Share this page
mazan da na Aura nayi Auren soyayya ,And it was a very beautiful moment kafun nazo na gane kuskurena so dont Judge BOOK by its cover". "Kaɗa kai tayi tace "ƙwarai we shouldn't Judge BOOK by its cover so shima Paki kar ki judging ɗin sa according to what you faced," "Wani abu deep inside me yana faɗa mun Paki Alkhairi ne sannan karki manta har Hafiz Ya mutu yana san ki ,kawai dai shi hanyar da Ya ɗauka dan yin rayuwar sa ne ba mai kyau ba ,amma kema kin san yana sanki," Allah Ya jiƙansa da Rahma. "Tashin motan umaimah tayi bata ce mata komai ba ,Motar da aka saka Dr Jabir ta bi ganin sun yi gaba ,tana kallo ta mirror Paki Ya shiga motar sa Ya biyo su. "Kallan ta Hindu tayi da ta kula da wanda take hange tace "you're young umaimah kar ki cutar da kan ki ,just Listen to your heart and fuck the society ". "Ba dai tace mata komai ba ta tashi motar ta ,ganin bata ce komai ɗin ba yasa Hindu yin shiru amma tasan a zuciyar Umaimah tunanin abunda ta faɗa mata ɗinne Take". "Gate ɗin wani ware house aka buɗe musu suka shiga, Dariya umaimah tasa lokacin da ta faka motarta ta kalli Hindu wadda ke mata kallan "dariyar Mai kike " Kafun tace "Kin san mai nakewa dariya ",wata dariyar ta kuma sakawa Kafun tace " "Idanun Jabir nake hangowa kilan yayi shiru ne dan yaji ina faɗin a lallab'a mun shi ,ai kuwa zai sha lallaba dan a idanun soldiers' ɗin chan ma ƙiris suke jira. "Tana kokarin fitowa a motan paki yazo Ya buɗe mata kofan motan idanun sa cikin nata,itama ɗin shi take kallo, Ganin Ya tare bakin kofar yasa Hindu buɗe side Ɗinta ta fita tana Mai murmusawa, Kallan sa take itama shiɗin ta ke kallo taƙi ce masa ƙala, Tsugunnawa, yayi kan gwiwar sa yace "abunda kika ce akan ko ina da hannu akan Clip ɗin chan yanzu Kin tabbatar da bani da hannu,And Koda wanda na sani ne muddin da hannun sa ciki bazan barshi ba sannan soyayyar da nake miki Mai tsafta ce,ba wai ina sha'awarki bane,ƙaunarki nake. "Bana fatan abunda zai b'ata maki suna duk ƙanƙantar sa,ba kece ba a clip ɗin chan amma kasancewar Fuskar ki ciki ba ƙaramun soya mun zuciya yake ba," "Dafa saitin zuciyar sa yayi yace "wani irin ƙuna haka nake jin zuciya ta ," Ƴar ƙwallar dake shirin zubowa a gefen idanun sa Ya goge yace "wallahi tallahi Umaimah ina mutuwar sanki ,wallahi ina miki san da bana yiwa kaina. "Ƴar da kike nuna kamar zamana cikin soyayyar ki abune mara dacewa, da ace da yarda zanyi na cire soyayyar ki da na yi Ɗan na faranta miki rai , Wallahi umaimah ina sanki da yawa babu abunda Ya dameni da past ɗin ki ni present ɗin ki ne a gaba na, Kiyi haƙuri idan soyayyata tana b'ata miki rai . Tashi tsaye yayi ya juya yana Mai goge idanun sa, Ba tare da Ya juyo ba yace"And na manta ban faɗa miki ba ,guy ɗin da yayi editing Clip ɗin yana ciki shi muka fara kamawa Kafun Ya sanar mana da Dr Jabir Ya bashi kuɗi masu yawa yayi editing amma bashi yayi uploading ba ,sannan an cire clip ɗin daga dukkan websites,". "Juyawa yayi Ya taka Ɗan shiga ciki," Baki ɗaya taji kamar an cire mata wata laka a jikin ta, Kalaman sa ne kawai ke mata yawo a kwakwalwa ,haka nan ta tsinci jin zafi a zuciyarta ta dalilin hawayen sa da ta gani, "Tafi minti goma zaune a motan Kafun ta tashi tabi bayan sa , Tun kafin ta shiga take jin ihun Dr Jabir yana ƙarb'ar warb'a hannun sojojin. "Zaune ta tarar da Hindu gefe guda tana Mai juya wayarta ,gefe guda kuma KB ne shima zaune sai Paki dake chan gefen Wanda yayi editing Clip ɗin wanda yasha Ɗan banzan duka ,daga gani sai da yasha luguɗen tsiya Kafun ya faɗi sunan Dr Jabir. "Kallan matashin yaran tayi tace "nawa suka biyaka?" Bakin sa kamar ansa goruba saboda kumburi kafin yayi mata alamu da hannu. "Ƙaramun tsaki KB yayi yace 500k fa,just 500k Ɗan kawai Ya b'ata sunan wasu ba tare da yasan Mai zai biyo baya ba,"Guy you messed with the wrong people. "Zama tayi akan kujerar dake facing Paki wanda koda wasa yaƙi bari su haɗa ido," Kallanta ta mayar kan Dr Jabir tace "ku tsaya da dukansa haka", "Matsawa tayi daf dashi tace "you're a very good doctor ,ina tuna lokacin farko da na fara aiki da kai,it was amazing saboda yarda mukayi aiki hand in hand," "I have been dreaming naga na samu likita da yasan abunda yake a kusa dani,"I wanted to work with you again and again saboda kasan Mai kake. "Ban sani ba ,a lokacin da kazo kace kana sona da wane motive kazo but i told you i wasn't interested da mutunci nayi rejecting offer ɗin ka idan zan tuna ,amma ka dauke sa something else,ban san mane Ya maida soyayyar da kace kana mun ba ta koma kiyyayya ," "Ko 'dan tun farko wani abu ne dama ka shirya?" "I wasn't understanding sudden diss ɗin ka akaina , "Bani da wani riƙo da nake dashi akan ka, I don't hate you, Nasan kilan you're just jealous of me And kana tunanin connection Ya kawoni nan,but i told you ranar a office ɗin Director ,ina matsayin da nake, da gumina,da hawayena ,da jinina . Da kasan gwagwarmayar da nasha Kafun nazo nan Bazaka ma fara tunanin kaini ƙasa ba. "But you decided to,ba tare da kayi tunani sau biyu ba kwakwalwarka ta baka wani banzan shawara na ɗora edited clip ɗin nan da Intern ɗina ." "Kasan kuwa abunda ka aikata?" Kasan girmansa kuwa ? Ƙaramun murmushi tayi tace "trust me anan gurin zan nuna maka ƙarfin izzar kuɗi ,'dan bayan sun gama chasa mun kai,za'a kaimin kai Asibitin kaje gaban board members ɗin da kasa suke nuna mun dan yatsa ka wanke ni". "Ɗagowa tayi ta kalli Paki wanda yayi saurin ɗauke idanun sa akan ta tace "shima ka wanke sa,then i will Call the press ka tabbata ka b'ude kazamin bakin ka kai da wanchan abun then i will decide your fate ɗan ban shirya yafe maka ba nan kusa. "Tashi tayi tace ina waje ku chasa munshi kamar yarda ake chasa shinkafa amma ku tabbatar baku taba bakin sa ba dan dashi nake san yayi magana,". Wayar tace ta hau ruri,Director ne ke kiran ta,tana ƙokarin ɗauka ta tsinci muryar Dr Jabir yana faɗin"bani na kawo idea ɗin ba wallahi". "Juyowa tayi tana Mai ƴar ƙaramar dariya tace"kana nufin kace mun ba kai da wancan abun bane kawai a cikin wannan haɗakar?" "Takowa tayi tace"its getting more interesting ,faɗa mun wanne shegen ɗan iska ne ɗayan, Wayartace ta sake ƙara, Daga masa hannu tayi tace "ɗan tsaya". "Dagawa tayi tasa a handsfree tace "director ina ji,barka da rana ,ina fatan ƙalau. "Cikin sassauta murya yace"Dr bulama ina kika kai Dr Jabir?" Don't do anything illegal with him,kar ki saka kanki ciki matsala,you will answer to the board. "Gyara zama tayi kamar yana kallanta tace"mr Director sir,ina fatan wanda Ya faɗa maka bai faɗa maka da hukuma nazo ba,Hukuma suka tafi da Jabir dikko har iri biyu," "Akwai Dodanni da malaikun duniya a ciki,sannan ni zakanyyar da zan cinye duk wanda yayi ƙokarin Wasa da jelata,". "Bana tsoran kowa a board ,i told you zan miƙa resignation letter na,kar ka manta sunana UMAIMAH USMAN BULAMA, diya guda ɗaya tilo a gurin attajirin Mai kuɗi nan,USMAN BULAMA"Idan kaga na tab'o nice naso na tab'u,nasan zakace nayi taƙama ko? "Ƙaramar dariya tayi tace wani lokacin sai da haka" Na faɗa maka zan kawo maka wanda yayi editing wannan clip ,sannan Next time dear Mr Director kar ka fara yanka huƙunci ba tare da ka san gaskiyar abin ba, "Gaskiyar kuma gata nan gaba na,muna nan tare da Dr Jabir muna wasan chess and two men down, Ina fatan ka iya chess kuma kasan me ake kira da two men down, So na zubar da biyu guda ɗayane nake ƙokarin saurare ka Katseni ta hanyar kira. "Kallan Dr Jabir tayi tace "maza gaisa da Dr mr director sir sai ka sanar damu wannan Strong opponent ɗin mu sai mu shirya Cos nasan kilan black horse ne ". "Cikin sheƙewar muryar Dr Jabir yace Hello sir" Murmushi ta kumayi tace Dr Director kaji Nephew ɗinka ko? Na'am? Yafaɗa ta ɗaya bangaren wayan. Ƙaramar dariya tayi tace "aw Sorry na manta ashe ba baka san nasan Nephew ɗinka bane ba Dr Jabir," Well a ranar da ka nema masa yafiya a gurina ranar nasan wanene shi a gurin ka, Ina fatan ba kaine Black horse ɗin mu ba,? "Well muna sauraranka Dr Jabir ,sweet uncle ɗinka ne Ya saka ka ko kuma wani mastermind ɗin ne da yafi kawun ka zarra da yayi tsautsayin taka ɗiyar BULAMA?" Duƙan desk ɗin dake tsakiya tayi cikin wani irin tsananin fushi dan taje maƙura. "Jin yayi shiru ne yasata nuna sojan da yafi ko wannen su girma da murɗewa tace" Mr hot soldier, daga gani a training ɗin da ka samu kana haɗawa da Gym ba,Cos you look build i must say. "Murmushi soldier ɗin yayi yace 'i work out twice a day". "Tsaki paki yayi yace "And who asked you sau nawa kake working out ?" Ba wannan Ya kawo ka nan ba. "Ƙasa yayi da kansa cikin girmama Yace Sorry young master . " "Dan karamun murmushi Hindu tayi lokacin da ta hango kishi karara a idanun Imam paki," "DR Bulama don't do anything you'll regret, "Muryan director ta wayar Ya karade store room ɗin, Murmushi tayi tace "naso na manta kana speaker fa,"Well idan Nephew ɗinka Ya buɗe baki yayi magana bazai samu ƙarin duka ba akan wanda yasha ,Amma idan Ya zab'i yayi shiru ni kaina Ban san Mai sojojin nan da suka gino ba zasuyi masa , And bana tunanin akwai abunda zan dana sani,amma jabir kuwa yana kan yi. Daga ɗayan bangaren Director yace "Jabir kayi magana mana wenene yasa ka" . Fashewa da kuka yayi yace"na yarda ina mutukar kishin yarda Allah yayiwa Dr bulama ƙokari da sanin kan Aiki,idanuna sun rufe har na kasa gane menene dai dai." "Idan ina ganinta ji nake kamar na hadiye zuciya na mutu ,i Am a second best a asibitin nan and i cant lose to a woman,i wanted to be the first best amma Dr bulama ta shiga mun gaba ta tsole mun ido, " "Da gaske lokacin da na nemi yafiyarta i mean it amma kwatsam tsohon mijinta HABIB ya kawo mun offer ɗin kaita ƙasa And da haka ma Ya bani 3million sabida da fari naƙi amince wa ". Dukkan wannan idea ɗin sa ne and tun ranar yabar Nigeria ,ji tayi baki ɗaya jikinta Ya hau karkarwar bacin rai Cos bata taba sanin Habib zai mata abu har haka ba,Cos a tunanin ta ita uwar dansa ce ko dan ɗansu baya Kai wannan limit ɗinba. "Cin Kwalarsa Paki da Ya tako gurin jin Ya ambaci Habib yayi yace"idan kayi ƙarya ka yarda dani zan cire girmanka na babbalaka na bawa kare kai. "Cike da tsoro yace "wallahi tallahi ba ƙarya neke masa ba Ai akwai transaction ɗinsa da wayan da mukai." Yanzu yana ina"paki ya tambaya," Kafaɗa mana Jabir"director Ya faɗa". Yana itally , Ya faɗa yana Mai fashewa da kuka. Cikin wata irin sassanyar muryar broken heart tace "ko birnin sin yaje sai na kamasa na saka an hukuntasa ". Mikewa tayi ta fita a store room ɗin tana Mai ignoring kiranta da suke. Da gudu paki ya bita da gudu, Da ƙar ya kamo hannunta , Chak ta tsaya , A hankali ta juyo idanunta ciki da hawaye tana Kallan idanun paki wanda Ya Marairaice mata da ido yace ,you cant drive a wannan yanayin sanann ina zaki. Itally, Ta bashi amsa tana Mai ƙokarin shanye kukanta Kafun tace "let go of me". Saurin sakar mata hannu yayi kamar shocking Ya kamasa, Tana ganin haka ta ruga motanta. Ko takan Hindu dake ihun ta tsaya batayi ba tayi wani mugun reverse ta fita. * Mun tai itally kamo habibu🥵🥵 Chuchujay ✍🏽 TBC. [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK AURE UKU (a hospital romance) By Chuchujay ✍🏽 Ga masu san a tallata musu hajarsu 09058191213. Episode 1⃣4⃣ A yarda umaimah ta figi motarta Allah ne kawai Ya kaita gida, A lokacin da ta tafi rasa abunyi paki yayi amma yana bukatar wanda zai hana umaimah zuwa italy, Kallan Hindu yayi yace"babu wanda zaki kira ki faɗa masa cos she cant go to italy, zan ji da komai ." "Ƙaramun murmushi tayi tace "do you love her that much"? "Shafa kansa yayi yace "with My life". "Murmushi tayi tace"tana da soft heart and im sure a zuciyarta kana da wani soft guri kawai ka bata maganin attitudes ɗinta " Ka fahimceni? Murmushi yayi yace "zai gwada ." Wayanta ta ciro ya kira Yaya Abubakar dan kaf gidan shine take da numbern sa shima ɗan umaimah ta tab'a ƙiran sa a wayanta ne. Ringing ɗaya Ya ɗauka, Bata b'ata lokaci ba wajen sanar masa abunda Ya faru tiryan tiryan, Godia yayi mata yace yanzu zai kira daddy sannan Umaimah baza taje italy' ba. "Tana gama wayan Paki yace "bari na bita, Yana ƙorakin shiga motar sa tayi folding hannun ta tace "dan saurayi idan ka tafi ni wanene xai maidani gida?" Sosa kai yayi yace "im Sorry dan Allah,"KB Zan barka nan ina nan dawowa. Shi da Hindu suka nufi gidan su umaimah . A bakin gate ɗin tamfatsetsan gidan Paki yayi parking motar sa , Kallan sa hindu tayi tace bari na maka iso a maimakon Umaimah i know she wont mind. A tare suka shiga ,kai tsaye part ɗin umaimah suka nufa ,dama ita ba gwanar kula maƙiyan umaimah bace a gidan , Sannan bata damu da shiga ta main gidan ba ,kofar da zata sadata da sashenta kawai take nufa. Tsayawa Paki yayi a bakin kofa, Juyowa tayi ta kallesa tace "yadai?" Dan Sosa kai yayi yace "i think ba dai dai bane na shigar mata guri kai tsaye bata san da zuwa na ba". "Karamun murmushi Hindu tayi tace "kar ka damu You're not going to find her naked i promise". Ƙasa yayi da kan sa cikin jin kunya, Gaba tayi yana biye da ita a baya, A cikin wani tamfatsetsan falo suka tsaya, Babu alamun ta dan haka hindu tace 'bari na ƙarasa inda idan kaje you might actually find her naked dan nasan yanzu haka tana chan tana shirin tafiya italy' cikin rashin sanin masu hanata na hanya. Zama yayi yana Mai Jin nauyin maganar Hindu wadda ya kula ita ko a jikin ta, Yana wannan zaman Nameer Ya shigo duba da shi yanzu ba zuwa makaranta yake ba ,yana shirin wucewa Abuja. "Turus Nameer yayi lokacin da yaga Paki," Da murmushi Paki Ya kalle sa yace"Big boy ." "Haɗe Nameer yayi yace"im not a boy,i Am a man Cos a sashen mu nine babba kuma protector ɗin mami , "Mai kake yi anan. Faɗaɗa murmushi Paki yayi cos fushin Nameer a gurin umaimah Ya kwaso shi, Yana Mai kokarin magana muryar umaimah ta katsesa a yayin da take fitowa daga sashen da Hindu tayi hannunta dauke da jaka tana faɗin"Hindu kima daina koƙarin tsayar dani 'fa,wallahi Habib sai Ya kwashe kashin sa a hannu tunda dai shi bai gaji mutunci ba,"Wallahi sai yaga kalar wulakanci na da bai tab'a gani ba. 'Mami Habib? Mai yayi miki, Mai Habib ɗin yayi miki. Muryar Nameer ta ziyarce ta cikin wani irin fushi ba kamar na yaro ba. "Turus tayi Kafun ta tako gareshi tace"Nameer yaushe kuka dawo kai da daddy"? "Yanzun nan ya bata amsa Kafun Ya sake cewa "mami Mai Habib yayi miki". Durƙusawa tayi dai dai tsayin sa tace "Nameer na faɗa maka ba sau ɗaya ba ka daina kiran sa Habib He's your father for God sake. " Ture hannunta da ta dafa kafaɗarsa yayi yace"mami he's not My father ,na faɗa miki ba sau ɗaya ba shi ba daddy na bane ,i might be using his name amma mami we are not related." "He lost that right mami a long time ago, ki faɗa mun abunda BASTARD ɗin nan yayi miki and i swear i will kill him. "Babu wanda yayi tsammanin Abinda Ya biyo baya,sosai umaimah ta ɗauke Nameer da mari Mai zafi idanunta cike da kwalla tace "who taught you that"? "Uban wanene Ya koya maka wannan?"You're calling your father a bastard har kana cewa zaka kashe shi. "Ni na koya maka wannan?" Tana kokarin sake marin sa hindu tayi saurin shiga tana cewa 'a'a Bulama. Sai a lokacinne ta kula da paki wanda ya janye Nameer daga gurin. "Sake nuna Nameer tayi da yatsa tace "i raised you to be better than that,"ko mene ke tsakani na da mahaifinka tsakanina da shi ne amma baka da right ɗin zagin sa har kana ikirarin zaka kashe sa. Kwace wa yayi daga hannun Paki Ya nufi hanyar da zata sadasa da inda ɗakinsa yake Kafun yace "amma mami ina da right ɗin tsanar sa and you can not do anything about that, i hate him and idan na girma na tsincin Ya miki abunda ban sani ba yanzu i will kill him,saboda you're My World . Da gudu ya shige, Zaman ɗirshen tayi a kasa tana Mai cewa "shekarun sa sha ɗaya kawai fa,"He's just 11,and ina Kallan tsanar mahaifin sa akan idanun sa,why me? Mai yasa kaddarata zata zo da haka? Yaro ƙarami amma a cikin kwayar idanun sa akwai kiyayya. "Habib shine wanda ya fara ja mun komai saboda duk da ba dan 'ina san shi na aure sa ba Atleast da yana da decent life i will get to adjust,amma yayi ruining komai ,sannan bai tsaya anan ba After 11 years yake san b'ata mun rayuwa". "Mene laifina Hindu?" What's My fault? "Yarda nameer yake yanzu Ya kike tunanin zai kasance idan nan gaba yaji labarin abun da yake faruwa a yanzu?" Nasan da ace daddy bai jama ƴan gidan nan kunne ba akan abunda suke yi ba da za'a samu mai faɗawa Nameer abun da yake faruwa , Sai kuma maine zai faru? Kuka sosai ta fashe dashi. Kukan da take haka paki yake jinsa har cikin ransa , Idanunsa ne suka fara kawo ruwa dan akan umaimah da damuwarta ya manta da Mai ake kira Dakiya da jarumta, Zuciyarsa ce ta ƙara karyewa da Ya fahimci a gidan mahaifinta ma ita da yaranta bawai zamane ake dasu na soyayya ba. Juyawa yayi ya fita dan idan Ya cigaba da tsayuwa bai san maine zai faru ba. Rungume ta Hindu tayi bayan fitar paki tana Mai lallashin ta, Zumbur Ta miƙe tace"sai naje italy' na kamo habib nasa an wulaƙanta mun shi a kasar nan,". "Baza kije italy' ba." Ɗaga kai tayi 'dan ganin Mai maganar, Da gudunta ta ruga gareshi ta faɗa jikinsa tana Mai faɗin"Daddy".cikin kuka, Shafa ƙanta yayi a hankali kana ya raba ta da jikin sa ya kamo hannunta Ya zaunar da ita kan kujera Ya zauna a ƙasa hannunsa cikin nata . shi kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa idan yana ganin umaimah ciki hali irin wannan. gefen ta yaya Abubakar yazo Ya zauna shima yana jin dama zai iya ɗauke mata kuncin dake damunta Ya maida kansa. Daddy ne yace "umaimahn daddy,"Ni kaɗai nasan abunda nake ji idan ina ganin hawayenki,jikina yana bani Nana surbajo bata farin ciki dani a duk inda take saboda i failed her, "Nine na ja miki komai sabida ni na haɗa Aurenki da Habib a karo na farko sannan na haɗa a Karo na biyu," Ki yafe mun umaimah ,soyayyarki ce ta rufe mun ido nayi tunanin gata ne na miki. Saurin goge hawayenta tayi tace"daddy mana,ni baka mun komai ba ,hasalima dalilin Auren na samu ƴaƴanda wasu ma da kuɗi suke nema amma sun rasa,"Ni'ima ce Allah yayi mun a lullube kuma ina gode masa a kullum daddy, "Idan ka cigaba da ɗorawa kanka laifi ni Bazan iya yafe wa kaina ba,"Ƙaddara tace da babu wayau ko dabarar da za'isa na tsallake , Mene kuma abun daɗin daddy? Ina da rayuwa kuma ina da lafiya shine yafi komai . Murmushi yayi ɗan yana san yaga da kanta ta lallashi kanta wanda a Yanzu tayi sannan Ya gamsu da ƴar ɗiyar sa Ta girma . Goge mata ƴar karamar kwallarta yayi yace "nan da awanni 48 za'a kawo mun Habib har gida ba sai Kin wahalar da kanki binshi italy' ba," Ba italy' ba ko ina ya buya a cikin duniyar nan ina da yarda zanyi a ɗukafar dashi gabanki sannan ban shirya sassauta masa ba ,tunda bayan shekara goma sha ɗaya bai ƙasa a gwiwa ba yazo dan bata miki, Nikuma na shirya yaƙi da duk wani Mai saki kuka yarinyar daddy. "Murmushi maganar da yayi ta karshe tayi ," Daddy ya kamata ka gane yarinyar nan ta girma fa yaranta uku fa amma Bazaka ɗaina shagwab'a taba . Yaya Abubakar Ya fada. Murmushi daddy yayi yace "ai ko duniya umaimah ta tara tana nan a yarinyar daddy." A haka suka gama lallashinta Kafun suka tafi, Bayan Ya rage daga ita dai Hindu a ɗakin ne ta kalleta tana tunanin ta inda zata fara tambayarta ina Paki, Ɗan shiru tayi Kafun tace "ke dawa kika dawo"im sorry na barki ke ɗaya." Ƙaramun murmushi Hindu tayi tace"kawai kice mun ina Imam paki,"To Inajin Ya wuce. "Ya wuce kuma?" Kallanta hindu tayi tana mai san gintse dariyarta tace "kina da matsala da hakan ne? Ɗan haɗe rai tayi tace "ina tambayane kawai ɗan Ya shigo har falo ba ba tare da izini na ba." Dariya Hindu tasa aranta tace "munafuka kina so kina yanga". ********* Kwance take kan Gadonta da dare tana Mai tariyo abubuwan da suka faru a yau, Tunanin Paki Shine abinda yafi damun kwakwalwarta dan duk yadda taso ta cire sa ta kasa. "Yau yazo sannan yaga wani bangare nata da ba kowa Ya sani ba, A lokacin tsintar kanta tayi da kasa yin shiru na abinda yake damunta 'dan Nameer Ya riga da Ya gama tabo mata damuwarta, Tsakanin ta da habib kiyayya ce amma bazata taba bari tsakanin sa da Nameer Ya zama kiyayya ba duk girman lefin da zai mata. Gyarawa Abdallah kwanciyarsa tayi daga kan cikinta dan yanzu baya yarda yayi bacci idai ba a gurinta ba a gurinta ɗin ma a jikinta, Murmushi tayi tana Mai kissing goshinta a zuciyarta tana Mai faɗin"ko me kaikuma Zan faɗa maka akan naka mahaifin idan ka girma?" Ta dai san baza ta tab'a faɗawa Abdallah mahaifinsa ɗan blood money bane komai rintsi,sannan Zatayi duk yarda Zatayi taga abun bai bibiyesa ba Tayi Wannan alwashin. Addua tayi masa tayiwa kanta , Tana rufe idanunta paki Ya cigaba da dawo mata, Jin tunaninsa zai addabeta yasata jawo wayanta ta shiga numbernsa da tayi saving da INTERN I'P . "Murmushi tayi a yayin da zuciyarta ke ingizata akan ta kirasa," Har ta danna zata ƙirasa Tayi saurin fita kamar an tsikare ta. "Karshe ta tsinci kanta da tura masa message "thank you for everything'." Tafi karfin minti nawa tana duba wayarta taga ko ya maida mata amma shiru,a haka har bacci b'arawo Ya kamata. Bangaren Paki kuwa. Yana fita a sashen umaimah ya fita a gidan baki ɗaya,motar sa Yashiga ,kai tsaye gida Ya nufa yana Mai jin zuciyarsa na Tafasa, "Yana ƙokarin haurawa sama yaji muryar nana na faɗin"an dawo daga kokerar ne?" Shine kake fama sanɗa kamar b'arawo? Ba tare a Ya Kalleta ba yace "Alhamdulillah ba'a Sino's biggest super market aka kamani ba da hannuna maƙale a baya ina zazzare ido kamar an ƙaɗa bera a buta ba". Ki barni yar da kika ganni nana dan Allah. Har Ya haura saman yana jin banbaminta da bala'inta na yau da kullum. Kai tsaye ɗakin ummu Ya nufa, Yana knocking sau ɗaya ta bashi izinin Ya shigo, Zaune Ya tarar da ita tana duba wani file, Zama yayi kan stool Ya gaida ta,. "Amsashi tayi tana Kallansa kafin tace lafiya dai ko?" Naga ka dawo da wuri. Saukowa yayi daga kan stool ɗin Ya zo kusa da ita ya zauna yana Mai ɗora kansa a kafaɗarta Kafun yace"Ummu zuciyata zafi take mun". Cikin rikidewa tace "wanne irin zuciya kuma muna zaune kalau Imam?" Hawayen dake maƙale a idanun sa ta hango,cikin tashin Hankali tace"tashi muje asibiti imam ba abun Wasa bane wannan harda kuka?" "Ƙaramun murmushi yayi yace dama akwai likita da zai mun magani ummu,". Dafa sa tayi tace Imam kasan dai baka da wanda zaka faɗawa damuwarka sama dani ko? "Just tell me ni da kai zamu gyara komai ,"i promise,akan clip ɗin chan ne,hope baka da hannu ciki? "Dan ajiyar zuciya yayi yace an kama waɗanda suka dora ma". Ajiyar zuciya tayi tace Alhamdulillah "Wallahi yarinyar jiki na raina ,na ji tausayinta Sosai". Tsintar kansa yayi da murmushi dan yasan mahaifiyarsa ce zata fara ƙarb'ar umaimah. Haka nan Ya barta ba tare da Ya faɗa mata komai ba yana Mai jiran lokaci. Yana tsaka da tunaninta da halin da Ya barota yaga saƙonta, Kamar an sashi a aljanna musamman da Ya tabbatar tayi saving layinsa kennan. "Har zai replying huɗubar Hindu ta dawo masa, " Haka Ya dane zuciyarsa ba tare da Ya mayar mata saƙon ba duk yada yaso kuwa. Chuchujay ✍🏽 T B C. [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqKDgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK AURE UKU (a hospital romance) By Chuchujay ✍🏽 Episode 1⃣5⃣➡1⃣6⃣ BAYAN SATI BIYU. "Mami ina ta cewa kiyi haƙuri amma mami kina ta ignoring ɗina gashi zan tafi". "Banza ta masa a karo na ba iyaka Kafun tace"zo nan Nameer," Babu musu Ya ƙarasa gare ta Ya zauna a gefen ta fuskar sa gwanin ban tausayi, "Kallan sa tayi na ɗan wani lokaci tana Mai jin soyayyar sa da tausayin sa kafin ta jawo sa jikinta ta rungume sa tsam," "Raba jikin ta tayi da nasa tace"Nameer ina san ka sosai nasan ka san wannan,and yanzu Abuja da zaka wuce ,kasa ma ranka karatu kaje ," Study hard Nameer ,i want to be proud of you ,kar kasawa

Chapter 6 of 15