duniya da lahira","to mungode yanzu kina da mane mi","a a Alhaji kowa guduna yake","ba komai amma zaki auri duk wanda na kawo miki",sadda kai tayi cikin kunya ta kaɗa kai"shike nan waye yasan gidan ku anan gidan","daga Aunty Babba sai Murtala","shikenan jeki amma tsaya ta kawo miki saƙo ki kai gidan naku",tana ta godiya yaja hannuna muka wuce tana binmu da kallo,muna shiga ya wuce wajen locker ya jawo ta saiga uban kuɗi a ciki ya za ra sannan ya miƙo min"kai ma ta"banyi mamaki ba ko na tsaya tambaya na karɓa na kawo ma ta hannunta na rawa ta karɓa sai zuba godiya take ta tashi ta fita kamar zata kifa,kaɗa kaina kawai nayi na wuce da gudu na ƙarasa na faɗa kansa"kai Babban Yaya kai ɗin na daban ne"rungumeni ya yi yana sumbatar bakina"to miye amfanin kuɗin sabida irinsu Abba yabar min kuɗin",hancina na shiga goga masa a fuska"Allah to ya haɓaka ta ta ninka haka sau malala gashin tinkiya",zaro ido ya yi"sai muyi ya ya da ita kuma","muyi ta rabawa mutane mana","haka ne to yanzu ya za ayi kenan wa ki ke ganin za'a haɗata dashi aure agidan nan",zugum nayi ina kallon fuskarsa"kaga dai mu a yanzu a gidajan mu ba bu wanda ya isa aure kuma ba za'a yiwa ƴan uwana kishiya ba sai a ma'aikatan gidannan ka nemi wani,yauwa ga Muryala ko Sabitu",murmushi ya yi yaban hannu muka tafa"Sabitu bai daɗe da aure ba amma Murtalan zamu tuntuɓa ko tare ma zamuje amma sai da yamma zamu bakin get neman aure ko",dariya na shigayi yana bina da kallo hannauwana ya haɗa ya riƙe"komai ki kai kyau yake miki tawan",kumatunsa na riƙe ina jijjigashi"kaima haka Sweet Yaya",kwanto da kaina ya yi jikinsa yana shafa bayana da haka na koma bacci shima haka.
Babu jimawa da kwanciyar mu sai ta tashi ita kuma wanka tayi tai sallah ƙarfe goma dan iskanci,wasu ƴan iskan kaya ta saka rabi sutura rabi tsirara ta dawo falo ta zauna dama yau ba ai break ba tun jiya tacewa Sadiya kar tayi dan haka tea kawai ta hala dama ya kawo kayan snacks su ta ɗauka taci ta ƙoshi ta ware kiɗa tana sha.
Munfi awa biyu muna baccin sannan muka farka a tare banyi sanyar komaiba na sauya riga zuwa iya gwiwa silki ce dan haka komai nawa ya fito ba ko ɗan kwali zan wuce kitchen na ganta kwance tana kaɗa kai"Hiii" na faɗa ma ta na wuceta tashi tayi,kutumar wannan yarinyar ita zata gaisar a haka wato jiya ganin idon mijinta ne yasa ta nuna ma ta ladabi hunnm zata riƙeta ne,ta maida kanta ta kwantar,sai gashi yafito cikin suit ash colour sun masifar karɓarsa ido ta zuba masa kamar zata cinyeshi dan ya tafi da ita,a kusa da ita ya zauna ya ɗau remort ya kashe kiɗan da yake shiri take nema sai batai magana ba ma ta shiga gaisheshi ya amsa yana kallon ƙofar kitchen ɗin sannan ya kalleta ya kalli flat da cup har biyu sai ya kalli dining baiga komai ba kaɗa kai kawai ya yi wato tana sane tai hakan kamar zai ma ta magana sai ya barta ya manna ma ta hauka dan ita kanta ta zata zai yi magana da baiga break fast ba a dining.
Ni kam arish na fere na soya sanna na soya ƙwai mai albasa na gasa snacks ɗin daya kawo na haɗo tea mai kayan ƙamshi cup biyu na ɗakko a babban tire na fito da sauri ya taso ya karɓa yana kallon me nayi daɗi ne ya kamashi ya aje a nan ƙasa ya jawo hannuna ya zauna dani ba wani sanya ya shiga bani abaki"ci da hannuna na jinjina miki"dariya kawai nayi na ɗaga ma ta hannu ta gabzan harara na janye idona akanta har muka gama tana binmu da kallo da kansa yakai kwanukan kitchen ya dawo"zan fita ni bayin Allah",da sauri na miƙe"adawo lafiya Babban Yaya Allah ya tsareka ya kare min kai a duk inda ka ke","ameen ameen Nana",ya juya ya fita nazo wuceta ta makan harara na shareta na wuce,ɗakin na gyara tsaf sannan na dawo na zauna ba jimawa na fito falon na wuce kitchen na fara haɗa me zan dafa rasa me zanyi nayi kawai na hau dambun kuskus dana akwai komai a gidan hayaniya naji ban kula ba dan nasan da alama baƙi tayi nafi awa biyu ina abu ɗaya sannan na gama na jiye a babbar coler sannan na fito zan wuce zuuuuu suka min da ido ta tafasa bance musu ba na wuce wata ce daga ciki tace"Hajar ashe a shema kishiyar taki ƙwaila ce",shewa sukai suka tafa tace"gata nan dai abin basu nuna ba amma a haka ake nuna min ansan komai kuma anyi komai",wallahi harzan kulata sai nafasa nayi niyar wucewa ɗaki naji sallamar Ya Rumana da gudu nabtaho na rungumeta"oyoyo Yayata",itama oyoyon take min na karɓi kayan hannunta ta ƙarasa shigowa"baƙi kukaita faɗa tana kallonsu cikin murmushi mugunta na dubesu nima nace"eh Ya Ruma ƙawayen Aunty Hajara ne gasu nan komai ya nuna amma basu kai inda za'a mora ba",wani irin juyowa sukai suna bina da kallo dai dai da ita ƙawar tasu ta kasa magana har muka wuce Ya Ruma na ƙunshe dariya dan ta lura kamar ramuwar gayyace tafi ta gayya zafi,muna shigewa ɗaki auka juya suna dubanta"ke dama wannan yarinyar haka take bata da mutunci",dakatar da ita ɗayar tayi"wallahi kome ta muku ku ku ka tanka dama wannan a fitsarun da ganint bazata bar kota kwanaba",su samu suyi maganar amma ɗayar ta hanasu dole sukai shiru,akan sofa Ya Ruma ta sauka tana faɗin "wash","sannu Ya Ruma ɗan nan namu na gaskiya yana gasa ki","soya ni dai Nana ni kaɗai nasan me nake jikina buɗe ga kayanki nan blander ku dai na niƙa komai ko","eh kusan kai bakwai ne da ita","to shikenan yanzu kwaso ta da kayan aikin ki muyi abinmu anan"to,nace na wuce ta gabansu basu tanka min ba na ɗakko abinda tace na dawo a nan ɗakin ta haɗa komai ta juye min a babban bokiti nasa a frig sannan na kawo ma ta kayan motsa baki muka hau hira dan tace bazataci abinci ba,har akai la'asar muna tare sai bayan ta ta tafi amma baƙin Aunty Hajara na nan,ban kulasu ba na wuce ciki na shiga wanka na fito na shirya cikin riga da siket na atamfa kamar ajikina aka ɗinka su nayi kwalliya na baje gashina a bayana na sha humra mai tada hankali na fito bina sukai da kallo suna dariya"maga me za'a shiryawa mijin bayan mun cinye abincin"ta tafasa bance musu ba na wuce abina cabinet na taka na ɗakko coler dana ɓoye dan tabbas saida na aiyana za ai min haka fitowa nayi da ita da kifin dana soya shi dama a locer nasa ban bari inda za'a gani ba,baki suka saki ganin ina shirya abincin kallon juna sukai ni kuwa sai waƙa nake "anzo gidan ƙawa an wuni",harare harare suka shiga yu,ba jimawa sai gashi ya shigo sallamarsa naji na fito da gudu daga kitchen na ɗaneshi da sauri ya riƙeni yana dariya"saiki faɗi Nana",murmushi nayi na ɗora goshina akan nasa"muddin kana kusa nasan bazan taɓa kaiwa ƙasa ba",dariya ya yi abinda basu taɓa gani ba ƙawayen mamaki ne ya kamasu sauka nayi na kama hannunsa"zo muje kaci abinci nasan yunwa ka ke ji kayi wanka daga baya","yanda ki ka ce tawaje na",har dining na kaishi ta tafasa baice ma ta ba ita da ƙawayenta fitowa nayi zan ɗakko ruwa naji sunce"anya kuwa wannan kishiyar taki yarinyace ni ban yarda yarinya bace bata shekare a ciki ba kuwa sannan aka haifeta",a fusace na juyo ina ma ta kallon baza ita mai maganar nace"shakaruna arba'in a ciki sannan aka haifoni kinga yanzu shekarun mu ɗaya dake kenan harma da Aunty Hajaran",a hautsine ta miƙe tayo kaina"nice shekara arba'in ɗin a gidan uabanwa nayi kama da me shekarun nan","haba Aunty Hajara kinyi mana komai naki fa na ƴan da ne ko baki luraba kishin na ƴan 1939 ki ke"wani irin dunƙule hannu tayi nai ma za na ture ƙawarta na gudu wajen Babban Yaya na ɓuya,kallon ƙawayen nata tayi"ku fitar min nan jakai kawai",haushi ne ya kamasu suka ɗauki jakunkunan su suka fita,ɗaki ta wuce kamar zatai hauka,fitowa nayi a bayansa ina dariya kai kawai ya kaɗa"Allah ya shiryeki Nana","ameen Babban Yaya"abincin ma ɗaki nakai naja shi muka gudu.
******
UK
Dama Hajiya Fulera tasan mutane masu yawa a UK hakan yasa ta tura kuli maƙudai aka sama ma ta muhalli acan kosa ta isa bata sami matsalar komai ba.
*****
Hajiya Harira kuwa ai sun zama kamar mahauakata sai kuka da dana sa ni take amma su Hajiya Salma damuwar su bata kai haka ba dan su suna da kuɗi kuma ƴan harƙalla ne amma ai wadda ta kwasa ta wajensi ko kaso ɗaya bisa ɗari batakai waccan ba,amma ba yanda suka iya sai dai su sukasan me suke ji a zukatansu.
Da magariba da Babban Yaya mukaje bakin get muka sami Murtala yana ganin mu ya taso"rankai daɗe sai ina","wurinka mukazo","to rankai daɗe Allah yasa ba laifi nayi ba","bakai komai ba kana da aure kuwa",baki ya kama"ina dashi yallaɓai","to zaka iya ƙarawa in na maka matar","da gudu ma kuwa rankai daɗe","madalla ɗan ina ne kai","Gezawa yallaɓai","ok to kasan yarinyar nan mai Hajara aiki Sadiya","eh yallaɓai","to gobe zamuje ka nemi auranta kafin muje garinku mu faɗawa ƴan uwanka",zubewa Murtala ya yi a wurin"nagode nagode yallaɓai","tashi mana sai goben"mukaar wurin sai godiya yake.
UMMU SADDIQ 🌹🌹🌹🌹
😀😀😀😀
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
27
Daddare Alhaji Baffa yasa aka kira masa su Hajiya Harira sai kuka take har zazzaɓi ya kamata,da yara huɗu an mata haka ta shiga uku ina ta kama ba uwa ba uba,kwantar musu da hankali ya shiga yi amma ina saima abin ya yi kamar turasu ake ba yadda ya iya haka ya barsu suka koma.
Iyyo kuwa ko a jikin ta dariya ma take musu,ta dubi Alhaji Baffa tace"wai riɗa riɗa dasu amma an musu wayo,ranar da za'ayi rabon abun kuwa nunawa kowa sukai kamar a kansu aka halicci wayo Hhhhhhhh",ta kwashe da dariya kaɗa kai kawai ya yi"har yau kina nan da halinki A'i","wallahi Alhaji abin ne abin dariya","to ai maganinsu kinga sun lura da duniya ko","hakane kam to Allah ya kyauta".
Daddare ko sau ɗaya bamu ganta ba saida ma na fito na haɗa tea ne naganta nuna ni tayi tamin alamar duka ni kuma na taɓe baki na shige ɗaki"ke kuma ke dawa ki ke taɓe baki",shagwaɓe fuska nayi na aje kofin na faɗa jikinsa,riƙe ni ya yi"kinga ki daina min wannan dirar girma fa ki ke",dariya ce takamani"Babban Yaya wallahi in kana magana kamar ba daga bakinka take fitowa ba",hancina yaja"ai za'a faɗawa haka wannan ɗan bakin naki bansan a ina ki ka koyi magana ba in ki ka sako zance sai na rasa me zance","ai bari kaji Babban Yaya niko in ina magana kawai ji nake tana zuwa tare da wani nannaɗaɗɗen rashin mutunci",dariya ya yi"ai naga alama kuwa ta wajena","Babban tea ɗin",ɗakkowa ya yi ya fara sha ina kallonsa"ya kai zaki sha ne",kai na ɗaga ya miƙo min,kafaɗa na kaƙale na nuna bakinsa,murmushi ya yi yazuba shayin a bakinsa ya kwanto da kaian ya ɗora bakinsa kan nawa ya juye min na shanye da haka yasha ya bani har ya ƙara zan tashi ya janyoni na faɗa gado ya kwanta kusa da ni zanyi magana ya ɗara bakinsa kan nawa ya shiga kiss na daban ƴar rigar ma jefar da ita ya yi ya hau murza ƙirjina cikin wannan lokacin ya kansa a wani yanayi da ranar ya jefa shi a wani hali da ƙyar ya samo kansa ni kuwa nayi bacci tuni,saida ya yo wanka sannan yazo ya sa ni ajikinsa ya kwanta shima bacci ya kwasheshi".
Washegari da farar safiya Mama ta aiko mana da kunu da waina naji daɗi sosai dan haka muna gama baccin safiya muka karya sannan na shirya muka fita ita hajiyar ma ko tashi batayi ba da Murtala mukaje har gidansu Sadiya ni na shiga sannan akai musu iso cikin gidan yasha mamakin gidan ginin har ya sauka kamar zai faɗo amma suna rayuwar farin ciki ba ruwansu,tunkan ya fara magana suka fara godiyar kuɗin jiya,ba komai ya faɗa musu sannan ya fara maganar da ta kawo sa,sunyi murna sosai kuma basu wani ja ba sukace ya turo sannan ya faɗa musu a gidan sa zata zauna ba'a ko ina ba,murna sosai da tsalle suka shiga yi sannan yace Baban su ya samo masu aikin gini a lissafa nawa za'a kashe a sauya ginin tunda gidansu ne in an gama lissafawa a faɗama Sadiya ta faɗa masa,kuka Baban yasa yana godiya da wannan muka fito sai shi mana albarka suke.
Nima a hanya kan kafaɗar sa na kwantar da kaina"Allah ya biya ka Babban Yaya","karki damu yiwa wani yiwa kaine bari mu biya ta wani wuri ki siyo kayan break fast saboda kinsan zan koma aiki kuma da wuri nake fita kinga kuma baa ɗkin ki nake ba kullum ko","hakane nawan muje",kaya sosai na ɗebo na girki sai mamaki yake a ina na sa ni wani glass na saida waya mukazo na turje ina kallon su sai yarfe hannu nake,kafaɗa ta ya riƙo"kina so ne",da sauri na ɗaga kai,zugeshi ya yi"ɗakko wadda ki ke so",da sauri na ɗakko wata kwankwaɗeɗiya mai cameras reras karɓa ya yi"tayi kyau muje",tsaywa nayi"Aunty Hajara fa","wa ya ce miki tana buƙatar waya wancan satin na siya ma ta wayar dubu ɗari uku taho nan",baki na kama"kai kuɗi har haka","eh mana Nana ai ba bu itace ɓarna","hakane kam to Allah ya rabamu da ita ya nesanta mu da ita","ameen ameen",kuɗi masu yawa ya biya a wurin sannan muka dawo gida sabon kitchen ware naje can ɓangarena na ɗakko nazo wani ɗan kwana na aje shi na jere komai akai,wayar ya haɗa yasa sim dama yana dasu sannan ya kunna ya miƙo min,ihu nayi na rungumeshi tare da kiss na godiya juyo da fuskata ya yi ya shigar da bakinsa nawa ya jima yana yanda yaso da dani ban hanasa ba,da kaina na rakasa toilet na haɗa masa ruwan wanka na fito na barsa duk bana jin daɗin barina da zai amma na share,yana fitowa ya shirya yaƙara fita,misalin huɗu na yamma ya shigo gidan Aunty Hajara ansha wanka cikin material ga kwalliyar aljanun nan da take tasha kuma nan har gida aka zo aka ma ta wai zata karɓi girki magunguna kuwa tasha bila adadin wai yaji ta sama dani,da sauri ta tashi ta rungumeshi bai gwasaleta shima ya rungumeta duk da yana kallona ban wani damuba ita da mijinta hannu na ɗaga masa"sannu da zuwa Babban Yaya",murmushi ya yi ya gane bazan taso bane,hannunsa ta kama zuwa ɗakinta sai dai ba'a saba ba da kansa ya yo wankan ba kayansa a ɗakin hakan yasa dolenta tabarshi ya fito,ina kwance kan sofa naji danshin ruwa a wuyana,ɗagowa nayi naga shine"lahh Babban Yaya ya ka shigo nan","ba kayana acan shine nazo wajenki ki saka min",zaro ido nayi"ka koma zan raba kayan na kawo ma ta nan ta aje amma yanzu kaje karta zargi wani abin",mamaki ya tsaya yana yi ta ya akai nasan waɗannan matsalolin amma baiyi mamaki ba ta wani wurin dan yasan aɓni akwai farin shige shige,baiƙi ta tawa ba ya fita ni kuma na tashi na fara kwasar kayan ina ajewa agefe sai naga bazan iya ɗauka ba sannan na danƙo su na fito ko gabana bana gani da ƙafa na doka ƙofar,suna ciki itafa yau mai miji sai shafa masa jiki take bugun yasashi yazo ya buɗe dan yasan nice,ba riga a jikinsa ta wani zo bayansa ta maƙalesa tsayawa ya yi yana kallon kayan kamar duka na ɗebo haushi ne ya kamani"Aunty Hajara ki karɓa mana ko ki matsa ya karɓa dan in suka zube ban ƙara ninkewa tabbas",harara ta tayi ta matsa konkunya bataji wai ita nan zata nuna min duniyanci ne tana taɓa shi na gani naji haushi,dariya ya ɓoye bayan ta matsa ya karɓa ni kuma na juya.
Da kansa ya shirya kayansa a sif tana kallonshi bata taya shi ba,bayan ya gama yasa kaya ta taso shi a gaba zuwa dining flat taja zata zuba mai abincin ya riƙe hannunta"bari na kira Nana tazo taci",a yanda ya yi maganar fuska ba walwala yasa ta bar zubawar ya tashi shi kuma,ina zauna da waya na rasa ma ina zan danna dan iya ba sama dariya da nake ta ma ta sai kace wani mutum,a bakin ƙofar ya tsaya yana kallona"sannu mai waya",ɗagowa nayi ina dariya"bari Babban Yaya na rasa ina zan danna",miƙo min ita nan na saita miki na baki wayata kuma ki kwashi numbers kamar hauka dan kowa ina number sa",da sauri na taso na kawo masa"to taho muje kici abinci",kafaɗa na noƙe"na ƙoshi ni sai dare zanci abinci","kin tabbata",kai na kaɗa ina komawa ciki shi kuma ya fita da wayar,wallahi yunwa nake ji sosai bana so naje saboda karna kashe ma ta karsashin da take dashi akan mijinta dan nasan tana ganina komai zai lalace ma ta ni kuma bana son na ɓata ma ta tunda a gidan ta nake duk da ita jawoni amma ba komai dai yana fitowa taga ba bu ni sai tayi murmushi yana kallonta amma ya share madadin ta tambaye shi sai ta yi shiru shima haka,saida yaci abincin sannan ya saita wayar ya shiga saka numbers yana savinga yanda zan gane,ganin hankalin shi ba ya kanta saita ƙwace wayar"zan fasa wannan wayar in baka maida hankalinka kaina ba","bani nan Hajara"tasan halinsa sarai saita miƙa masa ya aje yana kallon ta"ina jinki","ka taso muje ɗaki to" tashi ya yi ya bita yabar wayar a nan,basu jima da wucewa ba na fito ina sanɗa abincin na ɗiba na kwashe naman na ɗau lemo a hankali na koma ɗaki ahi kuma dawowa ya yi ya ɗau wayar ya ganni ina sanɗa kansa kawai ya girgiza a fili yace"Nana ba'a gane ina ki ka dosa lokaci ɗaya" ya ɗau wayar ya koma ɗakin dan ya lura yau a wurin Hajara ya shiga takwas ma ba uku ba.
Cinye abincin nayi na mayar da kwanon na dawo ina jiran waya amma shiru gajiya nayi babu shi babu wayar na taso na fito ƙofar na ƙwanƙwasa amma shiru na daɗe a wurin sannan ta buɗe ko kayan kirki babu a jikinta ni kuwa ba abinda ya daman na kalleta tsaf"me miji aban waya ta ko",tana wani goge goshi ta koma ta ɗakkomin shi kuwa gwanin ban gansa ba ma na karɓi waya ta nabar wurin,ƙwafa tayi taso ace naji haushin abin da tayi batasan indai nice ba tayi da dutsen dala Hhhhhh.
Ina zuwa na fara dubawa naga numbobi da yawa kira na shiga yi ina faɗar nayi waya sai murna ake tayani na ɗebo lokaci mai yawa ban gama ba ana kiran sallar magariba na tashi nayi anan na zauna da ƙur'ani na ina karatu har akai sallar isha ba jimawa da idarwa nayi bacci a wurin.
Hajara kuwa ta hana shi sakat bayan sallar isha yaje ya siyo abinda za'a ci amma tace ita zata kawo min bai hanata ba ya bata koda ta shigo ta gan ni ina bacci saita aje tayi fitar ta tace masa ta kawo ranar kam an sha amarci ni ina can ina bacci kamar matacciya baiyi tuanin banyi sallah ba saida ya dawo a masallaci rana ta fara fitowa sannan ya shigo"innanillahi"ya faɗa yana yowa kaina da sauri ɗagoni ya yi zuwa jikinsa"Nana kece a kwance a ƙasa kaicona wallahi",a hankali na buɗe idona da sauri na yunƙura"wayyo wuyana",na koma yadda nake ba shiri,wuyan ya dafe"sannu me yasa zaki kwanta a ƙasa"hankalin sa ne yakai kan ledar jiya"baki ci abinci ba ma",shagwaɓe fuska nayi"bayan daga sallar isha nayi bacci daka kawo abincin basai ka tashe ni ba",shiru ya yi cikin tsan tsar ɓacin raia yace"Hajara ta kawo miki kuma tace ta baki kin ma fara ci","ƙila a baccin ta bani",kaɗa kai ya yi"taso muje kiyi wanka ki gasa wuyan",da ƙyar na miƙe zuwa toilet ai shigo na hanasa kuwa na rufe ƙofar saida na gasa kamar yadda yace sannan nayi wanka da alwala na fito ɗaure da towel yama zaune gefen gadon nayi murmushi"au kana nan bakaje ka kwanta ba","kwanciya kuma zoki sallah ni muje ki ɗumama abincin ki kici",a gaban sa na shirya nai sallar ya taso ni gaba da ledar har kichen Sadiya na ta aikin ta tana ganin mu ta matsa tana gaishe mu"nifa Sadiya ki daina gaishe ni kinfa girmeni",dariya tayi"dole kuwa na gaishe ki ko yallaɓai","hakane mamana barta kina gaishe ta amma kaɗan",duk dariya mukai na yake tambayar ta masu aikin sunzo kuwa"eh sunzo ga takardar da suka ce a baka a kwai number wayarsu ma a jiki",karɓa ya yi"to ya yi saura ke me ake yi in za'ai aure koda yake kema ki lissafa ki kawo min takardar tunda ni ne Baban amarya in sai komai nawa da wuri ko Nanas",babban yatsana na ɗaga masa"haka yake Babban Yayan na mutunci",ba shiri sukai dariya ya yin da mamaki ya kashe Sadiya dama haka yake da sauƙin kai kodan yana gaban amarya ne,wani baƙauyen ashar mukaji bagatatan da sauri na ɗago kaina na kalli Aunty Hajara dan nasan sai ita shi kuwa ko motsi bai ba ya yinda jikin Sadiya ya kama rawa,ƙarasowa tayi tana wani kama ƙugu"mai aikina ce take hira da mijina saboda samun sake dan kutumar...",da hanzari nace"kai wallahi kar ki sa amana girgizar ƙasa salon a kifemu duka dan tayi hira da mijin ki miye gani dai ba taɓawa a sarar hannu",hannuwan ta ware tamin daƙuwa kamar wata ƴarta"ba komai Aunty Hajara kinyi sa'a da Yaya Hasiya miye dan kin zagen ai ni ƴarki ce",da gudu tayo kaina kamin kowa ya lura na shige ƙarƙashin dining ina dariya,shi ko kallon ta bai ba ma ya cigaba da maganar sa da Sadiya tana bashi amsa a tsorace maganar taso ta fahimta amma bata gane ta juyo garesu"me nake ji ne haka Habib",ina ƙarƙashin bencin na rigashi magana"aure zaiwa mai aikin kuma ku zauna gida ɗaya kinga gaba takaita ke kuma baya kuna aure gida ɗaya da mai aikin ki","zan kama ki Nana","in kin kamani ki soya ni",shiru tayi danta lura saina haukata ta inta biyemin,"Habib kaine zaka ma ta auren ina iyayen ta",bai saurare ta ba ya sakko a kan frig ɗin da yake"ina jiranki Sadiya","to yallaɓai nagode",dungure ma ta kai tayi"shi yasa ake cewa kar na ɗau ƴar aiki amma naƙiji",da sauri na katse ta"dama ki kai sa'a ke ba mijinki ta aura ba drivern sa ne","NANA"ta faɗa da ƙarfi,dariya na kwashe da ita ya yin da Sadiya ke ɓoye ta ta dan in ta yi ta taga banu,bazar bazar tabi bayansa zuwa ɗaki amma yana toilet taɓa ƙofar tayi tajita a kulle dole ta zauna zaman jiran sa,tana tafiya na fito na ɗauke abincin dana sa a oven da na ƙarasa haɗa tea ɗin sannan naba Sadiya cup"haɗa ki fece wallahi waccan matar in ta kama ki saita daka ki",dariya tayi"nagode ƙaramar Aunty","ki tsaya salo harta fito ɗauki ledar can ma za ki kawo na ɗiba miki wannan snacks ɗin ki tafi dashi",da sauri ta kawo na kwashe ma ta du na zuba ma ta madara da sugar da ovaltine nace"fece yasin dan na ma ta ɓarna"tana fita nima na gudu inata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 32