Share this page
duk wani abu da zai fito a bakin ki koda zagi nane domin ni akan ki mahaukacin masoyine, Ya ƙarasa yana Mai saka irish ɗin da Ya ɗauka a bakinsa a yayin da idanunsa ke cikin nata kamar zai fasa kwayar idanunta. "Wata iri ƙaramar dariya tayi Kafun tace "imam paki Ina san ka maida hankalinka kasani ni ba tsarar ka bace.." Tsk yayi da baƙinsa Kafun Ya karkaɗa dan yatsansa cikin rashin amincewa kafin yace"point of correction ni yayanki ne da wata ɗaya". Serious face tasa tace "lallai zamu samu matsala da kai a asibitin nan saboda i wont tolerate this," "Wani murmushin Ya kuma yace "nifa ba wai ina nemanki da hanyar banza bane umaimah Auren ki zanyi ". Nunasa tayi da ɗan yatsanta tace "DR Bulama,ba muyi kusancin da zaka kirani umaimah ba ,dafe goshinta tayi cikin rashin sanin Abunda zatace masa ta furta"get out ". "Yunƙurawa yayi kan table har sai da ya Kai saitin fuskarta Kafun yayi wani irin arnen murmushi ganin yarda Ya zaro idanu yace "Stop thinking silly ,im not going to kiss you Ina so naji ne idan da gaske kike san datse Alaƙar da na kulla mana ,amma ga mamakina sai naji zuciyarki tana luguɗe da sauri da sauri tana kiran Imam Paki,wanda Haka Ya tabbatar mun baki tsaneni ba". "Wata irin kunyace ta kamata musamman da Ya zaman zuciyar ta sai da tayi skipping beat. Murmushi yayi yace "abincinki zai huce zuwa anjima Zan dawo na sake duba lafiyarki dan yanzu aiki nane." Tashin sa keda wuya farouk Ya kwankwasa kofa, dama ta bashi Ya shigo, Kallan paki dake tsaye yayi Kafun Ya Kalle ta yace "Doctor kinyi baƙo and yana ta creating scene akan dole sai Ya ganki duk da bai da Appointment dake sannan baiyyi kama da mara lapia ba amma yace a faɗa miki Baban nameer ne " "Cikin wata irin faɗuwar gaba tace"Habib?"Mai yake yi anan? Ɗan kallanta Paki yayi yaga take yanayinta Ya chanza jinn ance baban nameer ,abu ɗaya Ya sani wanda shine wannan Habib ɗin ba baƙon maraba bane, "Baya san mata katsalandan musamman a yanzu da yake san gina Alaƙa da ita wadda yasan zaiyyi nasara, Juyawa yayi zai fita bayan tace da nurse farouk yace ya shigo. "Imam paki?" Tsaye yayi chak jin ta ambaci sunansa Kafun kuma Ya juyo yana Mai fuskantarta yace "na'am Abar alfaharina". Kamar bataji abunda yace yayin Amsawa ba tace zauna . Na'am? Ya tambaya kamar baiji Mai tace ba, Ɗaga masa gira guda ɗaya tayi tace "ba kana san soyayya dani ba"? Zama yayi kamar anyiwa yaro kyautar sweet yace "nace a turo ne?" Tsintar kanta tayi da yin ƙaramar dariya duba da yarda Ya faɗi maganar kafun tace"zan biya maka buƙatarka ne ta yanzu kacal ,bayan nan kuma ka fita hanyata ,just take it kamar im using you for now ". Shafa kwantaccen sajensa yayi Yace "im here use me like a tissue amma ki sani idan na ɗanɗana sai an ƙaramun,.." Tana koƙarin magana Habib ya turo kofar ya shigo, Dago Kai tayi ta kallesa , Ya chanza sosai kamar ba shi ba,girma Ya ƙara bayyana a tattare dashi Haka zalika kasumba da Ya tara wadda a da bashi da ita, Sallama yayi yana mai washe mata haƙora, Haɗe rai tayi ,jan kujera yayi Ya zauna yana Mai faɗin"umaimah ina wuni". "Wata ƴar dariya ce ta kwace mata jin gaisuwar da yayi mata Kafun tace "Ina fatan kayi wunin ka lafia habib sannan ina fatan abunda ya kawoka Mai amfani ne". "Da saurinsa yace "Wallahi Mai amfani ne umaimah ,Kallan Paki yayi wanda tun da Ya shigo yake Kallansa ," Mai da Kallan yayi kan umaimah yace"wannan Ya ɗan bamu Guri mana" Kallan paki tayi kafun ta kallesa tace "duk maganar da zakayi kayita a gabansa saboda tsakanina dashi babu wani boye boye saboda MIJIN da zan Aura ne,take gaban paki Ya yanke Ya faɗi jin abunda ta faɗa wanda yazo masa a ba zato babu tsammani,amma a wani bangaren kuma sai yaji dama daga zuciyarta maganar ke fita ,amma Shin wanene Wannan ɗin? " Shine tambayarsa. "Wata ƙaramar dariya yayi ya kalli Paki yace "haba umaimah ,wannan yaran kema Ai kinsan ba sa'an Aurenki bane Daga gani da kyar idan baki girmesa ba ,kodan kinga kina da kyan jiki?" Ajiyar zuciya tayi tace"Habib idan maganar kyan jikina kazo yi nima nasan yana da kyau ,zaka iya tashi ka tafi dan Ina da abun da yafi saurarenka amfani," Sniffing yayi yace "kalli nan umaimah ni nasan wasa ma kikeyi,dan Allah umaimah a bar maganar Wasa tunda kuma kince nayi gabansa zanyi yasan matsayin sa, "nazo ne akan Auren mu ,'dan Allah umaimah,nasan saki uku Ya shiga tsakanina dake amma Ai kinyi Aure har biyu wanda Addini a yanzu Ya ƙara hallarta mun ke,ki taimaka ki bani dama na rufa maki asiri Ko dan Nameer dake gurinki," "Nayi imani da Allah yaran nan yana buƙatar uba,Mai zai hana kizo mu sasanta kan mu?"Nasani daddy idan yaji daga gareki zai amince , "Umaimah look I'm a changed man wallahi duk abunda kika sanni dashi yanzu na bari." "Lokacin imam ya fahimci wanene Habib,duk da bai san menene ya raba su ba amma tabbas yasan abunda Ya raba su babu daɗi sannan daga jin furucin Habib bawai Ya dawo bane dan Ya tuba ,Ya dawo ne dan wani boyayyen burin sa" "Har a lokacin hankalin umaimah a kwance ,Kallan sa kawai take tana observing ɗinsa Kafun tace"Na yarda baka da kunya Habib, " "Yanzu da kazo ka ganni anan kana nufin asirina a tone kaganshi?" Ko na taba ce maka ka kawo taimako wa Nameer mai shekara sha daya yanzu? Kai kana tunanin idan ni kaɗai da kai muka rage a duniya zan sake zaman aure da kai? "Bana san sunan Nameer yasake fita a bakin ka saboda idan baka manta ba a yanzu baka da wata alaƙa dashi," Kalli nan' Ta nuna masa paki , Kallan pakin yayi kafun tace"ka kallesa da kyau nasan ka hango qualities ɗin da baka dashi," Ka kallesa da kyau,He's handsome,charismatic ,hot and breathtaking,ba sai na maka wani bayani ba kasan ta ko ina Ya fika ,to ka faɗa mun Habib ina dashi Mai zanyi da kai? Ka kalli kanka a mudubi kafin daƙikiyar kwakwalwarka ta baka shawarar zuwa inda nake? "Ajiyar zuciya tayi har a lokacin baza kace maganar daga bakinta take fitowa ba Kafun tace "ka tashi ka fita sannan zan manta da wannan maganar Ko dan darajar Nameer da Ya shiga tsakaninmu. " "Cike da bala'i yace"kaji mun ƴar iska 'fa ,ni zaki ma lalata har kina nuna mun wani kwartan yaro dake saka miki tayin igiyarsa da ba tayi kwari ba ,kuna kunshe a office kuna alfasha kice wai ya fini?" "Dan na zo maki da sauki kenan,Ko kina tunanin ban san karuwancin da kike da likitocin dake asibitin nan ba ?" To Ko wanne baya na yake sabida ni na fara farƙe ki na fara sanar dake menene wahala da zaƙin sex,ina fatan baki manta ba a yarda na ƙarbi budurcinki a wulaƙance a daren da a ka kawo ki gida na. Ina nan a Habib ɗin da kika sani kuma wallahi sai an ban ɗana tunda bake kika yiwa kanki ciki ba kika haifesa reproduction ne daga sperm ɗin. "Karshe ma Kin Auri ɗan kungiyar asiri masu tsafi da mutane gwara ni giya kawai nake sha banyi abunda za'a rataye ni har mutuwa ba,"Wama Ya sani shi wannan ɗin wanne kalar lalatace ne.... "Kai karshen zancensa yana dai dai da ƙaimasa naushi da paki wanda keta tafarfasa yayi a baki yana faman huci." CHUCHUJAY ✍🏽 TBC [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU (a hospital romance) By CHUCHUJAY EPISODE 8⃣ Wani irin tafarfasa paki yake Kafun yace "wallahi idan baka tashi ka fita ba zan karyaka na karya banza 'dan wallahi babu abunda zai faru". "Idan kana ganin kuma kuri nake kar ka tashi ka fita," Ganin irin tafarfasar da Paki yake yasa Habib tashi Yana faɗin"wallahi sai kasan ka nausheni dan wallahi Asirinku Ya gama tonuwa Kai da ita ," "Sannan Ai ba karya bane nine nan nafara daga daga da ita ,kai ni koda zan karbi budurcinta ka tambayeta ta fada maka a banza na karbeshi da wulaƙanci,a buge kuma yarda zaka gane a banza na ɗauki abunda kake bibiya,sannan maza biyu bayan ni suka bi gurin sai kuma waɗanda baka sani ba Kai kanka,ni nasan a yanzu Ya zama tafki" "Ba karamu ɗaci da takaici maganganun Habib suka bawa Umaimah ba musamman da Ya kasance a gaban Paki wanda ita ta jawowa kanta da tace Ya tsaya,she shouldn't have involved him, "Bata damu da mutane su san Aurenta ba amma abinda Habib ke faɗa sirrinta ne,rabon da amata wulaƙanci irin wannan har ta manta, "Naushi Paki yake Kai masa ta ko ina ta yarda Habib ɗin bashi da halin ramawa," "Security Landline ta kira wanda babu bata lokaci mutum uku suka shigo ,sakin sa paki yayi yace da Security ɗin su tafi dashi" "Har lokacin bakin Habib bai mutu ba ,babu abinda yake faɗi sai "wallahi sai kun san dani kukayi ,sannan kisa a ranki kamar na ɗauki Nameer ne,kuma sai na tona muku asirin iskancin da kuke" Har suka fitar dashi yana surutai, "Cije baki paki yayi yana kallan kofar da aka fita da Habib ,debating yake da zuciyarsa na ya juya ko kar ya juya." "Juyawa yayi inda idanunsu suka haɗu cikin na juna yayin da nata ke cike da kwallar dake san fitowa". "Cije bakinsa yayi yace"well im Sorry akan abunda Ya faru,He's a psychopath bai kamata ace kin saka maganar sa ba a zuciya ta dame ki " "Hannayen sa Ya dora akan kunnuwa sa da sigar toshewa yace "maganganun da Ya faɗa ,na toshe kunnuwa na ,kisa aranki banji ko ɗaya ba,sannan ki sani babu Abunda wani zai fada akanki naji soyayyarki tayi rauni a zuciyata,"Hasalima karamun sanki naji kamar anyi" "Dariya tasa cikin hawayen da yanzu suke reto a kuncinta kafun tace"Stop pretending kamar kasan ni wacece saboda wasu abubuwan da kaji a kaina,ka ɗaina tunani kai wani knight 'in a shining amour ne you are all scums duk hallayyar ku ɗaya ". "Zama yayi kan kujera yana Mai faɗin wallahi.." "Bai Kai ga ƙarasawa ba tayi watsi da kaya dake kan table ɗinta tace "GET OUT FROM HERE BEFORE I lOOSE IT". "Tashi yayi in surrending manner yana Mai ɗaga hannunsa sama yace "yi hakuri zan fita,". Babu musu ya juya Ya bar office ɗin. "Riƙe bakin ta tayi ta saka wani kuka Mai cin rai tace "oh GOD this is embarrassing ". Koda Ya fita Kai tsaye changing room Ya wuce yana Mai jin zuciyarsa na masa zafi,ga wata zazzafar soyayyar umaimah da tausayinsa da Ya kuma Shigarsa,kamar yarda ta faɗa baisan wace ita ba ,sannan shi a yanzu soyayyarta yake nema in yaso duk lokacin da taji Ya kamata zata bashi labarinta, "Tsoran da ya gani a idanun ta a yau dangane da maza shine yake kara bashi tsoro,dan ciwan da Habib Ya famo mata ba ƙarami bane ". Yana tsaka da wannan tunanin yaji an dafa shi" Ɗagowa yayi dan ganin wanene ne" "Cike da kulawa Kb yace "Paki naga fitowar wannan baƙon na DR Bulama da maganganun da yake faɗa sannan kaima naga fitowarka wanda Ya tabbatar mun akwai abunda ya faru ,"Wanene mutumin and Mai yasa ka zauma nan kana wannan tunanin, Hope ba abunda nake tunani bane? "Ganin yanayin fuskar Paki yasa KB cewa "No No No paki No dont tell me maganar da mukayi da Kai baka dauka ba?" "Cike da damuwa yace"wanda Ya fita office ɗinta Habib ne ,shine mijinta na farko . Kuresa da ido Kb yayi yace uhum"menene Abun damuwa a gurinka da tsohon mijinta Cos naji ance har dukan sa kayi" Ko zan ji dalilinka. "Kallan Kb yayi na wani lokaci kafin yace"Kb gayen nan ɗan iskane da kaddara kawai yasa umaimah Aurensa tun fari sannan maganganun da yazo yana faɗa akanta bakaji ba babu daɗi wanda na kasa jurewa! Shine ka dake sa? Da fari ma Mai kake a ciki a yayin da take zantawa da tsohon mijinta , Ba tare da Ya kallesa ba yace "ita tace na tsaya Cos ta ce masa we are in a relationship' wanda yayi pissing ɗinsa off " "Wani irin takaici ne Ya ziyarci Kb Kafun yace"yanzu ka yarda amfani da kaine kawai Zatayi Cos na tabbata gobe baza ta ganka tace maka honey ba ," "Paki wai ina tunanin ka Ya tafi,nida da zarar na sake sanin wani labarinta nake kara tabbatar da she's not the one,"Haba paki akwai mata da yawa da suke bibiyarka a waje maine zakayi da bazawara Mai issues akanta da yawa? "Sosai maganar KB ta Sosa masa Zuciya wanda tabbas da ace ba shine ba da babu abunda zai hanasa chasa sa yayi masa shegen dukan da bakinsa bazai kuma faɗar aibunta ba," "A zahiri kuwa sai cewa yayi"KB i Love her and thats All that matters sannan bazan boye maka ba maganganun da kake faɗa a kanta suna Sosa mun rai wallahi bana jin daɗi dan kawai kaine". "Marairaice fuska yayi yace"na faɗa maka ina santa ba da Wasa kuma nake ba ,shin haramun ne idan naso mace irinta,bafa wai mazinaciya bace ,Aure ne kawai tayi guda uku wanda batayi sa'arsu ba wannan ta samu ƴaƴa uku Shin menene laifinta a ciki,"? "Na yarda bansan Mai Ya fito da ita daga gidan mazajen ba amma tabbas wannan ɗan iskan da yazo a ido ma kasan ba mijin da zakawa ƙanwarka ko ƴarka, Sha'awa bane" "Juyowa yayi yana facing ɗinsa yace "KB dan Allah idan baza ka tayani san Umaimah ba ka daina zaginta a gabana ina jin ciwo," Wallahi ina mata san da idan na rasa ta zan shiga hali Mai wuya. "Karantarsa KB Ya nutsu yanayi,tabbas Tunda yake da paki daga yarintarsu har girmansu bai taba ganin irin wannan soyayyar a idanun imam ba" "Ya yarda yana santa amma yana ji masa ahalin gidan su ne wanda da wuya su karbi batun Umaimah kar ma ace nana" "Ajiyar zuciya yayi yace "naji Paki,idan kana san Dr Bulama bazan hana ka ba sannan bazan sake fadan abu mara kyau akan ta ba ,amma ni zan maka bincike akanta ,"amma 'fa wani hanzari ba gudu ba ,kasan babu yarda za'ayi ta so ka a yarda take" Sannan bama wannan ba,babu yarda za'ayi su Nana su amince da wannan maganar kaima kasan ba sai na faɗa maka ba, "Murmushi yayi a karo na farko yace "KB ni na yarda da kaina kuma nasan da yardar Allah umaimah zata soni ,sannan maganar yan gidan mu ,kabarni na fara samun soyayyar tukunna nasan yarda zan bullo masu". "Murmushi KB yayi yace shikenan abokina Allah Ya zama abunda yafi Alheri yanzu ka shere hawayen zamu shiga labor room dukkanmu da Dr Maryam ,sannan around 5 muna da lecture da masoyiyarka". "Tsaki paki yayi yace uwar hawaye zan share tunda Ai ka cika bokiti dashi," And anya Dr Bulama zata iya koyar da mu wani abu yau ɗinnan! "Ɗaga kafaɗa Kb yayi yace"well a yarda na lura bata Wasa da Aiki kila wannan abun bazai hanata ba". A tare suka fita inda suka shiga daƙin haihuwa dan ganin karban haihuwan practically duk da bashine ganinsu na farko ba. *** Zazzaune suke a karamun lecture hall ɗin dake cikin asbiitin suna Mai tsumayin Dr bulama, "Wani Sanyi imam yaji a zuciyarsa lokacin da yaga shigowarta," Fuskarta babu annuri amma hakan bashi ne Ya boye kyawnun fuskarta ba. Ƙaramun white board ta matso dashi a yayin da ta kunna system ɗinta yarda zai Kai ga projector ɗin da already akayi connecting , Cike da kwarewa ta fara koyar dasu wanda dukkansu suka bada hankalinsu akanta, Kamar ance ta ɗaga Kai ta hango Aisha shareef gefen Paki tana Mai kananan surutu inda shikuma hankalinsa baki ɗaya yana kanta, Buga maker ɗin tayi da ƙarfi yace "shareef you're get up from that seat sannan ina fatan kinsan nan ba filin soyayya bane,why Are you disturbing the guy bayan shi hankalinsa yana kan karatu" "Baki ɗayansu suka maida hankalinsu kan Aisha shareef wadda kunya ta kamata kamar ta nutse, Kasa tayi da kanta tace "sorry Dr . "This should be the last time da zan ganki zaune kusa da imam paki tunda naga Alama yana distracting ɗinki now dawo first roll". Babu musu ta sauko first roll d'in ta zauna tana mai jin haushin abunda umaimah tayi mata. Bayan lecture d'in Ya kare kowa Ya fita ,saura paki, Dago kai tayi ta kallesa ganin bai tashi ba,tace"Mr im done with your class zaka iya fita Next set zasu shigo," "Saukowa yayi yana Mai faɗaɗa murmushinsa ,har sai da yazo gabanta Kafun yace "were you jealous ?" Excuse me? Murmushi yayi yace "nevermind I LOVE YOU too,"Kafun tace wani Abu yayi saurin ficewa a hall ɗin , Binsa kawai tayi da kallo yayinda ta tsinci kanta da murmusawa. CHUCHUJAY ✍🏽 TBC [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK AURE UKU (a hospital romance) By Chuchujay. EPISODE 9⃣ Washe gari bata shiga Asibitin ba saboda weekend ne kuma musamman saturday ,sunday ne takan shiga , Tana tsaka da bacci taji ana ja mata ƙafa, "Yi tayi kamar bata san anayi ba ,"Cigaba da jan ƙafar yasata farkawa , Dariya nadiya tasa tace "hamma nameer i won dole ka bani Tab din ka na sati nayi game,"Ɗan bata rai yayi yace"mami why do You wake up We bet ne 'fa. "Tashi tace tace "akan me kuka yi betting ɗin tell mami" "Haurowa gadan da take Nadiya tayi tana Mai washe hakora tace "mami betting mukayi nace masa yau saturday mami na bacci amma nasan idan naja miki kafa zaki tashi ,shine hamma nameer yace Ai bazaki tashi ba Cos kina da gajiyan weekday ,amma idan kin tashi yasa mun tab ɗin sa na sati ɗaya". "Ƴar karamar dariya umaimah tayi Kafun ta kalli nameer dake faman haɗe rai zai bawa nadiya Tab ɗin sa tace"okay ku saurare ni,"Anything betting is haram,ko menene shi koda da wasa ne,a musulunci babu kyau 'dan Haka Banda Wasan betting, "Idan nameer zai baki tab ɗin sa aro ne to Ya baki amma ba wai ɗan Kin cinyesa a bet ba ,okay". "Kaɗa kai sukayi a tare inda Nameer yace dama mami banyi niya ba"cos duk ranar da na arama nadiya Tab ɗina sai ta cinye chaji tas take dawo mun dashi . "Mami nima Tab ina san na kalli johnny johnny hamma Nameer kuma baya bani, "Dariya Umaimah tasa ga maganar da Abdallah wanda yake shigowa da gudu shatu na binsa a baya yayi". "Ɗannowa yayi kan gadon yana Mai hawa jikinta yayin da ta rungumesa ," Zama shatu tayi bakin gadon tace"Adda ina kwana ?"Kin tashi kenan. "Murmushi tayi tace "wallahi shatu sun tashe ni zan ce ma ,ina fatan baku jira ni ba kun karya ." "Kaɗa kai tayi tace "ai Adda kema kin san rigimar Abdallah da rashin haƙurin sa ga yunwa ba zai bar mu shan ruwa ba musamman ace mun kai sha ɗaya ." "'Ɗan buɗe ido tayi tace "har sha daya ,kace na sha bacci,". "Mami mene plan ɗin yau ko za mu Roly park ne it have been a While,nameer Ya faɗa yana Mai Marairaice murya.. A tare suka haɗa baki wajen faɗin"roly park,suna chanting tare,". Zata yi magana taga wayanta na ringing da baƙuwar Number, Ɗauka tayi ta kara a kunnenta tana Mai faɗin hello a yayin da yaran nata suka cigaba da faɗin Roly park ,Roly park,. Daga ɗaya bangaren taji an kashe wayan 'dan Haka tace naji roly park kuje Auntyn ku ta shirya ku bari na yi wanka na ci abinci, "Ihu suka fara cike da murna ,kana suka fita nadiya na faɗin Yau zan ridding real horse". "Kallan shatu umaimah tayi bayan fitar nameer da nadiya tace"Auntyn yara shiryawa zakiyi muje fa". "Murmushi tayi tace "Adda kuje dai ku dawo kinsan ni ba ma'abociyar san fita bace,ina nan gida ina jiran ku,ga wankin su Abdallah chan ma nasa cikin washing machine ga gugan su kinsan ni da aiki muna haɗe amma wani zuwan zan biku. "Kallan ta Umaimah tayi cike da kulawa tace "shatu nasan halin ki fa kilan ki zauna kina aikin tunanin da kika saba ,in dai Aikine idan mun dawo ni da kaina zan taya ki". "Faɗaɗa murmushin nata tayi tace "Allah Adda kar ki damu ,ba wani tunani da zan tsaya dama akwai wani series film da nake kalo ,ina gama aiki zan cigaba har ku dawo," "Shikenan tunda kince Haka ,shafa kan Abdallah da yayi makale a jikinta tayi tace "malam Abdallah maza tashi kaje Aunty ta saka maka sweater a saman rigan nan Cos da sanyi,". ****** "Kai tsaye Roly park suka je ,park ne wanda aka tanada domin yara dan kuwa duk wani abu da yaro zaiso na dan Wasa akwai a gurin . "Kallo ɗaya zaka yiwa su nameer kasan suna cikin farin ciki,"Motan wasan dake ta juyawa da yara nadiya tayi da gudu tana cewa"mami this". "Murmushi umaimah tayi tace "okay lets go ,da gudun su sukaje gurin ,inda ita kuma taje siyan coin. "Sun jima a wurin motan ,dan coins ma sai da ta b'ata a lissafin siya,. Bayan sun bar gurin suka nufi gurin doku nan Wasa, "Nameer ne yace"mami ina nadiya tayi"? "Da mamaki ta juyo tace "nadiya ? Ina tayi"? Cikin lokaci ƙankani hankalin umaimah Ya tashi da ta fahimci Nadiya bata biyosu ba tun daga baya, Daukar Abdallah tayi ta riƙe hannun Nameer tana Mai san assuring kanta a gun suka barta ,tace"Nameer nasan tana chan gurin Cars ɗin chan ,muje zamu ganta" Kula da ɗan ruɗewar da tayi nameer yayi yace "mami nasan ma tana chan nadiya kuma da san mota ,ko sch mukaje sai mun shiga aji zaki ganta ta shigo," "Wata kwallane ya zubowa umaimah lokacin da sukaje gurin motar bata ga nadiya ba ,"Gogewa tayi tana Mai tambayar mutumin da suka siya coin a gurinsa ko ya ganta. "Kafun Ya bata amsa ta tsinci muryar nadiya tana mai faɗin"mami!!" Da saurinta ta juya,turus tayi ganin nadiyan da Paki ? Da gudu nadiya ta zo gurinta tana faɗin "mami meet My new friend ," "Wani kallan banza ta bata Kafun tace "ina kikaje when kin san i warned You ba sau ɗaya ba akan strangers kina so na fara dukanki ko?". " A yarda tayi maganan da harshness Ya tabbatarwa da Paki tayi fushine dan koda ta joyu sai da ya tsinci tashin hankalin da take shirrin boyewa, ". Boye nadiya yayi a bayan sa yace"calm down mummy And ni Ai kinsan ba stranger bane". And i saw this beautiful sweetheart buying her mothers favourite icecream. "Cikin fushi umaimah tace And taya kasan nice maman nata"? Smirking yayi yace "well i guess boyewar bata da amfani ,i was stalking you and nasan fuskarta a hoto sannan na kiraki earlier naji suna ihun kuje Roly park And nayi missing ɗinki sosai na rana ɗaya kawai ,cos na saba da saka ki a idanuna muddin idan kuma ban ganki ina shiga damuwa shi yasa da na samu dama na dama." Haɗe rai Nameer yayi yace"mr man who Are YOu?". Murmushi paki yayi ganin yarda nameer Ya haɗe ransa ,tsugunnawa yayi dai dai tsayin Nameer Yace "ni sunana Imam paki Sannan ni Abokin aikin mamanka ne Kaifa. "Sake cin mur Nameer yayi yace"Nameer Habib And im My mom's protector and i don't find You to my liking a bit ". "Dan buɗe baki paki yayi jin yarda angry young man ɗin ke nuna masa kuri kuri baya sansa,"Shafa kansa yayi yace "well dear Nameer i cant help it amma na tabbatar zaka so kazama frnd ɗina idan ka zauna dani" "Ni bana na so Ya zama frnd ɗin ka cos handsome uncle nawa ne ni kaɗai ,nadiya ta faɗa tana jin haushin yarda Nameer yake cewa baya san Paki ". Murmushi paki yayi Ya tashi kana yace "well beautiful princess its okay since ni dake team ne ,and im sure little Prince is on Our sida too ya ƙarasa maganar yana Mai miƙawa abdallah hannu akan yazo ," "Ganin Ya miƙo hannu yasa umaimah sakar masa shi ," Murmushi yayi yace "mamin mu wannan katan saurayin kike ɗauka?" "Da blank kallo ta kallesa tace "Paki zaka iya tafiya cos time ɗina ne yau da kids ɗina idan abune da Ya shafi aiki Ya kawo ka ka bari mu hadu ranar monday amma yanzu is My Family time". "Shafa gefen gashin sa yayi yace"nima Ai Family ne ko beautiful princess. " "Da tsalle Nadiya tace yes mami dan Allah ki bar uncle handsome mana i like him". "Tsintar kanta tayi da kaɗa idanun ta tace "what ever". "Murmushi yayi yace "After you Queen,"Murmushin da batayi tsammani bane ya kwace mata,wanda Ya sauka a idanun Paki. "Yarda nadiya da Abdallah suka Sake Suna Wasa dashi abun har mamaki yake bata musamman yarda Pakin Ya biye musu kamar yaro, " "Amma Nameer kuwa babu abun da yake sai Aukin haɗe rai karma ace yarda yaga maminsa ta ɗan saki jiki da Paki har tana dariya idan sukayi abun dariya". Bayan sun gama wasan su ne Abdallah Ya fara faɗin "mami Food ," "Food Abdallah ko ,nima kagan ni na fara jin yunwa ,juyowa yayi Ya kalli umaimah Ya turo baki yarda Abdallah yayi yace "mami food". "Dariya tasa tace "don't do that paki you look childish ,tsayawa Kallan dariyar da take yayi yana Mai sake admiring ɗinta ,jinsa yake kamar Ya mallaketa ,jinsu Nameer yake kamar shine Ya haife su,yaushe wannan bunrin nashi na Auren umaimah zai cika? Yaushe zata bashi dama Ya nuna mata soyayyar da bata taba gani ba a gurin ko wanne ɗa namiji?" "Snapping fingers ɗinta tayi a fuskansa tace" paki magana nake like forever tunanin mai kake?" "Shafa kansa yayi yace "naki" "Kaɗa kanta tayi tana Mai jin kumatunta na ja duk da ba yau Ya fara maganar yana tunanin nata ba amma a yau sai taji kunyar abun da Ya faɗa". "Restaurant suka shiga dan cin abinci,Family table suka zauna,kallo ɗaya zaka masu kaga sun burgeka Cos baza kace wai ba Family bane ". "Bayan sunyi order suna zaune suna jiran order

Chapter 4 of 15