Share this page
yaran nasu ragamar neman kudin da kasuwancin. Kowannen su yayi aure da iyalensa saidai ya’yan nasu mafi yawa basa zama a Nigeria kuma a cikin ya’yan ma (jikokin kenan nake nufi) duk basuyi aure ba a ciki kuwa harda Ammar da kuma wanda baza’a rasa ba, iyayen nasu Ammar har gobe suna a gida daya ne wato wannan dankareren estate din nasu saidai kafin su samu wannan hadin kan Abdullahi Algera yasha wahala saboda fitinar uwar ya’yansa da kuma suma cikin yaran akwai fitinannu da suka nuna bazasu iya zaman nan ba saifa da yayi da gaske kafin suka hakura suka zauna bayan an rushe duka estate din anyi masa ginan daya hadu da zamani wanda aka tabbatar da kaf estate din abuja ba’a taba gina wanda yakai wannan kashe kudi ba da tarin gyale gyale da luxurious abubuwa da aka zuba. Muhammad shine mahaifi ga Ammar.. ya’ya biyu kadai Allah ya bashi Ammar (abdullahi sunan gaskiyarsa) shine babban dansa sai Amal da take biya mishi , mahaifiyar su yar asalin niger ce cikin garin niamey buzaye na asali wanda basu da surki tun wani zaman meeting da suka taba yi shida abokan kasuwancinsa anan niamey a sannan ne muhammad ya hadu da ita kuma yaji a duniya bazai iya auren ko wace mace ba in ba ita ba saidai yan uwansa sunso kawo masa cikas inda sukace bazasu hada jini da yar talakawa ba wannan ba al’adar familyn Algera bace, nan fa akayita ruguntsumi gashi a lokacin Abdullahi (mahaifinsu) baya raye dan be dade da mutuwa ba lokacin..shi kuwa Muhammad yace ba wanda ya isa ya hanasa auren ta tunda suma ba wanda aka zabowa mace a cikinsu kowa shiya zaba matan ma da kansu suka kawo mazajensu wannan abun shiya fara raba kawunan su ita kuma mahaifiyar sa bata da ikon yin magana yanxu sai suce itace take zugashi hakan yasa bata fito tayi magana akai ba saidai ta bawa danta goyan baya ya auri duk wadda yakeso tana tare dashi, da yan uwan sukaga fa lallai ya musu taurin kai sai suka hana alwalin da yake daura musu aure suka hanashi ya daura na muhammad wannan abu yayi masa ciwo ganin haka yasa yaja limamin dake jamusu sallah suka tafi dashi da wasu partners dinsa na harkokin kasuwanci akaje niamey neman auren AMAYA ZUBAIR saidai take mahaifinta zubair yace kawai a daura auren dayake mutumine mai mugun son abin duniya balle yaga kudi da kansu suna magana, bayan kwana biyu suka tattara suka taho da amarya amma an hado ta da kanwar babanta wadda mijinta ya rasu ba jimawa sai suka taho tare dan ba wata babba bace batafi sheakara 30 ba a lokacin kuma diyar ta daya wadda dangin mijin suka kwace bayan mijin ya rasu , tun fa data raka Amaya taga irin tarin arzikin dake cikin estate din Algera tamkar a London take ta rantse ta maya tace bazata koma niger ba koda dukanta za’a dingayi a wannan gidan, ko ita amaya ta jinjina irin kudin familyn algera dukda ita Allah bai samata kwadayin abun duniya ba amma ta girgiza da al’amarin dukiyarsu, saidai fa ba anan gizo ke saka ba domin kuwa familyn algera tamkar su cinnamata wuta haka suke ji dan ko sakata cikin al’amarinsu basuyi saidai ita baidame taba dan kuwa mijinta yana bata kula sosai sosai shiyasa ta kauda kanta ta watsar dasu ga kuma Gwaggo laraba yar zaman daki itama tana bata shawarar ta kyalesu sudai sunga guri babu inda zasu kiyayya kuma mugun abunsu ya koma kansu wannan yasa ta watsar dayin duk familyn algera a haka tazo ta haifi ammar dinta wanda yaci sunan kakansa wato Abdullahi Muhammad algera bayan shekaru 5 ta haifi Amal daga nan sai tayi bari har sau biyu kuma bata sake ba ta dangana ta rungume yayanta da mijinta wannan shine takaitaccen labarin Algeras. Present day Zaune yake gefen wani irin gado da matukar kawata shi ya mugun haska dakin da yake ciki wanda paint din yake fari kal sai gadon navy blue gashi ba wani babba ba sai kudi, fari ne tas dashi irin farin nan na buzaye sak inka kallesa zaka ga kamarsa daya da hoton wata mace da take manne anan dakin jikin bango saika rantse kanwar sace saidai daga jikin hoton a gefe an rubuta Ammy da in baka kurewa gurin kallo ba bazakace rubutu bane hakan ya bani tabbacin mamar sace dogo ne sosai yana da fadi da kira da duk wani namiji mai ji da kansa yake da ita, matsakaitan idanu garesa da dogon hanci sai bakinsa da baya da girma fuskarsa kuwa doguwa ce shape dinta sai bakar sumar kansa datake kwance tasha gyara, fatarsa kai basai an fada maka tana samun gyara ba tamkar ka taba jini ya fito haka take kar kar kar da ita a kallo daya in kayi masa ka dinga santinsa kenan kuma bazaka so dai dai da second guda ya bar idanun ka ba, dogon wando ne jikinsa blue color irin masu laushin nan na barci saidai babu riga a jikinsa, waya yake amsawa saidai tunda daga sallama da yayi bai kara cewa komai ba saidai daga yadda idanun sa sukayi jawur lokaci daya zaka san tabbas cikin tashin hankali yake sauraron wayar har saida aka yi shiru daga cen bangaren kafin ya saki wani numfashi yanajin tamkar ya janyo wannan lokacin ya ganshi a 9ja “ stop crying ok “ Ya fada da wata irin murya mai amo kai dagaji kaji cikakken namiji wanda muryansa take a fashe saidai tarin nutsuwa da jin dadi da aka tashi dashi zakaji yana yin magana marar hayaniya,( sai naji muryansa kamar ta digazga wannan actorn na india saidai da take shi Ammar a hankali yake yinta) daga cen bangaren muryan mace tana kuka ta bayyana da yake wayan a speaker take “Yaya kanaji fa wai duk fadin gidanmu ace an shigo daga waje anyi kisan kai kuma an fita batare da an kama wanda yayi ba “ ta kara fashewa da kuka mai ciwo na rashin da suka tashi dashi a familyn algera. *** Najmah Ranar friday bamuje makaranta ba saboda good friday esther monday da akeyi hakan yasa muka baje a parlorn babanmu wanda daga baya ya koma dakinmu, nida aminatu ne kawai a ciki ko waccenmu tana kokarin kwashe muhimman abubuwan mu muna maidawa a sabuwar jakan da babanmu ya kawo mana kowa data islamiyya data boko , nikam ta islamiyya ta na fara daukowa na fara fiddo littattafan dake ciki wanda bamu gama dasu ba nake maidasu sabuwar jakan bayan na gama nabar wa’inda muka gama dasu a islamiyya cikin tsohuwar jakan tawa kamar yadda na fada muku a baya muna a haka baban mu ya shigo da sauri cikin farincikin ganinsa nace baba kaga komai nawa na maidoshi sabuwar dan ko kara daukan wannan bazan sake ba, saidai duk surutun da nake masa kamar baya cikin nutsuwar sa amma sai cikin dagiya yace “kin gama da wannan kenan” ya fada yana nuna min tsohuwar gyada masa kai nayi ina murmushi dan ni bankawo ko a raina yana cikin wata damuwa ba dan banfi shekara 14 ba lokacin , aminatu ma nan ta nuna masa ta ta , saidai bai kara ce mana komai ba ya sunkuya ya dauki tawa tare da fiddo wata jaka daga cikin leda baka ya saka a ciki ya nemi inda kayansa suke ya saka kafin nan ya juyo ya kalleni dama idanuna a kansa suke tunda ya dauki jakar tawa danni a nawa tunanin mezaiyyi da ita ai gara shima ya siyo sabuwa kamar yadda ya siyo mana saidai bayan kallona da yayi saiya sakarmin murmushi yace “ Allah ya muku albarka keda yan uwanki “ yana gama fadin haka yayi waje, ni kuma na amsa da amin ina binsa da kallo…….. _yaushe asirin abba zai tonu a idon duniya? _wata irin rayuwa najmah zatayi a wannan gidan? _waye ya dauke gawar anisa dan yayi musu yawo da hankali? _wani mataki baba doctor zai dauka a yanxu daya gano abba? _waye bokansu mommy yace zai bayyana? _waye ya mutu a cikin familyn algera? _wani mataki farouk zai dauka akan najmah? _ita jakar minene a cikinta da abba yakewa aunty azaba a saboda ita? _wani tanadi abba yayiwa islam? _waye keda hannu akan kisan su aminatu? _kuna ganin aunty zata iya kai wani lokaci kuwa ganin ciwonta ya tsananta? _yaushe najmah zatayi rayuwar farinciki? _Minene dalilin canzawar amira lokaci daya? _waye yayiwa abba da farouk labe lokacinda suna magana? _mezai faru idan mommy ta gamo abba yana tare da afiya? _shin anya farouk zai auri afiyya kuwa? Hmmm And Alot More….. Alhamdu lillah Anan na kawo karshen littafin TAWA RAYUWAR book 1 sai mu hadu a book 2 idan Allah ya kaimu nan da sati daya in shaa Allah dan warware muku wannan cakwakiyar kura kuren dake ciki Allah ya yafe min Duk dan adam ajizine koda za kuga kuskure ayi hakuri 09063174122 Wani mari ya kaiwa fuskata cikin razani na dawo hayyaci na sai kuma na fashe da kuka na yunkura na tashi da kyar nace“ Yaya Farouk dan allah kayi hakuri ….” Rufe bakinta tayi ganin kukan ya taho mata tun daga kahon zuciya sannan ta cigaba da cewa “ ka a tsawace yace “ banason maganar banza tashi mu tafi kano” Zaro idanu nayi inajin inama kasa zata tsage in shige in mutu kowa ya huta cikin in ina da banma san inada itaba nace “ me kake nufi? Ka sanar musu ne? Menene abinda nayi maka da zafi haka? Tabbas saki na da kayi banga laifin ka ba amma dan allah kada ka fadawa su abba abinda ya faru “ cikin sauri na rike kafafunsa ina kwantar da kaina akansu tamkar sune abinda suka ragemin a duniya, hankada ni yayi yana huci yace “ this is the last warning da zan miki akan taba jikina da zakiyi very stupid girl kawai, kuma idan baki tashi ba zaki ga abinda zai faru “ lumshe idanuna nayi inajin tabbas da zanga abinda zaisani in mutu yanxu dana je gurinsa na huta da duniya, zuciyata tayi rauni matuka baki bazai iya fadi ba , ga hannu na da kamar ba’a jikina yake ba mikewa nayi dama da hijab a jikina sai kawai na kama trolly daya na shiga janyowa batare dana kalli inda yaya Farouk yake ba dan tabbas nasan aikin gama ya gama. Kayana na dinga kaiwa na sawa sauran abubuwan banbi takan komai ba na koma cikin motar seat din gaba na zauna tuni idanuna sun bushe na saddakar da komai ga wani mayen zazzabi dake cin jikina, shigowa yayi motar ya kunna ya tada muka fara tafiya , kwantar da kaina nayi jikin kujeran na rufe idanuna ina adduar da duk tazo bakina dan nasan tawa ta kare ni kuma, tafiyar mintuna mukayi naji ya tsaya a wani gida wanda banma san unguwar ba fita yayi bayan minti 10 ya dawo ya kalleni a wulaqance yace in fito batare danayi magana ba na fito muka shiga gidan tare yana gaba ina binsa a baya a cikin gate din gidan daga gefe muka iske wani dattijo a zaune saman tabarma gefe kuma jika ce kamar irin ta wanzamai da sauran kayan aiki, sannu yayi min yace in zauna zai duba hannu na zama nayi na gaishe shi ya amsa da fara’a na mika mishi hannu na daya mugun kumbura ga ciwo daga ciki, subhanallah yace kafin ya farawa yaya Farouk fada akan ba’a kawo ni da wuri ba gashi hannun yayi tsami , wani ruwa ya dauko ya fara shafamin a hannun ai kamar an bude famfo na fara kuka ina kokarin kwace hannun amma malamin ya rike matuka ya hana hakan sai addua yake tofamin yana shafa hannun , nan fa aiki yayi aiki na farajin azaba har brain dina ihu na fara musu ina kokarin kwacewa malamin yacewa yaya Farouk ya rike ni kamar mai kyankyamina yazo ya kamani harda mugunta a lamarin nashi tun ina kuka da hawaye harna fara haka nan babu hawaye tas saida malam ya gyaramin hannun ashe gocewar kashi ne daga nan ya daure min zuwa lokacin na azabtu na galabaita ga zazzabi da tun yau da safe ya rufeni ga kuma damuwa abubuwa suka taru suka min yawa , nan ma ya kama goshina ya fara mulmula sa yana shafa man zafi akai fadin yadda nakeji tabbas bazai yiyuba saida yaga kullutun ya bace saura kadan kafin ya barni duk abinda ake ina jikin mugun ya matse ni da mugunta ina ji ina gani saida malam ya kammala kafin ya sakeni, nan yayi masa godiya ya fiddo kudi ya ajje masa sannan yace in taso mu tafi harna tas Tafiya muka ci gaba dayi anan na gane mun dauki hanyar kano kuma tun shigarmu mota babu wanda yayi magana har muka isa, direct kofar gidan mu ya ajje ni yace in fice masa daga mota sai sannan na sanya kuka na rashin yadda zan fara sanarwa aunty wannan abun kuma nasan tabbas saiya fadawa kawus dinmu cikin tsawa yace “ get out “ Da sauri na fito ina kare fuskata dan banason masu wucewa suma san nice balle maganar ta baza unguwa aure duka yau sati daya da kaini gidana gashi na dawo a yanayi marar dadi tabbas duk wanda ya kalleni indai yasan ni to sai yaga canji marar An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 10 of 10