"ka sake practicing essay ɗin nan idan kaje inda nake a adamawa. "
Chuchujay ✍🏽
Tbc.
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU
(a hospital romance )
By chuchujay
wattpad :@chuchujay
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j
Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.
Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,
Just follow and share i want audience domin baku.
Episode 2⃣9⃣➡3⃣0⃣
FRIDAY 12:00pm
Tun daga harabar gidan Bulama zaka san ana gagarumun taro,
Idan ka tsaya Kallan babban compound ɗin wanda aka ware gefe aka tsantsarasa cikin yanayi
na event zaka ce wani arnen hall ne aka kama 'dan gurin Ya tsaru ciki tsaruwa da decoration na
blue and white,
Gurin da amarya zata zauna kan sa abun kallo ne,
Biki ne ake na kwana ɗaya wanda duk wanda Ya hallarce sa zai daɗe yana tuna wannan biki,
(Da Alƙalami na da littafina na taka 'dan shiga cikin gidan Bulama dan ɗaiɗai kun mutanen da
nake gani basu gamsar dani ba ,mutum ɗaya nake san na saka a idanu na wato Umaimah
Bulama ,sannan ina san na tsinci labarin shin bikin wa ake gidan attajiri bulama).
Ahalin gidan maza da yan uwa da sukazo baki dayan su shirye suke cikin rich white
expensive getzner a yayin da bakin daddy kuwa yaƙi ruruwa,
Fita sukayi harabar gidan suna masu hawa Arnan motocin da suka mallaka domin isa baban
masallacin Sudais ƙashim domin gabatar da sallar juma'a da kuma ɗaurin Auren da zai kwashi
Alumma masu numfashi After All ɗaurin Aure ne za'ayi na ɗiyar Bulama tilo,wadda take tsoka
ɗaya a miya garesa,A karo na HUƊU.
Magana ta mutane dama baka isa ka tare ta ba muddin idan sukaso yin ta,haka nan maganar
Auren Paki da Umaimah ta ringa yawo a duniya kamar bonfire,ko wanne vlog da gossip page
idan kaje maganar su Ake,wasu suyi Negative magana wasu positive Har da masu faɗin
umaimah ta Auri ƙaninta,wasu suce asiri tayi masa ta Aure sa,wasu suce Auren kuɗi ne da dai
sauran su,sun gagara gane soyayyar dake tsakanin su,
A watan da aka saka na bikin su ba karamar soyayya suke nunawa juna ba ,kar ma ace paki
wanda baki ɗaya yarda take amsa masa soyayyar sa yasa shi kara zaucewa a soyayyarta ,
Wani lokacin har kunya yake bata a asibiti yarda yake zaƙewa soyayyarta ,tun ana gulmar har
An haƙura saboda basu bawa maganganun mutane attention ba ,love ɗinsu kawai suka saka a
gaba .
Maganar Auren su ba a wani saka ta da nesa ba saboda yazo Aure kuma ko wanne side sun
amince sannan Ita ba budurwa bace da za'a tsaya wani bata lokaci,dan haka iyayensu suka
taƙaice lokaci da yardar su,
Hajiya Nana kuwa kowa yayi mamakin yarda tayi shiru ta kwantar da hankalin ta kamar dama
tun farko ba ta ƙi Auren ba,
Babu wanda Ya maida hankali sa gareta dan kowa Ya saka shi ne as ta haƙura sannan tasan
rigima ne kawai ta saka a gaban ta.
***
Zaune Umaimah take bakin mirror tana gyara gelling gefen sumarta da tasha kananun kitso
wanda suka zuba bayan ta kasancewar ta mace mai yawaitar suma,
Tsantsaɗediyar kwalliya ce a fuskarta wadda batayi kadan ba bakuma tayi yawa ba,
Idan ka Kalle ta Zaka so ka kuma saka ta ciki Idanun ka saboda irin kyau ɗin da tayi mai ɗaukar
ido,hannun ta zane da ja da baƙin lalle,Abun ka da Mai haske sai wanda Ya kalla.
Daga gefe Hindu dake ta faman gyara ring light tace"beb yau Paki bana tunanin zai iya ɗauke
idanun sa akan ki ,kinga yarda kika kashe ni kuwa."
"Ƙaramar dariya tayi tace "babban show off ɗin bai wuce ace ina da ƙawa kuma yar uwa likita
sannan a wani hannun make up artist,girl idan nacewa wani ke kikayi kwalliyar nan ba lallai a
yarda ba fa,.
Murmushi Hindu tayi tana mai gyara gashinta tace "sai ma Kin fada musu na tsuma ki a
hamam ɗina na egypt zasu kara shan mamaki,i Just pray kar kisa ɗan mutane hauka cos i trust
me .
Dariya umaimah tasa tana Mai fadin ke fa abunki sai ke Masoyiya ,ni kam Buɗar kan nan da
za'abi ta tawa ma baza'ayi ba cos girl this is My fourth nikah,mene sabo a ciki
Dafata Hindu tayi tace"imam ne sabo a ciki,girl munji Auranki na Huɗu kenan but trust me jikina
Ya bani this is for the best sannan insha Allahu baza kice dama Kin sani ba,cos soyayyarki a
idanun imam gaskiya ce,sannan ahalin sa kowa Ya karbe ki,his mom loves you with all her
heart,Just cheer up ki saki jikin ki kiyi murna da ni'imar da Allah yayi miki,cos ba kowa yake
bawa wannan damar ba,
Ni yanzu ki kalleni mana turning 30 amma ko na fari banyi ba,Ai jira nake kawai a gama bikin ki
mu kaiki ,ko Ahmad yaƙi ko yaso sai munyi Aure,
Dariya Umaimah tasa tace "Poor Ahmad yaga rayuwa hannun Hindu,"
Suna cikin wannan hirar ƙaran text message Ya shigo mata daga layin paki,
Murmushi tayi tai clicking dan karantawa ,
"Ina Mai tayaki murna da farin cikin zama matar Imamu Paki cos yanzu Kun zama mallakin
juna,"
Murmushin da take faman yi ne yasa Hindu faɗin "An ɗaura hala",
Cike da murmushi tace "Allah yayi Hindu ,na zama matar Paki,i Just cant blv it sai kace a
mafarki,"
Godiya ta ɗaga hannun ta tana Mai godewa Allah ,
Guɗar da take tashi daga waje ne yasa Hindu saurin gyara mata rufin veil ɗinta a fuskarta tace
nasan yanzu su Aunty sadiya zasu shigo,tana tufe baki kuwa guɗarsu ta cigaba da ƙuwa zuwa
ɗakin Umaimah.
Fita sukazo sukayi da ita a yayin da manya ke binta suna ta faman feshe ta da turare har suka
kaita gurin da aka tanada domin zaman ta,
Ruwan kyalkyali mai kamshi aka fara mata kamar Ba gobe,a yayin da ake binta ta da turare mai
Arnen kamshi ana feshe ta ta ko ina,
Kowa cikin matan duk wadda zata fesa mata perfume sai ta aje kuɗi ko wani expensive jewelry
ɗin cikin kwaryan dake gefen ta,
Abunka da Aure na masu kuɗi wanda yazo da Al'ada Kowa da kalar bajintar da yake san Ya
nuna har da su hajiya waɗanda basu ƙaunarta ko kusa,amma a wannan rana dole suyi
pretending ,dan hatta hajiyan gold ta aje wanda babu wanda yasa Mai tsadar nata,
Jerin motar da suka fara shigowa ne ya sa hankalin mata masu guɗa Ya karkata kan zuwa
kamo ango Ya fanshe fuskar matan sa,
Cikin farar shaddar sa da tasha aiki jikin babbar riga ya fito,
Kansa ɗauke da zanna buƙar Mai bala'in kyau fara sai kafafun sa sanye cikin dolchs Halfcover
shoe offwhite,abu ɗaya yake ihu a jikin Paki wato MONEY MONEY,
Shine abunda jikinsa ke kira domin hatta agogan dake hannun sa pure diamond ne,
Gefen sa KB ne da abokanan su waɗan da suka sha gayu iya gayu,
Ƙanwar Dada ce taje ta kamo hannunsa tana Mai fadin maza je ka nemi Albarkar manya ka
buɗe mana fuskar matar ka 'dan kai ɗaya ake jira,
Cike da fara'a irin ta angon da Ya samu abunda yake marari Ya nufi manyan Umaimah ya
kwashi gaisuwa Kafun Ya nufi gurin amaryar sa domin buɗewa kowa fuskarta mai tsada Ya
ganta,
Sanin Al'adar yasashi zuwa da shirin sa "Diamond ring wanda yayi worthing maƙudan kuɗi Ya
ciro a cikin ɗan kamin box Ya kamo hannun Umaimah wanda Ya gaji da haɗuwa da lalle Ya zira
mata,"Tafi gurin Ya ɗauka da guda a yayin da Ya karbi stick ɗin da ke ɗauke da gashin ɗawisu
Ya ɗaga fuskar gyalenta,
Wani irin ajiyar zuciya Ya sauke lokacin da idanunsa sukayi tozali da kyakyawar fuskar
umaimahnsa Mai rikita masa dukkan tunaninsa,
Gam ta rufe idanun ta amma kan fuskar ta ɗauke da murmushi,
Ɗurkusa yayi dai dai saitin kunnenta yace "babyna ki buɗe idanunki ki kalli Imam ɗinki kisa
idanunki cikin nawa dan yau ni dake mun zama mata da miji,"
Buɗe idanunta tayi according to umarninsa,
Murmushi yayi yace"kin gaji da yin kyau matata,kaf a duniyar nan babu mace da take kasheni
da raina kamar ki,yau kin bani Aljanna a duniya,"
Babu abinda take sai murmushi dan kyan da paki yayi Ya gama tafiya da ita sanann ga wani
ƙwarjini da yayi mata wanda yasata neman magana a bakinta ta rasa,
Horn ɗin da aka hura ne Ya kawo conclusion na ceremony din a yayin da aka cigaba da sauran
Al'adu cikin farin ciki ga waɗanda suke yi da gaske,
Da dare Wurin 8,daddy Ya gama jaddada mata nasihan sa wanda ba shine karo na farko ba
,hakazalika yaya Abubakar sai hajiya wadda tata nasihar izgilanci ne dan maganar farko cewa
tayi"zamu fara irge kuma yaushe za'a ƙarkaɗe maki ɗakin ki."
Kasa mata shiru tayi dan haka ta cire kunyar wai ita amarya ce tace "Idan mun kawo ziyara kam
hajiya dole a kakkab'e tunda bayan kwana biyu shatu da yarana zasu bi bayana ,a kula mana
Kafun mu zo gaishe ku.".
Hajiya na shirin mayar mata da zagi daddy Ya shigo ɗakin.
Yaya Abubakar ne Ya tuƙa motar da aka kai Umaimah gidan Paki,
A cikin gidan su ginin da zasu zauna sabo yake wanda aka zubawa kayan alatu sannan babba
Mai zaman kansa ,
Idan aka tsaya zayyane maka Ya sashen Paki yake sai ka buɗe baki,dan guri aka buga kamar
baza'a mutu ba,
Bangaren su Ummu aka fara kaita amana Kafun aka maido ta sashen ta.
Bayan kowa Ya watse sai Ya zamana daga ita sai Hindu wadda ta tsaya zaman jiran a rako
ango ta Kama gabanta ,irin shaƙiyancin da ta ringa ma umaimah har sai da tasa ta fara Jin
kunya ,ganin hakan yasa Hindu ta cigaba da kwasarta yarda ranta yake buƙata.
Wuraren goma aka rako Paki ɗakin matar sa,
Babu wani b'ata lokaci bayan dukkan wani abu da Ya kamata ayi suka Kama gabansu yayin da
Kb Ya mayar da Hindu gida suka tafi suka barsu da fatan Alheri .
Awkwardly Umaimah ke zaune kan gado kamar yau ta fara Aure tana mai Kallan paki wanda
Ya zauna kan stool Yana Mai binta da ido kamar Yau Ya fara ganinta,
Cike da kunya tace "na chanja maka Kama ne ranka Ya daɗe Paki?"
Tasowa yayi Ya hawo kan gadon da take daf Da ita Ya kama hannun ta yace "Alhamdulillah
,ko yanzu na mutu na koma ga ubangijina bazan mutu ina Mai dana sani ba dan Ya bani kyauta
mafi mahimmanci a rayuwa ta,"
Hannunta Ya kama Ya ɗora a sautin zuciyarsa yace"kin ji yarda zuciyata ke bugawa saboda
ke,kilan ke baki jin yawan Abinda nake ji ,amma dan Allah umaimah ki soni koda kwatankwacin
karamin farcen ki ne,ki rike ni amana saboda akan ki ni kaina bana gane kaina.
Kallan sa take cikin ido tana tunanin abun Alherin da tayi Allah Ya azurtata da Paki,
Da Murmushi ta cire hannunta kan saitin zuciyarsa ta Kama hannunsa cikin lallausan nata cikin
wani salo na ƙauna tace"wane Ya faɗa maka bana sanka?
Zuciyata duk wani bugu da Zatayi da sunan ka take bugu mijina,ina mutukar sanka sannan zan
kula da kai nayi maka biyayya na kyautata maka ,insha Allahu bazan baka damar kuka dani
ba,duk da ɗan adam Ajizine shiyasa nake san tun yanzu ka yafen laifin da zan maka cikin sani
da kuma rashin sa,
Faɗaɗa murmushin sa yayi yace"indai nine zan ɗaga maki ƙafa ki shiga Aljanna ,na ɗaga
miki matata sannan na yafe maki duk abinda zaki mun sane da rashin sa."
Cikin jin daɗi tace"nagode mijina ,Allah Ya barmu tare,".
Dan ƙasa yayi da idanunsa yace"baby bazan maki abinda baki so ba and idan baki shirya
bani kanki ba a daren nan namu na farko ba i will wait ,ɗago idanun sa yayi yana Mai kankance
idan sa guɗa daya Ya nuna saman ƙaramun yatsansa yace "just let me kiss your soft lips ko sau
daya ne,"
Dariya tasa ganin yarda Ya maraimaraice da fuska tace"Habibi kana san malaiku suyi ta tsine
mun ko?
Kar ka manta da gangar jikina da ruhina duka naka ne ,na mallaka maka haka zalika Allah ma
Ya mallaka maka,amma kar ka manta im not a virgin ka daina wannan zumuɗin.
Sake jawota jikinsa yayi yace "it doesn't matter cos ke nake so ba virginity ɗinki ba ,i want to
unite with you not your virginity,and na gode da kika mallaka mun gangar jikin ki da ruhinki,dan
haka yanzu mu tashi muyi alwala mu godewa ubangijin mu ,na baki Abinci na miki wanka na
rabaki da tsinuwar malaiku,"
Dariya tasa tace"so you're this naughty,"
Tashi yayi yana Mai cire rigar navy blue ɗin kaftan ɗin dake jikin sa Ya barsa daga shi sai
singlet,
Daga gadon da Umaimah ke zaune ta saci kallan delicious jikin sa da Ya gino,
Murmushi yayi daga inda yake yace "ki daina satar kallona ki kalleni cos duka Jikina naki ne."
Shiga bathroom yayi Ya barta tana Mai jin kunyaa.
Bayan sunyi sallah sun mika godiyarsu ga ubangijinsu,ya kalleta yace vari nazo na ciyar dake
yarda bazan baki wahala ba.
NIMA ZAN CI KAZAR AI.
Muryar Nana ta gabato su a yayin da gangar jikinta ke kunnowa cikin ɗakin.
***********
Amma wannan Nana anyi yar ƙaniya,
Wai ta ina ta shigo🤧
chuchujay ✍🏽
TBC.
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU
(a hospital romance )
By chuchujay
wattpad :@chuchujay
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j
Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.
Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,
Just follow and share ❤.
Episode 3⃣3⃣➡3⃣4⃣
Kallan Umaimah paki yake cike da soyayya da tsantsar kauna,jinsa yake kamar soyayyar da
yake mata ma bata isa ba Ya kamata ace Ya kara,
Shafa kanta yake yana Mai kallan yarda ta ƙara masa wani irin kyau a baccin ma da take ,
Sosai Ya gajiyar da ita shi kansa Ya sani ,amma he couldn't help it cos Ya ƙasa rike kansa a
kanta,
Murmushi yayi yana Mai kissing goshin ta yace"Allah yayi miki albarka umaimah na,Allah Ya bar
mu tare Ya ƙara danƙon kauna a tsakanin mu,insha Allahu zanyi iya bakin kokarina naga na
faran ta maki."
Tashi yayi a gado Ya buɗe kofar a hankali Ya fita a dakin dan zuwa samar mata breakfast
,yana ƙokarin shiga kitchen ya tsinkayi knocking ,ɗakin sa Ya shiga Ya sako jallabiya Kafun Ya
yazo Ya buɗe kofar,
Afnan ce tsaye tana Mai washe masa baki hannunta ɗauke da basket tace"Good morning
Hamma,"
Murmushi yayi yace,Good morning little Sis shigo mana,
Shigowa tayi tana Mai yin dining Area domin aje basket ɗin tana Mai faɗin ,Adda bata tashi ba
hala,
Dan karamin murmushi yayi yace "tukunna, ki aje kiyi gaba sai mun shigo"
Dariyar ƙasa ƙasa tayi Kafun ta fita a sashen tana Mai jin daɗin samun farin cikin yayan ta,
Ɗakinsa Ya wuce domin shiryawa cos baya san ya tashi umaimah,
Bayan fitar sa ɗakin da wasu yan lokuta umaimah ta tashi tana Mai jinta over hills,she just
cant help falling for Paki saboda Shi ɗin na daban ne,he's unique ta ko wanne aspect,
Bayan ta gyara ko ina na ɗakin yayi fes duk da ba datti yayi ba ta shiga wanka dan sakewa da
kuma sake gasa jikinta cos she's sore saboda paki bai mata da wasa ba,tayi reaching orgasm
kafin shi,so tabarshi yasha budirin sa dan burinta yanzu a rayuwa bai wuce ta farantawa Paki
ba,
Bayan ta fito ta shirya cikin maroon cotton lace wanda akama ɗinkin Abuja bubu,sosai tayi
kyau a cikin sa kamar ka sace ka gudu,
Ɗan touching fuskanta tayi kafun ta ɗaura kallabinta ta feshe ko wanne sashen jikinta da
sassanyan turaren da ta samo a hamam ɗin Hindu ,kana jin kamshin sa sai kaso ka ƙara ji,
Takalmi ta ɗauko brown flat ta saka ta jawo wayarta tana Mai duba lokaci,
Karfe Goma na safe ,cikinta taji yana mata ƴar kuwa ,
Murmushi tayi tana tunanin ta inda zata fara saka hayateen ta a idanunta cos bata san ɗakin sa
ba,alamun mutum da taji a ɗakin kusa da nata ya tabbatar mata da nan ne nasa,
Kai tsaye ta Murɗa handle ɗin wanda Ya buɗe kamar dama ita yake jira,
Ɗagowa yayi Ya sauke idanun sa cikin nata faɗaɗa fara'arsa yayi yace "beb kin tashi ashe.
Murmushin itama ta maida masa tana Mai ƙare masa kallo,
Daga wanka Ya fito cos ƙugunsa ɗaure da towel a yayin da hot jikinsa ke ɗigar ruwa Kaɗan ,
da takonta na ƙwalisa ta ƙarasa tana Mai masa kallon ƙauna,
Ƙaramun towel ɗin dake hannun sa ta Karb'a a hankali ta fara goge masa ruwan daga cikinsa
cikin sigar kulawa,zaunar dashi tayi a kan stool tace "give me the honour hayatee,"
Murmushi yayi a yayin da ta jawo mansa tafara shafa masa cikin wani irin salo Mai ɗaukar
hankalin wanda ake yiwa,tana shafa bayansa da man ya jawota ta faɗo kan cinyarsa,
Saƙale hannunta tayi a kan kafaɗarsa tana Mai kallan ƙwayar idanunsa tace "Good morning
again sunshine,."
Kissing goshinta yayi yace "wiffey Kin san yanzu fa bazan na iya riƙe kaina ba a kanki cos
soyayarki kamar anƙaramun ita over night,i might want you anytime and anywhere, "
Cije lips ɗinta na ƙasa tayi tace "i wont mind,we can also have some kinky hospital romance
,bazan damu ba and nasan it will be interesting ,ta ƙarasa tana Mai kashe masa ido ɗaya,
Sake Matse ta yayi a jikinsa adam Apples ɗin sa na motsi yace "how about yanzu, cant you feel
me beneath,?
Im hard for you.
Jin yarda yayi hard ne yasata saurin tashi a jikinsa tana Mai faɗin the Number you're trying to
Call is not reachable At the moment please try again later hayatee,kiss ta masa blowing tana
Mai faɗin"ina jirankaa dining Area im famish,".
Murmushi yayi yana Mai jin sa a cloud nine a hankali Ya furta"she's cute"
He cant Blv wai yau shine ke a matsayin mijin umaimah,although dama jikinsa na bashi zai
mallaketa amma He's not expecting it this soon.
Farin transparent yadin sa mai masifa kyau ya saka kafun yayi combing sajensa da kansa Ya
feshe jikinsa da turare Ya mara mata baya,
Zaune ya tarar da ita tana mai danna wayanta a hankali ,chak taji Ya ɗagata batayi aune ba,
Ɗan shagwab'e fuska tayi tace "hayatee im famish kasan baka ɗaga mun kafa ba fa,ka kwashe
dukkan wani abincin dake cikina,"Pecking lips dinta yayi yace"shiyasa Ai yanzunan zan ciyar
dake ki ƙoshi,and kinyi kyau sosai cos komai kika sa jikin ki kyau kike masa ,murmushi tayi tana
Mai lajutar hancinsa tace"nafi kowa sa'ar miji a duniya,sannan kayiwa kayan jikinka kyau."
Shafa gefen fuskarta yayi Kafun ya kaita ya aje kan kujera Kafun yaje Ya dauko abincin Ya
dawo Ya zauna,
Cikin kulawa da soyayya suka ciyar da juna kafun suka fita tare dan zuwa gaida su Ummu,
A falo suka tarar da Abbu Nana ta sashi gaba tana masa maganar da basu san ta mene
ba,suna shiga tace "yauwa gasu nan ma kilallun basu iya zuwa gaida iyaye ba sai ƙarfe sha
ɗaya na safe,ko masu bautar rana kuwa yanzu sun gama bawa rana sujjada,".
Baki ɗaya ahalin gidan suna falon banda Hamma osama,har da inteesar da new born babynta
Ummussalma yar kwana arbain,
Zama umaimah tayi dai dai ƙafar Nana wadda tayi saurin ɗauke Kafarta kamar wuta ta tab'a
ta,ƙaramun murmushi umaimah tayi cike da kunya ta gaida sirikanta inda ƙannen mijinta suka
miƙo masu tasu gaisuwa cike da girmamawa da ƙauna,
Gaida Nana sukayi a tare a karo na biyu,tura baki tayi kamar bata ji su ba,
Inteesar ce tace "nana su hamma 'fa gaidaki suke.
Fiƙifiƙi tayi da idanunta tace"ki kiyayeni inti ,nafi kashi ɗoyi idan ka tab'a ni sannan najisu Ai
ganin damar amsawa ne banyi ba ko zan daku?"
Juyawa tayi tana Mai Kallan kofar da ake bi a fito falon tace"sameera kefa nake jira."
Kamar wasa sai ga sameera da akwatinta dana Nana tana ja niƙi niƙi,
Da mamaki ummu ta Kalleta tace"sai ina?"
Murguɗa baki Nana tayi tace"sai sashen imamu,yo dama bakiji abunda nake faɗawa muntari
ba kenan,to bari na maimaita maki tunda akwai tuwo a kunnenki,to zan koma sashen imamu
tare da Sameera wadda zata na min abincin da komai dan ban yarda da cin abinda aka dafa
gidan imamu ba,amma na yarda na zauna 'dan ni da kuke gani wallahi nan gani nan bari
dumamen mayya,
Tunda na haifo muntari to sai yarda nayi da kowa a gidan nan."
Shiru ummu tayi tana Mai kallan umaimah wadda taji baki ɗaya takaicin Nana Ya sake
kamata,
Dariya Affan yasa wadda ta saka kowa a gurin kallansa ,
Wayarsa Ya ɗora kan cinyarsa yace "Nana kenan,Nana duniya ,wato ke rigimar ki 'fa kullum
ƙara yawa yake maimakon ta ragu ,ni wallahi idan kina wani abun dariya ma kike bani,".
Tasowa tayi kamar zata dakeshi tace"ma'ana dai ni mahaukaciyace Apan,a'a kafito fili ka
kirani saban kamu sai nasan ka cika zaƙaƙƙen yaro mara mutunci,
Kamota Abbu yayi yace "Nana zauna muyi magana mana ,
Zama tayi tana Mai faman hura hanci Kafun tace "ayi dai magana mai kyau 'dan ko mutuwa
nayi baku kai gawata sashen imamu ba ban yafe maku ba kuma wallahi sai nayi ta muku gizau
na hana ku zaman lapia,idan ba haka ba ban cika mace ba,tana kai ƙarshe ta saka kuka. "
Baki ɗaya Abbu babu abunda ke rikitasa irin kukan Nana,da sauri Ya dawo gabanta yace "kiyi
haƙuri Nana zaki zauna sashen imam idan ma so kike su sai su bar maki gidan ke ki koma na
saka maki Yan aiki".
Snapping yatsanta tayi tace "La bazai iyu ba,ni da ka ganni ƙafata ƙafar imam duk inda zashi
dan babu yarda za'ayi na barshi shi kaɗai da wata matar muddin ba sameera ba shi yasa duk
inda Nasa ƙafa zata saka har sai ranar da imamu Ya Aureta".
Ƙokarin tashi imam yake umaimah tayi saurin kamo hannunsa tana Mai kaɗa masa kai,
Tashi ummu tayi ta bar gurin,tab'e baki Nana tayi tace "a banza anyiwa jaka tsarki da roman
ganda, ".
"Dama Mai zataji tunda dukkanta gandar ce,indai samira ce Gaki gata dama ni tun haɗuwata
da ita nasan sheɗaniya ce amma ki bari ta maki nata sigar nan zaki gane Mai ake nufi,
Afnan ta faɗa tana Mai tashi tabar gurin gudun kar Abbu yayi magana amma jin har tabar gurin
baice uffan ba Ya tabbatar mata da shima Baiji daɗin abinda ke faruwa ba.
Shegiya jikar masu jan kunne dama Mai kika iya a hausar banda lalube.
Tsaki tayi tace "kai muntari kai nake jira nikam" .
Ƙasa Abbu yayi da murya kamar baya san maganar yace"shikenan Nana abunda kikeso shi
za'ayi,"
Tashi yayi yana kare zancen saboda baya so Ya haɗa ido da imam dan babu ɗansa da yakewa
abunda bai kamata ba kamar Imam,shiyasa babu ɗan sa da yake ƙautatawa kamar sa dan shi
kaɗai yake bawa salary Mai tsoka duk wata wanda tuntuni Ya saba musu.
Washe baki sameera tayi tana Mai kama akwatin kana tace "Paki zo taimaka mun mana
tunda guri ɗaya zamu,"
Da wani irin fitinannan kallo Ya bita Kafun yace "ki godewa Allah ban tab'a dukan mace
ba,wallahi da yau idan na fara dukanki san na ballaki kaca kaca da mutanen minna zasu kasa
gane ki,sannan idan har kina san kanki da Arziƙi ki fara shirin tattara kayanki ki koma gidan ku
dan Allah".
Dariya Nana tasa tana Mai gutsurar goro tace "yaro man kaza,Ai sameerah da kake gani
Auranta kamar kayi ka gamane shiyasa zan koma gidan ka tare da ita tunda itama ma'aikaciyar
lafiya ce babu wani ma'aikacin lafiya da zai kwazirani."
Hannun umaimah da tayi sakalo tana Mai jin zuciyarta na mata zafi ya kama yace "beb tashi
muje ,"Tashi tsaye tayi tace "ka nunawa Nana gurin su bari naje gurin ummu."
Knocking kofar ɗakin ummu tayi wadda ta bata izini ta shigo,zaune ta tarar da ita kamar Ma
kuka take,tana ganin umaimah tayi saurin goge idanunta tace "umaimah kece shigo mana".
Babu musu ta shigo ,tana ƙokarin zama ƙasa ta kamota tace"No umaimah ban yarda da zaman
ƙasan nan ba,taso kizo ki zauna kusa dani,"Babu musu umaimah ta zauna gefen gadon,
Hannunta ummu ta kama tace"ki ɗaukeni uwa umaimah saboda na ɗauke ki ne a matsayin
intee da Afnan,nasan abunda Nana take bai kyautuwa,amma We just have to handle them mu
bisu hankali mu rabu dasu lafiya,
Kin ganni nan ,rashin jin daɗin Nana yafi jin daɗi na da ita yawa ,amma na yarda tana da kirki
kawai dai rigimarta ce damuwa,sau da dama nakan ɗauke ido idan na tuna alherinta ta wani
wajen,amma a bangarenki bana jin dadin abunda take maki,kiyi haƙuri na kasa yin komai a
lokacin da ake shirin kwace maki farin cikin ki,
Kiyi hakuri sannan zanyi ƙokari naga kun koma gidan ku sannan samira zan san yarda zanyi na
sa ta tafi gida."
Murmushi umaimah tayi tace ummu"a shekaru na marasa yawa rayuwa tayi kwallo dani
yarda take so,lokacin da nake buƙatar mahaifiyata bata kusa dani,haka na rayu cikin kaɗaici da
rashin uwa duk da yarda mahaifina ke ƙokari wajen ganin ya cike mun wannan gurbin,"
Gidan Aurena dukka bani da sa'a ,banyi tunanin zanji ina san Imam ba har haka amma na
yarda da Allah Ya bani wannan kaddarar tawace ta hanyar faranta min,ummu bana so Aurena
yayi failing shiyasa Nana ko sameera babu wanda zai zaman min matsala a abunda Ya shafi
zamantakewa ta daki ko mijina,
Ummu bana san ki saka kanki kan abunan saboda Nana nada babban iko akan Abbu ,shiyasa
bana so ni nazama matsalar Aurenki na shekaru da kika gina,
Insha Allah ni nasan yarda zan zauna da Nana har da kanta zata sama Aurenmu Albarka .
Kama hannunta ummu tayi tana petting kafin ta jawota jikinta ta rungume tana Mai jin hawaye
na zubo mata dan shes very emotional ,"Allah yayi maki albarka Ya saka maki albarka cikin
gidan ki,sannan ni ki ɗaukeni mahaifiyar da baki da ,zan cike maki wannan gurbin ,kar kiyi ƙasa
a gwiwa wajen zuwa ki sanar dani damuwarki."
Bayan tabar sashen Nana kai tsaye sashensu tayi tana Mai jin kwarin gwiwa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 15