Share this page
wuni yaa Ali" kallonta yake harya zauna "Lapia lau" yabata amsa a taqaice "Me zakici" ya buqata, wani irin takaishin shi taji ya tarnaqeta tace dashi "Meko zanci aina qoshi a qoshe nake" kallonta yayi sosai yace " Kinyi ordering wani abinci ne daga reception?" kallonshi tamkar zatai kuka tace "Sosai nayi harma na biyasu" murmushi yayi yace "To daga yanzu idan kinyi ki dena basu kudi nine zan biya komai idan na tashi" uhm kawai tace cikin takaici "Ya jikin Aunty huddy?" ta buqata "Taji sauqi amma tana can asibitin bazasu barta a wurin muba, sunce ma cikinta 8 month ne bama qirga da kyau, ita dince da kafiya tun a can tayi ultrasnd taqi ashe cikin yayi nisa, yanzu sunce anan wurinsu zasu barta, dakamar aikin tare zasu yishi su cire babyn kuma suyi aikin breast din" jinjina kanta tayi "lallai kam cikin yayi girma, Allahu ya bata lafiya me d'orewa" miqewa yayi yace "Zanje d'akina akwai abinda kike buqata?" d'agowa tayi ta hadiye wasu yawun takaici tare da cura manyan idanuwanta cikin nashi tace "Meko zan buqata ni Hafsatu Manga,bana buqatar komai se kad'aici" kallonta yayi yanaso ya gano ma'anar kalamanta amma san yanda fuskarta take a d'azu yanzun ma haka ne, be gane inda kalamanta suka dosa ba kad'aici kuma? Ma'anar ta bata buqatar takurawar dayake mata ne? Lallai ma batare dayayi magana ba ya juya kawai zuwa dakin shi yana mamakin sauyawar halin Manga sam ta zama wata kala kuma ta sauya kyawawan halayenta amma ya kula shi kadai take mawa........ Ammi tayi zaman dirshan wurin boka tana kora masa bayani akan taji shiru har anbar qasar tare da wannan yarinyar ihu bokan yayi yace "Daga yaron har yarinyar babu wanda aljani ke iya zuwa wurin shi, sabida sunada tsari me girma ajikinsu shi mijin ma gabaki daya acikin ambaton Allah yake wuni ita kuwa bata rabo da azkar da adu'o in kariya na tsari ajikinta, sannan ko wannensu yana sanye da zobe har er taki da baya bari wani shaidani ya iya zuwa kusa dasu komai qarfinsa, sabida haka babu abinda zan iyayi akai kije ki sauya shawara da tunani kawai, ga hanyoyi nan idan ta dameki ki sanya a kasheta kawai, hanya dayace dana kula zata iya bulle mana itace basu taba saduwa da mijin ba, zan iya tura mata cikin iska shima dan aljanin ze hura ne daga nesa, idan anje gwajin asibitin ma ze nuna cewar akwai cikin, kuma zeyita girma,idan kin yarda sena tura mata cikin na iska, mu rikitar da komai a tsakanin su kinga daganan ba aure se mutuwar sa kenan,idan auren ya mutu semu b'atar da zancen cikin kowa ya huta, murna sosai ta shigayi ta zazzage mai jakarta tabar wurin cikeda d'oki da murnar abinda zeje ya dawo...... Haka suka zauna a india na tsawon watanni biyu tunda sukaje banda gaisuwa ko hira Manga da Ali basayi abinci kuwa sedai tace mai ta karba amma yoghurt ne taketa sha da snacks kullum,tama rame sosai, Anyi aiki kuwa an cirowa fine girl me kyau sosai, breast dinma an cire dayan an kashe wurin da wuta kar ciwon ya dirar wa dayan yanzu huddy ta samu lafiya sosai batada wata damuwa, shirye shiryen dawowa suke tayi ita kuwa Manga se a wannan lokacin ta soma ciwo, haka suka dawo gida kullum cikin Amai take da yawan kasala, bata samun wadataccen bacci, wani yammaci ta shirya zuwa sashen ummu, dama tunda suka dawo a bangaren huddy ta sauka lokacin kwanansu uku da dawowa daga India, tana zuwa ta sakawa ummu kuka akan batajin dadin jikinta, ita sam batawa ummu kallon suruka kallon uwa ta dauketa yanda itama ta dauketa 'ya, "Toni Auta niba likita ba ba komai, bansan meke damunki ba ko asibiti zamu je?" shagwab'e fuska tayi tace barinje in gayawa Aunty huddy ta dubani to kobe yiba?" murmushi ummun tayi "Ki zauna anan barin wa huddyn waya, ai bakya riqa yawo ba bayan kince har jiri kike gani" kwantar da kanta tayi zaman jikin ummu, ta lumshe ido tanajin qaunar ummu har cikin ranta da ruhinta, mata me karamci da qaunarta..........Kallon ta sosai huddy tayi cikin dokawar qirji na kishi irin na mata bayan kwajin fitsarin daya mata ya fito kuma bincika yanayin al'adarta ta gano tayi tsallaken sati biyu be zoba ta kalli ummu tace "Ummu juna biyu ne da ita na tsawon wata d'aya da satuka biyu" Washe baki ummu tayi aranta tace ashe an angwance a India" ta kalli huddy tace tana fad'ad'a murmushinta "Lallai ma auta an gama girma, kije zanga en jikokina ta wurin auta, toki sani bana san kishiya,bazaku taru keda hudaisa kuna jeremun kishiyoyi ba muji zaki kawo, kinga yanzu me martaba bashida magana seta Ahasan yaga yarinya ze qyale tsohuwa" mayarda dubanta tayi zuwa ga huddy taci gaba "A rubuta mata magun gunan dazatasha tasamu sauqin wannan wahalan, tunda juna biyu beje ko ina ya kawo ba yasoma baiwa auta wahala, keni wannan koda mijine banayi,ze daddage yake baiwa Autan ummu wahala,ko Auta" sadda kanta tayi qasa qirjinta na wani irin mugun dokawa, harta ji jirin datakeji yana qaruwa, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un itace kalmar data furta a hankali, huddy senyaqe takeyi tace aranta wato ni inacan ina fama da kaina duk ciwon danake shi kuwa honey moon yaje da matarshi dukda yake nice na kafe akan sena tafi da ita....... "Zanje na rubuta sena baiwa abbin su Ahasan ya siyo mata, seta zauna anan kawai tunda ni bana zama" murmushi tayi tace "Dama bazan bada autana ba, tana nan kusa dani inshaa Allah" murmushi tayi ta juya sabida basa wasa da ummu" a parlor ta sami Ali Abbas ta zauna kusa dashi ya kalleta "Kin jima da yawa wani abinne?" murmushi tayi tace "Kasan halin ummu indai akan sha'anin Manga ne, dukta tashi hankalinta amma nisam bazan gaya maka komai ba seka bani goro" murmushi yayi yace yana kallonta "Zan bayar mana sanar dani menene? Wani abin farin cikinne ya samemu?" murmushi tayi itama tace "Manga ce da ciki wata d'aya da sati biyu, kaga har strip dinma na pt nazo maka dashi,kace angwancewa akayi daga India?" wani kallo ya wurga mata wanda ta kasa fassara ma'anarsa,yace cikin mamakin "Ciki kuma Manga kamar yaya?" murmushi tayi tace "Kamar yanda kamata ciki mana Haba Abbin Ahasan sekace wani mugun labari kalli sauyawar fuskarka kodai kaso seka gama shan angwanci ciki yashiga,to wane angwanci kuma bayan wannan anje honey moon an dawo da goro" da qyar ya saisaita nutsuwar shi ya qaqaro murmushi cikin hikima ya wayance mata yasa dariya yace "Mamaki nake ciki da wuri haka" ita kuwa kasan zuciyarta ma takaicin sa takeji tace "Kaine kayi shigar wuri baka jira ta tare ba, dole kaga ciki da sauri haka" murmushi yayi abinda be taba yiba fita da irin wannan jallabiyar dayake zaman gida da ita shi yayi, ya miqe kurun yayi ban garen fulani.....batanan da saurinta taje kaiwa sarki albishir shi kuwa ya shiga d'akin kai tsaye, kuka ya tarar tana yi ya cizgota ta miqe tsaye tana ganin yanayinshi ta shiga rudu murya na rawa ta furta "Na rantse da girman wanda rayuwa ta take hannunsa ban taba sanin wani d'a namijiba, bansan inda aka samo wannan cikin ba" Wani mahaukacin mari Ali ya dire mata seda taga taurari ba adadi, yace "Aruwa kika sha? Nace dan ubanki a ruwa kikasha cikin? Zaki kawomun hauka anan banza shegiya mara imani, dama duk shekarun nan maza kike bi ko? Se yanzu Allahu ya tona miki asiri, wlhy ki sani bazan tab'a lamuntar wannan jakancin ba, idan na karb'i cikin nan shege nake wlhy se duniya tasan abinda kika aikata, aini bawai wawa bane jahilar yarinya mara dangana kawai" kuka kawai tana bashi hakuri amma se fada yakeyi kallonshi ttayi "Dan Allah ka dena daga murya yaa Ali kar bayi su jiyo mu, se maganan ya zam tsegumi acikin gidannan, wlhy ka yadda dani ban taba aikata wani abu ba da igiyar aurenka" wani marin ya kuma dire mata ya cafki wuyanta, seda taga mutuwa kusa sannan ya turata ta fad'i akasa ya juya, yana kawowa qofa ummu dataje me martaba na fada ta dawo ya gani a tsaye ta qura masa ido cikin tukuma, ze iya cewa wannan ne karonta na farko data tsoma idanuwan ta acikin nasa,murya a qasa tace "Idan ka fitar da wannan maganar Allah ya isa ban yafe maka ba, ko zuhair ka sanarwa da zancen cikinnam cewar banaka bane ban yafe na, kuma bazan lamunci kace ba danka bane, da nakane kona waye kaji na gaya maka, wawa kawai dabesan ciwon kanshi ba" sadda kanshi yayi a qasa yawuce kawai batare da yayi magana ba sam......shiga cikin d'akin tayi ta zauna saman gado ta qurawa Manga ido tanaso ta gano gaskiyar ta, kallonta manga tayi tace tana kuka "Wlhy Ummu bansan komai ba, ba abinda na sani ban tabayiba wlhy sharri ne kawai dan Allah ki taimakamun ki nuna masa gaskiaya ummuna dan Allah" Rungumeta kawai ummu tayi tana bubbuga bayanta a hankali. Mom Nu'aiym *HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)* *👑ALI ABBAS👑* *Billy Galadanchi* *Sadaukarwa gareki qawa ta gari Fulany saddy*                                      13 D'agota tayi ta kalleta sosai tace "Auta kalleni nan dena kukan haka" d'agowa tayi ta kalleta sosai tace da ita "Auta ki kwantar da hankalinki ki dena kukannan, ki nutsu ki gaya mun gaskia abinda nake san sani" gyad'a mata kanta tayi amar to taci gaba "Sanar dani gaskia alokacin da yan fashi suka d'aukeku sun miki fyad'e?" tana kuka tace "Wlhy Ummu basu samu nasara ba ko kad'an akaina, Humaira ce kawai suka samu sa'arta amma banda ita bakowa harni" jinjina kanta tayi tace "Shirya tashi mu fita" ba musu suka fito a tare zuwa asibitin qwararru ta jiha, binciken dai ya nuna cikin watanshi d'aya da sati biyu kuka sosai Manga keyi harsuka dawo, wato dai ta tabbata cewar lallai cikinne da ita, to amma ta ina? Garin yaya hakan ta faru? Har suka isa bangaren su kuka takeyi, zama ummu ta qarayi ta fuskance ta tace "Autan Ummu sanar dani gaskia tsakaninki da Allah, na miki alqawarin zan yadda da komai zaki fad'a ke kuma kiji tsoron Allah ki sanar dani iya gaskiyan ki,Waye mahaifin wannan cikin?" da sauri ta d'ago ta kalleta tace "Wallahil Azeem ummu ban tab'a tarawa da wani namiji ba, ciki kuwa harda mijina *ALI ABBAS* bazan miki qaryaba ummu bansan mafarin wannan cikin ba, ban kuma san ubanshi ba" jinjina kai ummu cikeda al'ajabin wannan lamarin, indai har Manga ta haihu yaro ze bayyanar da ubanshi, amma tafi zargin Ali Abbas ne keson ya rabu da Manga yanzu kuma, qwafa tayi tace "Maza jeki ki kwanta ki huta, domin kuwa bacci nakeso kiyi, kar inji kin sanarwa kowa wannan maganar domin Ali Abbas shine ze karbi wannan yaron......." Batace komai ba se kurun ta kwanta badan tayi bacci ba sedan batasan mema zatayi ba. A b'angaren Ali Abbas kuwa yana zuwa d'aki wani baqin ciki datakaici ya tarnaqe shi, wato daga zuwansu india har wani ya hurewa Manga kunne harya la hanta mata rayuwa, shidai wlhy yaji gabaki daya ta sire masa arai, amma baze iya jayayya da hukuncin ummu ba....."     Yanda Manga taga rana haka garin Allah ya waye mata, koda aka kawo breakfast ma ko kallonshi batayi ba, tayi mamakin dalilin Ummu na qin zuwa ta dubata, tasani koda batazoba kullum takan aiko azo aduba ta, sabida main dakinta ba'a shiga da wuri wuri se ta fito....tana tsakiya da tunanin tajiyo sallamar wata hadima, d'agawa tayi ta kalleta ita kuwa ta zube a wurin "Ranki ya dad'e Inji Fulany wai kifito zaku fita" Ba musu ta miqe ta sanya hijab d'inta ta fito tabi bayan hadimar har suka isa gun mota ganin Ali Abbas a mota ya mugun qara tayar mata da hankali, kallon Ummu tayi tace kanta aqasa "Barka da kwana ummu" janyota ajiki ummu tayi dayake tana baya tace "Lafiya qalau Autan Ummu Hafsatu Manga, Allah ya miki Albarka,yaya jikin kuma?" qwallah ne ya taru a idonta ta kasa magana, seda suka hau hanya tace "Yaa Ali barka da kwana" A daqile ya amsa da "Lafiya" a tak'aice Ummu bataji dad'in yanda ya mata ba sam, gabaki d'aya tausayin Manga takeji sannan kuma batasan tonuwar asirin yarinyar, ta kasa gane kan wannan al'amarin amma sam batawa Manga tunanin bin maza, am mata shaidar halaye na gari sedai ko wani abin dabaze wuce qaddara ba, a yanda tayi lissafi ma da yan fashin sukai mata fyade da tuni cikin yakai wata biyar ai koma fi tunda aiba yau bane amma wannan daga ina, girgiza kanta tayi tana jinjina tunanin da me martaba yayi kai tsaye na kawar da wasu en Gulmace Gulmace daka iya tasowa acikin masarautar lallai wannan shikadaine mafita agaresu baki d'aya...... kai tsaye gidan Ali Abbas dake Arqillah gandu suka wuce, a babban parlor suka sauka dama babu wani na buqata a gidan sannan akwai hadimai, bayan sun zauna ummu ta kalleshi da kyau tace "Agaban idanka me martaba ya gama zartar da wannan hukuncin lallai ka kula da matarka sosai da sosai, Banasan wannan maganar da qara tashi harseta haihu tukunna, alwai abinda muke zargi akan wannan cikin kuma ta hakanne kurin zamu kai ga gano me ake ciki menene ma'anar wannan cikin,tunda yake tanada hadimai kwanaki biyu zaka musu anan sekayi biyu acan d'inma kayi biyu kana dai jina ko?" gyad'a mata kanshi yayi cikeda takaici ta miqe kawai tace "Autan ummu zan kiraki anjima, ayita zaman haquri kayan ki suna hanya, yanzukam kiyi zaman gidan mijinki shine mafi aa la agaremu baki daya, ban yarda da rashin kunya ba ko wani abin qi" Itama gyad'a mata kai kurun tayi batai magana ba daga nan ta fice, haka suka zauna shiru ita a tsorace shikuwa tamkar ya hallakata yakeji har wasu daqiqu da mintuna suka shud'e ba wani mewa waninsa magana, seda ya gaji dan kanshi sannan ya tashi ya shaqo wuyanta yace cikin fusata "Tun farkon had'uwa ta dake tausayine ya rinjayi hangen muyagun halayenki a wurina, daga bisani kuma narasa da wane mugun tsafin naku na buzayen daji kika yi sa'ar sacemun zuciyata na soma sanki, na tabbatar da zancen huddy na baya a yanzu cewar ku d'innan mayune, banda haka tayaya iyayena da kansu zan rantse musu cewar ni d'innan bani na miki ciki ba, bansan da wannan qazantar cikin ba amma su nuna sunfi yadda da qarairayinki akan gaskiyar dana sanar musu, wlhy ku baqaen mayu ne masu muguwar zuciya, kuma ni bazan koreki ba amma baqar wuya ce zata sanya ki gudu daga gidannan da qafafunki, matsafa kawai masu bin mutane da baqar yadiya azzalumai masheranta" kuka manga ta fashe dashi iya qarfinta "Haba Yaa Ali, banyi tunanin duk mutanen duniyar idan sun kasa yadda dani ba kai bazaka yadda dani ba, yaya kake qoqarin toshe idanka da kunnuwanka daga ganin zahiri wlhy ni bantaba aikata zina ba, kuma nida iyayena ba matsafa bane bakuma mayu bane" Tassss taji saukar wani gigitaccen marin da alokaci d'aya jini ya soma sakkowa daka cikin bakinta kuma ya zagaye mata ilahirin rabin idanta na hagu yana huci yace "Bazan qara baki wata damar dazak8 rainawa tunanina hankali ba, jaka kawai me zina da auren wani akanta, jahila me bakar zuciya Allah ya isanni wlhy akanki,kin cutar da masarautar mu kin tozartar da zuri'armu kin kawo mana b'ara gurbi acikin mu, na tabbatar a India kikayi cikinnan,Allah yayi ikonshi ki haifo ba'indiye sak,kinga sena miqaki dashi baki daya awurin uban shi mayya kawai" kuka ta durqushe wurin tanayi kurun batare datayi yunqurin kare kanta ba a karo na barkatai...... *Bayan wata hud'u* Banda duka zagi da cin zarafi babu abinda yake shiga tsakanin Manga da Ali dukta birkice yayinda cikinta ya zamto wani uban qato na ban mamaki ma dan bazaka yarda cewar wai watanni shida ne da cikin ba, yauma kamar kullum tana zaune ta rafka uban tagumi se kuka takeyi yana zabga mata zagi tamkar ba Ali Abbas me nutsuwa da hangen nesa ba "Allah Manga duk sanda na kalleki naga wannan cikin se in riqa jin tamkar in shaqeki sekin sheqa lahira, sam bakida mutunci kuma kin citar dani, wato duk tsawon shekarun nan cutane kike se yanzu ne Allah tona asirinki jakar banza kuma jahila, kina haihuwa zan karbi dan dan Allah ki tallafi rayuwarshi dakika gurgunta ke kuma seki koma ki taya dattijon ki kwarewa masu gate, asararriya kawai" Ita wasu lokutan ma mamaki yake bata har dake sanyawa ta manta ilahirin duniyar datake ciki, kamar kuma an tsikareshi ya miqe yabar gidan, sabida ranshiyana b'ace ya sanya bema tsaya kallon qofar d'akin huddy ba ya wuce d'akin shi muryan daya jiyo ne ana waya daga ban d'akin ya katse masa tunaninshi "Haba Ammy yaya zaki kunno wutar da Allah ne kadai ze iya kasheta, yanzu dani aka yiwa hakan zakiji dadi, mata da mijinta ki tashi hankulansu, ina namiji ze yadda da cikin daba nashi ba, kuma wannan aljanin da kika tura ki sani fa wlhy shima se Allah ya tambayeshi haqqin er mutane lahira,kuma wlhy bazan rufa asiri ba sena gayawa ummun Abbas kece kika turawa manga Aljani babu wani cikin datake dashi, tun lokacin da Ali yaji Manga nada ciki baya cikin nutsuwa yarinya duktabi ta fige ta lalace akan abinda bataji ba bata gani ba, dukda an haneta gayawa kowa amma wlhy sabida ta yarda dani seda ta sanar dani, amma ke Ammi kirana ma kike zancen waiko an saketa, Lallai wannan san kan naki ya tayar mun da hankali, bantaba ganin mutum me masifar sankai irin naki ba" shiru yajiyo alamun uwar ce ke zazzagawa er masifa ya sanya ya juya yabar dakin zuwa bangaren Ummu da sauri..... Mom N'aiym ce Kumun uzuri inata hidima shisa. *HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)* *👑ALI ABBAS👑* *Billy Galadanchi* *Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy* 14 Wayanshi ne yayi qara ya zaro ta jin yanayin sautin dake tashi ya tabbatar wa kanshi cewar me martaba ne, Dagawa yayi sannan yayi sallama a hankali "Kazo ina san ganin ka yanzu a fada" ya kashe kawai dama haka me martaba yakeyi idan ya gama fad'ar abinda ze fada seya kashe kawai, dafe kanshi yayi ya juya akalar shi zuwa fada yana mejin haushin wannan kiran ainun...... Huddy na kuka tace da mamanta "Ammy amma dai aikinsan cewar ba'a barin aikin Allah ayi na bawansa, ni nasan niyyan Alkhairi nake da sabida haka tsinuwarki bazata kamani da yardar Allah" tana gama fadar hakan ta kashe wayarta ma gabaki daya ta dauki hanyar b'angaren ummu zuciyarta na mata wani irin rad'ad'i shirkafa ai dole ta nemi zarewa ma gaba d'aya wlhy... Tana zuwa akai mata iso, taje bayan sun gaisa da ummu se kuma wasu sababbin hawaye tace murya na rawa "Ummu dan Allah karkiwa magana ta mummunar fassara wlhy banida masaniyar abinda mahaifiyata ke aikata se sati biyu dasu ka wuce, kuma nayi mata nasiha da wa'azin abinda take ba kyau amma batajiba wannan ya sanya nace ni agaskiaya zanzo da kaina na sanar dake halin da ake ciki, zancen cikin nan na Manga Ammy nane taje ta sanya akayi asirin da aka turo mata aljanin dake sanya ake ganin cikin koda a awon asibiti ne kuma yaketa hura cikin yake girma tamkar cikin gaske, wlhy ummu ba yanda banyi da itaba amma sam taqi ta gane taje ta sanya a karya asirin tunda ni nasani babu zaman lafiya tsakaninta da yaa Ali tunda gani yake shiba cikinsa bane ba, yanzun ma da ita na gama waya ta kasa ganewa ta tubarwa Allah ta raba er mutane da wannan takaicin datake ciki, yarinya duk tabi ta gama ramewa ta stuke ta lalace akan abinda bataji ba bata gani ba sam shine kurun nace nizan sanar dake, anemo malamai suyita adu'a ko Allah zesanya asirin ya karye kuma a tayani yiwa Abbin Ameer haquri wlhy ba laifi na bane banmasan da wannan abinba se daga baya" Nisawa Ummu tayi acikin zuciyarta tana godewa Allah daya karbi adu'arta gaskia ta bayyana "Ki kwantar da hankalinki huddy nina sani wlhy ba hannunki aviki koda baki fada ba, sanida na yaba da nutsuwar da addininki tuni, so ban taba zarginki ba,kuma Har a wurin Allah bakida laifi danke akayi amma kika nunawa duniya kinfison waninki akan kanki lallai kin cika er halak kuma darajarki da qimarki ayau tafi ta duk wata mace da yaro ze auro agidannan dama wacce ke ciki,k8nyi abinda dubunki bazasu yiba Allah ya miki albarka ya sanyaki a aljannar sa mad'aukakiya, ni zan sanar da yaro dame martaba se asan matakin daza'a d'auka akai inshaa Allah, mahaifiyarki kuwa kina mata adu'a plss karki wani en damu zata gane gaskia ne inshaa Allah ta tuba kedai kiyi mata biyayya indai bata sab'a abubuwan Allah daya gindaya wa bayin saba" Yaudai ta kasa hakuri kwanciya tayi saman jikin ummu tayi ta kuka tana rarrashinta har Bacci ya kwasheta a wurin..... Sosai me martaba ya tsorata da al'amarin mutane amma seya sanar wa Ali Abbas da Ummu kar wanda yayi wa Manga maganar ze kawo malamin daze yaqi abubuwan a hankali. Yaudai banda sauri babu abinda Ali Abbas keyi so yake yaje yaga Manga koda kallontane ya dingayi, da sallamar shi ya shiga cikin d'akin nata kasancewar ya duba sosai parlor batanan, halin daya saba taddata aciki yauma aciki ya taddata, tana zaune saman sallaya ta rafka tagumi,jin sallamarsa besa dakoda motsa ba se bakinta datake motsawa a hankali wanda ya tabbatar masa cewar amsa sallamar takeyi, abakin gado ya zauna yana jiranta yau seya tsinci kansa da mugun tausayi dajin kunyarta fiyeda kullum, se yanzu ya gano tsananin damuwar datake ciki,se yanzu yake hango gaskiyar ta,yanayin ta kawai ya isa ya sanarwa me lura da hankali cewar lallai she's innocent, tajima a zauna kanta taso, nesa dashi ta zauna da wannan qaton cikin daze kai girman cikin en shida, gashi ajikinta shi kad'ai yake girma komai nata yana nan yanda yake lafiya lau kawar kanta tayi gefe d'aya tunda ya gama zazzaga mata wannan uban zagin takejin wani matsanancin tsanarsa na qara d'arsuwa a ranta da qyar ta furta "Ina wuni" tausayinta me tsananin gaske ya mugun kamashi muryarshi na rawa yace "Lapia lau, na ganki wani kala yau, menene yake damunki?" kallon mamaki ta mishi dama kuma tanada damuwar setace dashi "Kasan ance idan yaro ya mutu acikkn uwa mahaifa rub'ewa takeyi uwar ma ta mutu idan ba'a gane da sauri ba, naji ance ciki yana motsi na bantab'a jin motsin dan Allah ka kaini gun Aunty huddy ta dubani" Wani uban tausayinta yaji ya kamashi daya sanya ba shiri yaje gareta ya rungume kasa daurewa yayi yau kad'ai tausayinta ya sanya ya soma yi mata kuka tamkar wani jinjiri "Bansa dayaya zan kalleki ba Manga bansan mezan ce dake ba, bansan ta ina zan fara ba, a bakina babu wasu ragowar kalmomi masu amfani dazan fad'a miki, tuni na b'atanci sun gama rinjayar su an sun kore su gaba d'aya sam banida hankali ni wawa ne jaki ne ni, kuma butulu wanda besan halacci ba, lallai na cutar dake matuqa kuma nasan dab guntun bayanin dake bakina be isa ya gamsar dake abinda zan aika miki ba, dan Allah badan mugun hali naba Manga ki gafarceni, tun tasowarki da bakin cikina kiike kwana dashi kike tashi, sanina da wanzuwana a rayuwarki be haifar miki komai ba se baqin ciki, Zuwana arayuwarki na kawar da hafsatu Manga yarinya me ban dariya da walwala da fara'a ga barkwanci mara qarewa, zuwana a rayuwarki na sauya ki daga mesan zama cikin mutane zuwa wacce batasan kowa a kusa dake, kasantuwa ta acikin rayuwarki ya sauya kika tashi daga me yawan magana zuwa kurma,bebiya kuma wacce batasan koda ganin mutane, Bayyanata arayuwarki ya sanya kika zama makauniya wacce bata gani sam, yanzu kuma gashi zamtowata jgo arayuwarki ya sanya kika zama abokiyar gabar wasu har suke bink8 da sharri,dan Allah kimun aikin gafara Manga" ita sam bata fahimce shiba gani take tamkar

Chapter 8 of 16