Share this page
saurarar wawtar ta yana dariya ba, da zaran ya tuna sanda tace mai wai yaya me rawani se dariya ta taso masa, bare yanda tace dashi "Da lunch box nake zuwa skul" da zaran ya tuna girmanta da yanda zata rarumi kula zuwa skul seyayi murmushi, har mamakin kanshi yakeyi abune mawuyaci ka ganshi yana murmushi bawai yanada baqin rai bane  nooo yakan jima beyi magana bane bare yayi murmushin ma.....    Zaune gadanga yake akan tebur dake tacikin harabar ajiye motocin gidan sanda Manga ta rugo da gudu tazo ta tsuguna kusa dashi tace "Yaa mu'allim gadanga barga da safiya" kallonta yayi yana murmushi dayake jimawa yanayi idan ya soma sannan yace "Manga ni wannan sunan yanamun tsawo, ki zab"a ko yaa mu'allim ko kuma yaa Gadanga" murmushi tayi "Tunda baban Manga yace ze baka aurena gwara kawai ince yaa gadanga Ango" kallon mamaki ya mata sannan da qyar labb'ansa suka iya furta "Aure kuma Mangan Innoh?" murmutayi "Ea mana, haka yace da Innoh a gabana,wai soyayyya muke kuma kai malamine, dan haka kuwa ze bakani ka aura, yaa Gadanga ni qawayena sunada saurayi suna bani labarinsu amma ni banida saurayi, ance da saurayi ake soyayya tonikam kaine saurayina tunda Baban Manga da kanshi yace muna soyayya" kallonta ya tsayayi harta idar sannan ya kawadda kanshi gefe d'aya ya soma magana a hankali "Manga banasan shirmen kinnan, kije ki nutsu kiyi karatu, bakince lauya zaki zamaba? Karna qarajin zancen soyayya a bakinki ko wani aure a yanzu, komai kikaji an fad'a sekinzo kina fad'a kokuma shi Baban Manga shine yace kizo ki sanar dani zancen da sukayi da Innoh?" narai narai tayi da ido sannan tace "Baya so na fad'a ya gaya a gabana, aiba komai bane kai kad'ai na gayawa se qawata Nana khadeejah, kuma tace mun dace da juna tunda kai kyakyawane,nikam indai zamu aure ka dena tafiya kana barina tonama dena zuwa makarantar daga yau, bakaji yanda nake san in ganmu a tare ba" shiru yayi sabida ya fahimci yarinyar sanshi take batare datasan da hakan ba, sam batada wayo ko kad'an,shi tausayi take bashi sosai sabida ya kula duk inda zama ya had'a da mutane zatasha wahala kasancewar tanada surutu harna wawta,batasan meye sirri ba sam!!.....bece da ita komai ba harta bar wurin jin Innoh na qwala mata kira..... Kwana bakwai kenan ta tafiyar Ali Abbas wani yammaci su gadanga sun idar da sallah a masallacin kofar gidan da isha,Ali Abbas ya qara dira a gidan, yau kam ajikin shigar qananun kaya yake dasukayi matuqar karb'ar fatar jikinshi....yayi kyau ainun yakuma qara haske da jiki ba laifi, Manga ce ta wangale masa gate d'in kasancewar Baban Manga yana masallaci har lokacin be fito ba, ita bata ganeshi ba shine ya ganeta yana parking ita kuwa harta qarasa rufe gate d'in zatai cikin gidansu tajiyo muryan shi "Hafsatu Manga, zo mana" juyowa tayi babu wani duhu kamar yanda ba wadataccen hasken dazata ganeshi kai tsaye beside ranar cikin rawani yake,sedai muryan ya mata kamar ta wanda ta sani, takowa tayi tazo tace "Waye gani?" murmushi yayi yace "Yayan kine Ali Abbas" washe baki tayi "Laa yaa me rawani yau kai kad'aine ina d'an banki to?" murmushi yayi yace "Zance nazo gun Huddy ki kiramun ita" kallonshi ta d'anyi tana murmushi "Nima nayi sabon saurayi sunanshi Gadanga yana masallaci, amma baya zuwar mun zance, zaku gaisa idan ka fito ko?"murmushin dai ya qarayi yace "Lallai ma yarinya ke yanzu har wani saurayine dake, naji to idan na gama zanzo mu gaisa,yanzu maza kimun kiran huddy, ki sanar mata ina sauri ne" batace komai ba ta kwasa aguje zuwa cikin gidan, kowa yasan halinta dan haka ba wanda ya damu da yanda ta shigo aguje, ta daiyi sallama kanta isa parlor d'in, ba wanda ya ansa sallamar tata se Ummi datace "Ke Mangan Inno me kikazoyi anan yanzu kuma,neman tsokana ko" kallonta tayi dama ita bawai ishashiyar nutsuwa ce da itaba tace "Nikam dama mezan zo na muku yanzu, Wannan me rawaninne yace azo akira masa Aunty Hudaisa, kuma yace a sanara mata yana sauri ne karta dade" da sauri huddy ta miqe tsaye zuwa cikin dakin domin gyara kanta, ba wanda ya kuma bi ta kanta se kallon hujaima tayi tace "Su hujaima musulman loko, ana nan ana karatun Allah badonshi ba sedon gudun bulalar yaa mu'allim" takaici hujaima taji tace "Ummi kinji manga waiba dan Allah nake bitar karatu ba" kallonta ummi tayi zatai magana manga ta rigata "kaji wawiya yo koni ai gudun bulala yake sanyawa nake bitar, ko babba kikaga yana zuwa makaranta yana bita idan dai beyi dan gudun duka ba dole zeyine dan gudun kar amar dariya" dariya ta baiwa ilahirin mutan parlor din ciki kuwa hadd hussy da farouk, suna shiri da hussy sosai kusan sa'anin junane, suna nan har huddy tafito ta wuce su....seda ta gama tsokana da sakasu dariya tukunna sannan ta fito a tsaye ta taddasu matsawa tayi kusa dasu tace "yaa Ali kaga sarkin zagwad'i ta riga er aiken zuwa ko? Kan na gama fad'a ma ta miqe, kayi sa'an mace kyakyawa kam" mamakin surutunta yake sekace wacce aka aiko ji wani shirme,ya sani kuma huddy taji kunya danyama kula da hakan, se yace cikin siqar wasa "Dama mana ina zagwad'i nazo ita me kikeso tayi ne? Nafita ai nida nazo" tab'e baki tayi "To Allah shibar qauna,yaa Ali ni nayi nan" takama hanyar gidansu be tsaidata ba ya kalli huddy yace "Huddy?" kallonshi tayi batai magana ba "ki dena damuwa da maganganun manga idan kin kula batada nutsuwa kuma tanada tarin quruciya akanta, abu d'aya zan sanar miki shine ki dena dukanta,iyayenta bazasuji dad'i ba ina horonki daki girmama talaka, da wannan halin kadai zaki samu karbuwa a masarautar mu, da kuma birnin zuciyata" murmushi tayi har hushiryarta ta bayyana tace "Zan kiyaye inshaa Allah" Mota ya bude ya dakko wata leda ya miqa mata, hannu biyu ta sanya ta karba sannan yace " Akwai waya da sabon sim aciki, tawace ni kadai, koda wane lokaci ki kasance riqe da wayar banasan tarin msd calls ba'a daga ba, bana san ganin call waiting kuma gwara nini kadai, sauran kayan kuma duk nakine,kiyi hakuri ranar ina uzuri ban tsaya mun gaisa da ke ba" fara'arta ta fad'ad'a sannan tace "yaa Ali nagode Allah ya qara girma da d'aukaka,Kariyar mahalicci tabika a duk inda kake, Allah ya sanya Alkhairi acikin tarayyarmu dakai, nagode sosai ba adadi Allah ya qara bud'i" murmushi yayi har cikin ranshi yanajin dad'in adu'ar huddy, yasani bezo da shiri. Santa ba, be kuma zo da shirin qiyayyarta ba sedai fa ya kula sosai soyayyar ta naso ta rinjaye shi,kyaunta yana burgeshi, kalamanta masu hikima na masa dad'i,tanada girmama mutane wannan ma ya masa...... A haka sukai sallama ya juya ya tafi...... Shiru gadanga yayi bayan ya gama jin bayanin Baban manga, tabbas baze iya yiwa baban manga musuba akan auren manga, kazalika sam baze iya cewa tsakanin santa da rashin santa wanne ne yakejiba, shidai abu daya ya sani bayasan rawar kan yarinyar,da uban surutun datake dashi, anso mutum ya auri mace me sirri yaya zeyi da auren Manga????? Da qyar ya iya tattaro nutsuwarshi yace "Ba laifi Baban Manga, ina godiya sosai da karamci Amma ina roqon alfarma abani lokaci kasancewar takamammen wurin dazan ajiyeta banida shi gashi kuma se anyi suturu da sauransu, zanso kuma ta kammala karatunta tukunna" murmushi Baban manga yayi "Babu komai gadanga, Allah yashige mana gaba,ya hore abin lalura, nidai alqawari d'aya zakamun shine ko bayan raina zaka auri manga, kadaiga manga batada wadatacciyar nutsuwa nayi mata sha'awarka ne sabida na kula duk abinda ka lurar da ita to tanabi, kaga kuwa zaka saisaita nutsuwarta inshaa Allahu" gadanga yaji tamkar an daura mai wani dutse aka, nauyin ya masa yawa matuqa,ina zeje da girman alqawari,kalmar aminta da qudurin baban manga tamasa nauyin fad'a a harshe wanda harya sanya yai shiru.... "Malam Gadanga kayi shiru, ina fatan baka tunanin inaso na maka dole ne?" murmushi gadanga yayi yaji kunya matuqa tamkar me koyon magana haka ya furta "Ba haka bane Baban Manga, nayi alqawarin Inshaa Allahu zan auri Manga ko bayan ranka" dad'i yaji matuqa yashi masa albarka sannan suka shiga masallaci domin gabatar da sallah isha..... Ko kad'an Gadanga be shirya aure ba yanzu, badan bayason manga ba sedan kawai yana ganin lokacin aurenshi beeyiba, mema ze cewa iyayenshi? Kodai kawai ya bari se an daura ya sanar dasu? Haka gadanga ya zauna cikin rashin sanin abinyi,tunaninshinya tsaya cak, yana matuqar dana sanin abubuwa da yawa, ya zanyi da manga???" wannan itace tambayar dayakewa kanshi ba qaqqautawa....... *Bayan wata hudu* Su manga sunyi candy amma har yanzu ba hankali kam,se du'ayi kawai, Dama skul d'aya take zuwa dasu hussy, kuma tunda ga ranar da Baban manga yayiwa Gadanga maganar Manga be qarayiba shisa ma hankalinsa ya kwanta ya dena neman solution gaba daya.....yau yana zaune asaman bencin daya saba zama Baban Manga yamai sallama, suka gaisa cikeda girmama yace "Gadanga dama zancen aurenka da Manga ne, kuma narigada na sanar da Alhj tuni, na sanar masa kaine ka zab'i seta kammala karatu gaba d'aya,tunda ta gama shine yamun zancen jiya akan na tuntub'eka aji ta bakinka" gabaki d'aya seda gadanga yaji tamkar ba'a duniya yake ba, sam be zata Baban Manga zewani gayawa me gidan su ba, yama rasa me zece seda yakuma cewa "Gadanga kayi shiru" nisawa yayi yace "Baban Manga ad'an qaramun lokaci, har yanzu ban gama had'awa manga kayan lefe ba, ban shirya wurin zamanmu a garinnan ba,tunda kaga ai nan nake aiki,bazeyiyu nakai Manga soba ba" nisawa yayi yace "Gadanga na fahimci damuwarka amma Alhj yace anan bayan gidan zaku zauna tunda kaga ba samari ne dashiba se faruk kad'ai,kaga kanaci gaba da aikinka, yakuma ce bayasan ka mata komai shine ze muku har kai, A sanshima jibi juma'a daurin aure,sekayi haramar sanarwa iyayenka" qirjin gadangane yayi mugun dokawa yasani sarai iyayenshi bazasu tab'a amince masa auren manga ba, tayaya ma ze tunkaresu da wannan maganar tunda yanada zabinsu ajiye? Ina zekai girman alqawarin daya d'aukar wa Baban Manga? Ta ina ze soma juyawa kanshi? Gyaran zamanshi yayi yace "Baban Manga, na sanar maka ni mutumin zaria ne a qauyen soba nake, banida kowa uwa ko uba duksun mutu, qanin mahaifinane zan masa waya yazo da kawuna, amma juma'a batai kadan ba, kuma ita Manga bata ra'ayin yin wani shagali ne? Zancen sadaqi dai zan biyawa kaina inada halin yin hakan" murmushi Baban Manga yayi yace "Ka rabu da manga ba hankaline ya isheta ba,kuma ba wani bidi'a da za'ayi, iyayenka kuma ai badamuwa ko basu zoba dama nine waliyinka Alhj kuma shine waliyin Manga shine da kanshi ya fad'i hakan" murmushi Gadanga yayi ya masa godiya sannan ya wuce Gadanga nasan Manga indan so,amma sam yasan aurenta babbar matsalane shida danginshi,juma'ar nan fa jibi ne? Saura kwana biyar aurenshi kenan yaya zeyi? Haka yayita saqawa da warwara harya daure dai ya sanarwa wanda ya dace suzo din..... ALi Abbas ma da Huddy aurensu nanda 4 months masu zuwa, shirye shirye tsakanin sokoto da kaduna ba'a magana an shiryawa bukin auren ba kad'an ba komai yaji a yanayin shirye shirye lokaci kawai ake jira,dama huddy ba yarinya bace,itace 'ya babba acikin 'ya'yayen Alhj Tahir Maude,bashida manyan yara maza farouk ne kawai yaronshi namiji kuma qaramine sosai, yanzu haka huddy shekarunta 32 a duniya,mijin aurene bata samuba se yanzu........ *Rana Bata qarya* Ranar juma'a kuwa kawun Gadanga da kuma qanin mahaifinshi sukazo daga soba aka d'aura auren Manga da gadanga, akan sadaki Naira dubu 30, duk yanda kike tunanin manga tashiga farin ciki abin ya wuce nan, sosai takeji da gadanga zama mu iya cewa tama fishi d'okin auren, anyi wuni ranar asabar batare da d'an uwan Baban Manga ko daya yazo ba kona Innoh kasancewar tunda ya baro gida be waiwaye su ba, Amarya tayi kyau ba laifi dama gata kyakyawa er jan buzu....a ranar aka miqa ta a BQ dake bayan gidan,wurin sahibinta gadanga..... *Yazo mata da kaji na ban mamaki har guda uku gasassu da yoghurt,yakuma kawo mata sababbin kaya akwatuna guda uku wanda ta tsorata da gani, acewarshi shine yafi cancanta yawa matarshi suturu.....ranar dai duk surutu irinna manga batai masa shiba har tsokanarta yake yau ina bakin amma takasa koda kallonshi ne...... Duk yanda Gadanga yaso ya had'a jikinshi da Manga ya kasa, zancen gaskia yana mugun qyamar yanayin warin buzaye,kuma harya zamewa Manga halitta,duk kuwa dayake cewar sunada tsafta sosai wannan ne ya sanya yakecin abincin su,amma dai yana yin qmashin nasu be masa ba sam.....da wannan ya sanya bayama kwanciya wuri daya da ita....so kawai yakeyi ya zauna ya natsu seya riqa koyar da ita yanda zatayi amfani sa turarukan da yake so da kuma yanda zata riqa kwalliya kalar wacce yakeso ya shirya wayar da manga dan dai yana santa matuqa......haka suka rayu da juna cikin kulawa daso da qauna, zuwa yanzu gadanga ya gama sakankancewa yana qaunar mangan shi..... *Bayan sati uku* Waya akawa gadanga akan qanin mahaifinshi baida lafiya sosai, a haka ya shirya tafiya zuwa duboshi Kallon shi Manga ta tsayayi tana kokarin tare hawayenta sabisa Inno ta sanar mata yanzu ta girma ta rage quruciya, amma sam ta kasa karo na farko daya rungumeta a jikinshi sosai yana bubbuga bayanta a hankali "Kiyi hakuri Hilwa (sunan dayake kiranta dashi kenan tun bayan aurensu, kalmar Hilwa yana nufin kyakyawa kenan da Larabci) gobe zan dawo inshaa Allah" d'ago da kanta tayi tana hawaye tace "Yaa Gadanga zan bika dan Allah,banaso ne ko kwana d'ayan kayi, ko masallaci kaje Allah Allah nake ka dawo, kuma idan ma kaje makarantar koyarwa har kuka nake,yaa gadanga kwana fa zakayi, dan Allah kaje dani" tausayinta yaji ba yanda za'ai ya tafi da ita duk yanda yaso,rungumeta ya qarayi "Hilwa kiyi hakuri, daga zaran naje yau ni kad'ai duk inda zamu na miki alqawarin tare zamuje,bakya ganin nima zanyi kewarki sosai.... Girgiza masa kanta tayi "yaa gadanga dan Allah kamun rai ka tafi dani, wlhy kewarka zata hallakani,bazan iya kwana gidan ni ka daibama" zuwa yanzu shima seda yayi kwallah, yace "Haba Hilwa,kingafa abinda yasanya bazanje dake ba,banida kudin motan dazamuje mu biyu mu dawo shisa" d'ago kanta tayi "Zanje na karb'o kud'ad'ena dana baiwa Inno ajiya semu tafi tare" Hannayenshi duka biyu ya saka ya tallafi fuskarta yace "Hilwa kinaso nayi fushi dake?" da sauri ta girgiza kai alamar aa, yace "Yauwa to idan bakyaso nayi,karna tab'aji kin dauki sirrinmu kin gayawa wani, idan inadashi sirrin mune, idan banidashi sirrin mune, idan muka samu sab'ani sirrin mune base kowa yajiba, idan muka tattauna matsalolin mu ma sirrin mune, ina fatar kin fahimceni sosai, banso koda su innoh kike gayawa sirrin mu,Zancen tafiya kuma kiyi hakuri namiki alqawarin wata rana tare zamuje" shiru tayi amma se kukan take haka ya saketa ya dauki jakarshi ya juya haryakai kofa taje ta rike mai kafa tana roqonshi "yaa gadanga kewarka zata kasheni dan Allah kamun rai, kaje dani wlhy zanyi kewarka kuka bazemun magani ba" yaji tausayinta matuqa jiki a sanyaye yace "Jeki dauki kayanki qwaya biyu kanna taro mana a daidaita sahun dazeje damu tasha kinji?" da sauri tayi ciki tana murna...... Sallama yawa Baban Manga ya wuce da sauri yabar unguwar akan babur...koda manga ta fito zatawa mahaifinta sallama seya sanar mata ai gadanga tuni ya wuce kuka kam tashashi, wayarta ta dauka tayi kiran wayar shi amma sam bata tafiya,tasha kuka kam a haka ta hakura tunda gadanga ya mata wayooo...... Ali Abbas yanata shirye shiryen zuwanshi kaduna gun huddy, ta isheshi da rigimar san zuwanshi akan tayi missing nashi sosai, duk yanda ya tuna huddynsa se yayi murmushi yarinyar tana burgeshi, banda halinta daya kula sam batasan talaka batada makusa a gunshi yana yabawa kyawawan d'abi'unta matuqa......kai tsaye gidansu ya wuce yana mamakin rashin samun wayarta dabayayi tunda ya taso, hakan ba d'abi arta bane indai yana hanya ta soma kiranshi kenan ba adadi... Baban manga ya wangale mishi gate yana danna kanshi cikin gidan ya hangosu tsatsaye har huddynsu da maminsu,da amminsu su farouk dama Alhj tahir mahaifin su huddy....beyi qasa a gwiwa ba yaje ya gaidasu suka amsashi cikin sakin fuska, yanaso yayi shiru amma ganin Manga nata kuka ya sanya ya tsaya,yaga kuma kowa yayi cirko cirko ana kallonta bame magana har wacce yake tsammanin itace uwarta kasancewar suna matuqar d'iban kamanni.... "Hafsatu Manga lafiya dai kukan kuma na meye ne?" Alhj Tahir ne yace dashi "Wlhy Ali mijintane ya b'ata yau sati uku, annemesa an sara, daga sunan zuwa gida gaida kawunsa da bashida lafiya yau sati uku,shine fa dukta tashi hankalinta haka" rike bakinshi yayi yace "Manga tanada aurene dama?" murmushi yayi yace "Dududu auren fa sati shida yanzu inaga, baka taba haduwa da mijin ba duk zuwanka,shine malamin dake koyar dasu karatun islama anan,yana kuma kula da shuke shuken gidan da wankin motoci" shiru ya d'anyi kanyace "Naje gidansu kuwa?" cire hula daddyn huddy yayi yace "Nanfa d'aya mundai san dan Zaria ne a qauyen soba,amma babu wanda yasan gidansu, kawunsa ma da qanin mahaifinsa dasukazo daurin aure ni bazan shaidasu ba idan na gansu, Anan muka hadu yazo neman aikin koyarda yara islamiyyya kuma banan yake kwanaba, mundai yaba da halayyarshi ne muka baiwa manga shi a matsayin miji" nisawa yayi yace "Hakane amma daddy mezai hana aje soban a bincika aji ai yafi ko kuwa?" "Munje tashar motar dake kai mutum soba ma, babu zancen wai suna daukan record, yanzu zancenka zamubi muje soban tunda ba wani nisa zuwa zariya, akira idi direba" sosa kanshi yai yace "Manga ai er gidanace, gwara nazo na biku daddy, na nemo mata mijinta kalli yanda take kuka hadda majina ko kunya" ya qarasa maganar cikin sigar tsokana, murmushi tayi kurin sabida tana cikin damuwa.....koda sukaje soba cewa aka musu babu wani suna me kamada wannan bare kawunnan shi ba wannan sunan a soba, kansu ya matuqar d'aurr suka juyo amma daddy ya hana a gayawa iyayenta kurin yace dasu dai basu gane iyayenshi ba a soba...... Haka dai Manga tayita hakuri tun ana jiran tsammanin dawowar gadanga har aka cire rai, kowa har daddy suka alaqanta b'atanshi da mutuwa, bazasu ce sun zagaye garin sobaba kuma a yanda malam gadanga yakeda sanin Allah baze tab'a yiyuwa ya aikata hakan ba, tunda da suka binciki yarinyar ba ba abinda ya tab'a shiga tsakaninsu idan ma mugunta ze mata aima shine ya nemi aurenta ba kumama ai daya ajiye takardar sakinta ya gudu, suna dai sakaran hatsari yayi bame kawo labarinshi, matsalar kuma har wanda yake kawowa ya wakilceshi idan baya nan ya sanar musu cewar baida labarin gadanga...... Manga gaba d'aya tayi sanyi tazama shiru shiru, dukta rame gwanin tausayi ba qaramin so takewa gadanga ba, bataji zata rayu idan har wai yanda ake zargi ya mutu ya mutu din, dukda yake ta gagara yadda da mutuwar tana gani ko yaushene ze dawo gareta inshaa Allah..... Saura sati biyu bikin huddy da Ali Abbas yazo kd, sanyawa yayi aka masa kiran Manga yace huddy ta basu wuri, ita bata kawo komai arantaba sabida tasani Manga tanada auren wani akanta, takuma sani tausayi sosai manga ke baiwa Ali Abbas, acewarsa yarinya me san wasa da raha duk ta zama wata iri daban, zama tayi bayan ta shigo parlor din tace cikin sanyin dake qoqarin zame mata d'abi'a "Barka da yamma yaa Ali,anzo lafiya?" kallonta yayi sannan ya nisa ya sanya hannu ya shafi sajensa sannan yace "Manga inaso kiyi hakuri da abubuwan dasuka faru a arayuwarki tunkan ki qarasa mallakar hankalinki, ki sani shi Allah haka yake al'amuranshi, kowace rayuwa tana had'uwa da jarabawa iri iri,hadisi ya inganta akan yadda da qaddara ta alkhairi data sharri, nasan bazaki rasa karanta hadisi na biyu ba acikin arbawuna hadith inda ake bayani gameda imani, anan aka bayyanar mana yin imani da kadddara ko wace irice, "wa tu'uminu bil qadari hairihi wa sharrihi" kinga anan zaki zama me imani me kyau akan yanda da kika dauki kaddararki dazamu iya kira mara kyau, dukkuwa dayake bakida masaniya gameda tanadin da mahalicci ya miki, nasani Manga baze yiyu inganki kamar da ba amma ki sani bazanso ganinki haka ba, ki nustsu dan Allah ki fauwalawa Allah lamuranki, ga waya nan nazo miki da ita, akwai number na aciki, dukkanin buqatunki kina sanar dani karkiyi shakkar komai ni yayankine, nayi magana da mahaifinki da daddy sun amince dana kula dake ba laifi bane, kuma banasan gaddama karnaji kin tambayi wani komai ni nan nine zaki kira zan miki komai,kuma idan har mijinki be dawo ba, aka soma daukar dalibai a jami'ar sokoto zaki koma gun huddy kici gaba da karatunki har Allah ya bayyanar da mijinki,kindai ga ai kece babba awurin iyayeni, kiyi karatu ki zama wani abu sabida ki taimaka musu, idan kuma ya dawo Alhamdulillah dama fatanmu kenan, idan yayi ra'ayi zan roqeshi ya barki idan bayaso ki hakura shine mafi aala.....godiya sosai ta masa sannan takoma b'angarensu domin tuni wuri su inno take kwana..... To masu karatu,ko ina Gadanga ya shiga?? Nifa tunani na ya tsaya cak!!!! Alqalamina se rawa yake ina kyautata zaton yanzu aka soma wasan......... Vote and comments plssssss [7/6, 8:07 AM] ‪+234 706 571 7620‬: *Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)* *👑ALI ABBAS 👑* Billy galadanchi Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*    Zeeyy qaseem,wannan shafin kuma nakine,Allah bar qauna....        03 Shagalin ya soma kankama,yayinda sam Manga bata wani d'okin bikin, mosti biyu da uku duk gani take tamkar zataga Gadanga agabanta, duk tayi rama tayi fayau da ita, yayin biki babu wanda daddy be mataba, gani yake tamkar komai shine sila na lalacewar rayuwarta mugun tausayinta yakeji, duk yanda sukaso ta sake jikinta abin yaci tura, zuwa yanzu yawan shirun datake ya sanya hatta Ummin su huddy tausayinta takeji, a wurinta ma take zama ba wurin Innoh ba, Allah ya d'aura mata tsananin qaunar gadangan ta ba iyakaa......   Anyi biki na gani na fad'a wanda har mamakin yanda ake dirzar naira Manga keyi, ranar da aka daura aure ranar akaje dinner, Ango gabaki d'aya ya gama rikicewa yaudai yasha qudurin nunawa duniya yanasan huddynsa.... Bayan sun ciyar da juna da weeding cake nasu da juice, sekuma suka juya wurin rawa rungume abarsa yayi ya riqe hannunta d'aya suka soma juywa a hankali abinsu....Runtse ido Manga tayi tana tariyo ranar da zasu rabu da gadanga rungumar daya mata, abin ya matuqar tsaya mata a wuya,wannan rawar dasuke bazata iya kalla ba, sulalewa tayi daga hall d'in taje can waje ta sadda kanta a qasa ta soma uban kuka ba qaqqautawa...har aka tashi wurin dinner tana kuka ranar kam fuskar nan ta haye tayi sukutum da ita.....   Koda za'aje kai Amarya sokoto Manga zazzab'i takeyi sosai, dole aka barta gun Ammin su hussy dayake daddy yace itada ummi base sunje ba, kullum cikin kuka take har Ammy ta fahimci bata samun bacci, ba qaramun tashin hankali ta shiga ba taje ta sanarwa daddy, Aka sake bazama neman gadanga aka koma har soba amma ba labarin ko wanda ya sanshi.....    Tunda Amarya tazo gidanta dake cikin masarautar sokoto takejin tsoro, fad'uwar gaba me tsanani yake shigarta,Allah sarki huddy dukda yawan shekarunta ta kame kanta sosai, kuma dukda tasan meye aure tana cike da tsoro tunda bawai sabawa tayi ba....haka dai Ango Ali Abbas yarima ya shigo part d'in cikin shiga ta alfarma a wannan yanayin na faduwar gaba ya sameta, zama kusa da ita yayi yace "Amarsu ta ango, hudaisa ta Ali Abbas, wannan lullub'in fa?" qara sunne kanta tayi  a qasa tana murza zoben hannunta da yan yatsunta da kunshinta daya ebe mai hankali yayi matukar kyau dukda yake fatarta baqa ce amma hakan be hanawa lallen samun kyakyawan matsugunni me kyau a jikintaba, hannunshi yakai ya riqo hannun nata a hankali ya shafi lallin yakai bakinshi kuma ya sumbaci lallin nata sannan ya furta "Huddy lallin nan yayi kyau matuqa,inasan kunshi sosai musamman a jikinki matana" bata d'agoba still se murmushi da takeyi, wanda yake sauka lokaci d'aya tare da hawayenta, hannunshi ya sanya ya yaye mata mayafin "Subhanallah huddyyy naaa, badai kuka bako? Na menene ko kadunan zaki koma?" kukan tane ya qaru ta duqar dakanta tashiga rerawa a hankali, janyota yayi sosai jikinshi ya sanya hannu ya goge mata hawayen nata sannan cikin sigar rarrashi ya futa "Huddyy keba yarinya

Chapter 2 of 16