Share this page
ta maganarki ace kinyi Aure uku amma Kin wa saurayi wayau Kin Auresa? Ɗaga girar sa guda ɗaya yayi cikin sigar tsokana lokacin da yayi maganar ƙarshen. Murmushi tayi tana Mai saurin kai idanun ta ƙasa dan wata irin kunya Ya bata,Kafun tace "duka" Ɗago idanunta tayi ta kalesa tace"look paki,im 29 kaima kuma you're 29 kamata yayi ace ka Auri macen da bata kaini a shekaru ba, Paki kana ji da jini a jiki ,bai kamata ka ja rayuwarka baya ba ta hanyar shiga cikin tawa alaƙarba, Kasan ni ne kawai as Dr Bulama amma Bakasan labari na ba, Trust me ,im not the type da zakayi getting involved da,last mijina ɗan Blood money ne and har takaba nayi masa ,Family ɗin ka ma would never Approve of us. " Saurin Mikewa tayi saboda zuciyarta ta fara melting wa Paki sannan cikin san kanta taji zuciyartata tana faɗa mata ta bashi dama ta jawosa rayuwarta amma baza tayi hakan ba . "I think mu bar abun nan a nan ,yes na yarda im attracted to you ,i mean who wouldn't,amma im not that selfish ,so please paki mu yanke wannan alaƙar da baza ta haifar mana da ɗa Mai ido ba. Hanyar fita ta nufa,da sauri yasha gaban ta yace "Im not perfect umaimah nasani i would never be perfect ,im not perfect amma na maki alƙwari zan baki dukkan soyayyar da nake da ita, Nasan bazan taba impressing ɗinki da kuɗi ba amma i will spoil you with love, Zan ɗauki su Nadiya kamar nawan Zan basu uba ,na miki wannan Alkawarin insha Allah." Ban san labarin ki ba ke na sani sannan bazan takura akan dole sai Kin faɗa mun labarinki ba ,Zan jiraki duk ranar da kika shirya faɗan mun Zan saurareki sannan ki sani duk munin past ɗinki bazai dameni ba , "Society kuwa ,Forget about it ,ni Zan zauna dake basu ba,sannan maganar iyayena they are mine kuma nasan yarda zanbi dasu," Clip kuwa ,wanda Ya fasa bashi second thought, ni dake da ahalin mu Ai munsan dai dai. .And yes Kafun na manta kar ki manta na baki wata ɗaya Ki Amince dani dan Allah. Yar ƙaramar dariya tayi tace "wata daya kamar shekara biyar yarda ka ke wani juyata," "Matsa na wuce and Zan kijiraka a asibiti da safe i will be expecting you. Dan shiru yayi yana san gano abunda take nufi zai magana ya tsinkayi muryar Nana na faɗin Au har ƙurya suka shiga ? Ke wacce irin uwace Habiba? Zaki bar ɗanki da baligar mace. Bari naje naci uban yar iskar yarinyar. Da sauri Paki Ya matsa bakin kofar jin yarda Nana ke neman balle kasa kofa.... Chuchujay✍🏽 T B C. [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU (a Hospital romance) By Chuchujay ✍🏽 Episode 1⃣9⃣➡2⃣0⃣ Kamar guguwa haka Nana ta faɗo cikin ɗakin , Tsaye Paki yake gefen Umaimah dan tana turo kofar Ya matsa , Wani irin kallo yake bata ran sa a mutukar bace Daga bayan ta ummu dake biye da ita tace "Nana yanzu Kin yarda imam baya da lafiya shine abunda Ya kawo umaimah nan ,amma ba abunda kike tunani ba". Kallan ummu dake maganar Nana tayi kafun ta matsa gurin Umaimah wadda ta fara ja da baya dan bata manta cizan da Ummu tayi mata ba saboda yarda Ya bar mata tabo, Shinshina ta Nana ta fara kamar wata kare Kafun tace "kwarankwatsa Habiba yarinyar nan kanshin turaren imamu take ,hakan kuma abu ɗaya yake nufi wanda Shine daga jikin sa take." Cikin bacin rai imam yace "subhanallah ,Nana menene haka wai?" Wacce irin magana ce daga jikina take? Duka ta kai masa wanda yayi saurin kaucewa tace "dan ubanka babu abunda ban sani ba musamman wanda Ya dan danganci mata irinta ,idan ba kinibibi ba uban menene Ya kawota duba imamu cikin gidan nan? Ko ance mata bamu da likitan da yake zuwa duba mune , Wanda ma yasha gwagwarmaya a filin daga ,Ya samu horo na sojoji mazan fama masu jini a jika . Kallan umaimah tayi wadda take ji a ranta da ace nana ba kakar paki bace ta daɗe da maganinta, Cikin yin fiki fiki da ido tace sameera zo ki gane mun bakinta kamar sumba suka sha dan naga Ya kumbura ko ido nane?. Da sauri sameera da ta biyo bayan su tace"zancen ki dutse Nana wallahi gashi nan da tazo bakin ta ba a haka yake ba ,ni dama tunda naga Ummu ta fito ,KB ma Ya fita nasan Akwai magana,amma nasan ummu bazata saurareni ba,ke kuma gashi baki gida,shi yasa kina shigowa naga Ya kamata na faɗa maki wannan zance kiyiwa tufkar hanci. Wani irin kallo Ummu ta bawa sameera kafin tace"anya sameera za'a tafi haka kuwa ?, Mene yake damunki,duka duka yaushe na bar su a dakin sannan menene laifi idan har likita da mara lafiya suka keb'e a ɗaki tare ? Haba dan Allah muna yiwa mutane zato Mai kyau mana. "Ba shakka habiba,ba shakka ƴar masu jan kunne har tasan wai ayiwa mutum zato Mai kyau, Gaskiya Muntari nikam Ya cuce ni da Ya Auro ki, Duk yan matan Fulani dake garin nan kyawawa Ya rasa wadda zai Aura sai wadda addinin ta ma yake da rauni, Ke da baki da tarbiyya ina zaki samu damar bawa wani,? Kan umaimah ta kuma yi wadda ta kai maƙura ,ta ɗaga hannu zata mareta tayi saurin rikewa. Wani karamin murmushi tayi a yayin da Nana ta saki baki tana Mai rafka salati, Sauke hannun nata Umaimah tayi da nutsuwa tace"Nana ke babba ce ,sannan ke kaka ce,kuma a matsayin ki na Nana'n imam na ɗauke ki kamar tawa,dan Allah ki bari sannan duk abunda kike tunani bashi ne Ya shiga tsakanina da Imam ba,ni ina da abunyi a asibiti , Kallanta ta mayar kan ummu tace "ummu imam is okay yanzu sannan Zan bawa KB magunguna Ya kawo masa ,stress ne kawai yake damun sa." Murmushi ummu tayi tana Mai jin umaimah a ranta kafin tace"na gode My daughter,Allah yayi miki albarka. Wani irin daɗi umaimah taji a lokacin da ta saka mata Albarkar dan rabonta da jin Kalmar nan gurin uwa har ta manta, Jakarta ta ɗauka tana mai mayar da kallanta kan imam Kafun tace Allah Ya ƙara sauki ,sai na ganka a asibiti, " Cikin zaƙuwa yace "insha Allahu gobe zaki ganni,ai tunda kika zo na warke ." Murmushi tayi masa ta ɗauki hanyar fita a ɗakin , Tana isa falon da suka zauna da ummu taji muryar Nana na faɗin"hylloooooo,ɗiyar Yan marasa kunya ni zakiyiwa fitsara cikin gidan ɗana ki fita Hankalinki a kwance bansa an karya mun ke ba." Appan ,Appan maza zo nan ,zo zo yau akwai bala'i an zagi uwar ubanka, Affan da suka dawo daga unguwa da Nana wanda baisan wainar da ake Toyawa bane Ya fito da saurinsa jin tana kwala kiran Appan kuma tana faɗin ana zagin ta Ya fito da saurinsa yana faɗin"Nana wanene wannan yake zaginki na miki maganinsa?" Turus Yayi ganin umaimah ,kallo ɗaya Ya gane fuskarta dan shi ba ma a case ɗinsu Ya santa ba dama tun tuni shi A wani hira da ka tab'a yi da Alhaji Bulama Along side da ita take burgesa musamman da ake faɗan nasarorinta As a young female surgeon Mai ƙarancin shekaru. Dr Umaimah Bulama a gidan mu? Wow wow,dafa Paki da Ya biyo Nana tare da kowa yayi yace "hamma ita ce dama Dr Bulaman, da kuke aiki tare,God wallahi kina burgeni, Takawa yayi zaije gurin ta Nana tasa hannu ta kamo masa hular sweater ɗin dake jikin sa tayo baya dashi kiiiiii tace"Ubanka muntari, Ni zakayiwa ɗiban albarka da rana tsaka,to sai in gani idan ni ko ita,nan a ɗakin imam Babu irin wankin babban bargon da batayi mun ba,sannan har gida ta biyo Yayan ka ta lalatashi. Saƙalo dukkan su sukayi suna mamakin yarda Nana bata kunyar gandara ƙarya. Har Umaimah ta juya zata tafi dan bata iyawa Nana da harigidonta taji an sake fincikota, Imam ne yayi yunƙuri yana Mai faɗin "wai Nana menene hakan? Nuna sa tayi da yatsa tace "kul ka kiyayeni,wallahi naci maka mutunci yanzu ,tunda dukkan ku kuna ganin kun kai akan karuwa zaku juyawa uwar uban ku baya,To wallahi ni nasan maganin ta ,sai taji dama bata kawo kanta iskanci gidan nan ba ,dan sai nasaka TEGA Ya cizar mata ƙaffafun 'da suka kawota. Finciƙar Umaimah ta farayi har sai da ta kaita Harabar gidan,a karo na farko umaimah tasa hannu ta bige na Nana wadda reaction ɗin Ya kuma zaubarata, Cikin jin zafin kiranta karuwa da tayi tace"Nana ni ba karuwa bace ,ki tambayi jikanki, Murmushi tayi da wani abu Ya ɗarsu a zuciyarta ,Ya kamata ta bawa tsohuwar nan maganin larurarta, Kamo hannun Nana tayi guda biyu tace "ina ta gujewa amma Nana kinƙi bari kinsa dole sai na faɗa miki gaskiyar abinda yake faruwa tsakani na da Imamun ki ," Petting hannun Nana tayi tace "nasan rashin sani yake saki yi mun komai,bari na sake gabatar miki da kaina,". Sunana Dr Umaimah Bulama ,ina harka ne ta farka mutane da ɗinke su a babban asibiti dake cikin garin nan na Adamawa, Ni bazawarace ,sannan nayi Aure ɗaya ɗaya har uku, Ɗan karamin murmushi tayi ganin yarda Nana ke mata wani irin kallo tana mai san kwace hannunta a nata ta kasa duba da yarda ta damke hannun sosai tace "A'h bari kiji Nanan mu,a kowanne Aure da nayi sai da na haihu, Na samu Nameer ,Nadiya da Abdallah,sannan a duk mazan da na Aura akwai tarihinsu ɗan daya ma yana cikin kungiyar tsafi, Kwalalo ido Nana tayi jin maganar tsafi ga kuma yarda Umaimah ta damƙe mata hannu inda ummu da Paki da Affan suke gefe suna kunshe dariyar su, Sameera kuma na kusa da Nana tana zazzaro ido kamar an kaɗa jab'a buta. Wani murmushin gefen Baki umaimah tayi ta ƙara matsowa kusa da Nana tace "wani abu da zai miki daɗi Nana Shine ni da Paki muna soyayyane sannan ina san na Aure miki shi na mayar dashi mijina na sunna kinga da haka zaki yarda ni ba karuwa bace tunda komai zai faru tsakanin mu sunnah ne," Ki yarda Nana'mu Ina san jikan nan naki sosai ,sakar hannun Nana tayi guda tace "zan mutu idan ban zama matar shi ba," Nasan da kikaji daga baki na zaki amince da Auran Imam da Umaimah dan na ƙosa nayi maki tausa. Sake matsa hannun Nana tayi kafin ta jawoshi saitin bakin ta ta sumbata, Fincike hannun Nana tayi tace "uban ubaki dan kan uwaki,kina kallo ko habiba,ba nace miki yarinyar nan yar iska bace ,kuna kallo kuna kuma jin abunda ta mun sannan ta faɗa ko, To wallahi sai dai kiyi bunga ,kiyi funfuna ki rub'e babu Aure akan mu baki ɗan mu,wanene Ya faɗa maki mu shashashune da basu da tunani, Dan ubanki ina kika taba jin wannan gambizar,duk kinyi kwararo a hakan kike so ki Auri yaran da yake sabo fes a leda,wanda nayi imani da Allah yana kaffa kaffa da kansa baya iskanci. Wallahi sai dai ki mutu sau ɗari 'dan muddin in ni nayi cikin muntari kuma na haifesa a cikina nayi rainan sa wallahi bazaki Auri imamu ba. " Wani murmushi umaimah tayi tace "yanzu da kanki Nana kinga kin gyara maganar da kikayi na muna iskanci nida Imam a ɗaki ,tunda Kin yarda shi sabo fes ne a leda kuma yana kaffa kaffa da mata ,kinga kuwa lafiyar sa kawai na duba a ɗakin chan sai kalaman soyayya da muka faɗawa juna, Ba komai Nana,ni na yafe miki tunda dai kinga inda daf da shigowa zuri'ar ki dole na maki ladabi na soki na kyaunace ki, Ni umaimah ina sanki har raina Kaka ta gari". Ai kamar ta kuma chinno Nana cikin Balai tace "wallahi karyarki yarinya ,imamu da kike gani jelar raƙumi tayi nesa da ƙasa sai yarinya irin sa,"Jawo sameera tayi gabanta tace"kinga wannan to irinsu ne ake faɗawa tubus tubus ba irinki marau marau ba,iyhe,"Kuma ki gaggauta barin gidan nan Kafun wallahi na sa a sako mun karen Chan TEGA Ya ciccinye mun yar banza. Juyawa umaimah tayi ga ummu wadda ke ta faman guntse dariyar ta ganin Yarda Nana ke hakikancewa tana maidawa umaimah magana, Zata so ace maganar da Umaimah ke faɗa gaske ne ,ita kanta ta gaji da Nana da halinta,tasan Umaimah ne zasu gwara tare amma ita kam Nana tafi karfin ta. Murmushi umaimah tayi tace "ummu ni Zan wuce". Murmushin ummu ta mayar mata tace "Allah yayi maki Albarka." "Ai kamar Ta sake hasala Nana ta Kalle ta tace "idan ke zaki sashi yayi mata Albarkar habiba 'dan Allah saka shi,Ai Albarka tayi gabas wannan fitsarariyar yarinyar tayi yamma ," Murmushi umaimah ta kumayi tana jin daɗin shaƙar da Nana wadda takai maƙurar shaƙuwa, "Ina sanki Nana,Sosai ,Kema ki samun Albarka na bar gidan nan da soyayyar mutane da dama,nasan kaima Affan ka karb'e ni ko?" Tamayar da tambayar ta ga Affan. Dafe saitin zuciyar sa Yayi yace "In a heart beat,Adda Umaimah". Kamar Nana zata haukace haka ta juya tana Mai zagin Affan Kafun ta jawo hannun Paki Ya dawo yana Mai facing Ɗin umaimah tace "maza faɗawa wannan fitsarariyar guzumar baka santa sannan kajata kamar shara ka fitar mun a gidan nan". Kallan Umaimah yayi cikin ido yace"Ina Sanki sosai Umaimah na ,idan na rasaki na tabbata Nana zata rasa ni 'dan mutuwa zanyi,gobe da safe insha Allahu da fuskata zaki fara karin kumallo cos nasan halin ki baki san cin abinci ,amma idan nazo da kaina Zan baki a baki. Wani irin sautin Awwnnnnnnn da aka saki daga baya ne yasa Umaimah juyawa, Afnan ce Tare da KB suna masu shigowa daga waje, Da gudu Afnan ta ƙaraso ra rungume Umaimah tace "get married to My brother already please ,murmushi Umaimah tayi tana Mai kalla Nana wadda ke tafarfasa kamar zata fashe, Raba jikin ta tayi da na Afnan tace "sweety you're so cute and kar ki damu nan da sabuwar shekara ni da Hamman ki zamuyi Aure kinga lokacin mun cika 30 years tare ,wata guda kawai ya bani," Cike da adoration Afnan tace"mafarkina hamma Ya samu,ina san na Auri age mate ɗina". Cikin jaraba Nana tace"kan ubanchan,Shekararki Ishirin da tara ma,kike tsaye nan cikin rashin jin kunya kike maganar Auren Imamu," Ke ki fita a idona na rufe 'fa, Kai kuma Imamu wallahi sai anyi saban lale 'dan wallahi ko ni ko ku, Ke kuma Afnan zanji dake ne , Juyawa tayi tana Mai cewa sameera "ke wuce muje ,bari na kira muntari duk abunda yake yazo gida yaji abunda iyalinsa suke mun da wata karuwa a Chan waje,Zan nuna musu na haifi ɗa sannan Ya haifu." Kallan ummu umaimah tayi tace "im sorry ummu ba niyata nayi disrespecting Nana ba,i just couldn't stand it,amma kamar na wuce limit ɗina". Murmushi ummu tayi tace"ki kwantar da Hankalinki kar ki damu ,'in dai Nana ce haka take a kullum . Sallama ta musu tana Mai tsintar kanta da cewa imam"ina jiran zuwanka gobe." Chuchujay✍🏽 T B C. Join my whatsapp Channel inda zaku samu tukuicin littafina na noorurrahman wanda yake paid ne,amma zan sadaukar maku dashi kyauta, Ina masu cewa suna san karantashi amma sabida na kuɗine basu samu ba. Ina masu neman discount , Yanzu ba babu buƙatar wannan duka Just Join my whatsapp Channel domin samun sa kyauta. https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU (a hospital romance) By Chuchujay ✍🏽 Episode 2⃣1⃣➡2⃣2⃣ Gaskiya Dr Bulama bazan iya Wanchan Aikin na cyst ɗin chan ba ,patient Ɗin 'fa Hiv positive ce Fa, Gaskiya i cant risk it kawai idan zakiji shawarata muyi mata transfer ko kuma mu ɗorata akan magani, Gaskiya bazan iyawa Mai HiV operation ba , Sauke glasses ɗin dake idanun ta umaimah tayi ta kalli Dr maryam dake ta faman mitar abun, System ɗinta ta juyo tana mai Kallan Dr maryam kafin tace "Dr maryam ki kalla da kyau,cyst ɗin matar nan yayi girman da idan ba'a cire ba zai zama cancerous, And 'dan kawai tana da Hiv shine baza'ayi mata aiki ba? Wanne policy ne Ya hana ,? Shikenan shi kuma Mai HIv ba mutum bane baza ayi masa aiki ba idan yana neman a cecesa? " We have precautions to follow kema kin sani,to menene zai sameki dan kin mata Aiki,bana tunanin zaki mutu. Okay naji its okay,kar kiyi i will take the lead,you can leave My cabin. Tashi umaimah tayi 'dan zuwa nurses station ,alamu tayiwa farouk Da yazo, Babu musu Ya taso yazo,cikin serious tone tace "zamuyi wa matanan aiki ,nasan baka da komai in schedules naka ,Dr maryam baza tayi ba so we are taking over ASAP arrange my team and prepare the operation theater,na tura maka details ɗin patient ɗin ," SOME HOURS LATER. Ko wannen su dake cikin OR ɗin sanye yake cikin gowns da aprons ,eyes wear,da face shield saboda gudun splash na jini,ko wani fluid na jikin mara lafiyan,sanann kowannen su hannunshi sanye da glove, Tsaye umaimah tayi akan Patient ɗin Kafun tace "Intern students This Patient is HIV positive, and zamuyi mata Aiki mu cire ovaries cysts ɗin da take dashi,so beware of needles injury, scalpels ko wani sharp object ɗin ,so Aikin nan tare zamuyi its high time ,ku kula needles Are not allowed to be bend da hannu,ko cirewa jikin syringe, Puncture resistant container ta nuna tace duk used abu na disposing Ya kasance anan. " Nurse farouk dake gefanta ta kalla wanda tasan He's Good at his work and komin menene tsananin risk na Aiki zaiyyi indai tana gefen sa ,itace tsananin yardar da sukayi da juna, Kaɗa mata kai yayi Kafun tayi murmushi, Paki wanda tunda ya shigo asibitin bai sata a idanun,sa ba sai da aka kirasu ,har cabin ɗinta Ya gama zagayen duniya bai ganta ba, Matsawa gefenta yayi cos shima Ya yarda indai da risk to Ya same su a tare. Murmushi tayi ganin abunda yayi, We are performing laparotomy instead of using laparoscopy since the cyst is large, Alamu tayiwa Nurse farouk wanda Ya fara bata kayan aiki tayi makin large cut a tummy ɗin patient ɗin wanda take jini Ya fara fita, Komai Ya dawo visible gareta tana gani a haka ta ciro Cyst ɗin,tasa a container ,miko hannu da tayi yasa paki dake adoring ɗinta mika mata abunda Zatayi staples , Kallan Dr Munnir tayi wanda yayi saurin ɗauke ido dan kar tace yazo yayi dan haka kawai ta maida hankalinta wajen staples ɗin. Bayan ta gama tace"our surgery is done," Nurse Fatima take this Cyst and ovary to the lab a duba ko cancerous ne,amma im positive its not ,cos idan Ya zama cancerous ne we will have to remove her womb,. Fita tayi ta barsu su karasa inda tana sa kafa paki Ya saka, Apron da Face wear ɗinta tayi disposing ,wash room ta shiga bayan ta cire gloves tana Mai saurin wanke hannunta throughout, Bayan ta gama ta fito, Gabanta Ya bayyana yana Mai faɗaɗa mata murmushin sa yace"i Love everything' about you Dr Bulama," Juyawa tayi ganin mutane na wucewa tace"Paki mutane zasu jika 'fa," Ƙaramar dariya yayi yace"I dont Care ,su jini,ko Kin manta abunda na faɗa a gaban management,ina sanki,and bazan daina ba ,sannan a da ni kaɗai nake yi amma yanzu mun zama mu biyu," Kaɗa kai tayi ta fara takawa zuwa cabin ɗinta inda shikuma yake binta a baya, Kowa kus kus ɗin yake saboda maganar da yafaɗa na yana santa Ya fito waje ,wasu su zageta wasu kuma suji haushin ta saboda samun Paki dan akwai masu crushing akan sa da yawa. Zama tayi kan kujerarta yayin da Ya zauna a wadda take facing Ɗin ta yana Mai ƙin ɗauke idanun sa akan ta, "Akwai wani abu a fuskana?"ta tambaye sa tana mai ɗaga masa gira, Dan rufe idanun sa yayi kana Ya buɗe yace"kyanki da yake ɗaukar hankalina a kullum ,Shine a fuskarki,." A kalla yasata murmusawa na babu adadi,dan Cije lebenta na ƙasa tayi tace "baku da wani abu da zakuyi ne yau".? Shafa kwantaccen sajensa yayi yace "Well duk Abunda zanyi yana tare dake Kin manta kece ogata,sai yarda kikayi dani,komai nawa na ɗamƙa miki ,sannan duk inda kika saka ƙafarki nan Zan saka tawa," And yauwa inasan san na tambayeki, Ina fatan kina nufin duk wani abu da kika faɗa jiya gaban su Ummu,cos ummu ta gama saka rai dake ,haka zalika siblings ɗina, Kowa yana sanki amma babu wanda ya kaini sanki,so please kar ki janye maganar ki na jiya duk da ina da yaƙinin dan Nana kikayi amma na tabbata Wani bangaren gaskiya ne, Kallan sa tayi cikin ido tace"yanzu idan nace kazo ka Aure ni zaka iya? Dafe zuciyar sa yayi yace"cikin bugun zuciya,i want to wife you sannan inasan muyi 30 years a ɗakin mu Im not joking cos duk Abunda Ya shafe ki ni bana ɗaukar sa abun Wasa,ko gobe kikace na Aure ki Zan yi ,trust me im loaded, Ƙaramun murmushi tayi tace "Im not After your money kaima ka sani ba,and i Just dont want to rush things' dan haka you will have to court me,Ya kamata kasanni sosai nima nasan ka ,like da dislikes ɗin ka da nawa,and a side ɗina bani da matsala ,side ɗinka ne " . Karshen maganan ta kai tana san ganin reaction ɗin sa Kafun tace "Im Sorry idan jiya na wuce iyaka". Yar Dariya yayi yana Mai tuna abinda Ya faru jiya Kafun yace "Well indai kin yarda dani,kin kaini gida a matsayin wanda kika zab'a zakiyi rayuwa da then nana baza ta zama matsala ba." Ɗan kasa tayi da murya kafun tace "beb ɗin ka fa". Fahimtar da sameera take yasa shi darawa yace"na jiyo kamshin kishi,Well sameera bazata taba zama threat tsakanina dake ba cos ke nake so ,sannan ni tsakanina da ita babu wata alaƙa ta soyayya,kawai alaƙace ta zumunci bayanta ba wata ,sanann tana internship ɗinta ne a sydney private hospital wanda na Uncle ɗinta ne and saboda tace a gida nan ɗin zata shi yasa suka barta, Sannan gidan mu sun bata masauki ne saboda sun ɗauketa an zama ɗaya duka daga Family ɗinta, Dan shiru tayi tana nazari ,ba wai tana tsoran Sameera bane,amma tabbas tasan akwai sauran rina a kaba, Fitar da tunanin sameera tayi a kanta kafun tace"you have to try hard to impress me 'fa paki cos na wuce stage ɗin da puppy love zai burgeni, "Can you handle me. Haɗe hannayen sa biyu yayi yace "ban fito ba sai da na shirya sannan ki yarda dani idan nace maki,bazaki tab'a tsallake soyayyar Paki ba."Kashe mata ido ɗaya yayi a ƙarshen maganar sa wanda Ya sakata giggling kamar wata high schooler, Buɗe kofar da akayi ne yasata saurin juyawa akan kujerarta tana Mai Kallan desktop ɗin dake gefen ta cikin Mazewa, Nurse farouk ne,haɗe rai tayi tace "yaushe kafara shigo mun babu Knocking ,"Ƙaramun murmushi yayi dan Ya fahimci abinda yake faruwa, Aje file ɗin dake hannun sa yayi yace "ayi mun afuwa to,file ɗin patient ɗin chan ne hardcopy na kawo miki kamar yarda kika buƙata,". Na barku lafiya ,da murmushi a fuskarsa Ya fita. Bayan fitar sa Paki Ya Kalleta yace"masoyiyata ki daina ƙokarin boye soyayyarmu dan yanzu abunda nake faɗa miki,kowa a asibitin nan yasan ina sanki,sannan a yanzu ma na sake ɗaura ɗamarar sanar da kowa soyayata gareki, Tashi yayi yana Mai blowing mata kisses da hannu ,Kafun Ya kama hanyar fita yana Mai faɗin we are going out for dinner yau since yau kina night ne". Kaɗa kanta tayi bayan fitar sa dan rabonta da jin yanayin da take ji game da paki tun kan Hafiz. A hall ɗin da suke zama Ya tarar da KB tare da Aisha shareef suna hira ,tana ganinsa ta washe masa haƙora tace "paKi ina kaje ne tun ɗazu ina nemanka since operation ɗin chan bangan ka ba," Zama yayi kusa da Kb yace "nace zance ne." Cikin rashin jin daɗin furucin nasa tace ,zance mana,naje zance gurin macen dake haukata mun lissafina a kullum idan na saka ta cikin idanuna, Ina tare da Dr Bulama tun ɗazun ,da kyar na iya yakicewa na taho saboda nasan yanzu Zatayi abu Mai muhimmanci ne. Da mamaki ta kalle sa tace"dama wai paki jita jitan nan ba karya bane,kai yanzu baka jin kunya ma?tayaya zakayi soyayya da bazawara wadda tayi Aure daya daya har uku ,har da ƴaƴanta fa, Amma kai ka kalle ka young,handsome and rich,Mai zai hana ka kalli matan dake gabanka. Shima da mamakin furucin nata yace "kina nufin yan mata irinki Zan kalla?kalli nan Aisha,I hope ban baki wrong signal ba,sannan with All due respect bana san kina faɗan abun banza akan Umaimah raina zai na baci naji bana san magana dake ,and yes ke ba irin matan da nake so bace ,irinta nake so dan haka respect it please." Dauke kai yayi da Ya gama maganan sa dan ta ɗan Sosa masa rai, Tashi tayi tace "kayi hakuri ban faɗa bane da wani abu," Bayan barinta gurin KB ya kallesa yace "mutumina why mana,Mai yasa zakayiwa Aisha magana a haka ne saboda Allah." Haɗe rai yayi yace"gwara nayi rejecting ɗinta tun kafun ta ɗauki hope ɗinta da nisa,ni one woman man ne,one army" Dariya KB yayi yace "zaka sani ne duk ranar da Nana ta mayar da kai sameerah and umaimah man". Ƙaramun tsaki yayi yace"bismillah ɗin ta tasan halina ai". Dariya sukayi a tare kowa da abun yake tunawa na Nana. *** Kamar yarda Ya faɗa da dare Ya fita da ita romantic dinner, Duk yarda take tunanin Paki Ya wuce nan gurin saboda yarda yake narkar da ita a soyayyarsa ba a magana,har asibiti ya maida ta cikin kulawa yana mai nuna mata matuƙar soyayyar ta da yake yi. Sai wurin 9 Ya shiga gida, Yana ƙokarin shiga sashensu yaji An ambaci sunansa da muryar da ya Jima bai ji a zahiri ba illa a waya. A/N Mundai kusa Aurawa paki umaimah and nan zamu tsunduma tafiyar Aurenta da paki,daɗi ne ko akasin haka?.Nidai nace daɗi ne kufa? Ku cigaba da bina kun sharhi dan ina mutuƙar kaunarku da sharhinku❤ Chuchujay ✍🏽 T B C. [11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU (a hospital romance) By

Chapter 8 of 15