallon abban nasa da a yanxu fuskar sa tamkar wanda aka aikowa da mutuwa ne, “Ko ta ina amin dan uwana yafini samun ci gaba, yana da mata ta gari ni kuma tawa ba haka take ba yana samun farinciki ni kuma babu shi a raina dukda na fishi kudi saidai yayi min zarra ta ko ina mahaifiyar mu harta mutu tana begen shi kuma tana tsananin nuna mana banbanci har mahaifinmu da kake gani yafi kaunarsa akanmu Amin yana da farinjinin al’umma mutane suna sonshi fiye damu duka wannan dalilin ne yasa bazan taba son zuri’ar saba kuma a baya ma banso su ba “ Izuwa lokacin farouk sharce gumin dake goshinsa kawai yakeyi dan tunda yake a rayuwarsa bai taba shiga shock irin haka ba kafin wannan zaman da sukeyi zai iya dafa alqur’ani mahaifinsu yafi kaunar ya’yan yan uwan nasa fiye da su kawu aliyu saidai ashe ba haka bane. “Kada ka ragawa najmah duk wata hanya da zaka bi dan ganin ka ruguza ta wadda daga karshe zaiyi sanadin MUTUWAR ta shi nakeson kabi, bawai dan bazan iya kasheta lokaci daya bane ba a’a nafi bukatar suyi mutuwar kaskanci saboda babansu ne ya jaza musu ko ita islam ina nan zuwa kanta akwai abinda nake jira ne “ a hankali aka saki labulen da tun zuwan Farouk ake labe a gurin ana sauraron abinda abba da farouk suke fadi (topa 😱) “Amma inaso kayi tunani da kyau farouk inaso ka cika min wannan burin nawa ka tashi kaje sai mun sake magana “ Jiki a sanyaye farouk ya mike duk yadda yake jin tsanar ya’yan kanin mahaifin nasa batare da sunyi masa komai ba sai yaji ashe akwai wanda ya fisa a haka ya fita yabar abba da har lokacin yake a cike saboda ya tuno da irin tarin ni’imar da Allah yayiwa dan uwansa.( hassada mugun ciwo duk ni’imar da Allah yayi masa amma baya gani ta dan uwansa ta tsone masa ido bayan a zahiri yafi dan uwansa komai fa kudi, mota, babban gida Amma kuma ta kaninsa yake kallo ya Allah kayi mana tsari da hassada da bakinciki da kyashi) **** “ me kike nufi da kalaman ki? “ Baba doctor ya fada yana kallon anna data biyoshi office dinsa wanda kafin nan saida ya tabbatar da tsaron wajen , ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke tace “ ciwon zuciyar da take dauke dashi dasu hawanjini wanda Allah ne kadai zai tsallakar da ita tabbas yayan mijinta hafiz shine yake tunzura wannan ciwo nata batare da yanajin tausayinta ba “ “A cukurkude kike min magana please relax ki fadamin duk abinda kika sani da yaren da zangane “ “Kafin bikin najma akwai ranar da islam da najmar suka fita siyayya ni kuma ban bisu ba kada a tafi a barta ita kadai hakan yasa har nayi niyyar fita na fasa, toilet na shige dake nan parlor jin cikina ya murda da shigata da sallamar kawun su hafiz duk daya saidai ina da tabbaci bai ganni ba saboda maganganun da yazo dasu “ tadan dakata yanayin fuskar ta yana kara sauyawa kafin taci gaba da cewa “ shigowa yayi saidai dukda ina bandaki ina jiyo sautin dariya mara karfi saikuma ya fara fadin yau gidan naki aunty yara babu kowa ne? Itadai aunty banji tayi masa magana ba sai kuma naji takunsa yana dube dube har daki saida ya tabbatar babu kowa kafin ya dawo fabanta yace “ faduwarki buri nane wanda idan na cika shi tabbas na gama samun jin dadin duniya, a yanxu na gama da najmah saura islam , su aminatu kuwa sun saukaka mini aikinsu batare dana sha wahala ba suka bar duniya, ke dama tuni na nakasa taki rayuwar, so kadan ya rage burina ya karasa cika akan ahalin Al’amin” A lokacin danaji wadannan furicin ba karamin tashin hankali na riski kaina ba saidai a take naga idan na fita tabbas bazai barni da raina ba tunda baiji tausayin yayan yan uwansa bazaiji tausayi na ba hakan yasa na toshe bakina gudun kada kuka ya kwace min nima ya fara farauta ta, a hankali aunty tace masa “ Allah baya barci ka rubuta ka ajje Asirinka zai tonu a lokacinda bakada wani majingina kuma duniya zatayi watsi da kai kamar yadda takeyin watsi da ya’yan baro “ ta kare maganar cikin kamar yar koyo saboda bakinta da yake a jirge haka kawun ya ci gaba da dariya ta mugunta bayan nan ya juya ya fita ni kam mamaki ya kusa kasheni jin abubuwan da yake fada sosai rayuwar aunty ta bani tausayi a hankali na bude kofa na leko dan tabbatar da ya tafi kafin na kalli aunty da numfashinta yake sama yana kasa da sauri da sauri in baka manta ba shine na danna kiranka na shaida maka ciwonta ya tashi har kazo kayi mata allura data saka ta barci ka kuma gargade mu akan mu kara kula da ita wannan shine abinda na sani kuma daga nan na gane kenan shine makasudin ciwonta shine sanadin hadin auren najma da farouk bayan yasan ba’a shiri kuma yayi hakannne da nufin cutarwa “ “Me kika sani game da mutuwar su amina da anisa “ “ aini banma san su ba saboda tun kafin inzo suka rasu gaskiya bansan komai ba “ Jinjina kai baba doctor yayi yace “tabbas ko bashi da hannu akan kisan yaran nan to yasan wanda sukayi “ wani tashin hankali anna ta kara shiga take taji tsoro ya dirar mata cikin bakinciki tace “ matukar kuwa zargin ka ya tabbata to hafiz ya cutar da aunty cuta mai tsanani kuma ubangiji bazai barsa ba wallahi “ *** TAWA RAYUWAR By maryama page 20 MANHATTAN NEW YORK CITY No. 10 broadway street manhattan wata yankin unguwa ce dake cikin kasar ta New York wanda indai baka kasance daga top 1 zuwa 20 na masu kudin duniya ba to tabbas zatayi maka wahalar zama dan gaban rijiya ba wajen wasan makaho bane , zama a cikin wannan yankin saika tabbatar da kudinka sun kai dan a cikin masu kudin duniya ma ba kowa ke zuwa ya shantake ba saboda tsabar luxury life din da ake bazawa wanda in ka biye yanxu zaka ga kudinka suna kasa a yanayin yankin wajen wata irin tarin ni’ima ce Allah yayi masa wanda idan kaje na week daya tabbas sai kasan ka huta a cikin wannan street na tsaya da alkalamina daidai wani irin gida wanda na rasa gane shin da zallar glass akayi ginin ko kuwa dai akwai wani abu da bansani ba, daukar idon da gidan yakeyi kuwa zai tabbatar maka da ba kananun kudi aka narka masa ba wajen kawata shi dukda gidan baya da uban girma amma ko makaho ka kawo ya laluba yasan tabbas anyi gida anan wanda saidai mutuwa. Bazamu tsaya a nan mu bata lokaci ba wajen fasalta wannan luxury house dinba dan haka zamu ci gaba saidai inason ku fasalta shi da kanku … duk kanin wani paint dake jikin gidan idan ka dauke glass din dake manne to white paint ne dayake daukar hankalin su kansu yan cikin street din saidai duk wannan gidan da tsaruwar sa da komai na African man ne kuma ba kowa bane illa AMMAR MUHAMMAD ALGERA one of the richest man in Africa. ALGERA shine ainihin sunan business dinsa dama familyn sa baki daya saboda sunan ya samo asali ne daga kakansa wanda ya haifi babansa wato ABDULLAHI ALGERA wanda a lokacinsa ma tabbas an dama dashi dan shima bazaka ciresa daga cikin jerin mutane 10 da suke da kudi africa ba saidai sarki goma zamani goma Sai gashi duk yadda Algera’s family suke takama da dukiyar babansu saida Ammar da yake jika yazo yayiwa kowa fintinkau wanda har gobe suke mamakin daukakar da Allah yayi masa kuma ba tare da dukiyar Algeras ba ya tara nasa. (Bari indan baku tarihin algeras a takaice yadda zaku fi gane inda muka dosa) ABDULLAHI ALGERA kamar yadda na sanar muku shine kakan Ammar yana da Ya’ya maza 4 sai mata biyu ,matan aurensa su biyu ne hajiya samiha da hajiya bilkisu, samiha ya’yanta 5 maza 3 mata 2 ita kuma bilkisu itace amaryar sa mai da guda daya, Asalin abdullahi algera dan garin kano ne anan aka haifesa anan ya girma har lokacin da Allah ya fara buda masa kofofin samunsa nan da nan ya fara habbaka sai gashi bayan dogon lokaci ana saka sa cikin jerun masu kudi a africa mutum ne mai karamci ga taimako duk inda yaji inda ake bukatar tallafi sai yakai masallatan daya gina kam basa kirguwa gidan marayun da ya bude tabbas al’umma sun amfana, daga kano ya dauke iyalensa suka koma abuja da zama inda ya gina wani mahaukacin estate wanda yake cikin jerun estate masu tsananin kyau da daukar hankali aka kuma narka dukiya aka zuba mai tarin yawa da baki bazai iya lissafata ba, Part 4 ne manya a ciki sai kuma wanda basu kaisu ba girma kusan guda 8 wanda bayan ya’yansa maza kowa ya dauki nasa sai sauran aka bassu a matsayin masaukin baki da yan uwa masu zuwa kwana. Ya’yan hajiya samiha sun hada da jabir, salamatu, samira, Hamza, latif sai kuma auta wanda bilkisu amarya ce ta haifesa wato muhammad wannan suke zuri’ar Alhaji abdullahi algera kuma sune suka kara kafa sunan algera a fadin duniya domin kuwa kowanne ba baya ba Allah ya horewa kowa nasa dukiyar harda matan ma kuwa saidai su matan ya’yansune a yanxu suke juya musu dukiyar su, amma mazan kowanne ba a zaune yake ba dukda wasu a cikinsu sun sakarwa

Chapter 9 of 10