Share this page
tayi tana Mai jin haushin yarda Dr Jabir ke mata katsalandan a aiki, Shiru nurse ɗin yayi bai ce komai ba 'dan yana tsoran fadar abunda zai bata mata rai Cos she's short temper wani lokaci musamman gareshi wanda tunda tazo suke aiki tare,amma sau da dama shi zai fadi alkhairinta saboda tana masa, Katse masa tunani tayi ta hanyar cewa"so ka tura mun detail ɗin patient ɗin,"? Kaɗa kai yayi Kafun yace "yes doctor" Jawo laptop ɗinta tayi tana faɗin "and I'm hungry jezzz!" Juyawa yayi yana faɗin bari naje na kawo miki breakfast, Saurin tafa hannu tayi alamun ya tsaya Kafun tayi saurin tashi tana cewa wait this is serious we Are going in for surgery now, Yanzunnan akai ta OR yanzun nan and i need the team available ASAP. Da sauri Nurse ɗin Ya fita ganin yarda ta fadin maganar ba Wasa. Koda taje operation Room already team ɗin na nan,hannunta da tayi sanitizing ta miƙa aka samata Hand Gloves Guda biyu,kana ta juya aka sa mata rigan operation then aka ɗaura mata face mask. Bayan gama operation ɗin cikin sa'a tana fitowa bayan tayi disposing Hand gloves ɗinta da face mask,ta juya zata tafi taji tayi gware da mutum papers ɗin hannunsa sun zube , Sorry kawai tace ta wuce ba tare da ta bawa wanda tayi gwaren da ba last kallo. CHUCHUJAY ✍🏽 [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU (a hospital romance) By CHUCHUJAY. EPISODE 3⃣ Kallo ya bita da shi a lokacin da ta rab'a ta gefansa ta wuce baƙinta da Kalmar Sorry wanda bayan nan Kallan Arziƙi daya bai ishe ta ba, Tab'asa yaji anyi, Dago wa yayi Ya kalli wanda Ya dafa shi ɗin Kafun yace "guy how far". Murmushi guy ɗin yayi yace wa kake kallone Haka PAKI? Yana mai tambayar nashi yana Kallan direction ɗin da yake kallo. Dafe ƙirji PAKI yayi yace "Rayuwata nake kallo Kb,haƙarkarina da Ya bata na tsinta yanzun nan". Dariya KB yasa sosai kafun yace "baka da lapia gaskiya ,ka bari sameera taji labari kaga wata kana faɗin kaga missing ribs ɗinka". Tafiya PAKI Ya fara KB na biye dashi kafin yace"tun da nake da Kai tsakanin ka da Allah ka taba ji nace maka ina san sammy?" Ita kaɗai take haukan ta wanda Ya kamata iyanzu kuma ku sani, She's not My type of girl,i mean guy she's just not the one. Kasan irin taste ɗin PAKI da na daɗe ina zayyana maka to yau na ganta cikin asibitin nan and insha Allahu sai ta zama ta IMAM MUKTAR PAKI. Bai tsaya jin Abunda KB zai ce ba yayi gaba inda kb ɗin Ya bisa a bayan yana faɗin,guy hold on ana kiran mu 'fa Cos za'ayi attaching ɗin mu da snr doctors. "To kawai yace masa suka nufi inda sauran young doctors ɗin suke". Zazzaune suke cikin maɗaiɗaicin hall ɗin dake asibintin a yayin da Ko wannesu ke sanye da Farar lab coat, Shigowarta ba karamun sa IMAM PAKI yayi ba cikin wani yanayi na shauki, Bai taba jin irin Haka akan Ko wacce ƴa mace ba,zungurar sa KB yayi yace abokina kar kace mun itace, Cikin wani irin yanayin farin ciki yace"Ya kagani ta haɗu Ko?" Ƴar karamar dariya KB yayi yace baka da lapia,bafa cikin mu take ba mutumina likitace Mai zaman kanta,sannan ka Kalleta da kyau PAKI she's off limit,a fuska ma idan ka Kalleta kasan no nonsense ce,Kai kilan ma wallahi matar Aure ce. Ba tare da Paki Ya ɗauke idanun sa akanta ba yace"KB jikina Ya bani ba matar Aure bace 'dan bazan taba jin yarda nake ji yanzu Haka akan matar Aure ba and da kake maganar she's off limit just look At me ,young and handsome ,sannan idan ita senior doctor ce nima Ai kasan jan Kai ne tunda bana wasa da abunda Ya shafi Aiki ,beside saboda dedication ɗina first class holder ne wanda ba sai na faɗa maka ba,not to brag amma kai ma kasan idan magana ake ta ƴaƴan banki daga su nake,amma mutumina ba ta wannan ake ba batu ake na soyayyar ta da ta caccakar mun zuciya ,"Kai dai kawai idan mun gama abunda zamuyi anan muyi bincike akan ta 'dan Ko sunanta ban sani ba, Ƙasa KB yayi da murya ganin Babban surgeon na asibitin Ya fara magana,yace"tana cikin hand book ni kam kamar naga hoton ta , And ".. Jan hannun sa Paki yayi yace "Kai yi shiru zata fara magana". "Sunana Dr Umaimah Bulama ,surgeon ce da zaku yi aiki da,and ba sai na faɗa ba ,nasan dukkan wanda yake zaune anan yasan Abunda Ya kawo sa ,ba wai har kace ta Wasa ba saboda we are not some Artist or any sort of entertainers, we are here to save life da taimakon Allah wanda I'm sure shine aim na duk wanda ke zaune anan gurin ,idan kuma kana da wani otherwise aim to i will tell you that nan gun ba gurinka bane, So ba wasa just do abunda Ya kawoka, If im right zaku ɗauki year a nan right?" Yes ma!wani matashin saurayi Ya faɗa daga gefen su Imam, Cigaba tayi da magana inda take cewa well,Ina muku fatan nasara a rayuwa And ina fatan zaku amafana da abunda zaku samu wanda za kuce gwanda da kukazo CITY HOSPITAL. Bayan ta kai karshen maganarta gurin Ya ɗauki tafi ,a yayin da umaimah ta shiga kalbin young interns ɗin , Babu abunda Imam yake baya ga kallon ta yana Mai jin ta sake burge sa dan hatta muryarta wani abu take masa a kunne. "Na shiga uku "Ya furta a hankali yarda KB kaɗai Ya jisa,shima ɗin maganar zuci ce ta fito fili, Dariya karama KB yayi yace "Ai tukunna ma Alaji baka fara shiga uku ba." Bai kula sa ba illa tasbihi da yake Ga ubangijin da Ya halliccesa Ya kuma halicci umaimah. Bayan an gama ƙarbarsu aka rabasu ƙarkashin likitocin ,a Haka kaddara ta taka gudunmawarta wajen jefa Paki da KB karkashin Umaimah, Sai wata yarinya Aisha shareef wadda ba ma makarantar su ɗaya da su Paki ba . Fita tayi dan tana da VIP patients' da zata gani bayan ta wakilta Nurse farouk kan yayi addressing interns ɗin dake karkashin ta Kafun tazo and su tabbatar sun tsaya tazo. Kallan KB imam yayi yace "kaji yin Allah ko?"Kai ni tunda na ganta nasan akwai wani boyayyen al'amarin da zai faru tsakanina da ita, Gyara zama KB yayi yace wait paki mubar maganar wasa wai dagaske kake maganar kana santa? Kalli 'fa ba tsararka bace,kar ka jama kan ka damuwa, Dafa kafaɗar KB yayi yace "kwantar da hankalinka ,zaka maimaita maganar nan lokacin da kaga na sata a ɗakina ,kar ka manta Paki ne 'fa,wanda Ko wacce mace ta mutarwa a campus " Suna wannan surutan Aisha shareef tazo yarinyar da aka sasu tare karkashin Umaimah, Da fara'arta tazo garesu ,zama tayi kujerar dake kallansu tace"sunana Aisha Shareef,And zamuna aiki tare ne, Washe mata haƙora KB yayi amma ita hankalinta yana kan Imam Paki wanda Ko inda take bai kalla ba dan yasan karshen maganar tace tana san shi. " Miƙamata hannu KB yayi yace sunana"KABIR ASHIR abokina nan kuma IMAM PAKI,hope we will get along."Babu musu ta kama hannun KB tana Mai faɗan sunnan Paki a zuciyarta dan sunan Ya dace dashi sosai. Bayan ta saki hannun KB ta juya ga Paki wanda hankalin sa ke kan waya ,hannunta ta miƙa masa domin handshake, Kallan hannun yayi sheƙeƙe kafin yace"last da na tuna ni dake ba muharramai bane sannan addinin musulunci bai yarda macen da ba maharramaka ba wani abu nata Ya ta b'a ka ,ban san wanne addini KB Ya shiga ba a yanzu da Ya kwakumi hannunki cikin nasa ,amma ni har yanzu ban fita ba ,bayan addini kuma I'm Allergic to handshakes cos it disgust me," Ganin yarda tayi da fuskarta gwanin ban tausayi sannan ta janye hannunta cikin sanyin gwiwa yasa Imam Paki cewa"hope zamuyi aiki Mai kyau tare". Washe masa hakoranta tayi jin abunda yace ,cikin farin cikin tace insha Allahu,. Bai sake ce mata komai ba Ya cigaba da danna wayansa inda yake jin suna hira su biyun kamar sun daɗe da sanin juna, Tunda Ya duƙufa kan wayansa #tag DR Umaimah Bulama yake sawa yana san ganin duk wani post da Ya shafe ,da Haka ya samo profile ɗinta wanda ba komai sai abun da Ya danganci Aiki, Har zai fita Ya ƙara komawa hashtag sunanta ,wani hoton ta ya gani a baƙin harvard university tayi murmushin daya bayyana well cleaned arranged white teeths ɗinta, Gefe guda kuma wata kyakyawar mace ce da bazata wuce sa'arta ba ta dora hannunta kan kafaɗarta itama tana Mai mayar da murmushin, Kana kallansu kasan suna cikin farin cikin irin na freshers da suka samu favorite course ɗinsu da suke ta mafarki, Sunan Mai Account d'in da ta dora ɗin Ya shiga #HinduSD# Scrolling Ya fara ,idanunsa ne suka sauka kan wani hoton Umaimah da yayi mutuƙar tafiya da imanin sa ,dimples ɗinta Ya lotsa sosai gwanin sha'awa , Hoton matric ne ,anyi tagging ɗinta ana wishing ɗinta happy birthday , Caption ɗin Ya duba yana san gani Ko ansa shekarunta, #happy 25 baby,out of sight is never out of mind ,hindu forever Love you. Irga shekarar da akayi posting ɗin yayi da yanzu yaga shekara Ashirin da Tara! Duba Month ɗin da akayi posting ɗin yayi yaga birthday date ɗin 9th march. Dan leƙowa cikin wayar KB yayi yana san ganin me yakeyi bayan tashin Aisha ,karaf idanun sa suka nuna masa hoton Umaimah,dafa sa yayi yace guy Abeg Stop this. Tsaki Paki yayi yace "rabu dani dan Allah ,nifa wallahi a yau kawai na kamu da san ta and guess what nigga"I'm 1 month older,wata ɗaya kawai na bata kuma bashi zai hanani cigaba da santa ba ," Ƙara dafasa KB yayi yace "Paki shekara ishirin da Tara 'fa ,taya kake tunanin bata da Aure ka rufa mana asiri,". Tsaki yayi ya miƙe yace "sai kuma kayi tayi ai". Sai wuraren shida na yamma umaimah ta nemesu,da rawar jiki Imam Ya ja KB sukaje cos duk yarda KB yaso su wuce sa haɗu gobe ƙi Paki yayi dan yana san sata cikin idanunsa . A office ɗinta suka sameta,alamu ta musu da hannu akan su zauna,ta ɗauki lokaci tana danne danne a system ɗinta yayin da Imam ya ƙura mata ido yana Kallanta, Bayan ta gama ta ture laptop ɗin ta kallesu tace"i guess mutum uku ne ya kuke ku biyu,And nace kujira ni". KB ne Ya amsa mata ta hanyar faɗin"eh ɗayar Aisha shareef ce abun gaggawa yasa ta tafiya gida amma ta sanar da Nurse Farouk." Kaɗa kai tayi tace "okay,"So I guess kun san ni cos nayi introducing kaina earlier so names? Kabir Ashir and Imam Muktar Paki. Kallan Kb wanda Ya bata amsan tayi kafun ta kalli Paki wanda yayi saurin ɗauke kansa tace" Wanene kurma a cikin ku? Cikin rashin fahimta Kb yace na'am? Dan karamun tsaki tayi tace "im sure mutum ɗaya bazai amfani da suna biyu ba," Cikin wata irin sassanyar murya Paki yace "im Sorry Dr"nine Imam muktar Paki" Kallansa tayi na wani lokaci kafun ta ɗauke idanunta tace "so welcome to My team,i have less to say,first idan kana team ɗina sai ka shirya cos bana san wasa ,aiki aiki,idan kuma na fahimci mutum ba aikin yazo yi ba i will talk to the management Akai shi wani gurin cos im not in for rubbish, we have operation tomorrow By 9,"Mara lapian nada blood clot a brain so za'ayi masa Aiki gobe and we are going to the OR together,you may leave. Har sun Kai bakin kofa tace "Paki" Juyowa yayi yayin da gabansa yayi wani mumunan faɗuwa, Nuna sa tayi da pen ɗinta tace"Ina fatan zaka rage kallo na and i just hope ba kallona kazo yi CITY HOSPITAL ba". Dariya sosai KB Ya ke sheƙa masa lokacin da suka isa motar paki, Dafa sa yayi yana kan dariyar yace "you fucked up Big time Paki,kaji haushi wallahi ,Bro control your self you don't even know this woman and daga gani Zatayi wulaƙanci she sounds Arrogant and wallahi Babu wuya Zatayi embarrassing naka,guy akwai mata da yawa Mai zakayi da tsohuwa she's 29 fa" Wani banzan kallo paki ya bashi yace"with the attitudes na sake jin ta tafi dani and yes she's 29 and wata ɗaya na bata amma bakaji nace maka Ya dameni ba, beside she doesn't look her age Kai nifa koda ta girme ba zai dameni ba abu ɗaya Nasani shine INA SANTA,and wallahi idan ka cigaba da faɗan aibunta sai dai kana tafiya gida kai kaɗai har ka gyara motar ka " Ɗaga hannu KB yayi yace "i rest My case". CHUCHUJAY ✍🏽 Follow me. Wattpad:@chuchujay Instagram:ameenatourh__ Facebook:https://www.facebook.com/groups/805959663295457/?ref=share Whatsapp group:https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK Telegram:https://t.me/chuchujaynovels Join My telegram channel ! 3 subscribers take me to 1000🥱 Arewabooks:https://arewabooks.com/book?id=653305e91c06f4783fc2ef84 To be continued. [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK AURE UKU (a hospital romance) By Chuchujay Episode 4⃣ BULAMA MANSION. 8:00pm Da blank tunani Umaimah taje gida,bayan tayi parking motarta ta nufi sashen da zai kaita bangaren Alhaji bulama, "An dawo daga karuwancin da ake fakewa da aiki kenan a bar mana ƴaƴa ratate a gida da sunan anje aiki alhalin yawan banzan ne kawai ake zuwa,ki daiyyi zuciya kiyi Aure ,Ko da yake Auren fa bai ƙarbeta ba" Muryar saleema matar yaya Aliyu autan hajiya zuwaira Ya daki kunnenta, Da hajiyan da sadiya matar Ya Abubakar da Atika matar usman sai raliya matar Umar sai saleemar mata Aliyu, Dukkansu suna zaune suna kallo a main palor wanda Hakan Ya tabbatar mata da yaran na tare da Daddynta, Tun Kafun ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin saleema tayi mata wannan raddin, Takowa tayi bakinta da sallama ta zauna kan stool dake gefe guda , "Hajiya Ina wuni,sannu da gida"umaimah ta faɗa ba tare da damuwa ba amma tasa ar ranta yau sai ta mayar wa da saleema raddin da ta mata, Ba tare da hajiya zuwaira ta ɗauke kanta daga Kallan da take ba tace lapia!. Likita bokan turai an dawo kennan, Sadiya ta faɗa wadda da ita kawai suke hirar Arziƙi sai wani lokacin raliya wadda bata cika sakewa da umaimah ɗin ba idan hajiya na nan, Amma Atika kuwa jirgi ɗaya Ya kwaso su da saleema, Murmushi umaimah tayi tace"wallahi yaya sadiya nasan su sultan ana chan ana damun Daddy,su Daddy Mai jikoki,"Gashi dai nawa uku,gurin yaya Abubakar Ga sultan ,sultana ga kuma Hameed ,gun yaya Usman ga ibi Ga rumaisah, Gun yaya umar ma ga sayyid ga na ciki ,gurin yaya Aliyu ne dai ba motsi Ko sai yayi ta biyu kilan juya Ya samo bamu sani ba,tunda har yanzu ta kasa aje yaran ratata. Ciƙe da balai saleema tace "uban wane Ya faɗa miki ana wa mutum gorin haihuwa,?"Hajiya kina jinta Ko ,gorin haihuwa 'fa take mun kuna jinta. Tashi tsaye umaimah tayi tace"inji uban da yace kiyi mun gorin zaman Aure". Bata jira jin mai hajiya take kokarin faɗa ba ta miƙe tayi ciki tana Mai faɗin gobe dan Allah idan kin ganni ki sake sakar bakin ki da bashi da gashi,nonsense. Koda ta haɗo kan yaranta ta kofar baya suka bi 'dan bama tasan abunda zai sake haɗa su, Zama tayi kan kujera Abdallah na kan cinyarta yana ta zuba mata surutun sa wanda galibi hirar Adda diya ne, kallan nadiya dake fama tutura baki tayi tace "lapia diya kike ta faman turo baki " Kuka tasa kamar tana jira tace"wallahi mami ni gidan Dada (kakar umaimah)zani na gaji da zaman gidan nan ,kullum cikin cin zalina hamma NAMEER yake yana kuma Kallan yarda hamma sultan ke ji da Adda sultana da hameed,amma ni ina yin abu zai buge ni ,kowa a gidan nan haka suke mun hamma sultan ne kawai bai mun Faɗa nidai mami nagaji,"Haka jiya hajiya ma cemun tayi wai ni da hamma NAMEER da Abdallah baban mu ba ɗaya ba kuma wai baban Abdallah barawone ɗan shan jini, Koma mami ba yau ta fara faɗa ba ni bana so . Wani iri umaimah taji a zuciyarta jin abunda nadiya ta faɗa ,dole zata ma tufkar hanci 'dan bazai taba iyuwa ba ace ana faɗawa yaran ta magana irin wannan. NAMEER ' Ta kwalawa nameer wanda Ya wuce ɗaki kira tayi dan yasan dama nadiya sai ta kai ƙararsa . Na'am mami' Ya faɗa yana Mai fitowa falan, Zama yayi yana faman zare ido, Kwantar da muryarta tayi cikin murya wadda uwa ke koƙarin jan ɗanta a jiki tace""Nameer Mai yasa kake dukan nadiya? Mai yasa ba kasan na zauna lapia When kaine babba amma kaine ka kasa jan kannen ka a jiki ,kana so kace mun idan Abdallah ya Kai duka shima zaka dake shi Ko? Haba nameer why Are doing this to your mother you're 11 years old for GOD sakes, Dawowa tayi kasan da yake zaune ta zauna ta jawo hannun sa tace "nameer ka ma mamin ka magana maine yake damuka?"Why Are you always this bitter. Kuka Ya fashe dashi yace "mami i dont like this house ,mami kamar yarda diya ta faɗa maki yan gidan nan basu da aiki sai faɗa mana mamin mu ta haife mu da baba daban sannan wai baki da time ɗinmu,and mami its frustrating da yasa nake venting anger na kan Nadiya, "Riƙe hannun umaimah yayi yace "mami 'dan Allah mubar gidan nan im sick of it" And wai mami ibi har a class yake faɗan wai mamin mu na da miji da yawa and the kid's are always tease me, wallahi mami saboda ke nake dagawa ibi kafa da tuni na daɗe da karya masa hannu,sai dai Uncle usman ya kasheni 'dan ranar ma 'dan ibi Ya tsokane ni na rama Ya buge ni. Wani irin zafi taji a ranta ,jawo sa jikin ta tayi ,kana tayiwa nadiya ma alamun tazo ,shafa kan nameer tayi tace "nameer what matters is na haife ku,"Menene 'dan baku sharing DAD ɗaya ku uku? Yes kai da Nadiya da Abdallah daddynku daban Cos kaddaran mamin ku shine Aure guda uku har ta sameku wanda rabon ku yasa ,sannan ina farin ciki sosai da Allah ya bani ku, Duka wannan doesn't matter ,abu ɗayane wanda zaku sa a ranku, maman ku ɗaya,ni maminku and Nothing is gonna Change that,sannan maganar bani da time dinku shima kunsan Ai ba gaske bane,i celebrate each of your birthday's tare and we had funs ,muna zuwa park tare wani ma maminsa na tare dasu amma basu samin wannan damar . I promise you guys babu mai sake teasing ɗinku a gidan nan,and duk wanda yayi muku a school just tell them that"you have a strong mom that love you." Abu ɗaya zaku mun shine ku tsaya ga junan ku like one big Family,im here ,nameer ,nadiya and Abdallah ,tafun hannunta ta buɗa tace team? A tare dukkanin su suka washe baki ,nameer ne Ya fara dora hannunsa kan na umaimah Kafun nadiya tasa then 3 years old Abdallah da shima yayi abunda sukayi yana dariya. Washe gari da kanta tayi dropping ɗinsu a school ba ta yarda sun bi school bus ɗin su na gida ba 'dan ta shirya,she's going to create havoc, Sanin suna da theater yasata shiga asibitin da wuri 'dan su shirya, Tana kokarin parking motarta taga baƙuwar mota a gurin, Da mamaki ta fito tana san taga uban da yayi parking motan sa gurin da take aje tata 'dan koma wane zai ƙarbi peace of mind ɗinta dan a zafinta tazo, Security ɗin dake gun ne Ya tako da saurinsa ganin bata paka motan nata ba,yana Mai girmamata yace"hajiya lapia dai ko" . Ƙaramun tsaki tayi tace"lapia ce zata sa ka ganni ban parking mota ta ba na shiga cikin asibiti bayan Ina da abunyi Mai amfani maimaƙon tsayawa maida zance da kai? Uban wanene Ya faka motarsa a inda nake aje tawa ? " Daga jin furucin ta yasan cewa tabbas akwai wanda Ya tab'a jar danjar ta ,'dan in dai dama kaji ta shigo tana faɗa to da damuwa ta shigo tana neman wanda zata saukewa 'dan haka ba tare da Ya damu da abunda tace ba yace"hajiya ga chan gefan kinga ba mota mai zai hana ki sa taki gun". Kamar tana jira tace"Kai bazan Aje ba,nace maka bazan aje ba Ko zaka mun dole ne?" Nurse faruk da ƙarasowarsa kenan ne Ya tako gun yana faɗin lapia? Kamar shima tana jiran sa tace ,lafia ne zaka ganni anan? Abeg aje a nemo mai motan nan yazo ya ɗauke gwangwanin sa i don't have time to waste, Kallan range rover ɗin da ta kira da gwangwani Nurse farouk yayi a ransa yace"lallai yau uwar ɗakin sa da fushi tazo". Cikin takun nan dake burge Yan mata Imam Paki ke Takowa inda umaimah suke,KB yaje ya bashi latest ɗin abunda umaimah keyi a waje, Tunda ya matso daf dasu yake wani irin murmushi Mai ƙayatarwa wanda umaimah tunda ta hangosa Take jin kamar tayi wiping wannan murmushin dake manne a fuskarsa , Motarsa ya shiga Kai tsaye Ya gyara parking a ɗayan gefan da akace tayi parking tata taƙi, Kamar tashin hankali Haka ta shigar da tata motar, Shi Ya fara fitowa Ya nufi motar tata ,tana koƙarin buɗe kofar yaje bakin kofar Ya tsaya , Ɗago Kai tayi ta kalle sa tace "Ina fatan kwakwalwarka bata samu matsala ba?"Ko wait ,kasha wani abune Kafun kazo nan? Ƙasa yayi da muryar sa yarda ita kaɗai zataji abunda yake cewa yace"eh nasha giya ce ta soyayya ,ita ke ɗawainiya dani" Murmushi yayi Mai kyau kana yace"a yin fushi ma Kin hadu DR babu wanda ya tab'a faɗa miki Haka? ". Ɗaure mata Kai abun yayi sosai dan bata san inda maganganun nasa suka dosa ba ,Zatayi magana cikin fushin da ta kwaso daga gida Ya ɗora hannunsa kan lips dinsa yace"shhh its not Good for your health and kar ki manta doctor jiya da kakkausar murya kika ce mana akwai aiki ,ban san dalilin da ya saka fushi a wannan fuskar taki Mai tsada ba ,amma inaso for now ki cire an jima sai a cigaba Ko Mai kikace ? Ya ƙarasa yana Mai ɗaga mata gira ". Saurin matsawa yayi a bakin kofar Ya kama hanya da sauri ganin abunda Ya gano na masifa idanun umaimah, Yanzu Ya shirya kuma bazai fasa bayyana mata soyayyarsa ba koda kuwa kullum zata na zaginsa ne. Tafi minti 30 tana zaune a inda ya barta , The guts kawai take Maimaitawa a zuciyar ta,lallai dole ta taka ma yaran nan birki cikin asibitin nan dan taga alama bashi da kunya. Dr Bulama saura 50 minutes a shiga surgery ɗinnan and you need to get ready ,ina fatan lapia dai Ko? Nurse farouk Ya faɗa 'dan gajiyar da yayi da tsayuwa. Wani irin kallo ta bashi Kafun ta fito a motan tana Mai cilla masa key dinta tace "kasan Mai zakayi". Ƙada kai yayi Ya ɗauko jakarta da wayanta yabita yana Mai tsinewa wanda Ya tab'o Dr bulama, Tana shiga cikin asibitin taji Dr Jabir yana faɗin"The mighty snr surgeon ina fatan Kin shirya faɗuwa a operation ɗin da zakiyi yau tunda naga tunda kika fara ba'a mutu ba amma Ina san ki sani wannan karan 2% chance of living patient ɗin keda ,idan zaki cire girman Kai ki bani aikin nan then na tabbatar miki it will be a success ". Juyowa tayi ciki takalminta mai tsini ta taka garesa ,ganin zata haɗe dashine yasa shi ja baya a yayin da ta bisa har sai da ya Kai maƙura,nuna masa dogon yatsanta tayi tace "da fari idan baka fita harka ta ba zan wulaƙantaka a asibitin nan,idan kuma kana ja dani ne Dr jabir mu zuba ni da kai. Kar kamanta nace bana sanka wanda nasan shi yasa kake shigemun saboda baƙin ciki, na manta ban faɗa maka tun ranar da ka fara cewa kana sona na so na faɗ maka kana buƙatar dentist dan kana da disgusting mouth odour "sadly im not a dentist, Snapping Hannayenta biyu tayi tace ka kula. Ta juya zata tafi kenan ta tsinci muryarsa yana faɗin,dama Mai zanyi da beljiun ,second hand ,Ko kina tunanin bamu san Aurenki Uku ba har da yara Uku, Duk kuɗin babanki da sanayyarsa a ƙasa da ketare Ya kasa zaunar dake ,ko kina tunanin bamusan rabawa matan manyar kasarnan jikinki ne ke hanaki zama guri ɗaya ba..... Follow me on wattpad :chuchujay Arewabook:https://arewabooks.com/book?id=653305e91c06f4783fc2ef84 IG:Ameenatourh__ Facebook:https://www.facebook.com/groups/805959663295457/?ref=share Chuchujay ✍🏽 To be continued . [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK AURE UKU (a hospital romance) BY CHUCHUJAY EPISODE 5⃣ Riƙe Paki dake koƙarin yin gurin KB yayi gam yace"no Paki ,no wannan maganar ba wadda zaka shiga bace ,damƙe hannu Paki yayi kamar zai kaiwa wani naushi yana Mai Cije haƙoran sa, yasan da fushin da tabbas idan Ya je gurin zai zubarwa da Dr Jabir haƙora ". Juyowa umaimah tayi a lokacin da maganar Dr Jabeer ta dakar mata zuciya dai dai saitin da yake mata ciwo, Ta daɗe tana jin rumours ana cewa tana rabawa matan masu kuɗi irin su jikin ta shi yake hana ta Aure, amma bata taba samun wanda Ya faɗa mata kan fuskarta ba, Bawai abun baya damun ta bane, yana damun ta musamman yarda jita jita ke cigaba da yaɗuwa akan ta, Shin wai ita ta ɗorawa kanta ƙaddarar da Allah Ya jarabceta da?. Ɗan karamun murmushi tayi tace "za kaga ƙarfin connection,ba kace kuɗin babana bai zaunar dani gidan Aure ba?"Zaka Ga yarda yarda kuɗin babana zai daure ka for defamation of character tunda baka taba ganin lokacin da na bawa Ko wacce mace jikina ba kamar yarda ka faɗa, I'm gonna show you what money can do here Jabir, If you'll excuse me. Juyawa tayi tana mai Jin wata kwalla na zubo mata wadda tayi saurin gogewa a lokacin guda kuma idanun ta suka sauka kan Paki wanda ke tsaye yana Kallan abunda ke faruwa ransa a mutuƙar bace kar ma ace Da Ya lura da kwallar cikin idanunta. Ɗauke idanunta tayi daga nashin ta nufi cabin ɗinta 'dan shirin Aikin da za tayi, Gama shirinta ke da wuya ta juya zata fito taga an buɗe kofar,ɗagowa tayi, Idanunta ne suka

Chapter 2 of 15