yasan yabar gida ba wata masarauta dazata baiwa iro aure shi kuwa baya had'a kanshi da talakawa, yanaso ne ya nuna masa kuskurensa.....tana dubawa taga Manga ta kira back da sauri dama tayita kiran number dinta bata shiga
"Ummu naa inasan nabar nan gidan ban gane me ake nufi da ajiye anan ba"
"Ki nutsu Auta gayamin kina ina yanzu?"
"Ummu nima ban sani ba wani gida kurun na farka na ganni ga gardawa da hadimai mata sunfi 30 a gidan hadda akwatin kayana, aciki ma na dakko wannan wayar tawa dana ajiye dan banga babban wayana ba"
"Tou ki saurara kiji,kakanki ne ya sanya aka b'oyeki sabida yanaso ya sanya lallai ALi Abbas ya sakeki, toki sani bazan iya haqura ba, bazan lamunci tarwatsewar rayuwar ku ba sabida haka nawa me martaba waya zezo gobe inshaa Allah, ki nutsu idan kakan naki yazo ki nuna masa sam ke bazaki komawa Ali Abbas ba, kema bakya so dama tsoro kike ji yanzu kuma tunda kinada gatanki abi miki haqqinki, zakiga ze saka a dawo dake cikin mutane ki nuna masa aje koma inane ke bazaki koma ba, ni kuwa kinga idan an kawo ki zansan yanda za'ayi in sace ki zuwa Niger dan na gano seda haka....."daganan ta kwashe komai na yanda akayi da mahaifin innoh dana baban manga ta sanar wa manga ta qara da cewar
"ko yanzu hankalin shi a tashe yake sabida bayasan sakin, kina addu'a kuma ki kula sosai kar wani yaga wayar hannun ki mu kasa gaisawa, zan saka yaro ya kiraki nanda mintuna biyar nasan kina buqatar hakan" da sauri tace
"Sosai Ummu,sosai nakeso inyi magana dashi ince ya kwantar da hankalin shi indai nice bazamu rabuba da yardar Allah" nisawa ummu ta qarajin tausayin su matuqa ta qudurta a ranta se inda qarfinta ya k'are.....
Manga na nan kwancen sega kiran Ali Abbas, dama kuma ta saka wayanta silent sabida tsaro, lumshe idanta tai tamkar yana ganin ta sannan ta sauke ajiyan zuciya datajiyo shi shima ya sauke fiye da nata kan yace komai ta soma kuka
"yaa Ali amma seda nace dakai zanbi Aunty ka barni na taho nan dabasa sona sam,yanzu gashi sun datse ni a wannan gidan sun hanani in ganka kuma nayi kewarka fa" ta qarashe maganar tana sheshekar kuka"
"Karkice zaki mun kuka mana Manga na, zaki qara d'agamun hankali ne fa,kinsan banasan b'acin ranki ko nan da can dan Allah ki kwantar da hankali, idan kikai yanda ummu tace qasar Nigeria ma bazani dake ba, Madina zan koma dake da zama gaba d'aya inda bame takurawa rayuwar ki kinji" shiru tayi ta tsagaita kukan tace
"Toni kamun labari bana jin dad'in komai kai kawai nakeso in gani" murmushi yayi ya soma mata wasa seda ta saki jikinta.....
Washe gari kuwa sega Shinan yazo da kanshi me martaba, cikeda da dabara Manga tagama ce masa batasan Ali Abbas bazata koma ba, ita koda ma su inno zasu koma nigeria bada ita ba dad'i kamar me ya dinga zabga mata albarka ya dauketa suka koma ainahin gidanshi...... Ba jimawa sarkin musulmi yazo daga sokoto da kanshi, en yamai ma sun qaraso aka zauna meeting akai akai yaqi amincewa da maganar su, haka aka kira ganin be yardaba ya sanya itama tace bazata koma ba, haka taro ya watse rayuka ba dad'i....Abinda be sani ba Manga daga fadar shi masarautar ta bari gaba d'aya ba tare da kowa ya sani ba, kai tsaye batare data dauki kayanta ko daya ba se wayarta babba da qarama da caja da jakar hannu.....tasha taje ta hau mota ta wuce Nigeria gaba daya abinta,message kurun tawa Ali Abbas akan tana hanyar Nigeria.....
Mom Nu'aiym
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
             25
Se washe gari su Ali Abbas suka bar garin gaba daya tare da me martaba, yayinda sargin yamai se masifa yakeyi akan sune suka sace Manga babu wanda yabi ta kanshi har Baban Manga suka had'o ba sallama suka sake baro masa gidan wannan karon baban Manga ya saka a rayuwarshi baze qara waiwayar gidaba ya kula sam mahaifinshi baze tab'a canjawa kuma yana shirin wargaza masa rayuwarshi data zuri'arshi baki d'aya,kuma mahaifin innoh ya bashi goyon baya a sokoto ya siya musu gida sannan yace tunda can Allah ya qaddari zaman nasu yaja jari abinsa yayi kasuwanci......
  Kallon kallo aka tsayayi tsakanin huddy da Manga bayan da Manga ta isa sokoto,
"Aunty huddy ina wuni?" shine abinda ta furta bayan da taga kallon bame qarewa bane,wani sheqeqe huddy ta kalleta ta zubar sannan tace
"Lapia lau,me kikazo yimun agida?" Mamakin kalamanta Manga keyi ta juya kawai zuwa d'akin dayake mallakinta tuni batare data bata amsa ba, itama huddy batabi ta kanta ba sabida aiki zataje ta wuce tana mamakin dawowar ta ayau bayan Ali Abbas yace shise washe gari, haka ta fice zuwa gidan batare data kira shiba a zatonta tare suka dawo, tana mamakin mesa ze turo mata manga gidanta bayan itama mangar tanada gidanta mallakinta wanda aka kaita cikinsa matsayin matarshi? Haushi kamar me haka ta qarasa office se mita take a zuci.....
Dayake dawowar mota sukayi yamma likis suka dawo sokoto,dama koda su Baban Manga suka zo anrigada an siya musu gida sedai se andan masa gyara kasancewar anginane ba wanda ya shiga anan fada aka musu masauki kan a kammala gyara, kai tsaye Ali Abbas part d'insu ya wuce Huddy yaci karo da ita a parlor tana shirin fita zuwa office kawar da kanta tayi daga dubansa batai magana ba, da kanshi ya qarasa gareta,harga Allah Ali Abbas yana matuqar san huddy ya kasa gane inda ta dosa a en kwanakinnan, kyakyawar runguma ya kai mata ya sumbace ta a goshi,hannu ya sanya ya tallafo hab'arta
"Baby ni kuma yau fushin me ake dani? Tun jiya nake kiranki bakya daukar wayana mesa? Murmushi ta sakar masa najin dadin yanda taga ya damu da ita sosai
"Kaine baka sanar dami tun jiya zaku dawo ba ai,se manga nagani kuma baka kwaba a gida ba" murmushi ya sakar mata shima
"Huddaisa nine nace dake tun jiya na dawo wlhy ni yau na dawo gidannan,da garin ma gabaki daya Manga ma da kika gani da kanta tai tahowarta jiya bazata iya zuwa yauba tace" sauke numfashi tayi tace
"Ina call ne kuma an kawo emergrncy yanzu akamun waya ga ambulance can ma tazo ta daukeni,so zan tafi sena dawo" qara matseta yayi sosai yace
"ki dawo da wuri my baby,ina buqatar kulawanki fa" murmushi jin dadin kalamanshi tayi ta hade bakinta da nashi adaidai lokacin da manga ta doso parlor din tafito dakinta,lobbyn ta koma da sauri girjinta ya soma dokawa da sauri bayau ne karanta na farko ganinsu a haka ba, amma lallai yau taji wani azaba dabatasan da akwai irinshi a duniya ba,hankalinta ya tashi matuqa,wani qololon baqin ciki ke mata yawo tsakanin cikinta da maqogwaronta ta kasa had'yeshi ta kuma kasa fito dashi.... Tanajin ambude kofar alamun Huddy zata fita ta fito tattaro nutsuwarta tayi gu d'aya bataso ya gane tace tana me rugowa da gudu
"Oyoyo yaa Ali" wara hannayenshi yayi yana dari ta fad'a qirjinshi da gudunta tana dariya,d'agata sama yayi yana jujjuya ta
"Hilwa na an qara nauyi kiga yanda nake gumi sabida na daukeki" ya furta daidai lokacin daya direta a qirjinsa bayan sun kwanta qasa ta masa rub da ciki suna shaqar numfashin juna
"Ni Gaskia karkace ina qara nauyi sabida banasan nae qatuwa kaje ka auromun sirirya tazo tana mun yanga" Huddy dake tsaye kallon kanta tayi yanda aure ya mayar da ita wata irin qatuwa tamkar ba ita ba, shi kuma dariya yayi sunma manta da ita wlhy manga ma ta zata ta wucene shisa ta ware suka jin dadin ganin junan su
"Hilwa kome zaki zama arayuwa nime qaunar kine a haka, ni sam bana san mace bushsashiya nafiso wannan qaton d'uwawun naki ya qara girma yayi goman haka ma" turo baki tayi cikeda shagwab'a tace tana me dukan girjinshi
"yaa Ali sam bakada kunya agaban kanka tsaye kanka cewa wannan abin" tsunkulinta ya shiga yi suka ruga d'akin da gudun su atare suna qyalqyala dariya, huddy dake tsaye jikin k'ofa share qwallan daya kwaranyo mata tai ta wuce kawai zuwa wurin aikinta rai a b'ace, wani azalzalallen kishi takeji mara misaltuwa...office ta rufe ta sanya kuka bayan ta isa, tafi 10 mnts tana kuka gata da Emergency case tunda waya ne aka mata, mamanta ta kira a waya tana d'agawa tace da ita
"Mommy wlhy bazan iyaba,kin mayi haquri dama haka kishi yake,wlhy mommy idan naci gaba da zama Manga koba itaba indai kiahiyace mutuwa zan, dan Allah ki sanya ko bokanki ne ya kashe auren Manga da yaa Ali wlhy na gaji bazan iya jure waba" wani qasaitaccen murmushi Mommy tayi yaudai zatasha dadin ta gashi har er ta tasoma gane kan garin,tunda har da kanta take zancen aje gun boka
"Yauwa 'yata dama na sanar dake bazak8 iyaba,wani aikin se boka d'an murus,gunshi zamuje nida haj mariya gobe da safe in saka ya kashe auren murus,kowa ya huta kinji yarinyar kirki,Allah ya miki albarka da kika gane wa ennan dangin na mayu mallake miki miji zasuyi" sallama sukayi sannan ta wuce zuwa office.
*Yamai*
Tunda aka bincika ba Manga ba dalilin ta hankalin sarki ya tashi, koda ya nemi a kira masa iro aka sanar masa baya gidan shima tun safe seya qara rikicewa, ganin dai har dare ba labarin dukansu ga wayanshi bata tafiya, ya gano sarai sun gudu ne shida ershi in kuwa hakane iro be kyauta masa ba akaro na biyu ya nuna masa ya isarwa kanshi,yayi bakin ciki matuqa,yakuma qudurta aranshi baze taba qyalewa ba,seya bi bayansu ai masarautar ta sokoto ba b'oyayya bace....
Ammin huddy taci nasarar zuwa gun bokanta inda ta karb'o wani ruwan da idan har huddy ta saka shi a abinci yaci, takumayi tsarki da ruwan tabashi na tsarkin yasha to kuwa baze qara ganin wata mace a idanshi ba se ita kawai, zeji ya tsani kowa.....
Kwance a saman jikin Ali Abbas Manga take tana wasa da kwantacciyar sumar data yi luff a saman faffad'an qirjinshi,idanta a lumshe yake tana jinta daban bazata kwatanta kalar dad'in datakeji ba a wannan yanayin, shi kuwa hannunshi nakan sumar kanta yana shafawa a hankali,magana yake mata da wata murya wacce ita kad'aice kalar sautin ke fita idan yana magana da ita shida kanshi besan dalili ba.....
"Manga bana san kowa yasan cewar Madina zamuje, inaso in samu nutsuwa mafi dad'in gaske atare dake,ki sani muna tare da mahassada iri iri a kewaye damu,kuma akwai masu bibiyrmu da mugun sharri sabida haka kowa ki sanar masa zaki koma Niger gun kakan ninki, akan wata sabga ta daban haka muka tsara dasu Abbu, ni kuma zanje lagos idan na wuce da kwana biyu seki biyoni baya a lagos din daganan semuje dubai mu wuce madina bayan sati uku" murmushi tayi tace
"Tooh yaa Ali,amma kwana biyun dazakayi da tafiya ka barni zanta kuka ma ko" dariya ya sanya hannu ya shafi nonuwanta
"Nima zanyi missing komai daya shafeki Hilwa,musamman abokanan wasan nan nawa guda biyu ina qaunar su sosai kuma bana so suna mun nisa" fuskarta ta cura a cikin qirjinsa alamun jin kunya tace
"yaa Ali kaiko tam shi kenan" cakulkuli ya soma yi mata ta zille tana dariya tayi hanyar toilet,manyan mazaunanta da heeps ya qurawa ido yanda suke juyi ya lashi lps dinshi ya qosa ya gansu a qasar saudi da ake wuni bacci, sesun sheqe ayarau, idan ma sukaje har phones dinshi kashewa zeyi a huta....
Washe gari Huddy har tasha taje ta karb'o saqon mugun abin da suka shirya itada uwarta, tazo tayi nasarar sanya masa a abinci yakuma ci sosai, har lokacin manga agidan take zama acewar sa kota koma gidanta tunda tafiya zatayi wahala ne kawai, ruwan maganin ma ta shige ktchn dama kuma tayi tsarki dasu ta boye a wani roba dan haka sirkawa kurun tayi ta soma juyawa,Manga datazo dakko masa ruwan na kallon ta da sauri kuwa taje ta kusa dashi ta zauna tana jiran qarasowar huddy har Abbas ya kula da rashin nutsuwar Manga din, se kallonta yakeyi suna nan zaune huddy ta shigo da cup a saman qaramin tray,yasani ba'a kawo masa ruwa haka dole se'a roba se mamakin ganin ruwa a cup yakeyi, bece komai ba ya miqa hannu ya karb'a, Manga na kallonshi harya kai cup bakinshi ya soma kurb'a ta rasa dalilin daya sanya ta kasa cewa karya sha.......
Mom Nu'aiym
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
   26
Ganin fa ze zuqa da kyau ya sanya da sauri tace
"Yaa Ali karka sha wannan ruwan karka had'iye plss zubar da wanda kasa a baki" besan mesa ya miqe ya fesar da wanda ke bakinshi ba yakuma wurgar da kofin dake hannun shi ya tarwatse ya wurin ya mayarda dubanshi gareta
"Meya faru da ruwan Allah ya soni ban shaba"
"Banaso yaa Ali na gaya maka abinda ke faruwa kazo ka tashi hankalinka abanza tu da Allah yasa bakasha ba aishi kenan" kallon ta yayi
"Manga banasan raini sanar dani meke faruwa" kallon ta ta mayar zuwaga huddy taketa faman zare ido tana had'a gummi tace
"Aunty huddy kin yadda ingaya mai?" zaro ido tayi
"Mezak8 gaya masa kuma? Aibeje canba tunda besha ba,kinga malama kiyi iya abinda ke gabanki kinj8 ni ba" dariya tayi sosai sannan tace
"Bazan tsura ido ina kallo mijina ya cutu ba sam, bazan lamunci a cutarmun dashi ba,kaga yaa Ali kasan mena gani?" kan yace wani abu da sauri huddy ta rufe bakin Manga jikinta se rawa yakeyi
"Me kike shirin yi ne wai Manga? Bakida hankali ne ki bari zamuyi magana tsakanin mu amma ba a nan ba" gyaran tsayuwarshi yayi ya kasa gane inda suka dosa ga uban gumi da take narkawa naba gaira ba dal8li duk da zafin sokoto ya sani sarai wlhy wannan sanyin na AC be isa kasa baiwa bawa ni'ima ba,cikin nutsuwa yace
"Huddy ki shiga hankalinki kina jina ai,Manga ke kuma sanar dani yanzu yanzun nan menene?? Meya faru da ruwan"
Koda Manga ta kalli huddy harta soma kuka ta sani wlhy aurenta ya qare daga ranar abin ma tsoro yake bata yanda ya faru so fast
"Kaga yaa Ali bari kaji bafa wani abin bane dama dazan shiga kitchen ne" rufe bakinta huddyn ta kumayi da hannunta tana girgiza mata kai alamar ta rufa asirinta,wannan karon manga ta harzuqa bige mata hannu tayi da qarfi..
"Bansan irin hakannan wlhy, idan ke baki san darajar mijinki ba nina sani, idan kuma ke bakisan lafiyarshi itace gatanmu ba toni na sani, gwara na gayamai me kikai masa sabida gove idan kin kawo mai ruwa a kofi ya dena sha,kinata wannan rawar jikin sekace wacce ke shirin yin kisa, kokinji nace kinyi wani laifi ne? Ki nutsu kinji ba yauwa" kallon Ali Abbas tayi
"D'azu ina zuwa kithen na tarar da wannan cup da irin qatuwar tsutsar nan me gashi aciki, masu sanya gabaki daya quraje su fito ajikinn mutum, shine fa nacewa buwa a jefar da cup din shine wannan matar ta hauni da zagi wai ba ubana bane ya siya mata kayan dazance a wurgar, nabata labarin illan tsutsar shine fa zagi ta uwa ta uba tace a jefar da tsutsan a wanke mata cuo din ta,yanzu sabida taga qarshena shine ta zuboma ruwa aciki,nikuwa bazan bari kasha ba wlhy" Kallon sa ya mayar ga huddy daketa mayarda numfarfashi cikin kasala, taji dadin rufin asirin da manga ta mata cox wannan dukme sauqi ne ai
"Mesa zaki kawon ruwa acup din to? Sabida kishi ne kokuma kasheni kawai kikeso kiyi?" matsawa tai kusa dashi ta kamo hannunshi
"Haba Abbi yazakace inaso in kashe ka? Nice fa hudaisan ka Abbi, wlhy mantawa nayi dabadan haka ba dana kawo ma a wani dan Allah kayi hakuri" murmushi ya sub'uce masa ganin dukta damu lokaci d'aya ya gaskata cewar kuskure ne da mantuwa
"Shi kenan a kiyaye gaba plss,irin wannan qwarin sunada had'ari kinga be kyautu ace ana mantawa da inda sukaje ba,gashi damunane be tsaya ba suketa yawo,zansaka ayi maganin feshi seku koma dayan bangaren na kwana daya" yana gamar fadan hakan ya koma cikin parlor din ya zauna abinshi......Juyawa huddy tayi dakinta manga tabi bayanta...
"Aunty huddy inasan sanin ruwan meye kika zubawa yaa Ali tare da swan kikeso ki bashi yasha?" kallonta huddy tai
"Manga wai ina wasa dakene?" murmushi manga tai
"Bakya wasa dani amma kina qoqarin cutar da mijina, na duba darajar su Ameer ne ya sanya kikaga na rufe tukunyar asirinki, wlhy kiyi a hankali da bin bokaye da malaman tsibbu inba haka ba wlhy nida kene a gidannan, sabida bazaki zauna kina cutar dashi ba a banza, daga kin gano matar ceni duk kin sauya halaye ina kallon ruwan da kika zuba a cup din baqi ne qirin kina sanya swan suka hade suka dawo fari, wlhy tsafine kurin zeyi wannan kuma kiji tsoron Allah kina aikata shirka a banza a wofi sabida san duniya" kasa magana Huddy tai tagano manga taga komai asirin ta kurun take rufe wa,juyawa manga tayi Ali ma dake bakin qofar ya koma ya zauna da sauri jin shiru alamune na juyowa za'a fito yana mamakin sauyawar halin huddy gakuma mamakin wai baqin ruwa ya sauya launi zuwa fari a cup, manga na fitowa tagama fusata shi d'inma bata kalleshi ba ta nufi d'akinta, tana zuwa dining ta manta zancen kwalbar cup data fashe ta taka daya qara ta k'walla ta sunkuya a wurin riqe da qafar, da sauri ya taso yazo ya riqeta yana tambayar ta lafiya, qafar data riqe ya kall,glass din ya kafe a ciki yana ta zubar jini, ya sake kallon ruwan a saman farin tile din sunyi baqin qirin dayan barin kuma fararen ruwa na gangara wanda sukai baqin kuma sun cure wuri d'aya, mamaki sosai yake huddy kasheshi zatayi kenan?? Akan tagano tanada kishiya anya ba manga ya dace tai wannan haukan ba kuwa? D'agata yayi zuwa kan kujera ya cire mata glass d'in a qafanta sannan yace yana share mata jinin da hanky dake hannunshi
"Baki kula da glasa d'in bane Hilwa?" qwallan datake tarewa ne ya silalo mata ta sanya hannu ta share su sannan tace
"Shap na manta wlhy banma kulaba" cikin tausayi yace
"Sannu Hilwa inaga se munje chemist ko hospital ma deep ne abin" kwab'e fuskan ta tae
"Yaa Ali me zasumun acan,dan Allah karka kaini,ka sanya mun kananzir jinin ze tsaya" harara ya wurga mata
"ke kina haukane kananzir kinsan chemical nawa ne aciki,maza ni ki tashi mu tafi" tabare fuskan tayi lokaci d'aya sega hawaye sharr be kulata ba ya d'agata suka bar gidan zuwa hospital har lokacin yana tsananin mamakin mugun abinda huddy ta aikata masa ko meye ribar ta oho......
Har akai kwana biyu baya kulata tayi ba ban vaki har ta gaji ya gagara sanar mata me kunnen sa ya jiye masa, ko Manga be sanar wa komai ba game da yaji zancen su, haka ya shirya ya wuce batare daya koda kulata ba ko mata sallama, abin duk yabi ya dameta, Manga ma bayan kwana d'aya ta sameshi a lagos da jirgi ta tafi....
Ammyn huddy ce tsugune a gaban boka tana sanar masa komai yanda ya faru, bayan ya gama saurarenta ya soma bugun qasa da kuma bincike binciken sa, a haka ya gano tare sukai tafiya ma suna dubai, ya gayawa Ammyn huddy ya qara da cewa
"Aljani zan tura ya shiga jikin ta ya sanya tae wata qasar daban daba tamuba bakuma inda ya dosa ba dan daganan Madina zashi, to tsayawa saka masa qiyayyar ta b'ata lokaci ne sabida haka zamu sauya akalar rayuwarta zuwa wata duniyar tare da sanya mantuwa a cikin kanta na duk wani abu data sani har abada" murmushi Ammyn huddy tae
"Madallah mun gode, yanzu meye ladan aikin?" wani zabura yae yace cikin ihu
"Mahaifar erki shine ladan aikin, idan kinso ki amince nizan tura a cirota idan kuma kinso ki gayamata, sedai zata iya yi mana gaddama"
"Nima 'ya'ya na nawa a duniya, ta samu mace da namiji, sun isheta rayuwar duniya aciro mahaifar aiba dole" wata mahaukaciyar dariya ya kwashe da ita yace
"Kije angama karki damu!!!" haka tabar wurin tanata murna ta sanya a ranta seta sanya anma kasheta gaba d'aya kowa ya huta kawai..
Kwance manga take asaman doguwar kujerar dake cikin parlor d'in, sanye take da yaloluwar rigar bacci iya gwiwa,tayi kyau matuqa sosai acikin rigar sumar kanta baje saman throw pillow na kujerar datake kai, wayanta take danna wa sanda ya shigo ya je ya janye sumar kanta data baje a kanta ya sumbace ta a goshi sannan yace
"Hilwa er dubai, kinga yanda cikin kwana ki biyu kikai fresh kuwa,lallai ke ba kalar Nigeria bace bazamu koma ba" Murmushi tae ta sanya ta shafi sajen fuskarsa,sunyi kusan dasuke jiyo bugun zuciyar junansu tace
"Kasan dai kafini jin dadin qasar nan, kalli yanda yanda kai kumatu,kuma Allah na iya kula da miji,a jikina fa kake bacci har safe,gashi kuma abinci ma sekace se a baki" dariya yayi yace
"Dakike ta tatsa na kamar me,kinga ni wanka zanyi zo muje ki tayani" murmushi tae
"Sanyi nakeji Yaa Ali, kaje kayi kayanka,idan ka gama zan tayaka shiryawa" hancinta yaja
"Zaki shafamun mai da turare da komai da komai" murmushi tae
"Rigima dai kakeji, yau ba wani wanka dazan sakaka,sedai kai ka sakani "
"Dama kin huta abinki, Auwal friend d'ina yana waje yana jirana, zamui wani lissafi" dariya tayi
"Ba komai kazomun da ice cream" wucewa yanayi yana murmushi da tsananin jin dad'in rayuwar dayake da Manga ya jima sosai yana tafkawa kanshi kuskure da qwarar kanshi" Kamar an tsikari Manga haka taji, haka kawai ta dire wayarta tayi hanyar waje, kofar d'akin ta bud'e ta fito ta soma tafiya gashi batada maraba da tsirara ita kanta bazatace ga inda ta nufaba, tadai san cewar babu nutsuwa akanta bata tunano komai daya shafi rayuwa......
Auwal daya ga manga mamakine ya kamashi amma ganin ko horn aka mata ta tsayawa se tsallaaken titi takeyi ya sanya ya fara tunanin da wata matsala binta yakeyi da qafa lokaci daya yana dannawa Ali Abbas kira ba qaqqautawa shi kuwa se faman shiri yake a gurguje yaqi daga wayar gani yake tamkar dan yana jiranshi a waje ne ......
Wata motace tasha gabanshi, kafin ta d'aga ya duba qasa da sama bega Manga ba, har tsorata yae ya soma ambaton Allah, yasan yanda me gidanshi kuma abokinshi ke tsananin qaunar Manga ya kuma kula sosai batama san inda kanta yake ba, adaidai lokacin ne wayanshi ya qara da sauri ya d'aga ganin Ali Abbas
"Auwal baka reception?" murya na rawa yace
"Yallab'ai, Manga ne ta fito da wannan rigan bana tunanin tasan inda kanta yake, gani nan kan hanyar dera market kuma ta b'acewa gani na sam, mota yakai biyar daya kusa kad'ata" tunowa yae dabe ganta a parlor ba kuma bata daki,wato sabida yana sauri be kula bata dakin ba da sauri ya ce
"kaman ya wai kana nufin da wannan rigan ta fice,yanzun nan muka gama magana, yanzu tsaya ma kai kana ina?" misalta mai komai yayi ya soma tiqar gudu zuwa hanyar...... Yayinda Auwal neman duniya yayi be ga koda me kamar Manga ba!!!!!!!!!
*Fan' s ina godiya da qauna, se kuma bayan sallah idan Allah yaso* Allah sa manga ta bata,haba haka kawai tazo ta raba masoya
#Team Huddy sak# Ana tare.
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
    27
Koda Ali Abbas yazo adu'a d'auke a bakinshi sabida iya tashin hankali ya shiga ciki,Â
"Ina kaga tabi ne?" ya tambaya a razane kanya bashi amsa ma ya hangota wata mota na shirin kad'e ta wani balarabe ya sanya hannu ya janyota da qargi ta fad'o j8kinsa, wani sanyin ganinta yaji lokaci d'aya wani azababben kashinta ya tasowa Ali Abbas da gudunshi ya nufeta har tsere suke shida yaron nashi karban ta yayi yana isa yace yana kallon ta "Hafsa lapiya kuwa? Mesa kika fito kuma a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 16