saman hannunta marar cannula na damke tamkar za’a raba mu idanuna suna cikowa da hawaye, idanu ta fara budewa har ta dorasu akan nawa kafin tayimin murmushi mai kayatar wa take tsananin kyawunta ya fito dukda tana jinya kuwa, dan mamana badai kyau ba komai ta hada na siffar mace cikakkiya saidai babu farinciki ko kadan a rayuwarta ko da yaushe cikin damuwa take da ciwo “ ina yan uwanki ?”
Ta tambaye ni a hankali kamar mai rada (wanda hakan tamkar dabi’ar tace magana a hankali cike da nutsuwa) “ sun tafi gida ni kadai na rage zan kwana “ waro ido tayi tace “ su kadai zasu kwana meyasa baza’a sallame mu ba banason rashina a kusa dasu “ ta karasa maganar tana niyyar tashi “ a’a jikin ki baiyi kwari ba nasan bazasu sallame mu ba gaskiya aunty, kuma ai allah yana tare damu kin manta kinsha fada mana haka?”
“Bazaki ganeba najmah babu uwar da zata so tayi nesa da yan matan ta kuma ta barsu su kasance su kadai a gida batare da ita ba, wannan duniyar cike dake da azzaluman mutane masu FUSKA BIYU “
“Allah yana tare damu aduk inda muke, kece kike fada mana haka “ na bata amsa ina kallonta, badan taso ba ta koma ta kwanta tana adduar da duk tazo bakinta akan yaran nata da basu tare bayan ta samu nutsuwa ta tashi na kamata har zuwa toilet ta dauro alwala tayi sallah da ake binta daga nan ta koma gado tana tunani kala kala a haka har bacci ya dauketa, nima ganin tayi bacci yasa na koma gadon dake facing din nata na kwanta da nawa tunanin har bacci barawo ya sace ni.
***
Kaka ne zaune ya hakince a kujeransa yana kallon farouk da yayi tamkar an aiko masa da sakon mutuwa bayan fada masa aurensa da yayi da najma wanda babu fashi
Shidai yana mamakin irin wannan abin acikin zuri’ar sa ace har ana kin wani kuma bai taba tunanin Farouk zai bijire masa ba ganin jihadi zaiyi saboda najma yar uwar sace kuma marainiya ce gashi duk shekarun su yakai ace suna dakin mazajensu amma shiru babu wanda yake da sha’awar aurensu kuma shi a nashi tunanin bayaso ya mutu batare dayaga a cikin su hudun ko wacce tana dakinta ba saboda yasan ya’yan nasa maza kansu da ya’yansu kadai suka sani shiyasa yake fafutikar ya aurar dasu , hakan yasa da kawo hafiz yazo da maganar bai musa ba amma shine Farouk yake neman bijire masa.
“ ka bude kunne da kyau kaji aure babu fashi matukar muna raye saidai idan ka matsa baza kayi ba to kuwa zan cireka cikin ahali na sai kaje ka nemi wasu dangin, “ a zabure Farouk ya dago yana waro ido cikin tsantsan mamakin kakan nasu wai akan wannan ifirituwar aljanar ake cewa za’a ciresa cikin ahalinsa? Sannan kaka ya cigaba da cewa “ ka shirya nan da 3month masu zuwa in shaa Allah banyi niyyar auren nan dan in musguna maka ba nayi ne don in gyara zumuncin dake tsakanin ku kuma bayan haka kamar kayi jihadi ne najma da yan uwanta abin tausayi ne Farouk….. nan dai yaci gaba dayi masa nasiha masu ratsa jiki amma kuma kawai jinsa farouk yake dan bayajin zai iya kallon najma a matsayin mace balle har ya sota ko ya dauketa matar sa daga nan ya tashi ya tafi gida nan ma kawu hafiz ya jaddada masa babu fashi yanaso ko baya so, amma bai nuna masa muguwar manufarsa tayin hakan ba ya bari sai idan anyi auren zai hada wa najma abinda farouk zaiji ya mata tsana fiye da mutuwar sa.
Mommy ma ganin babu yadda zatayi yasa ta hakura amma har yanxu tana nan tana tauna maganar da kawun ya fada mata amma ta kasa gane me yake nufi kuma tambayar duniya tayi masa yaki kulata hakan yasa ta zuba masa ido kawai, ta gefen afiya da sukeson hada su kuwa ta jingine maganar ne tanason a gama da auren najma kafin ta fiddo maganar afiyar ta yadda dole itama a bata hakkin ta na uwa wannan kenan.
***
Da safe na tashi bayan nayi sallah na fito indan mike kafata danaga jikin na aunty da sauki anan harabar asibitin nake tsaye dan nasan su amina zasu iya zuwa koda yaushe , jiniyar yan sanda naji da karan motoci dago kaina nayi ina zuba manyan idanuna a kofar get din inda motoci suketa kara bullowa masu shegen kyau da daukar ido ga kuma yan sanda daga gani escort ne aka musu, manyan jeep ne sunfi biyar sai kuma kuma motocin yan sandan guda biyu sai wasu hilux biyu suma, wanda fadar kudinsu bata lokaci ne, nidai da farko nayi tunanin shugaban kasa ne sosai na baje idanuna ina kare musu kallo nan naga shuwagabannin asibitin suna fitowa da gudu ko wanne dauke da farincikin ziyarar babban bakon, a hankali na janye idanuna kafin na juya cen bangaren inda muke ina jinjina lallai kudi sunyi a duniya ji yadda ake musu harna kusa shigewa na sake waigowa nan na sauke idanuna akan mutumin da aketa karewa ana bashi hanya ba wani sosai nake hango fuskan shiba saboda mutane nan dai na juya na shige.
Bayan kamar 30mins saiga su islam harda anisa ma da jikinta ya warke da kuma maryam tana dauke da basket nan fa suka baje aka hau hirar wannan bakon da yazo ashe suma sun ganshi wai tallafi ya kawowa asibitin inji maryam itama a gurin doctor taji yanzu, jikin mama a yau yayi sauki ganin haka yasaa doctor yace mu tafi gida an sallame mu nan muka kwashe kayan mu muka tafi gida.
-hmm ko fara wasan ba’ayi ba
TAWA RAYUWAR
By Maryama
Page 5
#womenofwords🤍
Bayan komawar mu gida nan makwaftan mu duk suka shigo suka duba aunty harda umma ma tazo da kuma matar kawu nassar wadda muke kira da mama dan babu laifi ita kadai ce suke dan gaisawa da mu, kuma yaranta basu cika fitina ba, hakan yasa ba ruwanta muna dan zumunci dukda ba sosai ba dan bata zama gurin aiki take tafiya asibiti, washe gari jikin aunty ya danyi sauki alhamdu lillah kuma muma mun dauki zancen auren mu mun ajje gefe ganin damuwa bazata karemu da komai ba, haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau tsawon kwana uku kenan da sallamo aunty zaune muke da safe kowa da aikin da take ni sharar tsakar gida nakeyi ita kuma islam wanke wanke amina kuma tana zauna tana wa aunty sintar kai (tsifa) anie kuma a zaune take da kofin koko a hannunta tanasha kowa dai da sha’anin da yakeyi sallama mukaji yaro ne ya shigo dan nan makwaftan mu bayan ya gaishe mu yace “aunty najmah kizo ana sallama da ke “ wanke wanken na saki na kalli isah yaron da aka aiko nace “waye yake kirana “
“Nima bansan shiba amma bari in tambayo “ ya fada , zai juya kenan aunty ta katseshi da cewa “isah jeka kawai gata nan zuwa “ da to ya amsa kafin ya fita nan na juya ina bukatar karin bayani gurin aunty batare data kalleni ba tace “ tashi kije “ zanyi magana ta bata rai haka nan na mike jiki a sanyaye dan bansan ko waye ba kuma wannan shine karo na farko da akace ayi sallama da ni a rayuwa ta hakan yasa na rasa ta cewa dole na tashi na shige daki, zani ne a jikina sai t shirt abin safiya ce ko wanka banyi ba dan haka na fesa turare na zura dogon hijab dina light pink data kara fiddo ainihin color dina ta maidani ajebo, sosai na karewa kaina kallo a mirror tabbas allah yayi min halitta mai kyau nidin ina da tsayi dan harna fi amina amma kuma islam kanmu daya kuma ina da diri mai kyau gani da haske irin na buzaye, idanuna suna da girma so masha allah sai dan karamin bakina mai dauke da pink color natural lips sai hancina shima yana da tsayi dan daidai, sosai nafi duk yan gidanmu kyau da komai da y’a mace zatayi alfahari shiyasa ma dangina suke nuna kishinsu a fili a kanmu.
Sanin ana jirana yasa na kara fesa turare mai sanyi na AYNAD INCENSE SPRAY kafin nayi hanzarin fita dukda ido suka bini islam ce ta kunshe dariyarta tana ayyana yau yaya najmah anyi kasuwa (😂😒 islam ta fiye tsokana) tunda na fito na hango shi tsaye jikin motarsa 406 ash color, yana sanye da shadda fara data yiwa fatar jikinsa kyau sosai.
Haka nan naji faduwar gaba tazo min batare dana shirya ba dan a jikina naji babu Alkhairi a zuwan nan nasa , shi kuma kafeni yayi da ido yana karemin kallo shi kansa mamakinsa bai wuce duk wannan kyawun da allah yayi min ba amma ko kadan baya kaunata balle ace har zai aureni in haifa masa ya’ya,
Da sallama na karasa murya na tana rawa dan wani irin kwarjini yayi min gasho still yaki janye idanunsa akaina, bayan sallama baice komai ba nan na gaishesa amma yaki amsamin yana kare min kallo ji nayi kamar in koma gida amma na danne zuciyata danna dauki alkawarin kwatarwa kaina yanci a matsayina na budurwa kuma mai aji nima dole in kama kaina in saka masa ido inga yadda zaiyi da al’amarina.
Tsayuwar minti biyar mukayi dan harna fara gajiya cikin kosawa na daga baki zanyi magana saidai tasa maganar ta Riga tawa fitowa “so nake kije ki cewa kaka a janye batun auren mu dake najmah “ da sauri na dago idanuna na kalleshi dauke da mamaki
Shi a matsayin sa na namiji ya kasa fada musu sai nice shafaffiya da mai zan dauki kafa inje ince a janye auren? Wani kallon uku saura kwata nayi masa dukda ba karamin daurewa nayi ba dan wani tsoronsa nakeji amma na dake nayi dariya mai karamin Saudi wadda iya kacinta lebe ne kawai nace “ ai kai ya kamata kaje tunda kaine namiji idan kuma ka barmin mazantakar toh sai inje?” Na kare tambayar da rainin hankali saidai a mamakina shima murmushi yayi yace “ don’t mind idan kinga hakan yafi miki “
Sosai raina ya baci da rainin hankalinsa amma saina boye nace “ idan har maganar janyewar aure ce ta kawowa zan iya tafiya ? Dan ban fito nan saboda ka dinga fadamin magana ba yaya Farouk “
“ lallai kina wasa da maciji najmah amma zan nuna miki iyakacin iyawarki zan tabbatar da cewar kinyi kukan da babu wanda zai iya lallashin ki , zakisan cewar gidana ba gidan aurenki bane zan maida rayuwar ki abar tausayi daga nan zaki banbance tsakanin nidake waye ake kira namiji, “ wani murmushi mai ciwo ne yazo min kafin nace masa “ya kake so inyi ne da rayuwata dan allah nifa auren nan bance inaso ba kamar yadda aka maka dole nima haka akamin, ina rokon ka idan har bazaka iya zama dani ba ka koma ka fadawa kaka dan yasan abin yi amma banaso ka daukeni mai laifi sannan a ganina koda wani kaji zai yiman abubuwan daka lissafa sai inda karfinka ya kare balle kuma kai kana a matsayin yaya na, jini na kuma dan uwana “ juyowa yayi ya kalleni kafin yayi murmushin da yake bani tsoro yace “ well kada ki damu na gama abinda ya kawo ni idan har kin dauki shawara ta fine rayuwar kice kuma bandamu da kina son auren ko baki soba wannan bashine a gaba naba “ daga haka bai kara cewa komai ba sai shigewa motarsa da yayi nima haka na juya gida inajin zafi da radadi a zuciya ta ganin tun ba’aje ko ina ba na fara fuskantar wulakanci daga wajensa wasu hawaye naji sun zubo min sai yanxu naji zuciyata ta kara rauni kuma ta kara karaya akan lamarin yaya Farouk.
Gida na juya har sannan ina hawaye wato shi bama duba aunty yazo ba bukatar sace ta kawo sa , a soro na tsaya na goge hawaye na dan bana bukatar karawa yan gidanmu tashin hankali bayan wanda suke ciki saida na tabbatar na goge kafin na aro murmushi na yafaawa fuskana sannan na shiga da sallama duk idanu suka zubamin kowa fuskar shi dauke da tambaya amma saina kara sawa kaina jarumta nayi murmushi tare da rufe fuskana da hijab waini kunya nan islam amina da anie suka fashe da dariya nan islam ta taso tana fadin “ wani mai sa’a ne wannan yazo gun habibty “ banza nayi mata na harareta kafin na shige parlor nan suka cigaba da tsokana ta suna dariya, banda aunty da tun shigowa ta taga damuwa a tare dani saidai ta jinjina min ganin irin jarumtar da nayi gurin boyewa amma a jikinta tanajin cewar farouk ne yazo, dan haka ta tashi batare data kula su amina ba ta shiga parlorn .
A zaune ta iske ni nayi tagumi abin duniya ya isheni hakan yasa ta tabbatar hasashen ta ya zama gaskiya, kafada ta tadafa nan na dago muka hada ido da ita duk dauriyar da nake ciki saida kwalla ta cika idanuna zanyi magana ta rigani da cewa “ farouk ne ko “ gyada mata kai nayi kawai zuwa sannan hawayena sun zubo batace min komai ba ta barni na cigaba da kuka na har saida taga zuciyata tadanyi sanyi ina sauke ajiyar zuciya kafin tace “ yaya kukayi dashi?” Ban boye mata komai ba na fada mata dalilin zuwansa, wasu numfashi masu zafi ta sauke har cikin ranta abin yana mata zafi, wai yau yar’tace ake gudu duk kuwa da irin kyawun fuska, sura da kyan halin da allah ya mata amma bawa baya wuce kaddarar sa da jarrabawarsa, nasiha tayi min mai ratsa jiki da kuma kwarin guiwa akan in kara dagewa da addua in shaa Allah komai zai wuce mun jima tana lallashina kafin tace inje in wanke fuskana in cigaba da hidima ta zata nemi Farouk suyi magana daga haka na fito kamar bani da damuwa muka ci gaba da hidima dukda acen kasan zuciyata inajin radadi da kuma tsanar yaya Farouk a raina.
***
Mota ce tashigo harabar gidan bayan masu gadi sun bude musu gate budurwa ce ta fito daga front na zaman banza wadda bazata wuce 25 years ba sai kuma wata mata daka gansu kaga uwa da ‘ya abida ce ta fito cikin takun izza zata shiga motar mommyn tata nan sukayi kicibus wani ihun murna tayi tana rungume budurwa “ oyoyo my afiya ure welcome “ dariya sukayi harda maman kafin suka shiga cikin gidan suna murnar ganin juna nan fa aka hau farinciki amra ce kawai bata gidan amma amira tana nan, mommy kuwa kamar ta maidasu cikinta, yar aiki su amira ta tura ta dauko trolleyn su dake booth daga nan sukayi dakin su ita kuma mommy taja mama nata dakin suna shiga mama yace “ yaya zulfa an yanka ta tashi fa “ wani kallo mommy ta bita dashi tace “ meke nan yiman bayani gwari gwari “
“Hmm kinsan nace miki zanje gurin malam malawi ko “ tacewa mommy kafin taci gaba da cewa “ in fada miki yanxu haka cemin yayi aikin da kika saka akawa yaran nan shekara kusan 10 baya yana gab da warware “ wani zabura mommy tayi tana dafe kirji tare da cewa “ na shiga uku ni zulfa’u “
“Hmm shiyasa ba shiri nace wannan ba maganar waya bace gara inzo face to face in fada miki gara musan abinyi tun wuri wallahi kindai san yace mana suna da karfin Tauraro ba kamar ma wannan shegiyar najmar daba dan wannan hatsabibin bokan namu ya taimaka mana aida yanxu duniya zancen najma ake da yan uwanta harda wannan farar uwar tasu “ wasu zufane suke karyowa mommy tama kasa magana dan tasan idan asirin ya karasa karyewa kan ya’yanta zai dawo hakan shine sharadin aiki.
Cikin gigicewa mommy tace “mujahida zama bai ganni ba wallahi ke kadai kikasan irin fadi tashin da nayi akan wannan jajayen yaran idan kuwa har aikin nan zai karye tabbas akwai babbar musiba tana binmu “ mujahida da take fuskantar yar uwar tata a cikin zuciya tace “ ke kadai musiba zai shafa Ahtoh nida y’a ta kam meyayi mana zafi “ mommy ta cigaba da share zufar dake kwance saman goshinta tana kada kai kamar kadangaruwa tace “ dole yau zamuyi tattaki muje gurinsa dan idan kinga na kyale zuri’ar nusaiba to bana raye “
Wayyo najmah💔
TAWA RAYUWAR
By maryama
Page 6
kafin ta kara da tace “ ai ta zama bata kama muba tashi zakiyi mu koma gurinsa kina jifa sharadinsa kan ya’yana zai dawo kuma kinsan an kusa sanyawa amira da amrah aure so kikeyi mazajen suce sun fasa? Tashi kawai mu tafi in akwai wani aikin ya kara mana dan banaso inga sunyi farinjini gara duk su mutu babu aure wallahi , kuma inaso ya mun aiki akansu farouk da hassan su tubure suce bazasu aure suba , kinga daga nan burina ya cika akan nusaiba “ mujahida da tun dazu take sauraren yayarta tace “ ki bari muyi a natse mana kinsan gaggawa aikin shaidan “numfasa mommy tayi kafin tace “ ai tunda tace zata goga dani nikuma zan tabbatar mata tayi ganganci a rayuwarta saita gwammaci mutuwar ya’yan nata, ni dinnan ba wata shegiya nan duniya da zata jera kishi dani yadda hafiz ya auro ni ni kadai haka zai mutu dani ni kadai (🤔ban gane ba meya hada mommy da aunty kishi? Amma dai muje zuwa zaku fahimta a gaba) “
“Hmm ni kuwa gani nake abi asannu kinga duk mazajenmu basu sani ba kum……” daga mata hannu mommy tayi tana bata fuska kafin tace “ saboda banda afiya asirin zai koma wa shiyasa zakice abi a sannu ko mujahida?””
“ a’a ba haka nake nufi ba kindai san doguwar tafiyar da zamuyi gara tunda kwana zamuyi mu barwa safe in shaa Allah ko kuwa “ ta fadi cikin tausasawar lafazi haka taci gaba da shawo kanta da kyar ta amince tace
“ allah ya kaimu “
***
A daki su amira labarin auren yayan nasu suka bama afiya sosai tayi bakin cikin jin haka nan tace tana son su rakata wajen najmar zata bige mata warning mai karfi akan mijinta (sannu uwar gida afiya 😂) abida ma zugata tayi akan su barwa la’asar sai suje inma duka ta kama su daki banza dan kallon kaskantacciya suke mata wadda ko aiki bazasu iya daukar taba.
Afiya she’s 25 tana da tsayi madaidaici sai uban farin bleaching dan asali baka ce amma yanxu tasha bleaching sosai har yellow take ga attach aka kuma ko kadan bata jin magana tare suke da amira duk wani club da hotels sun sani amma a boye suke lamarinsu batare da sanin iyayen su ba , kuma iyayen basu wani damu da tarbiyar suba suma yan uwansu maza kowa harkar sa yake dan suma bawani jin magana suke ba, gwara abida munafurcine kawai sana’arta da hada boom amma ba ruwanta da biyewa yan uwanta mata ita kuma amra har shan kwaya take dukda amira da abida sun sani amma basu damu ba wannan kenan
Zuwa yamma suka tashi kowacce tasha dogayen riguna dan yanxu abida ma ta kusa kamo su tsawo kuma dukda shekara 4 ne tsakaninsu amma kusan girman jikinsu daya batare dasun bi takan iyayen su ba suka fice anan cikin gate suka hadu da amra ta dawo daga yawon shashancin ta, itama jin inda zasu je tace su tafi tare da ita amma su biya su dauki hamida da hanifa cikin jan tsaki abida tace “ su wannan me zasu tsinana mana kawai mu kadai mun isa dan kinsan kafin hanifa ta shirya saitayi kusan awa 2 harsai anyi sallah magrib “ jin haka yasa suka yanke shawarar tafiya kawai.
***
Tankaden garin masara nakeyi islam kuma tana jajjagen kayan miya sai anie da amina dake zaune suna taya mu hira dan mune karfin gidan nida islam, ita amina asthma gareta ko wajen hayaki ba’ason suna zuwa anie kuma dama mun yafe aikinta saboda wannan lalurar da take fama dashi danma kwana biyu alhamdu lillah bai tashi ba, aunty kuma ta zagaya gidan umma aminiyar tata, maryam ma yau bata zoba ashe gidan kakar su ta tafi zata mata kwana biyu sai dazu da na fita muka hadu da saddiq yayan ta yake fadamin.
Karar takalma masu tsini mukaji dan haka muka maida hankalin mu kacokam kan kofa, saidai ganin wanda bamuyi zato ba yasa naji gabana ya fadi nan na tattaro jarumta nace “ ah sannun ku da zuwa yaya amira “ wani kallon kasa da sama suke binmu batare da sunyi magana ba dama nasan alkhairi dai bazai kawo su ba saidai tsarri , dan haka naja bakina na tsuke saidai jin tsakin da akayi yasa na dago na kalli islam da tayi tsakin tace “ ku nan fa gidan mutane ne kuka zo ya kamata kuyi sallama ai bawai kawai ku fadowa mutane gida ba sai kace awaki “ wani zaro idanu gaba dayan mu mukayi jin karshen maganar ta amira ce a fusace tace “ dan ***mu kike kira awaki saboda cin fuska waike tantiriya Wallahi saina koya miki hankali “ da karfi ta fusge hannun abida da take tausar ta amma tayi kunnen uwar shegu tayi kan islam tana zaginta cikin jin haushin kalmar data kirasu, saurin mikewa nayi na shiga gaban islam dako motsi batayi ba hakuri na fara ba yaya amiran amma tana zuwa ta daga hannu ta fesa mun mari kafin ta turani gefe sosai na bugu da bango saidai kafin in mike mukaji karan mari har ukku a jere cikin sauri na dago inga wa aka mara amira ce ta dafe kumatunta jin azaba ashe islam takai mata mari biyu anie takai mata daya amina kuma tana gefe hawaye ya wanke mata fuska duk surutunta amma kamar wata wawuya haka ta koma tun sanda taji maganar auren nan, nan fa abida tayi kukan kura itada amra suka fada su islam da fada amma inaaa take gidan ya hargitse dan wani naushin kawo wuka islam da anie suke musu ni kuma kasama tashi nayi dan bakaramin buguwa nayi da bango ba, afiya ma tsorone ya kamata ta lafe a bango ganin anawa su amra duka tasan inta shiga hadawa za’ayi da ita, amina ce ta ruga tayi waje tana kwala kiran sunan auntyn mu, suna tsakar gida suka farajin hayaniya da kukan amina da take tahowa nan cikin tashin hankali aunty ta mike itada umma da sauri suka fito a soro sukayi kicibus da amina nan ta shiga fada musu abinda ke faruwa da gudu aunty ta nufi gidan umma tana take mata baya itada aminatu.
Cikin sauri aunty ta kama islam da idanunta suka rufe ba abinda take banda jibgar amra da abida ita kuma anie dake dukan amira ummace ta kamata cikin huci islam tace “ ki barni in ji musu ciwo aunty basu da kunya wannan mutanen har zasu daki yaya najmah saboda tsabar rashin mutumci “
Sai sannan aunty ta juyo kaina goshina yadan bugu harya kumbura umma ce tayi saurin kamani tana min sannu ita kuma aunty fada tayi mana mu duka kafin ta bama su amira hakuri wanda daga wacce aka fasawa hanci sai mai baki duk jini sai abida da Goshin ta yayi tsini tsabar buga kanta da anie tayi, ita kuma afiya tun fitar amina ta ruga ta koma motar da sukazo da ita dan tsoro, hakuri aunty tadinga basu dukda tasan basu da gaskiya dan sune suka fara takalar su najma amma da yake babu tarbiyya suna mikewa amra tace “ wallahi basu ba ko ke uwar tasu sai mun dauki mataki mummuna akanki na …..” saukar mari sukaji take amra tayi wani ihu na azaba tana dafe kuncin ta duk kallo suka bini dashi cikin huci nace mata “ idan zaki kwana kina dukana bazan tanka miki ba amma idan har kika taba mahaifiyata ko yan uwana sai inda karfina ya kare ku fice mana a gida shashashu marasa tarbiyya “ sototo sukayi