haka" kallon rashin sani ta masa tace
"Mlm lapia dai" mamakin jin furucinta yae ya d'agata kurun se Auwal yawa wannan godiya ya rufa masa baya, kokarin sauka takeyi yayinda yaci karfin ta da adu'an dayaketa tofe ta dashi yana sassarfa ba qaqqautawa.....ahaka ya dira d'akin Ali Abbas ba qaramin me ilimi bane ta fannin addini, wannan ya sanya ko sanda ya aikatawa manga wannan shirmen mahaifinshi yaji zafinsa sosai sabida yafi kowa sanin haqqin aure, Zama yayi ya ebo ruwa a kofi yadinga adu'a yana tofawa aciki yana ebo ruwan yana shafe ilahirin jikinta dashi se wani kuka ta somayi dabesan ta da wannan amon muryan ba, Aljanin ne yayi magana akan shi adena qonashi turoshi akayi akan in ba'a dena qonashiba ze koma wurin wanda suka turoshi ya batar dasu a duniyar su, magana sosai ALI ABBAS yayi dashi yasha fama har kusan Asuba akan aljanin ya fita amma pir yaqi akan lallai seya aiwatar da abinda aka umarceshi dashi, seda yaga duk an qonashi sannan kuma yayi hanzarin fita tare da alqawarin baze qara waiwayarta ba, Ali abbas ajiyar zuciya ya sauke idashi duk yayi ja ya kalli yanda wani hayaqi ke fita daga bakin Manga ta bashi tsananin tausayi,harse yaushe ne Manga zata samu kwanciyar hankali dajin dad'i? Ya tambayi kanshi,me manga tayiwa su Ammyn huddy? Meta tsare musu? Menene laifin ta? Beji dadi ba sam sabida an gaya masa da sanya hannun Ammy aciki da huddy,yana san huddy mesa zata sauya? Da wannan kurun ta gama b'atawa kanta wayo a wurinsa ace musulmi da shirka irin wannan,sallah yaje yayi ya dawo ya daga manga dake baccin gajiya zuwa gado shida Auwal suka zauna tattauna matsalar haka kawai yaji Auwal ya kwanta masa yasan sirrin sa be boye masa komai ba ya gaya masa labarin rayuwar manga da tashi gaba daya Auwal yace
"Ni yallab'ai a ganina matarka dake gida zigata akeyi irin wannan tunda aikin datake ma na neman lada ne bawai sabida ta rasa abin bane datseshi zakayi ka dauketa itama daga Nigeria din ka kaita Madina inda kake shirin kai Mangan koda na wata shida ne ko kuma shekara d'aya,ina ganin sam be dace ka bari a wargaza mata rayuwaba harda Aikata shirka alhali kasan bawai haka bane halinta dacen" nisawa yayi yace
"Zanwa Ummu waya in sanar mata komai tayi shawara da me martaba yanda suka yanke hakan za'ayi ni ina tausayawa rayuwar Huddy ina tsoron ingantaccen hadisin nan ya tabbata akanta, dake sanar mana mutum ze kasance yana aikata Aiki irin na aljanna harse ya kasance tsakaninsa da ita be wuce kamu d'aya ba sekuma ya dawo ya aikata aiki irin na 'yan wuta kuma ya shige tsundum a wutar, kazalika masu aikata irin na wutan seya kasance tsakaninsu da wutar be wuce kamu d'aya ba sesu aikata aiki irin na en aljanna be wuce kamu d'aya ba seya aikata aiki irinna en aljanna kuma ya shigeta, dukda yake rayuwar kowa a hannun Allah take amma tun zuwanmu india an sanar dani dayan Maman ta ma ya kamu kuma idan hakan ta kasance sedai ajira lokaci sam huddy batada lafiya qarfin hali kurin takeyi kuma na sani amma kishi yana hanata ango rayuwarta na cikin garari se shirme takeyi me Manga ta musu? Yarinyar nan da Badan Allah ya taqaita mata wahala ba da baka gantaba wlhy daban masan ta fita ba Da Allah ma yasa kun hadu jiya kayi saurin ganeta, kaima gudun dakasha Allah ya saka maka alkhairi ya ceto rayuwarka sanda tsananin buqatar hakan Ameen" murmushi yayi yayinda shi kuma ya tashi zuwa dakin nasu, koda yaje ta farka amma ta kasa tashi, murmushi ya sakar mata ita dinma haka ta mayar masa da martanin murmushin sa, yace yana qoqarin boye mata meya faru
"Ki tashi kiyi sallah har tara ta gota se tashinki nakeyi kiyi sallah kinqi" zumburo baki tayi tace
"Nidai nayi mugun mafarki wai inata gudu bansan inda zani ba, ynzu kuma na farka gashi inata faman tsamun jiki na kasa tashi" zuwa yayi ya d'agata ya daura kan cinyarsa, sumba ya manna mata a goshi sannan ya cire mata yaloluwar rigar ya wurgar a gefe sannan ya d'aga ta cak zuwa ban daki,da kanshi ya had'a ruwan zafi ya mata wanka ya gaggasa mata jiki se shagwab'a take narka masa, yayinda takejin jik8nta tamkar ba nata ba dukda yake yayi mata matuqar nauyi, a haka ta dauro alwala ta dawo tae sallah breakfast kurun taci ta zari wayanta kallon sosai ya mata yace
"Manga inaso ki ajiye wayar nan zamuyi magana dake" nutsuwarta ta tattare gu d'aya shi kuma ya soma magana
"A d'an zaman nan damukayi dake na kula da abubuwa dayawa gamedake,da farko dai idan kikayi sallah Allah Allah kikeyi ki sallame ki dauki waya ko kallon tv ko karatun novels kodai wani abu mara muhimmanci a rayuwarki wanda ko a duniya baze qareki da komai ba bare kuma lahirarki, ki sani bakya san yawaita adu'o in tsari ko Azkhar dan Allah Manga ki taimaki rayuwarki ki dena wannan abun, yanada kyau matuqa ki ragewa baiwa waya muhimman lokutanki ki sani ba abu bane me kyau ace wai bakada lokacin mahaliccinka sena kanka, ki sani Allah baya buqatar komai daga wurinki kece kikeda tarin buqatu awurinsa wanda duniya kaf dama lahira shi kadai ya isa ya biya miki su, so ki nutsu ki riqe Allah mintuna biyar dai bayan ko wace sallah ya isheki kiyi adu'a bawai da zaran kin gama ki gaggauta miqewa shagalta da lamuran duniya ba,sannan kuma ki sani ina kulawa dake bakya adu'a yanzu idan zaki shiga ban daki, saka tufafi ma wannan yanzu mutane sun wurgarda yin bismillah kafin su saka kema kuma kina ciki, abubuwa masu muhimmanci an watsar sabida haka ki kiyaye, yanzu kina kewaye ko mahasada so kina azumin litinin da Alhamis da yawaita adu'o i da kuma istighfari, dan Allah ki kiyaye,kuma adena gayu na tsiraici ga kwalkiya nan da gayu masu aji, base ka wofintar da tsiraicinka ba dan Allah a kiyaye da yanayin shiga ina fatan kin gane?" jinjina kanta tayi
"Inshaa Allah yaa Ali zan kiyaye duk zanna yi" murmushi yayi ya yai alamu da hannunshi akan tazo
"Thats ma baby love,common lemme hug u" rungumeta yae sosai a jikinsa ya cura bakinsa a nata passionately yake kissing nata mutuniyar harta soma shid'ewa, cafko masa nashi bakin tayi ita ba qaqqautawa take kissing nashi batamasan sanda hannunta yayi tattaki zuwa cikin rigarshiba, gashin qirjinsa ta soma wasa dashi har zuwa saman nipples d'inshi wani dad'i takeji idan suna cikin irin wannan yanayin harda ke sanya take manta me takeyi, nonuwanta ya soma sosa mata a hankali seda ta kusan aomewa sannan ya kai harshensa ya soma wasa da nipples din....nidai ganin tamkar za'a samu matsala ayi sirri a gabana ya sanya na sulale na kauce wa masoyan.....
Tun bayan da akayi sallan asuba Ammyn huddy ta zari key ta fita tabar gidan, sanin halinta na ficewa aduk sanda taga dama ya sanya babu wanda ya nemeta har aka kwana aka wuni, seda yayanta qanana suka ga shirun yae yawa sannan suka fara nemanta inda ko labarin motarta babu bare ita gaba daya........ Ummu kuwa Ali abbas ya sanar mata komai sedai ya gaya mata be gayawa manga komai ba yadai bata adu'an dazata riqayi na tsari....baqaramun godiya ummu tawa Allah ba akan kubutar da manga dayayi, sannan ta shaida masa akan huddy kam se yanda mahaifin sa ya tsara....
Yaudai manga an dira a Madina, tun bayan kwana biyu data gabata suka samu labarin b'atar Ammyn huddy yayinda Ali Abbas ya kasa gayawa kowa meya sameta tunda a duk fadin duniya shine kurin ya sani se kuwa Auwal....Tunda suka isa Manga keta tsulala amai, acewarta sam batasan warin dakin dasuka sauka, ko ruwa tasha se amai dukta gama galabaita, ya sauya musu masauki kusan sau biyar amman haka taketa yin aman har washe garin ranar da suka isa wannan ya sanya yakaita asibiti badan yasoba, gwajin farko kuwa akace manga ciki ne da ita da wata daya kacal, an samu an tsayarda aman Ali abbas se rawan qafa akeyi aranshi yace wannan cikin a madina za'a haife masa abinshi kuma bama ze sanarwa kowa ba har Ummu se an haihu tukunna, se murna ake anata jijji da manga yayinda ita kuwa se narkewa takeyi tana shagwaba, dukta gama feqe qa ciwon kwana daya tayi fayau da ita.....
Mom Nu'aiym
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
28
Ammy bayan barinta gida duniya kawai ta shiga, haka ta dinga shiga daji batare datasan inda ta dosa ba, tayi tafiya mara adadi sabida da full tank ta fita a motar ta amma seda manta ya qare qat sannan taja burki ta tsaya sannan ta waiga ta kalli wurin, bata kawo komai akanta ba sabida sam tama manta wacece ita a wace duniyar take kuma menene ma rayuwar gaba d'aya.... Direwa tai ta soma bin hanya da qafa batareda tasan inda ta dosa ba
A b'angaren huddy kuwa tunda labarin b'acewar mahaifiyar ta ya risketa seta kasa nutsuwa tabbas tasan yanayin yanda sukai baran baran awaya akan abinda uwar tagaya mata ta sanya anwa Manga da mahaifarta takuma san idan basuci nasara ba k'aik'ayine ze koma kan masheqiya, Tayi kukan abinda Ammyn ta tawa manga da ita kanta rashin mahaifa ai musibane, tanan ne take samun take fitar da cututtuka yanzu idan akace babu ita aita shiga uku, ganin haka ya sanya taje hargun me martaba bata b'oye masa komai ba se kuka take, yayi bakin ciki ya kira mahaifinta suka dunguma zuwa kaduna harsu Baban Manga, Mahaifin huddy yayi kuka tamkar wani yaro yace
"Wlhy muhammad kasani tun aurena danuwarsu hudaisa nakeshan baqin cikinta kala kala, ko wancen batan da manga tayi wlhy da sanya hannunta,ayi mace ba imani yanzu nasan akwai wani a qasa, sabida bakasan dajin da aka samo motarta ba, dajine me nisan gaske wanda harya keta qasar mali, ni koda naga motar a hoto nasha mamaki en sanda ma acan suka barota sabida ba wayanda nabaiwa report bane suka ga motar sojojin da aka tura kwantar da tarzomane, kaga wannan shine tayi sharri ya dawo kanta tunda gashi Adama tace Ali ya sanar mata, ita batada mahaifa dayan matana ma ta sanya anyi tsafi an cire mata yanzu tacire ta erta idan ka duba duk sharrin kanta takeyiwa sabida neman abin duniya, nidai babu inda zanje nemanta wlhy kuma na saketa saki biyu idan an ganta asanar mata karta takomun gida, ke kuma huddaisa wlhy kika qara cutar da manga da gangan koda ta hanyar taka mata dan ya tsane indai da niyyar mitgunta ne Allah ya isa ban yafe miki ba, kije ki zauna da mijinki da kuma qanwarki lapiya ya fiye miki zama alkhairi sokuwa kawai dabatasan ciwon kanta ba, ke yanzu banda kike sakarai Mangan kike kishi da ita? Yarinyar da kike riqe kusan shekaru hudu idan kinada adalci ai abin a tausaya mata ce shine tsabar sankai kike shirme" kuka ta sanya ta dinga bashi haquri harseda me martaba suka sanya baki sannan ya haqura tanaji tana gani yace bazata jira harse anga uwartaba ta wuce Madina gun mijinta ta nemi gafarar sa.
Manga kuwa ciki yaqi ya bada had'in a angwance bata iya cin komai se tea da bread, dukta wani yamutse,shi kuwa se nan nan yakeyi da ita...yauma kamar kullum kwance take tayi matashin kai da cinyarsa yana shafa gashin kanta a hankali yace
"Hafsatu Manga inaso in sanar dake wani abu kuma banso ki tashi hankalin ki plss" gyaran kwanciyarta tayi
"Inajinka yaa gadanga indai ina tare dakai bana tunanin akwai wani abin daze d'aga hankali na har abada,koda hankalina ya tashi ma nasan zaka kwantar mun dashi" murmushi yae
"Manga ki sani Huddy koda ba matata bace itad'in er uwarki ce, bakida wani hurumin dazaki aminta da qaddarar da Allah ya gindayawa dukkaninku a matsayin ku na matana, Huddaisa zatazo Madina itama kuma tare da yara zatazo,na kula kina da tsananin kishi to ina rokonki da Allah ki rage nuna mata wannan kishin a zahiri ke kanki abinda kike mata sam bakya kyautawa koba komai ta cancanci ki mata kawaici sabida tin farko ta karbeki juyar mata da kai ne akayi, kuma yanzu ta gane komai so dan Allah ki bata girmanta ita kuma zan mata magana ta dauki abinta ta girmamaki kema" qirjinta ya d'an doka ta d'ago ta kalleshi tace
"To anan d'in zamu zauna dukanmu ne yaa Ali?" shafa kanta ya qarayi ya kula qirjinta ya doka
"Ba anan zamu zauna ba Manga nan ai hotel ne,kinsan saudi akwai tsaro sosai, dole sena jira an mana katin zama en kasa, sannan mu shirya kama gidan zama, sabida ni a nawa tsarin nida Niger kuma ba yanzu ba gaskia zanci gaba da aikin dana soma kuma tun kafin nazo an shirya komai na samu sun mayar dani" nisawa tayi ta shagwab'e fuska
"To kaima dai yaa Ali ka dena kakkamata a gabana kana mata kiss" murmushi yae yace
"Na dena idan shine bakyaso amma dai a kiyaye a zauna lafiya plss"
*Bayan kwana biyar*
A haka su huddy suka sauka tun a airport jikin dukansu su biyu ya mace sabida ko wacce kishin er uwarta take,Manga sororo tayi ganin yanda Ali Abbas ya nuna tsananin murnarshi ganin huddy atake ya rungumeta yakuma sumbaceta a kumatu tare da rungumar yaranshi duka biyu ya manna musu sumba suma, sun gaisa kafin huddy ta tako ta rungume Manga hade da riqe hannunta
"Er uwa kin rame meyake damunki?" murmushi tayi tace "Zazzab'i nake Aunty huddy amma na warke" kallonta ta mayar gun Ali Abbas tace
"Zazzab'in lapiya kodai yaro nane ze sauka inji Allah" murmu shi manga tae ta sadda kanta qasa lokaci daya ta tsinci kanta cikin tsananin jin kunyar kalaman na huddy, shi kuwa Ali Abbas cewa yae
"Ke muke jira ki gano mana bakin zaren babbar likita" dariya sukayi dukkansu sannan suka juya zuwa mota, a hotel suka sauka inda su Manga suke anan ya raba musu daki, inda bayan lokacin kwanciya yayi seya barwa manga su Ameer shi kuwa yaje dayan dakin da huddy, sun jima suna magana da dirzar soyayya kan daga bisani su zanta game da yanayin ciwon huddy ta gaya masa lallai batajin ko dayan nonon nata yana mata ciwo wanda suka yanke hukuncin zuwa ganin likita anan madina!!
*Bayan watanni biyar*
Zamane aka ginashi da amana tsakanin wannan mijin da matayenshi guda biyu, Manga kam ciki ya tasa watanninshi shida da kusan sati biyu, idan ka ganta bazakace da ciki ajikinta ba sam, mahaifiyar Huddy kuwa ko labarin wanda yaga wacce tai kama da ita ba a ganiba, anyi nema har an cire rai amma ba labari.....Huddaisa kuwa ciwon nan ya ciwo qarfinta ya tasota agaba kullum qara tasowa yakeyi, gashi sunyi wata uwar shaquwa da Manga idan ka gansu zaka dauka sister's ne bawai kishiyoyi ba, zaman lapia suke me ban sha'awa, huddy abubuwan sun mata yawa ga rashin ba'aga mahaifiyarta ba ga azabar ciwo Manga na kulawa da ita sosai tamkar mara juna biyu....
En kwanakinnan gaba d'aya huddy a rikice take, harma an kwantar da ita a asibiti, batada lapiya haryakai batasan metake ba,ta dawo se fauwalawa Allah lamuranta tayi tanata istigfari da adu'o i zuwa yanzu ta gama yaddarwa kanta cewa rayuwarta bame tsayi bace, likitocin sun tabbatar cancer dinta ya dawo ga dayan maman ta gashi ba mahaifa abubuwa goma dasha biyar,sumar kanta ta gama kakkab'ewa ma kaf, yaudai gabaki daya a rikice ta wuni se neman gafara takeyi tana kuka da barin wasiyya, akan yaranta da mahaifiyarta idan an ganta, Ali Abbas kasa tsayawa wurin yae sabida shima jikinshi ya mutu se manga ce tsaye riqe da hannunta tana mata adu'a a hankali taga ta soma yin laqos mamaki ya kama manga ta kalli injin da hancinta da bakinta suke ciki idanta ya wani birkice, tsoro me tsanani ya shigeta, ganin hannun ta saki ya tafi luu ya sanya tabi hannun shima da kallo, lokaci d'aya taji maranta yayi wani irin Murd'awa,dafe marar tayi ta kasa koda motsi se yarfe hannaye take, a haka Ali Abbas da doctor suka shigo suka sameta, kai tsaye doctor wurin huddy yae yayinda Ali Abbas yariqe Manga yana tambayarta lapiya, da qyar ta iya furta
"Ka duba Aunty huddy bata Numfashi sam, kalli idanta" saketa yayi ya juya a sukwane, girgiza masa kai doctor din yayi cikeda tausayi sannan ya dafa kafadarshi yace cikin harshen turanci
"I'm sorry to say, she's gone" Gabaki d'aya kan Ali Abbas kasa gane komai yayi,kanshi ya juye gaba daya zuwa wata duniyar yakasa d'aura tunanin sa amizanin fahimta me daidaito, lumshe idanshi yayi sannan a hankali ya mayarda dubanshi zuwa ga Hudaisa kwance tamkar me bacci an shafe mata ido ruf babu alamar numfashi atare da ita,se gani yake tamkar tana masa murmushi matsawa yayi ya riqo hannunta dayayi sanyi qalau yakasa koda zubar da hawaye kukan zuciya yakeyi yasani yakuma ji ajikinshi tun kwana biyu data wuce cewan hudaisa se Allah da tsawan rai amma tayi nisa,Maganar manga ne ta dawo dashi daga duniyar tunani dayaji tana salati
"Bayana nashiga uku" Dr din na mata sannu koda ya juyo gareta ta soma bleeding baiwar Allah, mutuwar er uwarta ya gama gigita tata duniyar, a haka aka kaita wani dakin amma ya zusuyi haihuwa ce da wata bakwai kacal, taci wuya kam amma cikin lokacin dabefi awa biyu ba ta haifo 'yarta er tsito tamkar ba mutum ba, er bakwaini se a kwalba aka direta.....
Allah ya jiqan ki huddy, masu karatu zakuga ina komai a gurguje wasu daga cikinku suka soma qorafi akan inajan labarin, shine zan datseshi abgurguje kowa ya huta.
Mom nu'aiym ce
Masu mun waya da masu mun txt da dm ta wtsp nagode sosai, naji sauqi cikin ikon Allah se Allah ya kaimu shafi na gaba nanan zuwa wanda yake kusa dana qarshe.
*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*
*👑ALI ABBAS👑*
*Billy Galadanchi*
*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*
29
Ali Abbas duk ya gama rud'ewa arayuwa besan dame zejiba,gashi sam yakasa gaskata rasuwar Huddyn sa, waya ya d'aga ya kira sume martaba bayan sun gama gaisawa yace da qyar
"Abba Hafsa ta haihu sedai yarinyar bakwaini ce amma tana nan lapia lau" murmushi tsohon yayi yace
"Lallai Ali ka soma tara iyali kace mata naketa samu haka,to Allah ya raya mana madeena ya baiwa uwar lapia,ya wurin su huddaisa kuma, nasan zata kula da ita sosai koda yake ba lapia bane da ita" kuka kawai Ali Abbas ya fashe dashi wanda ya tashi hankalin me martaba cikin gid'ima yace
"Subhanallah Ali lapia kuwa kuka kuma? Da kanka Aliyu? Menene yake faruwa kuma daga labarin murna?" cikin kuka yace
"AbbU Huddy ce ta rasu, gid'imewan mutuwanta ne ma ya haifarwa Manga da tasowar naquda, Ban taba kawowa huddy mutuwa ba yanzu Abba yaya zan rayu idan babu huddy Abbu?"
"Innalillahi wa inna illaihiraji'uun" itace kalmar da Abbu keta nanatawa bayan jin bayanin Ali Abbas, shi kanshi mutuwar hudaisa ta gama girgiza shi gyaran zaman rawaninshi dake shirin faduwa yayi da hannu d'aya yace
"Ka kwantar da Hankalin ka Ali,kasani ubangiji baya barin wani dan wani anan ko kadan, Inaso ka nutsu ka dinga mata adu'a a maimakon kukan nan dakaketa faman yi, kasani Huddy ta samu rana yau juma'a fa, yaushe abin yafaru?" girgiza kanshi ya dauke majina da bayan hannunshi yaukam maza na cikin rud'u
"Rashin lapian manga ya rudar dani, jira nake ashiga masallacin juma'a se ayi janazar acan inda zata samu mutane da yawa" nisawa abbu yayi yace
"Zan sanar da mahaifinta domin a iya sanina yana saudia din, idan yana madina seyaje ya sallace ta,Allah ya mata gafara ya sanya mutuwa hutu agareta Allahu ya bamu hakurin jure rashin ta,halinta na gari ya bita a duk inda take" sallama sukayi Ali Abbas ya qara bin gawar dake gabanshi da kallo ko shakka babu indai akanshi huddaisa zata aljannah tokuwa taje sumul domin babu shamaki ya daga mata qafar sa tafiya babu gargada, shida kanshi ya sani yayi rashin matarsa me nagarta da sanin Allah yana wa kanshi kuka domin huddy ba itace abin tausayi ba shine, yaya ze rayu babu hudaisa, a haka har kiran mahaifin huddy yashigo wayarsa ya d'aga cikin qunan rai, take yamai bayani anyi sa'a yana madeena sekashi yazo se rarrashin Ali Abbas yakeyi Manga ma anacen kwance anata kuka ba qaqqautawa ga yara suna wurinta se tambayan momyn su sukeyi gwanin tausayi gata kwance ba lapiyan jiki.
Huddy ta samu jama'a kam ba laifi kazancewar shi ranar juma'a ana idar da sallan juma'a aka sallaci gawarta da wasu mutane guda uku, aka kaisu kushewa, Ali Abbas se ciwo yakeyi a tsaitsaye mahaifinta ma yafi sati tare dasu,har me martaba da Ummu suka zo domin akula da Manga tare da wasu hadimai susu biyu.....
Kallon sosai Ali Abbas kewa jaririyar yar tashi yana jin santa yana ratsa ilahirin jikinsa, lumshe idanshi yayi yace "Allah ya rayarmun dake da sauran en uwanki Hudaisa, Allah ya sanya kiyi halin karamci irin na takwararki Allah ya baiwa mahaifiyarki lafiya Ameen" Yarinya kam a kwalba take kwana anan take wuni har akayi sati biyu seda tayi qwari tukunna sannan aka sallamesu.....
Manga har zuwa wannan lokacin bata dawo hayyacinta ba, yauma ban d'aki ta shige se faman ruwan hawaye takeyi ba qaqqautawa,kukan harda shesheka, Ali Abbas ganin ya jima a d'akin bata fito ba ya sanya yaje ya tsaya jikin qofar toilet din
"Hilwaty yada jimawa a toilet ki fito mana ko" share hawayenta tae ta saisaita nutsuwarta sannan seta fito kallo daya ya mata ya gano kuka tayi jan hannunta yayi suka zauna bakin gadon
"Hilwaty kuka kuma? Yanzu dama haqurin dakike bani akan rashin huddy ba gaskia bane, yaya zaki koma ban daki ki dinga kuka abinda ya dace ki zauna kinawa hudaisa fatan samun dacewa da rahamar Allah, dan Allah Hilwa ki dena kuka, kidena damuwa idan kina yawan kukannan zaki karyarmun da zuciya" kallon shi tayi
"Yaa Ali duk sanda na tuna da Aunty huddy nikan kasa tsayar da ruwan hawayena, mutuwan aunty hudaisa yamun ciwo ban taba kawo mata mutuwa ba,tayi ciwon dayafi wannan zafi amma sam bata mutuba se yanzu" hannunshi ya daura a bakinta yace
"haba mana hilwa, karki yi sab'o mana mutuwa ai se lokacinta yayi ake yinta bawai haka kurun ba, ki sani mutuwa ba'a gane wanda zeyita domin kuwa marasa lapia wanda suka bushe ma sun tashi sun dawo garau, masu lapia kuwa mutum yana a tsaye seya fadi kan a daga ya zama gawa sabida haka ki gane Allah yana saukar da ikon sane da iyawarshi aduk sanda yaso,alokacin dayaso bisa kuma wanda yaso hakan ta faru dashi, ba'a barin wani dan wani idan akama mutuwa kaqiyin tawakalli se a da d'a maka me mugun zafi yanzu a misali a rashin hakurin nan dakikai kurin sena mutu ki huta tunda bakya san kowa naki ya mutu" kallon shi tayi da sauri
"Dan Allah ka dena cewa zaka mutu yaa Ali,i shaa Allah bazaka mutu ba sena rigaka mutuwa kuma bama yanzu ba inshaa Allah" murmushi yayi yace
"Babu wanda yasan sanda waninsa koshi kanshi ze mutu,fatan dai kurun mu cika da imani muyi kyakyawan qarshe" sauke ajiyar zuciya tai ta lafe ajikinshi tana tunanin rayuwa yanzu shikenan ba huddy kenan bazasu qara ganinta ba bazasu qara jin muryanta ba, dariyarta yin hira da ita, ta tafi kenan dukkanin komai daya shafeta banda memorie's nata ta tafi kenan har abada?,runtse idanta tayi asarari ta furta "Allah ya jiqanki Aunty huddy, Allah ya miki rahama,Allah ya gafartq miki Annabi yasan da zauwanki Aunty huddy,halinki na gari ya biki.....matseta Ali Abbas ya qarayi banu wani option dayake da face ya zubar da hawayen dasuke qoqarin fasa idanshi su fito sabida baze iya haqura ba, shida kanshi qarfin hali yakeyi wani irin tausayin huddy da kanshi yakeji, ya tuna sanda tace dashi lokacin tana cikin azabar ciwo
"Abbi nasan cewar mutuwa zanyi amma wlhy banaso na mutu abbi, inaso in rayu dakai,inaso in rayu da yarana har girmansu, Abbi inaji ajikina bazan qara kosa kwana daya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 16