Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 *𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔* 𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠 Story & written by *FATIMA AMINU* *Ummu Saddi'q* chapter 1️⃣ "Wayyo Aunty Mamana! wayyo Aunty Mamana!! wayyo Aunty Mamana!!! za a kashe miki ni dan Allah Babban Yaya kayi haƙuri",belt ɗin hannun shi yaƙara naɗawa yana ɗagawa sama aka riƙe,ƙanƙame ido nayi amma naji shiru a hankali na buɗe ɗaya a kanne naga Aunty Mama,sutalewa nayi na miƙe ta bayanta na ƙanƙameta na saki kukan ƙarya"kai yanzu Habib miye abin duka jikin Nana kalli yanda ka naɗa belt kamar zaka daki Saddiq ko Ashiru",ajiyar zuciya ya yi yana lumshe kyawawan idanuwan sa akaina ya buɗesu dan yana ganina ina kallonsa duk da na ɓoye kaina"Aunty Mama kinsan me yarinyar nan takeyi alayi,sun fa taso islamiya wai ta tsayawa koyawa wasu yara rawa a kan hanya","kaii Babban Yaya"na faɗa ina tsaida kukan iskancin dana ke"ƙarya nayi kenan","a a ni bance ka gilla ba kawai dai ka gyara zancenka kace Dj ake na tsaya koya musu dan basu iya ba",dariya ce ta kama Aunty Mama"amma dai kasan Nana yarinyace ko ai ba dukanta zakayi ba faɗa zaka mata","haba Aunty Mama shekara sha ɗaya ne yarinya kullum ana taɓata kice yarinta sai yaushe zata girma","zata girma mana nan gaba kaɗan",maida belt ɗinsa jikinsa yake yace"ma gani ai girman wannan ai akwai matsala ciki","ba wata matsala kai dai jeka",yana fita na fito a bayanta kunne na ta kama ta murɗe"kinga Nana kiyi a hankali da Yayanku wataran zai yanka miki dukan da zaki kasa bacci",ƙanƙance ido nayi"to Aunty Mamana","muje ki cire wannan uniform ɗin kuma in ki ka bari Maman ku tasamu labarin abinda kikai to in shi bai dake ki ba ita ta zaneki",ɗage nayi na rufe ma ta baki"wai kiyi shiru dan Allah karma taji kinsan kamar dangin macizai take gun ji",kama bakin tayi"Nana ina rabaki da kiwon kyalla kina akuya ta haihu",dariya maganar ta bani na shiga ƙyalƙyalata"in tambayeki Aunty Mama ance ita ta haifeni amma meyasa bata sona yanda ki ke yi",dariya tayi"ba sonki ne batayi ba wannan rawar kan naki ne bata so",taɓe baki nayi na ɗaga kafaɗa"barta kawai muje kimin wankan","Allah ya shiryeki Nana","ameen Aunty Mamana". Rashin jina bai tsaya a iya haka ba kullum sai na jawo magana an kawo ƙarata amma da zarar za'amin hukunci sai Alhaji Baffa ko Aunty Mama wani ya tare, wannan yasa bama shiri da Maman mu daga harara sai ranƙwashi ke shiga tsakani na da ita nida Babban Yaya kuwa bana yadda ma mu haɗa hanya bare sahu. Ƴan gidanmu muna da yawa amma ba wai iya ƴaƴan Babanmu ba,family ne mu Baban su Babban Yaya shine Babba a gidan su sunanshi Alhaji Aminu amma Allah ya masa rasuwa yaransa goma sha uku kuma kowa na nan amma Babban yaya ne Babba a maza kaf familyn mu sai yayunsa mata akwai Aunty Hasiya da Aunty Mabaruka sai Aunty Aisha ƙanensa mata da yawa akwai Aziza, Maryam, Khadija,Nabila da dai sauran su sannan maza Hashim,Isma'il,Ibrahim,suma dai akwai wasu,sai Abban mu Alhaji Haruna amma anfi saninsa da Baffa,mu goma ne yaransa nice ta takwas duk sun girmeni sai ƙanina, yayuna biyar mata biyu maza ɗayan shine ƙanina matan,Fatima Asma'u,Usaina,Lubabatu,Amina,Saddiq sai ni sauran ƴan ɗakin Aunty Mamane,Ashiru,Ruma da Abdulkarem muna kiransa ƙarami,kuma suma su Baffa da mahaifi da mahaifiyar su,Baban su sunan sa Alhaji Abdulkarem amma anfi saninsa da Alhaji Baffa mahaifiyarsa kuma Hajiya Aisha amma muna kiranta Iyyo saboda masifarta son ungo shi yasa take masifar ƙaunar Babban Yaya amma tace kaf sauran ƴan mata suke kaiwa kuɗinsu dan bataga suna bawa iyayen su ba,mijinta ya fita sauƙi saidai magana ɗaya yake baya ta biyu, sai ƙannen Baffanmu huɗu Kawu Rabilu,Yaransa huɗu biyu maza Kamis da Sadis biyu mata Sumayya da Ruƙayya,Kawu Ibrahim yaransa nada yawa ga ƙananu sosai harda na goye amma acikinsu akwai Kamal Abduk aziz muna kiransa da Abdul sai Aisha da yake masu sunan muna da yawa Humaira muke kiranta da dai saura da yawa,Kawu Nuhu ɗansa ɗaya Haruna kuma mahaifiyarsa ta rasu ta gidan ba ita ta haifeshi ba kuma bata haihu ba itama sai dai tana da kirki amma sauran matan to akwai masu mutuci a ido,sai gwaggo Asama'u Yaranta huɗu,Aisha Zainab,Fatsima da Khadija duk mata ne amma fa bata da kirki ko kaɗan duk wannan abin zaman lafiyar gidan mu ke basu haushi dansu sun kasa zama lafiya saboda kishin juna da suke,amma Mama da Aunty Mama bama ka banbance ƴaƴan su dan dukkansu akwai kyau kuma farare Baffa ma fari shi yasa halittun gidan mu sai kallo,duk da sauran ma haka suke,musamman gidan su Babban Yaya dan Umma buzuwar chadi ce kuma iyayenta can yankin larabawa suke,Alhaji Baffa mutumin Nigar ne cikin tsantsar sahara amma sauran akwai sirki saboda aure aure da mazansu suke. Mama sunan ta Halima shuwa'arab ce ƴar chadi macece ita mai zafi shi yasa kaf gidan ba mai wasa da ita saima yanzu da jikoki suka fara tasowa dolenta tasau fuska,nice dama mai janta kuma cin ubana take,kamar dama hali yasan wuri Abba da Mama halinsu guda wallahi komai kamar haɗin baki suke yi dashi duk da ba zama yake ba, haka Aunty Mama sunan ta Halima,bafulatana ce sosai dan in tana yarensu saika ɗauka a ruga take,macece ita mai haƙuri da kirki haka ƴaƴan ta dan ta iya tafiyar da kowanne marajin magana bama ya ni nunamin soyayya da take yasa aɗakinta ma nake kuma ita kaɗai ke cewa na bari na bari nan take amma ko Babban Yaya sai mun kwafsa nake bari,zaman Mama da Aunty Mama abin ba'a cewa komai,ance harshe da haƙori ma ana samun saɓani to su suna sarrafa nasu bana ce na taɓa jinsu suna faɗa ba ko da hararar juna ne. Baffa mutum ne shi mai aƙida ɗan ahalussunna dan haka baya wasa inaga kamar dama ansan hali aka haɗa shi aure da Mama sai dai fa akwai kirki ya banbanta da sauran ƴan uwansa sukam sai a hankali wallahi kodan dama ba'a fara rayuwar birnin ba da wuri ba oho musu daga su har ƴaƴansu suna da matsalolin gaske,kaf ɗin mu alayi ɗaya muke saboda filayen Alhaji Baffa ne ya mallakawa kowa shine suka gina,mu ba masu kuɗi bane amma muna da rufin asiri gashi Baffa na aiki staff ne shi a companyn Fanta haka su Ya Saddiq duka suna aiki shi yana ma lagos,a tsarin kaf familyn du wata kowa da abinda zai aje tunda suka fara aiki kuma ba'a taɓa samun matsala da gidanmu ba sai dai sauran shi yasa suke shan zagi wajen Iyyo bata ragawa ɗa bare iyayen su dama sunfi shiri da Umman su Babban Yaya dan goya Iyyo ne kawai batayi amma har yanzu ita ke ma ta wanki ta mata kitso,shi yasa duk su Ya Ruma, Ya Aziza da Ya Mero kenan suke shan zagi tace basu iya komaiba sangartattu basu iya komai ba sai ɗinki da ɗaurin zoɓo,iyakarsu suce ma ta ai shima sana'a ce. vote share comments Sisters Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂ 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 *𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔* 𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠 Story & written by *FATIMA AMINU* *Ummu Saddi'q* chapter 2️⃣ Bayan shekara biyu na ƙara girma akan na da muna tsakar gida Ya Ruma namin kalba dan kaina baya kitsuwa,Babban Yaya ne ya shigo"My Life"fincike kan nayi na tashi da gudu tunkan ya ƙarasa shigowa na bisa bakin ƙofa,rungumeshi nayi"gani nan My Life",riƙoni ya yi muka shigo ciki kaina ya shafa kitso ake miki",girgizawa nayi"ok jeki a gama kizo ki rakani wani wuri"da sauri na cikashi naje na zauna kamo hannunta nayi na ɗora akaina"cigaba kinji yace unguwa zamu",kallonsa tayi Ya Ruma tayi tana dariya"Babban Yayan mu sai ina kuma kaida Life ɗin taka yau an shirya kenan","Eh to munshirya yau zance zata rakani","kai amma ina murna an samo mana Yaya kenan",murmushi nan da yake yi da ƙyar yasakar ma ta"an samo muku amma ba yanzu ba auren sai nan da shekara biyu dai dai da naku nima zanyi","shike nan Babbabn Yaya Allah ya sanya alkhairi ya kaimu lafiya",galla mata tsunkuli nayi"nidai kimin kitsona sai zuba ki ke kamar famfo ya lalace",ba shiri sukai dariya,nan ya wuce "ku gama bari naga Mama"gashin taja"wallahi ki kiyaye ni Nana ko na miki mara kyau kalli yadda ki ka tsunkule min fata","to yi haƙiri","au haƙiri ma zanyi",dariya nayi ma ta"to yi haƙuri",ƙwafa tayi ta cigaba. Ƙofar ɗakin ya ƙarasa"Assalamu alaikum Mama","amin wa'alaikumul salamu Habibu shigo mana",shigowa ya yi yana durƙusawa"ina wuni Mama","lafiya lau Habibullahi ya Umman naku","tana lafiya tace a gaisheki","ina amsawa zauna mana",cikin sadda kai ya zauna"baiyi magana ba saida ta kalleshi"Habibu yadai ka ke ta murmushi,ƙeyarsa ya shafa"dama fita zamuyi da Nana ne zata raka wurin yarinyar da nake ɗan neman aurenta","to shine saikazo ka tambayeni ai kaima ƙanwarka ce gatacan ta tasa Ruma wai saita ma ta kalba ƙananu irin wanda ake yowa asabon gari",ɗan murmushi ya yi kumatunsa ya lotsa","ai Nana akwai daru Mama",baki ta kama tana jijjaga kai"na fitar hankali ma dan ma uwar ta ta yau bata nan ai da yanzu gidannan yana nan kamar an kunna radio","ohh Aunty Mama bata nan","eh taje Dutse ana bikin ɗan ƙanin babansu shi can yake zaune da iyalansa","ok Allah ya dawo dasu lafiya","amin"...ɓurun na ban kaɗo labulen"Darling Yaya an gama","ok muje to",dakatar shi Mama tayi"kai Habibu tsaya kalleta fa ahaka zaka fita da ita,kee wuce ki watsa ruwa kisa wasu kayan",kafim Mama takai aya nakai uwar ɗakanta dama akwai bayi ciki wanka nayi da sabulu ba zancen fita danma fatar ba nunwa take ba,mai kawai na goga na zaƙulo rigar da aka ɗinka min kwanaki ta atamfa na zura na rasa mayafi na buɗe wajen kayan Mama na ɗakko ɗan kwalin abayarta na fito sai sauri nake","Kaiii Darling sis kinyi kyau",goshi Umma ta dafe"amma da alama makaho ne kai ko kalli yadda take ƙyalli kamar ta shafa mangyaɗa amma kace wai tayi kyau kee ƙyallari wuce muje a goge wannan man",tusani tayi agaba zuwa ɗakin wani towel ƙarami tasa ta goge min man tas sannan ta shafa min powder ta naɗa min gyalen duk saukar da ya yi saida kitsona ya zarta shi haka ta barin na fito,baki ya kama"ba magana yanzu Darling sis"Allah ko Darling Yaya muje to",miƙewa ya yi dai dai Mama na fitowa kansa ya duƙar"muntafi Mama","a dawo lafiya agaishe da ƴar tamu,kuma kayi a hankali da wannan karta bada kai a wurin mutane",ƙafa na fara bugawa aƙasa"niɗin niɗin","ke ɗin nasan ba'a abin arziƙi dake ne"tarar maganar ya yi"yau zatayi Mama",zama tayi" to gaka gata ai"fitowa mukai nasa takalmina halfcover baƙi yama ƙafar ɗas,fita mukai tacan ɓangaran Iyyo mukabi zai ɗauki mashin ɗinsa,tun daga nesa take kallonmu muna ƙarasowa tace"su kayya da kulla ina aka nufa kuma",hararar ta nayi"wallahi Iyyo kin fiya sa ido","in bansa ido ba hanci ki ke so nasa kaji min yarinya",dariya nayi Babban Yaya ya yi murmushi danshi dariyarsa ta siyarwa ce baya wa kowa ita,"kisa idonki Iyyo zance zan raka Sweety Yaya"haɓa ta riƙe tana taunar goro,"Kai Habibullahi yanzu da wannan zabayar zaka wurin budurwa salon ta razanata",zabura nayi"kambala'i Iyyo nice zabaya ko dayake bana ji haushi ba ai kalar mu guda daga suna har fata da jiki",haɓa ta tare da bayan hannu"Allah ya rufan asiri nayi kala da shawara kalleki fa muddin kaje da wannan sai kowa ya gudu","saboda ga dodo ko to budurwar ma in batai min ba canjata za'ayi ko Darling Yaya",numfashi yaja"zancenki haƙƙun Baby","kinji ko dan haka kisa saɓa tsohuwa","fata zansa dan uwaki Halima ƙarama ayi dai mugani in tusa zata hura wuya ku wuce kuban wuri ni kin dameni","mun tafi tsaffuwa ta tsaffo ni innai tusa bawuta zata hura ba gobara zata haddasa","to kaji dai kai Deli sai kai hankali karta soya ka",murmushi ya yi ya matso kusa da ita ya rage murya"ai Iyyo indai ita zata soyani ba matsala",hangame baki tayi tana ɗora hannuwanta aka"kai yau ina ganin rayuwa ku tafi ku bani wuri",dariya mukai ya kama hannuna muka wuce ina ma ta gwalo,kai ta girgiza"kai Allah ya shiryeki Nana kaima ƙato da kai Allah ya shiryaka",mashin ɗinsa lifan tsuntsun soyayya muka hau tun daga gareji muka fito tare dama yasa baƙin glass ɗin nan mai tsorata yara bai tsaya kula kowa ba muka wuce ina kallon yaran gidan Kawu Iro na hararata damasu akwai gulma. Munyi tafiya mai nisa sannan mukazo wata unguwa,unguwar sabuwace gidan da muka tsaya mai mugun kyau babba dashi a bakin gate ɗin yay parking sannan ya ƙwanƙwasa megadin ya fito,yashe baki ya yi"a a Alhaji ne ka shigo mana ya zaka tsaya anan",kama hannuna ya yi muka shiga sai kallona mutumin yake kamar zai faɗi,fakar idon Yaya nayi na galla mai harara ina zaro mai ido,saurin ɗauke kai ya yi yana musmus da baki bangane dai me yake cewa ba,har wajen wasu kujeru ya kaimu"Alhaji bismillah bari na kira Hajiyar",ya juya da sauri zuwa cikin gidan,zama Babban Yaya ya yi na zagaya bayansa na ratayo wuyansa na kwantar da kaina akan wuyansa,hannu ya miƙo ya shafa fuskata"lafiya dai ko","lau Yaya barni a haka","dama nace ki sake ni ne",ɗan murmushi nayi,dai dai wata murya na sallama,ɗagowa ya yi yana amsawa,kujera taja tazauna yana yanga"Habibina sannu da hanya","yauwa ya ki ke","lafiya a a da baƙuwa kazo min ne",sai a sannan na juyowa da kaina gareta"ina wuni","subahanallahi Habibina ina ka samo wannan"kasaƙe mukayi muna kallonta dan bamu gane ina zancenta yasa gaba ba,lura tayi bamu ganeba sai ta kamo hannuna dake wuyansa"naganta kyakykyawa ne",murmushi ya yi"ƙanwata ce",gabanta ta tsaidani kamar me neman wani abu a jikina take ƙare min kallo janye hannuna nayi na koma gabansa na rike mai hannu,gefensa ya maida ni na kwantar da kaina a kafaɗarsa"ya makaranta Hajara",fari tayi ta ido tana gyara wuyan riga cikin iyayi","lafiya lau Habibi amma wannan ƙanwar taka bata da yarda ko","ba wani rashin yadda tsabar salo ne wannan botsararriyar kece dai kikai sa'a abin bezo takanki ba",ƴar dariya tayi"a kabar min ita mana zuwa anjima kazo ka ɗauketa",kafin takai ayar maganarta na ɗago har gyalena na faɗuwa,gashina ta kallah"kai Habibi ƴar ƙanƙanuwa da ita kuke ma ta ƙarin gashi",murmushi ya yi yana kama kitson,cikin idona yake kalla"Hajara wannan gashin real ne haka ƴan gidan mu suke musamman ma ƴan gidan su",wani dam ƙirjinta ya buga nan da nana taji tashin hankali na shigarta inta fahimta yana nufin ba ƴar gidansu bace waro ido tayi"badai itace Nana ba","yauwa kin fahimta kenan itace Nana RUHIN YAYAN TA",wani kallo ta masa shi baima san tanayi ba maganar daga zuciyarsa take fitowa zuwa sarari ganin baima san me yake faɗaba,yasata barin zancen tai murmushi kawai ta bara abin a haɗuwar jinine dan yarinyar bata yarwa bace"amma Habibi maganarmu fa",ido cikin ido na kalleta amma hararar ta nake da kula da kyau,kansa na koma da shagwaɓa"ni bazan zaunaba gida zan tafi zanje islamiyya fa in na makara yasayyadi ba tausaya min zai ba cuwaɗa ni zaiyi","ok ƙanwarmu na fahimta sai ku tafi tare"shiru nayi ina kallon wani wurin,hirar da bansan kanta ba sukeyi shammatarsa nayi na galla masa mintsini,saurin gyara zama ya yi "kai kai kika tsunkuleni","to ka tashi mu tafi bakaji ana kiran la'asar ba in naje makaranta a latti dukana za'ayi",na ƙarashe kamar zanyi kuka saurin tashi ya yi yana gyaramin mayafin kaina,kallonta ya yi"zamu wuce Hajara banaso a daketa",ƙugu na kama kai kace wata sa'ar su ce"kamar gaske Darling Yaya kaimafa lakaɗata ka ke kamar jaka","eh mana in ban lakaɗeki ba so kike ki girma asangarce in kasa tanƙwara ki",kamar wadda ta gane me yace nace"naji dai muje",saƙare tayi tana mamaki kamar ma ya manta tana wurin,wannan sunan kumafa wai Darling Yaya,shine kawai ya tsaya ma ta arai",kama hannuna ya yi yana juyawa gareta"munwuce Hajara ki gaida ƴan gidan",numfashi taja"ku ɗan tsaya ina zuwa",ta wuce ciki ba jimawa ta dawo ɗauke da leda"ga wannan ƙanwata ki gaida mutanen gidan",karɓa nayi"nagode",nan ta rako mu har waje muka hau mashin ɗin muka wuce gida. vote share & comments Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂ 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 *𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔* 𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠 Story & written by *FATIMA AMINU* *Ummu Saddi'q* chapter 3️⃣ Ciki ta koma amma ta rasa ma wane tunani zata yi har yayarta ta lura da ita gyara zamanta tayi ta janye littafan gabanta ta kira sunan ya"lafiyanki kuwa Hajara",ajiyar zuciya taja tana gyara zamanta"wallahi sis ko wani abu ne ke damuna nama rasa wane mataki zan ɗora abin","tohh wane abu ne wannan kuwa","ba nace miki Habib yazo da wata ƙanwarsa ba","eh hakane","to gaskiya da ƙyar in ɗakinsu ɗaya a yanda yake nunawa,dan yarinyar nan kamar tana da wani babban matsayi a cikin rayuwarsa","to shine me ko ɗaki ɗaya ko ba ɗaki ɗaya ba saime,naji kince yarinya nasan dai bata kaiki ba ko?","kaini kuma sis bafa tafi shekara sha biyu ba ko sha uku","mitss shine kika bi duk kika ɗaga hankalinki dama yara ai sun gaji haka dole akwai wanda yafi wani haɗuwar jini a ƴan uwansu komu anan gidan ai hakane kinsan dai mu ba'a mana kishiya dan haka ki nutsu kawai ammanko aurenshi ki kai saikina ja baya da ita sannan a gabanshi kina nuna ma ta mugun so zakiga ta rage shiga jikinsa da kanta hikimar hakan saikin shiga gidansa zaki sa ni",wani ɗan ihu tayi"kaii amma nagode wallahi da narasa ina zan saka kaina",wani irin juya kai tayi na ƴan duniya"ai in kika shiga duhu ki nemo mu zamu feto dake cikin haske",tafawa sukai"to shike nan ai na ɗau haske,bari naje zamu fita da Mommy","ku dawo lafiya"ta tashi ta fita. *** Muna shigowa layin a ƙofar gidansu ya tsaya da gudu na sakko na shige Umma na wanki na ɗane bayanta"oyoyo Ummana"dariya tayi tana ɗauraye hannunta ɗagowa tayi tana riƙoni"yanzu na aika akira min ke akace kun fita da yayanku","Eh Umma zance mukaje","lallai to sannunku ina yake shi","Assalamu alaikum gani nan Umma me zaki bani","uwaka zan baka dama Yusuf ne yazo nemanka"kan ya yi magana nayi"Umma ga tsarabar nan ki cinye na tafi insa uniform lokacin islamiyya ya yi","a a tsaya kaiwa ƴan gidanku ai naku ne ni banacin waɗannan abubuwan kin sani kai maidata inda ka ɗakkota",kansa ya dafa,na dubeshi"baka da lafiya Babban Yaya",hararata ya yi ,nayi nace wa Umma"to Umma na tafi in kinyi murjin taliya zanzo na karɓa","to shikenan ki gaida maman taku",hannunsa na kama muka fito a ƙafa muka ƙarasa,da Ya Ashiru muka haɗu saboda jan magana na kalleshi"kai Yaya wallahi wannan wuyan rigar ya yi girma telan baima iyaba",kama baki ya yi ya tsaya yana kallona,hannu ya miƙo zai kamani"saina daka ki wallahi"hararar sa Babban Yaya ya yi"kai barnan","Allah Babban Yaya","to agaban nawa zaka duketa",wucewa ya yi yana ƙwafa"ai zan kamaki ne zai tafi ai",gwalo na faki idon Yaya na masa"wato gwalo kike masa ko ke kin raina uban kowa ko","Allah Babban Yaya ban raina kowa ba kawai wasa nake","saiki dage wataran wani yasaki jinya ai ko",dai dai muna shiga gidan da sallama,Mama ce ta amsa suna zaune a baranda da baƙuwa,"sannu da gida Mama","kun dawo Habibu","eh Mama gata nan zata tafi islamiya","to taje tasa kayanta dan yaran duk sun wuce ita kaɗai ta rage"suna magana na fito,ko takan ledar dana aje agaban Mama banbi ba"Darling Yaya ban biyar","biyar saikace wata ƴar tsana","goma to","gadai ashirin kiyi maza karki tsokani kowa","na maka alƙawari kuwa Babban Yaya","to aje","na tafi Mama","adawo lafiya",nayi waje da sauri"Mama na wuce sai anjima","to shike nan Habibu Allah ya kaimu",ya fita wannan matar kamar idonta zai faɗo sai kallonsa take da gani munafurci na cinta ne dama dillaliya ce an ƙware awannan fannin. Bata cewa Mama ƙala ba dan tasanta bata yadda da irin waɗannan maganganun na gulmar wasu, kayan da zata siya kawai ta ɗauka sannan ta bata kuɗinta dan su Mama basu yadda da bashi ba. Daga nan gidan bata wuce ko ina ba sai gidan Gwaggo Asama'u tana ganin ta fara washe baki dan basu da maraba dama gun gulma,wurin zama ta kawo ma ta sannan ta kawo ma ta ruwa,kujera ƴar zuƙunne ta jawo ta zauna"Hajiya Tasalla dama ana ganin ku",ruwan da take ƙyanƙyama ta aje tai gyatsa"gamu kuwa Hajiya Asama'u ya gida ya yaran da me gidan",wani taɓe baki "yara na nan shima yana nan" ya kasuwar fa","kasuwa gata da kyau ga kayan sabon ɗauka ki kwasa na kaiwacan gidan ƴan uwanki duk sun kwasa","oho saida ki ka kai musu suka ɗiba sannan zaki kawo min sauran","kwantar da hankalinki mana ba saura na kawo miki ba naki daban dama na kwasa harda ƴan matan ma na kawo musu humra ta musamman","ato shike nan miƙomin su na zaɓa",tana kwasa ne Tasalla ta kalleta gulma na sakatar ta"bakiji ba Ma'u","ina jinki Tasalla da tsegumine","Babba ma kuwa nace

Chapter 1 of 32