Share this page
shiga cikin nasa, Cire idanunta tayi cikin nasa tana Mai kashe wayanta , Muryarsa ta tsinta a yayin da yake faɗin,"zaki iya yin Aiki a haka".? Wata irin karamar dariya tayi ta ɗago da idanunta ta kallesa tace"first this is My personal cabin 'dan na tabbata a sama Kafun ka shigo kaga an saka Doctor Bulama's Cabin Nasan atleast ka iya karatu zuwa nan, Secondly we Are not that close beside ban san ka ba,ina so ka riƙe wannan Alaƙar ta supervisor da dalibi itace tsakanina da kai dan naga alama kana san wuce gona da iri,kasan limit ɗinka, Thirdly ina san ka sani,i dont mix duk wani abu da Ya shafi Aikina da wani abun duk girmansa so don't mistake what happened as My weakness Now get out." Gyara tsayuwar sa yayi yana Mai folding hannunsa a kirjinsa cikin blue kayan likitoci, a bangare ɗaya kuma yana mata wani irin kallo Mai kashe jiki, Coffee ɗin da ya kawo mata Ya aje kan table Ɗinta har lokacin idanun sa na kan idanunta Kafun yace"cold coffee ne 'dan nasan ba lallai kin karya ba,a lokutan da kika ware na Aikin da za'ayi kinci minti goma a waje ,komai yayi ready ke ake jira ,so take the coffee and ina san ki sani Ko Auren ki goma a duniya da yara kimanin faɗin duniya akwai wanda hakan bai dame sa ba da duk wani Abu da za'a faɗa akan ki. Juyawa yayi Ya fita a cabin Ɗin. Bin kofar tayi da kallo a yayin da taji cikin ta yayi wani ƙugin yunwa, Daga cup Ɗin coffee ɗin tayi ta shanye Cos bata san shiga O'R ba tare da tasa komai a cikinta ba, Amma tabbas za suyi magana dole tasa gayen nan a inda ya dace dashi. **** Kamar kullum yau ma bayan tayi sanitizing hannunta ta shiga operation room ɗin da hannunta a ware tana tsoran kar wani infected abun Ya tab'a ,dukkan team ɗinta sun hallara tare da IT student Ɗinta guda uku, Bayan ta zama set ta koma kan mara lafiyan da batama san duniyar da take ciki ba tace "hour nawa aikin nan zai dauka Dr Fatima?" 1 hours doctor "Dr fatima jnr ɗin umaimah ta faɗa professionally," Timer ɗin da akayi setting ta maida minti 40 wanda Ya bawa interns ɗinta mamaki karma ace Paki, Daga gefen su Aisha shareef tayi murmushi a hankali tace"i admired her naji ance she's the most fastest doctor here". Cike da kwarewa tace"zamu gama cikin 30 min And kamar yarda kowa yayi reading its not just hematoma But subdural Hematoma And the patient have 2% chance so Ya 'dan ganta da luck dinta But we would do our very best, A hankali ta fara neman larger access to blood clot ɗin,wanda shine (craniotomy), Inda ta cire section na ƙashin dake tare mata hanyar gudan jinin, Bayan ta kammala,ta replacing section na ƙashin kafun ta rufe soft tissues ɗin ta hanyar amfani da sutures . Maida hankalinta tayi kansu Paki tace "warkewar mara lafiyan kuma zamu barwa Allah ne but the operation is done and its a success ,And since nayi undergoing craniotomy warkewar zata dauki lokaci ,so yanzu za akai patient ɗin recovery room Kafun a kaita ICU once situation ɗin is stable she would be moved to the regular room har a sallameta,duk Mai tambaya Ya bini office, so nayi highlighting ɗinsa "Alamu tayiwa sauran doctors da nurses ɗin kan su dauka daga inda ta tsaya Kafun ta fita, Idanun Paki ne Ya sauka kan timer wanda sai yanzu ma yayi clicking 50 min, Faɗa yayi da bakinsa, Murmushi Dr Fatima tayi tace "she's the most fastest doctor da zaku gani a asibitin nan ,idan kuka maida hankali zaku karu da ita sosai. Kallansa Kb yayi bayan sun fita yace mutumina zo muje mu zanta mana. Babu musu Ya bishi duk da yana san zuwa gurin umaimah da excuse ɗin yana da tambaya, Kallan KB yayi bayan sun zauna yace"Paki kasan dai ni da Kai mun wuce abokai sai dai yan uwa ko? Ni da kai tare muka girma mun damu da damuwar juna da duk wani abu da zai zamar mana Mai kyau, Kalli nan Paki sameera yarinyace Mai kirki duk da nasan wani lokacin tana da rawar kai amma na yarda da san da take maka kuma zaka iya juyata duk yarda kake so amma mutumina kai kanka kasan maganar Dr umaimah ba abune Mai iyuwa ba ,kai kasani Ko kowa Ya amince Nana bazata taba yarda ba, Kai babu ma wanda zai taba Amince maka da maganar ta kaima ka sani, My guy Auren ta uku 'fa har da yara Uku,kasan maine Ya fito da ita daga gidan mijinta? Baka taba Aure bafa tayaya kake san duniya ta fara ɗaukar maganar nan? Bro ni nafi tunanin ma harda attitudes Ɗinta ya fito da ita gidan mazajen 'dan tana jin babanta Attajirine ,i mean guy she's rude with words, Na yarda rumours ɗin dake yawo akanta jitajita ne amma kasan gaskiyar ne?. Dan Allah imam ka sake wani tunanin amma hanyar nan da ka ɗauko mana ba mai bullewa bace kwata kwata , Ka rufa mana asiri kamar yada Allah Ya rufa mana ka ɗauke idanunka kan matar nan,idan kuma bakaji ba ni da kaina zanje na sanarwa da Abbi Abunda ke faruwa in yaso Ko asibitine mu chanza ,gwanda fa mu daki karfen nan da zafi. Shiru Paki yayi yana kallan kb wanda shima da idanun Ya bisa yana san jin amsar Paki , Dafa shi Paki yayi yace "kar ka damu ". Murmushi yayi masa shima Ya mayar masa kafin Ya tashi Ya nufi office ɗin Umaimah , Knocking yayi har sau biyu Kafun tace Ya shigo, Shiga yayi bakinsa ɗauke da sallama, Kallo ɗaya ta masa ta mayar da kanta kan abinda take, Politely Ya kalli kujerar dake gefenta yace "zan iya zama Dr"? Cire glasses ɗin idanunta tayi tace "zaka iya zama idan ka tabbata ba wani shirmen Ya kawo ka ba,". Zama yayi kan kujerar yace "Dr aikin ki na yau was amazing ,sai naji kin sake burgeni ta Ko ina". Wani banzan kallo ta bashi kafin tace"kana da wata tambayane regarding it?" Gyara zaman sa yayi Yace "nazo ki duba ni ne Dr bani da lafia," Dafa kirjinsa yayi dai dai saitin zuciyarsa yace "nan gun ke mun wani irin bugu muddin idan na saka idanuna akan mace ɗaya,"Baki daya tunani na tsayawa yake, ita ka dai nake gani,bana ganin Ko wacce mace bayanta sannan abunda Ya wuce dangane da ita baya gaba na sannan baya tunanina ita kaɗai ce ke ciki, Aje pen ɗin dake hannunta tayi tace" Well"kafi kowa sanin ni ba cardiologist bace sannan ni ba therapist bace da zan zauna sauraran damuwarka, babu wani abu da Ya shafeni a ciki so please Imam Paki idan kana san cigaba da Aiki a karkashina ina so ka sani Aiki shine abunda Ya dameni a cikin Asibitin nan,so please idan babu wani abu da zaka faɗa mun da Ya shafi Aikin da Ya haɗa ni da kai zaka iya bani guri ina Aikine. Wani irin murmushi yayi yace"amma Dr bulama abunda yake damuna Ya shafeki,nasan zaki ga magana ta kamar Shirme amma ina san ki sani wadda take hana mun wannan walwalar Sunanta DR UMAIMAH BULAMA, a kwana biyun da nayi da saninki soyayyarki ta shigeni wadda itace ake kira da Love at first sight . Ina Sanki,sannan zuciyata tace na sanar miki 'dan da zafi zafi ake dukan karfe sannan a bari Ya huce shine yake kawo rabon wani. Cikin kwanakin tasan Paki na da ido akanta wanda take ɗauka kamar admiration ne amma batayi tunanin izzarsa ta kai har Ya shigo cikin office ɗinta ba yace wai yana santa. Yar karamar dariya tayi tace"shekararka nawa?" Murmushin nan nasa da yasan yana ɗaukar hankali yan mata yayi yace"shekarata ashirin da tara amma a cikin shekarar tawa za'a ɗauke wata ɗaya wanda na baki,ma'ana na girmeki da shekara ɗaya tunda nasan Kema shekarun ki kenan," Sannan nasan kin yi Aure har sau uku sannan a kowanne Aure kina rabo, Ma'ana kinyiwa ƴaƴana yayyi, mene yafi wannan daɗi? Tun kafin na haihu yarana na da manyan su,sannan ina san ki sani idan na Aureki insha Allahu in dai ta gurinane bazan taba sakin ki ba da yardar Allah,ni na yarda a kaddarar Aurenki nawa ne na har Abada ,ki rufeni Ko na rufeki wanda jikina yana bani sai munga jikokin mu. She was speechless ,lallai fukafukansa sunyi girman da tashi Ya rage musu,ba ƙaramun tafarfasa ta tsinci ranta yanayi ba ,lallai Paki bai ga bangarenta mara kyau ba sannan Ya rainata irin rainin da babu wanda Ya taba mata,zatayi magana taji wayarta na ƙara, Director ne ke kiran ta ,ɗagawa tayi bakinta da salllama kafin tace "Yes sir im coming in a jiffy". Kashe wayan tayi ta tashi ta kalli Paki ta Nunasa da wayarta tace "maganar nan bata ƙare ba,i will look for you". Ta kai bakin kofa zata fita ta tsinci muyarsa yana Mai faɗin"shekara guda babu kwana biyu," A cikin shekara guda da zanyi a asibitin nan sai na sa miki soyayyata ,idan kuma a shekarar baki fara sona ba koda kaɗan ne nayi Alƙawari zan bar field din nan na har Abada ,zan chanza career ta nayi Alƙwari. Cije lebenta tayi na Ƙasa tasa kai ta fice a yayin da yayi wani murmushi yana Mai jin santa ta Ko ina, Yayi shirin da bazai ja da baya ba.... ************* Da salllama ta shiga office din ,batayi mamakin ganin Dr Jabir ba 'dan tafi tunanin abunda Ya haɗasu dazune yaje kunnensa, Zama tayi tana mai cewa"good day sir" Murmushi dattijon yayi yace Dr Bulama . Bayan Sun gama gaisawane yace "Dr bulama nasan ke likitace wadda tasan Mai takeyi na yarda dake da aikinki,"Duk da yarda kika yi appearing tough nasan deep zuciyarki akwai soft guri , Nan ga Dr Jabir akan abunda Ya faru dazun ,nasan kina da dukkan right ɗin da zakiyi suing dinsa amma Yazo takanas ya Sameni akan na kiraki na baki hakuri ,kinsan shi harshe.. Kallan Dr jabir tayi wanda yayi narai narai ido Tace "director ,ni kawai inasan Ya faɗa mun lokaci da yataba ganina ina rabawa mata jikina,director he's accusing me of something big 'fa, lesbianism 'fa," Yes kuɗin babana baisa na zauna gidan miji ba sannan nayi Aure sau uku na haihu sau uku bafa wai shine yake nufin Allah baya sona ba ko kaddarata bata da kyau, Amma 'dan me wani mutum ɗan Adam zai judging ɗina? Ina sane da duk ƙazafin da ake mun a cikin asibitin nan a,im arrogant ,rude,im here because of My father,we Are money ritualist,i Am a lesbian duk inaji 'fa jira kawai nake na samu mai fuskantata wanda yau na samu sannan a shirye nake na nuna masa karfin dukiyar da muke da ita, Im sick and tired sir,nazo gurin nan from scratch ,babu wanda yasan ta yaya na kawo nan gurin, Im here with My blood ,sweat and tears,ina matsayinane saboda dagewa, I wanted it from the start saboda yarda na rasa mahafiyata wa brain tumor And nayi Alƙawarin cetan mutane da dama, Ba fa wai ni na bawa kaina talent ba Allah ne, Ba ni nace Allah Ya bani fast hannu ba shi Ya bani 'dan yasan zai amfani al'umma so Mai yasa DR jabir keda damuwa da hakan 'dan nafi tunanin diss ne, Dafe fuskarta tayi tana Mai danne hawayen dake san zubo mata. Baki daya jikinsu yayi sanyi karma ace Dr Jabir,ture kujerar da yake zaune yayi Ya tsugunna kasa yana Mai faɗin"Dr bulama i was wrong na yarda har da baƙin cikin ma ,'dan Allah ki yafe mun". Kallansa tayi Kafun ta tashi tace "Forget about it "Kafun ta fita a office din. CHUCHUJAY✍🏽 To be continued . [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU (a hospital romance) by Chuchujay Episode 6⃣. Wai ni kam imamu yaushe zaka kawo mana mata ne gidan nan ,mun gaji da wannan gafara san banga ƙaho ba ,gaka dai geme geme kana shirin bawa talatin duka amma kamar an maka ƙwari Ko budurwar Arziƙi baka da ita, Muntari ? Ko ni ƙadai abun yake damu ne ,ga dai nan usama matarsa ciki na biyu ne da ita,nan ga inteesar cikin fari gare ta ,kanwar ka ma kenan ,idan kuma ba so yake na mutu banga jininka ba ,ko kuwa baka da lafiyar mazantaka ne. "Tari Paki Ya fara saboda kwarewar da yayi,ummu(mahaifiyarsa)ce ta miƙa masa ruwan da ta zuba zata sha tana Mai shafa masa baya". Tsaki Nana tayi tace "karyar soyayya kike nuna masa Habiba,idan da soyayya ki sa shi yayi Aure itace karshen kauna idan kuma ba maganar da na faɗa ta rashin lafiyar mazantakan bace Ko kuma leƙeleƙe. Affan ne Ya aje spoon ɗinsa Ya tashi a gun yana mai jin takaicin Nana"Ai kamar jira take ta koma kansa tana cewa" yo kaji mun shegen yaro,dan inawa Yayanka faɗa shine abun yayi maka ciwo?"To dake ni, Kaima ai yaci ace ka fara maganar Aure shekara ashirin da ɗaya kaida wannan Mai ido a loƙon" Haɗe rai Afnan tayi tace"nifa nana tunda nazo gurin nan ban miki magana ba,ke shikenan baki san a zauna lapia daga wannan sai wannnan". Wani salati Nana ta rafta ta kalli mahaifinnasu tace muntari kana ji Ko? Dama ai ance yarinya idan ta balaga ta fara nono da jini shikenan sai tana ganin dai dai take da kowa , Yanzu 'dan Allah muntari sabida tsabar ta'ada ta kafurai da kuka daura ma kanku Shine ke hanaku killace ƴaƴanku ,to wallahi muddin ni na haifeka kuma na isa da gidan nan da mutanen dake cikinsa to dole a aurar da yaran nan uku ,sun isheni ,ga rashin ɗa'a ga rashin kunya da rashin girmama na gaba dasu wanda suka koya gun uwarsu, Fuu Affan Ya bar gurin a yayin da Afnan tace "Ai sai kizo ki mun Auren tunda akan ki nake zaune a Gidan nan ,in dai fitina ne kin iyata saƙo saƙo, kece ba ga Ummu ba baga mu ba ,mene muka tsare miki ne ? Kuma ai Abbi kika haifa ba mu ba, Tsawar da mahaifinta ya daka mata yayi dai dai da kukan da Nana tasa tana Mai faɗin"Ai shikenan muntari tsakanina da ƴaƴanka kuma sai duka ,kwana kaɗan Ya rage su fara mun duka ,dama waccan figaggen yaran Apan Mai zubin jijiya yafi kowa haye mun sai kuma ita Apinan ɗin 'dan idan ban ƙaryaba har bangazata ta kusa yi jiya" Duk da sanin halinta da Abbi yayi bai hanasa cewa da Afnan ta bata haƙuri ba,sanin mahaifin nasu baya wasa da abunda Ya shafi nana yasa tace"kiyi haƙuri Nana ,sannan Ai Allah yana kallon,mu kuma shaidane ban bangaje ki ba kikace na kusa bangaje ki amma kije na yafe miki ladan haihuwar Abbi da kikayi,sannan ni ba sunana Apinan ba ,ba kuma sunan Affan Apan ba idan baki iya ba kice Hassan da usaina tunda su nasan bazai maki wahala ba". Kafun taji wata masifar ta Nana ta bar dining Area ɗin , Kallanta ta mayar kan Imam tana Mai binsa da idanu a yayin da ya maida hankalinsa yana Mai cin Abincinsa cikin nutsuwa, Cike da fitina tace "tuzuru ba magana ne," Still bai Kulata ba Ya ɗauki cup d'in chapman ɗin da ummu ta zuba masa Ya shanye yayi hamdala, Kafun Ya kalli mahaifiyarsa yace "ummu gaskiya sai an tara mata dubu tukunna za'a samu mace mai irin girkinki,gaskiya Abbi Ya iya zabe ,kalar hannunki kalar abincinki". Ai kamar Nana na jira tace"inji ubanka,ina dadi a abincinnan duk an cika kafu zabo duk da ansan likita ya hanani ci dole sai an kasheni kuma wallahi nan gani nan bari kabewar kan kabari,a hakan kuma zaka ƙare Kana santin abincin uwarka bana matarka ba,"Ai kuma ka shiga uku dani yanzu tunda Auranka Ya zungureni sai anyi zaka samu sauƙina. Tashi imam yayi yace Ummu ,Abbi sai da safenku,Nana ke kuma zan kawo maki wani magani Uku,safe ,uku rana, uku dare. Har ya kai hanyar da zata sadashi da bangarensa yanajin ƙananun kuka da masifar Nana wai Ya kirata tab'abbiya ,dole yasa ummu tashi sabida ruwan diban Albarkar da Nana ke mata wai ta haifa masu yara irin yaren ta marasa kunya kafurai. Mahaifin Imam Alhaji Muktar Paki mutum Paki ne dake cikin kaduna ,ta wani bangaren kuma mutanen Adamawa,a Adamawa Ya tashi 'dan nan Ya tarar da iyayen sa amma hakan bai hana sunansu na PAKI tasiri ba,su Biyar iyayensu suka haifa maza huɗu mace ɗaya inda maza biyu suka rasu Ya rage saura su uku, Sai Ya zamana shine babban gidan. Naval Officer ne wanda yake da matsayin admiral , A wani Zuwa da yayi America birnin New york Ya hadu da Habiba wadda take half Nigerian Half NewYorker ,mahaifinta ne ɗan nigeria mahaifiyarta kuma yar newyork,'dan Haka yaren hausa a bakinta kamar tana ƙasar,kasancewar su achan ɗin bai hanasu bin addini ba da hanya Mai kyau, Su biyu ne gurin iyayen su ita da yayanta Areefullah, A lokacin da Alhaji muntari Ya kawo maganar Aurenta Nigeria gida ba ƙaramun balli mahaifiyarsa hajja Hanne(Nana) ta tayar ba akan sam sam bata yarda Ya Auri kafura ba , Ƙarfin mijinta da kuma biyayyar da take masa ce tasa wannan Aure Ya ɗauro amma 'fa habici duk inda ta zauna, Bayan rasuwar mijinta wani ciwo da tayi ta tattara ta koma gidan Alhaji Muktar a lokaci ummu na da cikin imam ,babu irin zagin da bata sha gurin Nana duk da irin wahalar da tasha da ita duk da itama jinyar da take na ciki 'danma intisar wanda imamu kebi tana 'dan kama mata, Irin mitar Nana da halayyar ta a dole ummu ta saba tun tana sawa a ranta har ta saba musamman da ta lura da babu abunda zatayima Nana ta burgeta 'dan tun filazal ta nuna bata santa, A Haka dai suka cigaba da rayuwa har Allah Ya azurta ummu da yan biyu Affan da Afnan, Duk da halin Nana hakan bai hanata jin jikokinta a ranta ba kar ma ace imamu wanda duk jarabarta bai cika Kulata ba , Duk ranar kuwa da Abbi Ya dawo daga Abuja Ya bani da korafe korafe na an mata kaza an mata kaza kullum a haka take, Tayi nacin san ta sakewa Abbi Aure amma abun yaci tura 'dan duk yarda tabi sai Ya bulle dan shi baya da lokacin mata biyu,bama wannan ba shi yana san matarsa ita kadai kuma ta ishesa haka zalika ƴaƴa biyar ɗin da ta haifa masa Ya gode Allah duk da Allah ne bai sake basu rabo ba. ********** Bangaren umaimah kuwa koda ta koma gida tun a parking space yaya Aliyu ya tareta, Rabawa ta gefensa tayi zata wuce dan bata san masa rashin kunya sannan bata san ƙarar da energy Ɗinta akansa 'dan yau da batu Ta dawo wanda dole ayisa yau 'dan ita bata da time da safe kafun kuma ta yi Aikin kwana gwanda tayiwa tufkar hanci. Wani mari yaya Aliyu Ya ɗauke ta dashi wanda yazo mata a bazata, Juyowa tayi ta kallesa Idanunta Ya kawo ruwa hannunta dafe da kuncinta tace"mari 'fa Yaya Aliyu,you slapped me". Cike da masifa yace"na mareki ɗin Ko zaki rama ne? Ba dai ke kinyi wuyan da zakina wa matata gorin haihuwa ba wallahi nan gaba bulala Zansa na zaneki mara tarbiyya kawai sakariya wadda ta kasa killace kanta guri ɗaya gidan miji,menene Amfanin ƴaƴa irin naki masu uba daban daban ke ba akuya ba". No this can't keep on, da gudu ta yi ciki tana faɗin Daddy? Daddy Daddy im leaving this house. Cike da tashi hankali Alhaji Bulama Ya miƙe ganin yarda ta shigo tana kuka tana kiran sunsa , Lapia? Ya tambaya yana Mai rike hannunta, Cikin kuka tace "Daddy gidan nan zan bari nagaji da gidannan,ace ni da gidan ubana ni da yarana bamu huta ba ,Daddy abunda akewa su Nameer a gidannan is too much for kids there age ,sannan ba wannan ba yanzun nan 'fa marina Ya Ali yayi." Mari? Daddy Ya faɗa da mutuƙar mamaki. "Sai ki fadi Mai kika mashi Ya mareki Ai ba wai kawai kizo kice Ya mareki ba ,jiyan nan gabana babu ko kunya kika yiwa matarsa gorin haihuwa, Hajiya ta faɗa tana Mai kauda kai ". Cikin rufewar ido Umaimah tace"dama Ai hajiya zakiga nawa laifin amma baza kiga nasu ba tunda ni bake kika haifeni ba amma dake kika haife ni bazaki ƙi fadar bangren da matar Ya Ali ta fara mun gorin zaman Aure ba ,sannan dake kika haifeni bazaki tab'a faɗawa yarana cewa ubansu daban dabanba sannan uwarsu ta kasa zaman Aure ba,baza kuma ki taba barin yan uwansu suna kwararsu ba ko kuma matan ƴaƴanki, Yara kanana baza kuna wasa da mental health ɗinsu ba, Amma yayi dama ba gidan ne baki so na zauna ba? Zan bar miki ki zauna ke da ƴaƴanki, Fita tayi a ɗakin, tana jin daddy yana ƙwala mata kira amma ta ƙi sauraransa 'dan marin Aliyu Ya kaita bango, A Sashen yaya Abubakar ta ɗauko su NAMEER ,taji daɗi yarda bata tarar da yaya Abubakar ba,bata tsaya sauraran maman Sultan ba ta sakasu cikin mota ta ,kamar jira take gate man Ya buɗe mata ta figi motar zuwa titi. Wattpad:chuchujay AREWA BOOKS https://arewabooks.com/book?id=653305e91c06f4783fc2ef84 Facebook:https://www.facebook.com/groups/805959663295457/?ref=share CHUCHUJAY ✍🏽 TBC. [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU (a hospital romance) By. Chuchujay EPISODE 7⃣ Umaimah! Na'am Daddy . Gyaran murya yayi yana mai gyara zaman sa yace "umaimah naji komai da yake faruwa ,sannan ina Mai baki Haƙuri ga dukkan abunda ya faru wanda a yanzu Ya zama past ɗin da baza'a kuma maimaitawa ba nan gaba na miki Alƙawari, Yanzu ki ɗauko su Abdallah kizo mu koma gida zamu zauna a yi magana wadda na tabbatar miki babu makamancin Abunda Ya faru da zai kuma faruwa indai nine Mai gidan Bulama sannan marin da Ali Ya miki har haƙuri zai baki . Shiru tayi kafun tace"ni Daddy bana so Ya bani haƙuri kawai ina san Ya kiyaye Ko da Wasa kar Ya kuma marina, 'dan Allah Daddy idan ya kuma shari'ace zata rabani dashi, tunda dai su basu ɗauke ni yar uwar su ba,tun kuruciya ina sane da dukkan abunda suke min daga su har hajiya,yaya Abubakar ne kawai yake nuna ni tashi ce". Sannan ni Daddy ba zan koma gida ba, ba tare da na samu Mai kulamun dasu nadiya ba tunda Family na duk Albarkars u babu Mai sansu. Dafa ta yayi yace "umaiman daddy idan kina faɗan Haka har da Daddy fa". Ɗan karamun murmushi tayi tace"ni banda Kai Daddy dan nasan da ace kai mace ne zaka kula mun da yarana kamar Kai ka haifesu," Yanzu ma Dada tace zamu tafi da shatu ƴar baffa dikko ƙanin baffa da mijinta Ya rasu babu abunda take gida ni ko biyan ta ne zan nayi duk da tace bata so, Hankalina zai fi kwanciya idan tana tare dasu,sannan ba wai nace Aunty sadiya bata mun ba, Daddy itama Ga ɗawainiyar yaranta ga na su nadiya abun yana mata yawa, Dama kuma Nameer jiya yace mun yana san zai rubuta exam ɗin NTIS (Nigerian Turkish international school)na Abuja yayi jss to sss a chan wanda dama nima na dade Ina so. Murmushi daddy Ya faɗaɗa yace kinga shikenan sai suje tare da Ibrahim(ibi) ya samu ɗan uwa, kicin kicin tayi da ranta tace"Daddy nifa ba wai bana san Alaƙar su nameer ne da jikokin ka na gun su yaya usman ba kawai ni dai gwanda nameer yaje Abuja ɗin in yaso su suje na nan Adamawa ɗin. " Tabbas abunda zaisa umaimah ta nemi su ibi suyi nisa da nameer ba ƙaramun abu bane duba da yarda take nunawa yaran kauna , Shafa kanta yayi yace shikenan yarda kike so Haka za'ayi, yanzu dai kije gurin baffa ki kira su nameer ɗin mu koma gida tunda ai nasan Ko yanzu kikace shatun tazo zata zo Ai baza a tsaya ma dasu Nadiya karatu ba ,ga Abdallah ma za'ayi enrolling ɗinsa ya kamata kuma ace da kaina naje na saka shi. Bata san cigaba da musu da Daddyn nata 'dan Haka tace "to daddy". Sallama sukayi da Dada da baffa yayin da suka ɗauki shatu wadda a kalla umaimah zata bata shekaru huɗu da haihuwa , Taron gaggawa daddy ya kira a daren ranar wanda dukkan sun tabbatar da sun hallarta har da matan su kafin Ya buga musu zazzafan warning ɗin da Ya tabbatar suma zasu wa ƴaransu dan bazai lamunta ba su b'ata masa gida da negativity ba. Sanin Halinsa yasaka ko wannensu shiga taitayi. Washe gari da sassafe ta wuce asibiti inda daddy kamar yarda Ya faɗa Ya dauki Abdallah da kansa ya kaishi makarantar su Nadiyan domin saka shi. Tana zaune a office kamar kullum bayan Farouk Ya gama shigar mata da duk abunda take bukata ciki har da coffee ,bata nemi wani cookies ba 'dan yau da irish and egg sauce ɗin da shatu tawa su nadiya ta taho , A hankali take kurban coffee ɗin a yayin da hankalin ta guda yake kan system ɗinta tana studying wani method na surgery, Kulan irish ɗin ta buɗe ta faraci a hankali bayan tayi bismillah, Knocking taji a bakin door ɗinta, Sai da akayi a karo na biyu Kafun ta bawa Mai kwankwasawar izinin ya shigo , Da sallama a bakin sa ya shigo wanda jin muryarsa kaɗai sai da yasata kwarewa , Da saurinsa Ya tako yana faɗin Ya salam kinyi missing ɗina har haka kenan, Bottle Water ɗin dake gefen Kulan Ya ɗauko ya balle mirfin Ya miƙa mata ,babu musu ta ƙarba ta kafa bakin Gorar a bakinta . Sai da taji dai dai Kafun ta aje ruwan,kallan sa tayi tana Mai haɗe ranta tace "lapia"? Murmushi yayi yace "lapia ,da fari dai ina san saka Ki a ido nane domin a yanzu kallan ki shine yake kosar dani naji bana jin ko wacce irin yunwa," "Na biyu kuma idan kin manta ni ban manta ba kince ni dake zamuyi magana dan Haka yau da zumuɗina nazo Asibitin nan Cos i cant wait to hear

Chapter 3 of 15