work To do
cos zan je consulting room And i know you wont mind being beside me saboda kallan ka kawai
make me aroused ,
Dariya yayi wadda sound ɗinta kawai ke fita kafun yace "you have no idea cos im sure you'll be
the dead of me,.
Knocking ɗin da akayi a kofa ne Ya katse musu little moment ɗinsu,
Juyawa tayi tana Mai gyara jikinta yayin da Ya matsa a bakin kofar yana Mai buɗewa,Dr
maryam ce,kallan sa tayi lokacin da yake mai matsa mata gefe ta wuce,murmushi yaɗan mata
ganin irin kallan kurilla da take masa,
Bayan fitarsa still Shi take bi da kallo,gyaran murya umaimah tayi tace "Dr maryam he's My
husband incase you forget, "Ƙaramar dariya tayi tana mai zama tace "Dr Bulma wallahi ke Mai
sa'a ce ,OMG he's just hot wanda sai da kika Auresa ma ya sake fitowa,
Sosai umaimah ta tamke ranta tana Mai bala'in jin haushin Dr maryam kafun tace"na tabbata ba
kinzo bane dan kiyi discussing hotness ɗin mijina ba ,get to the point saboda ina da abunyi,"
Murmushi Dr maryam tayi tace"ayi haƙuri ,Allah Ya huci zuciyarki,but Its just a fact ,and yea
nazo ne dama kawai na gaishe ki sannan na miki godiyan cupcake Its so tasty musamman da
Ya fito daga daddaɗan hannun Amarya,GOD ,ni kaina na ƙosa nasamu wani ɗan achan achan
a yan INTERN Ɗin nan na Aure and seriously ina da ido akan Kabir Ashir ,da gaske nake kuma
cos naga abokin mijin ki ne,"
Wani irin kallo umaimah ta bata cos bata tuna kusanci har haka tsakanin su ba ,dariya
ƙarama tayi tana Mai ƙare mata kallo ,ta kasa yarda har yanzu akwai shameless mata,telescope
ta ɗauka da system ɗinta haɗe da wayanta tace"zaki iya zuwa ki sameshi kilan ki samu guri and
please take your eyes off my husband inda Kina so mu zauna lafiya ,cos akansa zamu iya
samun matsala babba musamman idan Kina ogling akansa ,tana ƙokarin fita ta jiyo muryar Dr
maryam na faɗin"rude bitch ".
Da mamaki ta juya tace"excuse you?"Is that suppose to be mine?
Cikin haɗe rai Dr maryam tace "kinji da kyau ai,just because kinyi using charm ma Paki kin aure
sa ba shine yake nufin kinfi kowa ba da zakina faɗama mutane magana anyhow",i never like
you ko kaɗan,always thinking highly of your self kina tunanin kinfi kowa a cikin asibitin nan,
you're just a piece of shit and a user.
Da ɗumbin mamaki umaimah take kallan ta cos in thousand years to come bata tab'a tunanin
wai Dr maryam maƙiyiyar tace ba.
Tashi Dr maryam tayi ganin fuskar mamakin dake kan fuskar umaimah,ita kanta taba san
abunda yazo kanta ta faɗi abunda ta faɗa ɗinba,kwashe tayi da dariya tana Mai dafa umaimah
tace "Im only joking wasa ne 'fa and kalla har kin ɗaukesa serious ,i was rehearsing Wani abu
ne,dama na daɗe ina san ganin reaction ɗinki,
Dafata tayi tace "sense of humour ɗinki kadan ne, "
Kallan hannun umaimah tayi kana ta kalle ta tace"take off your hand off me and get out from
My sight."
Sake magana Zatayi umaimah ta katseta tasake faɗin "ki fita nace maki maryam i dont wanna
loose my cool cos trust me you wont like this rude bitch worst attitude ,".
Batare da tace komai ba ta fice a office ɗin tana dana sanin sakin bakin ta,duk da abunda ta
faɗa ɗin haka take ji akan umaimah ,kawai tana washe mata baki ne amma deep down tasan
Irin Tsanar da da hassadar da take da ita wanda tasan ba ita kaɗai bace musamman kuma
yanzu da tayi wuff da young rich and hot INTERN Ɗin da suke da ido akai .
Bangaren Paki kuwa yana fita gurin KB Ya nufa yana Mai jinsa kamar babu wanda Ya kaisa
samun farin ciki,zama yayi kusa dashi ,rufe system ɗin da yake dannawa yayi yace mutumina
Ina cikin farin ciki fa wane aiki kuma zaka yi bayan ka rufe komai ka saurareni,
Kallansa KB yayi yace "mutumina yarda kake jin kan nan naka nima fa Ina san naji kaina
haka,kaga yarda kuwa kayi wani mulmul Kana wani faman sheƙi,?"
Allah da gaske nake dan Allah ku bani Afnan 'dan Wallahi na muto mata ba wai Kaɗan ba,
Dariya Paki yasa yace "well mutumina Ai kasan maths ɗin,wallahi indai ka samu soyayyar
Afnan mun baka mu Ai abun muyi farin ciki ne."
Shafa gefen fuskarsa yayi yace"well tace na nemi yardar Hammanta dama nasan bani da case
da kai cos wallahi maza na mutu fa,Bansan haka kaji da ka faɗa tarkon kauna ba sai da kibiyar
san Afnan Ya harbeni,dafe saitin zuciyarsa yayi yace"wayyo Allah na Hamma imam,
Duka Paki Ya kaimasa yace "dan iskan banza ,ka cigaba Paki zamuje Chan mu samo mata miji
a ƙyauye...."
Mijin tace!!
A tare suka juya dan ganin Mai furucin,Aisha shareef ce ta ƙaraso da murmushi ta ,guri ta samu
ta zauna tana sake faɗin"mijin tace da abokinsa,"Na same ku lafiya,
Ango baka da kirki koma dai nace abokinka ,nayi nayi Ya Kaini gidanka amma yaƙi,ɗazu kuma
sai gaka da madam ɗin ka Kana rike da Jakarta.
Ƙaramun murmushi yayi dan Ya fuskanci Ina tayi,gyara zamansa yayi yace "Allah sarki"Ai ni
nan da kike gani nan kafun tace ne,da ido ma idan ta kalle ni nasan Mai take so,and mata da
yawa abunda suke nema kenan ,to tawa matar kuwa ta samu ba boka ba malam kawai tsantsar
ƙaunacce,ke nifa hatta ke kallan KB nake maki tunda na samu umaimah,sannan gobe a bayana
kilan zaki ganta,gidanmu kuwa da Kinje Ai Inajin abunda zakice kuma ba'a magana dan zai
mutukar dameki.
Yana jin Kb na zungurarsa yayi shiru amma yaƙiyi dan dama ciki yake da ita ,tana san shiga
masa hanci da gudundune.
Dan tab'e baki tayi tace"ni kake ma kallan kato imam?"
Kada kai yayi yace "gardi ma kuwa."
Tashi tayi tace ni wasa nake maka amma idan kaji haushi kayi haƙuri.
Faɗada fara'asa yayi yace "nima Ai wai bafa 'dan kiji haushi na faɗa ba amsa ne kawai na
baki".
Batace komai ba tabar gurin kallansa KB yayi yace amma dai kai shegen kaya ne mutumina
,that was deep,
Tab'e baki yayi yace"Ai shi baki idan yasan abunda zai faɗa baisan Mai za'a dawo masa dashi
ba tawani zo kamar tsuntsuwa,yen yen yen ,haba."
*
A ranar ba umaimah ta basu lecture ba haka nan dai Ya gama yasa kansa busy cos yasan
idan yaje gurinta bazai barta tayi aiki ba ,
Bayan sun tashi a Aiki a tare suka fita yana Mai mata complaining yunwa yake ji,dubawa tayi
taga 6 na yamma,
Ɗan harararsa tayi tace "yanzu hubby maine Ya hanaka cin abinci,"Dan turo bakinsa yayi
yace"sabo da abincinki mana ,"
Murmushi tayi tace shikena muje gida cos Inajin saboda kai dole zan fara yin abinci Ina sakowa
a kula Ina tahowa dashi asibiti and da zamuje mu taho da yaranka ne amma tunda kana jin
yunwa muje gida ,
Dan tapping sitiyarin motar yayi baice mata komai ba har suka hau kan titi,
Maimakon taga sunyi hanyar gida sai taga sun ɗauki hanyar gidansu,ita kaɗai take smiling cos
sosai ta yarda Paki na san yaranta fiye da komai,
Cikin shigar bashi labari tace "beb kasan wani abu?"
Yau na sake yarda idan mutum zaiyyi abu kawai yayi ba tare da damuwan abunda wasu zasu
ce ba cos mutane are just fake,a fili zasu nuna suna sanka amma deep down da za'a basu
wuƙa kai zasu fara dab'awa,Its just sick,
Labarin abunda Dr maryam ta mata ta bashi,yar dariya yayi musamma part ɗin KB kafun shima
Ya bata labari Aisha inda a ƙarshe yake faɗin"aikuwa Dr maryam ta makara 'dan KB dai Afnan
yake so,
Da murnarta tace "GOD and sunyi matching fa,Allah dai Ya tabbatar da abunda yafi Alheri,a
haka suka isa suna hirarsu cikin nishaɗi"
Baki ɗayan su suka taho dasu harda shatu,surutu kawai Nadiya ke zuba masa yana biyeta har
suka isa gida.
CHUCHUJAY ✍🏽
Tbc.
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU
(a hospital romance )
By chuchujay
wattpad :@chuchujay
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j
Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.
Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,
Just follow and share ❤
Episode4⃣3⃣➡4⃣4⃣
TWO MONTHS LATER.
Jin alamun ana mata tafiyan tsutsa a tafin kafarta kamar a mafarki yasaka ta buɗe idanunta a
hankali tana tunanin ko Abdallah ne 'dan tasan hallayyarsa ce,
Tashi tayi zaune tana tunanin 'dan bazan dukan da Zatayi masa cos taga alamun bai daddara
dukan da yasha a gurin ta ba da safe,
Cike da bala'in da take ji a yanzu tace "Abdallah you're trying me again ba,"
Ga mamakinta kuma sai taga ko ina na ɗakin dim sannan babu alamun mutum a gurin,ɗan tsaki
tayi tana tunanin irin jarabar da Za tayi ga Paki idan Ya shigo gidan cos tun 10 ta kwanta da ta
gaji da zaman jiransa ,maganar abinci kuwa yanzu tama daina jiransa ,muddin bai dawo da wuri
ba zata saka abincinta ne taci ta rabu dashi,
Wayanta ta jawo taga 11:59pm,
Ƙwafa tayi tace "Baby you're dead ,kazo gidan nan ka sameni,bari ma na kulle ɗakina idan ka
dawo Ai kana da ɗaki zamu haɗe da safe,"
Saukowa tayi a kan gadon tana Mai saka takalmin da ke bakin gadon ta nufi kofar 'dan kullawa
,tana saka key ta juya dan komawa taga ɗakin baki ɗaya Ya ɗauki haske ,tsaye yake bakin
switch ɗin hannunsa ɗauke da balloons guda biyu,bin ɗakin tayi da kallo taga ko ina is well
decorated da roses wanda hakan Ya bata amsar inda take jin kamshin rose,
Daga jikin bango an rubuta HAPPY 30 WIFFY da decorated shining Papers,
Hannu tasa ta rufe bakinta tana Mai jin wasu hawaye na zubo mata lokacin da yafara Takowa
yana Mai faɗin"Happy birthday to you,Happy birthday to you,"
Takowa yayi gabanta da balloon ɗin a hannunsa wanda yake daure jikin wani box Mai kyau
,buɗe box ɗin yayi yaciro wata diamond chain siririya Ya zo daf da ita yana Mai faɗaɗa
murmushin sa Ya maƙala mata a wuya,
Kafun tace wani abu Ya jawo wani envelope Ya miƙa mata yana Mai faɗin "Happy 30 wiffy,"
Washe baki kawai take kamar wata wawiya kafun ta buɗe envelope ɗin da zumuɗin dan ganin
menene cikin ta,
Paper ne guda biyu ta ciro,a hankali tafara karanta na farkon ,property ownership ne na asibiti
Mai suna UMAIMAH PRIVATE HOSPITAL,
Da mamaki take kallan paper kafin ta buɗe ta biyu Mai ɗauke da yarjewa na lasisin Buɗe
asibitin,
Kallansa tayi tana Mai san saita kanta da kuma tabbatarwa da kanta abunda take
zargi,realization ne Ya dake ta lokacin da ta tuna ya karbi Blue print na asibitin ta ,sannan duk
lokacin da tayi masa maganar asibitin zaice mata ta bari tukunna wanda cikin yimasa biyayyah
ta bari ɗin,
Rungumesa tayi tana Mai fashewa da kuka tace "Baby dont tell me this,"
Shafa kanta yayi yana Mai kissing saman kanta yace "yes wiffy asibitin ki Ya kammala da duk
wani abu da kike buƙata a cikin sa abu kadan ne Ya rage ,im just Happy cos na samu na
mamaki wannan birthday surprise ɗin da nake mutuwan san na miki,
Raba jikinta tayi da nasa tana Mai kallan cikin idanunsa kafin ta taba Chain ɗin dake wuyanta
tace "Bansan wane Aikin lada ba nayi da yazama Allah ya mun kyautar ka,
Imagine wannan babban gift da ka bani wanda ban maka ko kwatankwacinsa ba da birthday ɗin
ka ba
Mai zanyi idan babu kai?
Mai zanyi na saka maka na faranta maka?
Hannunsa yasaka ya shafa cikinta yace"wane Ya faɗa maki baki bani kyauta Mai
muhimmanci ba,kyautar da kika bani tafi komai muhimmanci a rayuwata ,sannan yana ɗaya
daga cikin kyauta mafi girma da aka Tab'a bani,
Aurena da kikayi umaimah kyautace da Allah yayi mun babban bayan kyautar rayuwa da
lafiya,sannan mayar da yaranki nawa da kikayi shima gagaruwamar kyauta ce da kika mun,
Dan ɗukawa yayi yace sannan kuma gashi nan rabona a jikinki,
Mai kuma nake nema nikam a rayuwa bayan nayita kasancewa Mai yin kaunar ki da kuma yiwa
ubangiji ɗumbin godia,
And yes kafun na manta abinda zaki mun daya ne yanzu da nazama broke Kina buɗe asibitinki
Ya zaman nine employee na farko i want to work under you.
Sake rungumesa tayi tana Mai dariya cikin kuka tace "Allah Ya saka maka da Aljanna
mafificiya sannan Ya bani ikon faranta maka ta ko ina mijina,"Sake rungumeta yayi yasa
bakinsa dai dai kunenta yace "ɗan fara faranta mun tun a yanzu mana Masoyiya ,cos yunwar da
nake ji a yanzu taki ce,"
Dan dukan kirjinsa tayi tace"nasan baka ci abinci bama ,bari naje na sake maka warming,"
Sake matseta yayi a jikin sa yace "ni bana wani Jin yunwa i told you naki nake ji feed me baby,
Smooches tafara bashi a wuyansa kafun kuma ta bari tana ɗan kallansa tace"hey ina goruba
ta,"
Ɗan bude baki yayi yace *oopz yana mota kinga na manta ko?
Bari naje na ɗauko maki,
Ya juya zai fita ta kamosa tana Mai kashe masa ido ɗaya tace "'dan baba yanzu ba guriba yake
so ba ganawa yake san yayi da daddyn sa so come here,
Licking lips ɗinsa yayi Ya ƙarasa gareta yana yin sama da ita.
*******
Cikin Abubuwan da suka faru a watan shine tashinsu daga gidan su Paki suka koma gidan
da Paki Ya daɗe da tanfatsa mata wanda aka kashe maƙudan kuɗi akai da idan ka kalla zaka
fara tunanin anya babu taimakon mahaifinsa?
Abun guda ɗayane wanda paki baya wasa da, duk kuɗin da yake samu gurin mahaifinsa
kasancewar shi ba mutum ne Mai shashanci ba,
Baya shaye shaye sannan baya neman matan banza,kuɗin kuma da yake samu daily
bukatunsa sun masa yawa cos yana da mahaifinsa for wanann sannan ga hamma osama ma
Ya cigaba da b'atasa 'dan haka yayi tunani Mai kyau wajen saka kuɗaɗensa a kasuwa wanda
ko mahaifinsa da yake jin abubuwan da Ya mallaka yayi mamaki sannan yayi alfahari dashi ,
Kuɗinsa na iyalinsa ne 'dan haka yayi ƙokarin fara gina masu mahalli,
Yasan cewa babu kuɗin da zai nunawa umaimah Ya burgeta ,amma 'yaci alwashin hanata
kashema kanta da yaranta kuɗi muddin yana dasu cos Alhamdulilah yana da kuɗin,A cikin
gidan ko wanne yaran da ɗakinsa ,hatta Nameer da bai zo ba lokacin da suka koma an gyara
masa ɗakinsa da duk wani abu da zaya buƙata idan Ya dawo haka zalika gurin shatuh wadda
Paki Ya ɗauka kamar ƙanwarsa ta jini ,
koda Nameer yazo yayi Tunanin bazai ƙarbesa ba duk da yasan da Auren amma ga
mamakin kowa sai gani sukayi wani irin bond na shaƙuwa Ya hab'aka tsakaninsu ,
Shaƙuwa tsakanin sa da yaran baki daya bazakace wai na umaimah ne kaɗai ba,
Soyayya kuwa babu irin wadda Umaimah bata samu gurin Paki abun sai wanda ya gani duk
da kuwa dama zaman Aure zo mu zauna zo mu sab'ane amma sabanin nasu Mai irguwane,
A lokacin da paki yasan umaimah na ɗauke da cikinsa kamar zai zuba ruwa a ƙasa yasha
'dan hatta Abbu baiyyi kunyar faɗawa ba 'dan a yanzu sun gama sanin akan umaimah Ya daina
jin kunyar kowa,
Duk da cikin umaimah rigimammen cikine hakan bai taba sawa Ya sare da ita ba ko Ya nuna
mata gazawa ba Illa ma wata sabuwar ƙauna da yake nuna mata da kulawa wanda a cikin
asibiti ma har sun haƙura da gulmar,
Akwai ranar da ta tubure masa akan abincin baƙar mace take sanci ,kuma bana kasuwa ba a
dangi take so,haka nan yayi tabi karshe sai da Ya samu abincin bakar mace wanda tana loma
ɗaya tace bata ci,shi abun ma dariya yake basa .
*
Washe gari tana tashi da safe ta tashesa tana Mai shafa masa kwantaccen sajensa,yana
farkawa ta ɗaga masa gira ɗaya tace"Good morning Baby ,"
Cikin sexy hoarsely voice ɗinsa na safe Ya shafo fuskanta yace "morning Baby Mai ɗan baba
yake so,"
Murmushi tayi na salan rigima tace "to 'dan baba dai yau Ya tashi da wata sabuwa dan wai
tuwan shinkafa yake san ci miyar kuka,sannan wai 'fa kasan wa yake so Ya tuƙa?"
Kaɗa mata kai yayi yana Mai kwanto da ita kan kirjinsa yana Mai shirya rigimarta yace "sai Ya
fada da bakin maminsa".
Ɗan turo baki tayi tace "to wai dai na tsofaffi yake so kuma fa wai tsohuwarma Nana,"
Dagota yayi Ya zaunar da ita yace"wiffy Nana kuma?"
Haɗe rai tayi tana mai turo baki tace"bazan samu ba kenan ?"
Shikenan koƙarin sauka take a gadan idanun ta na kawo ruwa,Kamota yayi yace"oh come o'n
mana matan Paki,Mai zai hana ki samu?"
Kawai dai kinsan rigimar Nana ne yanzu ina Nana ina tuka tuwu,?
Goge kwallar dake zubo mata tayi tace"Allah Hubby ni dazan iya cirema kaina da na cire,ji nake
idan banci tuwan hannun Nana ba kamar zan mutu".
Saurin miƙewa yayi yace"bazama ki mutu ba ,yanzu brush kawai zanyi naje yau Nana taga ta
kanta".
*
Koda Ya isa gidan baki ɗaya yagansu suna breakfast,
Zama yayi bayan Ya gaida iyayen sa inda kannensa suma suka gaidashi,
Kallan Nana yayi wadda tunda ta amsa gaisuwarasa bata sake cewa komai ba ta cigaba da cin
abincinta dan tunda suka bar gidan take jin haushin su,
Kallanta yayi bayan Afnan tayi masa arranging plate yace"Masoyiya Mai yayi zafi Haka nan
naga kinata faman haɗe rai".
Murguda baki tayi tace"share ni ɗan nan,bana san kinibibi da neman ayi ,"
Shafa kansa yayi yace mai yayi zafi lailata ta,?
Haɗe rai takuma tace ni majnuni yana kasa ,Sannan shikaɗai yake da damar kirana lailah,
Lailarka na gida wadda ciki Ya fitowa a fuska.
Sai da yabi shaho yabi muzuru kafun Ya faɗi abinda Ya kawosa,
Miƙewa Nana tayi tace"kutmarkata'in nan,ni zan tuƙa tuwo da miya?"
Muntari kana ji ko?
Ɗankwalinta dake kanta ta kunce taci ɗamara tace "to wallahi koni ko umaimatu,wato rainin har
yakai nan ko?"
Dole kazo kana kaɗa wuya kamar jangwalagwada saboda zaka zageni,to wallahi ahir ɗinku sai
'in mata shegen dukan da zaisa ta haihu wata biyu baku shirya ba,bani da mutunci 'fa,nima
kwalluwar kaina ce,
Taci na habiba mana ko muntari Ya tuka,amma dayake nice karkataciyar kuka Mai daɗin hawa
dole a hauni,to a dakeni na tuƙa,
Dariyar da Afnan ke rikewace ta ƙwace ,
Kanta Nana ta koma tace "naci uwarki yanzunan shegiya Mai Kama da mujiya ,wuya kamar
mariƙin lema ,to wallahi nafi dalma zafi,"
Tana ƙoƙarin wucewa dakinta imam yayi saurin zuwa Ya kamo kafafunta yace"wallahi Nana da
kaina zan shiga kitchen ɗin na taya ki, nayi alƙawari,"
Da kyar da tsomawar bakin kowa na gurin Nana ta yarda ta shiga kitchen ɗin inda Ya bita yana
tayata yana kunshe dariyarsa musamman datana tuƙa tuwan,diban albarka kuwa babu irin
wadda Umaimah bata sha ba.
Lokacin da ya kaimata tuwan sai cewa tayi Ai ɗan baba Ya fasa ci,
Dariya Ya fashe da ita yana Mai hango reaction ɗin Nana idan tasan cewa umaimah bataci
wannan tuwan da Nana tayiwa laƙani da tuwan Alaƙaƙai ba.
*****
Sauranku last page oo🥱🥰
Zanci tuwan Nana dan Allah.
Chuchujay ✍🏽
Tbc.
AURE UKU
(a hospital romance )
By chuchujay
wattpad :@chuchujay
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j
Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.
Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,
Just follow and share ❤
FINAL EPISODE.
Jeka ka dawo Imam paki yake a bakin theatre room na Queen cleopatra Hospital dake
ƙasar misra yana Mai shafa fuskar sa a hankali,
Kallo ɗaya zakayi masa kasan cewa yana cikin tashin hankali wanda ba'a sawa rana.
Dafa sa Ummu tayi tana Mai faɗin"Imam kazo muje ka zauna dan Allah tun ɗazu kake abu daya
komai zai zama dai dai da ikon Allah ,Addu'ar mu bazata faɗi kasa nan ba Za'ayi aikin nan
lafiya,"
Hannunsa ta kamo ta zaunar dashi kafun ta buɗe ruwan gora ta miƙa masa ,
Babu musu Ya ƙarba ya daga a bakinsa Ya sha Mai isarsa kafun Ya sauke ya kalli Ummu cike
da damuwa yace"Ummu sun jima 'fa har yanzu shiru,"
Ganin yarda Ya ke cikin mutuƙar damuwa ne yasata fara bashi baki a hankali tana kwantar
masa da hankali.
Ji yake kamar Ya tashi Ya shiga ,tsinewa rashin samun licence ɗin sa yayi cos da ace yana da
shi da babu wanda Ya isa Ya hanasa ko tsayawa ne yayi akan matarsa ,
Dalilin zuwan su misra umaimah ta takura akan ita Chan take san haihuwa tun tana da
sauran wata ɗaya ta haihu,
Bai yi mata musu ba ya yarda da zuwan nata duk da bai samu sun wuce tare ba saboda
kammala medInternship ɗin sa wanda dole dole yasa shi tsayawa ganin yarda ta nace akan Ya
tsaya ɗin she will be okay musamman hindu na tare da ita sannan ga Afnan Ya haɗasu tare.
Satin ta biyu a garin Ya kammala abunda zaiyyi Ya bita .
Kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa wannan ciki ba abu ɗaya ke cikinsa ba ,ille kuwa
scanning ɗin farko aka ce musu Twins ne wanda murna gurin Paki ba'a saka mata rana,siyayya
kuwa da yayi kamar bashi da mafaɗi ,
Ciwo sosai ta fara da yaje tana Mai yan ƙananun naƙuda dan haka Ya tatarata suka koma
asibitin su hindu baki ɗaya wanda suke ta kulawa da ita kamar su maida ta ciki,abunka da
larabawa,
Yarda take nakudar ja da ja yasa da aka dubata suka tabbatar masu bazata iya haihuwa da
kanta ba dan babies ɗin sunyi girma da yawa sannan ciresu shine kawai zai tsallakar da uwa da
yaran,
Babu musu Paki yasa hannu inda suka tsaya a washe gari zasuyi aikin dan haka yakira Ummu
Ya tada mata hankali dole tayo takakkiya ta taho.
Suna wannan zaman jiran tsammanin Hindu ta fito tana Mai washe baki tace"Ummu,Imam
Congratulations,"
da saurinsa Ya tako inda take yana Mai faɗin"Hindu matana fa?"
Murmushi tayi tace "ka kwantar da hankalin ka baban uku ,matar ka da yaran ka suna cikin
koshin lafiya,"
Washe baki yayi yana Mai faɗin"Alhamdulillah ,Allah na gode maka,zan iya ganinsu?"
Shiru yayi lokaci guda kuma yana san tuna abunda tace cike da mamaki yace "yara nawa ma
kikace?"
Sake faɗaɗa fara'arta tayi tace "yara uku ,kai da umaimah kun samu triplet .
Da saurinsa Ya koma ga ummu yana Mai hawayen murna yace "Ummu Kina ji ko,
Wai yara uku 'fa,
Shafa gefen fuskarsa ummu tayi tace "naji imam,Allah Ya baka kyautar da ba kowa yake bawa
ba,
Alamu tayi ma da Hindu akan tazo,babu musu ta tako gareta,rungumeta tayi tace "ki zabi duk
kasar da kike san zuwa honey moon nan da sati uku idan an ɗaura maki Aure da Ahmad ,ko
Mai da kika sani zaku buƙata is on me na kwanakin da zakuyi ,shine tuƙuicina ,
Sake rungume ummu Hindu tayi tana mata godia kafun paki yace "na baki kyautar kujerun hajji
guda biyar ,kiyi yarda kikeso dasu now tell me ina matana da yarana ina san ganinsu, .
Murmushi tayi tace "an shiga dasu ɗakin hutu ta back door amma zaku iya shiga amma 'fa
bata farfaɗo ba,"
Kafun ta kuma cewa wani abu Ya nufi ɗakin da suke,
Kwance take idanun ta a rufe tana bacci yayin da hannunta ke ɗauke da drip,
Kamar Mai sanɗa haka Ya ƙarasa gareta Ya zauna a kujeran dake bakin gadon ya shafa gefen
fuskanta a hankali kafin ya sumbaci goshinta Ya furta "Thank you Wiffy,Allah na gode maka
daka bawa matata damar kaiwa wannan stage ɗin,wasu hawaye ne suka fara zubo masa a
kuncinsa yana Mai jin tsananin santa a cikin ransa yana masa yawo,"
Goge hawayen yayi da sauri jin Ummu da Hindu sun shigo tana Mai faɗin"Amma Hindu inace
yan biyu ne cikin ta".
"Eh ummu girman da sukayi sosai guda uku ne guda ɗayane Ya boye a gefen kafar ɗaya
wanda ba'a gani ba,amma ni nafi mayar dashi da ikon Allah wanda babu wanda Ya isa yayi
masa shishigi akan sanin maine a ciki,dama yana bamu dama ne muga abunda yaga dama
,yanzun ma hakan ya faru,cos Snr Dr ɗin ma da yayi Aikin bakiga yarda yake mamaki ba ,
Gasu nan mata biyu namiji ɗaya ,".
Sai a wannan lokacinne Imam Ya isa ga yaran nasa ummu na miƙa masa yana masu addua
yayin da idanunsa ke ɗauke da hawayen murna wanda shi kaɗai yasan yanayin da yake ji,
Suna fa?
Ummu ta tambaye sa bayan Ya aje su,
Murmushi yayi yana Mai riƙe da macen dake mutuƙar Kama da umaimah yace"Ummu bamu
yanke shawarar suna ba cos mun bari sai munga abunda muka samu ,and kingani yanzu muna
ma tunanin biyu amma uku nema sannan wannan damar na bawa umaimah Ummu matsayin
ƙyautarta ,ita zata zabi sunan da take so"
Murmushi ummu tayi tana Mai jin dadin yarda Paki Ya samu kyauna da kwanciyar hankali a
tattare da umaimah.
Koda labari Ya isa nigeria ba ƙaramun murna suka shiga ba da samun wannan gagarumar
kyautar a dangi karma ace kakanin dake bangaren iyayen yaran,
Hajiya Nana kuwa kamar ta jiƙa kasa ta zuba a ƙasa tasha dan murna 'dan rigima ta tayar akan
sai taje misra amma Abbu Ya tausheta akan suna sallamarsu zasu dawo ,dole ta haƙura.
Koda umaimah ta farfaɗo kamar imam zai cinyeta saboda murna da nuna mata tsantsar
godiya da kaunarsa,
Tsokana kam yashata gun Hindu wadda ko a jikinsa dan idanunsa sun riga da sun rufe.
Bayan sati guda suka koma nigeria wanda suka tarar ana jiransu da gagarumar tarba,
Iyalan na Bulama da Paki kowa ka tab'a da alherin da zai maka saboda tsantsar farin cikin da
suke ciki,
Kyautar yara uku a lokaci ɗaya Ai abun ka motsa aljihune duk maƙonka.
Ranar da aka ware domin raɗa ma yaran suna yara sukaci suna ,FAWHA,FAWZA sai
namijinsu FAWZAN,
Taro ne akayi na zo a gani 'dan duk wanda Ya hallarta sai ya tabbata da anyi haihuwar yaran
gata,Su Nadiya kuwa ji ake kamar an masu kyautar Aljanna .
A lokacin da ta fara Nursing yaran Asibitinta wanda ta chanza masa suna zuwa UMAIMAM
PRIVATE HOSPITAL ta damƙa a hannun Paki wanda yaƙi karban position ɗin da take san bashi
na founder ,Ya faɗan mata dream ɗinta ne
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 15