Share this page
kokari a maidani niger naje gida nayi IT na a chan. "Kaɗa kai Nana tayi tace"Allah sarki,bansan yaushe yaran nan zai gane soyayyar da samira ke masa ba,bari abunnan Ya mutu muzo a fara maganar Aurenku". "Da sauri Paki yace"ni da Sammy ba soyayya muke ba Nana 'dan Allah kibar haɗa maganganu." "Tabe baki tayi tace "Ai kuma sai kayi tayi Aurene kamar anyi." Zai magana Abbi Ya katse ta hanyar faɗin "babu inda sameera zata je nan gidan kamar nasu ne, na yarda bata kyauta ba amma babu inda zata je,zata zauna anan har sai ranar da taga yayi mata dai dai da ta tafi. "Zai magana ummu ta hanasa ta hanyar faɗin"imam ya isa haka ,kasan ba yau sameera ta saba zuwa nan ta zauna ba ,sameera Ai ta zama yar,gidannan,". "Tashi yayi baice komai ba ya musu sallama amma a ƙasan zuciyarsa hakan bai masa daɗi ba 'dan yasan Sammy ba tazo da alheri ba. "Sameera Hashim asalin gwarawan Niger minna ne ,tun secondary school take tare da KB da Imam a Federal government college Abuja," Tun junior class suke ture ,a lokacin sammy tayi ta shige musu har sai da ta zama ƙawarsu kuma ƙanwarsu ,sune ke shigar mata faɗa Cos a lokacin she's young ga tsoro ga tsokana, "A haka iyayensu suna zuwan musu visiting suka san sameera wanda a haka suka saba da iyayenta aka zama kamar ɗaya," Baya gama makarantar su suka samu Admission tare a NILE university tare inda ita take karantan Nursing su kuma medicine , Sau da dama sameera kan zo Adamawa kawai dan imam wanda dama tun suna secondary school ta fada masa tana sanashi amma shi Ya nuna mata a ƙanwa Ya ɗauketa, Iyayanta sun yarda da iyayen paki ɗan har ziyartar juna sukanyi sabida amintakar da ta shiga tsakaninsu dan haka duk lokacin da Sammy tace zata Adamawa basu hanata, "Ko a yanzu ma intern ɗin da tazo babu yarda iyayenta basuyi ba akan tayi a nan minna amma ta kafe ",su kuma iyayenta irin mutanennan ne da basu yawan kwab'ar ƴaƴansu a duk Abunda suka so Mai kyau da mara kyau,kawai buƙatarsu ta biya. *********** "Kallan umaimah da ta baro ɗakin daddy Hindu tayi tace "girl Ya dai?" Ƙaramun yake umaimah tayi tace "daddy is on it he's getting it investigated amma for now an gano location ɗin da aka saka clip ɗin, "Anan asibiti ne,im just wondering wanda yayi sannan Mai na masa? Dafata Hindu tayi tace "ki kwantar da Hankalinki komai zai zo Ya wuce,and about paki yarda kikayi treating ɗinsa bai yi ba." "Ɗan shiru tayi tana Mai tuno irin halin da Ya shiga,hes young sannan yanzu yake fighting ma career ɗinsa,"Ita kuwa duk wani abu da take mafarkin achieving tayi,sannan idan ta bar CITY hospital akwai asibitocin da dama da zasu ɗauketa,dole She will fight this for him. "Karshe ma a yanzu da blue print na asibitinta da zata buɗe sannan gini Ya ɗauki nisa ,so take Ya zamana ta gina katafaren asibitin da za'ayi alfahari da And ta tabbatar idan komai ya tafi mata dai dai hakan za'ayi." "Snapping yatsa Hindu ta mata tace girl are you 'in Love." "Da saurinta tace uwar Love ba Love ba". Dariya suka saka a tare kafin ta kalli Hindu tace "it been a l'ong time ". Hope ziyarar nan da kika kawo mun zaki kwana biyu sannan no hotel a nan zaki zauna. Murmushi Hindu tayi tana ɗaga hannu 'in surrender tace naji but maganan bina misra bai tashi ba dole ki zauna kiyi facing aikinki you're needed there girl. Indai kuma ba aiki zaki dawo Cleopatra Hospital ba wanda zan murnar haka ,.and guess what nayi saurayi balarabe sunansa Ahmad ,soon zan kawo shi kasar nan yaganku dangina Da kuka rage anan Cos Ya gama siye ummi a kasar nan. Dariya suka sa suka cigaba da hirar yaushe gamo har yara suka dawo. ******* Okay im still having test tomorrow but still tho. Trust me ,ina mutuƙar sanku Zaku cigaba da samun Double update ne kawai idan na gama test. School is stressing me for now Follow me on wattpad And arewa books @chuchujay https://www.facebook.com/groups/805959663295457/?ref=share Xx Chuchujay ✍🏽 Tbc [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU (a hospital romance ) By chuchujay wattpad :@chuchujay https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta. Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta, Just follow and share i want audience domin baku. Episode2⃣5⃣➡2⃣6⃣. Baki ɗaya haka nan Umaimah ta karasa ranarta a sukurkuce,bata san kasancewar paki a tare da ita ba Ya kamata sosai sai a yau da kwata kwata bata ji sa ba ko tagansa, Motar yaya Abubakar da ta gani a gida Shine Ya tabbatar mata da yana gida , Parking motar ta tayi a gefen tasa ta nufi sashen sa kai tsaye, Tun a ƙofa taganshi yana shirin shiga, Yana ganin ta Ya faɗaɗa fara'ar sa yace "umaimah Kin dawo kenan," Murmushi tayi tace" wallahi yaya na dawo and ganin motanka yasa nazo na gaishe ka cos na kwana biyu ban ganka ba, Shiga yayi tana biye dashi a baya, A falo ta tarar da iyalan sa ,da gudu yaran sukazo gareta suna mata oyoyo inda mahafiyarsu ke ta mata fara'a tana Mai faɗin dama wai kina gidan nan umaimah,yaushe rabon da na saki idona? Zama tayi tana Mai faɗin"maman sultan baza ki gane ba fitar ce da sassafe wani lokaci bana shigowa sai dare Chan,". "Gaskiya dai Allah Ya taimaka ,aikin ku Ai sai ku, Bari na kawo miki abinci, Da saurinta tace "a'a Aunty Im okay dama nazo magana ne kawai da yaya Abubakar." Ƙaramun murmushi tayi tace "bari na baku guri dan tsakanin ki da yayanki sai Allah" Bayan tafiyarta Ya Kalleta yace "umaimah Allah yasa lafiya," Murmushi tayi tana Mai Wasa da hannunta tace"Yaya dama ina san magana da kai ne,ko nace ina san na nemi shawarar ka saboda ina tsoran nayi abunda zai dameni,wasa ta cigaba dayi da hannunta Kafun tace"Yaya I've found someone ,i mean wanda yake san Ya Aureni and im not against it, I might sound somehow amma yaya Im loving the idea saboda ive fallen for this guy, Sannan yaya bai tab'a Aure ba and He's just a month older than me, Shine babban abunda nake tsoro sabida abunda mutane zasu ce,wasu zasu ga kamar Im selfish ina ƙokarin jansa cikin rayuwata bayan nasan ko Aure bai tab'a yi ba,amma yaya abunda nake ji a tattare dashi ko akan Hafiz banji ba,sannan yana mun soyayyar ni kaina takan bani tsoro, Ban san Ya zanyi ba, Duk abunda na fuskanta a rayuwa ta a wannan karan bana ganin komai sai alaƙata dashi Shiru Yaya Abubakar yayi bayan takai ƙarshen zancen ta Kafun yace"a ina yaran yake ,ɗan gidan wanene".? Licking lips ɗin ta tayi tace"Yaran Admiral Muktar paki ne" Riƙo hannun ta yayi yace kali nan umaimah,eh nasan abun sound somehow amma it doesn't matter ,nasan dole mutane zasuyi magana kamar yarda kika ce amma abu mafi muhimmanci Shine muddin idan zuciyarki ta kwanta dashi ta yarda dashi ki saurareta ,saboda you deserve some happiness Sannan yaran nan bake kika masa dole Ya soki ba ,shine yaji yana sanki kuma ya amince zaiyyi rayuwar sa dake so Allah wadai duk abunda mutane zasu faɗa. Babban farin ciki na Anan Shine ,yarda baki sare da Aure ba,bakice a'a ba saboda Hafiz ma Ai yazo maki da soyayya,nayi farin ciki mutuƙa da kika saka a zuciyarki ba kowane Ya zama ɗaya ba sannan da ikon Allah jikina Ya gama bani a wannan karan baza muyi dana sani ba, Duk abunda ke saki farin ciki umaimah nima yana sani ,and a rayuwata bani da buri da Ya wuce naga kinyi settling down a gidan mijinki,abu ɗaya Ya hanani magana wanda Shine gudun yarda zaki ɗauki maganar ,amma tunda yau da kanki kike so na miki Alƙawari zan tsaya miki kamar koda yaushe, Duk wani damuwar ki in dai ina da maganinta Zan maki,Just say the word,and kar ki damu i will talk to daddy . Murmushi tayi tace "nagode yaya ,kai ɗan uwa na gari ne,ina jinka a zuciya ta,ina ƙaunar ka saboda ka damu da damuwata kamar ciki ɗaya muka fito ,ko iya abinda na samu a gidan nan ke nan na godewa Allah. Gyara zaman sa yayi yace "ni dake umaimah Ai ciki ɗaya ne,ko baki san uba ɗaya ne ciki ɗaya ba? Kar na kuma ji kince ba cikin mu ɗaya ba ,da ni dake da umar da usman da Aliyu duk cikin mu ɗaya,it doesn't matter hallayyar su a kanki amma ni nasan suna ƙaunar ki suna kaunar ki ,kawai wani abu ne Chan na banza yake tare musu nuna maki,wa kike tunanin yake samun sa'a kamar tamu? Duk wanda Ya samu ƙanwa irin ki abun yayi alfahari da ita ne,kinsan yarda kaina yake ƙato idan naji abokai na nace wa "Ai Abubakar yayan young beautiful surgeon umaimah Bulama ne,sai kiji na kasa riƙe kaina 'dan har rawa yake kamar zai faɗi,its a real show up ". Dariya tasa tace"yaya!!!"ɗan hira suka tab'a Kafun tayi masa sallama ta wuce ,. Haka nan taji kamar an sauke mata dukkan wata damuwa ,ɗaura ɗamara tayi da zuciyarta wajen nunawa paki soyayyarta ,kamar yarda yayanta Ya nuna mata "Fuck the society as far as she's Happy " Koda ta shiga sashen su Abdallah da Nadiya sunyi bacci Shatu kawai ta tarar a falo tana kallo, Tana ganinta tace"sannu da zawa Adda,zama tayi kan kujera tana Mai cire takalmin ta Kafun tace"baki kwanta ba, Hamma tayi tace "wallahi Adda wai ina jiran shigiwarki ne ko zaki nemu wani Abu," "Shatuuhh!"Idan kina jin bacci Just go to sleep ki daina cewa zaki jirani ko zan buƙaci wani abun ,Babu abinda zan buƙata ,idan ma inaso zanyi da kaina ,Ai kina ma ƙokari in kina mun haka bazan na jin daɗi ba ,kefa yar uwata ce ba yar Aikina ba, Please! Murmushi tayi tace "kiyi haƙuri Adda ,a rayuwa ta kullum burina bai wuce naga na kyautata maki ba,kin san a yan uwan mu kece mace ta farko data fara ɗauka na ta jani jiki cos kowa maganar sa ɗaya ni nayi sanadin mutuwar shifaɗo ,bani da sa'a ,kowa yaki zuwa Ya nemi Aurena kamar wata Mai kanjamau,shiyasa a rayuwata yanzu Kin bani abunyi ,cos kula dasu nadiya ina jinsa har raina ina kaunar yin hakan,suna mutuƙar bani farin ciki. Kallanta umaimah tayi taga yarda tayi bul bul ta ƙara kyau ,Dafata tayi tace"shatuh i want the best For you sannan na ɗaukeki badan wani abu ba ace ma saboda Aikina and su nadiya na bukatar wani,amma nima ina bukatar ki kusa dani,and insha Allahu zaki gani ,sai na maki Auren kece raini ,Auren da masu yan gutsiri tsoma akan ki zasu ji kunya,"And yanzu ma maganar da nake miki na sama miki Niva open university kina gida zakiyi karatun ki,exam kawai zai kaiki, So insha Allahu monday bana komai zan dauke ki muje muyi komai,. Cike da murna ta rungume ta tace "nagode sosai Adda ,Allah ubangiji Ya faranta miki Ya shira maki yaranki." Shafa kanta tayi tace ameen ya rabbi, Wanka tayi bayan ta shiga ɗaki taci abinci ta jawo system ɗinta tana ɗan wani research ,a hankali takan duba wayarta taga koda saƙon paki ne Amma shiru,kamar ta sake ƙiran sa amma tayi ƙokari ta danne zuciyarta gudun kar ta bada kanta, A hakan nan ta gama abunda Zatayi ta kwanta amma tunanin ta baki ɗaya Ya karkata kan paki ,bacci b'arawo ne kawai Ya ɗauke ta tana Ayyana yarda yake. Washe gari kasancewar bazata Aiki ba yasa ta joining yan gidan breakfast duk da kuwa yaya usman da umar sun fita, Bayan sun gama cin abinci tana ƙoƙarin tashi daddy yace "umaimah ina san magana dake mai muhimmanci ,kizo sashena,," "Maganar baza'a iya yinta bane a cikin mu sai anje sashen ka Alhaji?" Maganace dai ta budurwar zuciya da ɗiyar ka take da ita sannan baki ɗaya bata san ta tsufa ba dan haka zuciyarta take mata kwaɗayin Abunda yafi karfin ta,Ai naji jita jitar sannan wayar da kayi jiya ta tabbatar mun ba jita jita bane. Hajiya ta faɗa tana Mai ƙora tea ɗin ta, Ƙaramar dariya Aliyu yayi yace "Ai ni umaimah ban tab'a sanin kina da san zuciya haka ba sai yau,ina ke ina yaran Admiral muktar ,dama dai ace babban ne ya iya maneji dake amma wanda bai taba Aure ba kuma tsaranki Ai Kema kinsani ba sai an faɗa maki ba ,san zuciyarki a fili yake sannan duk wanda yajiki yasan desperation ne ke damun ki kwana nawa aka gama yawo da sex clip ɗin ku a duniya sannan yanzu wata maganar Aure ta bayyana . " "Ai baka san wani abu ba Ali,ita dama sa'a ba ga kowa take ba,ka kalli umaimah a gurin nan ,bazan boye maka ba tafi kowa sa'a a yaran daddy ,i mean ka duba rayuwarta da kyau, a wannan karan ma sai gashi Allah ya kara buda mata sa'arta ta samu mutum irin imam paki,ba san zuciya bane ,rahmace ta ubangiji,Ya kamata ace ka gane hakan, Yaya Abubakar ya faɗa kamar ba shi Ya faɗa ba cos abincin sa ya cigaba daci calmly. Tsaki Hajiya tayi tace "kaji haushi Abubakar Ai ,indai akan umaimah ne nana Surbajo Kafun ta tafi ta barbaɗa maka " Dukan dining table ɗin da daddy yayi ne yasa ta saurin yin shiru,nunata yayi da yatsa yace "na faɗa maki ba sau daya ba ,ba biyu ba akan ki daina saka Surbajo a haukan ki amma baki ji ko? Zamu samu matsala fa,ki kiyaye sannan kai kuna Ali da kake faɗin san zuciya kaima kaso zuciyar ka haifu,. Kai daddy !! Matar yaya Ali ta faɗa a karo na farko tunda aka fara abin 'dan tun gargaɗin daddy babu wadda tayi gigin sake shiga shirgin umaimah ballantana yaran ta, Tashi daddy yayi yace umaimah oya , Babu musu ta mara masa, Zama yayi yace zauna umaimah , Babu musu ta zauna tana Mai narenare da ido 'dan abinda Ya faru a wajen Ya ɗan tabata,wai ace danginka ne ke adawa da kai. Cikin sakin fuska yace "umaimahn daddy menene baki faɗa mun ba?" Shiru tayi ba tace komai ba ,kallon idanun ta yayi yaga sun ciko da kwalla, Ajiyan zuciya yayi yace "kalli nan umaimah im not against duk wani abu da kika zab'a kuma kika ji a ranki Ya miki,Just go for it koda zai maki zafi daga baya, at least Ya saki farin ciki daga farko". Daddy bama zai sani baƙin ciki ba,kamun addu'a ,na zab'i Paki and wallahi daddy ba san zuciya bane ,abunda zuciya ta ke so ne sannan ban amince da zab'in ba sai da na tabbata da hankali na Ya kwanta,and daddy inaji a jikina he's not like Hafiz ,'dan Allah daddy support me i want this. Shiru yayi yana karantar yanayin ta,tabbas Umaimah ta tafi akan wannan yaran da bai sani ba dan ko magan nan bai kai mata ba amma ta kare,cikin san jawo da hankalin ta garesa yace "umaimah bai tab'a Aure bafa.sannan ke Kin tab'a Aure,yaranki uku fa,." Cike da kwarin gwiwar da bata san tana dashi ba tace "daddy Annabi Muhammad (SAW)Nana khadija ya fara Aura kuma she's even older ,daddy anan ma ban girmi Paki ba,babu inda addini Ya haramta Aurena dashi,"Daddy please kaine kawai kwarin gwiwata and jikina yana bani imam alheri ne a rayuwata, Ta karasa maganar tana Mai nare nare da ido. Ajiyan zuciya yayi mussaman ganin Yarda umaimah ta fito masa a mutum,tabbas soyayyar ta rufe mata ido,sannan shi he's looking out for her,baya san tazo Ya yaudareta kamar Hafiz amma ganin yarda bataji nauyinsa ba yasa shi cewa"shikenan princess ɗin daddy,duk abunda kika zab'a nima ina tare dashi sannan ina Addu'ar Allah yasa Shine zai rufeki ko ki rufesa,"Jiya mahaifin sa ya kirani yamun maganar so i thought kawai irin random mutane ne musamman scammers shi yasa ban tsaya jin sa ba nace masa wrong Number ,amma yanzu tunda naji ta bakin ki zan kirasa a sa rana mu haɗu ayi magana sannan ina san ganawa da shi yaran. Cikin kasa da kai tace"daddy sunan sa Imam", Dariya yasa yace jaira"to imam", Haka suka cigaba da zantawa tsakanin ɗiyar da tayi shaƙuwa Mai tsanani da mahaifinta . ************ Su umaimah an kamu 'fa,😂oh ba kunya. Bakina da goro. Chuchujay ✍🏽 TBC. [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU (a hospital romance ) By chuchujay wattpad :@chuchujay https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta. Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta, Just follow and share i want audience domin baku. Episode 2⃣7⃣➡2⃣8⃣ BAYAN SATI UKU. Iyaye sun zauna sun gana har maganar Aure ta shiga tsakani bayan dogon binciken da daddy yayi amma har a wannan stage ɗin umaimah bata sa Paki a ido ba haka zalika muryar sa,da fari ta damu ainun amma da daddy Ya sanar da ita sun gana da shi sai ta debesa ta watsar, Ko da gan gan bata tambayi kb inda yake ba duk da kuwa yarda zuciyata ke san sanin dalilin da yasa bai neme ta ba,bata san yi masa alƙalanci shi yasa kawai ta watsar dashi duk lokacin da yaji yayi masa dai dai yazo inda take yazo. Baki ɗaya yaran murna kawai suke za'aje kaiwa Nameer ziyara a makaranta, Da gudu nadiya ta shigo ɗakinta kanta ɗauke da purple ɗin headband tace "mami ki kalli band ɗin nan tayi da kayan jikina ,bana san naje school ɗin su hamma na bashi kunya a cikin frnds ɗin sa ace kanwar sa bata iya dressing ba," Kallan Baby purple ɗin gown ɗin dake jikinta samfarin Fendi tayi Kafun tayi mata alamu da hannu tace"you look amazing princess ," Blushing tayi tace "i love You mami," Da hanzarinta ta fita tana Mai faɗin,Aunty Aunty ina heels ɗina, Kaɗa kai tayi tace "Nadiya and her iyayi sai ita,"Ƙarasa shiryawan ta tayi cikin Simple but expensive ash jallabiyan ta ,gyara zaman minI veil ɗinta tayi Kafun ta ɗan yi touching fuskanta kana ta jawo flat ash and black D&G takalminta ta saka tana Mai jin zumuɗin san zuwa taga Nameer cos tayi kewarsa sosai,a hakan ma wai 'dan suna waya, A falo ta tarar da shatuh wadda itama taci nata gayun gefenta kuma Abdallah wanda ke ta faman san gyara butterfly tie ɗin sa, Tsigunnawa tayi ta Kama ta gyara masa kafin tace "there you go your highness", Kissing gefen kumatun ta yayi yace"thank you my Queen." Dariya shatuh dake gefensa tayi ganin yarda yaci magani kamar bashine yayi abunda yayi ba, Abdallah da halayyar sa ,idan yayi maka wani abin sai ka sake dubawa kace wannan shekarar sa nawa. **************** NIGERIAN TURKISH INTERNATIONAL COLLEGE ABUJA. Idan ka kalli AHALIN umaimah sai abun Ya baka sha'awa duk da kuwa da sultana wadda ita kadai ta samu zuwa amma sai ta saje dasu kamar ita ta haifo su, A hankali suke takawa zuwa inda aka tanada domin iyayen yara ranar visiting , Tun daga nesa Nameer Ya hango su,da gudu Ya ƙaraso gare su, Kafun umaimah tayi aune Ya ɗane yana Mai faɗin mamiiiiii, Rungumesa tayi a jikinta jin yarda Ya ƙanƙameta cike da murnar ganin ta, Nadiya dake gefe ne tayi gyaran murya tana Mai gyara kitsanta da Ya zubo ta ƙasan band dinta tace "hala baka ganni ba brother," Sakin umaimah yayi yace"come her naughty little Sis," Uhummm Cewan Abdallah, Alamu yayi masa da hannu akan shima yazo yayin da suka saka dariya, Sulatana ma dake gefe ganin Abinda sukayi itama sai ta faɗa jikinsu tana cewa nima hamma Nameer nayi kewarka sosai. Nikam da baibi ta kaina ba Ai ban shishshigi ba,shatuh ta faɗa tana Mai turo bakin Wasa, Ciresu yayi baki ɗaya a jikin sa yace"oh favourite Aunty mana ,kinsan namafi kewanki akan mami," Dariya tayi tace "shiyasa da ka fito ni ka fara rungumewa ba Mami ba." Rayuwar school ɗin su nameer sai dai kace kayi kewar yan gida ba wai kace kayi kewar abinda kake so a gida ba,after all kuɗin ka shagalinka, Murna kawai da farin ciki nameer yake musamman da ya kai umaimah ɗakin su dake na mutum huɗu yace "mami ki kalla bunk ɗina," Yarda yake ta farin ciki Shine Ya kara tabbatar wa da umaimah batayi wrong decision ba wajen kawo Nameer nan. "Hamma kam ina roommates ɗinka ni banga ko ɗaya ba, Nadiya ta faɗa tana mai waige waige, Dafa kafaɗarta yayi yace "little princess sunje tarar parents ɗin su ni ne lucky one cikin su da kuka zo da wuri, Dan far tayi da ido cike da iyayi tace "that's how much we love You". Kaɗa kai umaimah tayi tana Mai hango girman Nadiya,tasan dole akwai rikici dan iyayin cikin nadiya sai Allah, Bayan sun fita suna zaune suna hira suna ciye ciyen su Nameer nata faman basu labarin school, Kamar a mafarki Umaimah ta tsinci muryar sa ,sallama yayi hannun sa ɗauke da ledoji manya guda biyu,zama yayi a gefen Nameer yana Mai facing Umaimah yace "da kyar na gano ku," Uncle Handsome? Nadiya ta faɗa da mamakin ganin sa, Murmushi yayi yana mai mata Alama da tazo ,da saurin ta kuwa tazo tace"nazata mafarki nake ,"Dariya shatuh tasa Kaɗan jin kini binin Nadiya Kafun ta gaida sa inda Ya amsa mata cikin sakewa sosai, Abdallah dake gefen umaimah ma da saurin sa Ya taso ganin Nadiya ta ɗane cinyan sa ta zauna yace "sister thats my spot. Dariya PAKI yasa ya rungumesa jikin sa yace"your Royal highness ,. Giggling Abdallah yayi dan yana jin daɗi yaji Ya kirasa da hakan,alama yayiwa sultana da tazo su gaisa ,itama cike da ɗauki taje garesa. Good afternoon uncle"Nameer Ya faɗa babu yabo babu fallasa," Murmushi Paki yayi yace "Big boy ,afternoon ,Ya school," Ɗan ƙaramin murmushin yaƙe Nameer yayi yace "Alhamdulillah." Kaɗa Mai Paki yayi yana Mai san jan hirar tasa da Nameer yace "I had to fly daga lagos nazo na kawo maka ziyara,and i was thinking of abinda kake so ban sani ba cos kaƙi bari na sani so na siyan maka abunda nake so which nasan muna da same taste ne". Sake Wani murmushi Nameer yayi yace "nagode Uncle Allah Ya kara Arziƙi," Ya gajiyan ka kuma na wanchan ranar da kazo, Wani daɗi yaji a ransa dan yasan yanzu Ya fara jawo Nameer team ɗinsa. Ba wani gajiya big boy,it was nice cos nazo naganka ma maminka. Satar Kallan umaimah yayi wadda baki ɗaya ta mayar da hankalinta kan wayarta tun zuwan sa, Tunda ta ɗan saci kallansa taga ya sake wani irin mata kyau da kwarjini ta ɗauke kanta,wato ma He's 'in a Good shape amma Ya maida ta kamar wadda Babu ita, And bama gurin ta yayi niyan zuwa ba tunda Ai ya iya tasowa daga lagos yazo yaga Nameer and bama wannan ne na farko ba ,yazo Nameer ɗin kuma bai faɗa mata ba, Lallai Paki. Cikin sanyin murya yace "ranki ya daɗe ina wuni" Yi tayi kamar bata san bolar da ta kwaso sa ba, "Mami dake uncle handsome yake " Ɗauke idanun ta tayi daga kan waya tace "Nadiya ki kiyayeni 'fa ,Kin fini kunne ne?" Jin haka yasa shatuh fahimtar akwai wata a kasa 'dan haka tace "Nameer muje ka nuna mana basket ball field Ɗinku mana" Da sauri nadiya ta miƙe tace "yes please Bros,nima ina san na gani,Bayan tashin yaran ta ƙara haɗe ranta , Matsowa Ya farayi inda take yana puppy eyes"dagowa tayi ta kallesa tace "Paki don't dare me saboda you wont like me a bit, Hannayen sa yasa a kunne sa yana Mai yin puppy eyes yace "im Sorry baby". Cikin jin haushin sa tace don't baby me',as 'in kama maidani wadda Bansan abunda nake ba, 3 weeks 'fa,Paki ,ka mayar dani wadda Bansan san Mai nake ba,maganar Aure ke tsakanina da kai ,you met My father ,at least ko baka neme ni ba a phone call is okay, No koda message ne,amma gani shara,ko tafiyar ka ban sani ba ,da ace hamma bai zo ba dan bazan ma san ka yi tafiya ba,kasan mene paki? Just Forget about maganar Aure na da kai idan har ka shirya dauka ta serious ayi maganan amma yanzu let me even warn you,stay away from me. Cike da fushin da baisan tana dashi ba ta kare zancenta idanun ta a gefe, Ƙara matsowa kusa da ita yayi yace "im Sorry baby im very very Sorry ,kiyi haƙuri dan Allah and ki daina cewa ban ɗauke ki da muhimmanci ba,ke ce first priority ɗina ,yes na yarda ban kyauta ba da ban kira ki ba sannan banzo na faɗa maki zanbi hamma lagos ba,but honey im hand tie ,Nana was on My neck,ga sameerah,dole na kashe wayana and zuwan da nayi naga daddy i waited for you baki zo ba, And bana san zuwa asibiti saboda kar asan nazo,i was fighting for us, tafiya ta ɗinnan ne kawai yasa Nana bata cigaba da takurawa ɗin nan da maganar Auren sameera , And lastly i fall ill. Da saurinta ta ɗago ta kalle sa cike da damuwa tace ill? Fuskewa ta sake yi da ta fahimci damuwarta tace"that still doesn't justify your actions paki,im angry ". Juyar da kanta tayi, Sake dawowa gabanta yayi yace dan Allah Abar ƙauna kiyi haƙuri ,duk yarda zan faɗa maki bazaki gane ba amma rashin jin muryarki da banyi ba cikin satin Allah kaɗai yasan irin damuwar da na shiga wallahi, Dan Allah kiyi mun Afuwa bazan ƙara ba,and guess what? tafiyana cewa Nana akai ina Chan asibiti a kwance ban san inda kaina yake ba sannan ciwan sanki Ya ke san kashe ni, Dariya yasa yace "da ƙyar ta haƙura amma da sharaɗin a gidan mu zamu zauna a part din da daddy ya gina kwanan nan zamu zauna nasan she Means trouble amma we have no option dole mu bi nata ko na kwanaki Kaɗan ne, Im sorry baby im so selfish idan yazo kanki ,ina san ki kasance tawa ko yaya ne,dan Allah durlyn let me be the one for you,lets fight this together, Yarda yayi da ido kamar zai kuka ta kalla. Tashi tsaye tayi tace

Chapter 10 of 15