bayan ya zagi iyayenta ne yake bata hakuri bayan ya bar gidan yaga rashin dacewar hakan, besan da tanada encin kanta data shaqeshi ya sheqa lahira ba a yanda dai takejin mugun takaicinsa matuqa......
Koda malamai susu uku sukazo gidan mamaki manga tayi, cikin ikon Allah sega aljanin yayi bayanin komai gameda sharrin da aka aikoshi dashi, kuma yana bacewa cikin ma ya zama ba komai ajikinta, lallai Manga ta shiga tsoron daya sanyata firgici, bata tab'a zaton hakan ba, gashi anbarta a duhu da qyar aka samu nutsuwarta cokin hikima Ummu ta mata bayanin komai, kuka ta saka seda tabi ummu wanda sam Ali beso hakan ba ko kadan, awurin ummun taci gaba da zama har tsawon wata d'aya a wannan lokacin ne kuma aka turasu bautar qasa wanda ita kuma a kaduna aka kaita, dole aka soma shirin tafiya kd, har wannan lokacin kuwa bata nunawa kowa komai ba, abu d'aya ne dai ta qudurce a ranta ita da sokoto har abada inshaa Allah, kamar yanda tabar sokoto haka tabar Ali Abbas da rayuwarshi har abada......
Kwananta biyu a kaduna suka soma shirin shiga camp, tunda tazo Ali Abbas ke kiranta amma sam bata d'aga wayarshi, yau tana shiga b'angaren su Ammy ta gaidasu Ammyn tace da ita tazo da sauri taje bayan layinsu ta karbo mata saqo gun haj Azumi, bazatai musu ba haka ta juya bayan ta shaida mata karta tsaya gunsu Innoh zata sanar dasu tunda ba nisa da layin nasu, haka ta dauki hanya ita kadai gashi after 8 amma dukda haka bata kawo komai a ranta ba game da aiken.......tabar harabar gida da nisa ta kula wasu samari na binta anaya ga kuma wata mota dake tafiyar dirar hawaniya cikin yanga tamkar itama motar su take bi, cikin sassarfa ta qara mai amma ina ata nayanta kurun taji an rufe mata hanci da wani qyalle...........farkawa kurun tayi ta ganta acikin wani parlor me girman gaske kwance saman kujera, zare ido ta somayi a tsorace tana tariyo abinda ya faru, a bayanta tajiyo ana waya
"Mun samota hajiya amma dai gaskia kudin yayi kadan, Idan kina bamu dama semu miqawa su b'auna ita, kema zaki samu kud'i aiba kasheta zasuyi ba, zadai su ajiyeta ne ta dinga musu amai da kashin kudi mu kuma zasu bamu miliyan dari, kinga mu mudauki hamsin kema haka can musu kisan dabakeso ayi bakiyi ba kenan" dariya taji ya sheqe da ita meban tsoro sannan yace
"Se hajjaju tamu sekinji ni" tana zaune se zare ido takeyi taji yana wayar da wasu
"Ta aminta kasan hajiya ai ba wasa da naira, kuzo kawai irinta kukeso, e wacce kace dai" daganan ya dire call din ya zago ta gabanta ya tsuguna yana mana wani kallo, kan yace wani abu wasu sun shigo parlor din, kallo shi suka tsayayi kan wani yace
"Ka tabbatar budurwace batasan namiji ba?" kwashewa yayi da dariya yace
"Idan kunje ai zaku gani na rantse ma batasan Namiji ba karka damu kawai ayi sha'ani" dariya sukayi suka tafa daganan suka dauketa suka ajiye musu tsabar kud'i a jaka, giri riri aka jata zuwa waje, se kuka takeyi tana ambaton Allah......
Tunda akaji manga ta bata a zaune aka kwana bataje inda aka aiketa ba bakuma ta dawo gida ba, Ammy duktafi kowa rud'ewa sabida ba haka taso ba sam, ita yaran ma data tura sam sunce basu had'u da Mangar ba to yaya akayi hakan ta faru?" Tasani ita za'a tuhuma me take dashi na fad? Haka zata jajirce ta hakura dole ai tace ba ita bace tunda kam ba itan bace ba......
Manga naji tana gani aka yi tafiya me nisan gaske da ita bayan an rufe mata ido, mamaki ne ya damqeta ganin am mata saki tatas, an sanya mata jajayen kaya, abinda yafi daure kanta shine duk wani abu na addini mantashi tunda aka kawota cikin wannan gidan, gashi komai seda aka cire mata, ita gabaki daya ma ta dena kukan ta kangare kafff ta gama yadda cewar mutuwa zatayi, satinta d'aya ana tsafe tsafe akanta kandaga bisani a sanyata awani qaton rami batasan ko ina bane, sedai taga tana aman kud'i idan ma kashi zatayi dazaran ta gama setaga ya dawo tsabar kudi sababbi fill, kuma sunkai su biyar a wurin duk mata, sannan kuma sam ba mewa wani magana, gashi abinci se bayan kwana bakwai ake kawo musu kuma sannan ruwan so daya jal a rana......acikin sati biyu Manga ta gama lalacewa, kudin yana fitane tamkar da tsokar jikinta da jinin jikonta yake fita.....
Ali Abbas kuwa abubuwa sun tab'arb'are masa gaba d'aya ya gama haukacewa, rashin Manga ya zamto tamkar wani babban rashi na mutuwa atare dashi, gashi me martaba ya hana kowa tuhumar Ammy sabida mutunci na huddy sedai amata adu'a kawai......
*Lokacin zubarwa Manga da k'wallah yayi abin tausayi ce manga, yanzu story ya fara yanzu abubuwa zasu sauya salo, yanzu muka fara race din*
Mom Nu'aiym....
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
$
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
                    15
Ko shakka banayi aakwai saka hannunn Ammy a wannan abin da aka aikatawa Manga, yaya zakace nayi shiru? Kana sane fa da irin abubuwan da suke gudana agidannan,kakuma sani ina haquri, karfa ka manta inada gata nima, nima bawai wulaqantacciya bace,ba kuma er bayi bace a masarautar mu ka daukoni, a gidan sarkin agadez, kafi kowa sanin inada gata sabida ni dinnan haifaffiyar 'yace a wurin sarkin agadez, bazan lamunci cin kashi ba daga yanzu, 'yar tawa d'aya tilo zan qura ido a mun izgili akanta, na kwashe shekaru ina maka biyayya, na dade sosai ina maka kawaici, na rayu dakai acikin qunci da wulakancin iyayen gidanka, yaya Za'ayi Ibrahim kana dan masu gari guda d'aya a qasar Niger ka dawo nan sabida kawai baka sona da qaunata, daka gujewa gidan iyayenka da dangi duk akan qiyayyar dakakemun ka sauya sunan mahaifine har yanzu ibrahim? Zan shirya wlhy zanje yamai (Niami) da kaina na sanar wa me martaba yanda ka wulaqanta rayuwarmu dukda kasantuwarmu masu tsananin gata a duniya, kawai ka kawo mu nan an sace mun 'yata wlhy yanzu kam bazan yarda ba" nisawa Baban Manga yayi zuwa yanzu ya gano ya gama qure hakurin Innoh, dukda yasan Halima sam batada rashin kunya amma beji dadin wannan abin datake shirin yi ba na zuwa Yamai, sannan kuma ya sani tafishi gaskia dukda yake ya tauye mata haqqi ya sani yaune rana ta farko data tab'a daga muryarta sama da tasa, sanin kansa ne kuma cewa duk yanda bayasan halima yayi qarya yace bata burgeshi ta bangaren kawar dakai da haqurin ta
"Kibi komai a sannu Halima" kallonshi tayi bayan yayi furucin a sanyaye tace
"Idan kullum ka fada nayi shiru wlhy banda yau, bazan bi komai a sannu sabida badakai nayi naqudar Manga ba, haka kawai wlhy hakurin sati zanyi idan ba wani labari Yamai zanje, kai wlhy koma an samota wannan karan sena nunawa duniya Manga yarinyace me gata ta uwa ta uba, ina dalilin wannam cin kashin" yaudai Baban Manga ya kula sam Innoh bazata saurareshi ba wannan ya sanya ya juya kurun ya bar mata gidan zuciyar sa tana masa matuqar zafi ga rashin Manga da kuma jarabawowin data shiga yana ganin tamkar sabida abinda ya aikatawa iyayensa ne wanda yake ganin ada tamkar shine maganin su baki d'aya, amma yanzu ya hango tsananin wawtar daya tafka arayuwa, da ace be bijirewa iyayensa ba da ace be gudu daga gida ba, toda yanzu manga tana can ita ma ta auri dan gidan sarauta me nagarta wanda ze kula da ita, a ainahin qasar ta ta haihuwa....
  Ali Abbas kam ganin an share fiye da sati hud'u babu Manga ba labarinta gaba d'aya seya soma ciwo, wasa wasa fa haryakai kwance, ankuma kasa gane menene ciwon nashi, likitoci sesuce kurun damuwa ce ta masa yawa, daga qarshe dai aka gama gano cewar hawan jini ya kamashi sosai, kwance yake amma yakasa dena damuwa akan Manga,dukkuwa dayake damuwa ta mugun masa yawa arayuwarsa, besan ta ina ze faraba ta b'angaren neman Manga likitoci sunyi umarni akan ya dena damuwa amma ta yaya? Ina ze soma mantawa da hafsatun sa? Mangarsa kuma masoyiyarsa gaba d'aya, besan kalan azabar da Manga tajiba sanda ya guje mata se yanzu, ada dakaje da ita yola koda besan inda takeba yadai tabbatar tana lafiya lau be damu da yawa haka ba, yanzu kuwa daya tabbatar wa kanshi babu Manga kazalika babu labarin Manga se duk inda hankali nashi yake ya tashi tsaye qiqam, baida nutsuwa kullum tunaninshi an kasheta wannan tunanin yafi komai tayar da hankalin gadanga a b'angaren rashin Manga, shisa kullum hawan jinin amaimakon ya sauka qara hawa yake koda an sallamo shi daga asibiti kwana biyu ko uku an koma a rikice kuma, abubuwan sun masifar masa yawa ainun.....
 Manga yau ta rasa nutsuwarta gaba d'aya ta qanjame ta bushe ta gama ramewa, abu mafi ban tsoro data kula dashi shine wayanda ta tarar a wurin wasunsu basa magana wasu kuma sunayi, kuma wanda suke maganar anrubuta musu one yr a goshi acikinsu ne ta kula mutum uku sun mutu, da zaran sun fara amai kudi na fita babu qaqqautawa se kuma su dawo suna kashi yana dawowa kudi harsu soma zawo daga nan se zawon jini, kan kace meye jini ta baki hanci da kasan su, se shure shure se kuma mutuwa, ba mutuwar bace abin firgita fiyeda yanda za'azo agabansu a cire ma gawarwakin wasu sassa a jikinsu ana wani ihu da wasu surutai kuma se gawar tasoma ci da wuta harta zama toka, sesuzo suna raye raye suna kwashe tokar, hankalinta ne ya kaita ga cewar da zaran kayi shekara daya kaima haka za'ama kenan amfaninka ya qare? In kuwa hakane ita yanzu watanninta shida a wurin......kuma saura mata shida,kenan musulmai bazasu sallace taba? Kenan baza'a mata wankaba a mata sutura yanda akewa en uwa musulmai? Kenan dai ita da samun gatan mahaifinta ko mijinta ya sanya a qabari har abada? Kenan dai ita yanzu amaimakon amata salla matsafane zasu zo suna mata hauka akai? Sune zasuzo suna yayyab'eta suna yaga yaga da naman jikinta? Lallai tazo ta soma istigfari wataqila ta kuskurewa rabbu samawati wal ard ta wani b'agaren, ba kashin datakeyi ne na kudi ke damunta ba ko rashin abinci aa, wannan qasqantacciyar mutuwar dasuke yi....se a sannan ta soma tunawa da adu'o in daya dace ace ta somayI, se yanzu ta tunasu, aikam ta hau yi acikin zuciyarta sabida sam tunda tazo sedai zancen zuci bata magana gashi batama iya kuka, adu'o in ma data somayi yaune ta soma yinsu azuci dan duk ta manta da komai na addininta se yanzu.....
  "Haba Halima, tayaya zan zauna ina faman miki magana bakyaji, idan kinje yamai wlhy abakin aurenki, ban yarje miki zuwa yamai ba da wannan abin kunyar damukayi, ace kuma seda ermu ta b'ata zamu koma musu, ke bakida hankali ne, ki nutsu nasa ana mata adu'a kuma zata bayyana inshaa Allahu, ki kwantar da hankali wlhy na kiki alqawarin daga zaran ta bayyana zanje dake agadez inda en uwanki sannan daganan muje yamai a tare muma koma can gaba d'aya idan hakan kike so kinji?" ya qarashe maganar cikin sigar rarrashi, tana kuka ta gyad'a masa kai yayinda ya rungumota jikinsa gaba d'aya yana shafa bayanta a hankali......
  Yau Manga suna zaune aka kawo abincin su, kallon mamaki tawa abincin sabida bata taba kula cewar haka yake ba, tamkar dai an dafa tsutsa da wasu ruwa dabazata rabashi da majina ba, en uwanta se tutturawa suke yayinda ita kuma ta tasashi agaba amma ta kasa kai koda loma d'aya ne a bakinta, jikinta se wani qyarma yakeyi da alama adu'an da ake mata daga gida ya soma shiga jikinta ta soma gane cewar tana cikin hatsari tunda har take iya adu'a..... Dama wuri mafi wulaqanci aka ajiyesu qasa ce baki siminti, hannunta ta saka da taimakon fuck da aka sako saman abincin tayi gida ta zuba aciki ta rufa wurin ta zauna ta daddale da qafar ta ruwan ma koda ta kalleshi bada san rantaba da bismillah a zuci ta shanye, yunwa ce sun saba se bayan kwana uku ake basu abinci shima wani dan mitsitsi a wurin..... Tofa segashi kowa yana amai da kashi banda Manga, sam tunda bataci wannan abincin ba bata yi aman kudin ba ko kashin su, dataga haka kuwa tafi wata bataci sukuwa basu gane ba, tunda basa zuwa ebe kudin sedai su manga suga kudin suna bacewa da d'aya d'aya, acan b'angaren su kuwa sun kasa ganewa kan matsalar acewarsu sabida wanda suka mutu ne,dolene akawo sababbin d'auka.......
  *Bayan kwana biyu*
Manga na zaune zuwa yanzu abin duniya ya soma damunta, sabida zaman shirun yamata yawa, gashi yanzzu ta fahimci zata iya yin magana sab'anin da dasedai zancem suci, bazata mantaba tunda wayancan da suka mutu suka soma magana komai ya cab'e musu se mutuwa kuma, kuma ta kula an dena basu abincin kansu mutu kodai itama mutuwar zatayi ne? Ta tambayi kanta aikam rana ta farko se gashi tana hawaye, yaudai ta quduri niyyar sedai su kasheta seta hallaka su, a yanda ta lura mutane biyu ne kurun suke kawo musu abinci da ruwa sannan kowannensu bindiga ce saqale a aljihunsa, banda ita babu komai, Akwai wasu ruwa, data kula kullum suna wurin saman wata wutar dake waje da d'akin dasuke ciki, ta kula ba'a taba qara ruwan amma kullum akan sanyawa wutar garwasu kusan so biyar koma fiye, su kuwa ruwan sun dinga tafasa kenan batare dasun qone ba, qwafa tayi kurun, tayi sa'a mutum d'aya jal yazo kawo musu abinci, duqawa yake yana dire wa kowa abincin sa, a hankali cikin dabara ta kwanto key na kwad'on da ake rufe buglary din dasuke ciki dashi ta gama observing shine, ta b'oye a bayan ta d'aya daga cikin su ta ganta amma batace mata komai ba, haka ta nutsu a wurin zaman ta, gashi ko uwar manga ta ganta bazata gane taba yanda tayi wani mugun baqi ta koma wata qwarangwal sekace skeleton, haka ya gama basu abincin ya miqe ya rufe su ta waje suna kallonshi kasancewar bugler ne ya juya ya fita ya koma jan qofar ya rufe daga waje tan jin shiru ta kallesu tace
"Nasan duk kuna jina magana ne wasunku basa iyayi ku sani bazamu zauna muna musu kashin kud'i haka kawai ba, kuma amaimakon ma su barmu se su dinga kashemu daga qarshe su qwaqule mana kayan jiki su qona mu, ku bani hadin kai mu gudu, kunga key abu daya nakeso kuna bin umarnina a wannan tafiyar kawai kunaji na?" wasu daga cikinsu suka gyada mata kai yayinda wasun su suka qura mata ido ganin haka ya sanya tayi da turanci take suka washe baki anan ta kula wasun su qabi lune, bude kofar sukayi a hankali suka fito se suka rufe ta batare dasun saka key ba, dama wurin akwai yalwar duhu kam, can ba jimawa se gasunan sun shigo d'akin atare kwashe plates da cups dama haka sukeyi sannan sesu basu wani maganin da wani ruwa susha daganan se suyi bacci gaba d'aya....mamakin ganin wurin ba kwad'o suka soma yi, sannan kuma ya duba bega key ba sun kuma san ba window gashi basu d'aga daga bakin qofar ba sam konan da can, atare suka shiga inda su kuma suka fito da shirin su, suka rufesu da sauri da kwado dama b'oyewa sukayi a bayan durom da suke tsammanin na kero ne sunkai bakwai sebida dashi sukaga ake hura wutar, ruwan nan dake ta tafasa manga ta dakko ta d'agashi daga waje ta kwararawa shegu wata na tayata, sannan suka watsa garwasun daketa ruruwa suka sanya kwanon da ake dafa ruwan zafin dashi su tsiyoyo wannan man suka wasmtsa musu take wuta ta kama se ihu suke sukuwa sukayo hanyar waje da gudun su, amma sun kasa gane kan gidan ga wutar ta kai saman Roof seci takeyi, ta bangarensu suke jiyo ana yare iri iri ana kusanto inda suke, adu'o i manga ta soma yi iya qarfinta, sannan tace kowa ta riqe itace daya daga cikin wayanda suke wurin tace dasu idan sunzo ku riqa cewa Bismillahirahmanir raheem ku qwala musu,duk mutuwa zasuyi da yardar Allah, tanayi tana adu'a sega wasu mutane nan da jajayen kaya sunkai su goma suka nufatosu aikuwa Manga se adu'a take se kawai sukaga daya daga ciki yaje ya bude wata kofa yana cewa da harshen turanci su gudu kawai suna adu'a manga tace subi hanyar kawai Allah na tare dasu, gashi duk basa magana se ita kadai sedai zancen zuci, haka suka samu cikin ikon Allah suka fito daga gidan, sedai fa ga dukkan alamu acikin qungurmun daji suke, wanda baida iyaka, gashi lokacin sanyi ne kuma dukkanin su bamai riga ko wando basuda shi, wataqil wannan ne dalilin daya sanya ake kunna wannan ruwan,kuka kawai manga ta saka tace suzo su yanki daji kurun shine mafita gashi ita yunwa se addabanta yakeyi, bilhaq a haka suka darkaki dajin batare da sunsan inda suka nufa ba, a hanya mutum biyu suka mutu suna ji suna gani suka bar gawar anan, haka sukayi ta cin hanya seda suka kwashe kwana biyu suna cin dajin kansu kai ga titi, 35klmtrs to JEGA shine abinda suka gani a rubuce kan hanya,in hakane babu nisa da sokoto kenan,gashi lokacin a qiyasin su sha biyu na rana tayi, ga yunwa, haka suka isa wani qauye abin duk inda suka bi se ana gudun su waiga mahaukata ga mahaukata, wasu masu jin hausa sun fahimci kalmar yayinda wasu basu gane ba, manga se kuka take,kuma zuwa wannan lokacin duk suna magana, uku daga ciki yarbawa ne amma dukkansu kirista yayinda biyun ciki suke inyamurai suma kiristane....yayinda sauran suke musulmai kuma hausawa tantagarya, susu bakwai ne,biyun da suka rasu ne basu san qabilar su ba ko addinin su......
Haka suka taka har garin Jega kebbi state, Garine babba bazakace local govt bane ma sam, amma abin takaicin duk inda suka dosa guduwa akeyi, da qarfin tuwo sunzo wani shagon hijabai aka ka watse aiko manga ta janyo wa kowa daya manya har qasa tace su saka hakan kuwa akayi hijabai masu hannu dogwaye har qasa, sannan ta nufi wani shago tana zuwa gashi tayi wani zuru da ita tace
"Assalamu Alaikum" amsawa me wurin yana mamakin me jigi haka a tsaye harda baki radau
"Taimaka mana zakayi ka kaimu gun hukuma ko sarkin garinnan, wlhy yan shan jini suka kamamu, se bayan kwana uku abinci se yanzu Allah ya tserar damu muka yanko daji muka iso nan,gashi sabida muna tsirara kowa se gudun mu yakeyi, wannan hijaban ma wancen shagon dasuka gudu na kwaso mana su da kokai ka ganmu dole ka gudu anata mana kallon mahaukata" sosai ya gamsu da bayanin ta yace yana zuwa, yaje ya gayawa abokan kasuwan cinsa take aka rakasu gun sarkin Jega mutum adili me karamci, ba jimawa kuwa ya saurari komai da manga tazo mai dashi aka shigar dasu cikin gida aka basu abinci sukayi wanka sannan ya sake kiran Manga ya kula itace shugabar taron, haka yagama jin inda tafito cewar surukar sarkin musulmi ce yace ilai kuwa aranar zasu sokoto.........
Koda sarki yagan su sam be wayi Manga ba amma ya gane muryar kamar yasanta, haka ta bayyana komai se a sannan ya kula sosai manga ce, media da cops ya kira aka taru akazo jin zancen manga beko kira su ummu sunsan me ake ciki ba, kuka kuma agaban media yayishi sosai akan rashin kulawar gwamnati na tura sojoji yawon dazuka domin ceto rayuwar bil adama da ake sacewa ana cutar dasu, kowa yaga Manga baya shaidata seya qura mata ido, farin ma babu shi ko kadan ga kan qwam ba komai a ciki, a wannan lokacin kuwa Ali Abbas na bangaren su ba lafiya ko tashi da qyar yakeyi duk akan rashin Manga....
Sanda aka kaisu dukkansu gun Ummu ba qaramin kuka tayi ba,kuma karo na farko kenan dataje da kanta b'angaren su huddy tun bayan aurensu, ta sanar wa Ali Abbas yanda ake ciki cewar matarshi ta dawo ga bayanin labarin ta, sega mara lafiya a tsaye lolxxxx ba shiri ya bazama bangaren ummu, yaudai har Manganshi da kanta ta rungumeshi agaban ummu tana tsananin mamakin ramar dayayi da baqi sosai.....
Mom Nu'aiym.......
Vote plssss
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
*Ina godiya sosai pheey da alkhairin ki, Allah ya saka miki da alkhairi ya bar qauna,wannan shafin nakine ke kadai kiyi yanda kikeso dashi*
16
Koda Ali Abbas ya d'ago ya kalli Manga yaga yanda ta dawo se kawai ya sanya wani kuka me ban tausayi, wai Manganshi ce ta dawo qwarangwal tamkar ka busa ta fad'i, manga fara ta dawo baqa, Manga gajeruwa ce sedai ba cancan ba amma fa yanzu gabaki d'aya tayi wani tsawo sabida a bushe take, juyawa yayi ga ummu yana kukan yace
"Ummu kalli abinda aurena ya janyowa Manga? Kalli dalilin aurena abinda Manga ta zama, sam wlhy ban cancanci zama mijin Manga ba, tun ranar dana tsoma rayuwata acikin tata take fad'awa iftila'i iri iri, dana riqe igiyar aure da muhimmanci dabata shiga cikin wannan masifar ba,yanzu mezance wa iyayenta irin wa ennan musibun haka" hannunshi ummu ta kama
"Ka nutsu babana ka sani sarai bakajin dad'i godiya ya dacewa kawa Allah daya dawo mana da ita da rai dan bazamuce da lafiya ba sedai adu'a kawai, yanzu me martaba yace a dauketa a je da ita asibiti su mata qarin ruwa da sauran gwaje gwaje, sannan ta kwanta ta huta acan kuma dole amata adu'o i sabida sharrin matsafannan dabazamu san me suka mata ba ajiki, idan kana haka ita kuma fa ya zataji? Ka nutsu kawai kamata adu'a" shiru yayi yana me tsananin tausayawa Mangan shi.....
*Bayan kwana bakwai*
   Inno kam tasha kukan ganin yanda Manga ta dawo qata abar tausayi, tamkar ba ita ba, gabaki d'aya halittarta ta sauya dukuwa da yake sunzo ne bayanda komai ya lafa awurin manga sabida a kwana biyunnan harta wartsake ta soma cikowa, Kallonta tayi bayan kowa ya wuce adakin asibitin daga Manga se Inno tace da ita
"Mangan Innoh yau dai zan sanar miki tarihin rayuwata data mahaifinki abinda kika dad'e kinaso kiji, da farko dai mahaifinki sunanshi Ibrahimou Ahamadou mousa, sanin kowane har yanzu Ahamadou mousa shine sarkin garin yamai dake qasar Niger wanda tun shekaru arba'in dasuka wuce shine akan karagar mulkin, mahaifinki mutum ne da yake da kyakyawan usuli kasan cewar sa d'a d'aya tilo a wurin me martaba sarkin yamai Alhj Ahamadou mousa, yasanya ya taso a sangarce kuma cikin gata mara iyaka, tun a wancen lokacin a wajensa yayi karatu acan france, bayan ya kammala karatunsa ya dawo ya had'u da wata yarinyar er bawan gidansu,soyayyar gaskia ta haqiqa yake yiwa Aicha kazalika itama tana tsananin sansa, sun gama shirya cewar zasuyi aure yaje ya gabatar da ita awurin me martaba, amma qememe me martaba yaqi amincewa da buqatarsa, babu yanda beyiba,ba wurin wanda be jeba amma me martaba yace baze taba zubar da martabar masarautar saba ta hanyar aurawa sarki me jiran gado yar bawa ba, daga qarshe dai ina zaman zamana, mahaifina wanda ya kasance sarki a jihar agadez dake Niger ya umarceni akan auren d'an sarkin yamai,ni a wannan lokacin banida wani tsayayye kasancewar bama inda nake zuwa, dayake ni nafito a cikin dangi gaskia ba kamar mahaifinki ba dayake shi d'aya tilo ba wa ba qani awurin mahaifinshi da babarshi, Ranar daya soma kawomun ziyara yamun gargadi akan nace bana sanshi, ya sanar mun lallai zanyi bankwana da farin ciki kamar yanda zanyi bankwana da en uwana duk na sake aka daura aure na dashi, ban baiwa maganarshi muhimmanci ba haka kuwa aka daura aurena dashi bayan ansha biki na tare da kwanaki tara ranara ya tasheni da dare a haka ya sakoni a kotarsa muka bar gidan su, washe gari kuwa da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 16